AMRAH NAKESO CHAPTER 3
Abu na hud’u, ungo wannan.” Ta jawo wata lakar gabanta, wani abu ta zaro sannan ta mik’o min,
“Thermometer ce wannan. Duk sanda zazzab’i ya kama ta, komai k’ank’antarsa ku ringa amfani da wannan, zaku saka a armpit d’inta, matuk’ar kuka ga ya kai 37.5degreeC, ko kuma idan a baki kuka saka mata, ya wuce 38degreeC, to lallai ku hanzarta ku kai ta asibiti mafi kusa da ku, saboda ya riga da ya haura, ya kai minzalin da zai iya k’one mata baki d’aya jininta.
Amma idan kuka kawo ta, sai a d’auki mataki tun da wuri kafin abun ya yi nisa.
Abu na biyar, shi ne folic acid. Ya zamana kullum kuna bata folic acid, ko kad’an kar ku ringa mantawa, zai bada taimako sosai da sosai.
Na shida, ta yawaita shan ruwa, ba kuma wai ruwan sanyi ba. Ruwa sosai zaku yawaita bata, saboda shi dama ruwa waraka ce ta cututtuka da dama, not only sickler.
Da zarar tana shan ruwa wadatacce, zaku ga tana fitsari akai akai, wannan fitsarin nata sauk’i ne sosai.
Da zarar kuwa bata fitsari sosai, to lallai akwai damuwa, dole zaku kawo ta asibiti a duba ta.
Wannan su ne abubuwan da ya kamata ku kula, ku tabbatar kun fita hak’k’inta, in har kuka aikata kaf abubuwan dana lissafa maku, lallai zata kasance mai cutar sickler amma sauk’ak’k’a.
Abu na k’arshe, ku ringa mata addu’a, saboda ita addu’a takobin mumini ce.1
Sannan kuma kafin a saukar da cuta, sai da aka saukar da maganinta.
Allah maji kan bayinSa ne, mai karb’ar addu’ar bayinSa.
Ku ja yarinyarku a jiki, ku nuna mata soyayya, ku inganta abin da ya yi saura na rayuwarta, bakin gwargwadon iyawarku.” Dr. Xarah ta yi shiru daga nan cike da tausayi.
Sosai kuka ya ci k’arfina, Mallam ne kawai mai d’an kuzari, shi d’in ma da zarar an ganshi an san damuwa na tattare da zuciyarsa.
Murmushi ta k’irk’iro ta ce,
“Maman Amrah sai hak’uri, Allah’n da Ya d’aura mata cutar shi zai bata sau’ki.
Ba kuma wai dan ba Ya sonta ba ne, a’a, jarrabta ce, kuma babu wanda ya fi k’arfin Allah Ya jarrabce sa.1
Masha Allah, yarinyarku kyakkyawa da ita, gata b’ul-b’ul babu wanda zai kalle ta ya ce sickle cell ce.
Abin da ya rage, kawai ku yawaita bata abinci masu gina jiki, insha Allahu ba za a ta’ba ganewa ta jikinta ba.
A shawarce, saboda gaba, duk wanda zai nunar da yana sonta, ko ba dad’e ko ba jima, kar ku b’oye masa cutarta.
Saboda tun da wuri in ma bai san genotype d’insa ba sai ya nemi sani, idan har AS gare shi, duk irin son da yake mata dole ya hak’ura.
Idan kuma Allah Ya sa AA ne da shi, kun ga shi ke nan.”
Nannauyar ajiyar zuciya na sauke, na ce,
“Mun gode k’warai Likita. Insha Allahu zamu bi shawarwarinki, Allah Ya saka miki da alkhairi.
Amma likita, hakan ko yana da nasaba da mutuwar da yaranmu suke yi idan mun haihu? Amrah ce yarinya ta uku da muka haifa, sauran biyun duk sun rasu.”
STORY CONTINUES BELOW

Dr. Xarah ta ce,
“Tabbas ma kuwa, hakan zata iya kasancewa. Saboda wasu yaran idan nasu mai tsanani ne, ba a ma ganewa sai dai mutuwarsu kawai. It can be possible, mai tsananin ce tun wuri sai Allah Ya d’auke su.”
Shiru na yi kad’an ina nazari kafin na ce,
“To shi ke nan. Fatanmu dai, Allah ya sau’kak’a wa duk musulmin Allah.”
“Ameen. Idan kun fita sai ku nemi inda ake rijistar masu sickler, kyauta ake bayar da magungunansu a nan asibitin. Duk bayan sati biyu sai ku ringa zuwa kuna karb’ar mata.”
Ta dafa kan Amrah,
“Amrah! Sannu kin ji? Allah Ya baki lafiya. Ki ringa yi wa kanki addu’a ko?” Ta sakar mata murmushi.
Murmushin na k’irk’iro na ce,
“Insha Allahu zan ringa saka ta tana ma kanta. Bari mu tafi. Mun gode k’warai.” Muka mik’e.
Har a wannan lokacin Mallam bai ce komai ba, damuwa fal a fuskarsa.1
Ba mu bar asibitin ba, sai da muka mata rijista, aka bata magungunan wannan satin, sannan muka tafi.
K’arfe sha biyun rana ta wuce sanda muka isa, ta yi bacci hakan ya sa na kwantar da ita, sannan na nufi d’ora girkin rana.
Bayan azahar, sai ga Annur ya zo, hannunshi rik’e da launch box d’insa, bayansa kuma goye da jikarsa.
Da fara’arsa ya k’ariso inda take zaune, zama ya yi shi ma ya ce,
“Amrah…” ya bud’e launch box d’in ta shi.
“…ga sauran abincina nan na kawo miki. Ban cinye ba saboda ke…”
Ya ajiye a gabanta, sannan ya bud’e jikarsa,
“…wannan kuma chocolate ce na siyo miki. Kar ki ba kowa.” Ya fara bud’e mata ledar.
Daga inda nake na saki murmushi, sannan na iso inda suke.
“Wato dai Annur mu kake nufin kar ta ba ko? Ka yi dai-dai to.”
Mallam da ke zaune ya murmusa ya ce,
“Ahh to, mu ma idan mun samu na mu sai mu hana su ai.”
“Umma an karb’o result d’in nata kuwa?” Ya tambaye ni.
Zama na yi kusa da shi, na ce,
“An karb’o, Annur. Amrah sickler ce da ita.” Na yi saurin share hawayen da ya fito min.
“Sickler Ummah? Irin wadda Saddam yake da ita? Gaskiya k’arya ne. Shi fa jikinshi babu girma, sai aukin k’ashi kawai. Babban kai kuma da shanyayyun k’afafuwa gare shi. Shi ne kuma za a ce wai Amrah ita gare ta? Ummah ko dai ‘karya likitan yake maku?”
“Waye Saddam?” Na tambaye shi.
“Wani abokina ne. Sanda muna JS2 ma ya rasu.” Ya bani amsa cike da damuwa.
“To ai ka ga shi da Amrah ba d’aya ba. Ita wannan cutar dama kowa da yanda take zo masa. Wani da sauk’i, wani kuma babu sauk’i.
Akwai wanda take canza ma halitta, kaman yanda ka ce ta Saddam d’in. Ita kuma Amrah, ka ga ta ta mai sauk’i ce, sai mu gode wa Allah ke nan, tun da abun ya zo da haka.
Kar ka damu Annur, insha Allahu babu wata damuwa, Allah Yana tare da mu, kuma shi zai bata lafiya.
Kai dai kawai abin da nake so da kai, ka ringa saka ta a addu’a, kar ka fasa. Zata samu sau’ki kaman kowa.” Na sakar masa murmushi.
“To shi ke nan Umma. Zan ringa yi mata addu’a har ta samu sauk’i.”
“Yauwa d’an al-barka, yanzu ka tashi ka tafi, ka huta kafin lokacin Islamiyya ya yi.” Mallam ya fad’a bayan ya dafa masa kai.
D’aure fuska Annur ya yi, ya ce,
“Ni fa yau ba zan tafi ba, zan zauna a nan sai dare sannan. Har ma na sallami baba Amadu tun d’azu ya tafi.”
Cike da mamaki na ce,
“Wace irin magana kake yi Annur? To me zaka zauna ka yi a nan? Na ce maka Anrah ta ji sauk’i fa. Ka tashi ka tafi kar Mommy ta maka fad’a.”
Fir fir yaron nan ya ce ba zai tafi ba, shi fa yana nan zai yi jinyar Amrah ta yau.
Kumci na dafe, na ma rasa abin da zan yi.
Mallam cikin dabara ya ce,
“To ka tafi gida, ka ciro uniform d’inka sannan ka dawo, sai ka yi jinyar ta ta. Amma a haka, ai babu dad’i zama da uniform.” Ya masa murmushi.
Fuska ya sake tsukewa, yana neman y
in hawaye ya ce,
“Shi ke nan bara in tafi, tun da dai kora na kuke daga gidanku.” Sai ga hawaye sun fara masa sintiri a kumatu.
D’aukar launch box d’insa ya yi, da jikarsa, yana kuka ya kama hanyar tafiya.
Baki d’aya na ji zuciyata ta yi sanyi, ba zan iya barinsa ya tafi a haka ba, hakan ya sa na jawo sa, na ce,
“Yi ha’kuri yarona. Tun da baka son tafiyar, zauna abunka ka ji?”
“Umma ba dai ni kuke kora daga gidanku ba? Shi ke nan ma, ba zan sake zuwa gidanku ba.” Ya fizge hannunsa da na rik’e.
Da hanzari Mallam ya kamo shi, da fara’a ya ce,
“Zo nan abunka. Ka yi hak’uri ka zauna ka ji? Ko dan Amrah, ka ga har ta fara kuka.”
Kallon Amrah ya yi, ganin da gaske kukan take ya sa ya dawo da sauri, ya hau bubbuga bayanta yana bata hak’uri har ta yi shiru.
Daga nan suka hau wasansu, yana ta bata labarin makaranta, ita kuwa murmushi kawai take, dan bata san abin da yake fad’a ba.
Ko da abinci ya dahu, tare na zubo masu shi da ita, yana bata a hankali a baki.
Sai da ya tabbatar ta k’oshi, sannan shi ya fara ci.
*K’ARFE HUD’U DA RABI NA YAMMA (4:30PM)*
Wata budurwa ce ta shigo, hannunta rik’e da wata yarinya, wadda kallo guda zaka mata ka tabbatar ta had’a jini da Annur.+
Babu ko sallama suka shigo, biye da su wani matashi ne, sanye da matattun kaya, wanda na tabbatar cewa d’an koransu ne.
Tafe suke yana masu jinjina, had’e da kirari tamkar ya ga manyan Al-hazai.
Ko da ganinsu, tuni Annur ya mik’e tsaye, mamaki fal a fuskarsa ya ce,
“Aunty Saddiqa.”
Tabbatarwar da na yi cewa danginsa ne, ya sa da fara’ata, duk da yanayinsu da na gani, cike suke da izza da gadara, na ce,
“Lale marhabun da ku. Ku iso ga tabarma ku zauna.”
Kallon uku saura kwata Saddiqa ta bi ni da shi, bata ce min komai ba, sai dai ta kalli Annur cike da masifa ta ce,
“What’s wrong with you, boy? What are you doing here?”
Ta sake bin gidan da kallo a k’ask’ance,
“Wai me kake tsinta a gidan nan ne? Lukkat the floor…” ta nuna k’asa da hannunta, alamun k’yama,
“…a haka kake zaune, har kuma kake iya had’iyar yawu? Taso maza mu tafi, tun ban mammare ka ba.”
Iya ‘kuluwa na k’ulu, bana son raini da wulak’anci, musamman ma yanda ta zo har inda muke ta same mu, kuma take neman wula’kanta mu.
“Ya Noor abeg let’s go mana. Lukkat your uniforms, duk sun yi k’ura saboda floor d’in gidan, amma a haka kana zaune, ji k’azamar yarinyar da kake wasa da ita…” ta nuna Amrah.
Tun bata rufe bakinta ba, Annur ya hanzarta isa inda ta ke, ya mata wani mugun kallo, kafin ya ce,
“Islam, mind your tongue. Da ki tab’a Amrah, gwara ni ki yi min. Wai me ma…?”
Bai gama maganarsa ba, ya ji sautin tsawar da Saddiqa ta masa,
“Shaarrup your mouth Noor! K’arya Islam ta yi ne? Kullum kana fama da zuwa gidan da bai kamace ka ba, kana k’ok’arin gurguntar da rayuwar iliminka, a maimakon ginuwar da iyayenka suke maka. Me yake damunka? Me ya sa ba zaka fita harkar mutanen da basu cancanta..”
“Ya ishe ki haka!” Na fad’a a fusace.
K’arisowa na yi inda take, cike da takaici. Iya k’ok’ari na yi shi, na so a ce na iya daurewa, na k’yale ta. Amma ina, sam! Na ji zuciyata ba zata iya d’auka ba, ba zan iya jurar cin fuskar da Saddiqa take min ba.
“Na kula, duk girmamawar da na miki, ko kad’an ke baki ga hakan ba. Na kula, sam! Baki cancanci darajta kin da na yi, saboda Annur ba.
A rayuwata, bana son cin zarafi, da kuma cin fuska.
An fad’a miki tsoro ne ya sa ni yin shiru, bayan duk cin fuskar da kike min?
Wa ya fad’a miki shiru-shiru tsoro ne?
Ko kuwa an ce miki talauci hauka ne? A tunaninki bamu da wata daraja ne, saboda muna talakawa?
Annur da kike gani, ban tab’a jawo shi na ce ya zo inda muke ba, ban tab’a kiransa da sunan ya zo gidan nan ba.
Dan Allah na ro’ke ki, ki tafi ki bar mana gida.
Duk iya talaucinmu, mun rik’e shi, bamu fita yawo kwararo kwararo muna maula ba.
STORY CONTINUES BELOW

Ki fita, tun ban tara miki mutanen anguwa da sunan kin zo har gida, kina tak’ulana da fitina ba.
Na rok’e ki, ki kama k’aninki, ki kuma shaida masa, ya tsaya inda Allah Ya ajje sa. Dan na ga alama, zuwansa inda muke, babu abin da zai jawo mana, face b’acin rai.
Ki tafi kawai!” Na nuna mata k’ofa, gabana sai dukan uku-uku yake.
Hankalina a tashe yake, ko kad’an bana son fitina, bana son ana fitina a inda nake.
Wata irin muguwar dariya ta fasa, tana tafa hannuwanta.
Wannan gardin wanda suka zo da shi, ya bud’e baki zai min masifa ta yi saurin dakatar da shi.
“Barta!” Ta juyo gare ni.
“Ki fad’i komai Madam, its your time.” Ta had’a babbar yatsarta, da yatsar tsakiya, na hannun damanta ta murza su da k’arfi, har sau uku.
“Zaki san kin fad’a min bak’ak’en maganganu. Ba dai ni ba? Hmm!”
Islam cike da rashin kunya da fitsara ta ce,
“Matsiyata kawai. Ji yarinyar ma kayanta duk sun tsufa. Gashin kanta ko gyara babu. Lukkat everywhere…” ta hau yatsina tana kalle-kallen ko ina dake cikin gidan.
“Aunty Saddiqa mu yi mu tafi, dan kr wata cutar ta kama mu Please.” Ta hau dod’e hancinta.
Tuni Annur ya d’auke ta da mari, sai faman huci ya ke, ya ce,
“Wallahi Islam idan na sake jin bakinki, sai na kakkarya ki.”
“Ni kuma in b’ab’b’alla ka ba. Ai gaba da gabanta.” Saddiqa ta fad’a.
“And ka zo mu tafi, tun ban maka da k’arfi da yaji ba.”
Rai a b’ace, ya juyo ya kalle ni. Sosai hankalinshi ya tashi, ganin yanda damuwa ta dabai-baye duk ilahirin fuskata.
Ya duk’a daf da Amrah, murmushi ya k’irk’iro mata, ya ce,
“Zan tafi Babyna. Please don’t cry. Gobe da sassafe kafin in tafi School zan biyo in sake duba ki. Yi min dariya ko?”
Dariyar kuwa ta yi, sai dai ganin ya mik’e tsaye alamun tafiya zai yi, ya sa ta fasa kuka mai k’arfin gaske.
Yana k’ok’arin komawa mazauninta, da ‘karfi Saddiqa ta finciko sa, har sai da ya kusa buguwa da bango.
“Wallahi Annur, idan baka zo mun tafi ba sai na ci mutuncinka.”
Babu yanda ya iya, a haka ya bi bayan yayarsa da kuma k’anwarsa, yana yi yana waigen Amrah, da har yanzu take kuka kamar ranta zai fita.
Sai da suka tafi, na ji wani irin kuka wanda ba zan iya tsayar da shi ba, zafafan hawaye ke fita daga k’wayar idanuwana, wanda zan iya kiransu, da hawayen takaici.
Wuri na nema na zauna, ina mai ci gaba da ruwan hawaye, ga Amrah ma bata yi shiru ba.
Muna cikin hakan, sai ga Mallam ya shigo, biye da shi, k’aninshi ne mai suna Marwana.
Da sallama suka shigo, na amsa ina mai k’ok’arin tsayar da hawayen da har yanzu suka kasa tsayawa, had’e da jawo hab’ar zanina ina share wanda suka gama wanke min fuska.
Duk da k’ok’arin da na yi dan ganin na b’oye damuwata, hakan bai hana su Mallam fahimtar halin da nake ciki ba.
Da azama Mallam ya iso inda nake, fuskarsa ta nuna damuwa k’warai da ainun.
“B’oye damuwa sam bata cancanta a bisa fuskar da ruwan hawaye ya gama wankewa da ita ba. Halin jarumta, sam! Bai cancance ki a dai-dai wannan lokacin ba.
Ko mutum bai sanki ba a baya, idan har ya kalle ki a wannan lokacin, sai ya tabbatar da lallai kina cikin damuwa.
Ki fad’a min Murjanatu, wane irin abu ne ya faru da ke, wanda har
ya saka ki kuka?
Da alama dai ba ciwon Amrah ba ne, saboda ba haka zan same ta ba idan har shi d’in ne.
Yanayinku ke da ita, ya tabbatar min da cewa wani abu ne, wanda a tare ya b’ata maku rai.” Ya dakata daga nan, yana mai k’ok’arin zama a kusa da ni.
Marwana kuma, ya d’auki Amrah yana ta rurrugarta, har ya samu nasara ta yi shiru, babu b’ata lokaci, cikin mintunan da basu fi biyar ba, bacci ya d’auke ta.
Nannauyar ajiyar zuciya na sauke, na kalli Mallam na ce,
“Mallam ashe talakan da yake zaune inda Allah Ya ajje sa, ya rik’e talaucinsa, zai iya zama mai laifi ga masu wadatar dukiya?
Ashe rashin shiga shirgin wasu, zai iya jaza mana wata matsala, ga wanda suke ganin sun fi mu d’aukaka?
‘Yan uwan Annur ne suka zo…” na fad’a masa duk yanda muka yi da su har sanda suka tafi.
Cikin nuna halin ko in kula Mallam ya ce,
“To kuma shi ne ya zama abun damuwa da har kike asarar ruwan hawayenki?
Ni a ganina, ko kad’an wannan ba zai iya zama silar b’arnar hawayenki ba.
Ai da sauk’i, tun da ba gidansu kika je da nufin neman taimako ba. Har cikin gidanki suka same ki.
To sai me?”
Gyad’a kai na yi, na ce,
“Amma Mallam, baka ganin abin da suka min tamkar cin fuska ne a gare ni?
Duka a shekaru, Saddiqa ba zata wuce shekara goma sha tara zuwa ashirin ba.
Islam fa? Ko goma ban ce zata yi ba.
Amma a haka suka ringa cin zarafina, suna fad’a min magana, tamkar talauci hauka ne.”
Hawaye ya sake cin k’arfina.
“Haba Murjatu! Yanzu ke, yarinyar da ba zata wuce shekara ashirin ba ce ta sa kika zauna kike kuka?”
Marwana ya kwantar da Amrah bisa tabarma, ya ce,
“Yaya Abdallah, dole Maman Bilal (Sunan da dangina da na Mallam suke kirana da shi, tun sanda na haifi yarona na farko mai suna Bilal, kuma har ya rasu basu daina kirana da shi ba.) zata yi kuka. Abin da kake ganin bai kai ya kawo ba, yarinyar da ta yi k’anwa ta biyar da ita, amma ta tsaya tana fad’a mata maganganu, tana mata rashin kunya.
Wallahi, Allah ne Ya kyauta. Da a ce na tarar da su, suke mata fitsara, da duk abin da zai faru sai dai ya faru. Dan wallahi marin yara zan yi, in yaso sai mahaifin nasu, Alhaji Iqra Al-Hussein ya sa a d’aure ni, a kashe ni.”
Mallam ya ce,
“Sai hak’uri ai. Komai na duniyar nan, sai ana kai zuciya nesa. Wata rana sai labari.”
“Haka ne.” Na fad’a had’e da share hawayena.