AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 12 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 12 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 



MUN TSAYA

Cikin idanu Abdulkarim Dakata ke kallon jikan nasa, yana karanto zahirin abin da ke zuciyarshi ne zallah yake amayarwa. Ya amince gaskiyar zuciyarsa kawai yake gaya masa kuma Dr. Hamza bai gaya masa gaskiyar yadda ta kaya zuwansa Lagos wajen Attorney General ba. A matsayinsa na babba, tuni ya gano dalilin Dr. Hamza. Ya ce. “A kan me ka saki matarka?” Abdul’ azeez bai zaci wannan tambayar ba, don haka sosai ta ruda shi, ya hau kame-kame, abin da Abdulkarim Dakata ya tsinta cikin kame-ka

men nasa kawai shi ne; seeees Wallahi ba don bana sonta ba ne!!!”

Ya tausasa murya ya ce.

“Abdul’azeez, sai na san matsalarka gabadaya zan iya dosar mahaifinka. Ka tuna ba ni na haifar masa kai ba balle in tursasa shi kan duk hukuncin da ya yiwa rayuwarka. Feel free to discuss your problem with your junior grandpa. I’m at a door to help”

.

Hakan ne ya sanya wata irin nutsuwa da aminci cikin zuciyarsa. Ya samu kansa da warware wa Abdulkarim Dakata komai tun haduwarsa da Mu’ azatu, fitinannen son da ya samu zuciyarsa da yi mata rana daya bayan da in the first place mutuncin Babanta ya sa yake kula ta. Amma shi a a ransa ya san da farko ba son ta yake ba. Yanada buri mai yawa akan karatu da ya shafe masa tunanin soyayya ko yin aure a lokacin.Kuma ya sanar da Mu’azatu hakan amma rana daya ya samu kansa in ba aurenta yayi ba bazai taba nutsuwa ba. Kawo zancen Hafsat da Mammah ta yi masa rana daya, tunanin hanyoyin gujewa auren da ya yi ta yi ya rasa, don tsira da Mu’azatu. A karshe ya ga babu mafita (don Mammah ba da wasa ta dauki al’amarin ba) ban da ya nemi Hafsat su yi auren a kan yarjejeniya na zaman auren shekara daya da watanni daidai da lokacin da Mu’azatu zata gama law-school. Ya gaya masa tubalan da aka gina yarjejeniyar akai daidai da burin kowannensu. Ya dan yi shiru, kansa na kasa (feeling guilty). Tsohonminista Abdulkarim ya saki baki, hanci da ido yana jin wauta da kuruciya zallarta hadi da shiga hurumin Ubangiji duk saboda soyayyah . Ya ce a ransa‘to ita Mu’azatun da dia Www.bankinhausanovels.com.ng

mond aka kerata da dole sai an aure ta ko ta halin kaka?” Abdul’azeez ya kara sunkuyar da kansa cikin jin nauyin abin da zai fada.

“Uncle a cikin watanni na shidda da auren ne muka fara gane shayi ruwa ne daga ni har ita, don ita ma Hafsat na fara gane ta fara yi min soyayya irin ta kowacce mace ga mijinta, na ki ba ta dama ne ta nuna min don a ganina ta yi kankata da yin hakan. Ba a dade ba ni ma na soma experiencing sauyuka masu yawa a zuciyata a kanta. Na fara mancewa da Mu’azatu, muka zama _ kamar abokan juna, haka al’amarin ya ci gaba da rikidewa and this is where it landed me today .

Uncle kafin na saki Hafsat na yi nazari mai yawa, na tuna girman alkawari, amma ba don soyayyar Mu’azatu ta yi min yawan da ba zan iya hakura da ita ba. I just want to be out of hypocrates masu baki biyu. Ina so in cika alkawarin da na dauka ga Mu’azatu. Sai da na riga na sanya takardar a jakarta na soma regretting cewa abin da ya kamata in yi shi ne, in nemi fatawar malamai ba sakin ba.
Www.bankinhausanovels.com.ng
A garin iyayenta na yi niyyar karbe takardar ban samu ganinta ba, not even by phone , wanda ya nuna ta ga sakon sakin. Da na dawo Abuja na yi niyyar komawa Jimeta in same ta mu kashe zancen a tsakaninmu, Daddy ya katse min hanzari da tafiya U.S kammala karatun su Ishma. Na sa a raina da na dawo zan je in dauko ta mu kashe zancen in karbe takardar. Lokaci bai ba ni dama ba! Komai ya bayyana ga Mammah, ta yi min mummunar fassara, ta yi fushi da ni mai tsanani. Uncle ko ganina ba ta son yi, ta hadu da hawan jini duk a kaina, na san ko yanzu na mutu wuta zan je a kan fushinta. But I don’t have the guts to explain sannan ta ki ta bani dama. Jiya na je na bai wa Hafsat hakuri, mun shirya kanmu. Amma yau sai maganar aure kawai Daddy ke min, wane irin aure ka ke ganin zan iya yi a halin da nake ciki yanzu? Wane dadi ne Mu’azatu za ta ji a taredani alhalin zuciyata, tunanina da farin cikina duka suna ga Hafsat da tunanin hanyar da zan bi in shawo kan mahaifiyata? Daddy na tunanin auren son raina ne da kwanciyar hankali a gare ni while it is absolutely not! Wannan wani abu ne da ya zama past ( bygone) a wajena. I’m now after my present and future. Please Uncle ka taimake ni a fasa auren nan. Ba abinda zai kara min sai damuwa da rudani. Zan yi rafkanuwa (kaffara) ta rashin auren Mu’azatu”. Ya karasa muryarsa na son nuna karewar karfin zuciyar da yake amfani da ita wajen yin bayanin.

Kawu Abdulkarim tausayi ya kama shi, kamar ya ce da shi “ba ka bukatar yin wata rafkanuwa , iyayenta sun hana ka”. Sai ya ga in ya yi hakan bai kyautawa Babansa ba. A yadda ya fahimta auren ma ya dage sai ya yi masa ne don ya hukunta shi. A lokacin da suka riga suka koyawa zuciyarsa ta so matarsa. Fada ya shiga yi masa sosai kan abin da ya yi watoauren yarjejeniya ya ce.

“Ko ba ka santa ba albarkacin rikon da mahaifiyarku ke mata ba za ka iya sanya ta a makaranta ka nemo mata danginta saboda Allah ba? Sai don ta amince ka sake ta bayan wani lokaci? Ka manta cewa yarinya ce karama bata da (clear conscience). Abdul’azeez ina iliminka? Yarjejeniya a cikin aure Haramun ne!!! Ni ma bana bayan a maida aurenka da Hafsat, ban yarda kana sonta ba. Idan kuma ta koma ka kara komawa wajen Mu’azatun fa?”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Wannan karon ya kasa daurewa, duk da yadda yake kokarin yin hakan kuwa. Hawaye ya soma ya ce. “Wallahi-wallahi Uncle idan Hafsat ta dawo ba ni ba Mu’ azatu, ba ita kadai ba har duka sauran ‘ya’ya mata ma. Ni kaina ina mamakin abubuwan da na dinga yi a kanta, bayan a can karkashin zuciyata ba wani damuwa na yi da lamarinta ba, my feeling on them is incomparable! Kawu Abdulkarim I believed i’m destined to be punished with her love for my misdeeds. Taimaka min in gyara komai; tsakanina da Ubangijina, tsakanina da mahaifina, tsakanina da mahaifiyata, tsakanina da matata. Taimakaminka fahimtar dasubabu wanda yake sama da aikata kuskure. Balle ni Dansu”.

Ba abin da Abdulkarim bai yarda da shi ba a kalamansa, amma dole su kara ganar da shi kuskurensa don ya kiyaye a gaba, ya rike matarsa da daraja, ya daina daukar aure abin wasan yara.

“Tashi ka je na ji, zan nemi Ambassadan”’.

Appealing look (kallon roko) Abdul’azeez ke bin shi da shi, ya kauda kai saboda wani matsanancin tausayin yaron da ya shige shi. Abdul’azeez bai da niyyar tashi, sake gyara zama yake. Ya dan juyo ya dube shi da nutsuwa ya ce. “ Everything will be alright (komai zai zama daidai da yardar Allah).Amma fa tsakanina da Babanka, shine abokin zance na. Tsakaninka da Maryam kai da ita ne, wannan babu ni a ciki’”.

A marairaice Abdul’azeez ya ce. “Ba dai za ka bari a daura auren ba ko?” Yanayin muryarsa da helplessness din da ke cikinta ya baiwa Abdulka
rim dariya. Amma sai ya gintse ya ce. “Ai mun riga mun bada sadaki, ka ga babu dadi mu koma mu karbe ba tare da wani uzuri ba’.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Da sauri ya ce, “ Uncle I don’t want her in my life anymore (bana bukatar ta cikin rayuwata ko kankani). Ko kun daura zan saki’’.

Hararsa ya yi ya ce. “Saboda ka zama auri-saki ko?”

Sunkuyar da kai ya yi. “Ni ma ba so na bane in zama hakan, shi ya sa nake rokon kada a fara, da muguwar rawa gwamma kin tashi”’.

Murmushi Abdulkarim ya yi ya cire hular kansa ya ajiye a gefensa, ga tsilli-tsillin furfura nan ta fara baibaye kan irin ta Dr Hamza. Shida Dr. Hamza sa’anni ne tare sukayi wasan kasa duk da shi Abdulkarim yana matsayin kani ga mahaifinsa,ya dube shi cikin sigar zolaya.

“How could a man forget his first love so easily haka? (Ta yaya namiji zai mance soyayyarsa ta farko haka da sauki?) Na dauka nan ka zo gabana kana fadin in ba ita ba sai rijiya? Hafsat din akai kasuwa baka so? Is my grandson ‘loyal’ a cikin soyayyah? (Anya jikana amintacce ne a soyayyah)?”

Juyar da kansa ya yi wani barin daban, yana tuno tarin wautar da yayi, wai har Ishma ya bi yana roka ya auri Hafsat, ba don yaron mai hankali bane da tuni ya dade da daina gaisheshi, Uncle Abdulkarim kuwa bai san da me zai saka masa ba don ya tabbata ba don shi ba da rashin arzikin da zai yi wa iyayensa akan auren Hafsat yanada yawa duk akan mace, macen ma da ko asalin iyayenta bai sani ba, haduwar bariki kawai, babu wani abu na burgewa a tarbiyya da dabi’un ta. A hankalikamar mai yin rada, kamar baiso zancen ya fito ba ya ce.

“Uncle it is not love!”
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Mene ne to tsakaninka da ita in ba soyayyar gani kashe ni ba?”’Cikin hikimar bugun ciki Kawu Abdulkarim ya tambaya.

Wannan karon kallon Uncle din nasa yake kamar amininsa, aminin da ba shi da shi a tsayin rayuwarsa, bai taba tattauna sirrikan zuciyarsa irin wadannan da kowa ba, amma yadda Minister Abdulkarim ya saki jiki da shi yau yana jansa a jiki kamar sa’ansa cikin hikima da son sanin hakikanin matsalolinsa na aure, sai ya samu kansa da son gaya masa komai, watakila hakan yasa ya kara taimaka masa ya dawo da Hafsat cikin rayuwarsa da ta damalmale ta wargajeyanzu. Ya yarda sonta yake ba don Mammah ba, ko don ta shirya da shi. So ne mai zaman kansa, mai cin gashin kansa, wanda ba’a gina shi bisa kowanne tubali ba sai kauna zallah saboda Allah. Cikin kankanuwar murya ya ce.

“Tt is infatuation!”

A matsayinsa na wanda ya karanta ‘Forensic Psychology’ ya yarda Abdul’ azeez gaskiyar zuciyarsa ya gaya masa. Jinjina kai ya yi, ya dube shi cike da kauna. “Na fahimci komai. Ka kwantar da hankalinka, yanzu zan je wajen Ambassadan ka tafi gida ka huta. Amma ka ci gaba da lallaba Maryama ka santa da wuya ta yi fushi, amma idan ta yin ba ta iya yinsa ba. Ka jure dukkan punishments dinta ta fika son auren nan, amma ka bada mata kasa a ido”.
Sosai ya yarda da shawarwarin Kawun nasa, kuma dama ya dade da sawa ransa ko tsire shi Mammah zata yi zai jure, indai watarana zata huce ta dawo masa da Hafsat,suka yi sallama ya tafi bayan su Farhan sun rako shi jikin motarsa..
Www.bankinhausanovels.com.ng
‘Sun-city’ ya wuce, hankalinsa ya dan kwanta; ya san dai ya kashe maganar auren Mu’azatu wajen madaurin auren.Sai da ya zo barci ne ya gagara, kewar Hafsat ta hana shi ko da runtsawa, how he wish zai iya jin muryarta ko da bai ganta ba? How he wish suna kwance ne tare a gadon nan nasa suna rigimar duvet koda kwanciyar ta ‘kai da kafa’ ce yadda take cewa? Abubuwa da yawa yake tunowa na zamantakewarsu, masu dadin da marassa dadin. Marassa dadin su ne watannin farko na auren, halin ko in kulan da ya nuna mata, musamman ranar da aka kawo ta gidansa, ranar tarihin kowadanne ma’aurata. Amma ita Hafsat ba ta karar da komai a cikinta ba ban da bacin rai, ciwo, da kwanciya a asibiti. Ya tuno yadda ya kai ta asibitin ya watsar bai kara sanya ta cikin lissafinsa ba balle ya ciyar da ita. Wani kunci ya ziyarci zuciyarsa, ya kai tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa, ya ja duvet dinta ya rufe rabin jikinsa. Abubuwa da yawa ya cigaba da tunawa a wannan lokacin, yadda ta dinga wahalar shirya masa abinci yana barinta da shi, duk wai don kada ya saba da ita. Shin ashe mutum ya isa gujewa kaddararsa? Ya isa tsara wa kansa rayuwa? Ya tuno watannin farin cikin wadanda ba su yi nisa ba ya bi duk wata hanya ya tottoshe su don ya tsira da Mu’azatu! Wace irin makauniyar soyayya ya yi wa Mu’azatu wadda ta rufe idonsa har ya rasa clear conscience? Mene ne am
fanin irin wannan soyayyar ta a cutar da wani don a faranta wa wani? Sosai ya yi wa Mammansu uzurin matakin da ta ke dauka a kansa. Ya rufe fuska da tafukansa zuciyarsa na masa wani irin zZugi.

*********

Kamar yadda Minister Abdulkarim ya yi alkawari ga jikansa Abdul’azeez ya je ya samu Yayansa da Mammah a kan zancen. Sun tattauna sosai, ya gaya musu duk abin da Abdul’azeez ya gaya masa bai rage komai ba. Ya ce “Saboda tausayin da ya ba ni na so in gaya masa ba ya bukatar kaffara a kan ‘yar Attorney, sai kuma na yi tunanin tunda ba ka fada masa ba may be ba ka so ya sani ne a halin yanzu shi yasa na bishi a haka. Don Allah ku yi hakuri ku maida masa matarsa, he really repented, regretted, and wanted his wife back. Kada garin punishment ku koma daukar hakki, ita ma yarinyar tana son mijinta biyayya ta ke miki”.

Sai wannan lokacin Mammah ta san an hana Abdul’azeez auren Mu’azatu bonono Daddy yake musu ita da shi. Wani dan relief ta samu a zuciyarta ba don ta daina jin haushinsa ba, ga kuma labarin auren kwangila wanda a zahiri ba ta san hukuncinsa a addini ba da ya shiga kunnuwanta. Ta tabbata abinda ya fi wannan ma Hafsat za ta iya in aka sanya ta in dai a kan a barta ta yi karatu mai zurfi ne. Tausayin Hafsat ya kara kamata. Ta kudure a zuciyarta in har tana raye sai Hafsat ta zama Farfesa . Abdul’azeez kuwa tunda a kan budurwarsa ya saki Hafsat(wai ba don ba ya
sonta ba) _ she will make sure she made him understand the worth of what heabandoned negligently (sai ta tabbatar ta sa shi ya fahimci darajar abin da ya yi wa rikon sakainar kashi).
Www.bankinhausanovels.com.ng
Da wannan zaman nasu ya tashi, babu wata kakkwarar amsa daga bakinta. Daddy ya ce shi dama bai dauka da nisa ba, zai nemi Baffa Atiku a yl wa auren duba na addini sannan su gyara, kawai yana ganar da shi kuskurensa ne kafin ya bada goyon bayan maida auren ba tare da ma ‘yan Jimeta sun ji ba. Kuma dama ya gaya wa Maryam ta cire kanta daga sha’aninsu bakinsu daya ta ki ji. Sai dai har Abdulkarim ya tafi ba wanda ya ji ta bakinta a cikinsu.

A daren ranar kwana Daddy ya yi yana lallashin matarsa ta amince ya maida auren yaran, amma ta yi bakam ta ki ba shi amsa, har sai da ranshi ya yi mummunan baci, ya ce “Maryama saboda ba ni na dauki rikon Hafsatu ba shi ne za ki nuna min iyakata? To ai ni ma ina da iko a kanta tunda a gidana ta rayu karkashin kulawa ta kuma sunana ta ke bearing . Don haka ko ta ina aka je aka dawo nima ubanta ne ina da iko da ita. Don haka ba zan zuba ido yaran nan su ci gaba da zaman haramci ba. Da idanunki kin gani yana shiga dakinta ba da saninki ba yana bibiyar matarsa. Abdul’azeez ya yi kuskure, kuma ya yarda ya yi, in ya yi istigfari ba ki isa ki shiga tsakanin bawa da Ubangijinsa ba. Laifin da ya yi miki shi ne wanda ki ke da ikon yafewa ko kin yin hakan, amma ba wanda ya yi wa Ubangijinsa ba.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Kowa ya sani yin yarjejeniya a cikin aure shari’a ba ta so, ta yi hani, amma ba kowa ne ya
san hakan ba ko ya dauke shi da muhimmanci. Yau ko kisan kai Abdul’azeez ya aikata ba marriage contract ba, danki ne, ba ki da yadda za ki canza wannan. Ki gode wa Allah da bai yi saki uku ba, sannan bayan sakin al’amarin ya rikide zuwa yadda ki ke mafarkinsa. In ba ki gode wa Allah ba kada ki butulce wa ni’imarsa gare ki. A gobe za mu je Kano da su Kawu Abdulkarim gun Baffa a maida aurensu idan har shari’ah ta amince da hakan. Ki je ki yi ta fama da muguwar zuciyarki. Ina rokon Allah idan wannan shi ne gata na karshe da zan yi wa Abdul’ azeez ya sa in cika shi da sauran numfashina”.

Sai da ta ji zuciyarta ta raunana da wannan furucin nasa na karshe, sai kawai ta sa kuka. Juya mata baya ya yi ya kwanta, ta ci gaba da kukanta har ta yi ya ishe ta. Sannan ta share hawayen, ta ce cikin kuka.

“Na yarda a mayar da auren, amma wallahi sai na ga dama za ta tare”.

Dariya abin ya so ya baiwa Daddyn, wani zubin kamar ba ita ta haifi wadannan zaratan samarin ba, musamman idan tana gabansa, yajanyo ta gareshi yana fadin.

“Hakan ma mun gode, kwanciyar hankalinmu auren ya dawo dai-dai, kiyi ta rike ‘yar ki har ta fara furfura agabanki. Kuma ni ban ce mutuwa zan yi ba a hanyar Kano sai in kwana na ne ya kare, kin ji Maryamata?”’

28 2K oe ok OK

Washegari ta maida Hafsat makaranta da kanta, za ta zo ta dauke ta karfe hudu na yamma a gaban
department dinsu. Hafsat ba ta sha wahalar ganin Rabi’a Sada ba (Mami). Mami ta yi farin cikin ganinta sosai, ta gaya mata ta shiga damuwar rashin dawowarta ga shi ba ta san gidanta ba, wayarta ta buga har ta gaji. An wuce ta da karatu ba laifi, duk ta samu notes, handouts da courses outline a wajen Mami, ta gaya mata ta yi mata assignment har uku. Kuma tana yi mata attandences don jikinta ya bata ba zata watsar da karatun ta gabadaya haka kawai ba. Hafsat don farin ciki sai ta rungume Mami, ta yarda yanzu aboki rahma ne, sai dai zama da mutane ne da wuya, amma in ka yi katari da na kirki mai kaunarka da gaskiya amfaninsa yawa ne da shi. Mami ta mannewa tana highlighting dinta abubuwan da ba ta gane ba. Sun wuni tare ba abin da suke sai karatu. Ta kwafi time-table , sai dai cikin duk abubuwan da ta ke yi yana fado mata a rai, sai ta tambayi kanta ko me yake ciki? Ko ya ci abinci? Ko yana ina yanzun? Idan ta lura tunanin zai tafi da walwalarta da dan kwarin gwiwar da ta samu na son farantawa Mammah sai ta yi maza ta kira sunan Allah Al-Lateef, ta roke shi Ya karfafe ta da yin biyayyah ga uwarta, uwar da jinin haihuwa ne kawai bata diga mata ba a duniya. Ta tabbata duk son da Abdul’azeez ke ikirarin yana yi mata a yanzu, bai kai rabin wanda ta samu daga mahaifiyarsa ba.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana son nata ya zabi wata akanta? Yana son nata ya sake ta? Wannan kalma ta ‘saki’ na yi mata mugun ciwo kamar ba da amincewarta aka yi ta ba. A ranta sai ta ce, “Na amince ne a wani QARNI (centuary) na rashinsanin ciwon kai (period of barbarism). Ban san darajar miji a gun
matarsa ba. Ban san waye Abdul’azeez Dakata ba, idan yanzu ne zan iya rasa komai in koma matarsa!

To ai ya ce aurenmu yana nan, ya yi sakin kamar yadda ya yi alkawarin yinsa, kuma ya maida auren tun a lokacin. Wani gwauron numfashi ta sauke wanda ya sa Mami Sada juyowa ta dube ta. ‘ A sign of relief’ sunan numfashin nata. Murmushi ta yi wa Rabi’a Sadan ta ci gaba da rubutu.

Karfe hudu Mammah ta zo daukanta. Har gaisawa suka yi da Rabi’a, Hafsat ta gaya mata dimbin taimakon da Rabi’an ta yi mata. Sosai Mammah ta gode, suna tafe a kan hanya suna hirar makarantar har suka zo gida. Mammah ta gane Hafsat ta fara sakin ranta, ta daina yi mata fushi, watakila ta fara shiga karatun ta nutsu ne kamar yadda ta ke ankarar da ita. Watakila kuma don ba ta ganinsa ne. Koma dai mene ne daidai ta ke da kowannensu.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Da asubah ya nemi layin Abdul’azeez cikin sa’a ya samu, ya ce ya shirya yanzu ya fito su tafi Kano. Tun daga lokacin ya tabbatar Kakansa mai kaunarsa wato Abdulkarim Dakata ya yi kokarin da ya ce zai yi. Wata irin kaunar Uncle din ta sake mamaye shi. A gurguje ya yi wanka ya fiddo wata sabuwar shadda (filtex) ya saka, ya dora hula wadda ta dace da kalar shaddar wato coffee color, agogon hannunshi ‘ swatch -blustery’ kalarshi kenan, ya feshe jikinsa da turaren da yazame masa jiki sannan ya dauko duk abin da zai bukata ya fito. Gidan ya rufe gabadaya maigadinsa Dan fulani ya bude mishi kofa ya fita.

Duk mutanen gidan ba su fito ba sanda ya isa, a

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *