AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 1 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Abdul’azeez, tana son komai nasa, in ta ce za ta iya barinsa ga wata mace “yar uwarta, mai halitta irin tata data tabbata da cewa ba ta fita da komai ba ta fadi ba nauyi. Abin da ba za ta iya ba shi ne, tarayya da wata a son nasa, ko mallakarshi tare da wata.
Sai ta yi shiru da kukan tana goge hawaye, tana hadiyar zuciya. “Kin amince da abin da na fada Mu’azatu? Zan yi auren, zan rabu da ita a lokacin da iyayenki suka shirya aura min ke, zan aure ki’. Kallonsa ta yi cikin ido, tana kara jin wutar sonsa na fizgarta, losing him easily is not easy (rasa shi cikin sauki ba abu ne mai sauki ba). Ta samu muryarta na fita cikin tangardar harshe, Amma… amma….. ka san ba zan iya hada ka da wata ba ko? Ba zan iya zama da kishiya ba…Girgiza kai ya yi, “Ni ma ba zan iya zama da mata biyu ba. I know … na ce miki rabuwa da ita zan yi in lokaci ya yi, ki yarda da ni, ki amince da kalamaina. Bana magana don in bata lokacin ki da nawa. Ungo hannuna mu kulla alkawari…”. Ya mika mata karamin yatsansa, yana kallon cikin idanunta da yanayin da ta ke masifar so.
Wani tattausan murmushi ya subuce mata. Ta mika nata karamin yatsan, suka sarke su suna jifan juna da wani mayataccen murmushin SO. Sun amince an halicce su ne domin junansu. Don su zama abokan rayuwar juna, babu wata SUHAANAH da ta isa ta shiga tsakanin wannan soyayyar.
*********
To mai karatu, kai ka yarda da hakan? Anya kaddarorin rayuwa suna tafiya yadda muka tsara su ne? Anya Abdul’azeez bai yi kuskure ba? Abin da yake shirin yi me sunansa? Bravity ga Mu’azatu? Dishonestness ga Mammah? Unfairness ga
Suhaanah? Ko ko me yake nufi???
ZAMU TASHI
Sanin cewa Mammah na jiransa a gida ya sa ya ki shiga gidan da wuri. Bayan rabuwarsa da Mu’azatu ya tuko mota a hankali kamar wanda kwai ya fashewa a ciki ya taho gida. Da ya zo kofar gidan bai karaso ba ya kashe motar daga nesa, ya kifa kai a kan sitiyarin motar ya rufe idonsa. A wannan dan lokacin ya tsara komai, ya tsara kalaman da zai yi wa Suhaana amfani da su. Ya yayyafawa zuciyarsa ruwan sanyi a kan ta rage tsanar yarinyar, ta sake da ita, yadda za ta fahimci duk abin da yake nufi. A kananan shekarunta yana da_tabbacin shawo kanta ta yarda da tsarinsa ba zai yi masa wuya ba.
Sai da ya tabbatar ya shirya kalaman a kan harshensa ya yi bitarsu sun zauna sosai, sannan ya tashi motar a hankali ya karasa gida. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mammah da ke dakon shigowarsa tana jin sanda maigadi ya bude masa get ya shigo ya adana motar a mazauninta. Ya tattaro wayoyinsa da briefcase hadi da kamfutar laptop ya fito yana rataye da falmaran din bakar ‘suit’ din jikinsa a kafadunsa. Bai yi tsammanin ganinta a falon ba, don ya san karfe tara ta ke shiga barci, yanzu kuma tara har da rabi.
Ya sanya a ransa Baba Azumi zai sa ta yi masa magana da Addar, don haka ya shigo kansa tsaye.
Sai dai me? Tana zaune tana jiransa har lokacin. Ta cika ta yi fam a kan kushin din falon. Ya ja ya yi turus! Da suka hada ido, ta sassauta fushin da ke kan fuskarta, cikin sanyin murya ta ce, Na dauka ba ka kai wa magriba a waje in ba da wani muhimmin case a hannunka ba?” Ya nisa a hankali, “Yi hakuri Mammah, wallahi baki na yi suka tsayar da ni, sai yanzun na samu kaina”’. Ta so ta ce da shi, “Baki ko budurwar banzarka?” Ta ga cewa shiga personal-life dinshi ba girmanta ba ne, sai kawai ta mike ta nufi hanyar turakar maigidanta tana fadin, Ka je study room Addar za ta zo yanzu”. A ransa ya ce, “Ai a bari na ajiye kayan hannuna, na bawa cikina hakkinsa, na dan yi freshen up kada ta ganni a jigace haka ta san cewa ta shigo rayuwata, ta takura ta da yawa”’.
Ita dai Mammah ta yi wucewarta, shi kuma ya nufi dakinsa. Sai da ya gama duk abin da zai yi, ya yi wanka ya shirya cikin T. Shirt mara nauyi (black colour), an yi rubutu da farin fenti dara-dara
(HILFIGER). Ya hada da darkblue wandon (jeans), ya taje sumar kansa, ya feshe jikinsa da turaren ( EternityMoment). Zuciyarsa ma na hango masa EternityMoment dinsa da Mu’azatu kamar yau ne, in har yarinyar nan ta yarda su rufa wa juna asiri.
Ganin karfe goma na dare ya sa shi yin saurin fitowa ya janyo kofar dakin. Ya karasa cikin gidan ya shiga dakin Baba Azumi da zummar ya turata ta kira Suhaanar. Ya yi sallama daga bakin kofar, ta amsa tare da yi masa izinin shigowa. Lekawa ya yi kadan yana fadin, “Ba ki yi bacci ba?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai ya ga Suhaanar kwance bisa cinyoyinta tana lallabe mata sassalkan gashin kanta. Ba mu yi ba, muna dakon dawowarka ne, sai kuma Adda ta ce in yi mata kalba kafin ka dawo”. To ga ni na dawo, kuma ina jin barci. Ku yi hakuri da kalbar nan haka”’.
Suhaanah ta mike ta lalubi dankwalinta ta daura. Ya wuce ‘study room’ din da Mammah ta yi umarni, ya zauna yana jiranta yana kuma duba agogon hannunsa. Hafsat ta dubi Baba Azumi cikin damuwa, “Idan na je bayan ‘ina wuni’ sai me zan ce masa?”
Baba Azumi ta juya kai cikin murmushi, “Ni ma ban sani ba!”. “Haba Baba Azumi, ba ku koya min abin da zan ce ba za ku tura ni in yi hira da shi?” Ta fada
kamar za ta yi kuka. Baba Azumi ta kafe ta da ido, “Ni da wa kenan?” Ta yi shiru, ta sunkuyar da kai. Jikinta ya bata tayi rashin kunya. “Ita me ya sa ba ki yi mata wannan tambayar ba, sai ni marainiyar wayonki ko?” “Yi hakuri“Toh, tashi ki je yana jiranki, kin ji ya ce bacci yake ji”. Ta mike a kasalce ta yafa mayafin abayar Oman ruwan makuba da ke jikinta, kusan shigarta kenan dogayen riguna kala kala da wuya ka ganta da atamfa ko leshi sai in zasu Kano, a cewarta zani yana mata wahalar daurawa shikuma lace nauyi yake mata, ta nufi dakin karatun nasu.
Kanta a kasa ta yi sallama ta shiga. Ya dago a hankali yana kare ma sigarta kallo. Doguwa ce, siririya, kamannin Habibah sun kara fitowa a jikinta, sai dai za’a kira ta mai kuruciya da gogaggen jiki fiye da Habibah sanda ta ke raye. Kuma Habiba ta fita kaurin jiki. Kwakwalwarsa ta soma daukan caji tana tuno masa wata hira ta karshe da ya yi da mahaifiyarta….. Rai-rai-rai hirar ke dawo masa… anya tunaninsa a kan Addah gaskiya ne? Hafsat BA SHEGIYA BA CE… Inda amana shi zai gaya wa kowa cewa da ubanta. Sai dai me? He is not after that (ba wannan ne a gabansa ba), tashi rayuwar ce, ba ruwanshi da rayuwarta. Ta dade da zama, ta gaishe shi bai ji ba. Ko ya ji bai amsa ba, ba za ta iya tantancewa ba. Ba ki iya gaisuwa ba?” Ya tambaye ta bayan ya dawo daga duniyar tunaninsa. “Na ce ina wuni tun dazu ba ka amsa ba”. Ta fada fa ‘accent’ dinta mai nuna har yanzu Hausar ba ta gama daidaito a bakinta ba, yaren Dutch (flemish) ya riga ya daddatsa harshenta. Taushin muryarta kawai ya kara masa kwarin gwiwar za ta amince da duk abin da ya zo da shi, akwai innocence intonation a cikin muryarta. Sake gaisuwar zan amsa yanzu”’.
Ta dan saci kallonsa don tabbatar da shi din ne Yayan su Halim din nan, ko ba shi din ba ne? Wancan ko a murya ba shi da kirki, wannan a cikin muryarsa akwai sassaucl. Ina wuni?” “Lafiya lau, kun wuni lafiya?” “lafiya alhamdulillah”. Ya yi dan jim kafin ya ce, “Mammah ta sanar da ke aure za ta yi mana ko?”
“Ta sanar da ni”. Ta amsa kamar cikin rada, ba don ya kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, da ba zai ji ta ba. “To ke me ye ra’ayinki?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba tare da ta dago ta dube shi ba ta amsa. Hawaye suna son cikowa a idanunta. “Ni ba ni da wani ra’ayi sai nata, ni abin ikonta ce, ni mai biyayya ce ga dukkan umarninta”’. Sai ya ji ‘yar kunyar kansa ta kama shi. Ba ta haife ta ba, shi ta haifa, ita a shirye ta ke da ta yi mata biyayyar, shi da ta haifa, ya gaza. Shiru ya ratsa, kafin ya kira ta a hankali, da wani suna da ba wanda ya taba kiranta da shi a duniya. “Hafsah!” Wani irin sauti ne mai taushi yayi amfani da shi wurin kiran sunan, wanda ba wanda ya taba yi mata amfani da shi a yayin magana, don haka ta dago don ganin wanda ya kira ta da shi din. Abdul’azeez Hamzah Dakata ne. “Like father like son!”. Hafsat ta fada a zuciyarta. “He looks so much like his Dad…… kuruciya kawai ta bambanta su’.
Ba ta zurfafa kallon nasa ba, ta sunkuyar da kanta, ba ta zaci yana da sassauci haka ba a yadda ta sanshi a baya, duk da dai ta fahimci a kanta ne kawai yake zama tough din a kan sauran kannenshi ba haka yake ba, mu’amala ce mai kyau a tsakani su; irin ta babban Yaya da kannen da yake matukar ji da su. Shin ko hakan na da nasaba da kasancewar ita din ba jininsa ba ce, bata da mahaifi? Za ta so watarana ya amsa mata wannan tambayar. Mene ne babban burinki a rayuwa? Ina nufin, bayan auren da Mamanki ke son ki da shi me kika fi so a rayuwarki?” Ta tsinci muryar Abdul’azeez a tsakar kanta, kafin ta gama farfadowa daga dogon tunaninta. Ta dan daga kanta sama alamar tunani, kafin kalaman su fito a nitse daga bakinta. “In ci gaba da karatuna, karatu mai yawa har PhD”. Ya tsaida idanunsa a kan ta. “Sai kuma me?” Ta dan yi nuku-nuku ta kasa fada sai motsa baki ta ke yi. “Hafsah feel free with me, bayan matsayina na Yayanki ni din kuma yanzu mijinki ne in Allah ya yarda. Ina so ki saki jiki da ni ki gaya min me ki ke so a rayuwarki komai wahalarsa ko tsaurinsa?” Ta dan samu nutsuwa kadan, ta waiga ta tabbatar babu kowa cikin dakin karatun daga su sai Allah! Ta saci kallonsa kadan kamar mara gaskiya, sannan cikin in-ina ta ce, “Ina so…. inaso in nemo mahaifina a duk inda yake, na san mahaifiyata ta rasu, Halim ya taba gaya min ta rasu ne wajen haihuwata, amma shi ba’a sanshi ba, ba a san inda yake ba. Na sha tuntubar Mommah kan maganar sai ta ce in bar zancen sai na yi shekara goma sha takwas zata gaya mini, yanzu kuma shekaru na sha bakwai, shima Haleem din tun lokacin tace kada ya sake ya kara yi min zancen”’Abdul’azeez ya nutsu yana saurarenta, da ta gama, ya sarke yatsunsa cikin junansu yana kallonta kanta a sunkuye. Da kyar yake gane abin da ta ke cewa da Belgian Www.bankinhausanovels.com.ng harshenta, amma duk da haka yana ganewa, ya ce.
“Hafsa, na ji dukkan bayaninki, na kuma fahimta. Na farko na amince zan barki ki ci gaba da karatu bayan aurenmu, da kaina zan cike miki JAMB da ake yi a nan Nigeria, am sure za ki haye daga nan zan kai ki jami’a ki zabi duk abinda ki ke so ki karanta. Burin ki na biyu ganin mahaifinki ko?” Ta daga kanta a hankali, tana wasa da yatsun hannunta. Na yi miki alkawari ni da kaina zan nemo miki shi insha Allahu. Na san garin da yake!”’Ta dago kanta da sauri, ta ware manyan idanunta a kansa. Amma ta kasa magana. “Da gaske nake Hafsah. Har yayye ne da ke guda uku, amma ban san maza ne ko mata ne ba!!”’Kawai sai ya ga hawaye ya gangaro kan kundukukinta, masu dumi, wasu na korar wasu. Mamaki ya kama shi ainun, amma bai bar hakan ya nuna a kan fuskarsa ba. Na yi tunanin abin da za ki ji dadi ne, shiyasa na fada, amma sai in ga kina kuka?” Ta sunkuyar da kanta, sannan ta share ambaliyar hawayen da bayan hannunta. Ni ma ban san me ya sa ni kukan ba, amma watakila kukan farin ciki ne!!”’. Ya ce, ““Yadda zan zama sanadin farin cikin nan naki, nake rokon ke ma ki zama sanadin nawa farin cikin da ba mai samar da shi gare ni sai KE!” Ta dago jikakkun idanunta ta kalle shi.
“Ni me nake da shi da zan saka maka wannan farin cikin da za ka ba ni? Iyaka tunanina ba ni da komai”’.
Ya sauko daga kujerar da yake kai, ya zauna dabas a gabanta. Idonsa ya kai ga yatsun hannunta da suka sha adon jan lalle ‘yan sirara da su. Ya dawo da kallonsa kan fuskarta cikin nutsuwa, ya ce.
“Ba abin da za ki ba ni Hafsah, kawai amincewarki nake nema mu yi planning contract marriage (AUREN KWANGILA) tsakanina dake na tsawon shekara daya da wasu_ watanni kadan’”’. “Contract Marriage???”
Hafsat ta tambaya cikin mamaki. Kafin ya amsa ta dora. “Kana nufin auren da Mommah ke nufi mu yi, dama (contract marriage) ne?” Ta tambaye shi cikin yamutsa fuska sosai na rashin fahimta. “Ba haka nake nufi ba. Bana so ko kadan Mammah ta san wannan zancen. Zai tsaya ne a tsakanina da ke kawai, zan cika miki manyan burikanki na rayuwa da izinin Allah kafin cikar wa’adin nan. Ke ma kuma za ki taimaka min wajen cikar nawa burin, ki samu farin cikinki, ni ma a karshe in samu nawa ba tare da kowa ya san me muke ciki ba har zuwa karshen wa’adin”.
“Ban gane ba har yanzu, mene ne wa’adin? Sannan ta ya ya za a yi hakan ba tare da wani ya sani ba? Mene ne ma naka burin? Meyasa Mammah bata gaya min hakan ba?” Ta fada cikin tsananin shiga duhu, fuskarta da yanayinta gabadaya sun nuna hakan, sun bayyana tsananin rudun da kalamansa suka jefa ta.
Gaskiya hausarta da shekarunta sun yi kadan su fahimci abinda yake nufi kai tsaye. Tana bukatar ayi mata gwari-gwari. Hafsah ina da wadda nake so in aura, sunanta Mu’ azatu. Mahaifinta Malamina ne shekarunmu biyu tare kenan, mun fahimci juna mun amincewa juna. Sannan mun yi wa juna alkawarin aure komai runtsi to the very end .
Amma Mammah ta ce ba ta amince ba, Daddy ya mara mata baya sun ce ke zan aura ba ita ba. Hafsah kamar yadda ki ka fada min burikanki a yanzu, da yadda ki ke matukar sonsu, da burin
ganin cikarsu. Ni Mu’azatu ce burina a yanzu. Bayan ita duk wasu burirrikana na rayuwa zan iya ce miki Allah ya cika min su (Alhamdulillah). Www.bankinhausanovels.com.ng
Za’a yi mana aure kamar yadda Mammah ke sO, mu zauna gida daya, in sanya ki a makaranta ki yi ta karatunki. Aurenmu babu takura, domin kowa zaman kansa zai yi kamar yadda dai ki ke zaune yanzu a gaban Mammah, gida kawai za mu canza bayan shi ina tabbatar miki ba abin da zai canja.
A cikin wannan lokacin zan nemo miki inda mahaifinki da ‘yan uwanki suke. Da gaske ne mahaifiyarki ta rasu a kan idona, ba zan taba mantawa ba. Ba zan ce miki komai a kai ba, ki jira Mammah ta gaya miki kamar yadda ta yi alkawari. Idan na yi miki hakan ina ga na gama cika burikanki ko? Sai ni ma ki cika min nawa burin wanda ba shi da wahala, abu ne mai sauki Hafsah, shi ne ki amince in lokacin da na dibar wa Mu’azatu na aurenta ya cika za mu rabu, wato ZAN SAKE KI. Mu hadu mu bai wa Mammah uzuri da cewa halinmu bai daidaita ba, ko kuma haka kaddara ta tanadar mana. Mun rabu ne ba don ba ma son juna ba, sai don kowannenmu ya kasa jure halin dan uwansa. A wannan lokacin na san ba su da wani zabi sai su barni in auri Mu’ azatu, ke ma ki auri wanda ki ke so. Ga mahaifinki da ‘yan uwanki a gefe da kuma karatunki, ina fatan kin fahimce ni?”
Ta yi shiru na tsawon lokaci, idanunta na hango mata ranar da za ta kammala karatunta ga mahaifinta da danginsa a gefe, dasu Mammah, kamar yadda aka yi wa Abdul’azeez a (Law school). Hakika ranar za ta zamo_ ranar madaukakin farin ciki a gare ta wadda babu irinta… Me ki ka ce Hafsah?”
Ta tsinkayi muryar Abdul’azeez mara amo kuma mai taushi a can tsakar kanta. Ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi mai nisan zango. Ta yi ajiyar zuciya, sannan ta daga kanta a hankali ba tareda wani dogon tsinkaye ba ta ce, “Na amince”’.
Ya gyada kansa shi ma, “Haka nake son ji, idan da amincewarki to komai zai tafi daidai babu tangarda har zuwa lokacin da (contract) din zai kare. Mammah ba za ta yi irin fushin da ki ke tunani da mu ba, za ta fahimce mu, in har ki ka gaya mata da amincewarki aka yi komai, kika nuna mata ke ki ka zabi sakin don ba za ki iya da halina ba. Ni ma na fada mata na kasa jure halinki ne. Kada ki damu I can manage the situation. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai dai ina so wannan ya zama babban sirri a tsakaninmu Hafsah. Sirrin da babu wanda za ki fada wa mun yi shi duk duniyar nan.
Sannan bayan rabuwarmu insha Allahu zan zamo mai taimaka miki ta kowacce fuska a rayuwarki, na yi wannan alkawarin. I promised!
Sai da ta daga kanta alamun ta fahimce shi, sannan ya mike yana sanya wayoyinshi a aljihu.
“Ina ga iyaka abin da za mu tattauna din kenan, dare ya yi. Ki je ki kwanta”.
Ya mike ya nufi kofar fita daga dakin karatun kai tsaye without giving her a second look (ba tareda ya kara kallonta ba). “Yaa Azeez!”Ya ji ta kira shi a hankali. Sai ya ja birki ya tsaya a inda yake dab da kofar, hannunshi na kan handle din kofar. Cike da mamakin kiran sunansa da ta yi. Ba ta taba yin hakan ba ko da wasa a kafatanin rayuwarsu. Duk da cewa ta kira sunan ne kamar yadda sauran kannenshi ke fada amma a kunnenshi sai ya ji kamar wani abu daban ta fada ba sunan nasa ba. Ya juyo ya fuskanceta daga inda yake tsaye ba tare da ya dawo ba. Bata ko motsa daga inda ya barta ba, har zuwa lokacin kuma tana ta cakuda kyawawan yatsunta cikin junansu. Kanta a sunkuye. Na gode!”’Ta furta tana mai dago kai ta kalle shi. Ji ya yi kamar zuciyarsa ta yi tsalle ta fice daga kirjinsa tadawo kuma, da gaske ne (she’s so innocent) in ba haka ba me ya yi da har za’a gode masa? Shi a nasa tunanin ma in za’a dubi lamarin da idon basira ai babban laifi zai aikata a gare ta (saki a wajen diya mace). A gefe guda ga kuma tsallake maganar mahaifiyarsa da zai yi. Ai kuwa bai cancanci godiya ba ta kowanne bangare. Sai dai ko ta wajen Mu’azatu wadda zai tsallake umarnin iyayensa a kanta saboda farin cikinsu shi da ita. Bai san me zai ce mata ba, saboda haka kawai ya daga kai, sannan ya juya ya fita daga dakin karatun. Ya koma dakinsa idonsa cike da bacci da gajiya. Koda Mu’ azatu ta kira shi don su yi hirar daren da suka saba (midnight call) cewa ya yi da
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG