AUREN FANSA CHAPTER 8 BY ✍🏾 NIMCYLUV

AUREN FANSA CHAPTER 8 BY ✍🏾 NIMCYLUV

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Baya yay da kujerar ya kwanta yana ɗan cije baki, Mannal mmki ne ya kusa kasheta tama rasa me ne za tace dan baƙin ciki, lallai duniya ta lalace tunda kamar Ya Heemu ya kalli idanunta yace yana sonta yama manta da matsayinsa a wajanta, ya manta kallon ɗan data haifa take masa, Idanunta yay raurau zata saki kuka taji muryarsa yana faɗin “Shiru kada ki min kuka” haɗiye kukan tayi sai hawaye kawai daya shiga sauka daga cikin idanunta tace “Ya Heemu anya ƙalau kake?” Idanunsa a lumshe yana shafa ƙirjinsa bai ce mata komai ba, kamar zata saki ihu tace “Buɗe min ƙofa na fita, naga alama akwai abinda ke son juyar maka da tunani, to ai ko ɗan 30 yay rashin kunya yace yana so na, bare kai ɗan ciki na” wani lalataccen murmushi ya saki yana buɗe idanunsa, wani ƙyakƙyawan murmushi ya ƙara saki kafin ya gyara zamansa yay motar key ba

tare da yace komai ba, driving yaci gaba dayi jin A.cn motar tai masa kaɗan yasa ya fara ɓalle bottles ɗin gaban rigar sa, kanta ta sunkuyar ƙasa ta shiga duba wayar da ba tayi niyya ba, kai tsaye acct ɗinta na I.G ta shiga, posting ɗin farko na _Nimcyluv_ ne inda tai posting cover na littafin ta _ABU_MALEEK_ like and comment tayi sannan ta tambayi yaushe za’a fara, akace mata End of November!
Cif Ya Heemu ya zare rigar jikinsa ya zauna daga shi sai farar singlet wacce ta kama jikinsa six packs ɗinsa ya bayyana kusan rabin ƙirjinsa a bayyana yake, ya motsa fuska Yay sbd ƙishin ruwan daya keji, rabon da yaci abinci ma ya manta, a gaban gate ɗin tafkeken gida ya tsaya ya fara horn gate keeper ya buɗe da sauri ya zura hancin motar ciki, a parking space yay parking, yana tsayawa Mannal ta fara ƙoƙarin Fita amma ta kasa sbd yasa key, kallonsa tayi taga ya kifa kansa a steering motar, Murya a shagwaɓe wacce ta zama jinin jikinta tace “To zan fita” banza yay mata ta ƙara marai-raice fuska tace “Ya Heemu” idanunsa wanda sukai jaa ya ɗan ɗaga tare da saukesu a kanta can ƙasan maƙoshinsa yace “Yes! Mmyna” yadda ya kira sunan in emotional sound yasa taji bugun zcyarta ya sauya, ba tare data kallesa ba tace “Open the door”  matsuwa yay jikin kujerar ta, ita kuma ta manne da kujerar amma duk da haka sai da yay mata rumfa, ƙoƙarin buɗewa yakee ya kasa ganin haka yasa ya ajjiye hannunsa by mistake hannun ya samu wajan a cinyarta saurin rufe idanunta tayi tana mmkin sauyawar ta Ya Heemu, bakinta na rawa tace “Hahhhh…Hannunka” fasa buɗe ƙofar yay ya juya fuskarsa gaba ɗaya a dai-dai ta ta, ya shiga ƙare mata kallo yana ganin yadda ta runtsa idanunta, gaba ɗaya Mannal a dame take tana jin yadda hucin numfashinsa ke dakar masa fuska,gefe yay da fuskarsa bakinsa dai-dai kunanta yace “Gud night My beautiful lady” yana faɗin haka ya buɗe ƙofar kana yaja baya da sauri, da sauri itama ta fita har tana manta hand-bag ɗinta, dry ta bashi sosai ganin yadda jikinta ke rawa amma miskilanci irin na Ya Heemu yasa kawai ya ɗan cije baki ma dadadin yay dry ko Murmushi, key yaywa motar tare dayin reverse yabar gidan da wani irin speed.
Uncle da Arman sai Siyama ƴar Uncle da matarsa Khausar, suna zaune a Parlo su kaga kamar an cillo ta, sai rarraba idanu take tana sakin ajjiyar zuciya tare da juya bayanta, Arman ya miƙe tsaye yana kallon mahaifiyar tasa, kafin da sassarfa ya ƙara inda take tsaye yana zuwa ya shige jikinta ya faɗin “Mumy nayi kewarki” bata nutsuwa ko sukunin yi masa wani abu ko rarrashi duk da tasan cewa yana cikin damuwar rabuwarta da mahaifinsa da kuma baƙin cikin Auran budurwarsa da mahaifinsa yay, uwa Uba rashinta yay gaba ɗaya a Duniyar, kansa ta kamata tare da bashi light kiss a goshinsa kafin cikin sarƙewar murya tace “Miss u too My boy” tana faɗin haka ta shige wani part ko takan su Khausar bata bi ba, tana zuwa ta faɗa saman bed tare da dunƙulewa waje guda, tana rufe fuskarta da tafin hannunta. Khausar ta kalli Uncle tace “Uncle lfyarta lou kowa?” Miƙewa tsaye yay yace “Kamar baki santa ba” Arman yace “Lemme check” yana faɗin hakan ya nufi part ɗin data shiga, tana kwance ta danna kanta cikin pillow tana hargitsa gashin kanta taji ya turo Ƙofar, da sauri ta ɗauke hawayen fuskarta tare da ɗago kanta tana ƙaƙaro murmushi wanda kana ganinsa kasan na ƙarfi ne, amma sosai tai ƙoƙarin danne duk damuwarta.
Kallonta yay sosai yasan mahaifiyarsa tun ba yau ba, indai tana cikin damuwa haka take cusa kanta cikin pillow tai ta wargatsa gashin kanta, wannan abun da yaga ta nayi ya tabbatar tana da damuwa, ƙarasawa yay inda take zaune yana Kallonta ita kuma ta ɗauke kai tare Miƙewa tsaye zata shiga bathroom yay saurin faɗin “Abba ne ko?” Cak ta tsaya domin ta manta da Abban Arman ko su take da gske ta manta da shi, tana son mijinta fiye da sosai amma ya shayar da ita mmki wanda dole yasa ta janye jikinta, amma ba taƙi a yanzu ta koma masa ba sbd matsalar dake shirin kunnu mata.
Bata iya ce masa komai ba sai hanyar bathroom ɗin data nufa, Arman yace “Mumy yanzu ke nake kallo naji daɗi, Sai Ya Heemu” saurin kallonsa tayi ya miƙe tare zuwa gabanta yace “Mumy farin ciki na ta tafi, kema kin tafi Kano, Yaya kike son nayi? Nai ta zama gida ni ɗaya pls Mumy come back sbd ni” Uwa da ɗa sai Allah tausayin ɗan nata ya kamata hawaye taji suna shirin sakko mata sai kawai ta maza sbd kasancewar ta strong woman bata bari damuwa tayi ta siri a ranta.
Idanunsa cike da hawaye domin yay rashin kulawar ta ya shiga jikinta yana sakin ajjiyar zcy, tsayawa tayi tana jan numfashi kafin ta rungomesa tana bubbuga bayansa “Pls Mumy come back ki dawo gida zanwa Abba mgn” cikin nutsuwa da juriya tace “It’s difficult Habibty, ka manta” zare jikinsa yay yace “Mumy na manta? Na sanya idanu wani ya aurenki ko mene? So kike duniya ta fara lissafa min Auren Mahaifiyata i can’t Mumy Just watch and see” yana faɗin hakan ya fice da sauri.
Bayansa tabi da kallo kafin tai shiga bathroom tana zuwa ta zare kayan jikinta ta sakarwa kanta ruwan sanyi.
Ya Heemu gida ya nufa yana zuwa ya shiga part ɗinsa tare da zame raguwar rigar jikinsa ya nufi bathroom ya watsa, ruwa kana ya sauya 3 gauthier, zama yay a saman kujerar dake ƙawataccen Parlonsa ya shiga Operating system ɗinsa yana shan lemon power horse energy a hankali yana fesar da numfashi tare da lumshe idanunsa, searching yake akan _drugs abuse_ ya miƙar da dugwayen ƙafarsa saman senter table, yana gamawa ya shiga Youtube duba wani abu, Abinda yaci karo dashi shine _”LOVE AND CARE”_ samun kansa yay da play na vedio’n, mace aka fara haskawa sai kuma aka hasko Namiji ware idanunsa yay domin wannan shine karo na farko a rayuwarsa da zai ga abinda ya danganci love, Namijin yaga ya tashi yana zuwa ya rungome macen yana shirin zare mata riga Ya Heemu yay saurin rufe system yana zare ido yana ɗan juyawa, wahalalliyar ajjiyar zcy ya sauke a fili kuma ya taɓe baki yace “Iskancin banza” sai kuma ya miƙe tsaye yana surutai a ransa tayaya zai iya wannan abun da mace? Shi fa sam mantawa yake akwai wani relationship da mace da Namiji suke sai kuma ya ɗan taune bakinsa yace “Ibrahim Khalel da mata” yana faɗin hakan yay waje, a babban parlo ya samu Ummi tun daga nesa ya haɗe rai ganin Anut Meera itama tana ganinsa ta haɗe nata ran ta shiga zare ido tana jiran taji mene zai ce, Hanyar danning Area yay yana zuwa Ummi ta miƙe ta haɗa masa simpe White Rice with vegetables source wacce taji bushasshen kifi sai salad da carbege da tomato’s wanda aka yanka masa manya babu onion domin yace warin baki take sawa, man salad ya matsa masa tare lemon ya sanya dugwayen yatsunsa ya fara Bisimillah tare da sanya abincin a bakin, lumshe idanunsa yay domin yana ƙaunar girkin Ummi sosai, bai wani ci da yawa ba ya cakalkala ya tashi bayan ya wanke hannayensa, not too long ya fito da sanye da Sweater mai tsaga sai key a hannunsa, ba tare daya kalli Anut Meera ba yasa hannu ya ɗauki baby boy ɗinta ya saɓa a kafaɗa ya fara sauka downstairs, ɓata fuska tayi tace “Haba Ya Ruma wai me yasa Ya Heemu kemin haka ne dan Allah” dry Ummi tayi tace “Ai yay min dai-dai tunda ke baki da aiki sai barin gidanki kizo na wasu ai sai ki miƙe ga dai-dai kenan” tashi tayi tana haɗa fuska tace “wlh sai na haɗasa da Baffa”. A mota ta samesa Lil Khalel yana ta kuka shi kuma sai kallonsa yake ya rasa me zai masa, tana zuwa ta amshesa tace “Wai ke guda nawa kake da zaka diga bawa mutum umarni kamar wani Ubana ko Yayana, kada ka manta kamar uwa nake a gareka” key yaywa motar ya nufi waje sai da sukai nisa yace “Nifa Namiji ne ni” dry tayi tace “ƙwarai naga alama shiyasa kake tsoran mace ko” taɓe baki yay yana karya kwana yace “Goodness! Mace dai?” Tace “Ƙwarai ai idan bakai wasa ba a family za muyi tallanka” lumshe idanunsa yay ba tare da yace komai ba domin ta fara isarsa daman mgn a cikinta kamar me, ta ɗura da faɗin “Gashi da Ya Omer yace soon zai aure duk da ban san wace zai aura ba, amma kai ka tsaya iyaye Wannan sai na koya maka soyayyyar” Murmushi kawai yay yana danna horn a sanyaye yace “Talkative” buɗe motar tayi ta fita tana faɗin “Ƙaton kawai wannan budurwar ma ai tsoranka zatai” girgiza kai kawai yay a ransa yake faɗin duk shirmanki ƴarki ta kwashe shi sai a lokacin ma ya tuna da abinda tai masa siririn tsaki yaja da gudu yake jan motar, yana hanya Arman ya kirasa picking yay ta bluetooth ɗin kunansa daga can ɓangaren Arman yace “Friend kana ina ne?” Shiru Ya Heemu kafin yace “bana gida What’s up?” Cikin damuwa yace “pls ka rakani wajan Abban na bashi hqr a madadin Mumy bazan jure ganin su a haka, idan bata koma ba kenan wani zata aura shkknan a fara lissafa mata aure” shiru Ya Heemu yay yana sauraran Arman kafin yace “To All the best” da sauri Arman yace “Baza ka ba?” Kai tsaye Ya Heemu yace “that’s what i mean, zaka zubar mata da daraja ne” yana faɗin haka ya kashe kiran.
Washe gari Ya Heemu bai samu wani cikakken lokaci yana ta shirya tafiyarsa sai yamma ya dawo gida Yay wanka ya sanya blue ɗin Armless da p.cap tai masa kyau sosai ta rufe masa idanu sai jajayen laɓɓansa kawai da ake gani, yana fitowa ya haɗu da Ummi a firgice Kallonta yay ganin mgn yake son yi yasa tace “Ibrahim Khalel maza kawai Ameerah  inhaler ɗin nan jikinta ya tashi” kamar zai mgn sai kuma ya fasa ya karɓa, bai daɗe a hanya ba ya isa gidan a compound yaga motar Ya Omer ɗauke kai yay da ɗan sassarfa ya shiga ciki, kai tsaye part ɗinta ya nufa yana zuwa ya sameta kwance da sauri ya ɗaga ta tare da sanya mata inhaler ta fara shaƙa, cikin ikon Allah numfashinta ya fara dai-dai, ganin hakan yasa ya fita a Parlo ya samu Ya Omer yana dube², Ya Omer yace “Ka kawo mata, tunda na shigo nake neman Moha, coz ance a gida ta kwana amma ban ganta ba” juyawa Ya Heemu yay sbd jin ƙarar kiɗa na tashi a hankali ya fara bin sautin kiɗan harya isa gaban wani ƙaramin ɗaki, yana tura kansa ya ganta sanye da ƙaramin sket iya cinyoyinta sai ƙaramar riga mara hannu ga matasan ƙirjinta suna yawo ta saki gashin kanta har baya kamar dai a India tana bin waƙar Arjit sin, Yadda take ƙanannaɗa jiki ya bashi mmi, wato uwarta na can halin mutuwa ita kuma tana nan, da sassarfa ya ƙarasa inda take yana zuwa ya ɗauke ta da mari, wata gigitacciyyar ƙara ta fasa ta nayin kansa zata maƙale sa yay baya da sauri ya ciran wayar keɓel ta ƙara fasa wata ƙara tana faɗin “Dan Manzon Allah Ya Heemu kayi hqr ban sakewa” Ya Omer ya shigo da sauri bai tsaya jiran komai ba yasa hannu ba mayar da Moha bayansa ya haɗe fuska yana kallon Ya Heemu, cikin dakakkiyar murya Ya Heemu yace “Matsa” Ya Omer yace “Idan kuma naƙi fa” Wani cije baki Ya Heemu yay yace “Ka daina ganin ka girman billahi zan haɗa dakai” Ya Omer ya naɗe hannun riga yace “Ok Bisimillah” gadan² Ya Heemu yayo kansu da Sauri Moha ta ƙanƙame Ya Omer tana sakin Kuka, yana zuwa yasa hannu da ƙarfi ya fisge Ya Omer abinka da soja janyewa ɗaya yaywa Ya Omer yana shirin Zabga natay keɓel ɗin Ya Omer ya dunƙule hannunsa ya sakarwa Ya Heemu duka a ƙirjinsa, ko motsi Ya Heemu bai ba sai wani guntin jini daya fita ta hancinsa, ganin hakan yasa Moha sakin ihun Ya Heemu idanunsa kawai ya sauke akan Ya Omer kana ya kalli Moha sai kuma ya juya da sauri tare da ficewa daga cikin gidan baki ɗaya, a hanya yay Parking ya ɗauki ruwa ya wanke fuskarsa tass kana ya ɗauki strawberry dake gaban motar sa ya sanya a baki, kai tsaye gidan Uncle Ya nufa a Parlo ya samu Khausar da Uncle suna yin Kallo, Khausar tace “Su Ya Heemu manyan idanunka kenan?” Uncle yace “Ko gaisuwa da naje ban gansa ba” bai ce komai ba sai da suka gama mgn hannayensa sanye cikin aljihu yace “Mumy fa?” Khausar tace “Sai kace uwar taka kazo gani tana can part ɗin” bai ce komai ba sbd zafin da ƙirjinsa yake masa ya nufi part ɗin da take, a hankali ya tura ƙofar bedroom ɗin tana tsaye gaban mirror tana busar da gashin kanta da handrayer daga ita sai towel ruwa na zuba a jikinta, Kallonta ya fara frm head to toe kafin ya ɗauke idanunsa ya rufe ƙofar ƙarar ƙofar yasa ta juya sukai ido huɗu, zare ido tayi sannan ta kalli kayan jikinta shima jikin nata yake kallo ko a ƙafarsa bai damu da tsoran da taji ba, ƙafa ta ɗaga da gudu tai hanyar bathroom tako ɗaya biyu yasa ƙafa ya falleta ta baya zata faɗi yay saurin sanya hannunsa ta faɗa jikinsa…..

Ya Heemu kallon towel jikinta yay wanda ya kusa faɗuwa, da zarar kuma ya zame hannunsa to hannu zai tafi da towel ɗin baki ɗaya ne.

Ɗauƙe kansa yay yana Kallon wani wajan daban, kana ya ƙara sunkuya ya rufe ta da jikinsa wanda lokaci guda daddaɗan ƙamshin turarensa na Ohud Mood ya daki hancinta wanda ya tilasta mata rufe idanu tana jin faɗuwar gaba na ziyartar zcyarta.

Me Ya Heemu yake nufi da ita ne? Mai yasa baya jin kunyarta ta goyasa a bayanta, ta wanke masa fitsari tai masa wanka, amma shike mata Irin wannan ɗibar albarkar? Kenan zan iya yiwa mahaifiyarsa ko dai itace bai ɗauke ta matsayin uwa bane kamar yadda ta ɗauke sa matsayin ɗan ta.

A hankali Ya Heemu ya shiga zare hannayensa dake bayanta wanda ya tawo da towel ɗin yana warwarowa daga jikinta zuwa hannunsa.

Ganin abinda ke shirin faruwa yasa da sauri cikin firgici ta tasa hannu ta jawosa jikinta tare da ƙanƙamesa, bakinta a kunanta tace “what’s this Ya Heemu??? Are you out of your sense?” Bai kalleta ba dan shi kansa bai san abinda yake yi ba idanunsa a lumshe suke sbd shima bai shirya ganin abinda baya sha’awarsu da ace zata gane manufarsa da bata wahalar dashi harya shige mata haka ba.

Kodai zai fito fili ya faɗa asalin abinda ke ransa dama zcyarsa baki ɗaya ne? Ƙilan hakan zai sanya ta aminci maka, wata zcyar tace “You’re mad Ya Heemu, tayaya kake ganin zata amince maka bayan babu abinda tafi ƙauna a duniya sama da mahaifinta sai mijinta”

Ƙoƙarin cire hannunta take daga ƙirjinsa ko zata samu damar ƙwace towel ɗin hannunsa, addu’a take Allah yasa kada ya buɗe idanunsa.

Runtsa idanunsa Ya Heemu yay sbd zafin da yaji a wajan da Ya Omer ya dakesa, Mannal kam sai bata san da wani doka ba bare tasan cewa yana jin zafi a jikinsa hakan yasa ta ƙara murza hannunta dake ƙirjinsa, da sauri ya zame hannunsa dake bayanta cikin rashi Sa’a gaba ɗaya towel ya ware tass, a zabar da Ya Heemu yaji yasa ya ɗauki hannunsa yana ƙoƙarin kama hannunta dake ƙirjinsa domin ya cire kai tsaye hannunsa ya samu gurbin zama a saman left ƙirjinta, kansa yaji ya sara ta cikin idanunsa ya zare idanunsa ba tare daya buɗe ba, shidai yaji hannunsa ya riƙe abu kamar balloon abu mai tsayi da kuma faɗi ga taushi, hakan yaji zcyarsa bata yarda da abun ba yana son kuma ya tabbatar dan haka yasa hannu ya matse ƙirjin wani ihun azaba Mannal ta saka tana sakar masa cizo a hannu, da sauri Ya Heemu ya buɗe idanunsa, idanu ya zare kai tsaye kuma ya sauke ganinsa a hannunsa dake riƙe da ƙirjinta guda ɗaya, innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, a fili kuma ya furta “Yasubuhanallah” yana faɗin hakan ya saketa tai baya ta faɗi saman bed da sauri haɗi da gudu², yabar ɗakin dafe da ƙirjinsa da kansa sai zare ido yake kamar wanda yaga maciji, yaci Sa’a babu kowa a parlo da ɗan gudu yay wajan yana zuwa ya shige motarsa ya jata da wani irin gudu yabar cikin gidan.

A bakin titi yay parking yana ɗan kalle² kamar me neman wani abu, da sauri kuma ya ware hannunsa gaba ɗaya a ɗan ruɗe yake sai yarfe hannu yake ji yake kamar yanzu ne abin yake hannunsa, gaba ɗaya ya manta akwai wata halitta a jikin mace makamancin haka.

Rigar jikinsa ya zame ya zame gaba ɗaya ya cire singlet ɗin ya ɗaure tafin hannunsa a ciki sbd tunanin ko ruwan ƙirjinta ya taɓa masa hannu.

Gaba ɗaya ya marai-raice fuska kamar zai fasa ihu, a fili kuma ya taɓe baki yace “Na aza balloon ce ashe…,” Sai kuma yay saurin yin shiru yana jan idanunsa yana rufewa sai yanzu dokan da Ya Omer yay masa a ƙirji yake ɗan damunsa domin ko numfashi yaja sai yaji zafi sosai a ƙirjinsa.

Yana barin ɗakin Mannal ta mirgina saman gadon tana sakin kuka tare da miƙewa da sauri ta isa gaban mirror tare da zame towel ɗin ta kalli ƙirjin ta wanda Ya Heemu ya matse taga saman yay jaa, kuka ta ƙara saki tana faɗin “Wayyoooo Abba Mamana zafi” ta faɗa tana ƙara ƙanƙame jikinta gaba ɗaya ta rasa wanne abune hakan, Ya Heemu na son mayar da ita ƙwallon wasan sa..

Shi ko kunyar haɗa ido da ita  ba yayi, da wanne ido ma zai kalli Arman ta fahimci Ya Heemu sam bai san kunya ba, haka kuma gaya gudun abin kunya..

Shi baya son farin ciki a rayuwarsa ne? Banda haka ƙarami yaro kamar Ya Heemu me zatai dashi, me zai ɗauke mata, gaba ɗaya nawa yake a shekarun yana jin zai iya ɗauke dukkan buƙatun rayuwarta ne?

Miƙewa tayi bayan taci kuka ta ƙoshi kamar ƙaramar yarinya riga tasa body Short mara hannu ta fesa parfume tare da ɗaure kanta ko dinner ba tayi ba ta haye bed ta kwanta, tana ƙarasa karanta SIRRIN MU domin Littafin da yazo ƙarshe sai yafi daɗi, tana zuwa ƙarshen Labarin taga Announcement na sabon littafin Anty Ni’ima mai suna *ABU_MALEEK* labarin mai tsayi ne domin zai je book 1, 2,3 littafin na kuɗi for 500 for vip, 300 for regular, sosai tai mmki domin a yadda taji tsarin labarin da kuma sabbin abin da yake cikinsa ta ɗauka zai je 1k ko 2k murmushi tayi a fili tace “Nimcyluv i like your attitude kinyi taku” Sharp-Sharp ta shiga acct ɗinta taiwa Nimcyluv transfer 5k just for appreciate, Domin littafin SIRRIN MU ba ƙaramin daɗi yay ba, amma duk wannan daɗin da yay a hakan Nimcy tace bai kama ƙafar ABU_MALEEK ba. Ganin bata jin bacci sam sbd tashin hankalin da take ciki kuma bata ƙaunar damuwa tai tasiri a ranta sai kawai ta fara karanta SAI NA AURETA littafin Nimcy na farko wanda ta fara na kuɗi.

Ya Heemu na zuwa gida ya tarar ba kowa a parlo da kuzarinsa yake taka ƙafafuwansa zuwa part ɗinsa har lokacin kuma hannunsa a ɗaure yake.

Kai tsaye bathroom ya shiga ya zare singlet ɗin ya tara hannunsa a sink ruwa ya fara zuba, kana ta sanya detol ya shiga wanke hannayensa yana dirzawa, yana gamawa ya sakarwa kansa shower ruwa ya shiga ratsa jikinsa yana dukan baƙar fatarsa wacce har hasken baƙi take, yana gamawa ya sanya kayan a washing machine kana ya wanke bakinsa tass ya shiga busar da gashin kansa da abin gyaran kansa. wasu nightwear masu kyau da taushi ya ɗauka company Panjams White colour, gaba ɗaya rigar daya sanya tun daga wuyansa har zuwa ƙirjinsa a tsage take, wandon kuma gaba ɗayansa iya guiwa ne.

Bayan ya gama ya sanya bedroom sleeper suma white ya nufi kitchen ɗin dake part ɗinsa ya haɗa coffee mai zafi, yana ƙoƙarin kai coffee ɗin bakinsa yaji wani a zabar zafi, tsaki yaja kaɗan tunawa da Moha da yay he hate her wlh gaba ɗaya Yarinyar sam bata da kunya, kamar wacce aka sangarta.

Parlo ya koma ya zauna kana ya ɗauki remote ya sauya channel zuwa Aljazeera ya fara kallon labarai domin abinda yafi kalla kenan, sai kuma kallon Ball musamman idan ABU_MALEEK ne zai gabatar da wasan gayan ya iya buga ƙwallo.

System ɗinsa ya buɗe yana buɗewa ya samu abinda ya bari da sauri ya fice a wajan a fili yace “Ƴan iska” kai tsaye ya fara operating system yaci gaba da binciken da yake domin soon yake son gabatar da komai, domin tuni ya rubuta dakardar sauya muƙami daga Chief of Army zuwa Captain Khalel Sha’aban.

Washe gari tun da safe Mannal ta gama shirinta na barin garin zuwa Kano, domin dukkan abinda zai sanya ta haɗu da Ya Heemu yan zun kam gudunsa take.

A hankali ta fara sakkowa daga upstairs zuwa downstairs tana sanye da wani light purple ɗin lace mai White ɗin Flowers, anyi mata nrml ɗinkin duguwar riga mata brest_cup sai stones da aka jera mata a saman wuyan rigar har zuwa baya, rigar ta ɗan buɗe hakan ya baya faffaɗan west ɗinta damar juya son ransa ba tare da takura ba.

Ta sanya nrml passion ɗin neakless da ear-ring fuskarta fayau ba zaka taɓa cewa ta kwana tana kuka ba, ta murza ɗaurinta na gaban goshi bayan ta sauke gashinta a ƙasan wuyanta, hannunta riƙe da Iphone 12 max pro.

Cikin nutsuwa ta gama sakkowa tana nufar dinning area, cak ta tsaya sbd jin ƙamshin turarensa tsoro da fargaba suka saukar mata, haka nan taji bata yarda ba ƙilan abinda ya faru jiya yasa ta kejin hakan.. kanta a ƙasa ta ƙarasa tare da jan kujera ta zauna, abin mmkin tana zama taji tamkar ta zauna inda turaren yake, Arman dake zaune yana cin soyayyan dankali with vegetables source ya kalli mahaifiyar tasa shi kansa yana mmki ace ita ta haifesa shiyasa da yawan friends ɗinsa basa yarda sai sun tambayi Ya Heemu, ajjiyar zcy ya sauke kafin yace “Ina kwana Mumy?”  A hankali ta ɗaga kanta tare da watsa masa Idanunta wanda sukai jaa kana ta ɗauke tana jan mug domin haɗa tea shi kawai take tunanin zata iya sha, cikin jan ajin daya zama jikinta tace “Yaka tashi hope ba wata matsala” Arman yace “Yes Mumy, Mgnar  matsala kuma kin san akwai” tana zuba milk tace “Ok dear ina jinka” ya marai-raice fuska yace “Mumy how can you imagine life without you a gidan Abba, and ba wannan ba tayaya kike tunanin zan iya jure ganinki a gidan wani bana Abba ba, dan Allah Mumy ki koma sbd ni da kuma soyayyar da kike min” tunda ya fara mgn take shan tea ɗinta a hankali tana rufe idanunta, Yes tana son Abban Arman amma ta ina zata fara? Zata ƙasƙantar da kanta ne Just sbd she want come to him, this is difficult abu ne mai wahalar gske haka kuma bashi ya buƙaci hakan ba.

Jin tayi shiru ya kama hannunta ya riƙe cikin nasa kamar zai kuka yace “You’re my mother kinfi kowa sanin soyayyyar da nake maki Mom! Dan Allah sbd ni, ban san mene matsalar ki da Abba ba, amma koma mene ina son ya zama tarihi ko koma kamar da asalin masoyan Gsky, Mom! Yanzu duk kwalliyar ki da iya girkin da tsaftar ki sai dai wani ya mura?” Kamar daga sama taji saukar Muryarsa yana faɗin “Kai kuma kana baƙin ciki” girgiza kai Arman yay yace “No Ya Heemu is not like that, kai ma zaka tayani kishin Abba ai,dan Allah kasa baki”  Mannal kam tuni tayi suman zau ne, da sauri ta juya ta kalli inda yake no wonder ashe yana left hand ɗinta shiyasa gaba ɗaya ƙamshin sa ya gana gundirarta, yana zaune kai ba zaka taɓa cewa shi yay mgnar ba sbd yadda ya ɗauke yana duba wayar hannunsa, yana sanye da wasu blue ɗin suit, wanda sukai masifar haska baƙar fatarsa ya manna wani baƙin glasa a idanunsa ba zaka taɓa cewa ga halin da yake ciki ba.

Ɗauke kai tayi Uncle yay dry yace “Ya Heemu baku gaisa da Mumynku ba” idanunsa akan Wayarsa yana tsotsar strowbeery a bakinsa cikin tattausan Muryarsa mai kwarjinin gske irin ta ƙasaitattun maza yace “Mrng Mumy” Mannal wani baƙin ciki ya kamata ganin kallon da Uncle ke mata yasa tace “Ibrahim Ya gida” ajjiye wayar yay gaba ɗaya ya juya gareta yace “Mmy i miss You so much baki ko nemana” ya faɗa yana bata side hug kan Uba ta faɗa a ranta lallai Ya Heemu bashi da kunya ji yadda yake acting like duk abinda yake faɗa Gsky ne, Khausar tace “Ya Heemu kwana biyu Mmynka sai addu’a” ɗan Murmushi dole tayi kana a hankali ta ɗan rungome sa tare da shafa fuskarsa tace “Sorry Heemu na” tayi hakan ne domin ta nuna ta fishi iya tsiya, Arman yace “Mmy ni ko kiss ɗin da kike min a kumatu kin dai na” Ya Heemu na ɗan ɗauke kai tare da juyar da kansa dai-dai fuskarta yana aikata mata da wani kallo mai kashe jiki kafin a hankali yace “Nikam yanzu za’a rama min” zare ido tayi shima ya zare mata nasa idon yace “Ohhh!! Mom” runtsa idanunta tayi ta ɗura bakinra gefen baƙar fuskarsa ta masu small kiss, tana shirin ɗauke fuska yasa tattausan softness hands ɗinsa ya riƙe fuskarta mai taushi da laushi sai ƙyalli take yace “Ohhh Ya rabb! Uncle Mom cewa idanu take ne?” Uncle yace “Waya sani, tunda ta rabu da mijinta take cikin damuwa” Shiru Ya Heemu yay gani ta haɗe rai tamau fuska ba walwala dai-dai kunanta yace “Get ready, Soon you’re going to be Mrs Ibrahimul Khalel Sha’aban the richer young man” yana faɗin hakan ya zame fuskarsa yana taɓe baki kafin yace “Allah ya dai-dai ta” da sauri Arman yace “Amen Ya Heemu, Abba ma yace kije office ki samesa kuyi mgn” Ya Heemu ya ɗauki wyarsa ya ɗura a kunne kafin ya ɗan ɗaga Murya yace “Don’t ever try to go” sarai tasan da ita yake kallon Arman tayi tace “Ok My son” tana faɗin haka ta miƙe ko tea ɗin bata gama sha ba, upstairs tayi Uncle ya bita da kallo kafin yace “ita wannan halan bata san ta girma bane, shekaru sama da 40 ba wasa ba fa” Murmushi kawai Khausar tayi Arman kuma yay waje yana faɗin “Ya Heemu bari naje” ko inda yake Ya Heemu bai kalla ba sai da ya fice sannan Ya ɗan kalli Uncle yace “zan amshi abu gun Mumy” yana faɗin hakan yay upstairs yana ɗan shafa ƙirjinsa tana tsaye a parlon sama sai kai koma take tana ɗan yarfe hannu. Buɗe ƙofar yay ya shigo bata juya kamar zata ari baki tace “Ya Heemu ka fita a idanuna, idan baka da kunya ni ina da ita” waje yaja ya tsaya yana Kallonta yana kuma jin me take faɗa, wajansa ta ƙarasa inda yake tace “Let’s talk Ya Heemu, dan Allah dan Annabi mene yasa kake haka, kai baka san cewa Namiji ne wanda yake da ikon samun dukkan matar da yake so ba,  look at you Son, kana da kyau hankali ilimi ga kuɗi kaga ko ƴar sarki kace kana so billahi zaka samu…,” Saurin kai tafin hannunsa yay saman bakinta hakan yasa bata ƙarasa faɗin abinda tayi niyya ba, matsawa yay sosai kamar zai shige jikinta ɗaya hannunsa ya ɗura west ɗinta daga baya ganin tana ƙoƙarin faɗuwa, fuskarsa dab da ta ta, ya shiga sauke mata numfashi yana fesar da iska daga bakinsa kamar bazai ce komai sai kuma yace “Hate me or love me baya tsarin Khalel ina son amincewar ki, kisan cewa idan nayi niyar auran ki koda baki so sai nayi, why kike ƙoƙarin wahalar da kanki Mumy? Am your son, and you’re my Mom dan haka period sunayen mu zasu sauya daga haka zuwa miji da mata, ki dai na wahalar min da kanki” hannu tasa zata hankaɗa sa amma ko motsi bai ba, sai ma ƙara matse ta da yayi yana kallon tsakiyar idanunta wanda ya karanci ƙarancin rashin baccin dake damunta, ganin bashi da niyyar sakinta yasa ta sakar masa kuka ya riƙesa tare da tura fuskarta ƙirjinsa shiru yay domin babu wata ƴar mace data taɓa samun so close to him kamar Mannal, sai Moha wacce sai yaci ubanta yay mata doka taga babu sarki sai Allah shi ne take maƙale masa, sosai Mannal take kuka tana dokan Ya Heemu shi kam bai san me ake ba domin bai wani iya rarrashin mace ba, hasali ma kukanta bai damunsa ko kaɗan, ganin yadda take kuka wanda ya tabbatar daman ta daɗe tana tara kukan bata samu damar inda za tayi ba ne, sai yanzu da ƙirjinsa ya zame mata mafaka, sosai take kukan a wannan lokacin baƙin cikin abinda Abban Arman yay mata ya dawo mata sabu fil, ga rashin kirki da yaywa Dad ɗinta amma duk da haka zuciyarta shi take muradi tasha try kiransa amma kullum idan ta kirasa dry yake mata yana faɗin ta rasa mijin aure tsuhuwar mace like her babu wanda zai aureta, dan haka idan tana son ta koma gidansa dole sai tazo ta durƙosa akan ƙafafuwanta ta basa hqr akan idon ɗan ta, hakan zai sanya ya ƙara wanke laifinsa tunda ya shaidawa Arman cewa ita tace ya saketa.

🤔ANYA YA HEEMU ZAI SAMU DAMAR AURAN MANNAL KOWA? TEAM MANNAL ME KUKACE?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *