AMININ MAHAIFINA
CHAPTER 9
Aunty Shafa tana ta shirye-shiryen komawa nan da kwana biyu don haka bata zama a gida, tana ta faman ziyarce-xiyarce da sallama gidan en uwa da abokan arziki. Ranar juma’ah karfe sha biyu muka gama lectures, muna fitowa ni da Ramlah daga lecture hall din na hango Harith jingine da motar shi hannunshi rike da lemun team yana sha, yana ganin fitowar mu ya dago mana hannu. Ramlah ta kalleshi ta kalleni tace “wai meke tsakanin ki da Harith ne?” na girgiza kai, “to wa ya sani Ramlah? Nima kin ganni nan ban sani ba wlh” ta tabe baki, “to Allah ya kyauta!” nace “ameeeeen”. Daga nan muka yi sallama. Tun kafin in karasa ya bude min kofar motar, na shiga na zauna ya maida ya rufe. Yana shiga motar na fara jefa mishi korafi ko bari ya tashi motar ban yi ba, “Wai Harith ba nace na yafe zuwa dauka na da kake yi ba?” sai daya tashi motar muka fara tafiya kafin yace “I was just in the neighborhood ne, nayi dropping Sister gidan Amarya Murja ne, shine nace bari in biyo in dauke ki tunda nasan kin gama lectures dinki” nace “ni ban ga kana shirin komawa ba” ya juyo ya kalleni yana murmushi, “why?? Saboda kin gaji da ganina? To babu inda zan koma, na gama karatuna ai” na juya na kalleshi sosai, “woah! Da gaske?” yayi murmushi more like a grinning, “nayi kankanta koh?” kaina na gyada mishi ina kara kare mishi kallo, dariya ya saka har yana dukan sitiyari. Yayi parking a kofar gidanmu, na dauki handbag dina na rataya a kafada nace thanks fa! Ya gyada kai, “Anytime!”. Kallona ya tsaya yana yi, har na saka kafa ta daya waje na juyo ina kallonshi, “meye kake kallona?” murmushi yayi ya kalleni fuskarshi na nuna yana shirin yin serious magana ne, yace “Nafeesah! How about We come together with a plan and help ourselves??” na kalleshi cike da mamaki, “mu taimaki juna? Me kake nufi??” ya daga kafada kamar maganar da zai yi ba mai amfani bace, “you see, there’s this girl that I like…..” yayi shiru yana kallona, ban ji mamaki ba haka babu shock din da naji saboda maganar shi, to ma akan me zan ji mamaki? Hankalina na mayar kan shi gabadaya ina sauraron shi, ya cigaba “she likes me too, sai dai bata son muyi aure nan kusa. Tana karatu a Turkish ne a Abuja and sai nan da shekara biyu zata gama, ni kuma na kosa… U know….!!” ya daga min gira ni kuma na Harare shi, ya kauda kai. Gyaran murya nayi a hankali bayan na gama digesting maganganun shi, nace “to daka gaya min mai kake tunanin zan yi ne??” ya juyo yana fuskanta ta sosai, “I want us to just play a game ta yadda zamu samu wadanda muke so Cikin sauki.” nima na kara gyara zamana, “so??” yace “we will pretend to be lovers infront of them, I mean idan muka yi haka kishin mu zai sa su dawo kan hanya daga kaucewar da suka yi, zamu fara da Muneer ne ko menene? Tunda Ikhram ‘Cara Mia’ sai nan da two months zata zo gida” na hade fuska sosai, take naji raina ya wani baci, a xafafe na harare shi nace “idan har saboda Muneer kake zaton I’ll be your partner in this game then you are wrong Harith, Muneer has become ‘a past’ ya daina existing a duniyata!” ya sadda kanshi kasa embarrassingly, nace “But we can play it with someone, not Muneer dai” ya dago yana kallona fuskarshi dauke da murmushi, “Really Nafeesah? Oh you’re really going to save my life, thank you! But waye wanda zamu bugawa wasan?” nayi rolling idanuna, “just….. By the way meye ma’anar Cara Mia din da kace?” yayi murmushi sosai, “it means My Darling in Russia” na tabe baki nace “wani fi’ili!! Ni kam bari in shiga gida toh!” muka bude motar a tare muka fita yana cewa bari ya shiga ya gaida Mommy. +
A hankali rayuwa tana tafiya tana juyawa, cikin Ikon Allah minti yake shudewa ya zama awowi, awowi su koma raneku, raneku su koma satika kamar yanda satika suke juyewa su koma Watanni. Kimanin watanni biyu suka zo suka shude, ni da Harith mun yi developing wani irin shakuwa a tsakaninmu, da yawan mutane suna cewa soyayya ce a tsakaninmu ciki har da su Mommy da Ramlah, mu kadai dai muka san menene Ainihin Akalar mu da juna. A matukar gajiye muka shiga gidan ni da Daddy a safiyar ranar Sunday kenan muna ajiye numfashi daya bayan daya, Gym muka je wanda yake a cikin unguwar mu kamar yadda muke yi a cikin weekends. Muna shiga falon kicin na wuce na dauko mana ruwa mara sanyi na mikawa Daddy daya, nima na fara shan dayan. Sai da muka dan huta kafin muka wuce dakinmu, ruwa na watsa a jikina na saka kaya kawai na fita falo. Su Mommy har sun fara breakfast don haka nayi joining dinsu, a nutse muke cin abincin, ina jin Mommy tana gayawa Daddy bikin diyar wata Kawarta da za a fara cikin satin, tunda suka fara maganar na sha jinin jikina, a gaggauce na fara tura abincin ina so in tashi in bar musu wajen. Kamar daga sama naji Mommy ta jefo min tambayar da nake gudun tayi, “Ummiey Ke kam yaushe zaki gabatar da naki Mijin ne?” sau biyu kenan tana min maganar turo da wanda muke soyayya wanda nasan Harith take nufi, na turo baki tare da kara cusa fried plantain a cikin bakina, Mommy ta kalli Daddy tace “Habibty kana jin mu fa!” Daddy yayi dariya yace “ina jin ku, kina bukatar bakina ne?” Mommy cike da jin haushi tace “Allah Habibty hakan bai dace ba fa! Yarinya kamar Nafeesah saboda Allah ace har yanzu tana gabanmu babu zancen aure, ina mata zancen ta fitar da miji kuma wai ka wani dinga wani tambaya na ko bakin ka nake bukatar ji?? Anya Habibty kana ma so Nafeesah tayi aure ma kuwa?” Daddy ya kalleta a hankali, duk da cewa maganar Mommy ta taba ranshi amma bai nuna hakan ba, he was very calm. Yace “kema kin san ba abunda nake nufi ba kenan Habibty, naga shi auren nan nufin Allah ne. Duk iya kokarinmu da tursasawar mu a gare ta idan Allah bai nufa ba babu yadda zamu yi. Nima ina son in ga auren Uwata saboda nasan Martaba da Mutunci ‘Ya Mace suna gidan auren ta ba gidan Iyayen ta ba sai dai kin san bana so in tursasawa Uwata ko kadan. Kema din you are just desperate ne, amma duka-duka nawa Nafeesahr take? She’s just Twenty Two Habibty!!” Mommy ta dafe kanta, “Ya Allah meke damun ku ne Kun kasa gane abinda nake nufi?” Daddy ya dafa hannunta cikin sanyin murya yace “mun fahimta Habibty, sai dai muma ki fahimce mu mana. Na fada miki Auren nan….” tayi saurin cewa “naji, naji Habibty ba sai ka maimaita ba!” yayi murmushi, “ki dinga mata addu’ah kawai Habibty, amma tursasawar ki ba shine zai sa ko ya hana ba, only your prayers will” ta gyada kai gami da yin sighing cikin saddakarwa, “To Allah ya zaba mafi Alkhairi!” yace ameeen ko Ke fa Habibty? Na saki ajiyar zuciya a sace, muka ci gaba da cin abincin mu. Can kuma Mommy ta sake dagowa ta kalli sashin da nake, “amma meke tsakaninku ke da Harith ne?” na kalleta, “Mommy, sau dubu nawa kike so in gaya miki babu komi?” Mommy tace “to ku ne na rasa gane inda kuka sa gaba” ni dai na samu na lallaba na bar musu teburin kafin wata maganar ta sake bullowa. Wayata na cire a jikin Caji na shiga cikin whatsapp, dp din Abbu na daga, ya canza shi daga wani hoton shi daya dauka cikin suits bakake ya maida shi zuwa wanda suka dauka shi da ‘ya’yan shi kamar a wani restaurant ne ma, na kura musu idanu ina kallo ina murmushi, precious memories dinmu dasu suka dabaibaye ni, take naji wasu irin kewar su ta cika min ciki, har na latso lambar shi zan buga sai kuma na fasa, na sake latsawa na fasa, a tunanina idan Abbu shi yana namiji ya iya kauda kanshi daga gareni why not ni mace? Tun ranar da muka yi waya dashi bamu sake wata wayar ba sai kimanin sati biyu da suka wuce, shima tambayana yayi wai ko ina da muradin zuwa BUK inyi D.E ni kuma nace mishi A’ah, daga ranar bamu sake waya ba sai dai muna exchanging din text messages dashi. A hankali nayi tsaki tare da ajiye wayar. Littafan makarantana na dauko na fara karatu ko na samu in daina tunanin Abbu. Gabadaya lamarin shi ya fara daure min rai, idan ya kira ni a waya ko ya min text, kulawar dake cikinsu sai su sa inyi zaton so ne yasa hakan, amma yanayin yadda mu’amalar mu take ko kadan bata yi mun kama da wani abu mai kama da so ba. Yatsun hannuna na nutsa a cikin gashina ina jan tsaki ganin har lokacin dai tunanin Abbu ne a cikin raina. Tashi nayi tsam na fara canza tsarin dakina gabadaya bayan na cika dakin da sautin music har sai da Mommy ta leko ta min magana sannan na rage. +
Ranar Laraba a gajiye muka baro makaranta saboda Defense din IT da muka yi, da kyar na iya kai kaina bakin gate saboda gajiya inda nayi shatar tricycle zuwa gida, Harith baya Kaduna kwana biyu kenan, yaje New York wajen hado takardun shi saboda zai fara aiki. Na tura kofar gate din gidan na shiga, yamma tayi likis lokacin. Malam Idi maigadin gidanmu yana zaune a kan dan benci yana sauraron radio, na gaida shi ya amsa da fara’ar shi gami da min sannu da zuwa kafin na wuce falo. Ina shiga sallamar dana fara yi ta kakare a makogorona sakamakon Halittar da nayi ido hudu da ita……….Hafsy!!” na furta a hankali, surprisingly, shockingly. Yarinyar ta taso da gudunta ta nufo ni, da sauri na kai gwiwoyina kasa na tare ta muka rungume juna cikin farinciki muna dariya. Sai da muka nutsa na dago fuskarta daga jikina na kalleta da mamaki, “ya aka yi haka Hafsy? Waya kawo ki?” tace “Abbu ne!!” na zaro ido sosai, falon na karade da kallo babu kowa sai Mommy dake kallon TV abinta, a hankali kamar mai rada nace “Abbun yana ina?” tace “ya tafi wajen meeting, dama meeting zai zo anan shine nace sai ya kawo ni wajen ki” na gyada kai a hankali ina kokarin boye embarrassment din daya lullube ni, I am still a stupid again to think that musamman Abbu ya kawo Hafsy wajena ko shima yazo gani na ne, ko ni a su wa?? Na tashi na kama hannunta nace “taho muje dakina koh?” ta daga min Kai tana watso min jerarrun fararen hakoranta, na wa Mommy sannu da gida ta amsa tana jefo min wani kallo, ban kula da ita ba dai naja hannun Hafsy sai dakina. A can fa hirar yaushe gamo ta barke, naga ta kara girma Masha Allah kamar ba Ita ba…. Tace hutun makaranta suka samu jiya, su Qaseem suna gidan Anty Amernah ita kuma da Abbu yace zai zo Kaduna ta saka rigima sai daya taho da ita. Naja kumatun ta ina dariya nace Kin kyauta. Sai dana canza kayan jikina, muka fita muka ci abinci muka dawo daki na kunna mana cartoon muna kallo ni da ita, ga popcorn a gefenmu da lemu muna sha abinmu. Da yamma na dauke ta muka fita cikin gari, mun sha yawace yawacen mu har muka gaji, sai da aka kira sallar Magrib sannan muka dawo gida. Bayan mun gama dinner muka koma dakinmu, na bude jakar kayanta na fitar mata da kayan barci tasa muka kwanta. +
Washegari har cikin makarantar mu na shiga da ita, bani da lectures kawai yawo muka shiga. Daga karshe dai muka dire a gidan Anty Uwani. Bayan La’asar muna zaune a falo ni da su AbdulMaleek, The Space Between Us muke kallo a tashar MBC, Sultan Babban dan Anty Uwani ya kalleni cikin tsokana, “wai don Allah meye matsalar ki da wannan film din? Last time da kika zo gidan nan ma fa sai da kika kalleshi” nace “kawai film din ya burge ni ne” ya tabe baki, “a haka kuma idan aka cewa mutum yana acting like a child sai yace ba haka ba, Kun zauna nasara suna raina muku hankali Kun hau kai Kun zauna” filon kujera na dauka na jefa mishi ya cafe yana dariya. Daidai lokacin wayata tayi ringing, da sauri na daga ganin sunan Mom, “Ke kiyi sauri ku dawo Baban Hafsat yazo daukar ta!” wani irin faduwar gaba ta ziyarce ni kafin inji wani irin sanyi ya dabaibaye min jiki, jikina har rawa yake yi lokacin dana tashi ina lalubar gyalena da jakata, duk suka bini da kallo mai dauke da alamun tambaya. Na cewa Hafsy ta tashi mu tafi Abbu ne yazo, yarinyar ta tashi tana gunaguni da turo baki, ban ko bi ta kanta ba. Abinda na damu dashi a lokacin kawai shine in ganni a gaban Abbu, in dora idanuna akan fuskar Abbu. Anty Uwani ta fito daga kitchen, cikin mamaki take kallonmu, “ku kuma sai ina haka? Ba dai tafiya ba koh?” nace “Mommy ce ta kira ni yanzu tace muje Abbun Hafsat yazo tafiya da ita” ta kuma kicin ta dawo dauke da Leda wadda aka saka plastic roba a ciki wadda nasan dambun nama ne a ciki sana’ar ta kenan, bakery gareta wanda ake sarrafa fulawa ta hanyoyi daban-daban, suna kuma yin dambun nama a can. Ta mikawa Hafsy ledar tace “ga wannan sai kici a hanya koh?” Hafsy ta amsa tare da mata godiya, su Sultan suka raka mu har waje. Mun bata mintuna goma kyawawa bamu samu abun hawa ba gashi an aiki direban gidansu, Sultan yace “Kema ku jira direba ya dawo mana, sai ya kaiku. Nasan ba zai jima ba yanzu zai dawo” na girgiza kaina, a yadda nake jina dinnan a kagare, gani nake idan da halin inyi fuffuke da wallahi sai nayi, jiran Direban nan daidai yake da buguwar zuciyata ta tsage, nasan tsakanin doki da kaguwa ma ba zasu bar ni. Naja hannun Hafsy muka fara tattaki, Allah ya taimake mu kafin muyi nisa muka samu mai Adaidaita Sahu muka shiga. Bamu muka isa gida ba kuwa sai karfe Shida saura, a farfajiyar gidan Motar Abbu ce a fake a cikin gareji inda ake inda ake ajiye Motocin gidanmu. Zuciyata ta fara wani irin tsallen murna, duk yadda naso in boye farin cikina abun yaci tura. Sai dai muna shiga falo murnata ta koma ciki ganin falon wayam babu kowa, na dan hade fuska. Kamshin abinci na jiyo yana tashi nasan Mommy ce take girki, na shiga kicin din na sameta tana zuba abinci a cikin kuloli tana gani na tace “yauwa, zo ki dauki wannan ki kai sitting room daddynki yana can shi da Baban Hafsat” ban san lokacin dana saki ajiyar zuciya ba a sace, ashe yana sitting room ni ai nayi zaton ya gaji da jiranmu ne ya tafi. Kafin in shiga kicin din babu irin tunanin da ban yi ba a raina, kila ya gaji ya tafi, kila ma bai zo ba gabadaya, kila motar shi ce ta lalace ya ajiye tashi a gidanmu ya dauki ta Daddy ya tafi, tunanika dai barkatai. Mommy ta kalleni ganin yadda nake grinning ear to ear, tace “lafiya?” da sauri na gyara fuskata nace “babu komi” ta min nuni da Tray din data shirya flasks da jugs na ruwa da lemu akai, na cicciba na fita. Sitting room din yana can a karshen falon, kofar shi ta waje ake shiga ta bayan gidan inda ake hango dan karamin garden din gidanmu, amma akwai karamar kofa a falon gidan wadda muke shiga ta ciki. +
Na tsaya a kofar dakin ina kokarin daidaita nutsuwata, a lokacin babu abinda nake da burin yi irin in zubar da kayan hannuna in fada dakin ina tsalle da ihun murna in fada jikin Abbu, if that will not be possible kuma may be I should just shout? So that duniya da mutanen cikinta su san cewa ina cikin farinciki?? Ina jiyo sautin dariyar su dake tashi daga ciki, sautin dariyar shi kadai ma ta saka ni shivering ina ga kallon wadannan sparking brown oily eyes din nashi?? Na cije baki tare da yin knocking a bakin kofar, na tura na shiga a hankali kaina a kasa. Su biyun zaune suke a kan two seats wanda yake Fuskantar kofar shigowa, ina jin kaifafan idanun mutane biyu a kaina, hakan ya dan haddasa min hardewar kafafu. Na dora kayan akan table din dake tsakiyar dakin, na kuma zube anan kusa da teburin, “Abbu ina yini?” na furta a hankali kamar wadda take tsoron yin magana, cikin muryar nan tashi cike da ginshira ya amsa da “lafiya lau Nafeesah er Daddyn ta, kina lafiya?” Daddy ya mishi rada a kunne ban dai san me yace ba na dai ji sun kwashe da dariya a lokaci guda, na kara yin kasa da kaina ba tare dana amsa tambayar Abbun ba. Daddy yace “matso nan Uwata ki zuba mishi abincin, yanzu zai wuce” sai lokacin na dan daga kaina na kalleshi, ina dagowa muka hada ido dashi, nayi sauri na janye nawa idanun. Ban san ya aka yi ba kuma sai sake tsintar idanunshi a kaina nayi ina ga zuciyata taki aminta da hakan ne shi yasa na sake kallonshi ba tare dana shiryawa hakan ba, wannan kallon murmushi yake yi, yace ba tare daya dauke idanunshi daga kaina ba, “Ni fa ba yunwa nake ji ba, zan ci abinci idan muka isa gida” Daddy bai kula shi ba yace “zuba mishi abinci Uwata” na zaro plate na bude flask din na fara zuba Jollof din spaghetti sai da yawu na ya guda saboda yadda kamshinta yake tashi, na tsiyaya kunun aya mai sanyi a cikin cup na dora fork akan plate din na ja teburin zuwa gabanshi, kamshin turaren Hugo boss ya doki hancina lokacin dana matsa gab dashi, na dan lumshe idanu lokacin dana bude hanci na shaki kamshin ina jin wani irin shauki. Ina ajiyewa na kalli Daddy da niyar in tambaye shi ko in zuba mishi ne shima, yace “ni ba yanzu zan ci ba Uwata je ki kawai” na dan yi murmushi na mike na bar musu dakin. Hafsy na zaune akan kujera tana cin nata abincin Mommy kuma tana dakinta, na wuce dakina na shirya kayan Hafsy a cikin Jakarta. Na ciro wasu takalma dana siyo dama nace Hafsy zan ba shi, naje siyan takalmi ne irin shi ya burge ni kuma sosai sai dai babu size dina don haka na siya daidai size din Hafsy duk da ban san ranar da zan bata shi ba. Na kara duba wardrobe dina babu abinda na gani wanda zan bata sai kayan kwalliya kawai na kara mata, na dauki jakar na fita falo. Ina zama Daddy ya shigo falon yace Hafsy ta fita Abbu yana jiranta, tayi raurau da idanunta alamun bata so tafiya ba har ta bani dariya. Na kama hannunta na tasheta tsaye, Mommy ta fito daga dakinta hannunta dauke da leda ta mika mata, Daddy kuma ya ciro kudi daga aljihunshi ya bata. Na dauki jakar ta muka fita, Abbu har ya fiddo motar daga cikin gareji. Na budewa Hafsy passengers seat ta shiga ta zauna, na bude gidan baya na ajiye mata jakarta. Na kalli Abbu da shima yake kallona, cike da damuwa nace “Abbu ba zaku yi hakuri da tafiyar nan ba zuwa gobe kaga fa dare yayi” ya girgiza kai, “kar ki damu, ai In shaa Allah yanzu zamu isa, nan da Kano ai babu nisa” na rausayar da Kai gefe, “shi kenan since you insist, Allah ya kaiku lafiya” yace “Ameen” ya dauko wani kwali anyi wrapping dinshi da gift ribbon ya miko min, babu musu ko tambayar dalili nasa hannu na amsa, “nagode Allah ya saka da alkhairi” na furta a nutse, yayi murmushi “sai gani na biyu koh Nafee??” na kalleshi ina so in tambayeshi gani na biyu kuma as in how? Sai dai irin murmushin dake kan fuskarshi a lokacin ya daskarar dani na kasa daga bakina, ya tashi motar yana kara jifana da murmushi a hankali yaja suka fita, da kyar na samu kuzarin daga musu hannu ina waving dinsu har suka fita daga gate din gidanmu. Na juya a hankali na koma cikin gida, baby kowa a falon nasan suna daki zasu daura alwala saboda naji ana kiran sallar magrib. Nima na shiga dakina na ajiye abinda Ke hannuna akan gado naje na dauro alwala.
**********
Na kwanta rub da ciki akan gadona ina jujjuya wayata a hannu kamar ina jiran wani abu, koda yake jiran kira ko text din Abbu nake yi. Gabadaya raina ba a kwance yake ba da tafiyar nan ta dare da suka yi, gashi tun karfe shida da rabi har karfe tara babu alamun kiran shi bayan nasan duka-duka tafiyar bata fi ta awa biyu ba. Kamar yasan ina jiranshi, text din shi ya shigo wayata, “mun iso Kano lafiya lau, Pretty tana gaida ki” nayi saurin typing “Masha Allah! Sannunku da zuwa” na tura mishi. Sai a lokacin naji kuzari ya shige ni, na tashi zaune na bude kwarin daya bani. Tarkacen chocolates ne da cookies a ciki, daga kasan su na ciro wani frame, hannun mace da namiji ne sarke dana juna a jiki, anyi kananun rubutu da wani irin yare wanda ban fahimce shi ba, daga kasan hannun nasu dai anyi rubutu in bolds kuma in capital letter……. *”TOI ET MOI POUR TOUJOURS! (You And Me Forever)”* Na danyi tsaki kadan, ban san me yasa Abbu yake son rubuta min abu da wani yare na aljanu ba, saboda Allah how in hell would I be able to understand what is written there?? Na kara jan tsaki naje na rataye frame din a jikin bango.Abinci nake ci amma gabadaya hankalina baya kan abincin na dai san kawai ina kwaso abinci da spoon ina saka shi a cikin bakina, tunanina ya tafi ga yadda Mommy take acting weird tun zuwan Abbu, no tun zuwan Hafsy ma. Bayan su Abbu sun tafi jiya, mun gama dinner kenan na shiga daki Mommy ta biyo bayana, sam babu alamun wasa a fuskarta ta kalleni, “Ummiey me ke tsakanin ku da Baban Hafsat?” na kalleta da sauri kuma cike da mamaki, tambaya ce mai sauki, haka kuma amsar ta ba mai wahala bace, amma me yasa naji kamar ba’a taba tambayana tambaya mai wahala irin wannan ba? Saboda ni a karan kaina ban san me ke tsakanin mu ba. Kai na girgiza mata, “Mommy me kika gani ne?” ta Harare ni, “Ummiey ba cewa nayi ki tambaye ni ba, amsa nake bukatar ji; Me Ke Tsakanin Ku Ke Da Baban Hafsat?” na danyi shrugging kafadata ina kokarin nuna babu komi, “me ke tsakanin mu kuwa Mommy? He’s just Daddy’s Friend, and I stayed with them for a while I think that’s all!” tace “That’s all?!” na jinjina mata kai cikin tabbatarwa, “yes!” tayi shiru tana kallona kafin ta sauke ajiyar zuciya, “ko ma dai Menene Ummiey, Ina fata zaki tsaya a iya inda Allah ya ajiye ki, and alakarku ta tsaya a haka Nafeesah, No more…. Bana son wani magana ya fita daga baya kina jina??” kallonta nake cike da mamaki, me ke damun Mom ne haka yau? Duk da hakan ban fasa daga mata kai ba, sai lokacin naga tayi murmushi. “good! Hurry up and go to bed then” nan ma Kai na sake gyada mata, “sure Mom, good night” tayi murmushi ta juya ta bar dakin tare da ja min kofa. Sosai maganganun Mom suka tsaya min a rai, ranar haka na kwanta ina nanata maganar ta, ‘In tsaya a matsayin da Allah ya ajiye ni?? Kada wata magana ta sake fita bayan alakar mu ta yanzu? Tana nufin kenan ba zata amshi Abbu a matsayin miji na ba? ‘Miji??’ naji na sake maimaita kalmar., wa yace Abbu zai zama mijina? Ni kadai nake imagining komi a cikin raina ba tare da tunanin shi Abbu din me yake tunani ba. Ni kadai nake tunanika na na manta da cin amanar da nake shirin yi, to cin amana mana! Na zauna lafiya qalau da iyalan Abbu cikin mutunci da girmamawa, daga karshe kuma kawai sai aji na aure mai gida? Anya na kyautawa kaina dasu kuwa? Me zan ce musu to? Me zasu daukeni, maciya Amana ko me? Su Qaseem………. Shit!!! Me zasu dauke ni yanzu? Suddenly naji wata irin kunyar kaina ta kama ni, I wasn’t thinking straight and smart. Ni da Abbu belongs to different worlds, I think it’s time for me to let him go., let my dreams scattered just like how I did with my first love; Muneer!! Zuciyata tayi zafi sosai, m really an unlucky being!! Me yasa ban taba samun nasara akan soyayya ba a rayuwata? I mean me na rasa? I am a very beautiful and attractive young lady in my twenties, ina da kyau ina da diri ina da duk abinda namiji yake bukata a jikin mace but why?? Why???……. +
Ramlah ta dawo da hankalina cikin restaurant din ta hanyar jijjiga ni, “hey babe!! Come back to your senses!!” na zabura ina kallonta a tsorace kafin in Harare ta, “What?!” na fada almost shouting, tace “Ke zan tambaya, you were deep in a thought and you suddenly became teary, me ke faruwa dake ne yau?” na kai yatsa na dan taba idanuna, da gaske kuwa I was about to cry ga ruwan hawaye nan ya fara taruwa a idanuna. Ta rungume hannayenta a kirji tana kallona cike da tuhuma, na sauke kaina kasa kawai ina wasa da cokalina a cikin plate, I wasn’t ready to discuss the matter with anyone a lokacin, I wanted to dealt with anything on my own don haka na share Ramlah kamar ban san abinda take nufi da hakan ba har sai data kai ga yin magana, “ba zaki magantu bane har sai na matse bakin ki?” na kalleta, “Ramlah am sorry ok? When I’m really, zamu yi maganar please!!” na fada pleadingly don nasan halinta zata iya takura ni, hakan kuwa daidai yake da saka kuka na a cikin restaurant din makarantar mu. Tace “da gaske?” na gyada mata kai, tace “ok, kar ya dade fa kin san bana son jira koh?” na sake gyada mata kai. Na dauki lemun exotic na pineapple na kai bakina, kamar kamar ruwa haka na dinga zugar shi sai kwalin kawai na ajiye kasa. A tare muka mike muka fita daga restaurant din, muna fita naji Ramlah tana xunguri na a bayana, na harareta, baki ta tabe cikin gulma ta rada min “mutumin ki is coming” na kalli inda ta nuna min da idanunta, Muneer ne tafe shi da abokanan shi suna tahowa inda muke da alamu restaurant din zasu zo. Naji ana zancen auren shi da aka daura last week, personally ya turo min Invitation Card na bikin nashi amma a take na aika aka maida mishi Ita don ban ga abinda zan je inyi a wajen bikin ba. Tsaki naja na fara tafiya abina, Ramlah ta biyo bayana, muka yi clashing dasu amma Muneer ko glancing at our side bai yi ba. Na kara jan tsaki a raina nace “banza dan akuya!” satika uku da suka wuce he was still following me around like crazy yana begging dina akan in bashi second chance shine yanzu daga yin aure Sati daya yana share ni irin yaji dadin Amarya dinnan, na kara jan tsaki. As if I give a damn! Kamata yayi inji da damuwata ba wai ta wani Muneer ba. Hostel muka wuce ni da Ramlah saboda bamu da lectures ranar, next week zamu fara exams already mun yi covering lectures dinmu. Muna kan gadonta muna solving din wata problem a Calculus wayar ta tayi kara ta daga, ta dauki wayar ta kalli caller ID din, “Ni’ima ce” ta daga kiran tare da sakata a hands-free, “Guess what guys??” muryar Ni’imah ta doki kunnenmu cikin farinciki, muka hada baki wajen cewa “ya ne? Bamu mu sha please!” tace “umh…. Dama……” ta fara kauce kauce, Ramlah taja tsaki, “malama aiki muke yi idan ba zaki fada ba ki kashe wayar kawai” sai data gama kauce-kaucenta sannan tace “aure aka sa mana…. Nan da one month!!” “WHAT??!” muka fada cikin karaji in Unison. +
“What the f**k! Wannan ai rashin mutunci ne Ni’imah” inji Ramlah tana hararar wayar kamar Ni’imar tana gabanta ne, nima nace “Lallai mu da aka raina ne sai yanzu ake fada mana, ba zan zo ba don ma kiji” Ramlah ma ta cafe nan ma muka hau korafe-korafe har sai da muka rasa abin cewa sannan muka yi shiru, Ni’imah dai saurarenmu kawai take yi, ina jiyo dariyar Sa’adiya daga background din wayar. Tace “duka-duka jiya ne aka yi abin fa!” muka yi kus, ta cigaba, “muma bamu yi zaton abun will be so soon ba kawai jin su muka yi Kun gane? Now na isar da sakon da zan isar shikenan, Kun dai san you guys are needed one week before a fara bikin ko?” muka yi dariya ni da Ramlah, “yeah of course, ai dole ne. Thank God we’re finishing our exams nan da sati biyu” muka yi sallama dasu, littafin da muke karantawa muka maida gefe muka fara hirar yadda zamu gudanar da bikin, wannan hirar ita ta dauke min tunanina gabadaya akan maganar Mom da sauran su.
*****
Daddy ya kalleni, “yanzu Har Sati daya kawai saboda biki Uwata?” na turo baki gaba, “haba Daddy, su Ni’imah ne fa, kuma lokacin muna free tunda mun gama exams dinmu fa!” ya rausayar da kai, “ai shikenan! Allah ya kaimu” nayi tsalle akan kujera daga zaunen da nake ina clapping hannu, “nagode Daddy! That’s why you’re always the best!” na mishi thumbs up da duka hannuwana, yayi dariya. Naci gaba da duba littafin hannuna shi kuma ya cigaba da kallon tashar Sports. Can na tambayeshi game da DE form din da yace zai sa a cika min, yace “ni na ma manta wallahi. Bari zan sake yiwa Ibrahim Magana inji yadda ake ciki” nace “Daddy Abbu kuma? Me yasa shi? Ni da ABU nake so in cike?” yace “ba kya son zuwa BUK din ne, me yasa?” na turo baki na, “ni nafi so ina kusa daku Daddy yadda kullum ba zan sha wahalar ganin ku ba!” yayi dariya yace “Uwata kenan! To in kika yi aure kuma fa? Kin san dai dole ki bar gidan nan koh?” na sake turo wani bakin, Mommy ta shigo dakin hannunta dauke da plate wanda aka yanka fruits a ciki. Ta kalleni kafin ta maida kallonta ga Daddy, “Habibty ina fata ba gulma ta kuke yi ba koh?” Daddy yace “mun isa! Diyar ki ce take zancen bata so ta rabu damu” Mommy ta ajiye plate din a tsakiyar dakin duk muka sauka kan carpet tace “Rabuwa kuwa ai ya zama dole tunda dai ke diya mace ce kuma Aure zaki yi” ‘Ai fa an tabowa Mommy inda yake mata kaikayi’ na fada a cikin raina, kwana biyun nan dama Mommy kamar mai jira, da an danyi magana zata hau zancen aure da waye da waye. Sai da muka cinye fruits din tas na dauke plate din tare da musu sai da safe, na kai plate din kicin kafin na wuce dakina nayi shirin kwanciya barci. Na budo hoton Abbu a cikin gallery dina ina kallo kamar yadda ya zama Al’adar rayuwata kowane dare, na janye idanuna daga kan hoton nashi na maida su kan frame din daya bani. Ban san meye dalilin da yasa ya bani frame din ba, ban san me yasa nake jin wani irin warmness da calmness a tare dani a duk lokacin dana kalli frame din ba. Koma dai menene na yanke shawarar janye Idanuna da Zuciyata daga kan Abbu. We didn’t Deserve Each Other.