AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 10 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Mammah ta dago ido daga talabijin ta dube shi a sanda ya shigo falon yana daura agogon hannunsa, cikin shirinsa tsaf na shiga office. Daddadan kamshin turarensa (creed aventus) ya cika mata hanci. Hawayen farin ciki suka ciko a idanunta. A yau ga babban dan da ta haifa ya zama babbban mutum wani abin amfani ga al’umma, wahalar da suka sha a kansa wajen tarbiyya da neman iliminsa ba su fadi a banza ba. A cikin zuciyarta wannan addu’ar ta ke yi, wadda ba ta rabo da bakinta a duk lokacin da ta ga ‘ya’yanta za su fita; Rabbi ja’alni mugqimas-salaata wa min zurriyyaty, Rabbana wataqabbal du’a” .
Idan har iyaye za su kama wannan addu’ar a bakinsu a kan ‘ya’yansu, hakika za su zamo masu tsaida sallah, a idonsu ko a bayan idonsu. Sallah ita ce babban jigon kasancewa cikin nutsuwa da tsoron Allah ga matasa. Kuma ita ce abin da ke ba su wahala a yanzu shi yasa zina ta yawaita,
ZAMU TASHI
musifun rayuwa suka addabi matasanmu. Inka tsaida_ sallah hakika ka ribaci gabadayan rayuwarka, domin ita din garkuwa ce daga aikata alfasha da aikin munkari, shi ya sa Hajiya Maryam ba ta wasa da yi wa ‘ya’yanta wannan addu’ ar.
Rolex yake daurawa a damtsen hannunsa na hagu, ya yi fes! Ya yi wani irin fresh da shi. Duk kodewar da ya yi sabida wahalar karatu, yanzu ta bace. Kyawunsa da kwarjininsa sun kara fitowa fili. Sosai Mammah ta ke kallonsa tana marmasa wannan addu’ar a zuciyarta, har da addu’o’in nema masa tsari daga duk wani abin ki,makiya da mahassada, domin kwarai yaron nata ya burge ta, ya kuma ba ta sha’awa, ta ji wani wata sabuwar kauna sosai a kansa a zuciyarta. “Mammah na fito, na makara fa, yau ko karin kumallon wannan ‘yar taki ba ta bani ba”.
Mammah ta yi murmushi “Ga shi nan a kan tebir, ba ta jin dadi ne shi ya sa ban tashe ta ba. Mararta ke ciwo”. Cikin rashin damuwa ya ce “To ba sai a kai ta asibiti ba? Ni na tafi Mammah babu time din da zan tsaya karyawar ma fa, ana jirana”’. Mammah ta ce “bari in sa Azumi ta sanya a basket ta sa maka a mota”. Ya wuce yana fadin. “Toh, ta hanzarta”’.
Da ya dawo office bai samu Mammah a gida ba, Daddy ma bai dawo ba. Azumi ce kadai a gidan. Yana tafe yana waya da Mu’azatu kamar masifa. Yarinyar ta gama kame zuciyarsa da dadadan maganganunta na soyayya. Tana da baiwar sarrafa harshe da iya zance mai sace zuciyar masoyi, ba mamaki tunda lauya ce. Hakika ya yi nisa a son Mu’azatu da kyar in burin Mammah zai cika a kan kudirinta. Baba Azumi ya tarar tana mopping a babban falo “Mutanen gidan ba sa nan ne Mama Azumi?” “Sun je asibiti, amma yanzu za su dawo”Waye ba lafiya?” Ya fadi Www.bankinhausanovels.com.ng yana bude warmers din abinci da ke jere saman dining-table din falon cikin rashin baiwa zancen muhimmanci. “Addah ce”. In ji Azumi. Wace ce Addah?” Ya tambaya, don shi bilhaqqi bai san wata Addah ba bayan Kakarshi ta Kano. “Tna nufin Hafsat” Suhaana?”’Tta fa”Da ma sunan Adda aka sa mata ba HABIBA ba?” “Eh”. In ji Baba Azumi.Cikin ranta tana mai mamakin yadda akayi bai san hakan ba shekaru dai-dai har goma sha bakwai. Amma da tayi tunanin yadda baya zama tare dasu a duk tsayin lokacin sai ta kore mamakin. Ya zauna a kujera ya fara cin abincinsa cikin kwanciyar hankali.
Bai tambayi me ya same ta ba, don a ganinsa ba abin da ya shafe shi ba ne. Itama tsohuwar cigaba tayi da ayyukanta cikin falon bata kara ce dashi komai ba, saboda babu sabo tsakanin su sosai kamar su Ishma da suka karasa girma a hannu ta, kuma sosai yake mata wani irin kwarjini kamar maigidan gashi da wani irin tsare gida. Mammah da diyarta Hafsat a teburin likitar mata Dr. Hajara Bello a hamshakin asibitin (Diff Hospital) dake nan Asokoro. “Jinin al’ada ne za ta fara, ta dade bata fara ba, wasu yaran daga shekaru sha uku ma suke fara al’ada, ki kwantar da hankalinki. Da ya zubo shi kenan, (pain reliever) kadai za mu ba ta. Wasu matan kan yi fama da hakan idan za su fara al’ada. Wasu yana ci gaba har sai sun yi aure za su samu saukinsa, wasu har su haihu. Yanzu in za ta sake yin wani zai zo da sauki ba kamar wannan ba. Da ta fara irinsa a ba ta wadannan kwayoyin da na rubuta mata”. Mammah ta yi godiya ta karbi takardar maganin, suka fito. Ta tsaya a (Pharmacy) ta saya suka taho gida. Don azaba Hafsat ba ta san inda kanta yake ba. Suna tafe a hanya Mammah na mata sannu, tana shafa mata bayanta. Ta hada gumi kashirban. Hajiya Maryam na fadi a ranta, “Hafsatu an girma, daga yanzu zuwa kowanne lokaci za ki iya daukar ciki. Ki yi hakuri, kina so ko ba kya so, AURE zan yi miki’.
Sanda suka iso falo Abdul’azeez ya gama cin abincinsa, yana kokarin mikewa daga dining din. Idonsa ya sauka a kan Hafsat, wadda rabin jikinta ke rungume jikin Mammah, sai cije lebe take yi. Idanunta ko bata iya bude su, Mammah na rike da ita. Ya wuce hanyar dakinsa yana _fadin, “Mammah sannu da zuwa”. Cikin bacin rai Haj. Maryam ta kira sunansa.“Abdul’azeez!” Cak! Ya tsaya, don in ka ji Mammah ta kira sunansa to ranta ya baci ne. Bai juyo ba, amma ya dakata. Cikin fushi ta ce,
Baka ganina tareda mara lafiya ne? Is this a way to address a patient ?” “Yi hakuri Mammah”. Kawai ya ce. Tareda dukar da kansa kasa. Wannan halin nasa na ko’in’kula da al’amarin mutane yana bala’in bata haushi. Ta yi tsaki ta ja Hafsat suka wuce jin wayarsa na kara da wani lafiyayyen tune mai Www.bankinhausanovels.com.ng sanyaya zuciya da ta dade da fahimtar na Mu’ azatu ne. Domin duk sanda ya ji shi zai tashi ya kebe, in kuma daya tune din ne zai amsa shi a gaban kowa. Saida suka kai kofar dakin Hafsat ta juyo ta dube shi. “Za mu yi muhimmiyar magana ni da kai da Daddy, karfe goma na dare”. “Ok, Mammah”’,
Ya wuce dakinsa, su ma suka yi ciki. Hafsat ta sha magungunan ta ta kwanta, Mammah ta nufi dakin Daddy. Ba ta dade da hadiyar magungunan ba bacci mai nauyi ya dauke ta. Karfe goma daidai Daddy da Mammah suka fito karamin falonsa, bayan sun shirya komai cikin sirri a tsakaninsu. Abdul’azeez suke jira. Ba su dade da zama ba shi m ya shigo cikin kaftani na danyar farar shadda mai gautsi, sai maiko ta ke. Dawowarsa kenan daga gidan wata Antin Mu’azatu a Apo, Mu’azatun ta zo Abuja ta sauka a can don kawai ta ganshi, ta yi kewarsa da yawa, ya yi kewarta shi ma har yadda ba zai iya
kwatantawa ba. Shi kansa bai san adadin soyayyar da yake yi wa Mu’azatu ba, ta shiga ransa da yawa, yana shaukinta. Yana son karar da lokuta tare da ita don hakan na sanya shi nishadi. Yana sonta, ba ya gajiya da tausasan kalamanta masu kara masa kaunarta, yana son komai nata, ba shi da buri a halin yanzu sai na aurenta, su zama abokan rayuwar juna na har abada. Ya kudurce a ransa ba za’a tashi daga wannan zaman ba, ba tare da ya gabatar da maganar Mu’azatu ga iyayensa ba, su je su nema masa aurenta. Yana wannan tunanin yana murmushi cikin ransa, hango ranar da ya mallaki Mu’azatu yake yana kissima abubuwa iri-iri masu muhimmanci cikin rayuwarsa da za su gudana a ranar. Ya tsinkayi muryar Daddy can tsakar kansa. “In ka gama murmushin, sai ka arawa mahaifiyarka hankalinka”.
Da sauri ya dago kai ya dube su su biyun, sun masa kyau a idanunsa. Babu alamun tsufa ko kadan a tare da su, saboda tsabar kula da lafiya da samun hutu. Babu mai yarda sun ajiye Da kamarsa mai shekaru (29). Su ma kallonsa suke da murmushin cikin alfahari da shi a nasu zuciyoyin. Hakika ko ba su fada ba babu Da kamarsa a zukatansu. Sun dade suna ba shi ‘yancin kansa kan dukkan al’amuran rayuwarsa, amma a yau? Su ma suna son su motsa kwanjinsu na iyaye a kansa, ya yi musu alfarmar da ba su taba Www.bankinhausanovels.com.ng nema ba. Mintuna biyu suka share suna yi wa juna murmushin, kafin ya sadda kansa kasa.
“Mammah, ina fatan lafiya? Na shiga fargaba kan maganar da ki ka ce za mu yi muhimmiya, tun dazu ina babban falo sai yanzu da na ji saukowarku na shigo”. Mammah ta muskuta kadan, sannan ta ce “Maganar aure ne. Me ka shirya wa rayuwarka yanzu tunda gwagwarmayar neman ilimi da aikin yi sun kare?” Ya dago ya dubi Mammah, she’s talking now on behalf of Daddy, why ? Daddy da ke zaune ne ya kamata ya yi masa wannan tambayar ba ita ba, kasancewar ba ta yin hukunci a kan komai na rayuwarsu sai shi. Amma yanzu ya yi shiru yana duba jarida, kamar bai san me suke yi ba.“Ai Mammah a kan gabar maganar nake”. Ya fada cikin nutsuwa.
“Kamar ya ya?” Mammah ta tambaya kamar ba ta san me yake ciki ba. Na samu mata a Lagos”.
“Ga shi kuma ni ma na yi maka, tun shekaru masu yawa”Da hanzari ya cira kai ya dube ta, sai kuma ya sunkuyar. Mammah ta ci gaba da fadin.
“Ban san za ka iya ganin mace ka ce kana so ba ne shi ya sa na yi kan gaban kaina, saboda ni kullum kallon wani ustaz nake maka, wanda baida idon kallon mata, da sanin cewa ba za ka watsa min kasa a ido ba, kasancewar na san ban taba neman alfarma a gare ka ba a _ kafatanin rayuwarmu, shi ya sa na yi tunanin in na nema sau daya za ka yi min (alfarmar). Na dauka ba ka da buri a rayuwa sai na zama lauya, ban san kana da lokacin matan bariki ba a yadda ka ke tafiyar da rayuwarka”’. “Ba matar bariki ba ce”. Ya fada cikin gigicewa da karkarwar murya. Shi kansa bai san yaushe kalaman suka subuto daga bakinsa ba. Ban damu in santa ba, ko inda ta fito. Tunda ba abin da zan iya kulla mata a kanka. Bayan in ce mata ‘sorry’. Tunda ba’a yi shawara da ni ba kafin a soma ‘dating’ dinta. Ban san da ita ba, don haka don an ba ta hakuri ba zai zama laifi ba. Kai in ma na sani tuntuni birki zan taka akanta tun kan abin ya yi nisa, tunda kuwa ni ma ina da budurwar da na dade da tanadarma lauyan. Abdul’azeez ba shi kadai ne namiji ba, za ta samu wani a gaba, harma wanda ya fi shi, amma wannan Abdul’azeez din has a wife since ”Wani irin gumi ke barko masa tun daga tsakiyar sumar kansa har zuwa yatsar kafarsa. Me Mammah ke nufi ne a kan Mu’azatu? Ba fa duka kalamanta yake fahimta ba. Tun daga lokacin da ta ce “….. Ga shi kuma ni ma na yi maka mata tun Www.bankinhausanovels.com.ng shekaru masu yawa”.Sauran sama-sama ya ji su. Ai abin da ba zai taba yiwuwa ba ne a ce wata zai aura ba Mu’azatu ba.Ka yi shiru, sai zufa ka ke sharewa, me ye abin tashin hankali cikin maganganun mahaifiyarka?” Daddy ya yi magana lokaci na farko, bayan ya ajiye jaridar hannunsa a gefe. Tuni wani zazzabi-zazzabi ya rufe shi, idanunsa sun rufe ruf! Harshensa ya bushe karaf, babu digon yawu a bakinsa. Ya lashi busassun labbansa ya daure ya yi magana a sanyaye.Ai Daddy ban gane abin da Mammah ta ke fada ba ne sosai, ta yi maganar ya kamata inyi aure, na ce na samu matar da zan aura mun daidaita kanmu, ina gab da gabatar muku da ita ne”, “Ahh lallai’”. Inji Daddy. Wato duk dogon bayanin da ta yi maka ba ka fahima ba? To yaushe ka kurumce? Sai mu kai ka kasar da ba ka so a yo maka (hearing-aid). Ya fada a harzuke. “[‘m sorry Daddy, tunanina ne ya tafi nesa, amma wallahi da gaske ban fahimta ba”“To bari in yi maka dalla-dalla”’. Hajiya Maryam ta fada cikin hadiye fushi.“Na yi maka mata tun tuni, ita waccan din da ka ce kun daidaita ta yi hakuri ba za’a aure ta ba. Da kaina zan kira ta in ba ta hakuri. Mun dade muna bin ra’ayin ka, wannan karon alfarma ne na ce ka yi min, ka yi min biyayya a kan nawa ra’ayin sau daya tak! A rayuwa, ka auri zabina”Abdul’azeez ya kama kansa da hannuwansa biyu yana juyawa, “Wallahi Mamma ina son Mu’ azatu…….”Duk suka kama baki suka bi shi da kallo.
Abdul’ azeez ya ci gaba da cewa cikin gigicewa, “Mammah zan miki kowacce alfarma amma ki kauda wannan, in na yi haka na _ yaudari Mu’ azatu, na karya alkawari. Na karya zuciyarta na yi cin amanar kauna…… Babu wanda bai fusata ba a cikin iyayen. Cikin fushi Hajiya Maryam ta ce, “An ci amanar, an yi yaudarar, an karya zuciyar. Ta zo ta rufe mu da duka, wayar kuma da zan yi in ba ta hakurin na fasa. Soyayyar ta ci abu kazan-kazan ubanta!
Wallahi in ka ga ba a yi auren nan cikin watan nan ba, daya daga cikinku ne ya rasu, ko kai ko ADDAH! Mun ba ka kwana uku ka yi shawara da zuciyarka, da duk wanda ka yarda da shi na ka zabe mu, ko mace a kanmu. Tashi ka bani wuri”Ya dade bai tashi a wurin ba, yana zaune a inda yake. Zufar na kara kwarara fiye da farko. Dazu aka fahimtar dashi wacece da suna Addah a cikin gidansu, ba wata ba ce Www.bankinhausanovels.com.ng Hafsat-Suhaana ake nufi, wannan kankanuwar yarinyar data tashi gaban mahaifiyarsa, wadda aka haifa akan idonsa a Jeddah, ‘yar mai aikinsu Habibah, mara asali, ‘yar sakandire, shagwababbiya, wadda shi kwatakwata ko kyakkyawan kallo bai taba yi mata ba, bai taba daukarta a matsayin mutum ba. Cikin tashin hankali ya mike, ya isa gabansu ya tsugunna a kan gwiwoyinsa.Ku yi hakuri Mammah, na yi sa’insa da ku, ni ma ban so na yi ba. Na yi kuskure Mammah ki yafe min”. Sai hawaye a kan kafafunta. Zuciyar UWA, a take ta ji sanyi a zuciyarta. Ko da ma can fushin nata ba mai yawa ba ne, saboda ta san za a yi hakan. Ta kuma shirya karbar kowanne abomination dinsa. Yanzu an wuce wurin, tunda ta fada ya ji, ya yi reaction , lallashi yake bukata yanzu.
Hannu ta kai ta dago kansa, “Ya wuce Abdul’azeez. Ni dai in kana so ka faranta min, mu zauna lafiya ni da kai, to ka karbi zabina, ka yi min alfarma a kan hakan, ka yi min biyayya. Za ka samu duk abin da ka ke so a mace a tare da Addah, in ka yi hakuri zuwa gaba kadan. Duk da haka na ba ka kwana uku ka je ka yi shawara da zuciyarka ko da wanda ka yarda da shi, ka zo min da abin da ka yanke, ba ni lambar iyayen Mu’ azatun”’. Girgiza kai ya yi cikin sabon tashin hankali “Don Allah Mammah kar ki kira su, na roke ki da Allah. Suna da girma a idona, malamaina ne, sun yi min alheri mai yawa. Ni da kaina zan gaya musu a lokacin da ya dace, don Allah Mammah…” Hannu biyu ya daga alamar roko. Mamaki ya kara kashe iyayen a zaune. Wane irin so yake yi wa yarinyar haka? Anya Abdul’azeez ne? This stubborn child of her’s ? Duk ya sukurkurce sabida wata banzar yarinya? “Umh!” Mama ta ce, tare da daga kafadu da dan bude hannu har da kyabe baki (nuna alamu ne na ba ta da matsala da hakan, kuma ba ta takura ba, ba ta damu ba). Ya yi ta rike lambarsa, ita dai matsalarta a cika mata burinta, a auri Addarta, a rike mata ita cikin aminci. Cikin ‘ya’yanta hudu kuma shi ne zabinta, don ta san shi ne ya fi kowa nagarta, shi ne extraordinary . ‘As a mother (a matsayinta na uwa) wadda ta raine su dukkaninsu Www.bankinhausanovels.com.ng a tafin hannunta, tana da kyakkyawan yakinin an halicce su ne domin junansu, za su zauna lafiya cikin amana da juna. Za su gode mata watarana da wannan hadin da ta yi musu, za su yi alfahari da auren alherin da ta ke nufinsu da shi. Za su fahimci juna a hankali, su kaunaci juna, su zauna lafiya.
Haka Abdul’ azeez ya baro gaban iyayensa yana cikin rudu da tashin hankali da neman mafita cikin kwakwalwarsa. Mammah da Daddy sabgoginsu suka shiga cikin yin addu’a a zuciyarsu a kan Allah ya zaba masa mafi alkhairi a cikinsu. In wa’adin da suka dibar masa ya cika, ya zo ya ce ya amince shi kenan, in ya shafa wa idonsa toka ya ce zabinsla ya ke so ba za su takura shi ba, za su kyale shi ya auri wadda ya ke so, babu komai rayuwa ce, ka haifi Da a cikinka in ya girma ya yi ilmi ya ce, ya fi ka sanin abin da ya ke alkhairi a gare shi. Kwance yake rigingine yana fuskantar ceiling , tunanin mafita ga auren da iyayensa suka bijiro a gare shi yake yi, neman hanyar gujewa al’amarin yake ko ta halin kaka, saboda a gare shi abu ne da ba zai taba yiwuwa ba rabuwa da Mu/azatu, kuma wai wannan kwailar da aka haifa a kan idonsa ita ce matarsa. To me za ta ba shi? Me za ta yi masa? Aurenta ko child abuse ? Me zai dauka a jikinta? A yadda ya ci burin yin aure a dan tsukin nan, ya mori rayuwar aure kamar kowanne lafiyayyen matashi mai jini a jika kamarsa, wanda babu zina a tsarin rayuwarsa… a ZO ace wai wannan jaririyar ce matarsa? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un …… ita ya kama yana maimaitawa har nutsuwa ta zo masa. Me ya shiga kan Mammah ne? In ‘ya’yanta kawai ta ke so ta aura wa ‘yar tata ai ba shi kadai ne danta ba, akwai kanana daidai da ita, wannan ko jambaki bai taba ganin ta shafa ba balle hoda, kullum haka ta ke a kojale, ido ko kwalli babu. Ita Mammah ke ganin ya dace ta zame masa Www.bankinhausanovels.com.ng uwargida cikon farin ciki? Mahadin rayuwa abar hutawarsa? Ya san halin Mammah kwarai, tunda ta yi wannan furucin ba abin da zai sa/ba wanda zai sa ta canza. Sunansa sorry cikin farin cikin da ake samu a aure. Tunda ba za a aura masa wadda zuciya, ruhi da gangar jikinsa ke so ba. Sun manta da cewa kiyayyar namiji a kan mace ba karamin al’amari ba ne. Mace akewa auren dole a wanye lafiya amma ba cikakken namiji wanda ya san ‘yancinsa kamarsa ba.
Zuciyarsa ta yi duhu, idanunsa sun yi masa bakikkirin, har wani hayaki-hayaki yake gani yana fita daga idonsa, yana ji kuma yana gani wayarsa na haske da ruri da tune din Mu’ azatu, ya yi ya tsinke ya sake ci gaba, amma ko dan yatsansa ya kasa motsawa. Me zai ce wa Mu’azatu? Yarinyar da ta dauki soyayyar duniya da amanar duniya ta dora a kansa? Suka gama tsara rayuwarsu. yadda suke so? Ya san _ yadda Mu’ azatu ke da kishi a kansa, ta sha gaya masa ba za ta iya sharing dinsa da kowacce mace ba, don ma in yana da burin polygamy ya rushe, za ta iya rasa ranta a kan su mallake shi ita da wata. Duk kuma ya gaya mata cewa ya amince, shi da ma a tsarin rayuwarsa mace daya ce har bayan ransa. Duk wannan ya zama tarihi kenan? Zai rasa Mu’ azatu cikin dan lokaci kalilan? Dole ya yi wani abu, dole ya yi wata hikimar ta yadda ba zai samu matsala da iyayensa ba, ba kuma zai rasa mu’azatu ba.
Mammah ba uwa ce irin sauran iyaye ba, ita ko a cikin iyaye mata ta daban ce. Ta cancanci a yi mata biyayya kowacce iri ta ke so. Zai yi kokarin
kada ya bata mata, kuma shi ma ya faranta wa
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG