AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 





MUN TSAYA 

Mu’azatu please, I’m sorry”.
Sannan ya sake kira. Wannan karon ta amsa kiran, amma maimakon ta ce komai, kuka ta sanya masa. Kyale ta ya yi ta yi har ta gaji. Ta share hawayenta sannan ta ce, Na huce!”’Murmushi ya yi, ya gyara kwanciyarsa cikin ni’imtaccen gadonsa, ya ja ‘quilt’ ya rufe rabin jikinsa, ya canza rikon wayar daga dama zuwa hagu. “So soon haka?” Murmushi ta yi kamar yana ganinta. Idanunta jajir don kuka.
“Tunda ka san ka yi min laifin, ka kuma amsa ka yi, ka bani hakuri, ci gaba da fushin nawa na mene ne?”
“Au, ni ba ki san kin yi min laifi ba? Ki dubi tsabar idona ki ce wai…..” “In ana sulhu ba’a tone-tone”. Ta katse shi. “Ki yarda to ba ni kadai na yi laifi ba, dukkanmu mun yi wa juna. Kuma naki yafi yawa.
Mu’azatu bana son raini, ko da aure tsakaninmu

ZAMU TASHI 

bai kamata kice min kada in kusanci matata ba. Ina ruwanki? This is my personal world, mind your own business. I’m sorry (once again) for not picking your calls. In na ce ban yi kewarki ba na yi babbar karya. I love you Mu’ azatu, you are the goal I want to achieve now, believe me or not”. Wata doguwar ajiyar zuciya Mu’ azatu ta sauke, duk da kalamansa na farko sun yi radadi a zuciyarta, to na karshen sun wanke radadin. Haka yake, haka Allah ya halicce shi, ba ya boye gaskiyar abin da ke zuciyarsa don ya faranta maka, ba ya karya don a so shi, in za ka so shi ka so shi a yadda ka same shi. Ta dade da fahimtar hakan. T’m sorry too…”  And I love you more…” 

Dariya ta saki har da wata irin shesshekar shauki. Suka ci gaba da hirarsu yadda suka saba, amma ta yau ta fi ta kullum gardi. Bayan fitarsa da rufo kofarsa Hafsat tasowa ta yi ta dauki ledojin da ya aje ya fice ta bude. Sunkin gasassun kaji ne suyar (YAHUZA) da juice da fresh milk da daurin Www.bankinhausanovels.com.ng (shawarma) har guda biyar. Harira ta yi sallama ta yi mata izinin shigowa. Ta aje mata abincin da ta dafo (express). Cikin sanyin muryarta ta ce da ita, 

Ga shi kuma ya sayo, da baki dafa ba’’Ba komai, gobe sai in dumama in ci”Ta mika mata leda daya ta karba, ta yi godiya ta dau abincin da ta kawo ta fita tana fadin, Allah ya tashe mu lafiya, in kin ci ki sha magungunan nak”. Hafsat ta ce, “Insha Allah”. Ta fita ta rufo mata kofar. Zama ta yi a tsakar dakinta ta ci kazar nan ta koshi, ta sha magani sannan ta yi sallolin nafila kamar yadda ta saba. Ta sanya kayan barci masu laushi, ta yi addu’a ta kashe wuta mai haske, ta bar dim-light ta kwanta. Asuba ta gari Hafsat-Suhaana. 

******* 

Washegari da safe bayan ta yi sallar asubah ta yi wanka. Ta shirya tsaf cikin wata lallausar atamfar (holland) koriya shar, ta yi daurin kai soSai ya zauna mata a kai cif-cif gwanin ban sha’awa. Dressing din nan na hausawa da bai dameta ba, amma Mammah tace dole ta dinga yin shi yanzu ta rage zama da dogayen rigunan nan nata, ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi, wadanda Mammah ta cika mata gaban madubi da su. Ta zura kyawawan kafafunta cikin (flat shoe light green) samfurin polo ta fito falo. Motsin Harira ta ji a inda ta fahimci kitchen ne, sai ta bi ta can. Daga bakin kofa ta tsaya tana dan murmushi, Anty Harira ina kwana, mun tashi lafiya?” Harira ta saki dariya jin an kira ta da “Aunty”, ta juyo, “Lafiya kalau Hansatu, ya karfin jikin?” Na warware, ba inda ke min ciwo”. 

“Haka ake so, na kammala abincin kari ina zani-kai muku?” “Me ya sa ba ki jira ni na zo mun yi tare ba? fiya ma haka ki yi girki ke kadai”. Murmushi Harira ta yi, a ranta ta ce, “Mene ne amfanina?” A fili kuma ta ce, “Kina fama da rashin lafiya zanisa ki aiki Www.bankinhausanovels.com.ng Hansatu?” To na warke. Yanzu tare za mu dinga yi, ki yi shara, wanke-wanke da sauran ayyuka, ki bar min girki”. “Shi kenan Hansatu, tunda haka kinka bida. Zo ki gani, ashe gidan cike yake da kayan abinci, firinji cikke da nama da kihi har da markadadden kayan miya bokiti guda’”Hafsat ta idasa shiga kicin din suna dubawa tana sanya wa Mammah albarka cikin zuciyarta. Ita ta kwashe tangarayen da Harira ta zuba soyayyen dankali da Agada (plaintain) da farfesun kayan ciki ta kai kan kyakkyawan ‘dining table’ wanda aka yi wa muhalli a can wata kusurwa ta falon. Ta dawo ta dauki flask din shayi da tea cups da kayan hadin shayin duka ta jera su a dining ta samu wuri a daya daga jerin kujerun falon ta zauna. T.V ta ke son kunnawa, ba ta san ya za ta jona ta ba, sai ga shi ya fito rike da gown dinshi a hannu (bakar rigar lauyoyi) da wig a kansa (hular lauyoyi) yana tsuke tie din wuyansa. Gabadaya falon ya gauraye da kamshin masculine _turarensa (Creed Aventus) har Hafsat ta ji turaren jikinta ba kamshi yake ba. Kafafunsa cikin (black covers) kirar Italy sai shining suke yana takun nan nasa gab-gab-gab shi ba sauri ba, shi ba tafiya a hankali ba. Idanu suka hada sosai, dukkansu sai suka dauke kai cikin ko’in’kula. Ita ta fara dauke idonta ta mayar wani gefen, wata hudubar Mammah ta fado mata tun tana karama, ‘Duk inda ki ka ga babba ki gaishe shi ko da da shekara ya girme miki ”. Sakamakon hakan sai ta samu kanta da zamowa daga cikin kujerar da ta ke zaune cikin nutsuwa bakinta ya ambato kalmar, “Sabahul khair”. Da accent dinta mai taushi. 

Barrister Abdul’azeez Dakata ya mirgina kai ya amsa a ginshire, “Lafiya lau”. 

Ya ci gaba da tafiya a falon zai fice. Hafsat ta samu kanta da cewa, “Ga abincin karin kumallo”. Cikin harshenta na Brussels. Sai bayan ta fada ta shiga cikin nadama da juyayin wa ya aike ta? Bai ce ta shiga rayuwarsa ba a rayuwar auren da ya shirya musu. Amma ga mamakinta sai ya ba ta amsa da turanci, don shi ba wai ya kware a yaren nasu ba ne, amma yana ji. Don su Isma’el suna yi yana ji. 

“Na makara, amma a sanya a basket a sa min a mota”. (Yadda mahaifiyarsa ke masa kenan idan ya makara) Www.bankinhausanovels.com.ng 

Cikin nutsuwa ta mike ta shiga madafin ta dauko (food-basket) sabo fil ta dauko kanan food flasks masu kyau ta fito ta juye kowanne a flask daya. Ta dauki filas din ruwan zafi zata saka cikin basket din sai ya ce, “Bar wannan, inada kettle ina shan (coffee) a office”Kanta a kasa ta ce, “Toh”. Ya fice, ta bi bayansa tana dauke da kwandon. 

A jikin kofar motar ta tsaya ya bude ya shiga, sannan ya mika hannu ya bude (lock) din kujerar baya ta sanya ‘basket’ din. Sai ya ce mata, 

“Thank you”. Ya rufo kofar. Juyawa ta yi ta koma, shi kuma ya murza kan sityarin motarsa kirar (GMC) ya yi reverse Danfulani ya bude masa kofa ya fice. 

Kicin ta leka ta tadda Harira a ‘dining’ din kicin din tana karyawa, ta gyare ko’ina tsaf. Sannu da aiki Anty Harira, ki dinga zuba wa maigadin gidan nan abinci don Allah”. Harira ta ce, “Ba sai kin fada ba, na ba shi tun dazu’. Tace, “Ok”. 

Falo ta koma wajen kayan wuta ta yi ta kokari har ta jona T.V ta zauna da remote a hannunta, har ta nemo wata tashar Larabawa suna girkegirken kasar Turkiya da yadda ake sarrafa su. Sosai abin ya dauki hankalinta. Sai ta ji sha’awar gwada abin da suke koyarwa don haka ta shiga dakinta ta samo jotter da biro ta soma (jottingdown) daki-daki yadda za ta gane. Wani irin tsire suke nuna yadda ake yi na nikakken nama mai suna ( adana kebabi) da recipe din, a zuciyarta tana fadin ta samu abin yi yau, za ta gwada suci ita da Anty Harira. Sai wajen sha daya na safe ta kashe T.Vn ta leka kicin, Harira ba ta nan ta wuce dakinta. Nan ta hau hada kayan girkin da za ta bukata. Kafin karfe biyu na rana gidan ya gauraye da ni’imtaccen kamshin tsiren mutanen Turkiya. Ta kwashe shi daga oven ta zauna a nan dining din cikin kicin tana ci. Bayan ta dibarwa Harira. 

Kwana biyu ta sake yi don na farko yayi mata dadi. Harira ma wuni tayi tana santin tsiren, tana zaune a kicin tanaci tana tunani. Tunda ta zo yau kwana biyu ba ta yi magana da Mammah da su Isma’el ba, sosai ta ke cikin kewarsu. Ga shi ba ta da waya, ko sanda ta ke gida ba ta rike waya ko Www.bankinhausanovels.com.ng 

da wa za ta yi magana da wayar Mammah ta ke yi. Tana wannan tunanin tana kai lomar ‘ adana kebab’ dinta ba ta ankara ba sai ganin giftawar mutum ta yi har ta so ta tsorata. Da sauri ta waiwaya, Abdul’azeez ne. Kai tsaye ya wuce ga firji ya bude ya dauko gorar ruwan Faro mai sanyi ya bincire murfin ya kafa a bakinsa ya ringa kwankwada, sanyi da gardin ruwan na ratsawa har cikin kwakwalwarsa yana wanke gajiya da zafin da kwakwalwar ta kwaso. Ta dauke kai daga kallonsa yayin da ta sauke wata siririyar ajiyar zuciya, ina ma za ta iya? Da ta roke shi ya ara mata wayarsa ta kira Mammah da Baba Azumi da Yayanta Isma’el Dakata mazaunin kasar Amurka ko ta ji dadin zuciyarta daga matsewar da ta yi mata wuri guda sabida kewarsu. 

Wannan aure jinsa ta ke tamkar an kawo ta kurkuku, ya yanke alakarta da kowa nata, Mamanta ba ta kara bi ta kanta ba, miji kamar mala’ika kullum fuska babu walwala, in yasa kafa ya fice sai goshin maghriba yake shigowa gidan daga nan bata kara ganinsa sai wayewar gari in ya fito don tafiya office , in sun bashi abinci yana karba, in ta gaishe shi zai amsa, bayan wannan ba wata kalma dake kara hadasu, da alama ba ya son bude ido ya ga fuskarta, watakila bayan rashin so ita mummuna ce. Ita ma ba so ta ke ya so ta ba, amma akalla ya bude kofar da aurensa ya rufe mata na datse alaka tsakaninta da kowa nata. Ji ta yi idanunta sun cicciko da kwalla kafin ta yi aune kwallar ta zubo, sharr! Da sauri ta sa bayan hannunta tana sharewa. Har ya wuce ya 

bar kicin din yana mamakin me ya yi mata ya sanya ta kuka? Daga kawai ya shigo kitchen? Watakila ba ta son ganinsa ne, in ba haka ba shi bai ga laifin da ya yi mata ba. Alkawururrukan da ya daukar mata tun a yau har ya fara kokarin cika su. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ci gaba ta yi da cin abincinta tana hawaye, a haka Harira ta cimmata. Wai Abdul’azeez ya ce a sanya mishi abinci a mota zai koma ofis. Nuna mata inda ta zuba masa abincin ta yi da hannunta, har tsiren ta zuba masa mai yawa, ba ta so ta yi magana Harira ta gane kuka ta ke yi. Ta manta cewa gaba take da ita. Murmushi Harira ta yi, ta ce. Ki kai masa da kanki Hansatu, ki yi hakuri kin ji?” Wannan Hansatun da Harira ke kiranta da shi dariya yake bata, amma yau haushi ya bata. Ba ta ce komai ba ta mike ta dauki basket din ta fita.Yana cikin motar har ya kunnata ya rufe kofar da alama ita yake jira, ba ta yi masa magana ba ta bude kujerar gaba ta ajiye kwandon ta rufe kofar. Ya ja motarsa da hanzari ya bar harabar gidan, daman mantuwa ya yi ya dawo, amma ba al’adarsa ba ce dawowa gida cin abincin rana ba. Abin da ya tarar tana ci ne ya ba shi sha’awa har ya ce a ba shi abincin. Rayuwar amarya Hafsat-Suhaana da angon ta Abdul’azeez Dakata kenan a gidan aurensu har tsayin sati biyu. Za ta yi girki sau uku a rana, kuma babu wanda ba ya ci, na safe zai fita da shi, na rana da ba ya samun sukunin dawowa zai turo direban ofishinsu ya daukar masa, na dare kuma in ya dawo masallacin unguwarsu sallar isha’i zai ganshi a dining ya zauna ya ci. Weakness dinsa kenan (abinci) kuma da a ce Hafsat na da wayo da ta dade da gane hakan. Ba ya son abincin sayarwa sai ta kama dole. Sanda yake (schooling) shi yake dafawa kansa. Da ya tafi ‘Law-school’ daga gidansu Mu’azatu ake bashi. Da ya gama ya dawo gida mahaifiyarshi ta sangarce shi da dadadan girke-girkenta wadanda dandanonsu yanzu ya yi masa daidai da wanda Addarta ke bashi, wanda ke nuna ko dai ta koya ne a wajenta, ko kuma tare suke yi. (Kallon farko da yake yi mata na sangartacciya, 

ya soma gogewa). Yau yana (office) da la’asar ya samu wayar Mammah, ta ce da ya dawo ya dauko Harira da kayanta ya kawo mata ita za ta koma Www.bankinhausanovels.com.ng Sokoto. Mijinta yayi waya ta koma. Muryarsa ta nuna damuwa a sa’ilin da yake cewa. “Mammah da kin bashi hakuri zuwa gaba kadan, na ga alama suna jin dadin zama da junansu, kin ga ni in na fita tun safe sai karfe shida nake komawa gidan, tana debe mata kewa”. Mammah a dan hasale ta ce, “Sanda na kawo ta kai ka ba ni shawara? Ko kuwa mace da aurenta sai ta dawo gidanku da zama ta bar aurenta?” 

Ya yi murmushi, “A’ah, ba ni ba ne, kuma ai dama ba nufina ta dawo kwatakwata ba kamar two months haka, lokacin ta saba”To yanzu ma ban nemi shawararka ba, ka dauko ta ka kawo min ita na ce, in ka ga dama ka kwana ba ka koma gidan ba, ai zaman aure ne muma da haka muka saba a namu gidajen’”’. 

“Za a yi yadda ki ka ce Mammah”. Ta kashe wayarta, ya ajiye tashi a gefe cikin zuciyarsa yana jinjina rigima kala-kala irin ta mahaifiyarsu. A nata bangaren Hajiya Maryam Hamza Dakata murmushi ta yi tana rike da wayar a hannunta, ta dubi Daddy da ke gefenta ta gaya masa yadda suka yi da Abdul’azeez. Ya ajiye takardun dalibansa da yake (marking) ya dube ta sosai. “To ke me ya sa za ki raba su da mai aikin? Na san ba wata waya da mijinta yayi don naji Azumin na gaya miki ya tafi fatauci ne Shagamu. Rigima ce kawai irin taki ” 

Ta gyara zamanta tana fuskantarsa ta ce, “Daddy, daga baya ne na fahimci na yi kuskure da na tura ta. Ba aure irin na Adda da Abdul’azeez ake sanyawa ‘third-party’ ba, in hakan ta kasance ba za su yi irin shakuwar da nake so su yi ba. Miji na tausaya wa matarsa in ya ga hidimar gida da ta abincinsa ta yi mata yawa, har ya yi marmarin dauke mata wasu hidindimun idan ya san cewa ya barta a gida tun safe har yamma ita kadai, zai fi damuwa da komawa gida cikin lokaci ya ga halin da ta ke ciki, ko ya dinga kiranta a waya sabanin in ya san akwai wani tare da ita”Jinjina kai Daddy ya yi, ya ci gaba ‘marking’ dinsa yana mamakin Maryam, ya ce, “To sai yaushe kuma za ki barmu mu je mu gansu, nace in bazaki ba ni zani kin hanani, ko ki kira ta a waya ki ji lafiyarta? Allah Www.bankinhausanovels.com.ng kadai ya san yadda take cikin damuwa da wannan takunkumin naki”A nan kuma dariya ta yi, ta kafe shi da kyawawan idanunta, “Manta da su Daddy. Sai ranar da Abdul’azeez a kan karan-karansa ya ga ya dace ya saya wa Suhaana waya. Mu kuwa sai ta shekara zamu je”. 

******

Zaune ta ke a kan sallayarta bayan idar da sallar isha tana jan cazbaharta cikin istigfari, ta jiyo sallamar Harira daga bakin kofa. Juyawa ta yi suka hada ido, ta ganta ta sha lullubi dauke da katuwar (Ghana must go) dinta. Da sauri ta karashe lazimin ta shafa addu’ar cikin kulawa ta ce, “Aunty Harira ya ya dai?” Tana mata kallon mamaki. 

Harira ta rausayar da kai, “Hansatu Allah ya sada mu da alkhairi, zan koma gidan Mammanku ta turo a dauke ni”. Gaban Hafsat ne ya bada wani irin damm! Zuciyarta wadda da ma a karye ta ke kullum ta sake karyewa. Rasa me za ta ce ta yi, Harira na ta yi mata addu’ar fatan alheri, da zaman lafiya ita da mijinta ba ta iya ta amsa ba, sai jin (horn) din Abdul’azeez suka yi, wanda ya sa Harira sungumar jakarta ta wuce. Wani kuzari ya shige ta da ta tuna watakila rabuwarsu kenan har abada, ya kamata ta yi mata alheri ko ya ya ne, domin hakika ta ji dadin zama da Harira, mace mai saukin kai da sanin yakamata, mara shisshigi da sa’ido. Ta dade da fahimtar zaman da ta ke yi da mijinta ba zama ne na soyayya ba, amma ko da wasa bata taba tambayarta wani abu a kai ba. Kokari ta ke ta sanya ta a hanyar yadda za ta kyautatawa Abdul’azeez ko ba zai kula ta ba. Kullum sai ta tsaya ta ga sun shirya masa abinci sau uku a rana, mai rai da lafiya. In zai fita sai ta ce, ta raka shi da (basket) din karin kumallonsa, haka in ya dawo za ta ce ta fita ta kwaso kwanukan daga bayan motarsa, ta yi masa Www.bankinhausanovels.com.ng sannu da zuwa ko ranta ba ya so. Girki kawai ta sani, sai wanka da tsaftar jikinta, amma gyaran gida Harira ce. In ta ce ba za ta yi kewarta ba, ko ba ta ji dadin zama da ita ba, to tabbas ta yi karya ta kwana da yunwa. Idanunta babu dalili ma kawo kwalla suke yi, balle yau ta yi dalili. Da hanzari ta mike ta bude (wardrove) dinta. Manyan turamen atamfofin (Vlisco) ta kwaso har guda biyar da sinkin sabulai guda goma ta watsa a katuwar leda ta bi ta da su da sauri. Har ya tada motar ya yi reverse ya hango fitowarta da gudu-gudu ta madubi. Ya dan dakata har ta cimmasu. Bude kofar motar ta yi ta azawa Harira a cinya, sai ga hawayen sun zubo. 

Harira kanta daurewa ta ke yi, amma idanunta sun kada sun yi jazir. Ta daure ta kama hannun Hafsat ta ce, To me ye na kuka Hansatu na? Ai ana tare, Baba Azumi ta riga ta hada mu. Na yi miki alkawarin in ki ka haihu ni zan zo in yi miki jego, ke dai ki yi kokari kafin shekara mai zuwa ki haiho min santalelen ango ko kawa mai kirki kamarki, kin ji?” 

Kokarin jan motarsa ya soma don sun soma ba shi haushi. Maganganun Harira sun yi masa wani iri, Sai ya ji kamar da shi ta ke. Hafsat ta ja baya ta rufe mata kofar ya fizgi motar da gudu. Bashakka da cikin kasa ne da ya bule ta da kura, sai aka yi sa’a kananan fararen duwatsu ne shimfide da harabar gidan bakidayanta. Ciki ta koma ta fada gadonta tana kuka riris, kuka mai dalilai da yawa. Mammah ta daina sonta ne? Isma’el, Usman da Halim ma? Baba Azumi ma? Tunda Mammah ta yi mata aure kuma shi kenan ta rabu da ita? Auren da ta tabbatar ba dadinsa ta ke ji ba. ‘Yar Harirar da ta bata tana debe mata kewa ta dauke abarta duk don a takura WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG ta a nuna mata yanzu ba mai sonta? Ya ya Za ta yi rayuwa a gidan nan daga ita sai Abdul’azeez din da shara ta fita daraja a idonsa? “Ya Allah ka kawo min sauki ni Hafsatu, idan kuma mutuwa za ta fi min sauki ka gaggauta daukar raina in huta da zaman gidan nan”. Hafsat ta fada a fili. 

*********

Kusan kwanan da ta yi tana kuka shi ya sa washegari ta makara, don bayan ta idar da sallar asubah a nan kan sallayar barci ya sake yin awon gaba da ita. Ba ita ta farka ba sai bakwai da rabi, kuma lokacin ne Abdul’azeez ya ke tafiya aiki. Salati ta yi ta mike da ta dubi agogo ta fada toilet ta rage mararta ta wanko bakinta ta fito falo don wucewa kicin ta gani ko akwai abin da za ta iya ba shi na gaggawa duk da ta san da kyar ne in bai 

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *