ARNE CHAPTER 17

Me zan gani haka? Ayyuriri ,,,ahh Barin kira mutumiyata naji gaskiyan zance

Nan Hajiya mariya ta dialing number haj shafaatu ring daya ta dauka

Yar albarka taki ambato,yanzun nan nake shirin danna miki kira

Hmmmmi shafa,yanzu na gama ganin news a paper wai raphael ya canza suna _

Ke mariya ai banan ya tsaya ba ,alhji kabiru jiya yagama shafa min labarin komai,,,,musuluntar dashi sukayi

Dariya haj mariya ta kwashe dashi,sanda tayi mai isarta sannan tace

Toooo lallai alhaji yA dau abun da zafi,anata Dana Sha bana nan kenan

To karyan sa tasha karya gobe zan dawo mu Daura daga inda aka tsaya

Ai cewa nake ko tunda yanzu ya karbi kalma kya karbe shi,

Chab shafa kenan ,nifa tunda har jinin arna ne ke bin jijiyoyinsa na TSANESHI….fakat

Ah tou,ganemin fa ai

barewa ba tayi gudu danta yayi rarrafe ba

Toh shafa,mekike gani zanyi yanzu?

Niga gani nake kudin alhaji ne yasa ya koma musulunci ba tsakani da Allah ba

Tabbas… mariya yanzu kikayi magana,so yake ya Dada Shiga zuciyansa a samu a ja shi jiki fiye da yaranki

Ke dai kidawo muga irin salon abunda yadace a mishi

Yawwa shafa na,sai kinji ni…….

Komai an gyrashi an Dada qawata gidan don tarban Hajiya mariya

Tun saukar ta suke waya da shafa har ta iso gidan

Zagaye take da yaranta sunata hirarsu cikin jin dadi, raphael ne ya sauko shima ya rusuna ya gaishe ta

Fashewa tayi da dariya musulmi ko?

,ikon Allah, wasu musulman ma don’ wuta akayi su……domin su sukasan wani irin musulunci sukeyi

Me sunanka ma,? Uhmm kamilu koh?chab Allah ya isa ma suna mai dadi anyi asararsa

Zamewa faryal da zafar sukayi suka barta awajen don sungaji da ganin cin fuskar da mummy ke ma kaamil,

Hakuri kaamil yafara bata duk da  ba dalilinsa

Ko ajikinta ta cigaba,

kai wai meyasa bazaka bar min gida bane,

idan kasan darajar iyayenka arna ka fitA min agida karka sake dawowa har duniya tanade,nan ne zan hakura

Hajiya kiyi hakuri,,,yasake cewa

Ooh bazaka fita ba kenan,,,me manufarka ne wai.?

Kudin alhaji ko? Kaifa daga ganinka ma barawo ne….

Me dame ka taba dauka  agidan fadamin naji?

Da sauri Raphael ya dago kai ya kalleta cikin mamaki

Fada min mana cikin tsawa tafada,  

 

Hawaye ne ruri a idanun raphael zuciyarsa na kuna

Mariya? Taji an kirata,haba mariya,

Tashi kaamil share hawayenka ka wuce ciki

Ke kuma kisame ni a daki anjima

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *