AMRAH NAKESO CHAPTER 1

AMRAH NAKESO CHAPTER 1

Www.bankinhausanovels.com.ng 

_Ranar talata, karfe 4:25 na yamma._

Sanye take cikin zureriyar hijabi ruwan ƙasa mai hannu. Hannunta wanda ta fiddo wajen hijabin riƙe yake da wata makimanciyar jaka, a ɗayan hannun kuma wayarta ce ƙirar Samsung S7 edge.

A hankali cike da natsuwa take taku har ta isa bakin gate ɗin Islamiyar tasu.

Ɗalibai ne ke shiga manya da yara, maza da mata.

Ɗaga kanta ta yi a dai-dai saman gate ɗin ta kalli rubutun da aka yi wanda fenti ne fari sai rubutun kalar tsanwa an rubuta *MADRASATUL-AMRAH BNT ABDALLAH.* Da larabci aka yi rubutun sai kuma daga ƙasa aka rubuta da hausa.

Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa bayan ta gama karantawa ta gyaɗa kai hawaye na zirara daga idanuwanta.

Cikin makarantar ta nufa kai tsaye ta nufi ajinsu mai suna *FASLUL-KHAMIS (ALIYU BN ABI ƊALIB)*

Jiki a mace ta zauna kujerar gaba wadda ita ce kujerarsu. Saurin goge hawayenta ta yi jin Jidda na faɗin “To uwar hawaye. Wani abun ne hala?”

Murmushi ta ƙirƙiro tare da faɗin “Babu komai Jidda. Me kika gani?”

“Fuskarki na gani kamar kin yi kuka. Kuma na san baya miki wahala dama.” Jidda ta faɗa bayan ta dawo bisa kujerar ita ma ta zauna.

“Ko kaɗan ban yi kuka ba. Iskan nan da ake ne ina hanya ƙura da ƙasa suka buɗaɗe ni har cikin ido. Shi yasa idona ya canza launi, kuma ga raɗaɗi da yake yi min.”

“Allah sarki! Ba laifi kam ana iska. Allah Ya kyauta. Yau kin makara, lafiya dai ko?”

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce “Na yi lecture ne 2-4, ina dawowa a makare ko abinci ban tsaya na ci ba na taho Kuma gashi ma ashe malam bai shigo ba.”

Kafin Jidda ta bata amsa sai ga wani malami ya shigo hannunshi riƙe da Umdatul-ahkam.

Bayan ya yi sallama sun amsa ne suka gaishe shi tare da fito da littattafansu suka buɗo dai-dai inda zasu tashi.

Ɗaya bayan ɗaya sai da kowa ta karanto inda aka masu baya sannan malamin mai suna Malam Yusuf ya yi masu ƙari kasantuwar ya ga mafi rinjaye sun fahimci darasin da ya gabata.

Yana fita Mallam mai Fiqhu ya shigo shima ya masu darasin sannan aka tashi daga makarantar.

Bayan sun fita sai da budurwar ta sake ɗaga dara daran idanuwanta ta kalli sunan Islamiyyar cike da tausayi sannan ta sunkuyar da kanta ƙasa ta tafi gida. A zuciyarta tana mai tsananin ƙagara ranar jumu’a ta yi.

***

Da sallamarta ta shiga gidansu wanda yake ba wani babba sosai ba, sai dai daka ga gidan ka san suna da rufin asirinsu bakin gwargwado.

Wata matashiyar mata wadda ba zata wuce shekara talatin da biyar (35) ba ta amsa sallamar tana murmushi ta ce “Maryama an dawo?”

“Na dawo Mama. Aiki ake?” Ta tambaye ta bayan ta ƙarisa shiga Kitchen ɗin.

“Wallahi kuwa. Abbanki ne ya kirani wai yana son tuwon dare, shi ne fa na tashi da azama na ɗora masa. Har ma na gama tuwon miya ce ta rage.” Maman tata ta faɗa tana zuba man-ja a tukunya.2

“Kawo na ƙarisa miki Mama.” Maryama ta cire hijabinta ta rataye a kan ƙofar kitchen ɗin haɗe da jingine jakarta jikin bangon kitchen.

“A’a Maryama. Ke da kika dawo daga makaranta? Na tabbata a gajiye kike, saboda ko abincin rana baki ci ba kina dawowa daga lecture kika yi shirin islamiya. Je ki cire Uniform ki zo kafin nan na zuba miki abinci.”

“Wallahi Mama bana jin yunwa. Ki kawo na miki tun da dai ba wani aiki nake ba. Kullum ina makaranta ke ce kike yin komai. Dan Allah ki bari ni ma yau na samu wannan ladar.”

Mama ta murmusa ta ce “Tun da dai kin matsa gashi nan ki ƙarisa. Allah Ya miki albarka ke ma Ya haɗa ki da wanda zasu kyautata miki kamar yanda kike kyautata min.”

“Amin Mama.” Ta faɗa haɗe da karɓar ludayin miyar ta kwashe jajjagen tarugu da albasa da daddawa dake cikin turmi.

Cike da natsuwa Maryama ta kammala miyar busasshiyar kuɓewa ta barta a buɗe dan kar ta rufe ta tsinke.

Hijabi da jikarta ta ɗauka sannan ta nufi ɗakinta domin gabatar da sallar magrib.

Bayan ta gama ta zauna ta yi adhkar har lokacin isha’i ya yi sannan ta fito sanye da dogon hijabi har kasa ta nufi ɗakin Abbanta.

Zaune yake shi da Mamanta sai kuma ƙaninta zaune a kasa.

Cikin ladabi ta gaishe da Abban nata sannan ta ce “Sannu da hutawa Mama.” Ta zauna a ƙasa kusa da Muhammad.

“Yauwa Maryama. Ai ke ke da sannu.” Ta mata murmushi.

“Yaya Maryama sannu da aiki.” Muhammad ɗan kimanin shekara goma sha biyu ya faɗa.

“Yauwa ɗan albarka. Ya tahfiz ɗin?” Ta tambayeshi.

“Akwai wahala Yaya. Ko yau na sha zana duba bayana ki gani.” Ya faɗa yana ƙoƙarin ɗaga rigarshi ta baya.

“Ba sai ka ɗaga min ba dan ba tausayinka zan ji ba. Ban san me ya sa ba Muhammad baka son karatu.” Ta faɗa bayan ta haɗe fuskarta babu alamun wasa.

Cikin sigar a tausaya masa ya ce “Ina fa karatu Yaya. Malamin namu ne…” Ta yi saurin dakatar da shi,

“Kar ka ma malaminku sharri. Idan baka masa laifi ba ai ba zai dake ka ba. Ka ringa karatu sosai kuma ka guji aikata laifi ka ga idan akwai malamin da zai taɓa lafiyarka.”

Shiru ya yi kafin ya yi dariya abinku ga ƙaramin yaro ya ce “Kuma fa Yaya kin yi gaskiya. Kin ga Haneef shugaban ajinmu ba’a dukansa saboda kullum sai ya bayar da harda babu tangarɗa. Kuma baya laifi ko kaɗan.”

“Ka gani ba. Kai ma sai ka yi koyi da shi ai, idan baka son duka.” Ta faɗa tana masa murmushi.

“To Yaya. Bacci nake ji ma.” Ya yi hamma.

“Bara na kawo mana tuwo sannan kaci ka yi bacci ko?” Ta miƙe tsaye.

Mama ta ce “Ai ni dai kawaici na yi dan na ga kuna fira da Muhammad. Yunwa nake ji wallahi.”

Abba ya ce “To ai gashi nan zata kawo yanzu” Ya murmusa.

Ta nufi kitchen tana murmushi.

Misalin karfe tara suka kwanta kamar yanda suka saba da wuri suke kwanciya bacci gidan.

*RANAR JUMU’AH 10th January 2015*

Ranar da Maryama ke tsumaye ke nan. Ranar data matsu ta yi har tana ganin tsayin wannan ranar.

 k’agare take ta iso gida domin tafiya Islamiya, amma wani Malaminsu ya rik’e su har kusan k’arfe biyar na yamma. Yi take tana duba agogon wayarta, baki d’aya hankalinta ya koma ga ta tafi, har wasu hawaye take ji suna k’ok’arin fito mata.
Jin hak’urinta ya k’ure ya sa ta tattara ya-nata ya-nata ta mik’e tsaye, tun kafin ta fito daga row d’insu ta ji muryar malamin yana masu bankwana alamun ya gama lecture d’in ke nan.
Ajiyar zuciya ta sauke, had’e da godiya ga Allah sannan a hanzarce ta fita, ko k’awar tata ma bata tsaya jira ba.
Course mate d’insu Saifulla
hi ta gani bisa mashin d’inshi da alama yana jiran wani ne, amma Maryama sai da ta rok’e shi a kan ya taimaka ya tafi da ita sauri take.
Bai ko musa mata ba ya ce ta hau su tafi.
A maimakon ta kwatanta masa gidansu sai bata yi ba, islamiyyarsu kai tsaye ta sa ya kaita.
Cikin mamaki Saifullahi ya ce “Yau Friday ana Islamiyya ne Maryam?”
“Ba darasi zamu yi ba Saif, akwai abin da muke ne.” Ta bashi amsa tana mai k’ok’arin sauka daga bisa mashin d’in. “Na gode k’warai Allah ya bar zumunci.”
“Ameen Maryama. Allah ya bada sa’a. Sai anjima.” Ya tada mashin d’in ya tafi.
A gaggauce ta isa bakin gate d’in, ta samu mai gadin zaune da radio rik’e a hannunsa.
“Sannu Baba. Mun yi da kai da an yi la’asar zan zo kuma sai gashi na kasa cika al-k’awari ko? Yi hak’uri, wallahi wani malaminmu na tsaya ya sallame mu.”
Murmushi dattijon yayi ya ce “Babu komai ai. Kina lafiya ko?”
“Lafiya lau Baba. Mu tafi gidan nasu ko?” Ta tambaye shi.
D’aga mata kai ya yi tare da jawo ‘yar k’aramar k’ofar da ke jikin gate ya rufe da kwad’o sannan ya soka makullin a al-jihunsa.
Mashin d’insa ya hau sannan ita ma ta hau daga baya suka kama hanyar unguwar Gidan dawa da ke cikin Birnin Katsina.
Tafiya mai nisa ce ta sada su da gidan, kasantuwar akwai ‘yar tazara daga Islamiyyar.
Bayan sun isa Malam Sallau ya kashe babur d’insa sannan ya ce “To Maryama mun iso, kin ga gidan nan.”
K’ok’arin sauka ta yi a hankali bisa rashin sani har k’afarta ta d’an gogu a salansar mashin d’in, ta k’one kad’an.
“Subhanallahi!” Ta furta a hankali bayan ta k’arisa saukowa.
“Bi a hankali dai Maryama.” Ya fad’a bayan ya gyara tsayuwar babur d’in.
“Mu shiga ko?” Ta fad’a cikin sanyin murya.
“Anya kuwa? Ki shiga dai, ki sanar da su idan sun bani izinin shiga sai in shigo.”
Kallonshi ta yi kamar kar ta yi magana kuma dai ta daure ta ce “To Baba ai kuma basu san ni ba.”
Da murmushi ya ce “Babu komai ai. Ki shaida masu cewa tare kike da Mallam Sallau, ba damuwa.”
D’aga kai ta yi tare da shiga cikin gidan da sallama k’unshe a bakinta.
Gida ne ginin har k’asa irin na da, wanda kallo d’aya zaka masa ka tabbatar cewa gidan mabuk’ata ne.
Shiru ba’a amsa ba hakan ya bata damar sake yin wata sallamar nan ma dai shiru.
STORY CONTINUES BELOW
Sai a karo na uku sannan ta ji muryar dattijuwa ta amsa sallamar tana k’ok’arin fitowa daga cikin d’aki.
Ganin Maryama ya sa ta d’an saki murmushi irin ba wai dan ta santa ba, sai dan karamci kawai.
“Barka da zuwa. Iso daga ciki mana.” Matar ta fad’a fara’a k’unshe a fuskarta.
Kai ta d’aga alamar to, sannan ta k’arisa ciki.
Tabarma matar ta shimfid’a mata sannan ta bata izinin zama ta zauna.
“Sannu Mama. Ina yini.” Maryama ta furta cikin girmamawa.
“Lafiya k’alau ‘yan mata. Sannu fa.” Ta fad’a cikin rashin wayarta.
“Tare nake da Mallam Sallau, yana waje.” Ta fad’a tana kallon Matar.
“Allah sarki! Yo to kuma ai da sai ya shigo ko? Shi dai Mallam Sallau kullum kamar bak’o. Dan Allah je ki k’ira sa da sauri. Mallam!” Ta k’walawa mai gidanta k’ira.
Tashi Maryama ta yi ta nufi waje tare da k’iran Mallam Sallau. Tana gaba yana biye da ita suka shigo ciki.
Matar ce zaune a bisa tabarmar sai mai gidanta a kusa da ita yana murmushi.
Mik’ewa ta yi da sauri ta ce “Mallam Sallau zauna daga nan. ‘Yan mata zo mu shiga daga ciki ko?”
Da sauri Mallam Sallau ya ce “Ahh babu damuwa, ku zauna kawai, ai magana zamu yi.”
Hannu ya mik’awa mutumin zaunen suka gaisa sannan ya zauna a kusa da shi.
Maryama kuma aka shimfid’a masu wata tabarmar suka zauna tare da matar.
Bayan sun gama gaggaisawa ne Mallam Sallau ya ce,
“Wannan yarinyar sunanta Maryama. D’aya daga cikin d’aliban Islamiyar *AMRAH BNT ABDALLAH.* Ta jima tana son sanin tarihin rayuwar *Amrah* tun daga lokacin da aka yi wani wa’azi; wanda Malamin ya d”auko zancen *Amrah* tun bai yi nisa ba kuma sai lokaci ya k’are. Tun daga lokacin take son sanin *Wacece Amrah?* ta same ni da maganar ya fi sau biyar, tun ina gudunta da maganar dai har na ce ranar wannan jumu’ar ta zo zan kawo ta domin ta ji daga gare ku. Ina fatan hakan ba zai zama takura ba.”
Kallonsu suka mayar ga Maryama da ta d’an sunkiyar da kanta k’asa tana wasa da ‘yan yatsun hannunta.
Matar ta ce “Allah Sarki!” Tare da share d’an siririn hawayen da ya fito mata.
Shi kuwa mutumin cikin k’arfin hali ya ce “Babu wata takura Mallam Sallau. Sai dai kuma gashi yamma ta yi yanzu magrib ta gabato.”
Mallam Sallau zai yi magana Maryama ta yi saurin fad’in,
“Ehh wallahi. Babu damuwa ai ko gobe ma sai in zo ko da ni kad’ai ce. Tun da dai mun zo tare na ga gidan.”
“Haka ne. Allah Ya kaimu to.” Mutumin ya fad’a.
Cikin k’arfin hali Matar ta ce “Insha Allahu gobe zaki ji tarihin rayuwar *Amrah.* Zaki san ko wacece *Amrah Bnt Abdallah.* Ta sake share hawayen bisa kumatunta.
Sosai Maryama ke mamaki, lallai ta yarda cewa babu abin da ke cikin *Rayuwar Amrah* face tsabar tausayi, duk da yake bata san komai ba, abin da ta sani dai kawai ita Amrah d’in mace ce mai matuk’ar halin kirki, wacce ke da tarihi mai kyau kuma abin koyi.
Bankwana suka yi ta masu godiya sosai sannan suka fita waje ita da Mallam Sallau.
Har gida ya kai ta ta masa godiya sosai ta shiga ciki.
Tana shiga bata samu kowa a tsakar gida ba, kai tsaye ta zarce ciki.
Muhammad ne da gudu ya rungume ta yana fad’in “Yaya Maryama kin dad’e fa. Ina ta jiranki ki dawo ki koyan karatu, gashi gobe da sassafe zan bada harda kuma ban iya ba.”
Da murmushi ta ce masa “Wallahi Muhammad na je wani wuri ne bayan na tashi daga makaranta. Amma gashi na dawo ai yanzu sai mu yi. Mama fa?”
“Tana cikin d’aki yanzu Baba ya dawo ne. Zaki koyan yanzu ko sai an yi sallah?” Ya tambaye ta.
“Bari a yi sallah tukuna. Ka ga fa ko abinci ban ci ba. Kar ka damu insha Allahu zan koya maka har sai ka iya sannan zamu daina.” Ta sakar masa murmushi.
Shi ma murmushin ya sakar mata ya ce “Allah Ya yarda Yayata. Ki je yanzu ki yi wanka ki ci abinci ko?”
Kai ta d’aga masa sannan ta shige d’akinta.
Jakarta kawai ta ajje sannan ta yi wanka ta fito
Ta samu har Mama ta kawo mata abinci ta rufe da plate, ga kuma abin sha nan a jug da k’aramin cup
Murmushi ta yi mai cike da nuna jin-dad’i,
“Wayyo Mamana. Allah Ya saka miki da alkhairi.” Ta fad’a sannan ta zauna ta fara ci. Zuciyarta cike da tsumayen gobe ta yi, duk da yake cewa akwai Islamiyya kuma bata son ta yi fashi amma fa bata jin zata iya hak’ura har a tashi. Ta k’udurta cewa da yardar Allah gobe k’arfe goma a gidan su Amrah zata mata.
Bayan ta gama ne ta koyar da Muhammad karatu har ya iya sosai sannan ta koma d’akinta.
Wayarta ta latso lambar Jiddah, babu jimawa kuwa ta d’auka.

Sallama ta yi bayan sun gaisa ne take shaida mata cewa idan ta je Islamiyya gobe ta fad’a ba zata samu damar zuwa ba, akwai inda take son zuwa ne.
Jidda ta ce “Kin manta gobe akwai rehearzal (Gwajin koyo) k’arfe tara? Da dai kin yi hak’uri Maryama, ko idan kika yi naki ne sai ki tafi.”
Jinjina kai Maryama ta yi ta ce “Jiddah kin san fa ba lallai Mallam Ahmad ya bar ni tafiya ba duk iya k’wa-k’wata kuwa. Gashi kuma inda zan je yana da matuk’ar muhimmanci.”
“To shi ke nan babu damuwa. Zan sanar ma Mallam Yusuf shi ne mai sauk’in kai. Allah Ya taimaka.”
Murmushi Maryama ta yi ta ce “Yauwa na gode k’warai Jiddah. Sai da safe, ki gaishe da Mami.”
“Zata ji.” Ta tsinke wayar.
Jikin chaji ta jona wayar sannan ta koma ta kwanta. A zuciyarta tana nazarin wata magana wadda ita kad’ai ta saka ta fashewa da kuka.
Juye-juye kawai take yi bacci ya k’i d’aukarta, da k’yar ta samu ya d’auke ta a lokacin har sha biyun dare ta wuce.Washe gari tun da safe ta tashi ta hau shiri, k’arfe bakwai da rabi Muhammad ya shigo da gudu yana fad’in,+
“Yaya Maryama na shirya, wai ki fito in ji Baba.”
Juyowa ta yi ta kalle shi ba tare da ta ce komai ba, sai dai kuma kallon da ta masa kawai ya isa ya tabbatar masa da laifinsa.
“Yi hak’uri Yaya Maryama.” Ya fad’a a marairaice.
“Oya get out.” Ta gwada masa k’ofa da hannu.
Kama kunnuwansa ya yi ya ce,
“Zan yi yanzu Yaya.” Ya fita daga d’akin.
“Assalamu alaikum.” Ya fad’a da k’arfi wanda har sai da dariya ta nemi k’wace ma Maryama.
Amsa sallamar ta yi ta ce “Ko kai fa. Ka tafi kawai Muhammad. Ka ce da Baba akwai inda zan biya ne kafin in tafi. Kar in tsaida ku kuma na san tahfiz d’inku babu wasa. Ka ga ko karyawa ma ban yi ba.”
“To shi ke nan Yaya. Na tafi.” Ya yi gaba.
Addu’a ta masa sannan ta ci gaba da shirinta cike da natsuwa, wanda dama halinta ke nan, komai nata a natse ne, slow d’in nata ma har ya yi yawa kamar wacce k’wai ya fashe mawa a ciki.
Misalin takwas da kwata ta gama shiri ta fito falo, Mama ta samu zaune da littafin hisnul-muslim a hannunta tana karantawa.
Ganin haka ya sa ta nufi kitchen, ruwan lipton ta zubo sannan ta zuba soyayyar doya a plate ta dawo falon.
A hankali take karyawa har ta gama sannan ta fitar da kayakin ta kai su kitchen. Ko da ta dawo har Mama ta gama adhkar d’in.
Gaishe ta ta yi sannan ta ce,
“Mama har an gama?”
Da fara’a Mama ta ce,
“Wallahi kuwa na gama Maryama. Ya aka yi yau kika makara? Na san halin malaman nan naku fa wani lokaci ba sani ba sabo ne.”
“Ai da yake yau zamu fara rehearzal ne Mama. Duka d’aliban ma za’a ke fiddowa a fili muna yi a gabansu. Tun daga nan har lokacin walimar.” Maryama ta bata amsa tana k’ok’arin zura hijabinta da ta ninke ta d’ora a bisa hannun kujera.
“Af! To masha Allahu! Allah Ya taimaka. Dawowa ba yanzu ba ke nan ko?”
“Gaskiya kam Mama. Wata k’ila ma ta-zarce zamu yi har shida na yamma sannan mu dawo.” Maryama ta fad’a, ba kuma ‘karya ta yi ba, haka tsarin abun yake, sai dai kuma ita kam ba can zata nufa ba, sai idan ta gama abin da take da wuri ne zata je ko da da yamma ne.
“Bara na tafi Mama.” Ta fad’a tana k’ok’arin fiddo hannunta daga hannun hijabin.
“Allah Ya bada sa’a. Sai kin dawo.”
“Ameen Mama.” Ta fita daga d’akin.
Sai da ta koma d’akinta ta d’auko kud’i sannan ta fita.
A dai-daita sahu ta tsayar ta kwatanta masa unguwar.
K’arfe tara da minti ishirin ta mata a k’ofar gidan su Amrah. Bayan ta sallami mai adai-daita ta shiga gidan da sallamarta.
Amsawa matar gidan ta yi sannan Maryama ta shiga ciki da fara’a.
STORY CONTINUES BELOW
“Sannu da zuwa Maryama. Iso ciki.” Ta fad’a cikin karramawa.
Shigowar kuwa ta yi har falo matar ta kai ta. Wasu irin tsofaffin kujeru ne irin wanda sun ji duniya d’in nan, katifar jiki duk ta gama lalacewa sai zallar katako wanda idan mutum bai kula ba ma tsaf zai iya jin ciwo.
Bayan ta zauna matar ta ce,
“Bara na kawo miki koko. Sai dai kuma yanzun nan na ba almajiri k’osan, saboda kar ya sandare kuma ba cinsa zan yi ba, kokon ma a samus na zuba shi ne.”
“Wallahi Mama ki bar shi na gode. Sai da na karya ma sannan na baro gida.” Maryama ta fad’a.
“Eyyah! To shi ke nan ai. Ina zuwa.” Ta fita daga falon.
Babu jimawa sai gata ta dawo, zama ta yi daga d’an nesa da Maryama san nan ta ce,
“Yanzu zan baki labarin Amrah, Maryama.”
Gyara zama Maryama ta yi ta ce,
“To ina jin ki Mama.”
“Sunanta ke nan na yanka Amratu. Amrah muke kiranta da shi ni da mahaifinta.
Amrah ita ce ‘ya ta uku a gidan nan, sai dai kuma matsayin ita ce babba, kasantuwar duk yaran da muka haifa basa rayuwa.
Tun daga lokacin da muka haifi Amrah, mahaifinta ya d’auki soyayyar duniya ya d’ora a kanta, yake bata kulawa sosai fiye da sauran yaran da muke haifawa basa rayuwa.
Tun Amrah na da shekara d’aya a duniya take da wani laluri, na yawan k’ai-k’ayin tafin k’afa da kuma tafin hannu.
Abin mamamki, yarinyar da bata san wani abu ba a duniya, amma duk lokacin da tafin k’afarta ko hannunta ya dame ta da k’ai-k’ayi, da ‘karfi zata kama hannuna ko na mahaifinta tana kai wa a inda yake mata k’ai-‘kayin, da nufin a sosa mata.
Tun bamu fahimtar komai har ta kai ga mun fara fahimta, wato dai suna damunta da k’ai-‘kayi ne.
A lokacin da ta cika shekara biyu a duniya ne kuma cututtuka suka fara nata yawa, wato yawan zazzab’i, sannan kuma da yawan ciwon gab’ob’i.
Yarinya k’arama ‘yar shekara biyu, wacce ko maganar kirki bata iya ba, amma ta san ta ringa gwada duk inda ke mata ciwo tana fad’in,
“Hannu ciwo, cici ciwo, kai ciwo…” da dai sauransu.
Tun bana d’aukar abun serious har na fara damuwa, saboda har cikin dare idan abun ya tasar mata ko kad’an bama bacci, ita kuka ni kuka, mahaifinta ne kawai mai dakewa, yake k’arfafa min guiwa a ko da yaushe.
Ga ta da yawan yin zazzab’i, da zarar sauro ya cije ta sai zazzab’i, idan ta fara zazzab’in kuma shi ne sai wannan ciwon gab’ob’in wanda yake rikita mana lissafi.
Duk wannan abin da yake faruwa, ciwo da yake ta addabar Amrah, ko da wasa bamu tab’a gwada kai ta asibiti ba. Wani lokacin idan zazzab’in ya dame ta ne da kanshi Babanta yake zuwa chemist cewa ‘yarsa na zazzab’i, sai a bashi maganin zazza’bin kawai ya zo a bata.
Wata rana, k’anwata ta zo daga Kaduna, ta zo ganin gida shi ne ta zo min wuni, ta samu Amrah bata da lafiya, na tasa ta a gaba ina mammatsa mata duk gab’ob’inta da take gwada min suna mata ciwo.
Cikin tausayi ta ce,
“Wai Yaya Murja me yake damun yarinyar nan ne? Abin tausayi har ta iya fad’in inda ke mata ciwo? Alamun ma ta saba ke nan.”
Gyad’a kai na yi na ce,
“Zainabu ni kaina ban san me yake damun Amrah ba. Sai dai kawai na san zazza’bi ne idan ta yi shi yake sakar mata ciwon gab’ob’in nan
. Tun da nake haifar yarana suna mutuwa ban tab’a had’uwa da mai irin ciwon da Amrah ke yi ba. Zainabu na fara tsorata sosai wallahi.” Ta fashe da kuka tana kallon Amrah.
Ita kam Amrah baki ta wangale tana dariya, shi k’aramin yaro dama babu ruwanshi, yanzu zai gama kukan ciwo kuma yanzu zai kama dariya.
Zainabu ta numfasa sannan ta ce,
“Kuma ku baku tab’a kai ta asibiti ba?”
“Bamu tab’a ba Zainabu. Sai dai kawai Babanta da yake siyo mata magani. Yanzu haka tana da sauran panda yana nan bai k’are ba.” Na bata amsa.
“Gaskiya Yaya Murja ku daure dai ku kai ta asibiti. Kar a je ana ciwo daban, magani daban. Likita bashi da halin bada waraka, sai dai kuma yana bada tashi gudunmawar. Ki daure dai a kai ta d’in.”
Shiru na yi ina nazari a azuciyata. Na san tabbas gaskiya Zainabu ta fad’a min, sai dai kuma babu hali ne. Abincin da zamu ci ma wahala yake mana. Kuma ba wai zuwan ne nake ji ma ba, a’a, kud’in da za’a caje mu nake ma. Tun da dai komai na yanzu ya koma na kud’i.
“Kin yi shiru Yaya Murja. Gaskiya nake fad’a miki fa. Bai kamata ku zauna kuna ji kuna gani ciwo ya ringa cin yarinya ba. A ce wai yarinya da zarar ta yi zazzab’i sai k’asusuwanta su hau ciwo? Gaskiya akwai dai wata matsalar daban, ba wai zallar zazzab’i ba ne.”
Cikin k’arfin hali na ce,
“Insha Allahu ranar litinin zan kai ta asibiti. Ni kaina abin yana damu na bani da yanda zan yi ne.”
“To Allah Ya kai mu Yaya Murja. Allah kuma Ya bata lafiya.” Ta mik’e.
Bankwana muka yi sannan ta tafi ta bar ni da tunanin kalamanta, hawaye na zirara daga idanuwana zuwa kumcina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *