AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                Www.bankinhausanovels.com.ng 





MUN TSAYA 

Suhaana ta share hawaye da tafukanta, haka suka yi ta bata baki da lallashi daidai lokacin da Daddy ya leko dakin zai ma Mammah magana, ya tsinkayi kadan daga zantuttukansu. Tsaki ya yi ya dubi Mammah da ta kwantar da kan Hafsat a cinyoyinta, ya soma sakin sababi irin wanda ya saba muddin zai ga Hafsat a wuri na babu gaira babu dalili.
“Yanzu wannan gansamemiyar yarinyar ki ke dorawa a kan cinya? Gata mugun abu, to kar ki je garin da ba’a sallar ki tafi inda ki ka fito mana? Mtsw! Ni ina ki ka ajiye min takardun da na ba ki dazu da safe? Shi ne abin da ya kawo ni”. Tuni Hafsat ta hau Www.bankinhausanovels.com.ng mayarkyata irin wanda ta ke yi in Daddy na mata sababinsa wanda ta fahimci ita kadai yake yi wa a cikin gidan nan, hatta Baba Azumi gaisuwar mutunci ke shiga tsakaninsa da ita.
Mammah ta bata rai sosai, ba ta ce masa ko kanzil ba, ta mike ta dauko takardun a (bedside drawer) dinta ta ba shi ya juya ya fita yana ci gaba da fadansa. Ba ya son sangartar da ake yi wa yarinyar nan a gidan nan, shi ya sa ta raina shi, ko gaishe shi ba ta yi in ta ganshi kamar ta ga mala’ikan daukar ranta. A karshe suna jin sa yana fadin. “Maryam kin kusa kawo ni bango. Ai gida

ZAMU TASHI 

Nigeria zamu je sai kin san yadda za kiyi kin nemo dangin mahaifiyarta, ba zan sake kwasarta zuwa wata kasa ba, balle watarana tace ni ne ubanta, rayuwar Turai ba irin ta Saudi-Arabia bace”.
Da haka ya wuce. Hafsat ta shige bandakin Mammah da gudu ta rufo kofar ta murda mukulli, ta durkushe a jikin kofar tana wani irin kuka sosai.

*********

HAFSAT-SUHAANAH

Wato tunda ta taso, ta soma wayon fahimtar abubuwa yadda suke a zahirinsu, ta fahimci Daddy ba Babanta bane, ba tare da kowa ya zaunar da ita ya gaya mata ba. Ganin irin yadda yake Www.bankinhausanovels.com.ng mu’amalantarta, ba ta da soyayya ko kankani a kwayar idanunsa, idan ta hada da yadda yake mu’amalantar Ishma (Isma’el), Haleem da Usman da wannan babban nasu mai zuwa duk bayan watanni uku da yafi kowa rashin sakin fuska a gidan in ya zo, wanda su Usman ke kira Yaya Azeez ko Yaya Abdul’azeez, duk wanda ya zo bakinsu shi suke kiransa da shi. Abin da har gobe ba ta sani ba, ba kuma ta ke son ta sanin shi ne; Mommah mahaifiyarta ce da ta dauke ta cikin mahaifarta, ko Baba Azumi ce da wannan alhakin?
Babu wanda ya taba tararta gaba da gaba ya gaya mata amsoshin wadannan tambayoyin da suka dade da suna yi mata katutu a zuciya da kwakwalwa. Duk wani gibi na uwa da uba da dangi Mommah ta cike mata shi, ‘yan uwanta sun cike mata da kauna sahihiya, Daddy ne kawai matsalarta a duniya, ba ta san me ta yi masa ko ta ke yi masa wanda ya haifar da kiyayyarta a zuciyarsa ba. Kiri-kiri yake nuna bambanci tsakaninta da ‘yan uwanta, wanda hakan ya fassara mata ita din ba ‘yarsa ba ce , ba za ka taba tsanar ko kyarar abin da ka haifa ba.
Ba ta taba sanya Yaya Azeez cikin jerin mutanen da ke cikin rayuwarta ba. Ta dauke shi wani ‘total Www.bankinhausanovels.com.ng stranger’ (bako ba dan gidan ba), ta hada su shi da al’amarinsa ta aza a muhalli na daban, muhalli iri daya shi da Daddy muhallin wasu mutane biyu da ke ji mata ciwo a zuciya. Ba ta taba yin wani abu don ta kyautata wa Daddy ya nuna ‘appreciation’ (jin dadin) hakan ba, komi ta yi laifi ne, abin fada ne. In ba ta gaishe shi ba don ta gane ba ya son kowacce mu’amala ta hada su, ya sauke wa Mammah kwandon bala’in ta janyo ta raina shi. In ta gaishe shi ya ce ba ya son hayaniya alhalin ba haka taga yana mu’amala da sauran mutane ba. Ta kan tambayi kanta. Ni din to su waye suka haife ni? Idan Mammah ce ko Baba Azumi ina Babana? Ko da gaske akwai wanda ke da uwa ba tare da uba ba? Shin uwa ita kadai kan samar da dan adam cikin mahaifarta? Ko ni din daga sama na fado dakin Mommah?”
Tambayoyi ne da amonsu ba ya rabo da yi mata amsa-kuwwa cikin kunnuwanta kullum ranar Allah. Taci gaba da kuka mai sosa zuciya tunda ba ta da wanda zai amsa mata tambayoyin da suka addabe tan, balle ta ji sanyi-sanyi.
Baba Azumi ce ke dukan kofar sosai, tana fadin, “Hafsatu bude, bude kin ji Hafsatuna, kin ga Mammanki ma kuka ta ke yi, idan ba ki daina ba kin bude kofar kin fito ba itama bazata daina ba…..”..
Bude kofar ta yi da sauri ta karasa da gudu ta fada jikin Mammah. Ta rungume ta tsam tana fadin, “Addata ki yi hakuri da Babanki kin ji? Ki yi masa uzuri, uzuri sau saba’in Allah yace ki yi masa kafin ki tuhume shi da rashin adalci a gare ki”.
“Na yi masa Mommah, kullum kuma cikin yi masa nake, cewa da yake ba shi ne Babana ba Mommah shi ne abin da ke sa ni kuka. Idan ba shi ba ne wane ne? Mommah ko ke kadai ki ka haife ni? Ko Baba Azumi ce?”
Mammah ta kara matse yatsun hannunta, “Na gaya miki ni ce uwarki. Ni ce ubanki, nice komai naki, ki Www.bankinhausanovels.com.ng daina sanya tambaye-tambayen nan marasa ma’ana a zuciyarki balle su dame ki. Ni na gaya miki watarana Daddy zai so ki, yanzu akwai dalilin da ya sanya yake yawan yi miki fada in kin shekara goma sha takwas na yi alkawarin zan gaya miki komai”. Da haka suka ci gaba da harhada kayansu. Karfe goma na daren washegari jirgin KLM ya kwaso Ambasada da iyalinsa daga birnin Jeddah bayan sun je sun yi dawafin bankwana a dakin Allah mai alfarma. Bai dire su ko’ina ba sai garinsu na haihuwa (Kano) inda suka tadda kafatanin zuri’arsu manya da yara a filin jirgin saman Malam Aminu kano sun zo tarensu, aka rurrungume juna sannan suka rankaya ( main house ) dinsu da ke Unguwar Dakata.
Gidan Malam Abdullahi Dakata, a yau komawa ya yi kamar gidan biki, bikin ma irin gagarumin nan, kwansu da kwarkwatarsu suna tare da mutanen Jeddah, ana ta hirar yaushe gamo na abin da ya shafi junansu. Sun samu Inna Ramatu, wato mahaifiyar Ambasada babu lafiya sosai, ta kuma ki yarda a kai ta asibiti sai Uncle Idris ke duba ta a gida.
Ba yadda Dr. Hamza bai yi ba Inna ta yarda ya kai ta asibiti, ta ki amincewa, ta ce, “Kun raina kulawar da Idrisu ke ba ni ne? Asibitin me alhalin muna da malamin asibitin a gida?”
Cikin tausasawa yace, “Inna duk da haka gara a je asibiti, su ke da kayan aiki, Idris taimakon farko (first aid) yake yi muku don Allah ki amince mu je”.
Lallashin duniya Dr. Hamza ya yi, amma baiwar Allahn nan ta ki. Allahu akbar! Kwanansu uku a Kano Allah ya karbi ran Inna Ramatu, ranar litinin a kan sallayarta, bayan ta idar da sallar isha’i tana lazumi. Adda ce ta shigo mata da abincin darenta, sai ta yi tsammanin bacci ne ya dauke ta a kan sallayar. Ta ajiye abincin ta matsa ta dauko filo don ta gyara mata kwanciya, nan ta tarar Inna Allah ya amshi abinSa. Salatin Adda cikin fadin, “ Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un ”. Shi ya janyo hankalin jama’ar gidan da ke tsakar gida an shimfida manyan tabarmi suna jam’in sallar isha, wadda Daddy ke limanta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Fadin irin gigicewar da Ambasada hamza ya yi na rashin nagartacciyar mahaifiyarsa abin ba a cewa komai, sai dai a yi gumm! Zuciyar maza ta girgiza ta azabtu. Ba abin da yake so a duniya in ka cire Baffa da iyalinsa kamar tsohuwar nan tasa. Inna Ramatu uwa ce abin koyi, abar alfahari a gare shi. Ba ta haifi kowa ba sai shi, don haka ba karamin so ta ke yi masa ba. Kamar wani abokinta haka ta dauke shi. Duk damuwar da yake ciki da ya yi tozali da Innar nan tayi masa murmushin nan nata, zai neme ta ya rasa. Bare in ya zauna a gabanta tana yi masa nasihohi a kan rayuwa da yadda ake maganin kalubalenta don samun nasara cikin rayuwa. Inna kan ce, “Hamza kada ka bari duniya da daukakar da Allah ya baka susa ka wulakanta dan Adam, ko ya ya yake wallahi watarana zai yi maka rana. Ka ji tsoron Allah, ka rike sallah, ka taimaki na kasa da kai. Ka rike addininka su ne sirrin zama lafiya da cimma nasarar komai a rayuwa”’Gaskiya tun bayan rasuwar kakansa Malam Abdullahi Dakata ba a kara yi masa mutuwa ba. Don haka mutuwar Inna ta doke shi yadda ba’a zato. Da safe aka yi janazarta, lokacin da suka kama gawar ta shi da mahaifinsa suka sa a kabari, sai ya yanke jiki ya fadi. Haka Baffa Atiku ya taro shi, aka kwashe shi aka sa a mota aka yi asibiti da shi. Ya sha dirif ba adadi, kwanansa uku sannan ya dawo hayyacinsa. Dakin asibitin cika yake makil da ‘yan uwansa, ‘ya’ya da iyaye, duk wanda ya zo wucewa Sai ya tabbatar wannan majinyacin dan dangi ne. Ko da ya dawo gida ranar sadakar uku ya zauna wajen karbar gaisuwa ba shi da kuzari, tsoron duniya yake da abin da ke cikinta. Ya yarda ba komi ba ce komin daukakar da Allah ya yi maka, rana daya za ka fadi, kuma ba ka san ranar ba, ka je ka girbi abin da ka shuka. Ya kan tuno ‘memories’ na rayuwarsa da mahaifiyarsa da yadda ta yi ta hidima da shi tun yana yaro, ya samu gatan uwa har girmansa. Wani bai samu ko nononta ya sha ba, hakika gatan UWA ya fi komai dadi ga dan adam a duniya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Gabansa ya yi wata mummunar faduwa da wata fuska ta zo ta gilma ta gabansa. A sanda yake zaune yana wannan tunanin, ba wata ba ce yarinyar gidansa ce Suhaana (Hafsat) ta wuce ta gabansa ba tare da ta kula da shi ba, kasancewar ba shi kadai ba ne zaune a kan katuwar tabarmar da aka shimfida ba a kofar gidansu, shi da abokansa ne biyu da suka zo masa ta’aziyya daga Abuja, Ambassadan Najeriya a kasar Senegal Dr. Yahya Garba, da Ministan huldar kasuwanci da kamfanoni na kasa baki daya (minister of commerce and industry) John Akure, a gefe kawunsa Minister Abdulkarim Dakata ne da nashi jama’an suna ta karbar gaisuwa. Ido ya bi ta da shi har ta tsaya a inda aka aike ta, wata (kiosk) ce nan kusa da su mai fentin gidan wayar MTN (yellow), da alama shagon waya ne. Ta mika kudi aka ba ta katin waya na dubu da dari biyar ta juyo. Fuskar uwarta ta gilma masa saboda yadda suke bala’in kama, hatta tafiyarsu iri daya ce don yakan ganta a kai-akai in tana hidima da yaransa a falo ko tana shirya abinci a (dining) kafin Allah ya dau ranta. Ya hanga ya duba a fadin wajen nan duka ‘yan uwansa ne na jini, da aminan arziki. Ita wannan yarinyar ba ta da ko mutum daya da za ta nuna ta ce nata ne, ba ta da wanda za ta yi tinkaho da shi a duniya da sunan ‘IDENTITY’ dinta. Ya hana a bata nono, ga shi rai da alkawari, Allah ya raya ta har ta soma balaga. Kalmar ‘sannu’ wannan ba ta taba hada shi da ita ba alhalin ta rayu a gidansa cikin iyalinsa tsayin shekaru goma sha uku. Anya abin da yake yi a kan marainiyar Allahn nan Allah ba zai tambaye shi ba? A kan wata akida ta kafurai wadanda suka samar da ilimin BOKO? Mahaifinsa ya ba shi ilimin addini yadda ya kamata, mahaifiyarsa ta hore shi da zama mutum mai tausayi, da jin kan na kasa da shi ba tare da tunanin abin da gobe za ta haifar ba, ko abin da za a saka masa da shi ba. Ya tuno ayoyi na algur’ani mai tsarki da suka yi umarni da babbar murya da a kyautata wa maraya. Wa ammal yatima falaa taghar’ (DHUHA; 9). Wa yas’alunaka anil yatamaa, qul islahul lahum_ khair, fa’in tukhaalidu) hum fa ikhwanikum…. Wallahu ya’alamul mufsidu minal muslih, walau sha’Allahu la’a’anatakum, innallaha azizun hakim (Bagqrah; 220 )
‘Wa’ abudullah walaa tushriku bihi shai’an wa bil walidaini ihsanan, wa bi zilqurbaa wal yataamaa wal masaakin …” Har zuwa karshen ayar (Nisa’i; 36).
A karshen ayar Ubangiji subhanahu wata’ala ya kara da cewa.innallaha laa ya hibbu kulla mukhtalin fakhoor ” Fassara; Amma maraya kada ku cutar Www.bankinhausanovels.com.ng dashi/cinye gadonsa”’ Suna tambayar ka (Yaa Muhammadu) akan lamarin maraya, ka fada musu cewa abin da Allah yake umarni shine kyautata musu, idan kunyi cudanya dasu to ‘yan uwanku ne. Allah ya san mai gyarawa daga mai batawa a cikinku,da Allah ya so da ya shiryar da ku. Hakika Allah mai iko ne mai hikima cikin lamuransa. Ku bautawa allah shi kadai kada kuyi shirka da shi, ku kyautatawa iyayenku da ma’abota kusancin zumunci, da marayu da miskinai da makotan ku na gidaje da matafiyi da kwarkwarorinku/bayinku. Hakika Allah baya kaunar wanda yake marowaci mai fariya. Tunaninsa bai gushe ba ya ci gaba da tuna masa yadda ya wanzu yana kuntatawa maidakinsa ‘yar uwarsa, abar kaunarsa, matar rufin asirinsa don kawai ta yi jihadin yin ceton rai don Allah da neman sakamako a wurin Ubangiji. Ya muzguna musu tsayin shekaru goma sha uku ba tare da sun yi masa laifin komai ba, ba tare da zaman yarinyar tare da su ya rage shi da komai ba. Zai iya rantsewa tun daga ranar da yarinyar nan ta shigo gidansa yake ganin albarka da ci gaba iri-in a rayuwarsa. Maryam ko uwarta ba ta taba gaya wa cuzgunawar da yake yi mata a kan yarinyar nan ba, balle tashi uwar har Allah ya dauki ranta…Hawaye masu dumi suka biyo idanun Ambasada Hamza, bai damu da ya kai hannu ya share ba, haka ya barsu suna ta malala a kan kundukukinsa. Abokan nasa suka ci gaba da ba shi baki, ba su san kuka biyu yake yi ba, kukan rashin mahaifiya da kukan nadama. Rayuwa kenan.
Hafsatu ba ta san bidirin da Daddy ke yi da zuciya da kwakwalwarsa ba, ta sayo wa Mammah katin wayar da ta aike ta ta kamo hanyar dawowa, kanta na sunkuye ta ke tafiya don ba za ta iya daga ido ta dubi taron mazan nan da ke zazzaune a kofar gida ba. Kamar an ce da ita ‘dago kanki’ gab da za ta shiga gida ta dan daga kai saboda jikinta ya ba ta ana kallonta sosai, ai kuwa karaf sai idanunta cikin na Daddy. Ta ganshi yana shatatar hawaye kamar karamin yaro suka yi ido hudu da shi. Tuni ta gigice taci uban tuntube da wani dutse dake gefe ta fadi kiff! A kasa. Don ta tsammaci a cikin taron mutanen nan balbale ta zai yi da bala’in da ya saba.
Ji ta yi an sa hannu biyu an dago ta. Ta ji zafin faduwar sosai da sosai, gwiwoyinta duk sun kukkuje lebenta ya fashe jini ya wanke bakin. Ta cira ido a sannu cikin dauriya ta dubi wanda ya daga ta Hamza Atiku Dakata ne. “Wace irin tafiya ki ke yi haka Www.bankinhausanovels.com.ng Adda? Ba kya kallon abin da ke gabanki? Adda in don ni ki ka rude haka don Allah ki yi hakuri, kar ki sake firgita in kin gan ni, ba dodo ba ne ni, BABANKI ne”.
Hafsat-Suhaana, ba abinda ta iya yi banda ta runtse idanunta, mafarki ne kawai ire-iren mafarkan da ta saba yi a kan Daddyn, saboda yadda ta sa damuwa da lamarinsa a ranta. Ta ki bude idon don ba ta so ta farka daga wannan daddadan mafarki. Daddy ya sa hannu ya dauko hankicinsa daga aljihu fari tas ya shiga goge jinin da ke zuba daga bakinta. Tuni mutane wajen biyar suka taso suka isko su cikin girmamawa wani likita abokin Uncle Idris ya kama hannunta ya rusuna ya ce da Daddy zai tafi da ita asibiti, ya koma ya zauna ba komai.
Dr. Isah ya kama hannunta tana tafiya da kyar saboda azabar da gwiwoyinta ke mata. A gaban motarsa ya sanya ta, ya shiga motar ya ja zuwa wani (private hospital) da yake aiki, ya gyara mata ciwuwwukan ya sa magani ya nade da plasta. Ya bata wasu ‘yan magungunan a leda ya dawo da ita gida.
Tuni labari ya isa ga Mammah daga bakin dan Anty Mariya, wai Adda ta fadi a waje, Daddy ya sa a tafi da ita asibiti. Sai ta ji maganar banbarakwai, ina ruwan Daddy da Suhaana har da zai ce a kai ta wani waje? Kar dai fa ya aika da ita gidan marayun da yake ikirari! Ai sai ta zabura ta mike da gudunta zaninta na kwancewa tayi sa’ ar riko shi kafin ya kai kasa, ko mayafi babu a jikinta ta yi hanyar soro. Luba ce ta dau mayafi ta bi ta da shi ita ma da gudun. Uban karo suka yi ita da Daddy da ke kokarin shigowa, saura kadan ita ma ta fadi. Jikinta na bari, muryarta na karkarwa cikin son fashewa da kuka ta kama shi tana girgizawa. “Ina ka tura a kai ta? Ina ‘yata, ina marainiya ta, ina ‘yar amanata?”’
Gani da ta yi yana hawaye ya sa jikinta ya yi matukar sanyi. Ta fada jikinsa ta fashe da kuka.
“Don Allah kada ka raba ni da Addata, na roke ka Daddy duk abin da ka ke so zan ci gaba da yi, in har za ka barmu mu rayu tare. In ka ce ma ba za ta bi mu ba na yarda mu zauna a nan, ka kara aure ka tafi da matar, wallahi na amince”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Girgiza kai yake yi, ya raba ta da jikin sa, ya ce, “Cool down Maryam, I have realized my shortcomings and I promised to become a changed person. Zan taya ki son ‘yarki da kula da ita har karshen rayuwarmu. Trust me!” Ya fada cikin sanyin murya yana share mata hawaye da tafukansa.
Maryam faduwa ta yi, na ce a kai ta asibiti. Na rantse miki da Allah bayan wannan babu wani abu”.
Maryam Dakata ta bi shi da kallo, irin kallon kurillar nan na son karanto zuciyar mutum. Kamar Hafsat ita ma ta dauka mafarki ta ke yi. Ta sanshi, ta san halinshi ba ya fadar abin da ba haka yake a zuciyarsa ba, wani irin frank person ne shi, saboda ba ya shakkar kowa, ko ya fadi abu don ya faranta maka bayan ba shi ne a zuciyarsa ba. Kwayar idanunsa masu haske da sheki sun gaya mata komai, saboda ba yau ta sanshi ba. Hakika ta yi hakuri da shi shekaru rututu, yau ga ribar hakurinta ta girba. Da ma an ce mahakurci mawadaci, kuma komai ya yi farko zai yi karshe da ikon Allah. Sosai ta rungume mijinta tana kukan da a yanzu ya san na farin ciki ne. Luba da ta biyo ta da mayafi ta dade a soron
farko rike da mayafin tana jiranta. Da ta ji kamar tattaunawar sirri suke sai ba ta labe ba ta koma cikin gida, wannan ba tarbiyyar da Adda Hafsatu ta yi musu bace, (wato labe). Www.bankinhausanovels.com.ng
Ibrahima autan Adda ne ya taho cikin gidan don kiran Daddy ya gaya masa ya yi wasu manyan bakin daga lagos, sai ya tadda su a haka a soro. Da sauri ya juya zai koma, suka saki juna Daddy ya kira shi. Ya dawo kansa a sunkuye ya fadi sakonsa, Mammah ta koma cikin gida, shi kuma ya fita. Hafsat ta shigo tana dingishi ta sha plasta a baki da kafafu. Tun kafin ta zauna Mammah ta taso ta taro ta tana tambayarta, “Garin ya ya ki ka fadi?”
Kowa sai sannu yake yi mata, bakin ya haye ya yi suntum. Halim ya dube ta, sai ya kyalkyace da dariya. Ta harare shi da kumburarrun idanunta, ya yunkura zai fice yana ta dariya yana yi mata sannu, sannan yace “Ina ruwan alkubus! Ya hau ya yi fam!”
Baba Azumi ta kai masa duka ya fice da gudu.
Ta ce, “Mommah tuntube na yi da dutse. Ga katin wayar ga canjinki”. Ta mika mata abin da ta kudundune a hannunta na dama. Duk azabar da ta sha bai sa ta zubar dasu ba. Tsabar girmama komai na Maman ta. Mammah ta karba tana fadin, “Ni wannan katin waya da ba a je siyansa ba!”. Wata zuciyar tace da ita. Gara da aka je siyansa, watakila shi ne silar dawowar Daddy kan kyakkyawar turba”’.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *