AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 



Ya kare da cewa, ita din abar so ce ( a darling ) a zuciyarsa. Halayenta ababen yabo ne. A zamansa da ita ba ta zalunce shi ba. Rauninsa guda daya ne yana son Mu’azatu , kuma muddin yana aurenta iyayensa ba za su taba bari ya auri Mu’ azatu ba, da ya kasance kuma son da yake yi wa Mu’azatun ya rinjayi wanda yake yi mata sai ya zabi ya samu Www.bankinhausanovels.com.ng Mu’azatun ita ya rasa ta… Wannan ya isa ya nuna in har ita mai tsinkaye ce ta yarda ta amince da cewa Abdul’azeez ya fi son Mu’azatu a kanta. Koda yana sonta a yanzu bayan aurensu, son bai kai koda taki daya na wanda yake yi wa Mu’azatu ba…… Wani kuka ne ya taho mata da karfinsa, ta kai hannu ta toshe bakin don hana masa fitowaamma hakan ya gagara saboda karfin sa, daya hannun rike da takardar ta rufe ido ta soma sakin kukan sosai mai cakude da wani irin kishin Mu’azatu da tausayin kanta. Ji ta yi an sanya hannu an zare takardar daga hannunta. A razane ta bude idanunta da suka yi jajawur sai bulbular hawaye suke yi. MAMMAH ce! Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba tare da ta ce da ita komai ba ta juya ta fita da takardar a hannunta. Karshen tashin hankali Hafsat ta shige shi. Ba ta yi niyyar gayawa Mammah zancen nan daga bangarenta ba. Ta sanya a ranta ko ta kama za ta sani, to ba daga gareta ba. Ba ta da karfin gwiwar rungumar ganin halin da Maman nasu za ta fada a dalilin sakinta. Kuka ya dawo sabo a gare ta, a wannan karon ba kanta kadai ta ke yi wa kukan ba, har da Mamman

nasu, wadda ta dauki burin duniya ta dora wa auren nan. Da wahalhalun da ta sha kafin tabbatuwarsa, to amma me?
Wani sako can na zuciyarta wanke Abdul’ azeez yake yi da farin sabulu mai kamshi da cewa shi ma mutum ne kamar kowa, yana da hakki kan abin da zuciyarsa ke so wanda ba shi ya dorawa kansa ba,wanda Mammah ta yi amfani da power dinta na UWA ta danne masa. A kan

me ba za a barshi ya auri abin da ransa ke so ba don yana aurenta? Dole ya kalle ta a matsayin ‘barrier’ ga samun farin ciki a rayuwarsa da cikar burinsa na mallakar abin da yake so.
Tana cikin wannan tunanin ta ji an turo kofar dakinta. Mammah ce ta dawo, Daddy na bayanta. Da sauri ta mike zaune a kan gadon ta kuma sunkuyar da kanta, ba ta da guts na kallon fuskokinsu. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Tun yaushe ya ba ki wannan takardar?’”’ Daddy ya tambaya cikin taushin murya.
Kara dukar da kai ta yi, kafin ta soma magana cikin sanyin murya. “Daddy ba laifinsa ba ne, Daddy da amincewa ta……”. Ta soma shesshekar kuka, “Wallahi Daddy mun rabu ne ba don ba ma son juna ba, sai don kowannenmu ya kasa jure hali da dabi’un dan uwansa. Ku yarda haka kaddara ta tanadar mana…”. Ta karanto musu sak! Yadda Abdul’ azeez ya dade yana karanta mata.
Mammah ta saki baki tana kallonta idanu a waje. Daddy ya ce, “Duk na ji, amma wace yarjejeniya na ji ana magana a cikin takardar?”
Wani kugi Hafsat ta ji cikinta ya saki, tun farko me ya kai ta fiddo takardar nan a cikin gidan nan?
Don me ba ta barta a cikin jakarta ba har illa masha Allahu?
Wata tsawa Mammah ta daka mata saura kadan ta saki fitsari a wandonta, “Za ki bude baki ki gaya mana komai, ko sai na saba miki Hafsat?”
Kuka ta shiga yi sosai, amma ta ki fadin abin da suka tambayetan, maimakon hakan afuwa ta ke nemawa Abdul’azeez daga gare su. Saukowa ta yi daga gadon ta rarrafa ta kama kafafun Daddyn. “Don Allah don Annabi Daddy kada kuyi fushi da shi, ka aura wa Yayanmu Aunty Mu’azatu, Daddy yana sonta sosai.. amma Mammah ta ki ganewa”’An zo wurin”’. Tsohon Ambassador Hamza Atiku ya fada a ransa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hannu ya sa ya dago ta ya mikar da ita tsaye, sannan ya rungume ta abinda bai taba yi ba. Ya dago fuskarta cikin tafukan sa biyu yace. “Daina kukan nan haka Hafsa, zan aura masa ita. Amma sai kin min alkawarin ba sauran alaka tsakaninki da shi, kuma za ki maida hankali a karatunki. Mammanku ta gaya min tunda aka koma ko sau daya ba ki je ba”. Ya kama hannunta zuwa bakin gadonta suka zauna tare. Atlast! Alkawarin da ta dauka na taimakawa Yayan ya samu Mu’azatu zai cika. Ba ta damu da duk wani alkawarin da za’a ce ta yi ba. A shirye take da daukan su komai tsaurinsu indai Abdul’azeez zai samu cikar burin sa. Bata zame masa barrier din da yake kallonta ba. Daddy ya dube ta sosai cikin jajayen jikakkun idanunta.
“Alkawuran da zaki yimin su ne. Na farko, no phone calls between you and him (babu kiran waya tsakaninku). Zan canza miki layi, in zai yiwu ma ki hakura da wayar ki dinga amfani da ta Mamanku in kina son yin kira Jimeta ko su Isma’el. Na biyu za ki rungumi karatunki ki fito min da ‘A’ ko ‘B’ a kowanne course . A karshen kowacce semester kuma ina so in ga CGPA ya haura (4). Na uku, ko ya zo gidan nan babu wata alaka tsakaninku bayan irin taku ta baya, daga gaisuwa ban ce ki zauna inda yake ba. In kika yi min wannan alkawarin ni kuma ba Mu/’azatu kadai ba, ko mata uku bayan ita zan biya masa sadaki inyi masa lefe ya aura. Kin yi alkawari?”
Daga masa kai ta yi da sauri, wasu hawayen na yo mata ambaliya. Maimakon ta yi farin ciki ta sauke nauyin da ke kanta, sai ta ji duniyarta ta what ever Daddy is saying (ko me Daddy ke fada) wanda ba duka ta ke fahimta ba he mean good to all of them (yana nufin abu mai kyau garesu duka) . Kuma hakan shi ne kwanciyar hankalin Abdul’azeez. As long as Abdul’azeez ya samu kwanciyar hankali da cikar burinsa a kan Mu’azatun nan itama nata hankalin zai kwanta, za ta kasance cikin farin ciki a sabuwar Www.bankinhausanovels.com.ng rayuwarta. Duk da sunanta ya canza daga budurwa zuwa bazawara tana da yakinin zamanta tare da su zai mantar da ita duk wata rayuwa da ta yi tare da Abdul’azeez. Karatun da ta ki jini shi zai zamo abin yinta. Kafin Daddy ya mike Mammah ta juya ta fice ta barshi a dakin. Ko kafin ta kai dakinta ta ji wata irin hajijiya na kwasarta. Idanunta duhu ya mamaye mata su. Shi dai Daddy sai salatin Baba Azumi ya jiyotana tallafe da Mammah wadda ta
kusa yanke jiki ta fadi a kofar dakinta, ita kuma ta sanyo kai za ta fito daga dakin ne bayan ta gama mata shara. Da gudu ya fito, Hafsat na rufa masa baya. Ciccibarta ya yi ya ce Hafsat ta kira Salisu, Azumi ta dauko mata mayafi. Tare duka suka dunguma zuwa clinic mafi kusa da su a nan Asokoro wato ‘Diff Hospital’ wanda iyalin gidan ke amfani da shi kan lalurorin lafiyarsu.

*******

Jirgin ‘Emirate’ ya sauke Barrister Abdul’ azeez Hamza Atiku da samarin kannensa guda biyu masu tsananin kama da shi a filin jirgin saman Abuja. Zaratan matasan sanye suke cikin mabanbantan sittiru daidai da ra’ayin kowannensu. Kamanninsu daya a fuska da yanayin kirar jiki, sai dai halayya da dabi’a kowanne da irin nasa. Tun tali-tali duk mai bibiyar labarin nan zai fahimci cewa Abdul’azeez mutum ne mai ware kansa daga al’umma, mai alienated life, mai odd behaviours , mai extra-ordinary _ personality, mai naci a kan abinda ya sa gaba har sai ya kai ga cimmasa, mai wuyar sha’ani wanda ba’a sauyawa akida. Mai tafiyar da rayuwarsa a tsaka-tsaki; wanda bai damu da rayuwar hutu da jin dadi ba, wanda ya hora kansa da rayuwar gwagwarmaya irin ta kowanne dan Nigeria a lokacin da iyayensa da kannensa ke cikin daula. Wanda ya baiwa goal attainment matsayi mai muhimmanci cikin rayuwarsa. Bai hutar da kansa ba, bai samu kwanciyar hankali ba, sai da ya zamo abin da yake son zama a rayuwarsa. Yayin da Isma’el Dakata ya kasance totally op
posite na komai da ya danganci dan uwan nasa, shi mai son jama’a ne, mai son mu’amalolinsu, mai faram-faram, mai jan kowa a jiki, dan hutu kuma mai son rayuwa ta hutu da jin dadi. Bai san wata rayuwa ta daban ba bayan wadda ya taso a cikinta. Wanda ba ya zurfafawa a ra’ayi balle ya sanya wani abu cikin ransa har ya hana shi sukuni. Shekaru biyar cif Abdul’azeez ya bai wa Isma’eel. A halin yanzu ya kammala karatun digiri na farko daga jami’ar ‘Harvard’ yana da shekaru ashirin da bakwai, yayin da Abdul’ azeez ke cikin talatin da uku. Www.bankinhausanovels.com.ng
Usman kuwa, ya bambanta da su ta wurare da dama, dattijon hali gare shi da wani_ irin manyance. Sun girme shi da shekaru rututu don yanzu ne yake shiga ashirin da biyar amma in ka ji shi yana musu fada da nusasshe su al’amura na rayuwa tsammani za ka yi shi ne babba. Ba shi da ra’ayi nasa na kansa, shi dai duk abinda iyayensa ke so shi ne abin binsa. Watakila hakan ne dalilin da ya sayo masa kauna ta musamman a zuciyar iyayensu. Watakila kuma rashin kwaramniyarsa ne, watakila kuma duk ba hakan ba ne,; martaba umarninsu da yake yi ne a duk abin da suke so daga gare shi suna gani ko basa gani. Wadannan su. ne manyan ‘ya’yan tsohon Ambassador
Hamza Atiku Dakata. Salisu ya shiga loda jakunkunansu a ‘booth’ din mota ko kafin ya gama suna cikin motar, tsakanin Usman da Isma’el ne kawai muryansu ke tashi a cikin motar ana zuba yaren Dutch. Shi gogan yana kujerar mai zaman banza a gaban motar, wayarsa ce a hannunsa wadda ta kwashe dukkan
hankalinsa shi kadai ya san me yake yi a cikinta. Ga dukkan alamu kasar da suka fito ta amshe shi a ‘yan kwanakin da ya yi a cikinta bayan ya fito daga America. Mutum ne shi da ko yaya ya samu canjin wheather sai jikinsa ya nuna, in sanyi ne ko zafi duk za ka ga ya canza, musamman kasancewarshi ba ma’ abocin fita kasashen Turai ba. Yanzun da ya dan fita sosai choculate fatar jikinsa ta kara canzawa. Farar shadda ce sol a jikinsa mai tsananin taushi (hilton), kanshi babu hula, ya rage sumar kansa gabadaya da ya dauki lokaci baiyi hakan ba, yanayinsa da kalar fatarsa sai ya zama tamkar ‘Egyptian’ masu duhun fatar cikinsu har tsayi da rashin kaurin jikinsa. Zarazaran gashin idon sun kara kwanciya luf a saman idanunsa. Karan hancin ya kara fitowa sosai ya tsaya kyam a tsakiyar fuskarsa. Da ka ganshi ka ga Ambassador Hamza Atiku a zamanin kuruciyarsa.
Isma’e]l suna tafe a hanyar shiga Asokoro ya kasa shiru da wannan canzawar da Yayan nasa ya yi cikin kwanaki kalilan. Ya ce, “Yaya Azeez, wannan idan da kai muka zauna a Belgium na rantse da ba ka dawo ba tare da Belgian mace ba, da Hafsat ba ta samu wannan gemdin da sauki ba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Usman ya ce “Saboda me ka ce haka? Saboda ita ka dauketa mummuna ko? To a kunnenta”
Dariya ya yi, ya ce“ni dai ban ce ba. Amma dai tayi sa’a ta ko’ina ka sani.Wannan idan ka yi wata uku ai Hafsat ba za ta gane ka ba”.
Shiru ya yi musu kamar ba ya jinsu, sai dai ambatar sunan Hafsat da suke ta yi haifar da fargabahadi da faduwar gaba yake ta yi a cikin kirjinsa. Maimakon Salisu ya shiga Asokoro, sai ya dauke kan motar ya yi wani titin daban. Isma’el ke tambayarsa ina zai je? Salisu ya yi shiru. Ya kara tambayarsa, sai ya ce, “Asibiti”. A matukar gajarce.
Sai ganinsu suka yi ya shiga asibitin ‘Diff’ da su ba tare da wani gamsasshen bayani ba.
Mamaki hadi da fargaba ya soma ziyartar kowannensu. Amma ko fitowarsu daga jirgi sun yi magana da Daddy. Bai ce da su wani cikinsu babu lafiya ba. Bai ce da su wani na asibiti ba. Salisu lambar daki kawai ya gayawa Usman ya ci gaba da zamansa a motar. Da sassarfa suka karasa cikin asibitin suna duba dakunan har suka zo inda Salisu ya ce musu. Asibitin sananne ne a gare su don tun dawowarsu Nigeria da shi Daddy ke ta’ammali. Hannayensu su duka ukun suka daura a kan ‘handle’ din kofar dakin suka murda a tare tare da kutsa kai, wani na ture wani.
Maryam Dakata ce a kwance, robar karin ruwa sakale da hannunta. Idanunta biyu ba barci ta ke yi ba, sai dai idanun nata sun kankance. Daddy na zaune gabanta a kan farar kujera rike da hannunta marar allurar karin ruwan, daga can karshen dakin Hafsat ce a kan darduma tana sallah da katon hijabi a jikinta. Isma’el da Usman hada baki suka yi suka ambaci sunanta da dan karfi. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Mammah!” Tare da fiddo kyawawan idanunsu waje.
Abdul’ azeez jingina ya yi da kofar da ya rufe ya runtse idanunsa, ya yi catching numfashinsa heavily. Ko da ya bude idon sai cikin na Mammansa. Wani irin kallo ta ke masa da ya kasa fassarawa. Daga inda yake tsaye ya gane wadda ke sallah, ya kuma gane wadda ke kwance a kan gadon asibitin. A sannu ya yi lowering gaze dinsa saboda ya kasa jure kallon tsakiyar kwayar idanunta, kuma ta ki sassauta kallon nata a kansa. Ji yake tamkar bulala ta ke zuba masa a cikin jikinsa da wadannan idanun nata wadanda dasu
kadai take ladabtar dasu. Duk kalaman jimantawa da tambayoyin da Usman da Isma’el ke mata bata amsa ko daya ba. Abdul’ azeez din dai kawai ta ke kallo har suka ankara da cewa, kallon da ta ke masa na daban ne ba normal kallo bane ba. Duk sai suka yi shiru suma suka zuba masa idon suna son hango abin da Mammah ke kallo a tare da shi.
Numfashin da Hafsat ke shaka a dakin ta ji yana sauya mata bayan shigowar bakin bazatan nasu da bata san da zuwansu yau ba, yana kawo wani scent mai sanyaya zuciyarta a kullum. Tana jin shigowarsu, tana kuma jin muryoyinsu suna magana da mahaifiyarsu, amma bata ji muryar mamallakin creed -aventus ba sai scent din nasa kadai tunda bata ji yayi magana a wurinba. Ba ta san da wanzuwarsa a dakin ba sai dai feeling na presence dinsa a wurin overwhelmed her. Tangarda ta soma samu a tsakanin kirji da kofofin shakar numfashinta. Da ta yi wata sujjadah sai ta kasa dagowa. Daddy ya juya ya dube shi ya kuma dubi matarsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Kin kafe shi da ido, kin hana shi karasowa. Kin ga Allah Maryama ki daina yafawa kanki tashin hankali nima ki daga mini a kan abin da baki da hurumi a cikinsa. Kin jazawa kanki hawan jini a shekarun girmanki ni ma kina so ki lankaya min’. Fada ya shiga yi sosai wanda ya sa Hajiya Maryam rufe idanunta tare da juya fuskarta daya barin inda su Isma’el ke tsaye. Sun shiga damuwa sosai wadda ta fito baro-baro a kan fuskokinsu. Sannu suke mata a jejjere tana amsawa a hankali. Hankulansu sun yi matukar tashi da jin Mammah da hawan jini, da fadan da Daddy
ke yi wanda ba su san mafarinsa ba balle tsakiyarsa. A sannu Abdul’azeez ya tako zuwa gabanta idanunsa sun rine sun zama jawur kamar gauta, shi ya fahimci fadan da Daddy ke yi; LOKACI BAI BA SHI DAMA _ BA! ABUBUWAN BASU TAFI YADDA YA TSARA SU BA….KOMAI YA DAMALMALE MASA YADDA BAZAI IYA GYARAWA BA… Ta ji komai… ta dauko Hafsat kafin ya dawo. Ya Allah! Yaa Rabbi Sallim!”.
Abu daya ne ba shi da tabbacinsa, Hafsat ce ta gaya mata ya sake ta ko ita ta gane da kanta? Zuciyarsa ta ki amince masa cewa Hafsat ta tari Mammah gaba-da-gaba ta gaya mata. Ita din mai uzuri ce a gare shi. A dalilin sakin da ya yi wa Hafsat Mammah ke kwance a gadon asibiti?
Hannunshi karkarwa yake yi kadan sanda ya kai ya dafa hannunta da Daddy ya cika, ya ce cikin hardewar murya, “San…nu da jiki Mam… mah…”.
Tamkar ya dala mata wuta a kan hannunta haka ta yi maza ta janye abinta. Ta kuma ki dubanshi, rufe idonta ta yi gabadaya don ganinsa na tayar da wani danyen miki a zuciyarta. Ya ji mata ciwo a zuciya da ta ke ta rokon Allah cikin ranta ya yafe masa, kada ya kama shi da laifuffukan da ta ke kallonsa da su, muhimmi shi ne ‘yaudara’ a gare ta a kan budurwa, budurwar ma wata shaidaniya haduwar bariki, ya tozartata ya yaudare ta ya wulakanta ta a kanta. Sai ganin hawaye suka yi yana bin idonta. Www.bankinhausanovels.com.ng Abdul’azeez ya kara kidimewa, ya rude ya rasa inda zai sa kansa, ya tabbata wadannan hawayen na zuba ne adalilinsa ! Hannunta ya kara kamawa jiki na
rawa murya na rawa, alamu na shi ma gab yake da ya zubda nashi hawayen ya ce.
“Let me explain Mammah….. Please …….!!! Yana fadi yana mai hada hannayensa wuri guda.
Girgiza kai ta shiga yi, a nutse ta ce da shi. “ It is too late! Isma’el ku je gida, I want to be alone. Amma Hafsat ta zauna”’A sanyaye Isma’el ya ce. “Ok Mammah”. Ya russuna ya sumbaci goshinta ya dafe goshin da hannun damansa, sannan ya ce. “Get well soon Mum, please. I have a lot for you, without you the house will be boring”. (Ki warke da wuri Uwata, na zo miki da labari mai yawa. In babu ke gidan zai zama babu dadi).
Murmushi ta yi ta lumshe idanunta, dadin haihuwa da yawa kenan, in ba ka ji dadin daya ba za ka ji dadin daya. In daya ya bakanta maka sai daya ya faranta maka. Tana kallonsu suka wuce daya bayan daya, Abdul’azeez na waiwayenta. Ji yake kamar da ya fita din ba zai dawo ya tadda ita a raye ba. Fisabilillahi bai san abin da ya shiga kansa ba tun haduwarsa da Mu’azatu yake aikata shirmen da yake ta aikatawa. Jinsa yake yanzu kamar wanda aka tasar daga nannauyan barci. Tun satittikan da suka gabata kuma komai da ya danganci Mu’azatu na yin nesa-nesa da zuciyarsa. Hafsat na mamaye muhallin da dukkan kason dake cikin zuciyar da Mu’azatu ke zaune. Ya kasa fassara yanayin yadda ya tsinci kansa da yin tozali da ita a dakin duk da bai ga fuskarta gabadaya ba. The feeling is very emotional.

********

Tafe suke cikin kwazazzabo cikin farar mota

‘hilux’ mai hawa kowanne irin tudu da kwari cikin wani kauye wai shi Kufana a Southern Kaduna. Mu/’azatu na ta korafi, Regina ta ce, “Dadina da ke wutar ciki Mu’azatu, garaje da rashin hakuri. Tunda na ce miki matsala aka samu kuma zai gyara ki adana min wannan rashin hakurin naki har mu isa”’.
Dole Mu’azatu ta yi shiru ba don ta so ba. A ganinta Regina tana daukar al’amarinta da wasa don ba ita ta fada cikin abin da ta fada ba. Har suka iso karkashin wata bishiyar kanya nesa da wani hawan dutse. Regina ta faka motar. Tare suka fito ta sa mukulli ta rufe motar, fili ne fetal ba gida gaba ba gida baya, sai wani dogon dutse a tsakiyar filin. Wannan dutsen Regina da Mu’azatu suka nufa har suka iso gabansa, kowacce ta tattare zani suka fara hawa dutsen nan kamar kadangaru daya na zamowa daya na tallafo ta har suka iso bakin wani dogon kogo na rarakakken dutse, Mu’azatu takalmi, dankwali da mayafi duk a hannu saboda wahala, har hawaye ta ke yi. Zuwanta wannan wajen na biyu kenan bayan Regina ta ce in ka zo sau daya ba ka kara dawowa bukatarka ta gama biya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haduwarta ta farko da Abdul’azeez Dakata a ofishin mahaifinta ta fara sonsa kamar ta ciro rai ta ba shi. Ba irin kyautata masa da ba ta yi ba don ya so ta, bata taba tunanin neman soyayyarsa ta wata hanya bayan kyautatawa ba. Amma sai ya bada mata kasa a ido, ta hanyar nuna mata shi babu wannan a gabansa, yana da abin da ya kawo shi ‘Law School’ ta yi hakuri ya ci gaba da bata

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *