AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
Shigowar Daddy dakin nata yana tambayar wasu mukullansa ya sa ta farfadowa daga zazzafan tunanin da ta fada, wanda zuwa yanzu ya fara tafarfasa zuciyarta. Dagowa ta yi a hankali ta dube shi idanunta jazir. Da sauri Dr. Hamza ya karasa shigowa dakin, “Lafiya Maryama? Me ya faru? Mutuwa aka yi?” Ya kama dukkan hannayenta biyu ya rike cikin nasa. Ganin yadda hankalinsa ya tashi da ganin yanayinta ya sa ta nemo wa kanta murmushi wanda bai wuce iya fatar bakinta ba.
Bai kamata ta ce masa komai ba, tunda itama ba ta san me ke faruwa din ba. Ga shi Baba Azumi ta ce ta ba su lokaci, watakila da ya dawo sun koma gidansu komai zai wuce, ko harshe da hakori ai ana sabawa. Ita da ta yi auren soyayya da Prof. Hamza wane irin bacin rai ne bai jefa ta a ciki ba, kuma ta jure sun zauna a haka har aka zo gejin da bacin ran nata shi ne abu na karshe da yake guje mawa?
“Hafsat ce ba ta jin dadi”. Ta fada a hankali yadda zai kwantar da hankalinsa.
Ya ce, “Ai sai ku je asibiti a duba ta, ba ki zauna kina tagumi da jan ido ba”.
Ya dauki mukullayensa a kan lokar gadonta, ya juya. Har ya kai bakin kofa ya kama marikin kofar sai ya juyo da murmushi a kan fuskarsa.
“Ko amarya zan samu ne kwanan nan aka gaya min indirectly ?”
Duk yanayin da ta ke ciki sai da ta yi murmushi, a zuciyarta ta ce, “Ina ma hakan ne!”
Sai dai a matsayinta na mace, kuma babba ba ta ga wani alamu na juna biyu a tare da Hafsan ba. Jin ba ta ce komai ba ya lura kuma ba ta son magana sai ya fita, zuciyarsa na gaya masa kamar ta sakaya masa wani abu, amma ko ma mene ne in ta yi wari da bakinta za ta fada mishi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka suka zauna a gidan su uku tsayin sati biyun, ba sa ummm ba sa umm-umm. Baba Azumi ce kadai ke yi musu hira. Ita ma idan tayitayi ta rasa mai tayata sai ta yi shiru. Ana i-gobe Abdul’azeez da su Isma’el za su
dawo Hajiya Maryam ta ce wa Hafsat ta shirya ta koma gidanta, su tafi da Baba Azumi don ta taya ta su yi tiding gidan ta kwana, za ta turo Salisu ya dauke ta in Abdul’azeez ya sauka a Abuja.
Hajiya Maryam na ganin yadda Hafsat ta kidime ta rikice, ta gigice, a karshe ma kasa zaman wurin ta yi ganin yadda ita da Azumi suka zubo mata ido. Mikewa ta yi ta nufi daki, kafin ta isa da gudu-gudu ta karasa ta shige, kuka ya kufce mata, karshen tika-tika-tik! Me kuma za ta ce wa uwar tasu? Za ta ci gaba da boye sakin ne kuma? A dauke ta a maida ita gidanta bayan kuma auren babu shi, ya mutu?
Tambayoyin da ta ke ta jero wa kanta kenan ta rasa amsar ko daya.
Bayan tashinta da kulewarta Hajiya Maryam da Baba Azumi suka bi bayanta da kallo sannan
suka dubi juna, an rasa mai magana a cikinsu.
**********
ABDUL’ AZEEZ DAKATA
Shi kadai ya san yadda rayuwar ta
kasance masa a tsayin sati biyun nan da Hafsat tayi a Jimeta. Zai iya kiransu kwana goma sha hudu mafiya tsayi da fadi a ranakun rayuwarsa. Abin da ya sani kawai shi ne; ba ya iya zaman gidan, barci kadai ke kawo shi cikinsa. Da safe zai yi wanka ya tafi ‘office’ babu tunanin karin kumallo, sai ya je can dinhanjin cikinsa ya hana shi sukuni yake samu ya sha ‘coffee’ ya cika wa kansa aiki duk don ya hana kansa tunanin komai. Haka zai zauna babu ko tunanin abinci sai lodawa kansa aiki, sallah kadai ke tayar da shi.Ba shi zai baro ‘office’ ba sai karfe shidda na yamma Www.bankinhausanovels.com.ng Daga nan kuma kai tsaye gidansu zai wuce, a can zai yi sallar magriba da isha tare da Daddy, su ci abinci tare har Mammah ya zauna ya ki tashi har sai Daddy ya ce da shi dare ya yi, watarana har ya tsokane shi ko zai koma Jimeta ne a yi sati biyun tare da shi?
Daga Daddy har Hajiya Maryam sun fahimci yana cikin damuwa wadda cikinsu babu wanda tunaninsa bai ce da shi ta rashin maidakinsa a kusa ba ce. Don haka babu wanda ya bashi hankalinsa. Babu daren da zai zo ya wuce a tsayin kwanaki goma sha hudun nan da bai gwada kiran wayar Hafsat ba sama da sau hamsin a rana, amsar dai a kullum iri daya ce; wayar a kashe ta ke. Ya kasa amsa wayar Mu’azatu ko guda daya daga ranar da ya saki Hafsat! Abinda shi kansa bai san dalili ba; wadda ke can gidan su a _ birnin Lagos hakan ya dugunzuma nata hankalin. A ganinta yanzu lokacin farin cikinsu ne, lokacin cikar burinsu, me yake nufi da kin amsa wayarta idan shi ya kasa kiranta?
Kwanansa bakwai da baro Hafsat a Jimeta ya yanke wa zuciyarsa komawa. Wannan ne kadai mafita a gare shi, ya koma ya samu Hafsat ya gyara dingimemen kuskurensa ko rayuwarshi ta koma daidai, zai lallaba ta ya karbe takardar… ya yayyagata kafin kowa ya gani, zai maida ita dakinta kafin kowa ya ji. Ya godewa Allah ya yi sakin da addini ke so zuciya bata kaishi ta baro bakidaya ba! Idan ya samu ya dawo da Hafsat sai kuma ya san ya zai yi da Mu’azatu. A wannan gejin yana jin zai iya karya alkadarinsa ya zauna da su su biyun. Ya fahimci abin da yake kin fahimta da gangan; Hafsat ba ta shigo rayuwarsa don ta fita ba, ba ta shigo zuciyarsa don ta yi
KWANGILA ta wuce ba… Ba mata irinta ne ake aura a saki a lokacin da ake so ba. Ba mata irinta ake saki don a samo wasu ba. Ba mata irinta ke barin gidan auren su na farko zuwa wani, ba tareda kwakkwaran dalili ba. Irin Hafsat saidai wata kaddararta daban mai karfi ta raba su da gidansu na farko (mutuwa) amma ba common saki irin wannan ba. Ya yarda ya amince a cikin mata akwai virtuousones ;Their prices is per above rubies! Ba’a amfani da su don cimma wata manufa sai don biyan bukatar rai kadai! Ya yarda ya amince zuciyarsa SOYAYYAh ta ke wa Hafsat ba irin wadda ta ke yi wa Mu’azatu ba… Idan abinda yake ji a kan Hafsat shi ne ‘soyayyah’ zai so wani masanin ilmin zuciya ya taimaka mishi, ya fada mishi wanda yake ji a kan Mu’azatu kuma mene ne shi??? Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya tsaya, ya nutsu, ya kintata, ya yi estimating , sai ya samu cewa ‘the feeling is totally different…..Ba soyayyah kadai yake yi wa Hafsat Suhaanah ba, har da wata boyayyar kauna ‘yar usuli mai yawan kintace. Yana begen sake ganinta ko da sau daya ne, yana kewarta cikin gidansa… Har ila yau yana nadamar yin AUREN KWANGILA da ita… yana nadamar yin amfani da halitta mafi soyuwa a zuciyar mahaifiyarsa don son cimma wata manufa. Watakila Ubangiji ya canza zuciyarsa a kanta ne don Ya ganar da shi kuskurensa.
Duk ilmin addinin da yake da shi bai yi amfani da shi ba, ya sa kafa ya take saninsa saboda soyayyar Mu’azatu data rufe masa idanu. Sanin kansa ne babu wani aure na kwangila a cikin addini, kai duk wani aure da za a kafa shi a kan wasu sharudda ko a deba masa wa’adi bai inganta ba a addinin musulunci. Duk wani aure da za a yi shi ba ka kusanci iyalinka ba har tsayin watanni ukku ba tare da dalili ba, shi ma ba cikakken aure ba ne! Ya zauna ya cutar da Hafsat watanni goma sha biyar bai taba sauke nauyin auratayya da Allah ya dora a wuyansa ba ba tare da hujja wadda addini ne ya tsara ta ba. Babu mamaki don Allah ya hukunta shi da soyayyar Hafsat da ta hana shi nutsuwa a lokacin da ya haramtawa kansa ita. Ta tsayar da duk wasu ‘daily activities’ na rayuwar cikakken mutum a gare shi. A tsayin kwanakin nan bakidaya a dakin Hafsat yake kwana a kan gadonta. Barci gwanin iya sata kadai shi ke sace shi, shi ma duk inda assalatun fari ta ke zai bar idanunshi. Zuciyarshi ta dora daga inda ta tsaya na tunanin hanyar da zai bi ya maido Hafsat cikin rayuwarsa ba tare da kowa ya ji ya gani ba. Babu mafita ban da komawa ya cimmata a Jimeta.
Bai kara fahimtar cewa ya fita daga saiti ba, sai da ESQ Ahmad Kutama ya kawo wasu manyan ‘files’ ya ajiye a gabansa. Da mamaki yake dubansa kafin ya janyo kujera ya zauna a gabansa. Check these files for me properly, please ”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Janyo su ya yi gabansa yana dubawa, shi ya rubuta clues na shari’ar da za su yi sati uku masu zuwa, amma me? Clues din ba su da alaka da wannan shari’ar na wadda za su yi kafin waccan ce. Lumshe idonsa ya yi ya bude a hankali, “ I’m so sorry” . Kawai ya iya cewa. Ahmad ya bi shi da kallon tsaf! Ga shi dai ya yi shigarsa tsaf cikin ‘suit’ kalar ‘grey’ da ratsin fari ta ciki kamar yadda ya saba, but it’s obvious that he is definitely upset … alamu ma sun nuna kwana biyun nan he didn’t shave his face, sannan gashin kan ya cukurkude alamar ba ya samun extra kulawar da yake samu a baya duk da shi ba ma’abocin yawan askin bane amma kula yake da sumar sa sosai. Ya san yana da aure don har da shi aka raka shi dakin matarsa balle ya ce rikicin soyayyah ya fada. To me aure ba ya iya fadawa soyayya for the second time? Ahmad ya tambayi kansa. Bayan wannan shi dai ya san Abdul’azeez bai da matsala, dan gata ne na karshe, gatan da ya sa duk ya riga su aure. Saboda Babansa ne ya gina masa gida. Su kuwa sai haya suka kama cikin Abuja. Shi nasa wata biyu kenan, na Abdallah wata hudu. To ko kuma ta gidan ce ta ke birkita shi haka? Duk zai iya yiwuwa. Ya san Abdul’azeez da shegen zurfin ciki a kan abin da ya shafi matarsa. Bai taba zama yayi hirarta da wani a cikin su ba. Ko suna hirar ‘yammatansu kafin suyi aure shi baya magana. Haka bayan_ sunyi aure suna zancen amaren nasu a gabansa irin sun makarar dasu ko makamancin haka ko kai baya dagawa balle ya tofa. Amma duk da haka ya samu kansa da son taimaka masa koda da shawara ne don bai taba ganinsa cikin wannan halin ba. Ga shi al’amarin har yana so ya shafi aikinsa. Abdul’azeez din da ba ya barinsu su yi kuskure ko kankani yau shi ake yi wa gyara mai girma haka. Gyara zamansa ya yi ya fuskance shi sosai. “Me ye matsalarka Barrister?” Yau karo na farko a rayuwarsa neman wanda zai budawa cikinsa yake yi, ko zai samu wata shawara wadda ta fi tasa inganci. Ya yarda ya gama lalata rayuwarsa in bai je Jimeta a gobe ba har takardarsa ta je hannun mahaifiyarsa. Ba hukuncin da zata yi masa yake tsoro ba; bazata taba yarda da dawowar Suhaanah gareshi ba! Ta sha gaya musu opportunity comes only once in life (dama tana zuwarwa dan adam sau daya ne a rayuwa) kuyi amfani da ita a sanda kuka sameta. Yau ba yana son Hafsat-Suhaanah don Mammah ba ne, sonta yake a karan-kansa da soyayya mai azabtarwa. Bai san sanda ya buda baki ya ce da Ahmad. In an yi saki, ya ake a gyara? In an yi alkawari aka kasa cikawa daga baya ya ake a yi kaffara ?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Gaban Ahmad sai da ya fadi, bai san sanda ya ce a tsorace, ““ You mean ka saki Hafsat? Auren shekara daya kacal?Kai kuwa me tayi maka haka da zafi?”
Kamar zai kife shi da mari ya ce, “Ya zan tambaye ka, kuma ka bi ni da tambaya?”
“Ai ban san sakin wane iri ba ne”. Ya fada cikin sanyin jiki. Abdul’azeez ya kwantar da kansa a kan teburinsa. Murya a raunane ya ce. “ This is the deadly mistake i’ve ever made , na sake ta Ahmad, amma ina so in dawo da ita. Dubi yadda na zama cikin sati daya kacal da yin sakin. Da farko na yi zaton Mu’azatu nake so a kanta, yanzu da babu ita cikin gidan na gane Mu’azatun ba ta da matsayi mai yawa a tare da ni. Ka taimake ni Ahmad ba ni da idea”.
So yake ya ce da shi. “ Ai mun gaya maka,
watarana za ka so yarinyar nan ko da za ka yi mata kishiya”. To amma tausayin Abdul’azeez din ya hana shi fadin hakan, yanzu ba lokacin raddi ba ne. Lokacin neman mafita ne. Kuskure ne ya riga ya yi shi sai a nemi hanyar gyarawa in mai gyaruwar yayi. Bai nemi ba’asi ba, cike da fargaba ya ce. Sakin guda nawa ne?” Ba tare da ya dago ba ya ce, “I think daya ne. A gurguje ma na rubuta ina tsoron ta Zo ta ganni ina rubutawa. Ahmad ‘proffession’ dina bai kare ni da komai ba da na kasa gane ba hanyar samo Mu’ azatu na bi ba, hanyar kara tsanarta a zuciyar mahaifiya ta na bi. Hanyar kara nesanta kaina da ita na bi. A karshe in kare da babu ko dayansu muddin zancen sakin ya je kunnen Mammah”’. Ahmad ya dafe kai. “Yanzu ina Hafsat din?” “Tana garinsu Jimeta”’.
“Just call her now (kira ta yanzu) ka ce da ita “na maida ke dakinki’, shi ne muhimmi kafin komai. Ko ta yarda ko bata yarda ba; ta maidu”.
Wayar ya janyo cikin kasala duk da ya san ba samun nata zai yi ba, amma haka ya yi ta gwada jera kiran yana katsewa. Ya dubi Ahmad cikin rauni.
“Ta dade da yanke communication da ni, na tabbata ta dade da ganin takardar, da kyar in bata canza layin waya ba’. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ahmad dai haushin Abdul’azeez kamar ya kashe shi. Wai a kan wata da yake hange a waje ya saki ta gida, ba dole hakki ya rikide masa zuwa soyayya ba?
“Tunda gobe weekend ne za ka iya zuwa Jimetan, make sure ka kwace takardar ka kuma gaya mata ka maida ita ta ji da kunnenta. Ita kuma wannan Mu’azatun ajiye zancenta a gefe sai ka dawo da zabin mahaifiyarka. Abdul’ azeez kana tune da hakkin mahaifiya kuwa da karfin ikon da Allah ya ba ta cikin rayuwarka? Allah (S.W.A) Ya ce a bi ta, a bi ta, a bi ta kafin yace a bi uba. Amma budurwa??? Kana son ganin albarka cikin rayuwarka? Ta aura maka mace har mace mai daraja irin wannan ka saki? Inda hali mu tafi tare, mu hau jirgi don mu yi sauri. I really want to help” .
Daga office din kai tsaye gida ya wuce, ya samu Mammah da Daddy a falo suna cin abinci. Sun masa tayi, amma yau sam ya kasa cin abinci. Jiransu ya yi har suka kammala, Daddy ya dawo tsakiyar falo ya zauna a kujerun falon na alfarma. Budar bakin Daddy sai cewa ya yi.
“Za ka wakilce ni a ‘graduation’ din Isma’el da Usman a America da Brussels jibi, zaka fara halartar na Isma’el first ,sai ku wuce Brussels na Usman tare dashi, ni ayyuka sun min yawa, passport dinka daka bani na sabunta maka watannin baya ya jima a wajena don haka tuni na gama maka shirin komai, thumb print kawai zakaje kayi da safe namaka booking ma, sai ka zaba tsakanin jirgin safe ko na dare. Na gayawa shugabanku dazu ya baka leave na sati daya na tura ka wakilci kuma ya amince, zakayi sati daya sai ku dawo tare da su duka. In an kwana biyu kuma ni sai in je wa Haleem visit a Sweden”.
Dukkansu babu wanda bai lura da yanayin canzawar fuskarshi ba. Wata irin canzawa kamar an aiko masa da sakon mutuwa, fuskar har wani
brown ta koma. Da kyar ya iya hadiyar miyau, cikin damuwa ya ce. “Daddy Jimeta za ni gobe”.
Mammah ta ce“Jimeta kuma?” Cikin mamaki sosai, ta cigaba da cewa. “Dan zaman da za ta yi cikin ‘yan uwanta na sati biyu kacal za ka haramta mata karashe shi? Ina ce next week za ta dawo? To ban yarda ba, wannan rashin hakuri da rashin kawaici har ina?”. Daddy ma yana bayan Mammah, ya ce, “Ba za ka je Jimeta ba sai ka dawo daga ‘graduation’ din nan sai kaje ku taho tare”.
Ya amsa a ladabce,kansa na kasa, kasancewar yasa a ransa bazai kara jayayya da iyayensa ba har karshen rayuwarsa! Amma kallo daya za ka yi masa ka fahimci bai so wannan tafiya ba. Tamkar wata obstacle ce ga isa ga Hafsat da gyara gundumemen kuskurensa da wuri. Zuciyarsa na lallashinsa da cewa,Www.bankinhausanovels.com.ng Hafsat-Suhaanah will not expose his shortcomings, za ta yi masa uzuri kamar yadda ta saba, za ta rufa masa asiri kamar yadda ta saba, zata jira shi har ya dawo kafin ta dawo Abuja bazata dawo ita kadai ba komai dadewar da zai yi balle sati daya kacal, tunda ma ai shi zai je ya dauko ta wanda dole a jira ya dawo.
Abin da Abdul’azeez Dakata ya manta shi ne duk yadda muka kai ga tsara wa kanmu al’amura sai Allah ya nufa. Bai yiwuwa mu yi ta tafka kuskure yadda muke so mu ce zamu gyara komai a lokacin da muka ga dama. Allah yana ara mana dama mai dumbin yawa a rayuwa mu yi ta yin abin da muka ga dama, rana daya in Ya tashi kama mu ba Zai ba mu damar repenting na minti daya ba. Wasu al’amuran na zuwa_ cikin rayuwarmu don su zama iznah a gare mu.
HAFSAT DAKATA
Bayan shigewarta daki, Mammah ta mike don ta bi bayanta. Da sauri Baba Azumi ta kamota ta maidata ta zaunar.
“Kada ki bi ta. Bari sai ya dawo sai su tafi tare. Mu je yanzu ni da Salisu ni kadai in gyara gidan”’
Hajiya Maryam jiki a sanyaye ta koma ta zauna. Damuwarta ta fito sarari akan kyakkyawar fuskarta, amma Azumi ta shiga nuna mata cewa samun sabani tsakanin miji da mata wani abu ne wanda yake normal ba yau aka fara shi a doron duniya ba. Ko harshe da hakori ai ana sabawa. Ba irin tunanin da ba ta yi ba na abin da ya shiga tsakanin Abdul’azeez da Hafsan, sai dai ko kusa koda da taki daya tunaninta bai kawo saki ba. Wannan ko a mafarkinta bai taba zuwa ba.
Da daddare Hafsat takardar Abdul’azeez ta dauko daga jakarta, kwanciya ta yi a tsakiyar gadonta idanunta sun yi luhu-luhu sun kankance sabida kukan da ta ci a yau. Da Mammah ta ce ta tashi ta koma gidanta wani miki ne ya taso mata na kaunar gidan, maigidan da duk abin da ya shafe shi. Warware takardar ta yi tana so ta yi mata duba na tsanaki, ta fahimci hakikanin me Abdul’azeez ke nufi da kalamansa?Don kuwa a Jimeta daga sanda taji kalmar ‘saki’ cikin wasikar bata kara fahimtar sauran bayanan dake cikinta ba.
Abinda ta fahimto a karo na biyu da karanta takardar cikin nutsuwa da_ tsaida_hankali
shine;kalaman duka na yabo ne da rashin kushe a gare ta. Ya kare da cewa, ita din abar so ce ( a darling ) a zuciyarsa. Halayenta ababen yabo ne. A zamansa da ita ba ta zalunce shi ba. Rauninsa guda daya ne yana son Mu’azatu , kuma muddin yana aurenta iyayensa ba za su taba bari ya auri Mu’ azatu ba, da ya kasance kuma son da yake yi wa Mu’azatun ya rinjayi wanda yake yi mata sai ya zabi ya samu Www.bankinhausanovels.com.ng Mu’azatun ita ya rasa ta… Wannan ya isa ya nuna in har ita mai tsinkaye ce ta yarda ta amince da cewa Abdul’azeez ya fi son Mu’azatu a kanta. Koda yana sonta a yanzu bayan aurensu, son bai kai koda taki daya na wanda yake yi wa Mu’azatu ba…… Wani kuka ne ya taho mata da karfinsa, ta kai hannu ta toshe bakin don hana masa fitowaamma hakan ya gagara saboda karfin sa, daya hannun rike da takardar ta rufe ido ta soma sakin kukan sosai mai cakude da wani irin kishin Mu’azatu da tausayin kanta. Ji ta yi an sanya hannu an zare takardar daga hannunta. A razane ta bude idanunta da suka yi jajawur sai bulbular hawaye suke yi. MAMMAH ce! Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba tare da ta ce da ita komai ba ta juya ta fita da takardar a hannunta. Karshen tashin hankali Hafsat ta shige shi. Ba ta yi niyyar gayawa Mammah zancen nan daga bangarenta ba. Ta sanya a ranta ko ta kama za ta sani, to ba daga gareta ba. Ba ta da karfin gwiwar rungumar ganin halin da Maman nasu za ta fada a dalilin sakinta. Kuka ya dawo sabo a gare ta, a wannan karon ba kanta kadai ta ke yi wa kukan ba, har da Mamman
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG