AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 11 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 11 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Shin wai ita wace irin shashasha ce da ta yarda ta zauna ya gindaya mata abin da ya ga dama ta hau kai ta zauna don kawai tana so ta yi karatu ta ga danginta? Me ta rasa na dangi? Da me Daddy ya rage ta na mahaifi? Me ta rasa a uwa? Su Isma’eel aren’t enough? Isn’t Baba Azumi a great Grandma? lyalin Abdullahi Dakata bakidaya ba su ishe ta rayuwa ba?

KARATU! Zuciyarta ta ambato. Ko da ace Abdul’ azeez bai kai ta makaranta ba, ba ta da ilimin da zai isheta ta rayu da shi har karshen rayuwarta? Nasa ba zai ishe su ba? Gabadaya kwangilar na nufin……. za ta samu duk wadannan abubuwan, amma shi za ta rasa shi!!!

Wannan tunanin kadai ya sanya_ Hafsat Suhaanah ta ji zuciyarta ta yi wani matsanancin duhu kamar hadadden hadari mai tafe da guguwa da cida mai gigitarwa. Mai barazanar tafiya da mutum dungurugum in ya zauna a cikin wannan guguwa. To haka ta samu kanta kwatankwacin a cikin guguwa wadda in ta ci gaba da yin wannan

zazzafan tunanin guguwar nan da ke tarnaki a zuciyarta za ta tafi da ruhinta ta mutu, Abdul’ azeez ya huta da wannan kayan nadama da ya jefa ta a ciki. Zan amince in rasa komai, in dai zan tsira da shi…Conclusion na zuciyarta kenan. Amma ai kin riga kin yi alkawari, sannan yadda ki ka amince da hakan don ki tsira da shi , abin da ya yarda da shi kenan a kan Mu’azatu, har kuwa fushin iyayensa. Shima in har zai samu Mu’ azatu he can manage any situation!”. Zuciyarta ta yi wani bakikkirin, ga wani irin tukuki na fita daga cikinta. In ba ta yi kuskure ba za ta iya cewa, har tururi ta ke yi… ba ta ankara ba ta ji hawaye masu dumi suna sauka suna jika filon da ta ke kwance a kai.
Motsi ta sake yi kadan, har ga Allah ta gaji da wannan azabtacciyar kwanciya wadda ko motsi ba ta isa ta yi ba. A na me? Ita da gadonta d a dakinta? Tsaki ta saki, mai sauti. Www.bankinhausanovels.com.ng
Abdul’azeez, wanda zuwa wannan lokacin shi ma a nasa bangaren kwakwalwarsa neman tarwatsewa ta ke yi da tuno abin da ya faru dazu, ya janye ‘duvet’ din daga jikinsu bakidaya ya yi gefe da shi. Ya tashi ya zauna. Cikin shakakkiyar murya ya ce. Ni ki ke yi wa tsaki Hafsah!?” So ta ke ta ce, “ wanda ya tsargu dashi nake”. Ta tuna abin da hakan zai janyo. Ta fahimci abu na karshe da ya ki jini kenan (a kawo masa raini), amma fisabilillahi ya takura mata, ya zo dakinta ya hana ta barci, ya hanata sakewa a gadonta, ya muzgunawa zuciya da kwanyarta. Ya zo dakinta har gadonta ya hana ta sukuni. Tashi ta yi zaune ta dafe kanta da hannuwanta bibbiyu. Shi ma mikewa ya yi ya zauna ya jingina da filonsa. Da kallonsa ta ke da ta ga yadda yake kallonta sosai da kyawawan idanunsa. Me ye dalilinki na kin daukan waya ta?” Yadda ya yi maganar cikin kwantaccen sauti sosai ya kara lugwigwita zuciyarta. Wadda ta riga tayi rauni ta rasa duk wani karsashi da Allah ya halicce ta da shi akansa. Da farko shiru ta yi sai da ya kara nanatawa. Fuskarta ta kifa cikin tafukanta ta ba shi amsa cikin raunin murya. Barci nake yi”.
Wayarta ya zaro daga inda ya tura ta ya boye a bayan filonsa ya rike a hannunsa ba tare da saninta ba. “Barci ko kallon mijinki?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Muryar da ya yi amfani da ita wajen fadin hakan baya tsammanin ya taba magana da irinta a tsayin rayuwarsa. Duk da muryar ta karasa kassara ta, hakan bai hana ta yin jarumtakar kare kanta ba. A bayanta yake a kishingide, tana gabansa da kadan azaune ta mike kafafunta a kan gadon. Baya ganin fuskarta sai bayanta da kwantaccen gashin kanta wanda ke ta sheki da kyalli cikin dim-light din. Girgiza kanta ta yi cikin musanta zancensa.
“Ni ba ni da miji. Hasalima ban san da kasancewar kowa cikin dakin nan ba bayan ni Hafsat”’.
Murmushi ya yi, karfin gwiwarta ya kayatar da shi, ko da kuwa kalamanta sun masa ciwo. Wayar ya dora mata a kan cinyarta, “Wannan da ki ke kallo fa?”
Sosai ta razana, don ba ta taba tsammanin wayar nan tana hannunsa ba. Dauke wayar ta yi ta rike a hannunta, ta ba shi amsa. Mijin wucin-gadi ne!”.
Sai ga hawaye suna safka dai-daya a kan kundukukinta. Zuciyarta na yi mata wani irin ciwo da tsanar Abdul’azeez da duk abin da ya shafe shi. Da bai shiga rayuwarta ba, da yanzu duk haka ba ta faru ba. Da ba a aura mata shi ba, da yanzu tana gidansu tare da Mammanta, da ‘yan uwanta cikin sukunin zuciya. Gabadaya ya shiga zuciyarta ya kekketa ta, ta rasa abu guda daya da kwakwalwa da zuciyarta ke nufi da wannan walagigin da ta ke yi da ruhinta a kan Abdul’azeez Dakata, wanda bai san kowa ba sai kansa. Kowa ya mutu da ‘hurtings’ in dai shi zai tsira da wata banza “Mu’azatu” har mahaifiyarsa kuwa. “Hafsah!” Abdul’azeez ya kira ta muryarshi na rawa. Rawar da baiyi zato ba, bai san dalilin ta ba. Shi ya fadi kalmar ‘wucin-gadi’ yanzu da ta ba shi irinta ji ya yi kamar ta huda masa hanji. Ya rasa abin da ke masa dadi. Hannunta ya jawo da karfi ta fado jikinsa karo na farko a rayuwar aurensu. Kuka ta saki mara amo bare sauti, wannan kuka yana fitar da zafin da ke zuciyarta ne kawai, amma ba shi da sauti sai shessheka. Rungume ta ya yi sosai a tsakiyar kirjinsa da wata irin runguma mai tsananin karfi, kamar zai tsaga tsakiyar kirjinsa ya sanya ta cikin zuciyarsa, watakila hakan ne kadai zai saukaka masa abinda yake ji a wannan lokacin, har ta soma tunanin kashin bayanta zai karye.
Kokarin kwace kanta ta ke yi, amma ko gezau ta kasa ture wannan ‘giant’ wanda ya riga ya gama kekketa zuciyarta, yake shirin ‘dumping’ dinta nan ba da dadewa ba. Ina ruwansa da ita? Ina ruwansa da rayuwarta? Meye dalilin sa na zuwa dakinta yanzu? Yadda ta yi alkawari za ta cika da izinin Allah, ta san ba ta da matsayin samar wa zuciyarta abin da ta ke so a yanzu, wato ci gaba da rayuwa da shi har karshen rayuwarsu, fitina ce kawai da giggiwa irin na zuciya. Idan Abdul’azeez mai son kai ne (selfish) hakika ya kwatanta adalci a cikin (selfishness) dinsa. Ya kamata ita ma ta kwatanta, ba’a biye wa zuciya sai ta kai mutum ta baro. Ya ci gaba da rayuwa da ita alhalin babu soyayyarta ko digo a zuciyarsa? Ta ruguza masa farin ciki don amfanin kanta? Ko wannan shi ne kokari na karshe da za ta yi a rayuwarta sai ta tabbatar ABDUL’ AZEEZ ya auri MU’AZATU…… sai ta tabbatar ya cika burinsa… sai ta yi hobbasar da mahaifiyarsa ba ta yi fushi da shi ba a kan hakan. Daina mutsu-mutsun kwatar kannata ta yi ganin Www.bankinhausanovels.com.ng
cewa wahalar da kanta kawai take yi, bai yi mata sassaukan riko ba, bai rike ta da sauki don ta kwace a sanda ta so ba, yarike tane kakkarfan riko don dukkansu su samu nutsuwa daga azabtar da zukatan su ke yi, ta kwantar da kanta a kirjinsa kukanta na raguwa gradually har ta daina shi bakidaya. Hannunsa na dama ya sanya cikin yatsunta ya sarke su sosai cikin nasa kamar mai tsoron kada wani abu ya gitta a tsakaninsu ya raba wannan intimacy din, na hagun na rungume da ita tsan-tsan cikin jikinsa. A wannan lokacin ta tabbata da za’a tsaga jikinta ba za a samu digon jini ba; ya hau ya yi sama saboda duniyar gajimaren da ta tsinci kanta. Balle kuma data tsinci tattausan bakinsa cikin nata ya sarke su cikin na juna. Dukkaninsu idanunsu sun rufe sun manta da kowanne irin nau’in aure suke yi. Sun manta da duk wata kirkirarriyar yarjejeniya. Abin da suka sani kawai shi ne, su ma’aurata ne na hakika kuma suna tsananin bukatar junansu a yau. Al’amarin ya fi karfi daga Abdul’azeez a matsayinsa na namiji wanda ya kawo wadannan shekarun bai taba kusantar mace da irin wannan kusancin ba. Idanunsa sun rufe, hankalinsa ya gushe, ya soma sumbatarta da wata irin sumba mai tsayi da zurfi (hot kisses) a duk inda bakinsa ya kai daga fuska zuwa wuyanta cikin wata irin siga mai nuna tsananin bukatar miji zuwa ga matarsa……. Abubuwa da yawa ke yawo a kan Hafsat suna ankarar da ita rayuwar da Abdul’ azeez zai jefa ta idan ya samu wannan nasarar a kanta, kuma ya zo daga baya ya sallame ta kamar yadda ya kudurta; bazawara… second hand… ko mai ciki ko goyo babu aure, babu martabar zama a dakin aure……! Sai gantali a jami’a, amma ba ta da martabar da za’a kira ta matar aure, ko matar Barrister ABDUL’AZEEZ HAMZAH ATTIKOU!! Wannan sai MU’AZATU. Ita sunanta sauta ga wawa….. Bazawara under the age of twenty !!! Don haka a take ta soma ‘protest!’. Zuciyarta ba ta afu ga Abdul’azeez a yau don wannan rayuwar ba ne sai don ci gaba da rayuwa tare da shi matsayin ‘miji uban ‘ya’yanta’ har karshen rayuwarta.
‘Protest’ ta ke sosai da dukkan karfinta da Www.bankinhausanovels.com.ng iyawarta, wanda ke tasowa daga tun daga karkashin zuciyarta da umarnin kwakwalwar hankali da tunani, wanda hakan ya tayar da hankalin Abdul’azeez fiye da zatonsa. Lallashi ya koma, duk da ba cikin hayyacinsa yake lallashin ba ya san kalaman sun yi tsauri a ce Suhaanah yake gayawa su. Wannan jaririyar kanwar tasa da aka haifa akan idonsa ta girma a gaban mahaifiyarsa. Kalaman da yake gaya mata ta ki yarda ko kadan su yi tasiri a tare da ita, don ta amince na yaudara ne da neman cimma buri. Ba ta hango wa kanta komai a wannan lokacin sai zawarci babu budurci. Ko ciki da goyo babu aure. Wani mai matar za ta aura daga karshe bayan Abdul’ azeez ya kore ta, amma bata da damar gina ‘family’ nata na kanta mai ban sha’awa irin na gidansu sai na gidan wasu. Ko kishiyar Mu’azatu ba ta isa ta zama ba, sai ko kanwar mijinta.
Wani kuka ne ya taho tun daga kololuwar zuciyarta ta rusa masa shi tunda karfinta da bujirewarta sun yi kadan su raba ta da Abdul’azeez a daren yau. Sosai ya tsorata da kukan mai kama da na an yanki naman jikinta, ya koma gefe ya dafe kansa a gefen gado da dukkan hannuwansa, Wan
nan damar ta samu ta ja ‘duvet’ ta lullube jikinta tana ci gaba da rusa kuka kamar wadda aka aikowa sakon mutuwa. Haushi da bakin ciki ne ya sanya shi mikewa cikin zafin rai da ta fadar zuciya ya bar mata dakinta. Da sauri ta sauko ta murza wa dakin ‘key’ ta bar mukullin a jiki. Ba ta sani ba ko ta bar dakin a bude a yadda ya zuciyan nan, ba dawowa zai yi ba. Shi kadai ya san cikin halin da ya kwana.
Amma ga Hafsat abin ba haka ya ke ba. Bayan ta goge ido daga kukan kwatar kan data rakito ya kuma ceto ta barci ta yi har da munshari da saleba, cikin mafarkinta kalaman Abdul’azeez ne wadanda ya fada mata a lokacin da ya tashi daga Barrister Abdul’azeez zuwa MIJIN HAFSAH! Kalaman da ba za ta fada a fili kowa ya ji su ba saboda har gobe tana tantama a kansu. Su ke nanata kansu cikin barcinta suna kara armasa mata shi.
Sosai ta makara sallar asuba don a rayuwarta ba ta taba ganin dare mai tsayin na yau ba. Wanda ta sanya shi cikin darare masu dumbin tarihi a gare ta. Wani dare daga cikin dararen da ba za ta taba mantawa da su ba. Ko da ta yi sallah ta shiga ‘kitchen’ don sama musu abin da za su ci duk da ta makara, alamu ta gani na an yi girkin taliyar indomie da dafaffen kwai. Duk da lahadi ce yau ya ki zama a gidan, ba ta san inda ya tafi ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yadda ta yi girkin rana haka na dare ya tadda shi a ‘dining’ Abdul’azeez bai taba ba, kuma ta tabbatar ya dawo gidan, don ta ji motsinsa sake fita ya yi ba tare da ya neme ta ba. Murmushi ta
yi ta kwashe ta ajiye a kofar shigowa babban falonsu inda ta ke ajiyewa Danfulani abinci ya zo ya dauka da kansa.
“Fushi Yaya Azeez ya ke yi da ni?” Ta tambayi kanta. “Ya fi mini!”. Ta fada a fili. “Wannan al’amari ya fi karfina, sai Yayata abar son ka Mu’ azatu, tunda na gane shi ne muhimmi a cikin auren ba kamar yadda na zata ba. (It’s not a crime) idan akwai aure, kuma sai an kai zuciya nesa za’a iya bijirewa. Balle daga Abdul’ azeez din da ta yarda zuciyarta daban ta ke daukar kowanne al’ amarinsa.
Lumshe idonta ta yi tana tuno yadda ya ke ‘kissing’ idanun kansu ba su tsira ba. Labban bakinta ta cije don ji ta yi kamar yana bayanta yana sake ‘kissing’ din su.
“Ya Ilahi’”. Suhaanah ta fada a fili, tare da kwashe kwanukan daren ma ta koma kicin da su ta adana abincin a firji, ta rufo ‘kitchen’ din da sauri jin ‘horn’ din motarsa ya dawo gidan misalin karfe tara na dare. Gidan Barrister Sagir ya tafi, a can ya ci abincin dare, Hafsat ta jika nata ta cinye.
Daki ta shige da gudu ta rufe kofarta. Ba ta kara fitowa ba sai washegari bayan ta idar da sallar asubah ta fito ‘kitchen’ don hada masa abincin kari da zai fita shi, tunda ranar (office) ce.
Da wuri ya shirya don ya bata haushi, duk saurin da ta yi ta gama tana fitowa daga ‘kitchen’ din ta ga ficewarsa daga falon. Da sauri ta koma ‘kitchen’ ta dauko ‘basket’ din, amma tana fitowa yana yin ‘reverse’ zai fice daga gidan ga Danfu
lani ya wangale masa ‘get’. Yana hango fitowarta ta madubin motar har tana tuntube don sauri, ya fizgi motar da gudu ya fice daga gidan. Allah ne ya so ta kananan duwatsu ne shimfide da harabar gidan bakidaya, la-shakka da ta sha kura. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kasa daurewa ta yi sai da ta yi hawaye. Sabon salon da zamansu ya dauka kenan. A ganinta laifin da ta yi bai yi kamarin da zai yi wannan fushin ba. A kan gaskiyarta ta ke. Yaushe ta tashi daga matar wucin-gadi zuwa parmanent wife? A cikin ajandarsu babu auratayya. Ba kowa ya fahimtar da ita wannan shi ne aure ba, shekarunta da kwakwalwarta ne. Abin da ta ke ji a kan Abdul’azeez ma zuciyarta na son fahimtar da ita ma’anarsa da gangan ta ke kin karba. Idan wannan al’amari da Abdul’azeez ya bijiro a gare ta shi ne ‘aure’, hakika auren wani abu ne mai matukar girma kwarai, kuma zai iya ruguza duk wasu tubala da contracts da suka gina auren nasu a kai tunda ba za’a fara don a daina ba. Ga shi ta sha alwashin taimakawa Abdul’azeez ya samu abin da yake so, ya cika burin rayuwarsa.

******

Kwanaki sun shura ana wani irin zama mara dadi tsakanin Abdul’azeez Dakata da matarsa Hafsat-Suhaana. Shi yake fushi da ita ba ita ke fushi da shi ba, fushin da in za’a daura masa wuka a makoshi a tambaye shi dalilinsa ba zai iya fada ba. Hafsat ta fi shi gaskiya in har gaskiyar yake so. He attempted to cross the limit , ita kuma ta ankarar da shi. Me ye laifinta fisabilillahi? Ya daina cin abinci da ita, ya daina hira da ita. Ya daina zaman gidan.
Shakuwarsu da Sagir da iyalinsa ta karu a dalilin yawan zuwa gidan da yake yi yanzu don debe kewa, ko gidan iyayensa. A ganinsa janyewa Hafsat shi zai ceto shi daga katoton ramin da zuciyarsa ke son jefa shi, ramin da in ya kuskura ya fada sai ya yi tsalle dubu bai iya fitowa daga cikinsa ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dole ya lallashi Mu’azatunsa suka shirya domin ya yarda har da nisa da ita cikin dalilan shakuwarsa da Hafsat, shakuwar da ba za ta haifar da Da mai ido ba, sai tarin nadama.
Sau-tari ya kan samu kansa cikin zurfi a tunani, Hafsat matarsa ce da addini ya halasta mishi iyaye da duniya bakidaya suka shaida. Yana da damar kusantarta no matter what , rashin samun damar hakan na iya jefa shi cikin wani hali a yanzu da yake tsananin bukatar mace a tare da shi. Ya ture komai ya karbi hakkinsa, shi ya ga abin da ya gani, ba yarinya ce kankanuwa ba irin daukar da yake yi mata. Ko ‘protest’ din da ta yi masa ya nuna Hafsat na da wayonta, ta san abin da ta ke hangowa a cikin aurensu duk da tana da ‘feeling’ mai tsananin karfi a kansa wanda in ya yl rantsuwa ba zai yi kaffara a kan hakan ba wanda ya faru da ita bayan aurensu da zamansu tare na tsayin watanni, zuciyarsa ce ke karyatawa da gangan. Da hujjar cewa; yarinya ce, shekarunta ba su kai ta bambance da abin da zuciyarta ke so ba, sai wanda aka karkatata a kai. (Anya kuwa Abdul’ azeez?) .

*******

Shi da kansa ya soma saukowa daga dokin

fushin nasa ba tare da kowa ya lallashe shi ba. Ganin halin da fushin nasa ya jefa Hafsat. Ta shiga cikin matsananciyar damuwa da rashin walwala, in bai yi kuskure ba zai ce har ramewa ya ga ta yi jiya da ya saci kallonta tana gyaran falon, a lokacin yana zaune tsakiyar ‘3-seater’ ya mike kafafunsa da ‘system’ a kan cinyarsa yana duba wani aiki. Amma duk da haka ya sa a ransa zai rage kusancinsu don tserar da kwangilarsa. Daga jibi Alhamis zai soma azumin tadauwa’i don samun lafiyarsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Washegari suka wayi gari da baki na ba-zata. Mammah da Baba Azumi, Isma’el ya tuko su ya kawo su. Shi bai fito ba ma. Fitowarsa daga wanka kenan Danfulani ya kira shi ya sanar da shi wai suna da baki ga su zaune a cikin mota sun ce daga Asokoro ne. Bai tsaya goge ruwan jikinsa ba ya sanya kaya, bakin wandon Jeans da shudiyar T.Shirt ‘yar gidan ‘ Nordstrom’ . A gurguje ya fito don ya san babu wasu da ya sani a Asokoro sai iyayensa. Tlai-kuwa, Mammah da mai aikinta Azumi da kaninsa Isma’el ke fitowa daga mota.Mammah!” Ya fada cikin bayanannen farin ciki. Karasawa ya yi da sauri, shi ba abin ya rungume ta ba ta ce ya yi girma, shi kuma a yau ban da rungumar bai san me zai yi mata don nuna mata jin dadinsa ba da tako kafarta muhallinsu.
Hannayenta biyu ya kama, You are highly welcome to our humble abode Mammah”’.
Murmushi ta yi ta kwace hannunta tayi gaba, ya russuna ya gaida Azumi, ya ba wa Isma’el hannu, ya karbi ‘handbag’ din Mammah ya shige cikin gidan da sauri yana kwalawa Hafsat kira, “Hafsah! Hafsah!!’
Mammah ta ce, “Wannan kira haka ai sai ka bata tsoro. In ka kyale ta har dakin zan isko ta”.
Kwance ta ke lamo a cikin quilt kasancewarta mai yawan son dumi ko da gari babu sanyi, kanta a kan filo ta cure gashin kanta a gefe, kwance ta ke kawai ko wanka ta kasa tashi ta yi saboda nauyin zuciya. Ba tunanin kowa ta ke ba sai na Abdul’azeez din da ya hana zuciyarta zama lafiya a duk kwanakin nan, da tunanin hanyar da za ta bi ya daina fushi da ita. Kamar daga sama ta ji yana kwala mata kira da wata murya kamar ba tasa ba. Kasa amsawa ta yi, amma ta mike zaune cikin faduwar gaba. Sai ga shi ya shigo dakin, da sauri ya iso gare ta, har gadon ya isko ta ya zauna a bakin gadon. Hannunsa daya ya nutsa cikin sumar kansa ya riko hannunta da dayan ya dube ta cikin ido. “Mammah ce. Don Allah Hafsat ki rufa min asiri, mu koma shirin mu, na dade da hucewa wallahi
Yadda ya marairaice yana mata maganar ya yi bala’in bata dariya. Sosai ta dake ta dauke idonta daga kansa jin wani abu na fizgar zuciyarta daga cikin kwayan idanunsa. Ta rasa dalilin da ba ta iya jure kallon idanun Abdul’azeez masu dauke da wani maganadisu da ba ta taba ganinshi a idon kowa ba. Hannayenta biyu ya kamo ya matse su sosai cikin nasa.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *