AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 10 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
She is no longer the Hafsat he know mai son kyautata masa da neman kulawarsa ta kowacce fuska. Har in bata samu hakan ba ta shiga wani hali. Wannan kallo daya zaka yi mata ka fahimci so kawai ta ke ya tashi a wurinnan ya rabu da ita, ya kyale ta ya fita daga rayuwarta, zamansa tare da ita a yau ya takura ta (ba kamar wancan zamanin ba da babu abinda take so irin ta ganshi a kusa da ita by her side koda ba hira suke yi ba).Ko bata furta hakan ba an ce labarin zuciya a tambayi fuska . Idanuwan ta sun fada, yanayin ta bakidaya ya nuna. Wani abu da shi kuma bai shirya wa a yanzun ba, daga nan har gaban abada (wato fita daga sabgar tata).
Gyara zamansa ya yi ya kamo habarta da hannunsa na dama, a kokarinsa na son su dubi juna for the first time don yana tantamar anya Hafsat din da ya sani ce wannan? Amma maimakon hakan Hafsat sai ta rufe idanunta gabadaya, the long eye-lashes suka bi idon suka kwanta duk da a jike suke da hawaye. Rufe idon da ya birkita shi sai jin saukar harshensa ta yi saman fuskarta yana dauke hawayen da ke zuba, al’amarin da ya rikita Hafsat ya soma kwace duk wasu makaman yakinta, amma a hakan kokari ta ke ta nuna bijirewarta,
hankalinta in ya yi dubu ya tashi da ta tuna babu aure ko na kwangilar a tsakaninsu, ta kuma bude dukkan idanunta ta dube shi. Sai da ta gwammace ba ta bude idon ba don gaba daya kwayar idon Abdul’azeez tsoro ta bata, bata taba ganin sa cikin wannan halin ba _ (lasciviousness) zallah a cikinsu irin wadda bata taba gani daga gare shi ba. Baya ta yi da karfi ya riko ta.“Kada ki bari ta kai mu da haka Hafsah…., kada ki bari in sa miki karfi. Na ce na maida ke, ba tun yau ba Hafsah… kina nan a matsayin matata da amincewar kowa ko babu, and I need my wife NOW! ” Www.bankinhausanovels.com.ng
Sarai ta fahimci manufar Abdul’azeez cikin kwayan idanunsa kadai koda bai janye duk wani hijabi dake tsakaninsu a yau ya furta da bakinsa ba.Hafsat ta fahimci ‘ kuka ’ dinta, ko karfinta bai isa ya raba ta da Abdul’azeez a yau ba, ko daga irin rikon da yayi mata, ta soma tunano abin da zai iya faruwa in ta barshi ya rinjaye ta. The worst thing kusancinsu ga iyayensu, ga ta ga Mammah, sannan auren ma duk da yace ya mayar ita bata yarda da sahihanci da ingancinsa ba, ta fi yadda da gurbatacce ne tun wa’azin data ji a rediyo shekaranjiya akan yin yarjejeniya a cikin aure. Sai ta soma roko muryarta na shaking ba tare dasanin hakan kara triggering din shi yake yi ba. Ta kankame jikinta wuri guda ganin kamar baisan ma tana yi ba lamarin kara girmama yake yi, kafin da azama ta mike tsaye, muryarta na karkarwa hadi da jikinta gabadaya ta soma maganar da ba ta yi niyya ba tana hawaye.
“Yaya Azeez me ya sa haka don Allah? I’m no longer your wife . Kuma a gidanmu? Na hada ka da Allah ka tafi, ka yi hakuri na yi maka alkawarin zan saurare ka da duk abin da ka zo da shi, amma ba yau ba…….”.
Daga inda ta barshi zaune a kasa ba sauran kuzari ko na cikin cokali a tare da shi ya daga jikakkun idanunsa ya dube ta, tayi azamar sunkuyar da kanta.
“Then let me hug you properly Hafsabh ….. Ba zan yi wani abun bayan hakan ba __I promised .I just want to be closer to you again , in tabbatar I’m not that far from you….”.Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba yadda ta iya, tana ji kumatana gani ya mike, da wani irin rawar jiki ya rungume ta. Wata irin tight runguma tamkar zai tsaga zuciyarsa ya sanyata ciki don tsoron kada wani abu wai shi ‘rabuwa’ ya sakegittawa a tsakanin su. Wanda ya tabbatar target din iyayensa kenan bazasu taba sauraron sa ba. Babu wani uzri da zai kawo da zai yi tasiri a zukatansu. Hafsat din dama ita ce hope dinsa gata itama yau ta bashi mamaki, alamu sun nuna ko a da tana son sa kamar yadda ya dade da fahimta to yanzu ta daina son sa.Kanta na tsakiyar kirjinsa duk suka yi shiru, basa komai sai sauraron bugun zuciyar junansu. Kowanne
Tunanin da yake daban ne amma akan dan uwansa ne. Ita dai Hafsat a nata bangaren, Mu’azatu ce a kahon zuciyarta, ta tsaya mata a makogaro ta ki wucewa da wani irin kishi mai tsanani wanda ya sababba mata tsanar Abdul’azeez din baki daya don sanin irin zurfin son da ya ke mata. How could she live with a husband like him zuciyarsa na ga watanta? Abinda ta jura a baya ko kusa bazata iya jurar rabin-rabin sa yanzu ba saboda ta fara sanin ciwon kanta, don haka maganar su mayar da wannan gallababben auren a gareta ma bata taso ba ta je ta cigaba da kwankwadar bakin cikin Mu’azatu.Sai dai a yadda ya zo yau ya soma sanya shakku a zuciyarta could all these be fake ? Ana karya da emotion na zuciya da gangar jiki kuwa? Bai taba zama irin yau a gare ta ba. Jikinsa kansa wani irin rawa yake da ya samu ya rungumetan yadda ya bukata. To ina ya kai Mu’azatun? Fatanta dai a yanzu ya tafi, kada wani ya ji motsinsu a gidan nan ina za ta sanya kanta? Ina alkawarin da ta yi wa Daddy? Www.bankinhausanovels.com.ng
Zamewa ta yi daga jikinsa ta isa ga ‘wardrove’ ta fiddo doguwar riga da sauri ta sanya, saboda rikicewa a baibai ta sanya rigar. Ta dade da manta cewatawul ne kawai a jikinta. Koda suke auren ai bai taba kare mata kallo haka ba sai yau da batasan sunan auren nasu ba? Gashin kanta tarwatse a kafadunta duk ya hargitse, duk yana tsayeinda ta barshi yana kallonta daga ya koma bisa gadonta ya kishingide. Yadda ta ke yin komai a gaggauce ga hawaye na bulbula duk sai ta bashi tausayi. Please go Yaya Azeez… help me and go”. Ya kalli cikin idanunta ya lumshe mata lumsassun idanuwansa. “i will go Hafsah, but on one condition; switch on your phone”.
Ta sa bayan hannunta ta share idonta, a kagare ta ce. “Tana hannun Daddy?”’
Hannu ya zura cikin aljihun sassalkarmakubar shadda getzner da ke jikinsa wadda zuwa yanzu duk tayi squeezing ya fiddo babbar wayarsa ya mika mata. “ Use mine, I will call you tonight’. ( Yi amfani da tawa, zan kiraki cikin dare).
Karasowa ta yi tsakiyar dakin inda yake zaune a kan ‘rug’ ta mika hannu don ta karba ba wai don ta amince wa zuciyarta za ta yi abin da ya ce din ba, a’ah sai don ta samu ya tafi. Amma sai ya hada hannun nata da wayar ya janyo ta ta fado bisa cinyoyinsa. Hannayensa ya sa ya zagaye ta ya kwantar da kai bisa kafadarta, da muryar da a yanzu shi kansa ya ke tantamar kasantuwarta mallakinsa ya sake maimaita tambayar da yayi mata tun farkon shigowarsa dakin bata bashi amsa ba.
“Hafsah are we still friends?”
Rufe idanunta ta yi, cikin kokawa da numfashi hadi datsokar naman da ke cikin kirjinta (zuciya), wadda ke yi mata wani irin kai-kawo da sabon son Abdul’ azeez data binne da ransa ya taso bakidaya ya soma yabanya. Girgiza kai ta yi kai tsaye cikin rawar murya ta ce. “No, we are not”. “Ko da nace I’m sorry Hafsah ?” Mikewa ta yi da niyyar gudu ya sake fizgo ta, ya kankame ta cikin jikinsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
‘“Dubi yadda na zama Hafsah saboda rashinki,
ko abinci ba na ci, bana iya aiki a ofis, bana iya
shiga court , ba na barci Hafsah, ban san na aikata kuskure mafi muni ga rayuwa ta ba sai na ranar da na dawo daga Jimeta babu ke a gidan Hafsah! Sometimes our mistakes serves as an instrument of improving our imperfections and shortcomings. Daddy da Mammah sun shirya azabtar da ni a kan kuskurena Hafsah, amma in muka hada kai muka nuna musu muna son juna dole su kyalemu mu koma aurenmu. In sun ki Hafsat zan basu mamaki; sai dai nima in dawo nan mu zauna tare, amma komai mai sauki ne in kina bayana. Na rantse miki ba irin rayuwar da mukayi zamu maimaita ba ki daina tunanin komai ki dauke shi biyoni . Ki tausayawa Abdul’azeez dinki, ba shi da kowa yanzu a gidan nan daga Allah sai ke.
Duk wasu kalamai na namiji mai hikima Abdul’azeez ya yi amfani da su yau a kunnen Hafsat don ya wanke laifinsa, tare da jaddada mata babu wata mace a zuciyarsa sai ita. Mace mai rauni da saurin karaya, hadi da kasancewar zuciyar ta riga tanarke tayi raga-raga a soyayya na lokaci mai tsawo ba tareda ta samu martani ba. Yau har abinda mafarkinta bai taba bata ba Abdul’ azeez ya gaya mata. Tuni ta mance da wata Mu’ azatu, kashedin Daddy da duk batancin da Abdul’ azeez ya yi mata.Ta nemi duka makaman yakinta ta rasa duk kuwa da yadda tayi musu kyakkyawan riko a baya.Wadannan kalaman na Abdul’ azeez na ‘yan mintoci sun wanke duk wasu kasurguman laifukan sa da ta dade tana kallonsa dasu. A karshe ya ce mata aurensu yana nan ba abinda ya same shi tunda dama saki daya yayi,kuma tun tana Jimeta ya maida ta. Ta kashe waya saboda shi da tuni ya gaya mata. Amma zai kara bincike
a wurin malamai shima. Wadannan sauran igiyoyin biyu kuma zai kiyaye su yadda zai kiyaye ransa till eternity! Www.bankinhausanovels.com.ng
Tana so ta tambaye shi zancen Mu’azatu ba ta so ta bata wannan mood din da suke ciki. Wanda tsayin a shekara guda da watanninda suka yi gida daya basu taba kasancewa a cikin kwatankwacin irinsa ba. Kuma bata so ta bude baki tayi magana yaji kalaman bakinta kada ya ga hucewarta da yawa.Don haka ba ta dai ce komai ba, amma labarin zuciya a tambayi fuska. A fuskarta ya ga sassauci,kuma a kwayar idanunta yaga soyayyardake zuciyarta da yayi zaton tayi expire na regaining gradually (farfadowa a hankali). Tashi ta yi daga jikinsa ta koma gefen gado ta zauna. Mikewa ya yi ya kawo mata wayar har inda ta koma tazauna din. Ta karba ta ajiye a gefe ba tare da ta dube shi ba, ta ce. “ Please go, it’s almost past twelve Yaya Azeez”.
Za ka iya karanto damuwar da zamansa har wannan lokacin a dakin ya jefa ta a sautin muryarta kuma zaka iya gani akan kyakkyawar fuskarta karara. Kanta ya zo ya tsaya ya zuba hannayensa duka cikin aljihun kaftaninsa ya ce. “ I will . Amma me zan samu daga amaryata Hafsah da zai sa in yi barci mai dadi a yau?” Tsuke baki ta yi, sannan ta yi kicin-kicin da fuska, ta soma kunkuninta. Bakomai take cewa cikin kunkunin nata ba banda (nidai don Allah ka tafi)ya kasa jin me take cewa. Lebunanta biyu ya kama na sama dana kasa da yatsunsa biyu da babban yatsan sa iham da dan ali sabbab ya matse da karfi. Hannu ta kai ta doke hannunsa. Da mamaki yace. “Hafsah!!!”
Ta ce a kumbure. “Na’am”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ni ki ke bugewa?” Bata yi niyyar magana ba amma ta san halin sa sarai abu kadan zai ce ta masa rashin kunya koda shine bashi da gaskiya. Idonta ya cicciko da kwallah tace. To ba kai ne ba? Gashi ka kumbura min lebe. I just want you to go”. Kugunsa ya kama da dukkan hannayensa daga tsaye yana dubanta da wata irin siga. Idan na ki fa?” “T will not use your phone”. Ta amsa da sauri . Ok, lemme go now!” .
Ya ci gaba da tsayuwar kuma, yana kallon ta kamar ya hadiye ta.
Dafe kanta ta yi, sabida tsayuwar tasa a kanta na making dinta unease . Kanta har ya fara sarawa.
“Hafsah!” Ya sake kiranta, wannan karon sigar kiran da tasirinsa tun daga kwakwalwarta har yatsun kafarta.
Dagowa ta yi a hankali ta dube shi da rinannun idanunta.Sai dai kuma bata jima ba da dagowar da sauri ta maida kanta kasa. Bai taba yi mata wannan deep and lingering look din ba. Kamar yadda ya ce din ne, ‘he just need his wife’ ta ga hakan a kwayar idanunsa. Hafsat ta yarda in ba ta lallaba Yaya Azeez ya tafi ba yau zai kwanan mata a daki, ya hada ta da abin kunyar da ba ta da inda za ta kai nauyinsa. “Yaya Azeez don Allah ka tafi, call me as soon ka isa gida, we will talk about it” . Ta fada cikin sanyin murya, wadda ke nuna babu fushinsa a zuciyarta. Tsugunnawa ya yi ya dafa gwiwoyinta da hannayensa biyu. “Tunani nake Hafsah ko na je gidan wahala zan sha. Damuwa bazata barni inyi barci ba. Yau so nake na zama mijin Hafsah na hagqigah , ta yadda zan bar ma Mammah tabon da ba za ta iya raba mu ba. But I’m not sure and I’m afraid ko auren ya maidu ko bai maidu ba, wannan shine damuwata Hafsah. Yanzu za ta iya raba mu easily (asaukake)tunda ban tabbatar da aurena ba, babu iddata akanki’’. Magana yake da muryar da bai taba yi wa wata diya mace magana da irinta ba. Ita kanta Hafsan da ake yi wa maganar kunya ta jefa ta kuma ba sosai take jin ta ba. Abdul’azeez ya kai hannu ya dago_ habarta, runtse idanunta ta yi saboda har gobe wannan respect din da ta ke ganin Abdul’azeez da shi na babban Yayansu yana nan ba abinda ya Www.bankinhausanovels.com.ng canza, aka zo aka kara nauyin aure akan wancan. Yau kuma ga shi ya sanya ta a gaba yana gaya mata maganganun da suka fi karfin hankalinta. Kwantar da kanshi ya yi a cinyoyinta abin da ya kara ninka kunyar tata.“ Please Hafsah tell Mammah you love your husband ko da ba kya sona. I will make sure I made it realistic, I will teach you how to, balle ma na san kina sona tuntuni ko Hafsah? Ba za ki hukunta Yayanki a kan kuskurensa ba, bazaki duba baya ba gaba kawai zaki kalla ko? Kin min uzuri mai yawa a cikin zamanmu, ina rokon ki kara min da wannan ko da shi ne zai zama na karshe. Ki kula da wayar, ki barta a jikinki, a vibration ”’. Ta ce. “Toh!”. Dasauri, don dai ta samu ya tafi. Ya mike a kasalance, ya zura hannayensa cikin aljihun wandonsa. Ya soma takawa zai fice, sai kuma ya juyo.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG