AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 12 KARSHE END BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 12 KARSHE END BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

Washegari daidai wancan lokacin da suka zauna wato karfe goma na dare, yau din ma tun kafin cikar karfe goman Mammah da Daddy ke zaune a falon suna ww dakon shigowarsa. Goma na bugawa da minti biyar Barrister Abdul’ azeez ya yi sallama ga iyayensa.
Sosai Mamma ta bi shi da kallo, so ta ke ta karanto yanayin da yake ciki, fuskarsa kadarankadahan ta kasa karantar komai, sai dai ta fahimci ba ya cikin damuwa kamar wancan lokacin. Kyakkyawan sajen nan ya kara kwanciya a kan fuskarsa kamar wani bako daga Qatar. Shadda ce (Getzner) ruwan kasa a jikinsa, kansa da hula mai launin ruwan kasa mai Www.bankinhausanovels.com.ng haske. Dole duk macen da ta san ciwon kanta ta yi wa kanta sha’awar hada rayuwa da Abdul’azeez Dakata, domin baiwarwakin da Allah ya yi masa suna da yawa, don haka bata ga laifin wannan yarinyar ‘yar Lagos data yi masa kamun kazar kuku ba, gata take so ta yiwa kanta. Mammah ta fada a zuciyarta.
Gefen kafafunta ya karasa ya zauna. Daddy ya dube shi yana murmushi. “Yau tun safe ban ganka ba”.
Ya dan muskuta, “Na fita ne Daddy, ban jima da dawowa ba”. Sautin muryarsa kadai suka ji suka fahimci babu sauran damuwa a tare shi.
A tare Daddy da Mammah suka sauke ajiyar zuciya.
“To ya ya? Ina maganarmu ta kwana?” Prof. Dr. Hamzah Dakata ya tambaya cikin raha. Mammah ba ta tsoma baki ba. Ya sunkuyar da kai, “Mammah na amince ki aura min duk wadda ki ke so ko da sun kai goma, na hakura da Mu’azatu na karbi zabinki

ZAMU TASHI 

Mammah, ki yi hakuri da jayayyar da na yi da ke ranar bana cikin hayyacina. Mammah na amince, ku sa min albarka”’Kura masa ido ta yi cikin kallo na kurilla, ita dole so ta ke ta karanto zuciyarsa, da ta kasa fahimtar komai sai ta furta abin da ke zuciyarta. “Amma ya aka yi ka canza ra’ayinka haka da sauri Abdul’azeez? Na fa sanka farin sani, na sanka a kan ra’ayi da akidarka, anya babu wata Www.bankinhausanovels.com.ng makarkashiya a zuciyarka? Ba fa zan yarda a cutar min da Adda ba, daidai da kwayar zarrah!”
Ya hadiye wani miyau ji kake, mukut. Mammansa sau tari haka ta ke kamar psychologist , she reads their minds easily, duk wani motsinsu ta sani. Ya kara zama serious ya sunkuyar da kansa.


“Mammah dole ne in yi muku_ biyayya kowanne ra’ayi nake da shi. Na bi Allah, na bi umarninku. Zancen Mu’azatu na ajiye shi a gefe ba don na daina sonta ba, da ma iyayenta ba so suke su aurar da ita yanzu ba sai ta gama (Law School). Amma Mammah ita din ta yarda ta amince Za ta aure ni?” Har yanzu kansa a sunkuye yake, bai dago ba yake yin maganar cikin tsanaki. Hajiya maryam ta ce, “Sunanta ne ba ka sani ba?” Murmushi ya yi, ya ce, “To Mammah sunayen nata ne sai mutum ya rasa na kamawa…” Dariya ya ba su sosai. Zabi guda daya wanda ya fi kwanta maka a ciki ka dinga kiranta da shi, kai kadai”. Inji Daddy.
Cikin alamun jin kunya ya sadda kai bai ce komai ba.
Hajiya Maryam ta rufe zaman nasu da cewa. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Sai ka koya mata amincewa da auren naka, tunda ka fita hankali, daga ranar da aka daura muku aure’”’.

******

A daki ta samu Suhaana tana ninke fararen (innerwears) dinta da ta wanke tana jerawa a sif din da ta ware musu. Tunani ta ke yi a zuciyarta tun dawowarsu Nigeria Mommah ba ta kara yin zancen karatunta ba. Bayan ta san babban burinta shi ne ci gaba da karatun, tana matukar burin yau a ce ta zama wani abu a dalilin karatu, ta tsaya da kafafunta ta fuskanci rayuwa mai cike da kalubale da ke gabanta. Tun ba ta kawo haka ba ta san ita ba ‘yar Prof. Hamzah ba ce, ba ta san ubanta ba, ba ta san ta inda ta shigo hannunsu ba. Ba ta son yarda da gaskiyar da ke a bude “ita ba ‘yar Mommah ba ce”, amma dole ta yarda, rashin zama ‘yar Prof. Dakata na nufin rashin zama ‘yar Maryam Dakata, iyakar gaskiyar kenan. Ta share hawayen da suka cika mata ido da bayan hannunta, Mammah ta ce sai ta cika shekara goma sha takwas za ta gaya mata komai da ya kunshi rayuwarta. Tana so ta nemo uban nan da uwar nan nata ko ta samu cikakken farin ciki irin na kowa. Hakan kuma ba zai zama mai sauki ba sai ta yi ilimin zamani mai zurfi, ta yadda ba sai ta nemi taimakon kowa ba a sanda ta tashi aiwatar da wannan jan kalubale da ke gabanta.
Cikin wannan halin na zurfin tunani Hajiya Maryam ta same ta, har ta zauna kusa da ita ba ta sani ba, sai da ta kai hannu ta kama nata ta rike gam cikin nata. A sanyaye ta sauke idanunta a kan Mammah kwalla cike da idanunta. Hankalin Hajiya Maryam ya tashi, ta ce. Addah tunanin me ki ke yi haka har da hawaye? Har na shigo na zauna ba ki sani ba”.
Ta kai hannu ta dauke hawayen ta kakalo murmushi.
“Mammah ina tunanin yaushe zan ci gaba da karatu ne?” Hajiya Maryam ta yi jimm! Sannan ta girgiza kai, “Shi ne kuma har da hawaye? Kayya, in kuwa shi ne ki yi hakuri rana ta farko da zan gaza wajen yi Www.bankinhausanovels.com.ng miki abin da ki ke so, sai dai hakan ba yana nufin ba za ki yi ba kwata-kwata a rayuwarki. Za ki yi idan mijin aurenki na so, kuma ya amince ki yi a dakin aurenki, ki yi hakuri Addahta, ina da dalilai na masu yawa da ba zan iya barinki karatun jami’a a gabana ba, na fi gane in bi umarnin Ubangiji in yi miki AURE sai hankalina ya kwanta ya tsumma a randa. Abin da kuma na zo in nemi amincewarki a kai kenan. Hafsatu aure zan yi miki”“Aure Mommah?” Ta tambaya cikin mamaki, da alamun kuma cikin sautinta da fuskarta ba ta gama fahimtar me Mammah ke nufi ba.
“Eh, aure irin nawa ni da Daddy, ki bar gidan nan ki koma gidan mijinki, ku rayu tare ki haifo min jikoki in yi ta raino. Ku yi zamanku lafiya ke da mijinki, mu da ke sai ziyara, haka Allah da manzonsa suka ce a yi wa kowacce “ya mace idan ta kai munzali, kuma kin kai, kin fahimce ni?” Idanunta suka yi rau-rau, gab ta ke da ta saki kuka, muryarta na rawa ta ce, “Mommah karatuna fa? Mommah in na rabu da ke da Baba Azumi ni da wa zan zauna?” Murmushin kwantar da hankali Hajiya Maryam ta yi mata tare da dafa kafadunta, cikin idanu ta ke kallonta. Kwayar idanuwanta na nuna zahirin kaunar da ta ke mata.
“Kwantar da hankalinki Addah, aure abu ne da kowacce ‘ya mace ta gada, kuma gaba yake da kowanne burinta. Shi fa wannan karatun na zamani ba Allah ne ya ce a yi shi kafin a yi aure ba. Duka da haka shi ma abu ne mai amfani, amma ko kusa amfaninsa bai kai aure ba. Ki fahimci abin da na fada miki a baya dalla-dalla, za ki yi karatun jami’a idan mijinki na so, kuma ya amince a gidanki. Amma yanzu aure zan yi miki, za ki bar mu ni da Baba Azumi ki zauna a gidan mijinki yadda kowacce mace da ki ka sani ke zaune a gidan miji. Amma na yi miki alkawarin duk sanda ki ka so ki ganmu za ki ganmu, zan Zo gidanki ko cikin dare ne kin ji Addahta?” Ta gyada kai alamar ta fahimta, sai kuma ta fada jikinta ta saka kuka. Bayanta Hajiya Maryam ke shafawa tana lallashinta. “Yi hakuri kin ji Addahna? Ba zan kai ki inda za ki cutu ba, ba zan bari a bata miki rai da gangan ba sai in ba na raye. Ki yi hakuri ki yi min biyayya yadda shi ma da ya fi ki shekaru ya yi mini. Na yi miki alkawarin insha Allahu dukkanku ba za ku yi da na sani ba, sai kun yi alfahari da wannan aure naku, sai kun gode min watarana”’Baba Azumi daga falo tana shara ta ke jin tashin muryar Mammah da alamun kukan ‘yar gidanta. Ta ajiye tsintsiyar ta taho. A bakin kofa ta tsaya tana kallon ikon Allah.
Kukan me ta ke yi? Ke fa abin kuka ba ya miki wuya, don Mamarki na shagwaba ki?” Murmushi Hajiya Maryam ta yi, “Wannan kukan mai dalili ne. Yau Mommah ta yi laifi dole ta ke lallashi, kukan aure ne na rabuwa da Mammah da Baba Azumi, ko Suhaana?”
Ta daga kai ta ce, “Eh”’Duk sai ta ba su dariya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mammah ta share mata hawaye, Azumi ta ce “To ai mijin na gida ne, ba za ki yi nisa da mu ba. Ni na taba ganin auren gata ma irin naki Hansai? Babban Yaya gabadaya fa, uban gida magajin gida, lauya na al’ummah na Hansatu bada kanka a sare, Yayan Isma’ila, Yayan Usmanu, Da daya tamkar da goma Mammah ta zabo miki duk cikinsu. Daina kuka kin ji? Yi farin ciki ki gode wa Mamarki, ita mai sonki ce”.
Nan fa Hafsat ta hau zazzare ido tsakanin Mammah da Baba Azumi tana so su yi mata karin bayani, wane Babban Yayan Baba Azumi ke nufi? Sai dai ba ta samu komai daga karin bayanin da ta ke son jin ba don Mammah ficewa ta yi kawai tana murmushin wannan kirari da Azumi ta yiwa Abdul’azeez.Da yake tayi maganar da ita tun jiya. Inda ta bada goyon bayanta dari bisa dari da kyakkyawar addu’a. Baba Azumi kuma ta wuce ta ci gaba da shararta suka barta cikin ci-da-zuci, sakar zucci da tunanin zuci mai nauyi. Ba dai wannan ‘baren’ (total stranger) na cikin ‘ya’ yan gidan nan ba? Ba dai wannan wanda ya fi kowa odd hali cikin gidansu ne ake nufin zai zama mijin nata ba????

**********

“Kina ina Mu’ azatu?”

“Har yanzu ina Apo, sai gobe zan bar abuja, mene ne? You sound worried?” “A ina zan same ki? Magana ce mai muhimmanci da ba ta bukatar distraction , gidan Anty kuma ba ya rabo da jama’a”. “To ko in zo office dinka yanzu? Sai direba ya kawo ni, ina ganin za mu iya tattauna kowacce irin magana a can”. Ta fada cikin faduwar gaba, jin muryar Abdul’azeez na rawa, abin da ba ta taba ji daga gare shi ba. “Alright” Kawai ya ce ya kashe wayarsa. Mota kirar matrix ta sauke Mu’azatu Rufa’i a Federal High Court da ke kan titin (OAU Quaters, Kashim Ibrahim Way Maitama, Abuja), cikin tafiyarta mai kama da tana taku a kan kwai ta karasa zuwa ofishoshinsu. Daya bayan daya ta ke wucewa tana duba sunayen da ke rubuce jikin wani dan karfe a saman kowacce kofa har ta zo inda ta ke nema. Barr. Abdul’azeez H. Dakata’. Shi ke rubuce a saman ofishi mai lamba (24). Ta kwankwasa daga ciki ya amsa, ta murda ta shiga. A kan doguwar kujerar leather ruwan kasa yake zaune cikin daya daga kujerun tattaunawa da baki da ke ofishin. Sanyin air-condition ya ratsa ta kamar yadda ya mamaye ofishin da kamshin turaren mamallakinsa. Mu’azatu na mamakin son sanyi irin na Abdul’azeez a gida ne, a mota ne, a ofis ko yaushe za ka same shi ya kure A.C shi ba wanda ya yi rayuwa a kasar sanyi ba. “Koma ki yi sallama malama, sannan ki shigo”. Ya fada cikin sanyin murya. “Ai na yi knocking ka ce in shigo”. “To ni bana son knocking saboda ni ba arne ba ne, Sau nawa zan gaya miki?”
Ta zumbura baki, ta koma ta yi sallamar ya amsa. A ranta tana fadin “yana cikin damuwar ma ba ya fasa ba da order, order dai! Da kyar nan gaba in bai zama Alkali ba”Kusa da shi ta zauna suka zuba ma juna ido, idanunsa sun kada sun yi jajir. Ba ta taba ganinsa Www.bankinhausanovels.com.ng cikin rashin nutsuwa irin na yau ba. Duk ya birkice kamar ba shi ba (smart-guy) mai tafiya da imaninta, yau har wani cukurkudewa gashin kansa ya yi ga wani gashin fuska ya karu na babu gaira babu dalili.
“Wai me ke faruwa ne Abdul’azeez? You look worried . You sound worried , ni ma ka dugunzumar min da hankali, da ina da hawan jini na tabbata da yanzu kafin na iso ofishinnan ya hau”. Ta fada a jere ko numfashi ba ta tsaya ta shaka ba. Tana rufe baki ya ba ta amsa.
“Duk a dalilinki ne Mu’ azatu’”’. “A dalilina? To me ya faru?” Kin yarda ina sonki Mu’azatu?” na yarda, amma me ya kawo wannan tambayar?” Ta fada da hanzari. “Na tambaye ki ne saboda ki yarda da ni, ki yarda da abin da zan gaya miki babu karya ko yaudara. Ba ni da nufin su gare ki shi ya sa na yanke shawarar gaya miki gaskiyar halin da nake ciki da iyayena a yanzu, kada ki ji a wani wuri daban ki yi wa zancen fassara a baibai ko ki yi tunanin na yaudare ki, amma in muka hada kai muka amince da juna za mu shawo kan mastalar, mu samu cikar burinmu a lokacin da ya dace da burin iyayenki. Kin yarda da ni Mw’ azatu?” Jikinta a sanyaye ta ce, “I trust you ka sani, ko mene ne ka gaya mini zan fahimta. Amma don Allah kada ka ce Mu’ azatu ba zan aure ki ba…!!!” Sai hawaye. Karo na farko da ya yi kuskuren kai hannu ya rungumo Mu’azatu a jikinsa. Nasa idanun na fidda kwalla. How he wish Mammah za ta fahimci karfin wannan soyayyar? Ba zai iya barin Mu’azatu saboda wata mace ‘yar uwarta ba, wadda ya tabbata ba ta da abin da ya fi na Mu’ azatun, ba ta fita da komai ba. Sai ma dai ace bata kaita ba. Ko ma ta fitan shi son da yake wa Mu’azatu (has no reason), wato babu dalili. Abin da ya sani kawai yana sonta, ita ma tana sonshi, ba don uwa-uwa ba ce sai ya ce wannan abun da da ta yi masa zalunci ne. Ba ruwanta da feeling dinsa, ita dai kawai a biya mata tata bukatar. Kwalla mai zafi ta gangaro masa, ya yi saurin dauke ta kafin Mu,azatu ta gani. A lokaci guda kuma ya sake ta ya janyo ta suka kalli juna. Ba zan taba cewa ba zan aure ki ba, it’s a promise . Zan aure ki komi runtsi, yanzu dai ki ba ni hadin kai ki ji damuwar tawa, kina kara min damuwa da fitar hawayenki Mu’azatu, bayan na kira ki ne don mu fahimci ta yadda za mu billowa matsalar, ba fa wata gagaruma bace (we can overcome it)”Mu’azatu ta share hawayenta, ta ba shi hankalinta. “Mu’azatu, kin san girman iyaye, kin san karfin ikonsu a kanmu, kin san tsattsauran umarnin Ubangiji a kanmu na mu yi musu biyayya, Ya ce (Ubangiji) “Wa qada rabbuka alla ta’abudu illa iyyahu Wa bil walidayni ihsaana ’, Ya kara da cewa, ‘ Wala taqul-lahuma uffin walaa tanhar humaa wa qul-lahumaa qaulan-kareema’ (Isra’i). A wata ayar ya kara cewa, ° Daga bautarsa sai kyautayi ga iyaye ……. Allah (SWA) ya kara cewa ma mu dinga nema musu gafara ko suna raye, kamar yadda suka ji kanmu muna kanana. ‘Wakhfidh lahuma janahazzilli minar rahmati Wa qul rabbir-hamhumaa kama rabba_ yaani saghira… (Isra’1) . Www.bankinhausanovels.com.ng
Mu’azatu duka wannan kadan ne daga ayoyin Ubangiji da suka yi umarnin mu zamo masu kyautayi da biyayya a gare su, wallahi Mu’azatu duk da wannan sanin sai da na sa kafa na take, na yi PROTEST (tawaye). Na yi jayayya da su a kanki, na shiga na fita ta wasu hanyoyin duk don in kaucewa umarninsu in tsira da ke…….” Mu’azatu ta shiga girgiza masa kai alamar, “A’ ah”Ya ce, “Yes, ban yi nasara ba ai, don haka na amsa wa bukatarsu. AURE za su yi min Mu’ azatu da wata macen ba ke ba…..!!!”Girgiza kai kawai Mu’ azatu ke yi, numfashi na neman dauke mata, tana neman shidewa. Tallafo ta ya yi ya rungume suna amfani da nasa numfashin. Kawai sai ga kira a wayarsa da ke gefe, juyawa yayi a hankali yana kallon sunan da ke yawo a fuskar wayar * Precious Mammah ’. Da sauri ya saki Mu’azatu don gani ya yi kamar itace tsaye a kansa ta kama shi rike da macen da ba tashi ba, rike da macen da ba su halatta mashi ba. Bayan ture Mu’azatu da ya yi daga jikinsa har dada ja baya ya yi ya sanya rata sosai a tsakaninsu. Hannunsa na kyarma ya amsa wayar Mammah. “Kana ina?”
Ta tambaya cikin muryarta mai sanyi. Kunuwanta na zuko mata kukan Mu’ azatu. Ina… ina… office Mam….mah…” Idan ka gama da ita, to ka zo ka gana da ita wannan ita ma. I think is high time ku fara fahimtar juna lokaci yana kurewa”. Ta kashe wayarta tare da sakin tsaki, “Me ake da matan bariki? Bin namiji har ofis don rashin mafadi?” Ta fadi cikin bacin rai da tafasar zuciya. Anya wannan yarinyar ba za ta zame wa Hafsat barazana ba in an yi auren nan? Anya da gaske Abdul’azeez yake zai iya rabuwa da ita? Tunanin da ya cunkushe zuciyar Hajiya Maryam kenan. Shi kuwa Abdul’azeez a sanyaye ya ajiye wayar, kalaman Mammah tas! A kunnen Mu’azatu, kamar da gayya ma Maman nashi Www.bankinhausanovels.com.ng ta fada don ta ji, Kamar ta bugo da gayya ne don sanin cewa suna tare a lokacin, ta tabbatar mata da abin da ya gaya mata. Kafin ya ankara sai ganin Mu’azatu ya yi ta kai bakin kofa ta kama ‘handle’ za ta murda. Yunkurawa daya ya yi, Mu’azatu ta ganshi gabanta ya kare kofar, ya sha gabanta. Kokari yake su hada idanu, amma ta ki. Kuka kawai ta ke yi. Ta gama gane irin auren da ake son yi masa, irin na yarinya (sweet 16) din nan da (Proffessional) wanda ya gama mallakar hankalin kansa, to ita zai rainawa hankali? Kamar shi za a yi wa auren dole idan ba yana so ba? Ko macen da ta yi karatu irin nasa ana yi wa auren dole balle shi namiji? Shi ne ya zauna yana tsarata yana jawo mata ayoyi shi ga Ustazu? Da wata makirar Mammansa mai muryar karuwai.
Cikin tsananin fusata ta dube shi, “Ka ba ni hanya in wuce Malam, lest you regret knowing me (don kada ka yi nadamar sanina”’. Minti goma za ki kara min kacal, zan ba ki hanyar…” Cikin gunjin kuka ta ce, “Bana son kara jin kowacce kalma daga gare ka, Allah ya hada kowa da rabonsa…..Ya runtse ido. Ji ya yi saukar kalaman tamkar digar dalma a zuciyarsa. Duk kokarin da na yi da wanda nake yi da wanda zan yi DOMINKI abin da za ki ce min kenan Mu’azatu? A halaka fa zan saka kaina don in tsira da ke Mu’ azatu…” Ta zame kasa, kan gwiwoyinta ta kifa kai tana kuka. Shi ma ya bi ta ya durkushe.
‘Wallahi zan aure ki Mu’azatu komai rintsi. Ki barni in yi auren don in zauna lafiya da iyayen a. Na yi miki alkawarin na SHEKARA DAYA ne da wasu watanni, lokacin kin kammala BL dinki”. Ta dago rinannun idanunta jike da hawaye, ta dube shi. Bai iya karya don ya burge ba! Wannan halinsa ne da ta dade da sani. Ba ya yi maka karya don ya faranta maka, kai shi kwata-kwata a halayyarsa babu karya, yana fadin abin da ke zuciyarsa ne kawai ba tare da tunanin zai yi maka dadi ko akasinsa ba. Tana son Www.bankinhausanovels.com.ng Abdul’azeez, tana son komai nasa, in ta ce za ta iya barinsa ga wata mace “yar uwarta, mai halitta irin tata data tabbata da cewa ba ta fita da komai ba ta fadi ba nauyi. Abin da ba za ta iya ba shi ne, tarayya da wata a son nasa, ko mallakarshi tare da wata.
Sai ta yi shiru da kukan tana goge hawaye, tana hadiyar zuciya. “Kin amince da abin da na fada Mu’azatu? Zan yi auren, zan rabu da ita a lokacin da iyayenki suka shirya aura min ke, zan aure ki’. Kallonsa ta yi cikin ido, tana kara jin wutar sonsa na fizgarta, losing him easily is not easy (rasa shi cikin sauki ba abu ne mai sauki ba). Ta samu muryarta na fita cikin tangardar harshe, Amma… amma….. ka san ba zan iya hada ka da wata ba ko? Ba zan iya zama da kishiya ba…Girgiza kai ya yi, “Ni ma ba zan iya zama da mata biyu ba. I know … na ce miki rabuwa da ita zan yi in lokaci ya yi, ki yarda da ni, ki amince da kalamaina. Bana magana don in bata lokacin ki da nawa. Ungo hannuna mu kulla alkawari…”. Ya mika mata karamin yatsansa, yana kallon cikin idanunta da yanayin da ta ke masifar so.
Wani tattausan murmushi ya subuce mata. Ta mika nata karamin yatsan, suka sarke su suna jifan juna da wani mayataccen murmushin SO. Sun amince an halicce su ne domin junansu. Don su zama abokan rayuwar juna, babu wata SUHAANAH da ta isa ta shiga tsakanin wannan soyayyar.

*********

To mai karatu, kai ka yarda da hakan? Anya kaddarorin rayuwa suna tafiya yadda muka tsara su ne? Anya Abdul’azeez bai yi kuskure ba? Abin da yake shirin yi me sunansa? Bravity ga Mu’azatu? Dishonestness ga Mammah? Unfairness ga
Suhaanah? Ko ko me yake nufi???

Hmmm mu tara a book 2

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *