AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 9 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
. Baba Azumi ta ce, “To shi kuma Daddy fa? A hannun wa ku ka barshi a Abuja in anyi yadda kike tunani din?” Hafsat ta ce, “Sai ya dinga zuwa mana week-end”. Baba Azumi ta ce, “Wa zai dinga ba shi abinci to? Sai dai in kin yarda ya kara auren wata matar bayan Mamanki”. Hafsat ta girgiza kai da karfi, “In haka ne gara in yarda mu zauna a Abuja tare”. Baba Azumi ta kyalkyale da dariya, ta ce, “Na lura Hansai kishi za ki yi”. Hafsat ta ce, “Mene ne kishi?” “Dadina da ke Hausa ba ta ishe ki ba, kishi shi ne ka ji ba ka son hada abin da ka ke so da wani, ku amfana dashi tare, kin gane?” “Na gane, to dama wa zai so ya yi sharing abinda yake so? Ai abin da ka ke so ba ka son shi da kishiya”. Mammah na kicin tana jinsu tana murmushi. Baba Azumi ta dafe haba, “Ke nan ba za ki auri mai mata ba ko ke a karo miki Hafsatu? Ni kin ga kishiyoyi uku na zauna da su a aurena na fari. Ra-nar da mijinki zai kara aure ki ce sai mun zo da katafila danne kirji?”
ZAMU TASHI
Hafsat ta yi mata zuru da ido, Kafin cikin sanyin murya tace. “Wane ne mijin? Baba Azumi an gaya miki zan iya matsawa daga kusa da Mammah ne balle inyi aure?”’ Baba Azumi ta yi shiru, cikin zuciyarta ta ce. “Bari dai in yi shiru haka, kada Mammah ta ji mu ta ce zan gurbata mata tunanin ‘ya, ‘yarta ba irin ‘ya’ yanmu ba ce, rainon Turai ce”.Ta mika mata wayarta, “Ungo latso min Isma’eela mu gaisa, na kwana biyu ban ji shi ba”Ta yi hakan ne don kawar da waccan hirar tasu.
Maryam Dakata da ke kicin tana saurarensu ba tareda sun sani ba, juya ludayi kawai ta ke a miya sakamakon wani sabon tunani da ya shige ta mai nauyi a zuciya. Yadda Hafsat ta girma lafiya, ta rayu cikin aminci babu tabarbarewar tarbiyyar zamani da ta kafofin sadarwa ko kawayen banza, yarinya ta gari mai karancin budewar idanu na masifofin zamani, yaddatake jin labarin Nigeria da yadda mutanen cikinta suka koma muddin ta bar Hafsat ta shiga jami’a a Najeriya ba abu ne mai wuya ba kawaye ko samarin banza su sauya mata Hafsatunta ba. Su rusa mata ginin nan da ta yi shekara da shekaru tana yi a rana daya. Tana da labarin duk abubuwan da ke faruwa a jami’o’in Najeriya da wajenta, wanda tabarbarewar zamani hadi da shigowar tafi-da -gidanka da watsar da fadar Allah da Manzo (S.A.W) da kyawawan al’adunmu na iyaye da kakanni ya haifar. Wallahi-wallahi aure za ta yi wa Hafsat da Www.bankinhausanovels.com.ng
sun koma Nigeria a shekarunta goma sha bakwai, ba za ta barta ta je jami’a babu aure ba. Wannan ne kadai kwanciyar hankalinta. Ta runtse idonta da karfi ta bude, sa’ilin da wani tunani ya ziyarce ta, wanene MIJIN? Kamar yadda Hafsat ta ce. Wa ya ce yana sonta? Wa zai aure ta bai san ubanta ba? Wa zai aure ta koda yana son ta ba tare da watarana ya yi mata gori ko ya tozartata ba? Wa zai aure ta idan ya ji cewa ita da Dr. Hamza ba su ne iyayenta na haihuwa ba? “Babu!”
Zuciyarta ta ba ta amsa, “Ko da an samu babu wanda zai yi mata riko na gaskiya da amana irin yadda ki ke so ta samu a gidan aure in ba wanda ki ke da iko da shi ba… abin nufi, wanda kika haifa daga mahaifarki, wanda za ki sa shi ya yi, ya yi. Ki hana, ya hanu, ya yi mata ba daidai ba ki tsawatar da dukkan ikon ki. Su hudun nan duk kina da iko da su… amman guda ukun ‘yan uwan jini ta dauke su, abokan shawara. Idan wata mu’amala bayan wannan ta billa a tsakaninsu ba za ta gasgata ta ba, za ta kalle ta a mafarki ba reality ba. Wancan din dai da ba ta sani ba, wanda yake matsayin stranger a gareta ba ta san komai a kansa ba, ya fi dukkaninsu yin biyayya a gare ki. Ya fi su rashin shakuwa da ke wanda hakan ya haifar da ganin kimarki da jin nauyi cikin idanunsa fiye da dukkanninsu. In ki ka yi umarni ba zai tsallake ba, in kika sa kara ba zai gitta ba, yana so ko ba ya so. Wata zuciyar tace. Www.bankinhausanovels.com.ng
“balle ma wane lafiyayyen matashi zan wanke Hafsat in baiwa ya ce min ba ya so???” Sai murmushi ta ke yi ita kadai tana juya miya a kan wuta, zuciyarta jinta ta ke kamar an wanke ta da ruwan alkausara. Ta soma kidayar kwanakin da suka rage musu komawa gida Najeriya.
***********
A yau ake yaye su daga ‘Law School’ a jihar Lagos (call to bar ceremony). Bayan kwashe shekara daya cikin gwagwarmayar wannan makaranta,sadaukar da kai da juriya, wadda rayuwar cikinta tafi kama data secondary school boarding, ya sake fito da kwalin (BL) wanda ya bashi shaidar zama cikakken Lawyer. Barrister Abdul’azeez Hamzah Atiku, sanye cikin (black robe) da (WIG) dinsa. Ya yi kyau har fiye da yadda ya kamata a ce ya yi kyan, domin da gaske ya yi kyan babu karya. Gefensa iyayensa ne Hamza da Maryam, daya gefen Baba Azumi ce rike da hannun kyakkyawar budurwar zubin fulanin Yola. Kallo daya ya yi mata ya gane ta, ya ce cikin zuciyarsa,
“Yar Habiba ce ta girma haka. To shi girman yara mata bashi da wuya ne? Haka ya ga ‘yammatan Dakata duk sunyi irin wannan girman su Saima dasu Khalisa_ sa’anninta cikin dan kankanin lokaci. Yanzu ta ma rikide gabadaya ta koma Habiban, sai dai ita a goge ta ke sumul kamar tarwada. Kai ka ce ba ta taka kasa”. Fuskarta da yanayin zubin halittar ta baiyi kama dana cikakkun ‘yammatan Nigeria ba, tafi kama da ruwa biyu, wadanda a turance ake kira halfcast . Daga yanayin rashin sakewarta a wajen mutum Www.bankinhausanovels.com.ng zai gane bata saba shiga taron mutane irin haka ba, watakila shi ya sa dattijuwa Azumi ta rike hannunta. Sanye take da wata_ tsadaddiyar doguwar riga da mayafin ta ruwan bula mai turuwa sakar kasar Oman da takalmi mara tudun dunduniya dan shafal samfurin vincci . Shima ruwan bulan ne mai turuwa. Duk iyalin Abdullahi Dakata sun bakunci ‘Law School’ ta jihar Lagos a yau. The Barrister was now call to the Bar …… Inji Abdulkarim Dakata, ya fada_ tareda rungume jikan nasa cikin dariya. Haka Dr Idris da matarsa Dr. Tauheeda suka karaso wurin Uncle Idris ya rungume shi yana fadin “congratulations my grandson”. Shi dai murmushi yake yi, cikinsa kuma sai kartawa yake, weakness dinsa kenan ba ya jure yunwa, rabonsa da abinci tun jiya. In ka lura sosai za ka ga yana dan kalle-kalle kamar yana jiran wani. Ta yi masa alkawarin kawo musu lunch shi da bakinsa. Amma har yanzu bai ganta ba. Ga Baba Abdulkarim ya fara cewa a tafi a nemi restaurant mafi kusa su ci abinci su wuce ba za su kwana a Lagos ba. A hankali ta ke tuko kankanuwar motarta tana nema mata matsugunni a parking lot. Kallo daya ta yi wa ‘yan Dakata ta gane su domin duk suna kama da juna mazansu da matansu. Ta fito cikin shiga ta alfarma, sanye cikin wani tattausan (swiss lace) kalar kore me haske da ratsin kore mai duhu, ta murza daurin kai ya zauna tsaf a kanta cikin kwarewa da gogewa da yin hakan. Siririn mayafin da ta yafo kore ne me haske kalar dogon takalmin kafarta. Wadanda ke bayan motarta su ma suka fito suka bude ‘booth’ suka shiga fito da sundukan abinci dirka-dirka na alfarma suka doso iyalin Dakata.
Www.bankinhausanovels.com.ng Sakin baki suka yi suna kallo ana jere musu abinci na alfarma a kan kilishin da suka shimfida, kamin kyakkyawar budurwar ta soma gaishe su kanta a sunkuye cikin nuna kunya. Su dai amsawa suke fuska a sake, shi kuma ya dauke kai yana waya bai bada fuskar da za a fahimci wani bayani daga gare shi ba, har ta zo ta gifta shi za ta wuce. Suka hada ido suka jefi juna da murmushi, sannan ta wuce ta tada motarta, hadimanta suka shiga suka tafi. Mu’azatu’ sunanta, diyar tsohon ‘Attorney General of the Federation’. A baya ya rike mukamin zababben shugaba na ‘Nigerian Bar Association (NBA), sannan kuma ‘Senior Advocate of Nigeria (SAN) Habibu Rufa’i. A yanzu haka shi ke da mukamin (Director General of the Nigerian Law School) ta jihar Lagos daya daga cikin manyan malamansa a ‘Law school’ duk da shi baya koyarwa amma jininsa da Abdul’azeez ya hadu, yana zuwa neman karin ilmi wajensa. Haduwarsu ta farko da Mu’azatu tun farkon shigowarsa ‘Law school’ ne. Gidan mahaifinta cikin ‘Law school’ din ne a matsayinsa na (DG), asalinsu ‘yan Jigawa ne. Ta fara ganinsa a ofishin mahaifinta ya zo neman wani haske daga gare shi. Haduwarsu ta biyu a falon mahaifinta ne ya gayyato shi cin abincin rana.
Mu’azatu ta rasa nutsuwarta tun ganinta na farko da dan Hamza Dakata, shi ma dai bai san me ya Sa ba ya ji yarinyar ta dan kwanta masa da farko suka fara gaisuwar mutunci saboda Babanta , amma_ ba’ a jima ba Mu’azatu ta fiddo soyayyarta gare shi a fili. Da farko ya nuna rashin amincewarsa don yana da abin da ya sa a gaba fiye da soyayyar a lokacin, sannan soyayyar wani abu ne da baya cikin lissafinsa nan kusa, amma abin mamaki ba a jima ba ta rinjaye shi ya fara sonta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Itama Mu’azatu law ta ke karantawa a LASU (Lagos state university). Yarinya ce ‘yar kwalisa, kuma ‘yar gata domin ita kenan ga iyayenta. Ana ji da Mu’azatu kamar tsoka daya a miya. Duk da haka tana da tarbiyyarta daidai gwargwado, sai kuma idanunta da suka bude sosai da rayuwar Lagos wadda babu tsarin al’adun mu a ciki, matsalarta kadai girman kai da ji da kai, amma ai ta san a inda ta ke yin shi, banda ga wanda zuciya da ruhinta ke so. Don haka Abdul’azeez bai san wannan side din nata ba.
Abdul’ azeez bai taba kawowa ransa soyayya ba nan kusa, balle aure. Gani yake a lokacin har gobe ba’a haifi macen da zai so ba. He’s very selective and choosy when it comes to matar aure. Amma da shigowar Mu’azatu rayuwarsa ta rusa komai, duk da cewa da farko ta sha wahala kafin ya amincewa soyayyar ta. Mu’azatu ta fahimci matsalar Abdul’azeez da zaman ‘law school’ abinci ne. Ba ya son abincin sayarwa har ya gwammace ya yi ta cin snacks da kayan gwangwani a dakinsa in bai samu lokaci ya dafa da kansa ba. Tun haduwarsu ta fahimci hakan, tuni ta dauke nauyin cikinsa sau uku a rana da abincin gidansu. Da farko bai yarda ba don sanin cewa yau da gobe sai Allah, amma ta dage kan na gida ne, ba musamman ta ke yi ba. Balle ya ce tana shan wahala. Daga karshe ma da ya ki yarda dangana maganar ta yi da mahaifinta, wanda Abdul’azeez din ke matukar girmamawa, baki da baki ya kira shi ya ce da shi daga ranar kwanon abincinsa uku a rana ya koma gidansa. Www.bankinhausanovels.com.ng Da wannan damar Mu’azatu ta samu kasancewa da Abdul’azeez koyaushe in ba ta makaranta, har sabo mai karfi da makauniyar soyayya ta shiga tsakaninsu. In daya bai ga daya ba a rana sai ya gaza sukuni. Tsohon Attorney General Habib ya fi ‘yarsa farin cikin samun Abdul’azeez a matsayin mijin da ta tsayar za ta aura sabida ya gane yaron dan baiwa ne kuma ya san daga inda ya fito, ya san wanene mahaifinsa daga jin sunansa, sannan Abdul’azeez din ya tabbatar musu babu matsala daga iyayensa don su ba ma a kasar suke ba. Www.bankinhausanovels.com.ng Da wannan suka ci gaba da murza tsaftattacciyar soyayyarsu wadda ba sa bari ta shafi lokutan karatunsu, an ce wai sai hali ya zo daya ake tafiya tare. Ita ma Mu’azatu kwaruwa ce a karatun Law don kuwa tsotsa ta yi daga uwa da uba. Abdul’azeez kuma na son babbar yarinyar mai manyan kwalaye irin nasa, wadda ba sai ya sha wahala wajen sarrafata ba, gogaggiya, kilalliya. Don haka Mu’ azatu ta yi daidai da tsarin da yake son matarsa da shi ta kowanne fanni, ya sa ta kori duk wasu masu sonta ya yi mata alkawarin aure Www.bankinhausanovels.com.ng duk lokacin da ya shirya yin aure. A yadda ya kudurta a baya, bayan kwalin BL zai wuce ne ya yi Masters (L.LM ko MBCL) kafin ya yi aure, amma zuwan Mu’azatu zuciya da ruhinsa, ya sa ba abinda ya sa a gaba yanzu irin na ya shiga kotu ya fara aiki ya aure Mu’ azatu ko hankalinsu ya kwanta bakidayansu. Abdul’ azeez bai taba zina ba, bai taba sha’ awar ta ba, kullum kuma yana kara rokon Allah ya kare shi, don haka ya ga cewa yin aurensa da Mu’azatu a yanzu shi ne abu mafi a’alah a gare shi, domin kwarai yake yaki da shaidan da zuciyarsa yadda Mu’azatu ke nanike mishi, ta ke shiga har inda yake a duk lokacin da ta so. Sun yi alkawurruka masu yawa a daren jiya shi da Mu’azatu, duka na aure ne komai runtsi, ko da Daddynsa ya ce sai ya yi L.LM zai yi aure ya yi mata alkawarin zai aure ta komai daren dadewa. Shi ne yau Mu’azatu ta kawowa iyayensa da ‘yan uwansa abinci. Ba tare da sun tambaya ba suka gane komai; suruka suka kusan yi. Adda Hafsatu ce kawai ta ce yarinyar ba ta yi mata ba, idanunta a tsaitsaye kamar na kurege, sannan ba ta sonshi da auren bariki, ya je Kano ya samo yarinya ‘yar usuli, babu irin matan da ba a kyankyashe a Kanon Dabo ba, Jalla babbar hausa, yaro ko da me ka zo an fi ka.
Murmushi kawai ya yi a ransa yana fadin, irin kazaman yaran nan da ko alwala ba su iya ba, Adda ta ke so in je in auro? To da aikina zan ji ko da rainon karamar yarinya? Www.bankinhausanovels.com.ng Mammah dai babu wanda ya gane halin da ta ke ciki a kan Mu azatu, ta yi kokari ta boye Www.bankinhausanovels.com.ng
bacin ranta da kaduwarta. Ita a yadda ma ta dauki Abdul’azeez ba shi da zabi in dai a kan mace ne, ganin yadda neman ilimi ya zama priority dinsa fiye da komai. Ashe duk namiji komai tsaurin halinsa sunansa namiji in dai a kan mace ne. Har murmushin da suka yi wa juna shi da Mu’azatu ta gani. Mammah ta yi ajiyar zuciya a cikin jirgin Azman da suka hawo zai maida su Abuja. A fili ta ce. “Humm! Tabdi! Ashe za mu sabunta yakin duniya na biyu (world warlI) ni da Abdul’ azeez idan ya ce wannan mai tsayayyun idanun zai kwaso mini”. Www.bankinhausanovels.com.ng Daddy da ke gefenta da jaridar ‘daily Nigerian’ a hannu ya juyo ya dube ta. Ke da wa ki ke magana?” Ni da zuciyata. Ban ji ka ce komai a kan wannan yarinyar da Abdul’azeez ya kwaso ba”Me zan ce to? Bai isa auren ba ne ko me?” Mammah ta shiga girgiza kai, (showing resentment), “Ni ban ce bai isa aure ba. Amma na riga na yi mishi mata tun ina Brussels”Wace ce?’ In ji Daddy cikin mamaki.Addata!!!” Ta fada kai tsaye, tun kafin ya gama rufe bakinsa. Duk da ya gane wadda ta ke nufi, amma yana so ya kara tabbatarwa, “Kina nufin Hafsatu?’”’ Tta fa Daddy…” Ta warware masa daga hirarsu da Baba Azumi da ta ji wadda ta haifar mata da wannan tunanin, har tunaninnikan da ta samu kanta da yi a lokacin. Ta kare da cewa. “Daddy ina ganin wannan shi ne gata na karshe da zan yi wa Hafsat in san cewa na cike ladana, shi ma Abdul’azeez hankali na zai kwanta ko bayan raina saboda na san na hada shi da matar rufin asiri, nagartacciya wadda zai yi alfahari da ni a kanta a nan gaba”’. Gyada kai Prof. Hamza ke yi yana murmushi, “Mammah the match-maker …Suka kyalkyale da dariya gabadaya. Ta tsayar da dariyar tana dubanshi cikin ido.
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ka bar maganar wasa Daddy, mene ne ra’ayinka?”
“Ra’ayina? Ra’ayina shi ne ko kusa ba sai an yi yakin duniya na biyu ba, in kin yi masa umarni zai yi miki biyayya ko ba ya so. Amma ki sa a ranki ba a taba sanya wannan dan naki ya so abin da ba ra’ayinsa ba. Kin kwana da sanin wannan”’Jikinta ko kadan baiyi sanyi ba da wannan tuna tarwada ta Daddy. Yana rufe baki ta dora.“Su yi zaman aure cikin aminci shi ne ya dame ni ba su so juna ba. Soyayya ba lallai ta faru a sanda ake son faruwarta ba, ni in za su zauna lafiya to su tsufa babu soyayyar”.
*********
Sun dade a Abuja Daddy yana cuku-cukun komawa aikinsa na koyarwa a jami’a, kafin jami’ar Abuja ta dauke shi a matsayinsa na Farfesa. Sauyin rayuwar ba kadan ba ne, sai dai ga mutum wanda ya san mece ce rayuwa ya kuma yarda samu da rashi duk na Allah ne irin Hamza Atiku hakan ba zai sa su kasance cikin damuwa ba. Zuciyarsa a sake ta ke, yana ci gaba da harkokinsa cikin karbar canjin rayuwar da ya same shi rana daya, shi da iyalinsa.
Ba karamin hikima da dabara ya yi ba wajen bude wa ‘ya’yansa account a lokacin da duniya ke gara masa. Hakika ya tara musu abin da zai dauki nauyin karatunsu a ko’ina suke cikin duniya, har su gama su kama aiki, su dogara da kansu. Sati daya bayan ‘call to Bar ceremony’ Abdul’azeez ya dawo gida cikin iyayensa da ‘yan uwansa. An tura shi Federal High Court ta Abuja, inda zai fara aiki sati biyu masu zuwa. A zaman Abdul’azeez cikin satin Mamma ta kasa sukuni, tana hankalce da mu’amalarsa da kowa na gidan, inda ta gane abubuwa da dama a tare da dan nata, wadanda a da ba ta sansu ba.
Nisan muhalli na lokaci mai tsawo ya yi mata shamaki da shi. Ta fahimci ya yi nisa a soyayyar Mu’azatu Rufa’i, gab yake da ya bayyana hakan gare su. Gaisuwa kadai ke hada shi da Suhaana, bayan wannan ba wani abu. A kokarin Hajiya Maryam na son sanya sabo da shakuwa a tsakanin ‘ya’yan nata biyu, sai ta maida Suhaana mai hidimar Abdul’azeez; gyaran dakinshi kullum in ya fita motsa jiki da safe; kai masa karin kumallo in ya gama ya koma daki. Haka lokacin cin abincin rana da dare, ita Mamman ke aike ta kirawo shi dining , har a gama cin abincin kallo wannan Hafsat ba ta samu. Ba abin
da ya damu Suhaana, kullum cikin walwalarta ta ke, tunda ba ya kyararta, ba ya yi mata kallon banza, kusan kullum yana kwance cikin doguwar kujerar hutawa da ke gefe guda a falon gidan, yana waya da Mu’azatu. Www.bankinhausanovels.com.ng Sati biyu suka cika, Barrister Abdul’azeez Hamza Atiku ya shiga Federal High Court a matsayin lauyan gwamnati na kasa mai rajin kare hakkin ‘yan kasa. Idan ya fito fully robed (dressed in black gown and wig) sai ka yi masa kallo na biyu sabida yadda kayan suka amshe shi, suka zauna cif a jikinsa, suka fito da ilhama da cikar halittarsa.
Mammah ta dago ido daga talabijin ta dube shi a sanda ya shigo falon yana daura agogon hannunsa, cikin shirinsa tsaf na shiga office. Daddadan kamshin turarensa (creed aventus) ya cika mata hanci. Hawayen farin ciki suka ciko a idanunta. A yau ga babban dan da ta haifa ya zama babbban mutum wani abin amfani ga al’umma, wahalar da suka sha a kansa wajen tarbiyya da neman iliminsa ba su fadi a banza ba. A cikin zuciyarta wannan addu’ar ta ke yi, wadda ba ta rabo da bakinta a duk lokacin da ta ga ‘ya’yanta za su fita; Rabbi ja’alni mugqimas-salaata wa min zurriyyaty, Rabbana wataqabbal du’a” .
Idan har iyaye za su kama wannan addu’ar a bakinsu a kan ‘ya’yansu, hakika za su zamo masu tsaida sallah, a idonsu ko a bayan idonsu. Sallah ita ce babban jigon kasancewa cikin nutsuwa da tsoron Allah ga matasa. Kuma ita ce abin da ke ba su wahala a yanzu shi yasa zina ta yawaita,