AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 3 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
Wani barci ne mai nauyi ya sure ta gabanin asubahi, bayan ta idar da sallar asubah. Ba ita ta farka ba sai wayewar gari tangararan. Lokacin tuni Abdul’azeez ya tsufa a ‘office’. Takaicin kanta ne mai tsanani ya kamata. Haka ta mike ta yi wanka ta shiga kicin don sama wa cikinta abin da zai ci.
Abdul’azeez bai dawo gidan ba har ta yi shirin barci, gidansu ya tafi a can ya ci abinci. Hatta Mammah ta lura cikin damuwa yake, amma da bai furta ba sai ta kyale shi. Yana gidan har karfe goma, Mammah ke tambayarsa ko ya gaya wa Hafsat maganar tafiyarsu Yola? Ya ce, abubuwa sun masa yawa, ya manta. Amma da ya koma zai gaya mata. Fada sosai Mammah ta hau yi masa na ba ya daukan abubuwan kowa da muhimmanci sai nasa. Hakuri ya ba ta ya kuma tabbatar mata yau zai gaya mata.
Da ya dawo ta dade da shigewa daki ta kashe wuta ta kwanta. Ko ta yi barci ko ba ta yi ba, ba zai iya cewa ba. ‘Text’ ya yi mata a ciki ya ce ta shirya kayanta da na bukata wanda zai yi mata sati biyu za su tafi jihar Adamawa jibi dukkansu, har su Mammah.
Washegari tana kunna waya abin da ta fara gani
kenan. Sai kawai ta ji gabanta ya fadi, me za su je yowa a Yola? Wa suka sani a can? Har kuma sati biyu? Allah ya so ta hutunsu na sati hudu ne. A hakan dai cike da zullumi ta soma shiri tun a lokacin.
Karin kumallo mai kyau ta shirya ma Abdul’azeez a safiyar ranar. Amma sai tsintar bude masa get da fitarsa ta yi tun kafin lokacin da ya saba tafiya office ya yi. Jikinta ya kara yin sanyi fiye da yadda yake a mace tun daren jiya. Haka ta kare wunin
sukuku tana shirya kayanta cikin ‘travelling bag’.
Haka ya yi ta zillewa haduwarsu har zuwa ranar tafiya. Ba su hadu ba sai asubahin ranar da ya fito cikin shiri da nashi jakar kayan marasa yawa. A falo ya same ta a shirye don kusan kwanan zaune ta yi saboda zuciyarta ta kasa sukuni balle ta yi barci. Jikinta ne kawai yake ba ta canjin Abdul’azeez yana da nasaba da wannan tafiyar.Ya kalle ta kasa-kasa yace ta koma daki ta canza mayafi wannan yayi Www.bankinhausanovels.com.ng shara-shara, nan ta ajiye hand-bag dinta ta koma dakin don bin umarninsa. Mamaki fal ranta don ita bata ga laifin mayafin data yafa ba, yanada kauri ba laifi kuma yanada girma, ita data fi amfani da abaya ma da dan mayafinsu bai taba cewa komai ba sai yau akan babban gyale. Tunda suka shiga mota ta gaishe shi, ya amsa bai kara ce mata komai ba. Nauyin da zuciyarsa ta yi kawai ya ishe shi. Www.bankinhausanovels.com.ng
A Asokoro ma ba su bata lokaci ba kowa a shirye yake. A motoci za su yi tafiyar. Manyan jifa-jifai uku na Dr. Hamza, sun biya sun dauki Uncle Abdulkarim da yaransa, za su tsaya a Kano su dauki su Adda Hafsatu don Anty Zuwaira ta ce ita kam ba za ta samu zuwa ba. Sanin halinta mijin bai takura ta ba.
Wajejen karfe sha daya na rana suna cikin Kano. Babu bata lokaci su Adda ma sun shirya su kawai ake jira su iso. Motar farko Abdul’ azeez ke ja, Hafsat da Mammah, Baba Azumi da Adda Hafsatu da Daddy ne a ciki, ta biyu Baffa Atiku, Dr. Idris Dakata, matarsa Dr. Tawheedah, matar Ibrahimada Minister Abdulkareem da dansa Ramadan ne a ciki, Ibrahima ke jan su, ta karshe su Aunty Luba, Murja, Mariya, Furerah, Usman da Haleem dasu Farhan, direban Daddy Salisu ke janye da ita suka kama hanyar Adamawa. Daddy ya ce, ba za su daura musu nauyi ba, Hotel zai kama musu gabadaya in sun isa.
Ana ta hirarraki a motar banda Hafsat da Abdul’azeez, wanda ke tuki cikin nutsuwa da kwarewar tuki. Daddy ne a gefensa, a kujerar baya ta farko ita da Mammah ne, a ta biyu Baba Azumi da Adda Hafsatu. Hafsat kwantar da kanta ta yi a kujerar gabanta tun tana tunane-tunane har ta rasa na kamawa, barcin da ta ci bashinsa ya yi awon gaba da ita. In lokacin sallah ya yi suna tsayawa a gidan mai su yi sallah su ci abincin da Mammah ta yo musu guzuri sannan su ci gaba.
Akai-akai suna waya shi da Sagir har Allah ya kai su Jimeta lafiya, misalin goma na dare. Don haka ya gaya wa Sagir ba za su samu shigowa a daren ba sai gobe da safe sun wuce masauki. Sagir ya yi korafin cewa, don me ba za su karaso su sauka gidansu ba? Ya ce, suna da yawa ne, san
nan shi ma ba tsarinsa ba ne tsarin Daddy ne su yi hakuri. Sagir ya ce ya fada masa sunan hotel din da suke, zai kawo abincin da aka tanadar musu. Ya gaya masa sunan (Jireh Suites).
A ‘reception’ din hotel din ya tarbi Sagir, ya karbi kabakin abincin ya kakkai musu, Mammah da Daddy daki daya suke, Baffa Atiku shi kadai. AbdulkarimDakata shikadai a dakinsa, Dr.Idris da matarsa Dr. Tawheedah daki daya, Usman, Uncle Ibrahim,Haleem dasu Farhan daki daya, Sauran ‘yan tafiya duka mata ne daki guda suka hada. Daga ‘reception’ Sagir ya koma. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sun ci sun sha daga abincin fulanin usli, sun sha fura da nono kindirmo har sun gode Allah, sannan kowannen ya nemi makwanci don huta gajiya. Abdul’azeez na tare da Baffa Atiku, Hafsat na tare da su Aunty Luba, Daddy dai ya dauka daki daya Abdul’azeez din ya kama musu shi da Hafsat din tunda shi ya kakkama dakunan,ko kusa ba wanda ya gaya mata abin da ya kawo su wannan gari mai dumbin albarka.
Shi da Baffa Atiku suka kwana, wannan kadai ya debe masa kaso hamsin na daga damuwar da ke nukurkusar zuciyarsa. Domin dai Baffan kusan kwana suka yi yana ba shi labarin kuruciyarsa, ya gaya masa “ he’s brave, genius, and patriotic” tun yana yaro, babu abin da ke girgiza shi a kan ra’ayinsa da determinations dinsa na son zama babban lauyan gwamnati. Yana so ya ci gaba da zama hakan a yanzu da ya zama cikakken mutum mamallakin iyali. Ya cigaba da amfani da wadannan qualities din akan aikinsa da iyalinsa. Ji ya yi gwiwoyinsa sun yi wani irin sagewa…
Does these qualities are still with him? Da sauri ya girgiza kai cikin musanta hakan da cewa “No,
they are absolutely not. He’s only brave on Mu’azatu yanzu, but not on anybody and anything else . Juyar da kai ya yi ya ci gaba da sauraron labaran da Kakansa ke ba shi na rayuwarsa ta baya, yana diba yana zuba su a sikeli yana auna su da rayuwarsa ta yanzu.Sai ya ga cewa; ratar da ke a tsakani mai tsananin fadi da girma ce tunda ya kasa yi wa kowa bravity da patriotic din sai Mu’azatu!!!
A dakin iyayen, Mammah na shirin kwanciya ta ce da mijinta Dr. Hamza. “Ko ka lura da sauyin yanayi a tare da Abdul’azeez da Addah? Tunda muka taho ba sa magana da junansu har muka iso. Sannan da ya zo kama daki bai kama musu tare ba ina lura. Haka kawai sai in ji gabana yana yankewa ya fadi in na kalle su tun tahowarmu”. Daddy ya ja bargo ya rufa ya kashe fitila mai haske. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Tsohuwar nan kin fiya sa ido, ina ruwanki da tsakanin miji da mata? In kuma fadan masoya ne suka yi a tsakaninsu fa? Ko harshe da hakori ai ana sabawa. Don Allah kada ki bata min daren yau da ‘Psychological Investigations’ dinki. Kanwar Haleem nake so mu samo tunda gobe za a kwace Hafsat…”. Ya fada yana murmushi don son gusar mata da damuwarta. Fuska ta yi sosai jin fatan da yake mata (gobe za’a kwace Hafsat), sannan ta isa gare shi tana fadin, ‘Mai raba ni da ‘yata ko girgizar kasa albarka. Mu je dai su ganta su san da zamanta, su san labarin tasu diyar, in koma da abata’’.
********
WASHEGARI
An tara maza da mata, babba da yaro na nesa da na kusa, na zuri’ar Malam Hashim Babba Jimeta. Da zuri’ar Dr. Bashar Maijama’a Numan, wanda shi ma dan nan asalin Yola ne daga karamar hukumar NUMAN. Kamar yadda Malam Babba da Dada suka bada umarni; duk wani jininsu ya hallara an ga Habibah.
Tunda Sagir ya shigo da bakin falon ganawar wannan family kowa yake raba ido ya ga ta inda Habiba za ta billo, tunda an gaya musu wadanda suka rike ta ne suka kawo ta. Tun fitowarsu Mammah ta ja mayafin Hafsat ta rufe mata rabin fuska, ta ce ta rufe fuskarta ta kalli gabanta, sai ta ce ta bude za ta bude.
Ita dai Addah mamaki ya hana ta cewa komai, saboda ita dai tun tasowarta ba ta san suna da ‘yan uwa a Yola ba. Jikin tsohuwa Dada da Malam Babba ya yi sanyi ganin har wadannan baki suka gama shigowa suka zazzauna babu Habiba babu alamunta.
Gaggaisawa aka fara yi, sannan Malam ya bude taron da addu’a. Daddy ya gabatar da kansu su ma suka gabatar da kansu a matsayin iyayen Habiba da ‘yan uwanta, ga kuma mijin aurenta Prof. Bashar Mai-jama’a, karshe Malam ya tambaye su wane labari suke dauke da shi game da ‘yarsa Habiba? Sannan ina ta ke yanzu? Dr. Bashar ya kara da cewa,
“Lafiya nake zaune da maidakina Habiba tun ina matsayin Malamin makarantar sakandire. Rana daya na tsiri karo aure sakamakon kowa da rubutacciyar kaddararsa ta aure, amma ba don Habiba ta gaza da ni ta kowanne bangare ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yaranmu uku, Modibbo (Ridhwan), da Abdurrahman sai auta Imamu a lokacin da na auro Hajara. Tun zuwan Hajara gidan ya ki zama lafiya, fitintinu iri-iri kullum da tashin hankalin da zan dawo na taras. Amma duk sanda na yi bincike a kan rikicin zan tadda Hajara ce ta tado shi. Zaman lafiyan ya kara tabarbarewa a gidan lokacin da Habiba ta samu ciki na hudu, Hajara kuma ta kwashe shekaru uku a gidan kenan babu ciki ba dalilinsa. Wannan ciki ya kara daga hankalin Hajara ta fiddo ainahin kalarta a fili, mace ce mai tsananin hassada akan abinda Allah bai bata ba.
Na sha ji tana fadi wa Habiba “wannan cikin ba dai ki haife shi a gidan nan ba, ko dai ya bi rariya ko ki haife shi akan titi”.Sai in tsawatar da kakkausan harshe, in kuma gaya mata Allah ya fi ta. Mugun bakinta ya kare a kanta. Saboda Habiba ba ta da fushi bata iya tashin hankali ba,rashin katabus dinta yayi yawa, shi ya sa Hajara ke mata duk cin kashin da ta ga dama. Ido wannan Habiba bazata daga ta dube ta ba. A karshe ni na koma kishiyar, saboda ni nake tare wa Habiba fadan in ina nan, in bana nan kuwa tana shan ukuba a hannun Hajara. Sabida haka ne na ga gara in sauwakewa Hajara auren nan ko ma samu kwanciyar hankali ni da iyalina. Na saki Hajara saki daya, amma ta ki tafiya, tace gara ma in barta ta zauna a dakinta, don in ta tafi biyu-babu zan yi, don kuwa ta sha alwashin Habiba ba za ta haife cikinta cikin gidan nan ba. A karshe ta karfi na fidda Hajara daga gidana, na watso mata kayanta waje, wannan shi ne dalilin rabuwata da Hajara na farko.
Na maida hankali ga kula da Habiba duk da cikin ba mai matsala bane sam kamar haihuwarta na baya, ji nakeyi kamar wannan ne karo na farko da za’a yimin haihuwa bansan dalili ba. Muka ci gaba da kula da yaranmu da zamanmu cikin rufin asiri da kwanciyar hankali.
Wata rana cikin Habiba nada wata biyu ba kadan na wayi gari na tafi wajen aiki inda nake koyarwa a makarantar ‘yammata ta (GGSS YOLA). Na dawo na tadda su Abdurrahman zugum-zugum a gida su kadai. Na kama Imamu da ke ta kuka na aza bisa cinyana ina tambayarsu ina Mamansu ta je ba ta gaya min ba, ba ta kuma tafi da Imamu ba? Suka ce ai ta tafi unguwa tun kan su dawo makaranta, shi ma Imamu shi kadai suka same shi a kofar gida. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka na shiga kicin na shiga nema musu abin da za su ci, muka ci gaba da zaman jiran dawowar Habiba, ina cike da mamakin abinda tayi don bata taba yin haka ba koda wasa, ba inda take zuwa bata nemi izni na ba, sannan wai ta bar karamin yaro kamar Imamu a kofar gida. Har rana ta fadi ba ta dawo ba.
Ban kawo komai a raina ba na sanya a raina cewa, babbar lalura ce ta fidda ita tunda ba ta taba yin hakan ba. Da naga dare ya yi ne hankalina ya soma tashi, ga Abdurrahman da Imamu sun ishe
ni da kuka. Don haka na sako su a gaba muka taho gidan Dada nan Demsawo, mu muna (Upper Luggere) a lokacin.
Tafiyar da har yau ba ta dawo ba kenan, ga ‘ya’ yanta duk sun zama maza, ban da Modibbo babu wanda zai iya tuna ta sai a hoto. Mun dukufa addu’a muna rokon Allah ya bayyana ta ba dare ba rana, mahaifinta kun ganshi nan ya yi shekaru ba ya bacci, ya kuma ce a duk istikharar da yake yi a kan Habiba Allah ba ya nuna masa komai a kanta. Dada ce ta ci gaba da rainon su Imamu ta ki bai wa kowa a gidannan su ko nawa dangin.
Rana daya na tsinci kaina ba abinda nake so sai dawo da Hajara gidana, na dawo da ita muka ci gaba da zama, amma Dada ta hana ta jikokinta.
Watanni shidda da bacewar Habiba malamai babu adadi Malam Babba ya baza, shima ba’a barshi a baya ba, suka mike suna addu’a dare da rana a kan kowanne boyayyen al’amari ne tattare da Habiba Allah ya bayyana mana, Ya kuma maido ta gida lafiya cikin iyalinta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Rannan na dawo aiki na tadda cincirindon mutane a kofar gidana. Ana hango ni aka shiga darewa ana bani hanya. Hajara ce ta ke hauka tuburan a tsakiyar unguwa, ta kekketa sutturar jikinta duk da yadda matan makwabta ke kokarin rufe mata tsiraici abu ya ci tura, da an saka za ta yage su, tana fadin duk irin sharrin da ta rinka shukawa a zamanta da Habiba. Wallahi wasu ko da wasa ban sansu ba, Habiba ba ta taba fada min ba. A karshe ta ke fadin, ita ta yi wa Habiba ‘kurciya’ ta bar Yola, kuma ko za ta mutu a haukace Habiba ta tafi kenan ba za ta dawo ba. Gidana ma da ta dawo asiri ta yi min ta dawo, kuma ban isa in karya shi ba saboda a kogin Niger-Delta ta jefa”’.
A sanda ya zo nan hawaye sun jika fuskarsa, ya sanya gefen babbar rigarsa yana sharewa. Hafsat Suhaanah, wadda zuwa yanzu ta fahimci ko a ina suke, da kuma dalilin zuwansu, da ko wane ne wannan farin bafillacen ma’abocin zati da kamala. Jikinta tsuma ya hau yi, tsigogin jikinta suka shiga tashi, ta kura masa ido ba ta ko kiftawa.
Wani irin ‘feeling’ ta ke ji yana fizgar zuciyarta irin wanda ba ta taba ji a kan kowa ba. Ci gaba ta yi da kallonsa, wannan ‘feeling’ na kara cika kowanne sako na zuciyarta. Shin ko wannan shi ne abin da kowanne Da ya ke ji a kan mahaifansa, su ma mahaifan suke ji a kan ‘ya’ yansu wanda Daddy ya kasa ji a kanta a baya???
Mammah ta lura da jikin Hafsat rawa yake yi, kuma ta bude idonta daga lullubin dolen da ta saka ta tana ta kallon Dr. Bashar Mai-jama’a Numan. Jawo ta jikinta ta yi, ta kwantar da kanta a cinyoyinta. Hafsat ta rufe idanunta hawayen farin ciki suka shiga kwaranyo mata. Farfesa Bashar ya ci gaba da bada labarinsa bayan ya tsane hawayen idanunsa da hannun babbar rigarsa.
“Cuta ta karshe Hajara ta yi min, ba ni kadai ba, har iyayen da suka tsugunna suka haifi Habiba. Tunda duk son da nake mata ban kai su ba. A lokacin na damka ta hannun iyayenta na sake ta www.bankinhausanovels.com.ng
saki uku. Ni da su, (Malam Babba da Dada) da sauran ‘yan uwanta na ciki daya da ‘ya’yan da ta haifa muka rungumi kaddara. Domin a shekarar farko in Malam ya yi istikhara yana gaya mana ya ganta lafiya cikin kwanciyar hankali a duk inda ta ke. Amma a shekaru na gaba sai ya ce ba ya ganin komai a kanta sai duhu . Allah ya rufe masa al’amarinta.
Yaya Tijjani babban Yayansu, kasancewar ma’aikacin gidan talabijin ne na jihar Yola, ya yi hobbasa iri-iri wajen neman Habiba a kafafen yada labarai har yau ba amo ba labari, babu ko wanda ya ce ya taba ganinta sai a wannan shekarar da dan wajenku, abokin Sagir ya zo daurin auren Modibbo ya ce mana yana da labarinta, ya san inda ta ke, zai dawo mana da cikakken bayani a kanta bayan watanni hudu.
Ya gaya musu cewa, shekaru takwas ya kwashe bai kara aure ba, kasancewar matan bakidaya tsoro suke ba shi, kuma yana sanya ran zai ga Habiba komai daren dadewa bai taba fidda rai ba”.
Kuka Hafsat ta fara yi cikin mayafinta lokacin da Dr. Bashar ya dasa ayah. Mammah ma kukan ne ya ci karfinta. Da fari tausayin iyayen Habiba ta ke ji, amma yanzu Dr. Bashar yafi bata tausayi. Da ace Habiba ta yi tsawon rai zai fi kowa bukatarta a yanzu ko mata ukku gare shi.Daddy da Abdul’azeez hankalinsu na_ kan Mammah da Addah wadanda kukansu ya soma fitowa fili har aka soma maida hankali gare su duk da dai fuskar Hafsat na rufe cikin mayafinta.
Wani iri Abdul’azeez ke ji a ransa da kukan Hafsat, yadda shi kansa ba zai iya fassarawa ba. Mammah ta share hawayenta cikin murya mai sanyi ta soma ba su labari.
Tun daga sanda aminiyarta Hajiya Halima matar Controller ta kawo mata Habiba da kuma bayanin da Haliman ta yi mata a kan Habiban na yadda ta same ta, zuwa yi mata fasfo da visa da tafiyarsu Jeddah, yadda ta gane Habiba na da ciki bayan tsautsayi ya sameta sun je asibiti haihuwar gaggawa ta sameta. A nan ne ta dago ido ta dubi ahalin Habiba sun zubo mata na mujiya caaa! Kamar idanunsu sa fado.
Russunar da kwayar idonta ta yi kasa, muryarta cike da alhini ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“I’m sorry, ina mai baku hakurin sanar da ku cewa, Habibah ta rasu a wurin haihuwar diyarta Hafsat-Suhaanah…!!!”” Ta yaye lullubin kan Hafsat ta ce, “Je ki ga mahaifinki Hafsat!”’.
Hawaye ne suke bulbula daga idanunsu bakidaya, in ka dauke yara-yaran matasa da aka haifa a bayan batan Habiban. Hatta Yaya Tijjani kuka yake yi, Fusam, Sa’ade mai binta da Haladu, sun ko kasa kallon Hafsat din. Fuskar Dr. Bashar cikin tafukansa yana ta gunjin kuka, amma hakan bai hana shi dagowa ya mikowa Hafsat hannu ba. Wadda ita ma nata kukan ya tsananta, kanta ko kallabi babu. Wani ‘ignition’ Abdul’azeez ya samu zuciyarsa na yi da kallon Hafsat cikin wannan hali. Shi ba abun
ya je ya mikar da ita tsaye ya rungume ta ba, komai ya kare a tsakaninsu. Ya riga ya yanke
hukuncin da tun ba’a je ko’ina ba ya soma shiga halin ha’uw’la’i akan ingancinsa.
Kasa jure ganin wannan abin tausayin ya yi, ya tashi ya fice zuciyarsa na wani irin zabalbala. Ga shi ya riga ya aiwatar da komai, tun a Abuja ya sanyawa Hafsat takardar sakin cikin ‘handbag’ dinta a lokacin da ya sanyata ta koma daki wai ta canzo mayafi, tsabar shikansa yana jin kunyar bata takardar sakin a hannunta. Saboda shi ma ya san ko giyar wake ya sha ba zai iya fuskantarta ido cikin ido ya ba ta wannan takardar sakin ba, duk da abu ne da ta kwana da sanin kasancewarsa, to amma akwai Www.bankinhausanovels.com.ng KARAMCI da KYAUTATAWA a cikin zamansu, wanda ba zai taba gogewa daga tarihin rayuwarsa ba, kuma ba zai gushe yana kallon Hafsatu da su ba. Da sassarfa ya isa ga motarsu ya bude ya shige ya maida kofar ya rufe, ya kwantar da kai a kan sitiyarin ya kai hannu ya dafe kirjinsa daidai saitin da ke azabtar da shi. “ME NA AIKATA???” Yake fadi a fili.
*********
Da rarrafe Hafsat ta rarrafa ta isa ga Dr. Bashar kafin ta karaso ya taso ya cimmata, ya sanya ta tsakiyar hannayensa ya rungume. Yanayin da Hafsat ta samu kanta a wannan lokacin ba ta taba tsintar kanta a kololuwar dadin irinsa ba. A tsaye suke tsakiyar taron nan kusan minti goma kafin Dada ta mike ta rabo ta da uban ta kamo hannunta.
War hadosabajo’am Hafsatu (Zo nan kawata Hafsatu)”. In ji tsohuwa Dada.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG