AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 2 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Na gode!”’Ta furta tana mai dago kai ta kalle shi. Ji ya yi kamar zuciyarsa ta yi tsalle ta fice daga kirjinsa tadawo kuma, da gaske ne (she’s so innocent) in ba haka ba me ya yi da har za’a gode masa? Shi a nasa tunanin ma in za’a dubi lamarin da idon basira ai babban laifi zai aikata a gare ta (saki a wajen diya mace). A gefe guda ga kuma tsallake maganar mahaifiyarsa da zai yi. Ai kuwa bai cancanci godiya ba ta kowanne bangare. Sai dai ko ta wajen Mu’azatu wadda zai tsallake umarnin iyayensa a kanta saboda farin cikinsu shi da ita. Bai san me zai ce mata ba, saboda haka kawai ya daga kai, sannan ya juya ya fita daga dakin karatun. Ya koma dakinsa idonsa cike da bacci da gajiya. Koda Mu’ azatu ta kira shi don su yi hirar daren da suka saba (midnight call) cewa ya yi da
ZAMU TASHI
ita, ta yi hakuri bacci yake ji. Kuma ya yi magana mai yawa saboda ita a daren nan. Ya yi alwala ya yi nafila raka’a biyu, ya roki Allah ya rufe bakin Hafsah kar ta tona masa asiri a wajen Mammah komai runtsi. Duk da dai ya lura yadda ta ke son cika burikanta zai iya danne komai, wanda haka yake har zuciyar Suhaanan.
**********?
Kwana ta yi tana juya maganganun da suka yi na karatunta da nemo mahaifinta a zuciya da Www.bankinhausanovels.com.ng kwakwalwarta. Su kadai ta ke tunani a matsayin matsalolinta yanzu a rayuwa, ga shi ta samu wanda ya yi alkawarin dauke mata su. A kan me kuwa ba za ta yi masa yadda yake so ba ita ma? Auren ko kadan ba ya kanta dama, bata da wani hope a kansa ko experience kan abin da ya kunsa sosai balle har ta sa shi a lissafinta. Ta amince ne dama saboda Mammah don ta amincewa ranta babu abin da Mammah za ta nema a wajenta ta kasa yi mata muddin tana da iko, amma sam ba ya gabanta. Sai ga shi a yanzu ya juye ya zama sanadin alkhairi a gare ta, sanadin da zai kai ga cikar burikan
rayuwarta (karatu da mahaifinta, itama ta ganta da UBA, wanda zata bugi kirji tace nata ne ). Ta faranta wa Mammah, sannan ita ma ta samu farin cikinta. Har ila yau, shi ma ya samu nasa cikar burin. A iyaka dan kankanin — tunaninta, me ya fi wannan kwangilar sauki da riba
*********
Gadan-gadan Tsohon Ambasada Hamza Atiku da maidakinsa Hajiya Maryam suke shirye
shiryen auren ‘ya’yansu, auren da suke so ya bar tarihi a dangi don haka ba karamin shiri suke masa ba. Soyayyar Abdul’azeez da Mu’azatu sai abin da ya karu, kullum suna tare a waya, ko ta biyo shi office ko shi in ya tashi ya je can inda ta sauka gidan Antinta har ta koma gida Lagos ba abin da ya sauya.
Ba ya yi mata zancen komai game da aurensa, ita ma ba ta tambaya, ba ta taba neman sanin yarinyar da za’a aura masa din ba, shi ma bai taba yin wannan gwanintar ba. Zai iya cewa daga ranar da suka yi magana ta farko shi da Suhaana ko a hanya ba su kara haduwa ba, duk da cewa gida daya suke kwana. Yana riga kowa fita a gidan, sannan ba ya dawowa da wuri. Mammah ma ba ta kara damuwa da su kebe din ba don su kara fahimtar juna, shirye-shiryen biki kawai ta ke, hankalinta kwance, don ta lura ‘yar damuwar da Suhaana ta ke ciki bayan ta yi mata zancen auren tun daga ranar da suka yi magana ita da Abdul’azeez ta rabu da ita, ta saki ranta tana bata hadin kai a kan komai. Biki ya rage saura sati Www.bankinhausanovels.com.ng uku tuni an bugo I.V an fara rabo cikin dangi. A yadda Mammah ta tsara za su taho Kano ne, a nan za a yi komai, liyafar cin abincin dare (dinner) kawai za a yi a Abuja washegarin daurin aure. Kullum za ka ganta tana waya da mutanen Dakata ana ta shirye-shirye. Ta fannin Daddy kokari yake ya kammala ginin da yake yi wa Abdul’azeez a Estate din (Sun-City). Wani kyakkyawan ‘Mansion’ mai hawa daya da ya dauki shekaru yana gininsa yana dakatawa tun yana Ambasada, yanzu ya maida hankali yana so a kammala komai cikin lokaci. Mammah zaune a kayataccen falonta cikin kwalliya ta kece raini kamar kullum. Waya ta ke yi da aminiyarta ta cikin Abuja, Hajiya Halima matar Controller, magana suke yi a kan babarbariya mai gyaran jiki da Hajiya Haliman za ta turo ta fara gyara amarya daga yau har ranar da za a kai ta dakinta. Wannan shi ne gudunmawarta.
Sosai Mammah ta yi godiya, ta daga murya ta kira Hafsat wadda ke dakinta tana gyaran kayanta da aka kawo daga wanki da guga. Ta ajiye rigar hannunta ta fito ta tadda Mammah a falo, tun kafin ta zauna Mammah ta ce.
“Ki yi shiri gobe za mu wuce Kano, kuma Hajiya Halima ta turo mai gyaran jiki za ta zo ta fara miki daga yau, tare da ita za mu tafi kano”. Suhaana tace, “Mommah me jikina ya yi da za a gyara shi? Na yi dauda ne?” Dariya Hajiya Maryam ta yi, ta rike hannunta cikin nata. “Kullum Adda ta tsaf ta ke, kal-kal kamar tarwada saboda wanka. Shi gyaran aure daban yake, ba irin wanda ki ka saba yi ba’.
Hafsat har tausayin Mammah ta ke ji a ranta in ta yi duba da yadda ta dauki ranta ta dora akan auren ta ke kuma zumudin auren nasu. Ba ta taba ganin abin da Mammah ke farin ciki da shi a duniya irin auren nan nasu ba. Ya ya za ta jia ranta idan ta gaya mata na wucin gadi ne ba mai dorewa ba ne, ta kyale wata mai gyaran jiki? Ai ko Ya Azeex bai ce ta boye ba, ita a karan-kanta ba za ta iya fada ba.
Karfe shida na yammacin washegari suka isa birnin Kano, ta Dabo ci gari, jallah babbar hausa, yaro ko da me ka zo an fi ka, mai Dala da gwauron Dutse, Kano tumbin Giwa, ta sarki Ado Allah ya yi maka rahma.Abdul’ azeez bai taho tare da su ba, yana Abuja sai ana saura kwana daya daurin aure zai taho tare da tawagar lauyoyin chambarsu. Mai gyaran jiki mai suna Fannah ta shiga aikinta a kan Suhaana. Eh, lallai, ta yarda da abin da Mammah ta ce, shi gyaran auren daban yake, kuma wannan da ake mata ba karami ba ne. Ganin yadda cikin kwana uku fatar jikinta ke wani irin salki da sheki. Ga Addar babu Www.bankinhausanovels.com.ng kawaye sai ‘ya’yan dangi ne suka zama kawayen nata su Halima ‘yar Anty Luba, Saima da Khalisa ‘ya’yan Anti Mariya da Anty Furairah duk da ta dan girme su don cikinsu ba wadda tayi candy. Gayya sosai Hajiya Maryam da kannenta suka yi. Ta bangaren maza ma ba karamar gayya Dr. Hamza ya yi ba shi da sauran ‘yan uwansa. Ba’a maganar Minister Abdulkareem Dakata ya yo babbar gayyata ta manya Zuwa daurin auren jikan nasa. An yi kamu ranar alhamis, juma’a aka yi wunin biki a nan main house nasu. A yammacin ranar wato ana I gobe daurin aure Abdul’azeez da abokan aikinsa suka iso. Tsohon Minista Abdulkareem Dakata mai masaukin baki ya yi musu masauki a gidan saukar baki na “Tahir Guest Palace’.
Washegari asabar karfe goma daidai na safe daruruwan jama’a suka shaida daurin auren Abdul’ azeez da Hafsat a kan sadaki naira dubu hamsin lakadan, wanda ya fito daga aljihun Abdulkarim Dakata. Aka yi addu’o’i masu yawa aka shafa. Daga nan maza suka wuce liyafar cin abinci acan Tahir wadda Dr. Hamza ya shirya, mata kuma suna shirin tafiya Mothers Night a daren ranar a (FABS EVENT CENTRE) wanda Hajiya Maryam ta shirya.
Rana ta farko da fuskar Hafsat-Suhaanah ta soma daukan make-up na zamani a rayuwarta. Ta koma tamkar wata sabuwar kyakkyawar halitta ta daban, wadda aka baro daga cikin kwai don kyau da ban sha’awa. Hatta Anty Zuwaira da ke adawa da auren a zuciyarta sakin baki ta yi tana kallon Hafsat, ta kuma yarda har ranta_ yarinyar kyakkyawa ce tun asali, kawai ta raina asalinta ne har gobe tana ganin wautar Hajiya Maryam na hada wannan auren, yaro irin Abdul’azeez yarinya ‘yar asali, ‘yar gata, ‘yar babban gida ta dace da shi ba ‘yar mai aiki ba. A ra’ayinta fa. Amma tunda ita ta haifi abinta wa ya isa ya yi magana? Ta yi tsaki ta dauke kanta daga kallon yarinyar. Wadda Hajiya Maryam ta shirya cikin wani rantsattsen leshi baki mai ratsin silver, goggoron kanta silver, dankunne da sarka, takalmi da purse duka silver. Duk wanda ya daga kai ya dube ta sai ya ce, “Masha – Allah’. Hannunta cikin na Mammah wadda ita ma ta sha nata adon cikin wani pitch tattausan leshi cotton, kawayenta su Anty Halima na take mata baya cikin tasu shigar ta Www.bankinhausanovels.com.ng alfarma suka shiga motoci zuwa (Fabs Event Centre). Taron na mata ne zallah, don haka babu bukatar zuwan ango da abokansa. Sai dinner ta gobe da za a yi a Abuja ne zasu halarta, washegari lahadi za’a yi ta (by-couple), wato kowa da mijinta. Iyakar (programmes) din da suka tsara kenan babu jan dogon biki, kuma alhamdulillah komai ya kayatar. An ci an sha, an yi hotuna da ‘vedio’ kala-kala don tarihi aka watse. Suna fitowa daga mota za su shiga gida Abdul’azeez da wasu abokansa biyu, Barrister Abdallah da Barrister Adebayo na tsaye a dakalin kofar gidan suna magana. Yana cikin farar shadda kal (hilton) da babbar rigar rataye a kafadunsa. Hasken fitilar kofar gidan ya haske masa yaran matasan ‘yammatan dake fitowa daga mota, fuskar Hafsat tarwai a tsakiyar ‘yammatan. Ya gyara tsayuwa yana kallonsu suna shige shi daya bayan daya zuwa cikin gida. A ransa ya ce, ina ruwan (sweet sixteens), gaba daya kawayen ma wadanda duk ya sansu a dangi yara ne kamarta. Abin ya ba shi dariya sosai, sai da ya yi murmushi. Adebayo ya ce “ Wow! Abdul’ azeez you have a beautiful wife, looking gourgeous”’Abdul’azeez ya galla masa harara, ita ma ya juya ya galla mata tata, ya dauke kai suka ci gaba da maganarsu da Abdallah.
Ta ga hararar da ya yi mata sosai, don wajen akwai wadatar haske duk da dare ne. Jikinta ya yi sanyi dama a sanyayen yake. Tun lokacin da aka tabbatar mata an daura mata aure jikinta ya mutu,
bakinta ya mutu. Mammah ta lura da hakan, amma ba ta ce mata komai ba. Is normal ai, mace ta canza sanda aka daura mata aure. Nauyi ne babba ya hau kanta, ta zama karkashin mulkin wani, ta zama UWA, ai kuwa nauyin ba karami ba ne. Washegari da safe kowa na gidan ya tashi ne da shirin wucewa Abuja. Karfe tara daidai motocinsu suka tashi zuwa Abuja dauke da amarya, shi ma angon da tashi tawagar sun kama hanya, zuwa azahar suna cikin Asokoro gidan tsohon Ambasada Hamza Atiku. Nan kowa ya ci abinci aka huta. Su Anty Halima suka wuce gidan amarya don kara gyaggyara komai, wato jeren da suka tsaya ma’aikatan kamfanoni suka yi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai shirin tafiya ‘dinner’ wadda za a yi a (Aclass). Ana yi mata kwalliya, amma gabanta faduwa yake yi jin ana fadin har da angon da abokansa za’a yi dinar, idan ta tuno da muguwar hararar da ya zabga mata a Kano ba laifin tsaye babu na zaune. Amma sai Abdul’azeez ya bada mamaki, har aka yi dinnar aka kare bai ba da wata matsala ba. Ko nuna wata kafa da za’a gane baya maraba da auren Hafsat. Da aka tashi ne dai ya bi abokansa bai tsaya bi ta kanta ba ko motar da ta kawo su tare, sai ita kadai aka dauko a motar aka dawo da ita gida.
Sai shirin tafiya kai amarya. Nan fa ake yinta. Yau za’a raba Suhaanah da Mommah, Suhaanah da Baba Azumi. Kuka ta ke kamar na fitar rai ko Mammah ta ji tausayinta ta barta su ci gaba da rayuwarsu tare. Ita kanta Hajiya Maryam dauriya
kawai ta ke yi, amma zuciyarta ta gama karyewa. Baba Azumi dai sai kewaye ta shige ta kulle, sannan aka iya fitar da Hafsat zuwa falon Daddy. Albarka kawai ya sa mata ya ce su je da ita, zai biyo ta gidanta ya yi mata fadan. Kawai sai aka ga Mammah ta dauko mayafi ta yafa ta kama hannun Hafsat zuwa mota ta ce da ita za’a je. Su Hajiya Halima na tsokanarta wai surukar sabon qarni. Murmushi kawai tayi tana shanye hawayenta. Sannan ne Hafsat ta rage kukan motoci suka kama hanyar ‘Sun-city’.
A daidai wannan lokacin Abdul’azeez yana dakinsa na gidansu. Ya kulle kansa yana waya da Mu’azatu, kuka ta ke yi masa sosai cikin matsanancin tashin hankali. Gani ta ke ta rasa Abdul’azeez ta gama, yau zai shiga dakin amaryarsa shi ke nan fa! Shi kuma lallashinta yake yana kara tabbatar mata da alkawarinsu. Amma ina! Mu’ azatu jinsa kawai ta ke, ta kasa yarda duk da ta san har zuciyarsa yake nufin alkawarin, amma tunda ta ga hotunan bikin da yarinyar da yake cewa ba ya so din a wayoyin Www.bankinhausanovels.com.ng abokansa hankalinta ya yi mugun tashi. Ta dauka wata bakauya aka aura masa da farko, ko wata wadda ba ta amsa sunan mace ba, amma idonta ya gane mata Hafsat-Suhaana Addar Mammah kwance a kafadun mahaifiyarsa, ta kuma gansu tare a hotunan sun sha anko sun durkako (A-class) inda aka yi dinar kamar don su aka halicci juna. Tuni ta daina yarda da kalaman bakinsa duk da cewa duk cikin hotunan da aka nuna mata din babu inda ta ga ya kama Hafsat ko ya mannu da ita don nuna soyayya. Da ya gaji da lallashinta, amma ta ki daina kukan, sai ya yi shiru. Amma bai kashe wayar ba, bai san kuma da kalaman da zai yi amfani da su Mu’ azatu ta yarda da shi ba. A ganinsa duk wasu kalamai da yake da su sun kare. Ta sanshi ai, ta san halinsa, ta san babu karya cikin halayensa. Ya yarda ya auri Hafsat ne don ya samu hanyar aurenta, kuma babu soyayyarta ko kankani cikin zuciyarsa. Me ya sa ba za ta yarda ba? Shirun nasa sai ya kara tunzura ta, ta ci gaba da gursheken kuka. Zuciyarsa ta dinga bugawa fat-fat-fat, tsigar jikinsa ta dinga tashi. Enough, is enough Mu’azatu, ki gaya min yanzu me ki ke so na yi?”
An zo gabar da ta ke so don haka ta sassauta kukan. “Abdul’azeez na dade ina yi maka tanadin kaina, ina tattala maka budurcina, ban taba wasa da shi ba. Ban taba sha’awar bada shi ga waninka ba, kullum burina ya zamo kai ne za ka karbe shi cikin girma da daraja. A yau wata ta riga ni samunka, da ka kusance ta ta gama janye min kai komai rashin son da ka ke mata. Wallahi in ka kusance ta na hakura da kai har abada ko kai ne autan maza. Zan roki Allah ya cire min sonka ko ya zama ajali na a kan in yi sharing dinka da wata, ni wannan ne kawai damuwa ta’Shiru ya yi kamar ruwa ya cinye shi. Shi kansa bai san me ya sa ya yi shirun ba. Mu’azatu ta baro Www.bankinhausanovels.com.ng zance wanda shi kansa ya girmi kwakwalwarsa. A ganinsa bai kamata ta shiga wannan hurumin ba duk da akan-kansa bai taba kawo yiwuwar hakan cikin rayuwar auren kwangilar da zai yi da Hafsat ba, amma ai matarsa ce, koda yace da Hafsat kayyadadden zama zasu yi iyayensu da suka daura auren da tsarkakakkiyar niyya suka daura shi kamar yadda addinin muslunci yayi umarni, ba su san da wani abu bayan wannan ba, don haka ko ta ina aka je aka dawo sunan Hafsat matarsa, an taba gindayawa miji hukuncin kada ya kusanci matarsa? Koda yake son Mu’azatu shi fa ba sakarai ba ne da zai zauna mace ta gindaya masa abin da ta ke so ta ce dole sai ya bi ba. Don haka ransa ya baci sosai da maganar Mu’azatu kawai sai ji ta yi ya kashe wayar.
Matsanancin tsoro da mamaki suka taru suka lullube Mu’ azatu. Ta ciro wayar daga kunnenta ta duba sosai, ya kashe. Tunda suke tare bai taba kashe mata waya ba, me hakan ke nufi???
******
“Yan kawo amarya sun ajiye ta sun juya, Mammah kuwa da dabara ta samu ta fice. Aka barta daga ita sai Harira ‘yar Baba Azumi a dakin da aka tanada don mai aiki a gidan. Harira matar aure ce da ‘ya’ya hudu, lokacin da Baba Azumi ta gayyato su biki daga Sokoto Mammah ta yaba da hankalinta da kazar-kazar dinta don su suka yi ta tsaftace gidan lokacin biki da rabon abinci, ta roki Baba Azumi ta barta ta zauna da Adda ta debe mata kewa zuwa Www.bankinhausanovels.com.ng sati biyu kacal. Kafin lokacin ta saba da sabuwar rayuwarta ta saki ranta. Baba Azumi ta amince, don haka aka bar Harira a gidan tare da Hafsat.
Tunda Harira ta shige dakinta ta rufe kofa ba ta sake fitowa ba. Hafsat-Suhaanah, ta ci kukanta ta gaji har ta gode Allah, hawayen suka tsaya don kansu. Kanta ya sara ya soma ciwo ta kwanta lamo! A kan filo ta rufe jikinta da mayafinta, ta takure a can gefen gadon ta soma ajiyar zuciya.
Ko da ya kashe wayar da suke yi da Mu’azatu komawa ya yi ya jingina bayansa da kofar dakin nasa. Ya lumshe ido zuwa dan lokaci ya bude ya zura wayarsa a aljihunsa. Lokacin ya tuna su Abdallah suna kofar gida suna jiransa su raka shi gidansa. Toilet ya shiga ya yi wanka ya canja kayan jikinsa da wani sassalkan yadin filtex (milk colour) ya taje sumar kansa, ya sanya hular da ta dace da kayan nasa, ya daura agogon (swatch) a damtsen hannunsa ya fesa turare har kala uku. Ya janyo manyan jakunkunan da ya hada kayansa na dakin nasa, ya sanya takalmi sabo dal! Ya fito da jakunkunan sannan ya janyo kofar dakin nasa ya fita.
Gidan babu kowa a falo, duk sun dawo daga kai amarya sun gaji sun kwanta, gobe kowa zai kama gabansa. Har ya fice bai hadu da kowa ba, ya tadda abokansa a waje zaune kan fararen kujerun da ke harabar gidan suna hira. Yana fitowa suka mike suka karbe shi jakunkunan suka shiga motocinsu suka wuce (Sun-city). Kofar gidan akwai maigadi wani Danfulani da Daddy ya samar musu, ya bude musu (gate) suka shigo da motocinsu, suka yi parking suka firfito. Dukkaninsu Lauyoyi ne, na gwamnati da masu zaman kansu. Shi ya bude kofar falon suka shiga,
kowa ya nemi inda ya yi masa ya zauna a lafiyayyen (European parlor) da Mammah ta shirya, in ka wuce shi za ka tadda (African parlor) wanda bai kai shi girma ba, wanda ya ji shimfidun gargajiya da adon carpet din fata na jikin bango da su tum-tum abin gwanin ban sha’awa kai kace sun hada jini da sarauta ne. A cikin wannan (African parlour) kofofi ne guda biyu wadanda suka kunshi dakunan barci biyu, daya Www.bankinhausanovels.com.ng nasa, daya na matar gidan. Daddy ya kawo shi ya ga gidan tun sanda ake gininsa don haka ya san kansa. A kowanne dakin barci akwai makewayi, kicin (madafi) yana gab da shiga kofar falon farko, wato ba a cikin falon aka yi shi ba. Akwai ‘yar doguwar baranda a kofar shigowa falon, wadda aka aje fararen tukwanen fulawoyi masu kyawun gani da fararen kujerun roba. Harabar gidan za ta iya cin motoci uku ba tare da kowacce ta gogi ‘yar uwarta ba. Dakin maigadi na jikin gate, dakin mai aiki yana daga bayan ginin falon, wato sai an fito daga ‘main building’ din an zagaya ta baya za a tadda dakin mai aiki. Yadda su ESQ Abdallah suka nemi wuri suka zauna cikin tausasan kujerun falon haka shi ma ya nema ya zauna. Barrister Taufeeq shi ne karshen shigowa yana janye da jakunkunansa yana daga tsaye ya ce, “Dare fa ya yi, ka shigar da kayan Malam ka fito mana da amarya mu saya maka bakinta, mu yi muku addu’a mu koma namu gidajen”.
Harararsa ya yi ya mike ya karbi jakunkunan ya yi ciki. A ransa ya ce, wai su saya min bakinta, to in yi me da shi?
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG