AMININ MAHAIFINA CHAPTER 8

AMININ MAHAIFINA







CHAPTER 8







Kalmar ‘Are You Ok’ kalma ce da nake matukar tsoro idan ina cikin halin damuwa. I am a very emotional person, shi yasa idan ina cikin halin damuwa bana son mutane a kusa dani saboda gudun su tambaye ni lafiya? Don zan iya fashewa da kuka, ni a gare ni tambayar are you ok kamar fama min gyambo ne. Yanzu ma sai da nayi iyaka kokarin da zanyi na danne kukan da yake kokarin barke min nace “m fine Abbu, kawai bana jin dadin jikina ne” ya kalleni kawai nasan bai yarda da abinda nace ba, ban ga laifin shi ba don yadda nake a hargitsen nan babu wanda zai yarda wai gajiya ce ta maida ni haka. Ya kalleni sosai kamar wanda yake so yayi magana sai kuma kawai ya maida kallonshi ga titi, a raina naji dadin hakan nasan tambaya daya zai kara jefo min zan fashe da kuka, kuka kuma ba abinda nayi niyar in ci gaba dayi bane saboda Muneer. Har yayi parking a parking lot din dept din Microbiology, na yunkura zan bude motar ya tsayar dani ta hanyar kiran sunana, na Juya a hankali na kalleshi. Idanuwan shi fes a kaina suke, naji wani slight rawar jiki kafin in sadda kaina kasa, muryar shi a sanyaye yace “akwai abinda yake damunki Nafeesah wanda kika ki gaya min and I wouldn’t force you to tell me, kawai ina so in gaya miki cewa komi na rayuwa sai da hakuri, koma menene yake damun ki kiyi hakuri ki dauke shi a ba komi. Idan ma wani abu ne kika rasa kike ganin kamar ba zaki iya hakuri da rashin ba kada ki manta Allah yana tare da Ke. Shi ya mana alkawarin canza mana abinda yake sharri ne a gare mu zuwa ga mafi alkhairin shi don haka ki roke shi game da abinda yafi alkhairi a gare ki ba kiyi holding into something wanda yake ba alkhairin ki bane kin gane?” na gyada kaina a hankali maganganun shi sun shige ni. Abinda ya kamata in tuna kenan a lokacin da naga hoton Muneer da amaryar shi jiya, abinda ya kamata inyi kenan ba wai in kira shi ba ina kara fallasa kaina da disappointing kaina, sai yanzu naga cewar hakika abinda nayi jiya ban kyauta ba, naji kunyar kaina ta kama ni har ma data Muneer din, ko da wane ido zan sake kallonshi kuma yanzu??. Nace “na gane Abbu nagode sosai, In shaa Allahu zan yi amfani da shawarar ka” yace “good” shiru ya biyo baya a cikin motar, can naji ya sake magana cikin whisper, kamar kuma wanda yake tsoron yin maganar, “anjima kuma sai gida koh?” na gyada kaina a sanyaye, barin rayuwar Abbu da iyalan shi!! Tunani ne mara dadi dake fadar min da gaba a duk lokacin da ya fado min a cikin raina don haka nake iyaka kokarina wajen ganin na kauda tunanin daga cikin raina. Na sake tsintar muryar shi yana tambayana, “da gaske zaki dinga zuwa kina mana weekend?” nace ehh, a cikin raina nasan fada kawai nake yi ba don zan dinga zuwa ba sai don kawai kada su dameni da tambaya. Kamar yasan abinda nake tunani, yace “da gaske kike ko kuma kina fada ne kawai?” shiru nayi wannan karon, yayi murmushi tare da kallona kawai yace na gane. Dash board ya bude ya ciro wata karamar jaka fara mai hannu ya miko min, na amsa fuskana dauke da alamun tambaya, yace “it’s a small thank u gift, thank u for staying with us Nafeesah, we enjoyed having u in our life and we wish you will come back to us forever!” na dan rausayar da kaina cikin alamun rashin gane inda maganar tashi ta saka gaba, me yake nufi ne? Murmushi yayi ganin ya saka kwalwa na cikin rudani. Yayi murmushi yace “oya! Up you go! Naga abokan ki suna jiran ki tun dazu” sai lokacin idanuna suka koma ga inda muke zaune, su Ni’ima na hango tsaye a kofar shiga lab dinmu suna hirarsu da Ramlah, cikin sauri na jefa jakar daya bani cikin handbag dita na mishi godiya tare da bude murfin motar na fita. Gabadaya kallo suke bina dashi cike da alamun tambaya nasan bai wuce na mamakin abinda muka tsaya hirantawa da Abbu bane tun dazu, naja fuska tare da kara gyara zaman gilashi na a fuskana. Tun kafin in karasa wajen su suka iso gare ni, Saadiya da Ni’ima suka kamo hannuna Ramlah kuma ta dafa kafadata, cike da damuwa suke tambayana, “Nafeesah are you ok?” ni duk sai naji sun ma bani haushi, na cire gilashin idona ina kallonsu cike da takaici, “why?? Saboda crush dina zai yi aure sai kuke zaton karewar rayuwata ne yazo ko me?” gabadayan su were relieved da yadda suka ga nayi, Ramlah tace “yeah! I thought about more than that ma, nayi zaton zan ganki kamar sabuwar kamu ne wallahi sai kuma na ganki da hankalinki dai, but are you really ok?” na gyada kaina “yeah, I am Ramlah but that doesn’t mean ban ji haushin abinda Muneer ya min ba” Ramlah ta rungume ni da sauri tana tapping bayana, “ohh my poor friend, Am really sorry. Don Allah kiyi hakuri, nasan in shaa Allah wanda yafi Muneer alkhairi a gare ki yana nan zuwa” na danyi murmushi, kwatankwacin abinda Abbu ya gama fada min. Na janye daga jikinta ina kallon su Ni’ima dake tsaye suna kallonmu nace “ba kuna da lectures ba wai me kuke yi anan?” Sa’adiya tace “wallahi Ramlah ce ta kira mu wai muzo mu tayata baki hakuri don tasan yau a hargitse zaki xo sai kuma muka ga akasin haka” ajiyar zuciya nayi nace “na hargitse kam Sady but Alhamdullillah na dawo cikin hayyaci na kuje kawai” suka mana sallama suka tafi mu kuma muka shiga lab. Ranar babu aikin da muka yi, sallama muka yi da staff da lab attendants na dept din don haka wajen karfe sha daya muka bar lab din cike da kewar mutanen da muka zauna dasu. Wajen su Ni’ima muka je na kara musu sallama, daga nan na wuce gida. Ita Ramlah tana Kano tukun. +

Ina zuwa gida na kara hada kan kayana na zauna zaman jiran Daddy don yace shi zai zo ya dauke ni. Bayan an fito daga masallaci sai gashi har da Mommy, sai da muka yi Sallar La’asar sannan muka yi sallama da iyalan Ibrahim Galadanchi cike da kewa, kauna da zullumi. Zullumin ko zan sake ganin su a rayuwata ko kuwa? Zullumin ko zan iya da korar wadannan kananun feelings da nake ji game da Abbu? Zullumin ko zan iya yin normal rayuwa kamar da wadda nake yi a gaban Iyaye na? Magana ta gaskiya watanni shida da nayi tare da Iyalan Ibrahim Galadanchi watanni ne masu muhimmanci da tarihi a gare ni, sun koya min abubuwa da dama a rayuwata, sun kuma gaya min ainihin abinda ni, Zuciya, da gangar jikina suke so da Muradi.

Na daga idanu a hankali na kalli Hafsy dake hannun Babanta tana rusa kuka da iyakar karfinta tana ihun Ita sai ta bini, na kalli su Qaseem suma duk fuskokinsu cike suke da jimami har da kwalla a cikin idanunsu, hakika bahaushe yayi gaskiya da yace ‘Sabo turken Wawa’ dana kalli fuskar Abbu kuwa sai da naji kamar in balle murfin motar in fito ince na fasa komawa gidan. Damuwar dake fuskar shi was obvious, na karance ta kuru-kuru cikin idanunshi, kallona yake yi da dukka idanunshi, yanayin shi ya min kama da wani wanda yake tsoron rasa wani abu mai matukar muhimmanci a gare shi. Daddy ya bude murfin motar ya shigo ya mata key, Abbu da iyalan shi suka daga mana hannu bakinsu dauke da addu’ar Allah ya kiyaye hanyar yayin da naji kwalla ta cika min idanu, Daddy ya ja motar muka tafi. Nabi gidan da kallo idanuna cike da kwallah, Allah kenan! Kamar a ranar ne nazo gidan, na tuna sanda su Daddy zasu tafi kukan rabuwa dasu nayi, gashi yau kuma ina kukan rabuwa da iyalan Abbu. Tafi tafiya na fara bajewa daga kukan dana fara, su Daddy hirarsu suke tayi game da karamcin iyalan Abbu, ni kam kallon gefen hanya nake yi kawai. Barci ya dauke ni bani na tashi ba sai da muka isa gidanmu shima Mommy ce ta tashe ni, na fito daga motar fuskana a washe ina kallon gidanmu, Finally dai! I am back!. Muka dauki wasu kayan muka shiga dasu yayin da Maigadi ya shigo da sauran, Dakina a shirye na tarar dashi kamar ina gidan don haka ina shiga na ajiye jakar hannuna akan kujera daya dake dakin na zube akan gado ina ajiyar numfashi.Ana kiran sallah Mommy ta leko dakina tace in fito Daddy zai ja mu sallah, sai lokacin na tashi daga kwanciyar da nayi na shiga bayi na dauro alwala na fito, dogon hijabi na dauka na tafi dakin Daddy. Wani dan karamin dakine a cikin dakin shi wanda yake aiwatar da ibadojin shi a ciki, dakin lullube yake da darduma sai tashin kamshi yake yi, shelves shelves na littafan addini a gefe a shirye gwanin ban sha’awa. Daddy ya ja mu sallah, muna gamawa ni da Mommy muka dauko littafin Arrijalu Wan-nisa’u fil Jannah Daddy ya ja mana karatu har aka kira sallar Ishai muka yi. Muka fita zamu yi dinner amma abinci fa yace sam bai ga wajen zama a cikina ba, Mommy ta kalli yadda nake ta juya cokali a cikin Irish Supper data mana wanda yana daya daga cikin favorites dina, na tabbata saboda ni tayi shi amma na kasa ci, tace “Baby lafiyan ki lau kuwa kin kasa cin abinci?” Daddy ya dago yana kallona, cikin sauri na girgiza kai nace “m fine Mom, cikina ne a cike kawai” Daddy ya tsiyayo Pineapple and coconut juice da Mommyn ta hada ya miko min, na amsa tare da kaiwa bakina na kur6a, aikuwa har da lumshe idanuna saboda gardi da sanyin daya ratsa ni, da taimakon lemun na dan samu na kara tura abincin haka nan kafin na musu sai da safe na tafi dakina. Ina shiga na fara kokarin kimtsa kayana cikin wardrobe duk a kokarina na kauda tunanikan dake dankare a cikin raina. Na janyo handbag dita ina kokarin rataye ta a bags rack naji nauyi a ciki, cike da mamaki na zura hannuna ciki na fito da karamar jakar da Abbu ya bani da safe, a hankali na zauna a gefen gado tare da janyo dan karamin purple akwatin dake ciki, cike da mamaki na fiddo shi ina jujjuya shi a hannuna. Ina budewa na zaro idanu sakamakon wata siririyar sarka dana gani a ciki da dankunnenta har da zobe, sarka doesn’t look that out of ordinary but daga ganinta kasan ba karamar sarka bace. Hannuna rawa ya shiga yi na rasa abinda zanyi, tashi nayi da dan akwatin a hannuna na fita falo, su Daddy suna zaune suna kallo duk suka bini da kallo, na zauna a gefen Daddy tare da mika mishi akwatin nace Abbu ne ya bani dazu, da mamaki Daddy ya karbi akwatin yana jijjiga shi a hannunshi yace “Shi Ibrahim din ne ya baki wannan sarkar?” na gyada kai a hankali, ni kaina na kasa yarda da hakan gani nake kamar a mafarki, Daddy yace “amma me yasa?” na jijjiga kai “nima ban Sani ba Dad kawai bani yayi” Mommy ta karbi sarkar itama ta dudduba, ta kalli Daddy tace “da alamun sarkar Babba ce fa Habibiy, Anya zamu karba kuwa?” Daddy yace “abinda nake tunani kenan exactly…” yace min “ki je daki ki kwanta, da safe zan tuntube Ibrahim din inji” nace “toh” na musu sai da safe na wuce dakina. Ina kwanciya barci ya kwashe ni, after all it has been one exhausting and stressful day.Washegari Daddy ya dawo min da sarkar da Abbu ya bani, ban tambayi abinda ya cewa Abbu ba ni dai yana bani na bude na zura zoben a cikin yatsa na. A ranar sai ga Anty Ameenah ta kira ni, korafi ta min akan na tafi ba tare dana musu sallama ba, hakuri nayi ta bata akan cewa Lokaci ne ban samu ba, bata hakura ba sai dana dauki alkawarin cewa zan je gidanta musamman sannan. Bayan mun gama wayar shiru nayi ina kallon wayar a raina ina tuhumar kaina akan ba mutane false hope na ganina da ziyartar su bayan nasan cewa ba haka bane a cikin raina. +

Nayi shiru akan gado duk kadaici ya ishe ni, a raina na raya da ace a gidan Abbu nake da war haka ko dai muna hira dasu Hafsy, ina kicin ina girki ko kuma muna wasa a gym kamar yadda muka saba kwanan nan idan bama aikin komi. Wayata na janyo na latso lambar Abbu, sai kuma na kasa danna mishi kiran, a raina ina mamakin kaina me zan ce mishi ne idan ya dauka? Me zan ce mishi ne dalilin da yasa na kira shi?? Kawai sai na maida akalar wayar zuwa ga Anty Mubeenah, ta shiga tayi ta ringing amma ba a dauka ba, shiru na bata mintuna biyar ko zata kira amma bata kira ba sai na kira wayar Abdullahi, cikin ikon Allah ya dauka, cike da doki muka gaida dashi. Nace ya bani Hafsy mu gaisa yace ai tana gida yau bata je makaranta ba, nace me yasa? Yace ai Tun jiya take kukan Ita lallai sai an kawo ta wajena shine yau ta tashi da zazzabi, a raina naji ba dadi don haka nace idan sun koma gida ya kira ni yace toh. Yana kashe wayar na kira Ni’ima, muna gama gaisawa tace “yanzu kuwa Babban Yaya ya bar nan” nayi jim ina kokarin yin maraba da sunan shi da naji ta ambata, haka kawai naji zuciyata ta dauki bugu da karfi, “umh ya su Mama?” nayi Kokari na kauda hirar Abbu da take kokarin sakowa amma duk da haka ban tsira ba, “next week ne bikin bude kamfanin shi a Beijing, how I wish zan samu zuwa” na hangame baki cikin mamaki nace “Da gaske?” tace wallahi kuwa. Nace “Masha Allah! Lallai zan kira shi in taya shi murna, na dade da jin labarin bude kamfanin wajen Bala Malam, ni nayi zaton ma an jima da budewa ashe har yanzu?” tace “kin san dama bude kamfani a kasar waje is not something easy musamman ga wanda yake ba dan kasar ba, don ma abokin aikin nashi haifaffen Beijing din ne shi yasa” na gyada kai. Tace “Hajiyar mu tayi mamakin tafiyar ki fa dazu da Babban Yaya yana gaya mata, tayi ta korafin baki masu bankwana ba” a raina naji babu dadi, sai lokacin naji ban kyauta ba, haka na baro Kano bayan Iyalan Abbu da Anty Haleemah babu wanda na wa sallama, nace “in shaa Allah duk ranar dana kara shigowa Kano zan zo in gaishe ta” tace better! Muka dan kara hira kafin muka yi sallama. Later in the evening Daddy ya dauke mu muka fita yawon gari, shiga nan fita nan har gidan Anty Uwani muka je acan ma muka yi sallar Magriba kafin muka juyo gida.Sai dana gama shirin kwanciya barci misalin karfe tara na dare sannan na turawa Abbu text message, *”Abbu naji ance zaku bude kamfanin ku next week, Allah ya sanya Albarka da Alkhairi. And thank you for the necklace, it’s beautiful, I like it!”*. +

Minti biyar tsakani naji Wayata tana vibrating, da sauri na janyo ta, as expected; Abbu ne. Sashe daya na zuciyata cike yake da murnar jin muryar Abbu yayin da a gefe daya nake jin wata er fargaba da tsoro dana rasa ko na menene a cikin raina. Na daga wayar da sallama cikin wata siririyar murya wadda ban san ina da Ita ba. A nashi bangaren sai da yaji wani yarr! Hakan ne ya haddasa mishi sanyin jiki da sanyin murya a lokaci guda, shima cikin sanyin muryar ya amsa min, yace “Why didn’t you call early?” ban fahimci abinda yace ba nace “naga dare yayi ne shi yasa na maka text” wanda a hakikanin gaskiya ba haka bane ba, ina jin tsoron abinda jin muryar Abbu zai haddasa min a cikin jikina ne, yace “it’s just nine fa, ya kike anyway?” nace “lafiya lau…… Naga sarkar daka bani, nagode sosai” ya dan yi er dariya, “shine Daddyn ki ya kira ni yau tun da safe yana interrogating dina kamar wani wanda yayi kyauta da abinda bai dace ba, sha ya bani dariya sosai ya kuma burge ni” naji na dan saki murmushi, ina so inji ana yabon iyayena, nace “sarkar ce Abbu naji Mommy tace babba ce, why would you give me such a precious thing?” na tambaye shi abinda nake ta tunani tun dazu, me yasa zai bani sarka babba haka ni ba diyar shi ba ni ba matar shi ba, in fact bamu hada ko wace irin alaka dashi ba sai ta Diyar Aboki da Abokin Uba? Ya katse ni ta hanyar cewa “Because I can ofcoure! So ya kika ga sarkar? Ina fata ta burge ki?” na kalli zoben hannuna naga yadda ta kayata hannun nawa sosai, nace “Sosai ma Abbu, zoben ya zauna a hannuna perfectly kamar don ni aka yi shi” yace “ai dama saboda Ke aka yi shi din” na danyi jim ina so kada in yiwa amsar tashi fahimtar da ba kenan ba, na maida akalar hirar tamu zuwa wata daban ta hanyar tambayar shi ina su Hafsy! Yace “pretty ta sha kuka tun jiya har dan zazzabi tayi saboda tafiyar ki” nace “Allah sarki Hafsy! I really miss her so much!” ba zato naji yace “ni fa?!” tsit nayi ina kifta idanu, maganar tazo min a bazata, ya sake cewa “ni fa? Didn’t you miss me?” cikin wata irin seductive murya, Ya Allah! Me Abbu yake nufi da innocent rayuwata ne yake min magana cikin irin wannan muryar? Na tabbata da a kusa dashi nake babu abinda zai hana ni jefa jikina kan shi, cikin rawar murya numfashi na har daukewa yake nace “Abbu… Sai…. Da safe. I gotta go” daga can bangaren shi ya dan hade ran shi, a hankali yace “you are not enjoying having my company?” nayi saurin girgiza kaina, idan da mutumin da nafi jin dadin hira dashi duk duniyar nan wanda nake ganin ko kwana zamu yi akan waya muna hira ba zan gaji dashi ba to Abbu ne sai dai ina tsoron abinda zai je ya dawo, bana fata in sake dandana abinda naji daga Muneer a wajen ko wani namiji kenan ya zama dole in janye jikina daga Abbu tun kafin inyi ending up hurting my self. Nace “m just a bit sleepy ne Abbu” yace “ok, yakamata kiyi barci kam. Sweet dreams to you” “Thanks…. And same to you!” na karasa fada more like a whisper to myself, ban sani ba ko yaji ko bai ji ba? Bana ma so yaji din ni, nayi sauri na kashe wayar. Makale ta nayi a kirjina daidai saitin zuciyata ina ajiyar zuciya idanuna a lumshe, na kwashe Lokaci mai tsawo a haka kafin in silale kan gado in kwanta. Babu abinda ya dinga dawo min a cikin kaina irin fuskar Abbu, yanayin yadda yake gudanar da rayuwar shi very cool and impressive, murmushin shi, yanayin kallon shi, zubin halittar shi…. A takaice dai da tunanin Abbu nayi barci a ranar. Wasu irin mafarkai na dinga yi barkatai kala-kala kuma cikin su babu wanda ban ga Abbu a ciki ba. Muna zaune akan wani lilo ni dashi a wani hadadden lambu mai cike da ni’imah, hira muke yi dashi duk da bana sanin abinda yake fada amma murmushi nake tayi a mafarkin har ina hadawa da dariya, ya dauko strawberry da fork ya miko min, na daga bakina kenan zan karba naji an daka min duka a kafada ba shiri na tashi daga mafarkin da nake, hannuna dafe da kafadata inda yake min xugi na tashi zaune ina kallon wanda ya aikata wannan danyen aiki. Mommy ce tsaye a kaina tana hararata, tunda naga haka nasan abinda nayi. Da sauri na kai duba na zuwa jikina, as I expected; babu riga. Da sauri naja bargo na rufe zuwa wuyana tare da sadda kaina kasa, nasan cewa yau mai kwatana a hannun Mom sai Allah. Cikin hararar da take jifa na dashi tace “Yanzu saboda Allah Ummiey har yanzu baki daina wannan rashin hankalin da kike yi ba? Haka kika je gidan mutane dama kina musu tallar halittar jikin ki?” da sauri na girgiza mata kai, “A’ah wallahi Mom, bana yi a can” tace sai anan koh saboda kin raina ni ko” nayi saurin girgiza kai nan ma “Allah Mommy ba haka bane, ni fa ban ma san lokacin dana cire rigar ba” tace “rufa min baki nan uwar en zagin baki tun yaushe nake miki fada game da haka Ummiey? Amma saboda taurin kai saboda kin maida ni abokiyar wasan ki baki ji koh?” tuni hawaye suka ciko min ido abinda nasan Mommy bata so kenan, cikin shagwaba nace “Allah Mommy da gaske nake. Nima fa ban san lokacin da nake cirewa ba, kawai ji nake yi kamar rigar ta na shake ni sai in kasa numfashi shi yasa nake cire rigar kuma fa na daina Allah da gaske, ban san ya aka yi na cire jiya ba” ta kalleni kafin ta kauda kai ta juya zata bar dakin, “sai ki tashi ai kiyi sallah koh? An kira tun dazu” na bita da kallo har ta bar dakin, sighing nayi a hankali tare da lalubo rigata da nayi jifa da Ita a kasan gado na zura, saukowa nayi daga kan gadon na fada bandaki.Yana ajiye wayar ya lumshe idanunshi tare da maida bayan shi ya jinginar da study table din da yake kai a zaune. Nafeesah! Nafeesah!! Sunan dake ta shawagi kenan a tsakiyar kanshi a lokacin, Allah kadai yasan iyaka adadin kewar ta da yayi. Shi kan shi yau sai da yayi Kokari ya iya sauka daga kan gadon shi, gidan da Babu Nafeesah! Teburin cin abincin da babu Nafeesah!! Rayuwar da babu Nafeesah!!! Abinda yayi ta jinjinawa a cikin ranshi kenan yana tunanin ko zai iya surviving a haka?! A hankali ya bude idanunshi tare da gyara zaman shi, hannunshi ya dora akan system din dake gabanshi ya cigaba da typing din da yake yi kafin Nafeesah ta kira shi ya fada cikin shaukin ta.
Kofar dakin shi yaji an turo, an shigo, tare da maida kofar aka rufe. Da mamaki ya daga idanunshi da suka gama rinewa da shaukin Nafeesah ya kalli Mubeenah dake tunkaro shi. Shi a karan kanshi ba zai iya tuna Lokaci na karshe daya ganta a tsakiyar dakin shi ba, ya jijjiga cikin wani irin takaici na babu gaira babu dalili daya ziyarce shi she has ruined it! She just ruined dan guntun farincikin daya mamaye zuciyar shi for a while. Kallo ya bita dashi har ta zauna a gefen gadon shi, sanye take da doguwar rigar barci har kasa, jelar kitson kanta da aka mata fiye da watanni biyu da suka wuce (lol) ya fito ta cikin hular data saka a kanta ya zubo har kan kafadunta. Kan shi ya dauke ya maida ga rubutun da yake yi, ya kwashe kyawawan mintuna arba’in kafin ya gama. Ya kashe system din tare da tashi ya fada bayi, brush yayi tare da dauro alwala kamar yadda yake a Al’adar rayuwar shi. Ya fito ya tsaya a gaban mirror, turare mai sanyin kamshi ya fesa a gabban jikinshi ya koma kan gado daga can daya gefen da Mubeenah take a zaune har lokacin, light off yayi ya kwanta. Mubeenah data gama kuluwa da abinda yayi, tace “haba Ibrahim wannan wane irin rashin mutunci ne kana gani na zaka yi wani banza dani ka maida ni kamar wata invisible human being?” ya kalli sashen da take duk da baya ganinta saboda duhun da dakin yayi, yace “au! Ai ban yi zaton cewa kina da abun cewa bane, na sani ko zuwa kika yi kawai kiga yadda dakina yake duba da yadda kika share watanni ba tare da kin leko ba?” ta dan ja siririn tsaki, ” amma dai kasan cewa bana zuwa dakin ka haka nan koh?” ya gyada kanshi a hankali, a zuciyar shi yace ‘right! Bana ganin ki a dakina sai idan kina bukatar either kudina ko jikina!’ yayin da wani irin bakin ciki da takaici ya mamaye zuciyar shi. Tashi zaune yayi tare da kunna wutar dakin ya juya yana kallonta, “What do you want then?” ta dan yamutsa fuska “ina bukatar kudi ne!” ya kalleta sosai, “kudi kuma? Har nawa?” tace “one hundred and fifty k” ya gyara zaman da yayi sosai “n why would I?” ta wani hade fuska, “it’s for you Ibrahim! Material ne zan saya da jewelries na zuwa bikin bude kamfanin ka kaga kuwa it’s worth it” shi gabadaya ya ma kasa magana, kallonta kawai yake yi har ta dire maganar ta. Yace “duka duka yaushe kika amshi 50k a wajena Mubeenah? Wai saboda meye na bude miki saloon? Ina ce dama saboda idan bukatu irin haka sun taso kiyi amfani dasu ba tare da kin tambaye ni ba ne?” ta wani lankwashe murya Ita ala dole kissa tace “kasan cinikin saloon din ne kwana biyu sai a hankali babu customers shi yasa, yanzu haka bani da ko sisi a account dina” ya girgiza kai kawai, Mubeenah! Bai san wace irin mata ce Ita ba, Kwatakwata bata da damuwar yanayin da mutum yake ciki ko zai shiga, Ita dai kawai a bata abinda take so sai a samu zaman lafiya. Yace “Mubeenah! Baki ganin halin da ake ciki ne yanzu? Dinkin dubu dari a wannan zamanin Mubeenah ki duba mana, ina laifin hamsin?” hararar shi tayi a kaikaice tana mai turo baki, “kaga ni fa ba cewa nayi ka zauna kana bani labarai ba. Kudi, zaka bani ko A’ah?!” Murmushi yayi a sanyaye yace “zan baki mana uwargida sarautar mata….. Amma zo kiji kafin nan…” ya janyo ta zuwa jikinshi, cikin sauri ta zame, ya bita da kallo mai dauke da alamun tambaya. Fir taki amincewa dashi sai da tayi tsayin daka taga a take ya tura mata kudin cikin account dinta sannan ta amince. Shima haka nan ta tsaya abinta shi kadai yake kidan shi da rawar shi tana kwance male-male kamar ruwa. Ba a jima ba ya mirgina daya gefen gadon yayi ruf da ciki idanunshi a lumshe, duk dokin da yake yi sai yaji ya kau daga ranshi saboda yadda tayi kamar bata jindadin kasancewa dashi, he means ta ya za ayi ace mace ana having s*x da Ita amma Ita ko a jikinta, karewa ma Allah-Allah take yi ya sauka daga kanta, does it make sense? (Qalubale a gare ku mata, akwai ire-iren ku kuna nan libge cikin lungu da sako na wannan duniyar, a gyara dan Allah!). Bayan nan Kwatakwata baya jin dadin kasancewa da Ita shima, koda yake abu ne daya riga ya saba dashi. Yana tunanin tun wajen haihuwar Hafsat Mubeenah ta karu kuma bata maida hankali wajen ganin cewa an dinke ta ba, ko don bata damu dashi bane? To shi dai tun daga nan ya daina fahimtar Mubeenah, haka nan yake maleji dai ko don raya Sunnah da kuma kare kai daga dattin Zinah to yanzu abun dai ya fara wuce misali. Yana jin lokacin data tashi ta zura kayan jikinta ta fita daga dakin, bata damu da yadda miji ya juya mata baya suna tsakiyar auratayya ba, bata damu taji dalilin daya saka shi aikata haka ba balle tayi tunanin gyara, Ita dai kawai tunda ta samu abinda take muradi to an wuce wajen. Da kyar ya tashi ya fada toilet yayi wanka da ruwa mai sanyi, babu abinda ta6a Mubeenah ya jayo mishi sai kara hargitsa mishi tunani da kwalwa da yayi. Ya fito ya canza kayan barcin shi kafin ya kwanta, zuciyar shi cike da tunanika barkatai, mafi yawa daga cikin su shine ‘He had to make Nafeesah his ASAP, kafin wani ya riga shi ya shiga uku’.
3

Sati na daya a gida ina hutu, babu inda nake zuwa daga farfajiyar gidanmu shan iska sai kicin, bana aikin komi sai na kallo da chatting, hankalina a kwance yake duk da cewa har zuwa lokacin kewar Abbu da iyalan shi na taba raina babu abinda ya ragu, har yau ina jin abun kamar a ranar na bar gidan. Muna waya dasu Hafsy sosai, zan iya cewa ma kusan kullum sai mun yi waya dasu. Ina kwance a tsakiyar gadona da system a gabana ina duba wasu docs a ciki. Ranar asabar ce daga ni sai Mommy a gidan, Daddy yaje Abuja wajen wani meeting. Mommy ta leko dakina, dagowa nayi na kalleta tace “ki tashi ki shirya muje Airport mu dauko Antynki Shafa” wani irin tsalle nayi na diro daga kan gadon na riko hannunta, cike da doki nace “Mommy da gaske? Yaushe tazo?” tace “she’s yet to land, nan da awa daya may b” nayi sauri na fada bandaki ina ihun murna, Mommy kai kawai ta girgiza ta juya. Anty Shafa’atu matar autan su Daddyn mu ce suna zaune a New York, Gynaecologist ce wadda tasan aikinta. Ina matukar son matar saboda nima tana sona, matar ta hadu ne ta kowane fanni, ga kyau ga iya kwalliya ga iya girki, duk lokacin data zo ina makale da Ita ina koyon girki da kwalliya a wajenta. Dan su daya Mukhlis dan kimanin shekaru uku, idan kaga yaron sai ka rantse da Allah dan turawa ne saboda kyan shi. A gurguje nayi wanka na fito, kwalliyar da nayi ba wata ta azo a gani bace amma nayi kyau sosai musamman dawowar nan da nayi nayi wani fresh dani. Doguwar riga fitted gown nasa ta wani yadi navy blue, nayi rolling da gyale shima navy blue na saka takalmi mai dan tsini navy blue, kyakkyawar farar kafata ta fito a fito sosai a cikin takalmin tayi kyau, cikin jikkuna na ciro wata er karama ta vintage ruwan kayan jikina itama na rataya a kafadata, falo na fita. Mommy bata gama shiryawa ba don haka ne nayi amfani da damar nan na tsaya kashewa kaina selfie. Tana fitowa muka wuce, a cikin karamar Motar Mommy din Vibe muka fita, Ita take tukin mota don ni har lokacin ban iya tuka mota ba, Daddy ya fara koya min ban maida hankali na bane shi yasa. Lokacin da muka isa Airport din basu kai ga sauka ba don haka muka tsaya a lounge room muna jiran su. Ba a dauki mintuna ashirin ba jirgin ya sauka, muka tashi muka fita muna jiran su. Ina hango fitowar ta na fara daga mata hannu har ina hadawa da tsalle, suna fitowa na ruga na rungumeta ina tsallen murna a jikinta. Ta dago kaina daga jikinta tana kallona tana dariya, “Haba Ummiey ni me zaki ce min? Shekaru nawa rabon da ki kirani mu gaisa ni nayi ma zaton kin manta dani ai” nayi er dariya nace “Aunty kin san waya daga nan zuwa inda kuke minti daya fa zan iya sayen atamfa da kudin, wannan marra kuma ta economising kudi ce shi yasa, Ke kuma ba kya kira na kema” taja hancina tana dariya, “Ummiey kina nan da dadin bakin nan naki, ba a taba kada ki a xance” Mommy ta karaso wajen mu suka gaisa da Anty Shafa, sai da muka nutsa na kula da ban ga Mukhlis ba, nace “Anty baki zo da Mukhlis bane?” bayanta ta waiwaya tace “nazo dashi mana, yana wajen Harith”. Tana rufe baki wani dogon gaye, fari tas dashi kamar Antyn ya tsaya a gabanmu, akan kafadar shi kyakkyawan babe ne yana wasa da abun wasa na yara, da sauri nace “Mukhlis!” yaron ya juyo ya kalleni na en sakwanni kafin ya dauke kan shi, ina mika hannu zan dauke shi yayi sauri ya makale a jikin gayen, baki na kama cike da mamaki, nace lallai Mukhlis har ka manta dani? Last time da zaku koma kuwa da kyar aka banbare ka daga jikina. Anty tace “ai kwanaki sun ja Ummiey, ya kara wayau da shekaru fa” Mommy data gaji da tsayuwa tace mu tafi koh? Sai lokacin wannan gayen yayi magana, cikin wani irin yanga-yanga ko fi’ili zan ce, “Sis, ni zan wuce gida ne fa” tace “ok, ni sai na tsaya a gidan su Yaya sannan. May b da dare in shigo” ya wani tabe baki tare da mika mata Mukhlis, sai lokacin ya kalli Mommy ya gaishe ta, ta amsa da fara’ar ta tare da tambayar Anty “wannan ko kanin ki ne?” tace “ehh, yana karatu ne a can NY din, ya biyo ni wajen biki ne” sai lokacin naji ashe bikin kanwarta Murjanatu tazo. Gayen ya kalleni a fuzge yana wani shan kamshi, wai “sannu koh??” don ba don idon su Anty a wajen ba da wallahi ba zan ko kalleshi ba, a fuzge nima na amsa mishi, “kaima sannunka” Anty tace “can we please? Na gaji da tsayuwar nan” muka nufi motar Mommy muka shiga, ina kallon idanun gayen nan a kaina lokacin da muka ja motar muka tafi, baki na murguda mishi yayin da naga ya saki murmushi yana muttering wasu kalmomi da ban fahimta ba. Already dama an gyarawa Anty daki tun jiya don haka muna zuwa ta fada dakin don watsa ruwa, na shiga dakina na shimfidar da Mukhlis a kan gadona saboda yayi barci. Na fita naje na fara dauko abinci ina kai mata dakinta, kafin ta fito na shirya mata komi don haka zama kawai tayi ta fara cin abinci na zauna a gefenta muna en hirarrakin mu har ta gama cin abincin, sallah tayi ta kwanta nima na koma dakina na kwanta a gefen Mukhlis.Anty Shafa ta fito daga dakin da aka mata masauki tana jan hannun Mukhlis, muna zaune a cikin falo Bayan mun gama cin abinci, ina gefen Mommy a zaune kawai muna hira da ita. Anty tace “Ummiey zo ki raka ni mana?” Na kalli Mommy kafin in maida kallona ga Antyn, Mommy tace “ni fa ba hana ki zan yi ba kike wani kallona, tashi ku tafi mana” murmushi nayi na tashi na shiga dakina, wandon jeans ne a jikina da shirt don haka na saka doguwar hijabi na fita muka wuce gidan su Anty. A Shagari road suke basu da nisa da inda muke don haka tricycle muka yi shata har kofar gidansu, gidan Babban gida ne da parts parts. Mahaifin su matan shi uku saboda haka gidan su gidan iyali ne sosai, Anty Shafa itace autar uwargidan Hajiya Maryam wadda ta rasu shekaru biyu da suka wuce. Muna shiga gidan gida ya dauki sowar murnar zuwanta, da kyar muka samu muka shiga part din Hajiya Talatu uwar gida a halin da ake ciki. Muka shiga har uwar dakanta inda muka sameta akan gado a hakimce, cike da girmamawa muka gaidata ta wani amsa da kyar kamar wadda aka takurawa, dana kalleta sosai sai naga kamanninsu da gayen nan na airport na tabe baki a raina nace ashe gado yayi. Bamu yi minti goma ba muka tashi muka wuce daya part din, Ita dayar da naji suna cewa Hajiya Amarya ba laifi tana da fara’a. Anan sashen nata en sannu da zuwa suka yi ta shigi da fici. Sai wajen karfe goma na dare muka musu sallama, na saba Mukhlis dake ta shakar barci a kafadata. Muna fita waje muka jiyo horn din mota a gefenmu, muka juya. Wata jar mota er karama da Ita mai kyau, Anty tace muje, Harith ne zai mika mu gida. Sai dana turo baki kafin na bi bayanta, haka kawai naji gayen bai kwanta min a rai ba. Na bude gidan baya na zauna a gefen Anty, Harith ya juyo ya kalli Antyn kafin ya kalleni ya sake kallonta, “amma dai ina fata ba Driver zaku maida ni ba ko Sis?” Anty tace min dan Allah tashi ki koma gaba diyata. Ba yanda na iya na fita na koma gaban, ya tashi motar muka tafi. Babu wanda yayi magana a cikinmu har muka isa kofar gidanmu, yayi parking muka fita, Anty tace mishi “sai da safe koh?” bai amsa ba sai kallona da yayi, “enmata babu godiya ne?” ban san lokacin dana wurga mishi harara ba na juya na wuce abina, na kula he’s very arrogant. Anty ta biyo bayana tana ce min wai kar in damu dashi, haka halinshi yake. Ban ma tanka mata ba don a tunanina ai sai ka damu da mutum ne sannan al’amuran shi suke damun ka. Sai da muka shimfidar da Mukhlis sannan na mata sai da safe na wuce dakina, cikin mintuna sha biyar na gama duk shirin da zan yi na kwanta barci. 1

Washegari aka fara bikin gidan su Anty Shafa, tun da safe ta tafi ni kam ko wajen bikin ban leka ba Mommy ce ma taje. Ina gida da yamma Malamin dake koya min karatu yazo ya kara min, lokacin Mommy ta dawo muka shiga kicin muka girka Jollof macaroni da fried chicken, muna girkin nake tambayarta Mama Sauda da yake kwana biyu ta sha rashin lafiya don haka suka maidata kauyen su tace ai taji sauki tuni, Daddy ne yace tayi zamanta a can kawai, na gyada kai.
Ni kadai ce a cikin falon lokacin da Anty Shafa ta dawo, na mata sannu da zuwa tace “tare muke da Harith wai yunwa yake ji, Allah sa akwai abincin?” na kalli dinning nace “akwai, sai dai ban tunanin zai ishe ku ku biyu” tace “nooo, ni nace abinci a gida, shine wai ba zai ci abincin biki ba, he can be picky about foods sometimes” na tabe baki nace shi ya sani ai. Anty tayi murmushi tare da juyawa don mishi iso ni kuma na leka dakin Mommy na fada mata. Ina dawowa falon yana zaune a daya daga cikin kujerun falon, Mukhlis yana cinyar shi, yaron yana ganina ya sauka daga kan cinyar shi ya rugo ya rungume ni, na tare shi ina dariya nace “mun shirya yanzu kenan?” Anty tace dama shi ai kwana daya ake Sabo dashi. Saboda idon Anty ne yasa na kalli sashen da Harith yake, “sannu” kawai nace, ban tsaya jiran amsawar shi ba na wuce dinning nayi serving dinshi abincin a plate na kai gaban shi na ajiye, kan kujera na koma na zauna na ja Mukhlis jikina ina jan shi da hira. Ya kalleni yace ‘enmata baki bani ruwa ba” sai dana kalleshi kafin na tashi kicin naje na dauko ruwa mai sanyi a fridge na kawo na ajiye mishi, yace “sorry! Bana shan ruwa mai sanyi” na ciza lebe tare da dauke goran ruwan na je na canzo mishi da mara sanyi na kai mishi ya sake kallona yace “Baku da lemu ne haka kamar fanta ko peach?” zuwa lokacin nasan cewa he’s doing it on purpose, ban ko kalleshi ba na koma na zauna abina, ya kalli Anty ya wani lankwashe murya, “Anty lemu nake so” tace Bari in dauko maka to, wanne kake so? Yayi saurin cewa “no no Anty, da girman ki ki dauko mun lemu haba! Bari yarinyar can ta dauko min mana” ban san lokacin da wani irin murmushin takaici ya subucewa fatar bakina ba, lallai ma Harith! Wai yarinya! Anty da bata kula da game din da yake bugawa ba ta tashi tsaye tace “Ummiey don Allah taimake shi da lemu, bari in rage kayan jikina” ta shige dakinta ni kuma naci gaba da wasana ni da Mukhlis, kallona yayi yace “baki ji abinda Sis tace ba? Ki bani lemu!” ban kalli sashen da yake ba nace “the kitchen door is over there….” na nuna mishi da yatsa ta, “zaka iya zuwa ka dauko da kanka, m not someone da u can be ordering around ni kuma in biye maka kamar wata er aikin ka” yayi wani irin smirking tare da dan shafa gefen wuyan shi, “seems like u r one Rude babe, I like it!” a xafafe na jefa mishi harara, “hey watch ur mouth!” ya tsuke baki yana jifana da wani irin kallo, “if not ki raba ni dashi?” tsaki kawai naja na kauda kaina gefe don na kula da neman magana ne kawai yake yi. Anty ta fito daga dakinta ta zauna a gefen Harith, ganin yadda nake jifan shi da harara ta dube shi cike da tuhuma tace “Me ka mata Harith?” ya kalleta kafin ya kalleni cikin dage gira, “Me na miki?” tashi kawai nayi na bar musu falon don na kula idan na zauna Harith zai iya sawa in zage shi a gaban Yayar shi abinda bana so kenan. Dakina na koma na fara chatting, a facebook na ga wani page da wani daga cikin friends dina yayi liking, *Hon. Ibrahim Galadanchi Official Fans Page* cikin mamaki na shiga page din, da gaske Abbu dinne. A Profile pic din da aka dora Abbu ne ya saka wata shadda Skye blue dinkin Abacha, shaddar ta matukar yi mishi kyau, kwarjinin shi da kyawun shi sun fito kamar ka kira shi a hoton ya amsa saboda yadda hoton ya dauku sosai. Na kura mishi ido na dan lokaci kafin na janye kaina, jikina yayi wani irin sanyi wanda ganin hoton Abbu da nayi yanzu ya haddasa min, sai kuma wani tunani daya darsu a raina, kenan Abbu har yanzu yana kan bakan shi akan fitowa siyasa? Ni dana ji shiru kwana biyu ban ji zancen ba nayi zaton ko ya hakura ne ashe bai hakura ba. Kenan idan har na aure shi sai dai in janye kiyayyar siyasa dana sawa raina, kenan zan zama matar dan siyasa? Murmushi nake yi kamar wata doluwa da nayi wannan tunanin, na sake janyo wayata nayi liking din page din. Ranar haka na bata Lokaci na wajen saving din pics din Abbu da suke cikin page din, sai wajen karfe sha biyu na kashe wayar na kwanta.
Sati biyu tsakani muka koma makaranta, ba wani bata lokaci muka shiga lectures ba sauki, Ramlah tuni ta dawo, muka hadu da sauran abokan mu muka fara karatu ka’in da na’in ba sassautawa. Wajen karfe biyar na dawo daga makaranta, mai adaidaita din da nayi shata ya ajiye ni a kofar gidanmu. Na fito ina karewa jar Renault Clio dake fake a kofar gidanmu, dan siririn tsaki naja sanin mamallakin motar; Harith ne. Kwana biyu ya maida gidanmu kamar wani gidan zuwan shi, ya saba dasu Mommy da Daddy sosai cikin dan lokacin sau tari idan bai je gida ba zaka ji Mommy tana ta jajen shi, yayin da a gefe guda har zuwa lokacin mun kasa getting along dashi. Harith yana da yawan tsokana, ni kaina wani lokacin idan yana tsokanata I couldn’t resist murmushi duk da is hardly in dara, matsalar Harith daya zuwa biyu, girman kai da son showing up Baban shi mai kudi ne kuma yana karatu a kasar waje, gashi bai iya magana ba, magana duk yadda tazo mishi zai kwabawa mutum ne yayi gaba abinshi duk da dai na fahimci hakan a jinin shi yake but still ni fa sam mutane masu halayen Harith basu cikin en kayana. Kudin mai adaidaitan na ciro na bashi na wuce cikin gida. Sanye nake da wandon jeans pencil da shirt mai tsawo wadda ta sauka har kuguna, na dora bakar rigar kimono a kai tana daya daga cikin tsarabar da Anty Shafa ta kawo min. A hankali nayi ssallama na shiga falon, Harith na zaune akan kujera ya baje shi da Mukhlis suna shan tangerine, Gabadaya sun lalata wajen da bawon lemu, yana ganina ya saki murmushi tare da dago min hannu, “Hii Rudie!” harara na jefa mishi na zauna akan kujera ina kokarin daukar Mukhlis daya xo min oyoyo, na bude jakata na ciro chocolate din Milk Dairy na fasa na mika mishi, Harith bai daddara da hararar dana jefa mishi ba yace “Chocolate aka kawo mana yau? A miko min nawa to” ko kallonshi ban sake yi ba. Mommy ta fito daga kicin hannunta dauke da goran ruwa, ta miko min na amsa tare da dauke Mukhlis daga kan cinyata, tana ganin chocolate din hannunshi ta fara mita, “Ummiey na hana ki ba yaron nan chocolates da sweets amma kin ki, kina so ki lalatawa yaro hakori tun yanzu koh?” nace “Mommy babu abinda zasu mishi yanzu, bayan haka ma ai idan ya girma zai zubda hakoran wasu su fita ne koh?” ta Harare ni “Allah ya shirya min Ke Ummiey, ban san yaushe zaki girma ba” Harith yayi tsulum yace “Mommy kin san wauta irin ta en fari sai a hankali, musamman ma Ita da abun ya hade mata biyu ga faranci ga autanci” kallonshi nayi cike da takaici, nace “wai don Allah meye matsalata da kai ne Harith? Bana shiga harkar ka ka daina shiga tawa pa!” ya wani rausayar da kai innocently, “haba Ummiey, me na miki? Daga fadar gaskiya?” tashi nayi kawai na dauki jakata na shige daki, kayan jikina na cire na duba Lokaci naga da saura kafin a kira Magriba don haka na fita. Tuni Mommy ta gama girki don haka nayi joining dinsu a kallon da suke yi, mommy na tambaya ko ina Anty Shafa? Tace taje gidan su ne yini, Mom ta miko min tangerines masu kyau a bare an shirya su cikin plate tace Harith ne ya kawo musu su ci, na saci kallon inda yake zaune, idanunshi fes suna kaina, muna hada ido ya kanne min ido daya da sauri na janye kaina na dora su akan Mommy.
Ina kwance ina sana’ar chatting dina, naga wata sabuwar number ta turo min comment akan hotona dana dora akan status dina na Whatsapp ranar da safe, kayan dana saka ne ranar nayi murmushi hannuna dauke da mug din coffee, cewa aka yi “you look so cute n gorgeous Nafeesah” na danyi frowning tare da tura “who?….” ba a dauki lokaci ba sai ga reply, Hoton Harith ne ya wani kashe ido daya yana smirking da alamun a lokacin ya dauke shi, tsaki naja na tura mishi, “what? Are you a stalker? Or may be a pervert??” bai turo amsa ba, na tabe baki naci gaba da chatting dina. Wayana tayi kara, number ce duk da haka ban fasa dauka ba, ina kara ta a kunne muryar Harith ta doki dodon kunnena, “Ba a taba jifa na da kalma mai muni a rayuwa irin wannan ba, amma naji dadin sunayen, ban sani ba kila na cancance su ne!” nayi rolling idanuna kamar yana gabana, nace “meye na kira na da daren nan?” yace “just…… Manta kawai. Amma you seems to be avoiding me tunda na shigo rayuwar ki Nafeesah, why? Or may be are you afraid to fall for me??” wata mahaukaciyar dariya na saki har ina kwarewa, “stop being ridiculous Harith. You are not my type, rashin zama kusa da kai da bana yi ba avoiding dinka nake yi ba ko tsoron fadawa tarkon son ka ne ko wace shirme kake fada, i found you very annoying and I don’t want to get along with annoying people” ya danyi shiru, cikin raina naji babu dadin maganar dana mishi ba sai dai Harith yana shigar min hanci da yawa I really want to get rid of him. Gyaran murya yayi yace cikin murya mai sanyi kamar ba tashi ba, “and I promise to become your type Nafeesahh, I promise you that…. Nooo, challenge you, deal??” bai jira amsa na ba ya kashe wayar ya bar ni da waya a hannu baki a bude cike da mamakin maganganun shi.
+

Washegari sai karfe tara da kwata na fito daga dakina cikin shirin makaranta saboda ranar sai karfe goma nake da Lecture, nawa Mommy da Anty Shafa sallama na fita. Shiru-shiru ina tsaye a bakin titi babu alamun wucewar abun hawa, na kara hangar tsawon titin da zai sada ni da Babban titi inda zan samu bus na tabbata idan nace sai na fita bakin titi zan makara ne, na kara duba agogon hannuna karfe tara da rabi ta wuce, na danyi siririn tsaki tare da daga kafa na fara tafiya ina tuhumar kaina dalilin daya hana ni ajiye direba kamar yadda Daddy yaso tun farkon shigata KadPoly ni kuma na kekashe kasa nace A’ah. Motar Harith kawai na gani a gabana kamar wanda aka jefo daga sama, ya tsaya a daidai saitina tare da zuge gilashin motar ya leko da kanshi waje, “will you mind a lift en mata?” ban tsaya neman magana ba na zagaya daya gefen na shiga, yaja motar muka fara tafiya, sai dana mula na mule sannan nace mishi “ka tashi lafiya?” yayi murmushi, “kamar yadda kika tashi ba” daga haka yaja bakin shi yayi shiru har muka isa makaranta, ba karamin jin dadin hakan nayi ba. Yana yin parking na bude murfin motar na fita, dan dukawa nayi ina kallonshi yayin da shima yake kallona, nace “thanks pa!” thumbs up ya min da hannunshi, “Always baby….. Yaushe zaki gama lectures?” nace Four in shaa Allah” yace “idan na samu lokaci zan biyo in dauke ki” nace “noo, you don’t have to do that plss” bai amsa ba ya tashi motar ya tafi, a hankali nima na juya na tunkari hall din da zamu yi lecture din.

Karfe hudu dai dai muka fito daga lecture hall din da muka yi na 1-4, ni da Ramlah muke tafe a hankali a cewarta sai ta raka ni bakin gate, muna gab da fita daga parking lot kawai muka ga tsayuwar mutum a gabanmu kamar daga sama., Muneer ne! Na daga idanu na kalleshi a hankali, tunda abun nan ya faru ban kara waya dashi ba haka tunda muka dawo school bamu taba haduwa dashi ba. He was still the same Muneer kamar yadda na san shi, dogo, wankan tarwada….., Ramlah ta jefa mishi wata irin harara, “Malam Lafiya zaka tare mutane a hanya kamar wani tsoron thug?” bai kula da Ita ba idanuwanshi na kaina, ya kira sunana cikin sanyayyar muryar shi wadda ada nake jinta tamkar busar sarewa amma a yanzu, jinta nayi kamar kukan jaki. Yace “Nafeesah! Dan Allah zaki iya bani minti biyar muyi magana?” Ramlah ta yunkuro zata yi magana nayi saurin dakatar da ita, “it’s okay Ramlah I’ve got this. I’ll talk to him” ta kalleni sosai kafin ta dan matsa gaba ta bamu waje, na kalleshi a tsaitsaye, “so me kake son fada Ango-Muneer??” na fada sarcastically. Yace “Nafeesah I am really sorry akan abinda ya faru that night, sai daga baya na fahimci I acted rudely towards you, am sorry. Ba niyya na kenan ba na in tozarta ki, ban….” nayi saurin katse
shi, “kaga Muneer! Idan akan wannan maganar ne kada ka damu, I’ve move on already, ni kaina sai daga baya na fahimci kuskuren da nayi na makalewa wanda baya sona. Kai ni sai daga baya ne ma na fahimci ashe ba sonka ne nake yi ba, burge ni kawai kake yi ni kuma da yake I was stupid then I thought it was love ashe it wasn’t….” fuskar shi dauke take da wani irin expression wanda ya kusa saka ni dariya a take, daga ganin yadda yayi bai ji dadin maganar da nayi ba. Ko yana tunanin dana ganshi zan zube a gabanshi ina rokon ya aure ni ne? Ya kalleni da fuskarshi cike da damuwa, “Nafeesah……! Would you please give me a second chance? I promise to be what you want me to be, wallahi sai daga baya na fahimci cewa ina son ki, plss ki bani wata dama” ga mamakina maimakon farin ciki sai naji zuciyata tayi wani irin baki, lallai ma Muneer ni zai rainawa wayau? Fuska na hade nace “Muneer ka riga kayi wasa da damar ka in which I am very grateful for that don haka tun wuri kaje ka rungumi amaryar ka kafin kwado ya maka kafa itama ka rasa ta. All the best!” na zagaya ta gefen shi na wuce, da sauri ya tari gabana, “plsssss Nafeesah! Just a second chance! I know u love me, and I know that u didn’t get over ur feelings for me!!” cike da wani irin jin haushin shi da kuma kaina ma gabadaya nace “feelings my a**!! Yaudarar kan ka kake so kayi Muneer, I don’t Love you any more!!” na fada cikin daga murya, “now if u can please fuck the hell out of my sight plsssss, you are disgusting!!” amma da alamun ko kadan maganganuna basu shiga kunnen shi ba, kokarin matsowa gare ni ya fara yi da sauri naja da baya, just when he was about to take another step closer na jiyo muryar Harith daga bayan mu, “Nafeesah my Love!!”A hankali na juya na kalleshi, ya sake wanka yasa wani wandon jeans din Vogo da rigar CK mai V-neck, ya matso kusa dani ya tsaya gab dani yana kallon Muneer fuskar shi a cunkushe, sun dauki lokaci suna kallon-kallo shi da Muneer babu wanda yayi magana a cikin su, sai da naga shirun yayi yawa sannan na daga kafa na fara tafiya, na kalleshi nace “muje koh?” babu musu ya biyo bayana muka jera muka tafi, muna fara tafiyar ya tsaya cak tare da juyawa ya kalli Muneer da shima ya juyo yana kallonmu, yatsa ya nuna mishi cikin kashedi yace “and dude, stay out of my Fiancé side, if not…..” ya juya ya cigaba da tafiya cikin takama har yana hadawa da wani bouncing, na bi bayan shi ina dan murmushin jin dadin shocked and horror expression din dana gani akan fuskar Muneer. Ramlah dake tsaye a gefe tana kallon dramar da muke bugawa ta kamo hannuna taja gefe tana tambayana wai da gaske na daina son Muneer? In ka kalli fuskarta a lokacin sai ta baka dariya, grinning take ear to ear kamar yaron da aka ba kyauta alewar bounty. Na sabule hannunta daga nawa nace mata “kinga jirana ake yi, anjima zamu yi magana” muka yi sallama na wuce na shiga motar Harith har ya tashe ta don haka ja kawai yayi muka wuce. Harara na jefa mishi, ya juyo ya kalleni “what??” nace “what was that for? That fiancé thing??” yayi rolling idanunshi, “baki gane bane? I was just trying to save you from him so that next time ba zai kara damun ki ba koda bana nan, by the way waye shi?” na danyi sighing softly kafin na kalleshi fuskana a dan hade don ya dauki maganar da zan mishi seriously nace “sanin waye Muneer ko rashin sa babu abinda zai tsinana maka don haka stay out of it, maganar fiancé kuma kada ka kara koda cikin wasa ne kuwa ko trying to help kamar yadda kace” ya kalleni yana murmushi cikin tsokana, “ko dai baki son inji cewa crush dinki ne yayi dumping dinki kuma ya dawo yace yana son ki?” kaina na kawar gefe naki kallonshi, naki jinin a tuna min da tarin yarinta da rashin hankalin da nayi akan Muneer. Amma Harith bai kyaleni ba cewa ya sake yi “tunda baya sonki me zai hana ki zo mu sasanta dake?” a fusace na kalleshi “stop messing with me fa Harith!!” ya tabe baki, “well, m not ai dama” nace “to ni nan da kake gani na I am taken ka gane?” ya juyo ya kura min ido na dan lokaci kafin ya maida hankalin shi ga tukin da yake yi yana chuckling, ban kula shi ba na janyo wayata ina latse-latse har muka isa gida. Yau ko godiya bai samu albarkacin jin ta ba, na fita daga motar har ina banging nayi cikin gida. Kai tsaye dakina na shige, nayi jifa da jakata akan gado kafin nabi bayanta nima na kwanta a rigingine ina tariyo abinda ya faru a makaranta ranar. +

Vibrating din da wayata ya dauka daga cikin jakata ne ya dawo dani cikin hankalina, na danyi tsaki lokacin da nake laluben wayar, da kyar na iya bude idanuna da suka fara min nauyi saboda gajiya da barci na dora su akan fuskar wayar, sunan dana gani yana bouncing a jikin screen din wayar ne yasa naji zuciyata ta fara daka tsalle cikin wani irin farin ciki. Ya Allah! Yaushe rabona da inji muryar Abbu a rayuwa har na manta, Kun ganni nan kullum ina cikin page dinshi a facebook ina bibiyar rayuwar shi amma na kasa samun kwarin gwiwar kiran shi duk da cewa nayi kewar shi kuwa fiye da tsammanin mai karatu. Ganin kiran yana shirin katsewa yasa nayi saurin dagawa, sallama na mishi a nutse kuma cikin Karya murya, ya amsa cikin wannan muryar tashi cike da kasaita da wani irin huskiness daya kusa saka ni narkewa akan katifata saboda yadda naji wani electricity yana yawo a magudanar jini na. Daga can naji yana magana wadda tayi sanadiyar dawo dani duniyar Earth daga tafiyar da nayi zuwa Mars, cewa yayi “wato Nafeesah idan shekara zamu dauka ba tare da mun gaisa ba hakan bai dame ki ba koh? Ba kya neman mutane idan ba neman ki aka yi ba koh?” da sauri nace “Abbu ba haka bane ba fa!” yayi wata irin sassanyar dariya, “to ya ne Nafeesah?” na dan sosa wuyana tare da dan gyara muryata ina kokarin boye yadda dariyar Abbu ta kassara min gabbai, nace “Abbu muna karatu ne kuma dai bana so in kira ka ko kana aiki ko wani abu in takura ka” ‘ina tsoron ka gaji dani, ina tsoron yin sabo da abinda zai zo yayi hurting dina daga baya” yace “that’s not an excuse Nafeesah, when you feel like calling me just don’t hesitate and call, zan amsa a duk inda nake no matter what m doing” na gyada kai kamar yana ganina nace “toh Abbu” ya sauya akalar hirar zuwa ta harkar karatuna, mun dauki lokaci muna hira kafin yace “Jiya muka dawo daga Beijing, nayo miki lodin tsarabar favorites chocolate crunch dinki, gabadaya na manta baki gidan ashe” nayi shiru kamar ba zanyi magana ba, wani irin dunkulallen abu ne naji ya makale min a kirji da kyar na iya danne shi na bude baki nace “Eyyah!! How I wish ina nan” yace “that’s what m saying” nace “a ba Hafsy shi kawai, Allah ya nufa ba rabo na bane shi yasa” yace “um-uhm, abinda yake naki ne dole ki zaki ci shi Nafeesah. Pretty da kowa yaci nashi don haka kema dole naki zaki ce” na saki murmushi cikin jin dadin maganar shi, a hankali kuma cike da wani irin expectation nace “to ya za ayi yanzu?” shima yayi kasa da muryar shi har tafi tawa yin low, “ya za ayi? M thinking of coming to give it to you, Personally!” na karkada kunnena kamar ban ji sosai ba, sai dana dan yi hesitating kafin a hankali na maimaita “you?? Personally???!” sai dai can kasar zuciyata tsoro ne ya cikata, ina tsoron yace ba haka yace ba kila yace ba haka yake nufi ba…. Ya wanke min zargina ta hanyar cewa “yes, I’ll come to you in baki tsarabar ki Nafeesah!!”. Murnar dana ji ta cika min ciki ta ware a take lokacin da confusion ya dabaibaye ni, nace “amma why would you??” yace “because…. Because…… I…….!!” numfashi na ya dauke yayi sama yaki dawowa, na tabbata zuciyata ta buga sau dari cikin sakwannin da basu fi goma ba ina jiran inji karshen maganar shi, “….. Because I Can Of course Nafeesah!!” sai a lokacin numfashi na ya dawo kasa daga sama din da yayi, na fara yaki da zuciyata wajen ganin gudun da take yi marar adadi da numfashina da yake daidaituwa sun daidaita, a gefe guda wani irin disappointment ne ya lullube min zuciya. I’m such an idiot to think that Abbu zai fada min kalaman so! Yakamata in dawo daga duniyar Fantasy da Tunanin cewa wai Abbu zai so ni, Abbu yana da matar shi har da ‘ya’ya abinsu and duk da cewa maimakon Happily, they are peacefully living together rather. Yace “besides Tu Me Manques!!” na dan yamutsa fuska, “Too mey Manqwe? Me kenan??” yayi er dariya, “just….. Sai anjima dai kawai. And please kiyi Kokari ki dinga kira na fa!” daga haka ya kashe wayar ya barni jiki a sanyaye kuma a sankame. Ajiyar zuciya na saki a hankali tare da saka kaina cikin tafukan hannuwana biyu ina jijjigawa, ji nayi xuciyata ta dauki wani irin zafi, na fara jefawa kaina tambayoyi da suka fara shirin tarwatsa min kwanya, Me ke damuna da Rayuwa ta ne? Me yasa nake son Mazan da basa sona ne? Me yasa zuciyata zata dinga jefa ni cikin damuwa ne a koda yaushe?? Bayan son Muneer da shi bashi ma da mata balle yaya, xuciyata tayi tsalle ta koma kan mutum mai iyali kamar Abbu, Abbu da yake Abokin Daddy na. Me zan fito in gayawa duniya? Anya Duniya ba zata zage ni ba kuwa?? Na dage kullum ina kara nutsa kaina cikin son kogin Abbu ba tare da nayi la’akari da halin da zan jefa kaina da iyayena a ciki ba….. Kafadata naji an dafa, an dago da sauri na kalli Anty Shafa wadda take zaune a gefen gado inda nake zaune, na riga nayi nisa a duniyar tunani ban ma san lokacin data shigo dakin ba.
Fuskarta dauke da damuwa tace min “lafiyan ki lau Nafeesah? Tun dazu nake magana a kanki amma ba kya jina” kai kawai na girgiza mata to ince mata me? ‘Abokin Baba na nake so shi kuma baya so na?’ nasan zagina kawai zata yi ko ta ce bani da hankali, don haka na bame bakina nayi shiru, it’s better to deal with it on my own. Tace “you are lying Nafeesah! ga damuwa nan kwance akan fuskar ki ina gani, kar ki boye min komi kinji? Tell me, me ya faru?” kallonta nayi tare da sake girgiza mata kai ina jifanta da murmushin dani kaina nasan ko idanuna bai Kai ba balle xuciyata, nace “babu komi Anty, it’s just a minor headache” ta kalleni cikin rashin yarda yayin da naci gaba da haske ta da murmushi kawai, sighing tayi tare da mikewa tsaye tace Mommynki ce take cigiyar ki dama shine nace bari in leko in gani ko lafiya? Na mike tsaye nace “bari inje in ganta lafiya na lau” Anty dai ta juya ta fita, na ajiye numfashi a hankali kafin na bi bayanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *