AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 12 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 12 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 



Mammah ta ce, “Wannan kira haka ai sai ka bata tsoro. In ka kyale ta har dakin zan isko ta”.
Kwance ta ke lamo a cikin quilt kasancewarta mai yawan son dumi ko da gari babu sanyi, kanta a kan filo ta cure gashin kanta a gefe, kwance ta ke kawai ko wanka ta kasa tashi ta yi saboda nauyin zuciya. Ba tunanin kowa ta ke ba sai na Abdul’azeez din da ya hana zuciyarta zama lafiya a duk kwanakin nan, da tunanin hanyar da za ta bi ya daina fushi da ita. Kamar daga sama ta ji yana kwala mata kira da wata murya kamar ba tasa ba. Kasa amsawa ta yi, amma ta mike zaune cikin faduwar gaba. Sai ga shi ya shigo dakin, da sauri ya iso gare ta, har gadon ya isko ta ya zauna a bakin gadon. Hannunsa daya ya nutsa cikin sumar kansa ya riko hannunta da dayan ya dube ta cikin ido. “Mammah ce. Don Allah Hafsat ki rufa min asiri, mu koma shirin mu, na dade da hucewa wallahi
Yadda ya marairaice yana mata maganar ya yi bala’in bata dariya. Sosai ta dake ta dauke idonta daga kansa jin wani abu na fizgar zuciyarta daga cikin kwayan idanunsa. Ta rasa dalilin da ba ta iya jure kallon idanun Abdul’azeez masu dauke da wani maganadisu da ba ta taba ganinshi a idon kowa ba. Hannayenta biyu ya kamo ya matse su sosai cikin nasa.

“Kina jina Hafsah? Don Allah ki manta komai, ni ne mai laifi na yarda, babu lokacin magana save it , Za mu yi ta in sun tafi. Duk wani punishment ki tanadar min ki ajiye komai yawan sa zan dauka, amma yanzu ki saki ranki don Allah”. Daga kanta ta yi alamar ta ji, kuma ta amince. Sai jin sallamar Mammah su kai a bakin kofa, da sauri Hafsat ta janye hannayenta daga cikin nasa. Mammah ta yi kamar ba ta gani ba.


“Ba dai sai yanzu ki ka tashi daga barci ba?”
Saukowa ta yi daga gadon da gudu ta yi kan Mammah ta rungume ta kankam. Abdul’azeez yayi maza ya ce,
“Ba ta jin dadi ne. Tun jiya ta ke fama da zazzabi, amma na ji yanzu ya sauka”. “Ni ki cika ni, kada ki kada ni”Da kyar Mammah ta samu Hafsat ta cika ta suka zauna tare. Dakin ta ke bi da kallo, komai tsaf a gyare ban da gadon. Ta ce, “Zazzabi? Ba sai a je asibiti ba? Ana raina zazzabi ne?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta kafe Abdul’ azeez da ido. Sunkuyar da kai ya yi don gudun haduwar kwayar idanunsu. Ya san halinta sarai, kallo daya za ta yi masa ta karanto karya, ko gaskiya a kalamansa. Ba shi kadai ba har sauran ‘ya’ yanta. Hafsat tuni ta yi ‘kitchen’ ta soma tattaro abin saukar baki, kusan duk abin motsa baki da lemukan da suke da su a firji ta kwaso, Isma’el na tsokanarta, Baba Azumi na tare mata.
“Su matar gida manya, sai dai kuma babu wanka babu kwalliya”. Baba Azumi ta ce, “Eh din, ta dai fi wannan budurwarka mai kama da shamuwa da wasu kafafunta a bubbude kamar tayar mota, ko ba ta yi wanka da kwalliyar ba”.
Dariya ya yi, ya ce, “Wallahi Wasila ta fi Adda kyau, ga gayu, ga class, amma wannan tsami gayen sai Yaya ya hada da hakuri, don bana jin ko girki ta iya”’Kumburi sosai ta yi tana hararar Isma’el, Mammah da Abdul’ azeez suka fito. Mommah, kin ga IIla’ila ko? Wai ni ce tsamigaye?”
Mammah ta ce, “Ba dole ya ce miki tsami-gaye ba? Karfe goma na safe amma ba ki wanka ba, ba ki dafa wa miyinki abin kari ba, ba ki gyara gadonki ba balle ki yi masa kwalliya”. Kamar za ta fashe da kuka ta ce, “Wallahi Mammah ina yi, yau ne kawai’.
Abdul’azeez ya harari Isma’el kasa-kasa ba tareda Mammah ta gani ba. “Mammah na fa gaya miki ba ta jin dadi”.
“Kana kare ta ne kawai, amma ba zan yi miki uzuri ba Addah, shi ya sa ban gaya muku zan zo ba, zuwana na farko ga yadda na tadda ke”.
Hafsat ta soma kuka kamar ta ce da Mammah in ta dafa abincin ba ya ci, ya daina kula ta dalilin hautsinewarta kenan, ta tuna rokon da ya yi mata yanzun nan na ta rufa masa asiri. In yaso kome zata yi masa tayi masa in sun tafi. Amma Abdul’azeez ya cuce ta. Duk yadda ta ke hana idonta barci ta hada masa (varities) na abinci mai rai da motsi kullum sai dai ta zubar, ko ta baiwa Www.bankinhausanovels.com.ng
maigadi, bama ya zama a gidan balle ya san me take ciki, yadda ta ke kalkale gidan nan da kwalliyar da ta ke dandasawa ko kallo ba ta ishe shi ba, yau daya sun tashi a banza! Ganin tana kuka zuciyar Hajiya Maryam ta tabu. Abdul’ azeez cikin damuwa ya ce, “Ishma, me ya sa ba ka iya wasa ba ne? Ni na ce da kai ba ta girki?” Isma’el fa ba ya gajiya da tsokana, sai dai in bai ga abin fada ba, ya ce,
“To Yaya a zubo mana man, tunda an dafa?” Mammah ta janyo Hafsat jikinta. Rabu da Isma’el Addah, ni na dafo mana abincin saboda bana so ki sha wahala’’.
Ta dubi Baba Azumi, “Karbi mukullin ‘boot’ a shigo da coolers din nan gabadaya”’.
Isma’eel ya yi mata gwalo ya mike suka fita shi da Baba Azumi. Ta sake bara baki tana kuka, wai ya yi mata gwalo. Abdul’azeez abin ya ba shi dariya, ya ce, “Me ya sa ki ka zo da shi ne Mammah? Da Usman ki ka dauko”. Ka san Usman da gudu a titi, ni kuma bana son gudu shi ya sa na dauko shi. Haleem kuma ya je Kano. Na manta takura miki zai yi Addah”.
“Allah ba zan je gidansa ba, kuma ba zan je bikinsa ba”. In ji Hafsat. Karaf! A kunnensa yana shigowa dauke da ‘food-warmers’ din Mammah masu tsananin kyau, ya ajiyesu tsakiyar falon ya ce,
“Ai gara kada ki zo din, balle ki koya wa Wasilata kazanta, rashin girki da rashin gyara”Abdul’azeez ya dau filon kujera ya jefa shi da
shi. Filon ya cafe da hannayensa yana fadin, “In ba za ki koyi gayu ba, na rantse sai na yi wa Yaya budurwa ‘yar gayu ko cikin kannen Wasila
Sosai Abdul’azeez ya fusata, ya ce, “Fita daga gidan nan Isma’el, tunda babu gadonka a cikinsa”.
Hannayensa biyu ya hada irin na rokon afuwa yana kallon Hafsat,
“!’m so sorry uwargidan Ya Azeez. Amma kafata kafar uwata”’. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mammah ta girgiza kai, “Ni ma ba za mu jera ba, tunda kana fatan a yi wa Adda h ta kishiya!”.
“Na tuba na bi Allah na bi ku dukkanku. Baba Azumi ki gaya musu wasa nake, amma ai ita Adda ta sani ko a cikin kanne ita ta musamman din Illa’ila ce”Zumburo masa baki Hafsat ta yi, A’ah, yanzu ka daina sona”.
Dariya ya yi wadda ta fiddo fararen hakoransa bakidayansu, “Ke me ya sa ba wuya ne ki ce an daina sonki? Haka Mammah ta bamu labari kince ta daina sonki don ta yi miki laifi. An gaya miki ana fara son mutum don a daina ne? You’re special sis, ke da Yaya Azeez mutu-ka-raba takalmin kaza, ba ‘yar gayu ba, ko ‘yar sarkin Istanbul haka za ta ganku ta barku. Na tsaya miki Hansai, am I nice now ? Mammah na wanke kaina yanzu?” Mammah ta shimfida ledar cin abinci a tsakiyar falon gargajiyansu (African parlour) ta soma shirya ‘plates’ tana serving ba ta kula shi ba. Can kuma ta ce, In mutum ya ce shiga abin da ba ruwansa shi ne sana’arsa, ai sai kowa ya ja baki ya yi shiru ya zuba masa ido ya yi ta yi har Allah ya gajisshe shi’Hafsa ta ce, “Sosai kuwa Mammah”’. Ta faki idon Mammah ta yi masa gwalo.
Abdul’azeez bai kara kula su ba, wayar hannunsa yake daddannawa yana duba sakonni.
Funkason fulawa ne da sinasir da miyar agushi wada ta ji alayyahu da ganyen ugu da naman saniya Mammah ta dafo musu. Ita ta yi ‘serving’ kowa. Daga Abdul’azeez har Hafsat sun ji dadin abincin, sun bude ciki sosai sai ci suke don rabon kowannensu da cin kwakkwaran abinci cikin sukunin zuciya tun fadansu. Babu wanda ya kara samun nutsuwar zuciya irin wanda ya samu a yau. Lallai UWA rahma ce, kuma komai girman Dan Adam yana bukatarta. Allah ka kara wa iyayenmu lafiya da nisan kwana mai albarka. Wadanda suka rasa nasu kayi musu rahma kama rabbayaany saghira . Mammah sarkin sa’ido ta yi mamakin irin yadda suke ta narkar abincin nan. Ga shi da alama kowannensu ya rame idonsa ya fada, sai satar kallon junansu suke. Ko dai gaskiyar Isma’el ne Hafsat ba ta girki? Amma da wuya hakan ta kasance don dai ita dai ta san ba sakaran kiwo ta yi wa Addarta ba. Kusan koyaushe tare suke girki in tana gida, musamman da suka dawo Nigeria inda ba ta zuwa makaranta. Wani lokacin ma ita take jan ragamar girkin gidan bakidaya. Ta yi ajiyar zuciya har sai da kowa ya dago ya dube ta. Ta kudurce a ranta za ta binciki Hafsat ta tabbatar tana dafawa mijinta abinci ko bata dafawa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Garin kalle-kallen Hajiya Maryam idonta ya fada kan kasaitaccen hoton Mu’ azatu kafe a bangon gabas maso kudu na falon. Idonta ta kafa wa hoton tana son tuno inda ta san fuskar, kamar ta taba ganinta a wani wuri amma duk kokarinta ta kasa tuno inda ta gantan. “Addah wace ce wannan?”
Ta tambaya cikin mamaki tana mai nuna musu hoton da dan alinta. A lokaci guda ita da Abdul’azeez suka kai idonsu ga inda Mammah ke nunawa. Gudun jini ne ya katse a jiki da jijiyoyin Abdul’ azeez zuciyarsa ta yi wani irin bugu, wani rugugi ya ratsa a cikin kansa. Tun sanda ya kafa hoton don ya bakantawa Hafsat bai kara tunanin zaman nasa kuskure bane, ko tunanin wani zai iya zuwa ya gani ya tambaya balle Mammah, mutum ta karshe da bai taba kawowa ba cikin masu ziyartar gidansa sabida fillancinta na alkunya. Hafsat ya duba da sauri suka hada ido, ta yi saurin dauke kanta ganin ragaita da muzantar da ke cikin kwayar idanunsa. Saura kadan dariya ta kufce mata, amma ta hadiye.
Da ma an ce in za ka gina ramin mugunta…. ka gina shi gajere don ba ka sani ba ko kai za ka rufta. Halacci da yawa ya yi mata a rayuwar aurensu ta tsayin watanni shidda, ko da ya bata mata, to alherinsa ya rinjayi kuskurensa. Ta tuno ranar da ta san ko ita wace ce a cikinsu Abdul’azeez bai kyamace ta ba! Ya ce da ita; ita ba shegiya ba ce da ubanta a gaban iyaye da ‘yan uwansa. Ya ce, uwar da ta haife ta ba ta yi kama da mutuniyar banza ba. Mace ce mai cikar mutunci, mai kirkin gaske. Ya sha alwashin nemo mata uban da ya haife ta da nemo mata ‘yan uwanta na jini ya sadar da ita gare su cikin dan lokaci kalilan. Kafin a yi haka Abdul’azeez ya yi mata alheri da kyautayi mai yawa a cikin gidan nan… yayi abubuwa da yawa don ya faranta mata. She adores him much… she respects him a lot… Duk wata kulawa da ya kamata a baiwa mace a gidan aure yana bata kafin suyi fada. Samun bakinta ta yi da budewa yana bai wa mahaifiyarsa amsa ba tare da ta shirya kalaman a kan harshenta kafin ta furta su ba.
“Kawata ce Mammah… sunanta Fa’izah”.
Abdul’ azeez ya yi baya ya lumshe idonsa yana maida numfashi, ya dauki mintuna bai bude ba. Ya yi kasa da kansa, Hajiya Maryam mamaki ya kashe ta a zaune.
“Kawa Addah? Shi ne ki ka makala ta a bangon dakinki? Kullum miyinki na tozali da ita? To bakya kishin mijin ne? Ko kuwa son _ shi ne ba kya yi? Da gani ma wannan ai ta girme ki sosai kuma da kyar in ba ta da aure? Ni yaushe ma ki ka canza hali har ki ka saki jiki da kawaye? Maza-maza sauke shi tun kafin in sabar miki’. Www.bankinhausanovels.com.ng
Jiki na rawa Hafsat ta mike ta hau kici-kicin sauke hoton, amma ta kasa. Mammah ta juya akalar fadanta kan Abdul’ azeez.
“Ban so zuwa gidan nan ba, ashe rashin zuwan nawa kuskure ne babba, kana ina Addah ta yi kawance da wannan mai soyayyen idon kamar an soya gyada marau-marau ba ka tsawatar ba? Dubi
kirjinta duk rabi a waje bakinta kamar na karuwai don jambaki an kafe ta a falonka wai matsayin kawar matar gida, kai kuma ka bari. Za ki sauke hoton nan ko sai na kwankwatsa shi a tsakiyar dakin nan?” Hafsat ta soma hawaye, duk ta bi ta gigice, ba ta taba jin Mammah na fada haka ba. Jikinta da Hannunta sai rawa yake haka hoton, ga shi ta kasa cire shi. Tasowa ya yi ya iso gare ta gabadaya jikinsa ya mutu, “Lemme help!”. Ya fada mata cikin kunnuwanta a hankali da tattausan lafazi.
Zagaye ta ya yi cikin hannayensa kamar ya rungume ta, a haka ya ciro hoton ya sauke shi kasa. Mammah ta bi su da kallo, duk su biyun sun sunkuyar da kai, sai ta kasa ci gaba da fadan. Suka koma inda suka tashi suka zazzauna. Isma’el ya ce, “Ni wallahi ma kamar na santa”. Abdul’azeez ya galla masa harara, gabansa na cigaba da bugawa. Mammah ma ta ce, “Ah toh, ni ma kaina kallon sani nake mata. A ina ta santa?” Ta jefa tambayar ga Abdul’azeez.
Shiru ya yi kamar ba da shi ake ba, sai da Mammah ta kara maimaitawa. Cikin sanyin murya Hafsat ta ce, “makwabciyata ce”’. “Tana da aure?” Girgiza kai ta yi a hankali alamar “babu”.
Hajiya Maryam ta ji kamar ta rufe Adda da duka don haushi, wane irin kwancaccen kai ne da ita? A yi mutum kamar sakarai bai san halin da
duniya ke ciki ba sam? Ko dai ba ta kishin miyin ne? Watakila don ba sonsa ta ke ba, amma ko yaron goye ai ya san kishi. Zuciyarta ta zo wuya da yawa, in ta ci gaba da kallon Hafsat dukanta za ta yi. Mikewa ta yi tana gyara daurin zaninta da mayafi alamar tafiya. Baba Azumi ma ta mike, “Isma’el tattara kwanukan nan ka kai mota, mu za mu wuce, sai gani na biyu”Idanun Hafsat suka kawo ruwa, ta tabbatar ba karamin bata wa Mammah rai ta yi ba. Zuwanta gidan kenan na farko tunda ta aurar da ita, amma ba ta tsinci komai cikinsa ba sai bacin rai. A kan laifin da ba nata ba. Hasalima wanda ya yi laifin ya yi ne don ya wulakantata ya nuna mata ita ba wata tsiya ba ce a gare shi. Ga shi ta juye komai a kanta don shi ya tsira daga fushin mahaifiyarsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ga mamakinta ta kasa yin nadamar abin da ta yi ko kadan; gara ranta ya baci da na Abdul’azeez dinta! Duk yadda ya so su hada ido don nuna mata godiyar da ke cikin idanunsa ta ki yarda. Haushin sa take ji kamar ta rufe shi da duka. Ba ta yi don ya gode mata ba, tunaninta yanzu na yadda za ta shawo kan Mammah ne ta daina fushi da ita.
Har mota suka rako su, ta bude wa Mammah kofar mazaunin baya ta zauna, ta dora mata jakarta a cinya. Azumi da Isma’el direba na gaba. Kasa rufe murfin motar ta yi ta tsugunna a kan gwiwoyinta ta kwantar da kai a kan cinyar Mammah ta soma kuka. Baba Azumi ta ce, “Me ya yi zafi Addar Mamanta? Ba za ki yi ba daidai a yi miki fada ba?”
“Kin san shagwababbu ba su yarda sun yi kuskure, Mammah da kin kyale mata hoton ta, har Yaya Azeez ya ji yana son Fa’izar ya auro ta mu ga karshen kawance”’. Cewar Isma’el.
Ciro kai ta yi fuskar nan jage-jage da hawaye ta ke harararsa. Dariya yake sosai har ta keta, ya ce, “Ni ki matsa in ja mota za ni zance wajen Wasilata kina bata min lokaci”.
Duk yadda ta so Mammah ta sakar mata fuska ta ki yin hakan, har Isma’el ya ja motar Danfulani ya bude musu suka hau kwalta don barin shiyyar rukunin gidajen (Sun-City). Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi dai Abdul’azeez ba baki sai ido, hannun damansa ya sanya cikin tarin sumar kansa yana cakudawa. Daya daga cikin al’adunsa in ya san yayi ba daidai ba. Yau ba don wasu dalilai masu yawa ba, tsugunnawa zai yi ya goya HafsatSuhaana, ya kai ta har tsakiyar gadonsa. Yayi mata godiya ta musamman. Duk da haka zai gaya mata ya gode da irin godiyar da ta dace. Su Mammah na ficewa ta yi cikin gida da sauri ko kallonsa bata yi ba. Da hoton Mu’azatu da suka sauke ta fara cin karo. Tsaki ta yi ta bi ta kansa da takalmi ta wuce dakinta. Ta turo kofar za ta rufe ya sa hannayensa ya tare.
Karfi ta sa wajen son rufe kofar ya nuna mata nata karfin rabin cokali ne, domin turowa daya ya yi ya shigo dakin ya maida kofar ya rufe. Jingina ta yi da kofar ta rufe idonta hawaye na zuba.
Habarta ya kama da hannun damansa ya dago fuskarta, ji yake kamar ya sanya harshensa ya
dauke hawayen da ke zuba kamar an sunce famfo, wata zuciyar na hana shi. Maimakon hakan, yatsunsa biyu Hafsat ta ji a saman fuskarta suna share hawayen. Sosai ta kara tamke idonta sakamakon jin wani abu mai kama da jan wutar lantarki na bin jikinta. “Yi min komai da zuciyarki ta ga I deserve as a punishment Suhaana, amma ki kwantar da hankalinki, ina mai tabbatar miki Mammah ba za ta iya dogon fushi da ke ba, so kawai ta ke ta nuna miki kin yi wauta, amma ba fushi ta ke da ke ba”.
Magana Abdul’azeez ke yi kasa-kasa, ta yadda ba don ta kasance cikin masu kyakkyawan ji ba, da ba za ta ji shi ba.
Wata irin kasala ta ji tana saukar mata, bude idonta ta yi a hankali ta dube shi. Damuwarsa kadan ce a kan abin da ya faru. Ji ta yi ya janyo ta jikinsa a hankali ya hade su sun zama mutum daya. Sosai ta ji nutsuwa na shigarta hawayen idonta na daukewa. Kamshin jikinsa na jefa ta cikin wani irin shauki mai wuyar fassarawa. Dankwalin kanta ya zame ya fadi kasa gashin kanta ya wargaje ya rufe hannayen Abdul’azeez da ke zagaye da ita. Ba ta iya aune ba ta ji hannayensa cikin gashin kanta, bakinsa kuma cikin nata. Kissing dinta yake yi tun daga kololuwar zuciyarsa. Al’amarin da ya jefa su cikin wani irin Www.bankinhausanovels.com.ng yanayi dukkaninsu da ba su taba ji ba a rayuwarsu. Daga can tsakiyar unguwa aka kwada kiran sallar la’asar. A yau duk jarumtar Hafsat ta kasa yin ‘protest’ din, ta kuma kasa yin kowanne kokari na juya wa Abdul’azeez baya, ta nemi duk wani kyakkyawan tunani da ke cikin kanta ta rasa.
Ladanin ya ci gaba da kwada kiran sallah har tsakiyar kwanyar Hafsat. Tana cikin mutane masu matukar kiyaye lokacin sallah. Zame jikinta ta yi, an yi sa’a rikon da ya yi mata ba mai karfi ba ne sabida shi kansa ba shi da karfin, dukkansu zubewa sukai a kan marbles kowanne na kokawar nemo consciousness dinsa. Kafin kunya matsananciya ta zo ta lullube Hafsat, ta sanya kanta cikin kafafunta ta kasa dagowa. Abdul’ azeez ta ji ya kwantar da kai a gadon bayanta ya yi shiru kamar ba ya jin kiran sallar da ake ta yi. Muskutawa ta yi cikin jin nauyi ta yi masa magana. “Yaya Azeez ana kiran sallah?”
“Ina ji Hafsat, na kasa tashi ne”’. “Ko in daga ka?”.
Ya jinjina kai, dariya na son kama shi duk da halin da yake ciki,wai ta daga shi kamar wani dan ta, har yanzu bai sauke kai daga gadon bayanta ba,
“It’s not easy daga kato iri na. Amma tunda kince zaki iya zo ki gwada. Menene punishment dina na laifuffukan da nayi miki? Above all (fiye da komai) a yau, kuma a yanzu, ina so in ce miki NA GODE!”
Murmushi ta yi duk da ta san ba kallonta yake ba. Cikin taushin murya tace.
“Punishment apologised. NAGODE din ta me ce ce?”
Dagowa ya yi daga kwanciyar da ya yi a bayanta ya juyo da ita gabansa suka fuskanci juna, kwayan idanunsa ya kalmashe a cikin nata ta yadda ba za ta iya dauke su ba in ba shi ya aminta da hakan ba.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *