AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 13 KARSHE BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 13 KARSHE BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 


kowanne na kokawar nemo consciousness dinsa. Kafin kunya matsananciya ta zo ta lullube Hafsat, ta sanya kanta cikin kafafunta ta kasa dagowa. Abdul’ azeez ta ji ya kwantar da kai a gadon bayanta ya yi shiru kamar ba ya jin kiran sallar da ake ta yi. Muskutawa ta yi cikin jin nauyi ta yi masa magana. “Yaya Azeez ana kiran sallah?”
“Ina ji Hafsat, na kasa tashi ne”’. “Ko in daga ka?”.
Ya jinjina kai, dariya na son kama shi duk da halin da yake ciki,wai ta daga shi kamar wani dan ta, har yanzu bai sauke kai daga gadon bayanta ba,
“It’s not easy daga kato iri na. Amma tunda kince zaki iya zo ki gwada. Menene punishment dina na laifuffukan da nayi miki? Above all (fiye da komai) a yau, kuma a yanzu, ina so in ce miki NA GODE!”
Murmushi ta yi duk da ta san ba kallonta yake ba. Cikin taushin murya tace.
“Punishment apologised. NAGODE din ta me ce ce?”
Dagowa ya yi daga kwanciyar da ya yi a bayanta ya juyo da ita gabansa suka fuskanci juna, kwayan idanunsa ya kalmashe a cikin nata ta yadda ba za ta iya dauke su ba in ba shi ya aminta da hakan ba.

“For everything!”.

Ya ba ta amsa da murya mai cike da mazantaka, da wani irin respect gareta cikin kwayar idanunsa. Tana so ta dauke idonta amma ta kasa sabida bai ba ta damar hakan ba. “Ban yi don ka gode min ba Yaya Azeez, yi wa kai ne. Amma ni ma ka yi min alfarma; ka maida hoton Aunty Mu’azatu dakinka, tunda ban fiya shiga ba”Abdul’ azeez bai taba jin ya ji nauyin mace a rayuwarsa irin

wadda ya ji yau na matarsa Hafsat ba. Ko bata fada ba bai yi niyyar maida hoton Mu’ azatu falo again ba don mahaifiya ba wasa ba ce. Baya son tuna kalaman da Mammah ta yi amfani da su a kan Mu’azatu wadanda sun kara farkar da shi ya san cewa akwai babban aiki a gabansa. Mammah ba za ta taba son Mu’azatu ba komin sauyin da lokaci zai kawo. Shi ma kuma ba zai daina sonta ba komin sauyin da lokacin zai kawo. Www.bankinhausanovels.com.ng
Babban kuskuren Abdul’azeez tunda ya fara soyayya da Mu’azatu bai taba baiwa Allah zabi a kai ba. Bai taba cewa idan alkhairi ce a gareshi Allah ya mallaka masa ita ba. Abin da ya sani kawai shine yana sonta, dole ya same ta don ita ce daidai da ra’ayinsa, sannan bai iya jure zama ‘loser’ a komai. Not even in the court of justice . In aka kada shi a Shari’ah (wanda da wuya ake samun hakan) har ciwo yake yi. Allah ya halicce shi mutum mai nasara a dukkan abin da ya sa gaba. Yana da yakinin a gaba ma zai yi nasara, zai samu Mu’azatu kuma zai daidaita da mahaifiyarsa a kanta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ita dai Hafsat tunda ta samu kalamanta suka jefa shi a tunani ta sulale ta yi bandaki. Sanda ta fito babu shi a dakin, sai kamshin turarensa. TAji
yar zuciya ta yi ta matsa gefen ibadarta ta tayar da sallah.
Bayan ta idar da sallah ta yi nafilfilinta sunkuyawa ta yi ta fada a tunani, abin da ya faru tsakaninsu ‘yan mintuna kalilan ta ke tunawa da shauki mai yawa. Fondest thought! Wato tunani mafi soyuwa a zuciya. Ko ba a gaya mata ba, wannan shi ne romance na tsakanin miji da mata da a shekarunta da rayuwar da ta yi ta tsayin lokaci a cikin masu jajayen kunnuwa ya kamata a ce ta sani. To amma ai kuma masoya ke yinsa kuma ba ya faruwa sai da soyayya. Wannan na nufin….. wannan na nufin… tsakaninta da Abdul’azeez Dakata akwai SOYAYYAH???
Tambaya ce da ta yi tsananin zurfi a kwakwalwarta har barin kanta ya soma ciwo. Wata murya ce daga can kasan ranta ta ke cautioning din da kakkausar murya. “Ki yi a hankali Hafsat! Be very careful!! Wannan rayuwar da Abdul’azeez ya soma jefa ki a ciki kuma zuciyarki da gangar jikinki suka karbe ta da hannu bibbiyu will ruin your entire future. Tunda ya ce ‘MATAR WUCIN-GADI ce ke, wani abu da Hausawa ke kira ‘dandani haukaci’, ya maida ke ‘emotional’, kuma ya yi ‘dumping’ dinki ya dauki wadda yake yi wa so na hakika. Da ma dai a ce! Zai dauke ki da irin matsayin da zuciyarki ta dauke shi ne a yanzu, amma ki zama jaruma, ki so kanki, ki yiwa kanki da rayuwar ki gata ki ja babban layi a kan wannan al’amarin
kowa ya tsaya a ‘limit’ dinsa har zuwa karshen tafiyar. Wani karfin zuciya ne ya shigi Hafsa a wannan lokacin. Ta yarda gaskiya ce zallah super ego side dinta ke gaya mata psychologically . Ta ci gaba da karfafawa kanta gwiwa da cewa, gara Www.bankinhausanovels.com.ng Abdul’azeez ya yi ta fushi da ita, amma za ta tserar da martabarta no matter what  Yana son kansa da yawa duk da akwai adalci a cikin (selfishness) dinsa. Ya kamata ita ma ta so kanta, ta tanadarwa mai sonta na hakika abin da zai yi alfahari da ita. Wanda ba komai ba ne sai “cikakkiyar Addah Hafsatu……”. Haka kawai ta ji kuka ya zo mata, wanda ba na komai ba ne sai na tausayin kanta.

*********

A masallacin unguwarsu irin fadan da Abdul’azeez ke yi wa kansa kenan. To amma ya ya zai yi ne? Shi kansa yana mamakin al’amarinsa da Hafsat, yadda yake zama ba shi ba muddin za su kadaice. Yana bukatar amini da zai gayawa damuwarsa, ya ba shi shawara. Sai dai kuma Allah ya halicce shi wani mutum mai son rike duk wani sirri da ya shafi iyalinsa. Hatta Mu’azatu ba ta san tsakaninsa da Hafsat ba. A tunaninta rayuwa suke kamar kowadanne ma’aurata in ta yi la’akari da yadda ta kusa rasa shi a kan kalamanta kan aurensa, ranar da za’a kai Hafsat gidansa. Gabadaya manyan abokan aikinsa wadanda suka zame masa amin ai na jiki a yanzu wato Abdallah, Taufeeq, Esq Ahmad and co. Kalamansu na yabo da alkhairi ne a kan Hafsat tun lokacin aurensu. Yarinyar da komai nata da kamalarta sun kayatar da kowannensu, duk da sun lura kamar Abdul’ azeez ba ya sonta. Ba tare ya yi karatu da su ba, wajen aiki ne ya hada su, don haka ba su da labarin Mu’azatu ko wani abu da ya shafe ta. Hotunan bikin su data gani ba’a wurin dayan su bane a wajen wasu Lauyoyi ne data sani wadanda suma a Federal High Court suke. Abdallah ya taba gaya masa ko bai son yarinyar nan wani lokaci zai zo da zai so ta, ko da zai yi mata kishiya. A lokacin ya ce da shi, “Allah ya kiyashe ni zama da mata biyu”. Kuma haka yake har kokon ransa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bai taba mafarkin zama da mace sama da daya ba a burikan rayuwarsa. Yana kuma rokon Allah kada ya jarabce shi. A komai yana so yayi koyi da mahaifinsa. He want to build a GREAT and understanding family kamar nasu, irin na Dakata bakidaya wanda babu hatsaniya a cikinsa. Ga shi lokaci sai gudu yake yi, yana tunatar da shi manyan al’amuran da ke gabansa. Tafe yake daga masallaci zuwa gida yana tuki a hankali yana wannan tunanin cikin neman mafita ga rayuwarsa. Yadda yake tafiyar da motar tsammani za ka yi tayoyinta sun lalace ne. A haka dai har Allah ya nufa ya zo gida.
Yadda ya bar gidan haka ya dawo ya same shi. Ya fahimci Hafsat ba ta fito ba. Dakin nata ya leka duk jikinsa a sanyaye yake, tana durkushe a kan sallaya ita ba sallah ba, ita ba barci ba. Ya dade rike da murfin kofar yana_kallonta, abubuwan da suka faru a dakin mintuna kalilan da suka gabata na dawo masa. Wani gajeren lokaci ne da ya kasa gushewa a cikin rai da zuciyarsa. Ajiyar zuciya mai nauyi ta subuce masa, wadda ta ankarar da Addah wanzuwarsa a dakin, duk da kafin hakan, kamshin jikinsa ya ziyarci hancinta. Ba ta kawo shi ba ne saboda yadda suka cakuda da juna a yau sosai ita kanta kamshin ‘creed aventus’ ta koma yi bakidayanta. Kasa dagowa ta yi ta dube shi sabida nauyinsa da ta samu kanta a ciki tun faruwar al’amarin kamar wannan shi ne karo na farko, sai daya kira sunanta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dagowa ta yi ta zauna sosai ta dafa gado da hannunta na dama, amma ga mamakinta ta kasa kallonshi cikin ido. Murmushi ya yi ya shigo har tsakiyar dakin ya tsaya, hannayensa duka biyu zube cikin aljihun bakin ‘jeans’ din da ke jikinsa.
“Yau da wuri zan kwanta, saboda gobe lahadi ina so zan yi sammako, za mu je jihar Adamawa daurin auren kanin wani abokin aikina a Yola, zai zo da asubah ya dauke ni, zan samu abokiyar kwana a dakina yau? Bana jin dadin jikina sosai, ina tsoron kada cikin dare zazzabi ya rufe ni’.
Kunkuni Hafsat ta hau yi tana zumburo baki,“ka ji min wani sabon batu!”, ya kasa jin me ta ke cewa.
Sake matsowa ya yi ya zauna a gefen gadon daidai hannunta. Da sauri ta janye hannun, “A’ah Hafsah na fara cizo ne?”Ta yi masa shiru. “To zan samu ‘yar tayin kwanan?” Sunkuyar da kai ta yi tana magana ciki-ciki, sauka ya yi daga gefen gadon ya zauna a kusa da ita sosai ko ya samu ya fahimci me take cewa. Ta yi saurin ja da baya kamar wadda aka danawa shocking . Da mamaki yake kallonta, ta sunkuyar da kai ta ki yarda su hada ido. “‘Wani abu ya faru ne bayan na fita?” Ya tambaya da murya ta nutsuwa. Tareda halartowa kansa nutsuwar don son fahimtar inda ta dosa. Girgiza kai ta yi a hankali, “Ba abin da ya faru!”’Na ga kina ta guduna ne, Hafsat yaushe ta kaimu da haka???” Kwalla ya hango ta taru a gefen idonta tana ta kokarin maida ita. Kafin ta ankara ya dago fuskarta sai kawai ta sake su ta ba su damar silalowa yadda suka ga dama. “Yaa Sattaru Sutrukal jameel A fitata da dawowata na yi wani abu da ya bata miki rai?” Girgiza kai ta yi. Www.bankinhausanovels.com.ng
“To tashi mu je na ce ki taya ni kwana, ina da tafiya gobe da asuba saboda a yammacin gobe za mu dawo. Haka kawai yau bana son barin ki kwana ke daya”.
Mikewa ta yi ba don ranta na so ba, sai don a dan zamanta da shi ta fahimci shi mutum ne mai naci a kan abin da ya sa kansa, ba ya niyyar abu ya fasa. Wardrove dinta ta bude ta dauko kayan barci masu kauri ta shige ‘toilet’, brush ta fara yi sannan ta yi wanka ta sanya su. Kanta cikin ‘shower-cap’ ta fito sai digar ruwa ta ke. Fatar jikinta ta kara yin fresh , sai kamshin bathrobb din da tayi amfani dashi na desire -dunhill takeyi, ga mamakinta har zuwa wannan lokacin yana zaune a gefen gadonta, wayarta da ta sanya a caji ce rike a hannunsa, ‘gallery’ din wayar ya shiga. Hotunansa ne birjik duk a ciki wadanda Isma’el ke turo mata, da wadanda bai san a ina ta same su ba. Ga kuma na ‘dinner’ dinsu da aka yi a ‘A Class’.
Dagowa ya yi da zummar tambayarta inda ta same su? Amma sai ya ji harshensa ya sarke. Wata irin kalar fata gareta mai santsi, mara duhu kuma mara haske sosai, kai ka ce ta fito ne daga jinsin birnin Bassaso Bari na kasar Somalia. Wayar ta subuce daga hannunsa ta fadi kasa. Turo baki ta yi tana Www.bankinhausanovels.com.ng tambayarsa don me yake mata bincike a waya? Ita ta taba taba wayarsa? Budar bakinsa sai cewa ya yi, “Don na isa!”. Ya fadi hakan yana jifanta da wani irin tattausan kallo, wanda shi akan-kansa bai san yana yi ba. Ta sake cuno bakin ta tsugunna a gabansa za ta dauki wayarta, ya ce, “Wallahi ki ka sake cuno min baki I will kiss it …” ba shiri maida bakinta daidai. Duk wani abu da zai sake jawo wani abu makamancin wannan yanzu bata maraba da shi. Ta dade da shata masa babban layi. Sabuwar Suhaana ce wannan wadda ta san ciwon kanta. Ba wadda zata zauna dan Dakata na yi mata walagigi da rayuwa ba. Za ta mike ya take hannunta mai rike da wayar. Wata “yar kara ta saki, “Yayan Haleem za ka ji min ciwo”. Idanunta suka cicciko. “Ki gaya min abin da ki ke fadi don na ce ki taya ni kwana!”. Ta runtse ido don zafi don sosai yake murje mata yatsu da yatsun kafarsa. Da sauri ta ce, “Ba fa wani abu na ce ba, cewa na yi sai dai in a kwanta kai da kafa”’Me ye kwanciya kai da kafa?”’
“Don Allah ka daga min hannu, sai in maka bayani”’.
Tausayi ta bashi sosai ganin yadda idonta har ya tara hawaye. Hannun ya kamo ya rike cikin nasa yana murza mata, abinki da farin mutum har yayi jawur. Ta matse kwalla da hannun hagunta, “So sorry!” Ya ce a hankali. Yi min bayani ina jinki, mene ne kwanciya kai da kafa?”
“Ka sanya kanka inda na ajiye kafata, ko ni in sanya inda ka ajiye kafarka”. Dariya Abdul’ azeez ya yi, “Saboda me to?” Ta yi shiru tare da kwace hannunta da karfi ganin ya fara canza yanayin murza mata yatsun, wayarta ta dauka ta yi gaba. Ya bi bayanta.
Sai da ya rufe ko’ina na gidan ya kashe wuta da kayan wuta, sannan ya same ta a dakin. Ta jefa filo a kan ‘resting chair’ ta yi kwanciyarta ta rufa da zanin atamfarta. Yana shigowa ya ce,
“Me ya yi zafi na kwana a kujera Hansatuwa Addar Mammanta? Na yarda a yi kwanciyar kai da kafa!”’.
Tashi ta yi tana murmushi jin sunan da ya kira ta da shi, “Ka yi alkawari?” “Alkawarin me?” Ba za ka canza ‘position’ din kwanciyar ba”. “Na yi alkawari Hafsat, amma in kafata ta tsokale miki ido ba ruwana”. Kana juye-juye ne in kana barci?”
“Juye-juye kai! Har da mirgine-mirgine”’. Www.bankinhausanovels.com.ng
“To ni zan je karshen gado, kai kuma ka zauna a farko, kuma ‘still’ kai da kafa”’. Yayi ‘yar dariya.
“In aka yi hakan bargon ba zai ishe mu ba”.
“Dauko wani, kowa ya rufa da guda daya”. Ya marairaice fuska, Ga shi kuma guda daya ne Babana ya sai min, kasancewar ni ba mai jin sanyi bane, hasalima ba in ba lokacin sanyi ba ni bana rufa, ke ce Mammanki ta saya miki su da yawa. Na gansu kalakala a dakinki. Watakila da zata iya cikinta zata maida ke kada kiji sanyi, kiyi ta samun heat ”. Murmushi ta yi. “To bari in je in dauko nawa”’.
“Ok, go!”Ta mike ta nufi kofa ta murda ta fita. Da dan banzan gudu ta dawo ganin wani uban duhu. Gabadaya fitilun gidan ya kashe bai bar ko guda daya ba. Dariya sosai Abdul’azeez yake yi. Ya mike ya isa ga dan firjinsa, madarar oldenburger fresh milk ya zubo a kofi ya kawo mata. Zama ta yi a gefen gadon tana ta fushin dariyar da yake mata.
Mika mata ya yi, “Karbi ki sha, ba kyau kwana da yunwa, daga ni har ke ba mu yi ‘dinner’ ba”.
Ba musu ta karba ta kwankwade, don yayi gaskiya yunwa take ji, ya kara mata ta shanye ta ba shi kofin ta haye can karshen gadon ta rufa da zanin atamfarta. Zama ya yi a farkon gadon yana shan madarar a hankali. Dauki duvet din ki rufa ke daya, na bar miki’Ta kuwa janye ta kudundune a cikinsa. Shi ina zai iya rufa da wani quilt bayan zai kwana cikin zafi babu AC sabida ita? Dama tsokanar ta yakeyi. Sai da ya gama abin da zai yi, ya yi addu’a, sannan ya yi (light off) ya kwanta.
Shi ya tashe ta da asubah suka yi sallah jam’i tare. Cikin sauri ya yi wanka ya shirya cikin farar shaddah kal ‘yar ciki da babban riga sun sha aiki da zare ruwan kasa , ya kafa hula zanna-bukar ruwan kasa ya daura agogon ‘rolex’ a damtsen hannunsa duk Hafsat na kwance tana kallonsa.

MU HADU A LITTAFI NA UKU

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *