ARNE CHAPTER 9 BY Surayyah.M.S
Bayan wata biyu a gidan alhaji ,raphael ya warware
normal kamar bashi ba
Zaune yake a kofar masallacin gidan yana sauraron zafar dake karatun Qur’ani bayan sallar asubahi.
Nitsuwa yayi tamkar wanda yasan abunda ake cewa…….har cikin ransa abun na Sanya shi jin nitsuwa
Shyasa ma ya nace kullum sai ya biyosa ko a sace ne ya labe yana ji
Karfe 7.saura suka nufi gida tare ,asace raphael ya shiga dakinsa domin kuwa Hajiya ta hanasa hada hanya da su zafar
Shikuwa kullum yana like duk enda zasuje dashi
musamman ma zafar da ke sa’arsa ne,,,sai ya buya a gefe guda har ya gama harkokinsa kafin su dawo
Hajiya kuwa bata damu ba ma saboda a dakinsa tace yadinga zama kar ya fito mata cikin gida.
Alhaji abdullhi dan kimanin shekaru 45yrs bafulatani ne dan asali kauyar Adamawa a Nigeria
mahifinsa alhaji Muhammad ja’EH da
,mahaifiyarsa Hajiya salima ita kuma asalin yar Ethiopia cr…
a tsaye yake duk da shekaru tafara ja, kynwun halittarsa bata boyewa,
mutum ne mai ilimi sosai da sanin yanayin zaman takewa …..kafaffen mai kudi ne wanda ya samo asali ne tun daga mahaifinsa….ya mallaki kamfanoni a Nigeria da kasashe daba daban a waje.
Alhaji abdullhi da Hajiya mariya auren zumunta akai musu …ita kuma yar Ethiopia ce
ta wajen mahaifinta
,mariya dai yar dangin mahaifiyar su alhji abdullahi ne Hajiya salima
Farace Sol ,tanada kyw Nagani nafada,..sai dai arziki da rurin mallakar duniya tasa ta zarmewa cikin tsananin son abun duniya
Hajiya mariya bata haihu da wuri a gidan alhaji ba kasancewarsa mai wahalar zama waje daya da kuma Kaddaran Allah…
shekarunsu na hudu da aure ne Allah ya fara bata haihuwa nan aka samo zafar.kafin faryal da ta fito bayan shekara 4 da haihuwar zafar….
Farare ne sol ga bakin gashi yaleyale mai tsayi kwnce akansu sai manya manyar idanunsu,,in kagansu ma zaka dauka yaran larabawa ne…
,taso ta sangarta su da son nuna abun duniya da sakalci irin na yaran manya
amma ena ‘enna salima mahaifiyar alhaji da shi kanshi alhaji sun Sha karfinta wajen tarbiyartar da yaransa
Don’ kuwa ilmin addini ya fara nema musu a gida tun suna kanana sosai ana musu kamr lesson, da malaminsu malam mamman wanda yake zuwa
Wekend tun 10na safe
Faryal duk da ma ita karama CE shekarunta 9 a duniya kawae amma Allah ya azurtata da tausayi da kaifin basira, tanada taurin kai amma zuciyarta Nada saukin tarairaya…
Ga shi Allah ya bata ilimi domin har takara suke da yayan ta wajen daukar karatu…..
Sun girma cike da kauna da tausayin junansu,
nasihohi da wa:azi. Da malam mamman ke yawan musu na mussamman shine yayi tasiri akan Dada gyra tarbiyansu da nagartan su
Domin kuwa Alhji abdullhi ya umurce shi da ya ware lokaci na mussamman na koya musu dabia bisa ka idodin musulunci da basu tarihin akan
halayen manzon Allah SAW.
Komai tare ake musu gurin bacci ne kawae kowa da nashi
dakin.