BA SONTA NAKE BA CHAPTER 15
FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Zaune suke a falonta suna ta hira da qawarta Hafsat wadda ta zo gidanta a yau. Zara ce take ta ba qawarta labarin encounter dinta da Ruqayya a ‘yan kwanakin nan yayinda Hafsat take ta kwasar dariya. Zara tace “wallahi bestie gani nake yi kamar Ya Farouq ya fi son ta saboda ta haifa mishi baby” Hafsat tayi dariya tace “bestie you are very funny I swear, zan iya rantse miki Ya Farouq ya fi sonki, ni mamaki ma nake yi yadda har yake qoqarin kamanta adalci a tsakanin ku domin kuwa its not easy at all” Zara ta turo baki tace “how I wish ma babu ita a rayuwar shi kwata kwata, da kullum yana nan. His presence alone gives me joy, I am so happy yau zai dawo” Hafsat tana dariya tace “now I understand cewa you are obsessed with Ya Farouq” Zara tana dariya tace “call it anything babes, i just can’t live without him” Kafin Hafsat tayi Magana ne wayar Zara tayi ringing. Ko da ta duba sunan Farouq ta gani. Murmushi tayi tare da fadin “kamar ya san maganar shi nake yi” Hafsat tana dariya. Ko da ta amsa wayar yanayin yadda ta ji muryar shi ne yasa hankalinta ya dan tashi. Ji nayi tace “Ya Farouq are you okay?? you sound a bit low” A dayan bangaren ajiyar zuciya yayi yace “Junior is ill, he was admitted jiya daddare” gani nayi Zara ta zaro idanuwa tare da fadin “subhanalillah, I am on my way” Bayan ta kashe wayar ne ta miqe tare da fadin “bestie Junior babu lafiya and I think its serious” Hafsat tace “subhanalillah, dauko veil dinki mu je”. CENTRAL HOSPITAL Tsaye yake tare da Dr. Zainab wadda ta kasance head din Paediatrics na asibitin. Dr Zainab is extremely good domin kuwa ta san aikin ta sossai. Junior wanda har suma ya dinga yi a yanzu ya samu bacci. Ruqayya ce zaune a gefen shi yayinda su Hajjaju suke zaune a waiting room hankalin su a tashe. Dr Zainab ce tace ma Farouq “Sir I am going to run some few tests and get back to you” Farouq yace “thanks doc” Dr Zainab ta kalli Ruqayya tace “please idan ya farka, ki bashi abinci ya ci” Ruqayya tace “okay doctor” Bayan ta fita ne Farouq ya matsa wurin Ruqayya wadda take ta share hawaye ya riqo hannun ta yace “hey relax, he will be fine kin ji?” girgiza kanta tayi. Farouq ya shafa kan Junior sannan yayi mishi kiss a goshi yace “Insha Allah you are going to be fine my champ” Su Hajjaju dai ganin likita ta fita ne yasa suka shigo. Aliya ce ta rungume Ruqayya wadda take ta zubar da hawaye. Mamy ta kalli Farouq tace “me ake ciki ne? ya yanayin jikin nashi?” Farouq yayi musu bayanin halin da Junior yake ciki. STORY CONTINUES BELOW ********** Zara ce ta qwanqwaso qofar dakin ta shigo tare da qawarta Hafsat. Bayan sun gaida kowa a dakin ne ta nufi wurin Farouq wanda yake zaune yana kallonta tun lokacin da ta shigo. Gani nayi ta duqa tayi mishi kiss a kumatu sannan ta shafa fuskar shi tace “Ya Farouq how is he?” Yayi murmushi yace “he will be fine, thanks for coming baby angel” Zara tayi murmushi tace “Allah ya bashi lafiya” ta kalli Ruqayya wadda take ta dalla mata harara tace “Anty Ruqy ya mai jikin?” Ruqayya tace “Alhamdulillah” yayinda take ta hararar ta. Zara tana nan a gefen Farouq yayinda take riqe da hannun shi. Hajjaju kuwa sai kallon Ruqayya take yi wadda take ta dalla ma Zara harara har a ranta tana fadin “aikin banza, wannan yarinyar ai dole ta sace zuciyar shi” Junior ne ya farka cikin kuka wanda ya tada hankulan su gaba daya, babu wanda bai yi qoqarin lallashin shi a dakin ba amma yaro kamar ma ziga shi ake yi. Zara wadda bata gwada sa’ar ta a kan shi ba ce tace “Anty Ruqy dan bani shi in gani” Ruqayya wadda take kallon Zara cikin rashin fahimta ne tace “bar shi kawai” Farouq ne yace “let her try mana” Ruqayya tana hararar Zara ta miqa mata Junior. Aikuwa kamar dama jira yake yi Zara ta dauke shi sai gani nayi ya daina kuka yayinda yake ta kallon ta. Ita kuwa Zara tana rungume da shi yayinda take ta yi mishi wasa. Gaba daya dakin anyi mamaki musamman Ruqayya. Mamy ce tace “dama dai yara suna son ki Princess” Sadiq ne yace “qila sun san tana son su ne itama shiyasa” Farouq dai kallonta yake yi yana murmushi yayinda Hafsat ta boye dariyarta na wani mugun kallon da Ruqayya da Aliya suke yi ma qawarta. Hatta abincin ma Zara ta bashi domin kuwa ya qi amincewa Ruqayya ta bashi. (Ni kuwa nace dama dai bai saba da ita ba tunda wurin Nanny yake zama) Zara kuwa cikin siyasa ta bashi wanda bayan ya cinye ne ya koma bacci yayinda ta kwantar da shi bisa gadon ahankali sannan ta shafa kanshi tace “get well soon my dear” Gani nayi Farouq yana latsa wayar shi, bayan ya gama ne ya kalli Zara wadda wayarta tayi qara alamar an aiko mata da message. Ko da ta duba sunan shi ta gani. Da sauri ta bude ta ga saqo kamar haka: “You look cute with Junior, Can’t wait to see you become a Mom. I love you” Gani nayi ta dago kai da sauri ta kalle shi tana murmushi yayinda ya kashe mata ido daya. Ruqayya wadda ta kula da su ji tayi kamar ta mutu don baqin ciki. Gani nayi ya miqe ya kalli Ruqayya yace “hey bari in je in duba patients dina” ya kalli su Mamy yace “I will be back” ************ STORY CONTINUES BELOW Gab da sallar la’asar ne su Mamy suka shirya komawa gida wanda suka yi alqawarin dawowa bayan magrib don duba Junior. Dayake Hafsat ma ta tafi akan zata dawo tare da Mukhtar anjima sai Zara ma ta miqe tace “bari in bi ku Mamy tunda dama da motar bestie muka zo” Bayan sunyi sallama da su Hajjaju ne suka fito. Gani nayi Zara ta kalli Sadiq tace “Ya Sadiq bari iyi ma Ya Farouq sallama in zo” murmushi yayi yace “toh madam strategy” Zara ta fashe da dariya. Zaune yake a ofis dinshi yana duba wasu reports ta shigo. Ko da ya daga kai ya kalle ta sai gani nayi yayi murmushi yace “hey beautiful” Zara tana murmushi ta qarasa wurinshi tare da zagayawa ta bayan shi ta kwanto da kanta bisa kafadar shi tayi mishi kiss a kumatu tace “hey Handsome, zan bi su Mamy gida. Na san cewa yau a nan zaka kwana saboda Junior, nima idan mun dawo duba shi anjima sai Ya Sadiq ya sauke ni gida” Murmushi yayi yace “its okay My Baby angel, thank you for taking care of Junior” Zara ta birkita gashin kanshi tare da zagayowa ta zauna bisa cinyar shi tace “you don’t need to thank me, Junior is your son and my son, you love him and I love you so I definitely love him too” Kumatun ta ya ja sannan yace “I adore you my Baby angel” Ta hada goshinta da nashi yayinda hancin ta ya gogi nashi tace “I adore you too my love” Ta miqe tare da fadin “see you later, Allah ya bashi lafiya. Bari in je kafin su Mamy su tafi su bar ni” Haka Zara ta fita ta bar qamshin ta a ofis dinshi wanda yake bala’in so. Gani nayi ya lumshe idanuwa tare da fadin “you are the best thing that has ever happened to me Zara” *********** Farouq yana Zaune a ofis dinshi tare da Dr Zainab wadda ta kawo mishi test results din Junior. Gani nayi yana bin test results din daya bayan daya. Yana kai kan wani report ne na ga hankalin shi ya tashi da har ya miqe tsaye cikin mamaki yace “what??” tuni zufa ta fara karyo mishi. (Wait what??? Me ya gani???🙄) Da sauri ya kalli Dr Zainab yace “did you confirm this at all??” Dr Zainab ta gyara glasses din idonta tace “We had to run the test 3 times Sir because it really got me confused too” Gani nayi Farouq ya runtse idanuwa tare da girgiza kai yace “Ya Salaam” Sakin numfashi yayi tare da fadin “I need to confirm this myself” Dr Zainab ta miqe tare da fadin “its okay Sir” A gaban Farouq ne aka qara tabbatar da result din. Gani nayi ya Kalli Dr Zainab ran shi a bace yace “not a word to the mother” tace “okay Sir” Ko da ya fito daga Lab din fita daga asibitin yayi yayinda zuciyar shi take ta tafasa. Hankalin shi yayi mugun tashi yayinda yake ta tunani kala kala. STORY CONTINUES BELOW Gani nayi ya shige motar shi ya ja ya bar asibitin. (Me ke faruwa ne???🤔) AL-HUSSAIN MANSION Zaune take a falon Mamy tana kallon tashar Zee Tv sai kawai ta gan shi ya shigo cikin tashin hankali. Zara ta miqe ta nufi wurin shi a rude tace “Ya farouq lafiya? Wani abu ya samu Junior ne?” girgiza kai yayi alamar a’a yayinda ya ja ta zuwa kujera suka zauna. Gani nayi ya kwanta kan cinyarta tare da rufe idanuwan shi. Zara ta dafa goshin shi ta ji zafi, cikin rudani tace “Ya Farouq, you are not doing well, let me get you..” Katse ta yayi tare da fadin “I will be fine, just stay here with me” Zara wadda hankalin ta yake a tashe tayi ajiyar zuciya sannan tace “Sorry ya Farouq” yayinda ta dinga shafa kanshi. Tsawon lokaci Farouq yana kwance a kan cinyar Zara wanda yake ta sakin ajiyar zuciya. Zara dai ta tabbatar akwai abinda yake damun shi a yanzu. Gaba daya ta shiga damuwa. Mamy da ta shigo falon ganin Farouq a kwance ne tayi mamaki sossai, kallon Zara tayi tace “ya na gan shi anan kuma? Yaushe ya zo? Junior fa?” Zara wadda take Magana muryar ta qasa qasa ne tace “Mamy kamar stress ne, yace idan ya huta he will be fine but Junior is fine” Mamy tayi murmushi tace “ooh, shine ake magana qasa qasa don kar a dame shi?” Zara tayi murmushi. Sadiq ne ya shigo Falon cikin masifa yana fadin “ke kullum kallon India..”3 Gani nayi Zara ta sa hannu a baki da sauri yayinda tace “ssshhhh” Sadiq wanda ya ga Farouq a kwance ne yayi mamaki. Muryar Zara qasa qasa tace “Ya Sadiq rage murya kar ka tada shi” Mamy wadda take zaune tayi dariya yayinda sadiq ya zaro idanuwa cikin mamaki ya koma kusa da Mamy yana tambayar ta abinda ke faruwa. Mamy tana dariya tayi mishi bayani. Gani nayi Sadiq ya girgiza kai yace “ashe mun shiga uku kenan, bazamu yi magana ba har sai ya tashi” Haka kuwa suka cigaba da Magana cikin rada don kar su tada shi. ********** Gab da magrib ne na ga Farouq ya motsa, ko da ya bude idanuwan shi sunyi Ja. Gani nayi Zara ta dafa goshin shi tare da fadin “Ya Farouq ka tashi? How are you feeling?” Sakin numfashi yayi tare da fadin “I am fine Baby angel, qarfe nawa ne? lets go home” Zara tace “almost time for magrib, besides I thought asibiti zaka koma” Tashi yayi zaune tare da fadin “sai mun je gida first” Muryar Mamy suka ji tace “yanzu zamu iya yin magana normal tunda ya tashi ko?” STORY CONTINUES BELOW Zara ta fashe da dariya yayinda Farouq ya girgiza kai yana murmushi ya miqe tsaye ya kalli sadiq yace “let’s go and pray” Bayan sallan Magrib ne Farouq da Zara suka tafi gida. A yau kuwa dukda dare ne haka nan Farouq din ya bar ma Zara ta tuqa su domin kuwa jin jikin shi yayi babu qwari ko alama. (Hmmm… lallai kuwa something is definately wrong🤔) Mamy dai bayan sallan Isha’I ta sa Sadiq ya mayar da ita asibiti don duba Junior. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Dakin shi ta shigo riqe da tray a hannun ta. Farouq wanda yake zaune a kan resting chair din dakinshi yayi nisa a tunani da bai ji shigowar ta ba. Ko da ta ajiye tray din dawowa tayi gaban shi ta tsugunna tare da riqe hannun shi tace “Ya Farouq ga fruit salad just as you like it” girgiza kai yayi alamar a’a. Ajiyar zuciya Zara tayi tace “Ya Farouq I know cewa wani abu yana damun ka, Honestly speaking I am worried seeing you like this” Ta tashi ta zauna gefen shi tare da hugging dinshi tace “Your problem is my problem, even if I may not solve your problem I might be able to comfort you” Tayi mishi kiss a kumatu tace “please share with me” (Ni kaina na matsu in ji abinda yake damun Farouq🤨) Ajiyar zuciya yayi tare da runtse idanuwan shi ya bude. Farouq dai bai so ya fadi ma Zara ba amma a dalilin matsa mishi da tayi ne na ga ya dafe kai sannan yace “Junior is suffering from sickle cell anaemia” Ji nayi Zara tace “what???” (Nima nace wait what???🙄🙄) Cikin mamaki ta cigaba da fadin “you mean sickler ne, how is it possible Ya Farouq? I thought..” Katse ta yayi tare da fadin “I am AA and she is AS, Junior is SS??” Yayi maganar cikin tambaya. Ya ja numfashi sannan yace “I just.. I just.. I am confused.. What the hell is going on? Does it mean Junior…” Kasa qarasa maganar shi yayi yayinda yayi resting bayan shi a kujera tare da runtse idanuwan shi cikin qunar rai. Zara wadda take cike da mamaki ta dafa shi tace “Ya Farouq now I understand why you are worried. Gaskiya AA and AS can never result to SS, so its either junior is not yours or akwai mistake a Genotype dinku” Ta girgiza kai tace “and I definitely won’t believe the latter” Farouq yayi ajiyar zuciya wanda a yau dinnan yayi sun fi dari yace “does that mean Junior is really not my child?? Toh na waye?? Why would Ruqayya betray me like this?” Zara dai shiru tayi tana tunanin kamar ta taba jin maganar a wani wuri.1 Shiru ne ya ratsa dakin na kusan tsawon mintuna biyar yayinda suka tsunduma cikin tunani. STORY CONTINUES BELOW Gani nayi Zara ta girgiza kai tare da riqo hannun shi tace “Ya Farouq I think there is a way to confirm your doubt” Kallon ta yayi cike da mamaki yace “tell me” kai tsaye tace “Paternity DNA test” (Hehehehe… Riqe wuta Zara🤣) Gani nayi ya shafa kan shi tare da fadin “oh my goodness, why didn’t I think of that?” Zara tace “I guess its because you are confused ne, I am sorry” Janyo Zara yayi jikinshi yace “thanks My Baby angel, i really need to find out even though its painful” A haka dai cikin siyasa Zara ta sa Farouq ya sha Fruit Salad din yayinda take ta fadi mishi kalamai masu sanyaya rai. ********** Ko da suka kwanta bacci Zara ta dade tana tunani. Qoqarin tunowa take yi inda ta taba jin cewa yaron Ruqayya ba na Farouq bane. A haka kuwa har bacci ya kwashe ta. Shi dai Farouq idanuwan shi biyu domin kuwa ya kasa yin bacci kwata kwata saboda tsananin tashin hankali. Wuraren qarfe biyu na dare Zara tana kwance a jikin Farouq tana bacci sai kawai ta sa ihu tare da maqale shi tana kuka tana fadin “wayyo Allah kai na..” Farouq wanda ya razana matuqa ne ya rungume ta yayinda yake qoqarin kwantar mata da hankali. Ji nayi yace “hey baby angel what is it?” Cikin kuka Zara tace “Ya Farouq please help me, kai na” yayinda ta jiqe da zufa. Farouq yace “ssshhh, relax My baby angel. I am here” yayinda yake shafa kan ta. A hankali Zara ta samu natsuwa amma fa har yanzu kuka take yi. Farouq wanda yake rungume da ita ne yace “Baby angel what happened? Mafarki kika yi?” Zara wadda take sheshekar kuka tace “Ya Farouq wannan ba mafarki bane, I really felt it” yace “okay tell me what happened” Zara tace “Anty Ruqy ce zaune a dakinta tare da qawarta suna hira, shine na ji su suna maganan wani Musty..” Gani nayi Farouq ya zaro idanuwa cikin mamaki yace “Musty??” Zara wadda take kuka tace “ka san shi ne?” ya girgiza kan shi alamar a’a sannan yace “go ahead” Zara ta cigaba da fadin “shine na ji suna maganar cikin Ruqayya ba naka bane wai nashi ne” ta ja numfashi sannan tace “bayan nayi confronting dinsu and was about coming down the staircase she pushed me and I hit my head” Gani nayi ta qara fashewa da kuka yayinda ta dafe kanta wanda yake azabar ciwo. Farouq wanda jikinshi yayi sanyi gani nayi ya matse Zara a jikinshi yayinda ya runtse idanuwan shi. Babu abinda yake fadi a ranshi sai “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un” A yanzu kuwa Farouq ya hada pieces na puzzle din. Ji yayi Zara tana fadin “Ya Farouq it felt so real, I am scared” Farouq yace “ssshhh, it was just a dream my baby angel. i will always be there for you. Insha Allah nothing will happen to you, relax” Zara dai sai da Farouq ya bata magani ta sha domin kuwa jikinta yayi zafi sossai, ga kuma kanta da yake ta azabar ciwo. A haka dai ya lallabata da qyar ta koma bacci. Yana shafa kanta ne yayi mata kiss sannan yace “Allah sarki my Zara, this is definitely the memory you lost” Farouq dai komawa yayi kan resting chair dinshi ya zauna yayinda ya dafe kanshi wanda yake yi mishi azabar ciwo. Gaba daya ji yayi rayuwar shi ta birkice, mamaki yake yi as to how bai yi realizing all this tuntuni ba. Ajiyar zuciya yayi tare da fadin “does she think she could betray me and get away so easily?” ya girgiza kai sannan yace “you are soo gonna pay Ruqayya” *********** CENTRAL HOSPITAL Farouq ne zaune tare da daya daga cikin Medical laboratory technicians na asibitin mai suna Kennedy wanda zaiyi running mishi DNA test.+ Kennedy yayi mishi alqawarin kawo mishi result din kafin yamma. Farouq ya ja mishi kunne akan baya so a samu kuskure ko alama wanda kennedy din ya tabbatar mishi da cewa zai kawo mishi correct result. Kennedy ya miqe zai fita ne Ruqayya ta shigo ofis din. bayan ya gaishe ta ne ya fita. Farouq wanda yake zaune a kan kujerar shi kallon ta yayi yayinda ran shi yake a bace. Ruqayya wadda itama ran ta yake a bace ne tace “Honey meyasa tun jiya ina ta kiran ka a waya baka dauka? asali ma tunda ka bar asibitin nan baka dawo ba. Ka manta cewa ka bar Junior a asibiti babu lafiya? You couldn’t even come to check on him this morning. Is Junior’s wellbeing not important anymore?” Farouq wanda ya qura mata ido ne yake mamaki. Ranar daren farkon su ya tuno da yadda tayi mishi qaryar cewa anyi raping dinta.. Ganin hankalin shi baya tare da ita ne tace “Honey i am talking to you” Gani nayi yayi dan murmushin takaici sannan yace “I had a serious headache jiya, how is Junior doing?” Cikin rashin yarda tace “ko kuma Zara ta hana ka fitowa ba?” Yana danna laptop dinshi Yace “hakan ma ba laifi bane ai” Ruqayya ta bata rai sannan tace “dama ina so in tambaye ka, wai me yake damun Junior ne?” Farouq yace “just fever” Tayi ajiyar zuciya tace “toh amma yaushe za’a sallame shi, ni na gaji da zaman asibitin nan” Farouq ya kalli agogo tare da fadin “zuwa yamma insha Allah” ya miqe yayinda ya cigaba da fadin “bari in je in duba patients dina I will come check on Junior” ********** Ko da Farouq ya shiga duba Junior ya tarar har Mamy ta zo, ya zauna yayi wasa sossai da Junior. Hira sossai ya zauna aka yi da shi sannan ya fita. ******** Da yamma ne Farouq yana zaune a ofis dinshi Kennedy ya kawo mishi DNA test result din. Bayan Kennedy ya fita ne na ga Farouq riqe da envelope din yana ta juyawa. Tsawon mintuna biyar yana kallon envelope din yayinda yake ta tunanin abinda zai gani. Gani nayi yayi ajiyar zuciya sannan ya bude. STORY CONTINUES BELOW Bayan ya karanta ne ya girgiza kai tare da yin wani murmushin takaici yace “Negative, its certain that I am not Junior’s Dad, what a betrayal” Numfashi ya saki tare da fadin “Allah ya isa tsakani na da ke”. Farouq ya dade zaune a ofis dinshi yana tunanin irin wulaqancin da zai yi ma Ruqayya. Dr. Zainab ce tayi knocking qofar shi sannan ta shigo riqe da takardun sallaman Junior. Bayan ta zauna ne tace “Sir, the discharge papers. Akwai magungunan da Nurse zata hado. Please ayi qoqari a bi prescriptions din yadda yakamata” Farouq yace “its okay doc, thank you”. Tare da Dr Zainab din suka fita yayinda take ta yi mishi bayanin condition din Junior din wanda a yanzu haka Farouq bai damu da sanin halin da yake ciki ba musamman idan ya tuna cutar shi da aka yi. Bayan ta gama yi mishi bayani ne ya wuce dakin Junior din. Farouq yana gab da shiga dakin da aka kwantar da Junior ne ya ji muryar Ruqayya da Aliya suna hira. Ya dan tsaya bakin qofar don jin abinda suke fadi. (Ni kuwa nace dama ya saba… balle yanzu da dalili🤣) Ruqayya ce tace “Musty ya cika rigima wallahi, wai shi dole sai ya zo ya duba Junior” Aliya tace “toh ki bar shi ya zo mana tunda babu wanda ya san shi. ko da Farouq ya ganshi ai dama a matsayin cousin dinki ya san shi” Ruqayya tace “hmmm, ai duk ba wannan ba, ni fa kamarnin Musty da Junior ya fara daukowa shi yake bani tsoro, kin kuwa san Musty yana ganin Junior zai tabbatar da cewa dan shi ne” Ta gyara zama sannan tace “shegiyar yarinyar nan ma ranan a gidan Mamy sai da ta nemi ta tona mun asiri wai Junior baya kama da mu” Aliya tace “hmmm, ai perfect opportunity kenan kika samu na kawar da ita lokacin da kika turata ta fado daga kan steps dinnan” Ruqayya tayi tsaki tace “wallahi kuwa qawata, da ta mutu lokacin da na huta” Aliya tace “ni dai yanzu shawarar da zan baki idan Musty yayi auren nan ki qyale shi haka nan” Ruqayya tace “wallahi qawata I tried to leave him several times amma na kasa, the thing is I so much love Farouq amma kuma bazan iya barin Musty ba” Tayi ajiyar zuciya sannan tace “yanzu haka babbar matsala ta wannan yarinyar, na kula ta qwace mun Farouq gaba daya… yarinya kamar karuwa??” Tayi maganar cikin tambaya. Farouq wanda yake sauraron su gaba daya jikin shi yayi sanyi. A Yanzu dai ya qarasa confirming komai. Gani nayi ya runtse idanuwa tare da sakin numfashi sannan yayi composing kan shi ya shiga dakin. A razane suka dago kai suna kallon shi. Farouq wanda yake tsaye a bakin qofar cikin mamaki yace “what?? Weren’t you guys expecting me? Ko Magana ta ake yi?” STORY CONTINUES BELOW Ruqayya wadda zuciyar ta take ta harbawa ne tace “ehm, Honey its not that, what are you doing here?” Murmushi yayi yace “na zo in fada miki cewa Junior has been discharged, so pack up. Za’a kawo miki magungunan shi” Ruqayya wadda tayi murna tace “Alhamdulillah dama na gaji da zaman asibitin” Farouq ne yace “zan kira driver ya kai ku gida.. uhm I mean gidan Hajjaju” (What???🙄) Ruqayya ta zaro idanuwa tare da fadin “what?? Ban gane gidan Hajjaju ba” Aliya wadda take sauraron su itama ta cika da mamaki. Farouq yace “sorry I forgot to tell you cewa na dan sa ayi renovating mun gidan, akwai gyare gyaren da nake so ayi mun” Cikin mamaki Ruqayya tace “renovation Honey?? Duka yaushe aka gina gidan?” Yana kallon ta yace “hey, I wasn’t supposed to even tell you, do you want to ruin the surprise ne or what?” Ruqayya dai jin yace surprise sai ta washe baki tana dariya tace “Sorry Honey” Yayi murmushi sannan ya fita. Bayan ya fita ne Aliya ta kalli Ruqayya tace “kina tunanin ya ji mu?” Ruqayya tayi ajiyar zuciya tace “wallahi qawata ban sani ba, but I think da ya ji mu he would have reacted” (Habawa Ruqs…) FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Bayan Sallar isha’I ne ya shigo gidan. Ganin Zara bata main section din gidan ne yasa ya nufi sashen ta domin babu abinda yake so irin ya ji ta kusa da shi. Farouq ya zagaye sashen Zara gaba daya bai ganta ba, wayar shi ya fiddo ya kira ta. Sai da ta kusa gama ringing ne ta amsa cikin sallama. Ajiyar zuciya yayi yace “Baby angel where are you? Na dawo ina ta neman ki” A dayan bangaren ne Zara tace “ina kicin Ya Farouq” Yace “okay I am coming” Tsaye take tana qoqarin garnishing Chocolate Mousse dinta da straw berries. Farouq wanda ya shigo kicin din qarasawa yayi ta bayanta yayi hugging dinta tare da kwantar da kanshi bisa kafadarta yana ta shaqar qamshinta tare da yi mata kisses a wuyan ta. Zara wadda ta lumshe idanuwa tace “welcome Ya Farouq, ina ta missing dinka” Muryar shi qasa qasa yace “liar” Tayi murmushi tace “dagaske, I was missing you so much that I even forgot I was supposed to prepare dinner” Ta dan bata rai sannan tace “I even called you several times this evening and you didn’t pick” STORY CONTINUES BELOW Farouq ya juyo da ita ta fuskance shi yace “I am sorry my love, I had so many things to take care of” tayi murmushi sannan tace “its okay” Strawberry din da tayi garnishing Chocolate Mousse dinta ne ta ga ya sa hannu ya dauka ya fara ci. Hararar shi tayi cikin shagwaba tace “bad manners Ya Farouq, instead of ka jira sai nayi serving tukunna?” Wani ya qara dauka sannan yace “toh wai dama ba nawa bane? Duk daya ne ai idan na cinye a nan” Ganin idan ta qyale shi zai cinye ne yasa ta janyo shi suka zauna a kan kujerun kicin island sannan tace “so tell me, maganar Junior” Farouq ya girgiza kai yace “he is not mine” tana riqe da hannun shi tace “I am sorry, kar ka damu your Zara will give you triplets insha Allah” Farouq yayi murmushi yace “thanks my angel, can’t wait” Zara tana murmushi tace “toh Anty Ruqy fa?” Wannan karon janyo ta yayi ta zauna bisa cinyar shi yace “forget about her, I have plans for her. Yanzu dai daga ni sai ke, that’s how it is going to be” Zara cikin murna ta rungume shi tare da fadin “i am glad Ya Farouq, A dream come true for me” Yana murmushi yace “I love you my Baby angel” Daga nan kuwa ya fara aika mata da saqonnin kisses kala kala wanda ta biye mishi. Ganin Farouq ya fara kashe mata jiki ne ta ankara tare da miqewa da sauri tace “wallahi Ya Farouq bazaka sa kazata ta qone ba” Dariya yayi tare da girgiza kai yayinda ta koma wurin oven don duba kazar da take gasawa. Ji tayi yace “hey” ta juyo ta kalle shi tana murmushi, Yace “I love you very much” kashe mishi ido daya tayi tare da blowing mishi kisses. Ya miqe yana murmushi yace “let me go and freshen up, I will be waiting for my desert tunda ance sai anyi serving dina sannan zan ci” Zara dai dariya ta dinga yi mishi har ya fita. Farouq bai dade da fita daga kicin din ba ne wayar shi ta fara ringing. Zara ta hango wayar akan kitchen Island tace “manta wayar yayi anan..” yayinda ta matsa don daukar wayar ta kai mishi. Ko da ta kalli fuskar wayar ‘Wifey’ ta gani. Ran ta a bace tayi tsaki tace “macuciya kawai” Gani nayi Zara tayi rejecting call din yayinda tayi setting yadda call din Ruqayyar zai dinga tafiya straight to Voicemail idan ta kira shi.2 Ta mayar da wayar ta ajiye sannan tace “sai mu ga yadda zaki same shi a wayar, stupid woman” (Da kyau Zara🤣) ************ Bayan sun kammala dinner ne Farouq ya raka Zara dakinta tayi wanka sannan tayi shirin bacci. Ko da suka dawo dakin Farouq gani yayi Zara ta dauki remote ta canza zuwa tashar Zee Tv. Girgiza kai yayi yace “oh my Goodness, not again” Tana dariya ta kwanta a kan qirjin shi tace “sorry Ya Farouq just thirty Minutes za’a gama” STORY CONTINUES BELOW Ji tayi yace “have you ever been to India?” Tace “nope, amma kuma I’d love to go” ta dago kanta tana kallon shi tace “please Ya Farouq mu je mana. Dama ina son ganin Salman Khan da Ranbir Kapoor…” Kafin ta qarasa yace “what?? Kina nufin wasu gardawan maza zaki je gani?? Aikuwa bazaki je ba” Fashewa tayi da dariya tace “are you jealous??” ya bata rai tare da hararar ta. Kiss tayi mishi sannan tace “babu wanda zai maye gurbin ka a zuciya ta Ya Farouq, I love you so much that I can’t live without you but please take me to India” Murmushi yayi yace “I will take you wherever you want to go my baby angel, as long as I remain your top priority” Ya ja mata kumatu tare da fadin “ki shirya sati mai zuwa zamu je duk qasar da kike so for as long as you want” Cikin murna tace “dagaske??” yace “yes Baby” ihu tayi tare da fadin “you are the best” Aikuwa daga nan ta fara lissafo mishi sunayen qasashen da take so ta je wadanda bata taba zuwa ba. Shi dai Farouq kallonta kawai yake yi yana murmushi domin kuwa ko me Zara take yi birge shi take yi. Tun tana surutu yana ganewa har ya daina ganewa a qarshe ma bakinshi ya tura cikin nata wanda ya sa tayi shiru yayinda suka fada wata duniyar. Tuni ya mantar da ita kallon Indian da take yi, bata ma san lokacin da ya kashe TV din ba. ************* Tunda aka sallami Junior Farouq bai qara bi ta kan Ruqayya ba. Su Mamy dai sun je har gidan iyayen ta sun dubo shi. Ko da Mamy ta tambayi Farouq dalilin da yasa Ruqayya ta koma gida sai cewa yayi gyara ake yi a gidan ta. Asali ma Farouq rufe gidan Ruqayya yayi yayinda masu aikin gidan suke zaune a quarters dinsu. (Nikuwa nace mugu🤣)2 ALHAJI ABUBAKAR BULAMA MANSION Zaune take da qawarta a dakinta inda take ta masifa akan abinda Farouq yake yi mata. Yanzu haka ta kira shi a waya ya fi a qirga amma call dinta suna ta tafiya voicemail. Aliya ce tace “kiyi haquri qawata, maybe he is busy ne” Ruqayya cikin bacin rai ta girgiza kai tace “I don’t think so, a yanzu na tabbatar wannan ‘yar iskar yarinyar ce tayi mishi asiri” Aliya tace “qawata kin tabbata ba wani sirrinki ya gano ba?” Ruqayya wadda ta harzuqa tace “I doubt, da ya gano wani abu ba zai yi shiru ya qyale ni ba” Gani nayi ta miqe tace “you know what? Tashi mu je ki raka ni, yau sai na nemo shi duk inda ya shiga. He has to face me” (Toh fa🤔) *********** Asibitin Farouq suka fara zuwa amma aka ce bai zo ba don haka ne Ruqayya ta tabbatar yana gidan Zara gashi kuma basu san gidan ba. STORY CONTINUES BELOW Dabara ta fado ma Ruqayya ta kira Sadiq a waya ta tambaye shi. Shi kuwa Sadiq ba tare da tunanin komai ba ya fada mata address din gidan. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Tun da suka iso gaban gate din gidan zuciyar Ruqayya ta tsinke. Kallon qawarta tayi tace “anya nan Sadiq yayi mana kwatance kuwa?” Aliya tace “nan ne mana, yanzu wai dama nan ne gidan Zara?? Shine kika bari aka ajiye ta a wannan luxurious mansion din?” Ruqayya wadda take ji kamar ta mutu tace “Wallahi Farouq ya raina mun wayau” Ta girgiza kai tace “mu qarasa mu tabbatar first” Ko da suka shiga suka faka a harabar gidan sai suka koma kamar qauyawa. Daya daga cikin masu aikin gidan ce tayi musu jagora har babban falon gidan inda suka qarasa rudewa. Ni dai gani nayi Ruqayya da qawarta sun saki baki suna qare ma gidan kallo. Ji suka yi mai aikin tace “ku zauna bari in sanar musu zuwan ku” Kafin ta dauki wayar intercom ne Ruqayya tace “bari kawai zan qarasa, I am his wife” Mai aikin dai gani tayi Ruqayya ta haura sama yayinda Aliya ta zauna a nan tana jiranta. Zaune yake a falon shi yayinda Zara take bisa cinyar shi suna shan fruit. Zara ta dauki Grape ta sa a bakinta sannan ta matso da bakinta saitin nashi yayinda ya kama ragowar Grape din da yake bakinta wanda bayan ya gutsira ne sukayi locking lips din juna. A daidai wannan lokacin ne kuwa Ruqayya ta shigo falon. Tsayawa tayi cak tana kallon ikon Allah. Hawaye ne suka fara bin fuskar Ruqayya yayinda ta qarasa shiga falon wanda motsinta ya sa suka juyo. Cikin mamaki Zara tace “Meye haka??” Ruqayya wadda ta share hawayen fuskarta ne ta nuna Zara da yatsa tace “Wallahi baki isa ba, Honey is mine too and you just can’t take him away from me” Farouq wanda yake kallon Ruqayya bai ce komai ba. Zara ce ta sauka daga kan cinyar shi ta nufi wurin Ruqayya tace “ban gane abinda kike fadi ba, Ya Farouq is mine alone plus he was never yours in the first place. Don Allah ki taimaka ki fita mun daga gida” Kafin Zara ta rufe bakinta ne Ruqayya ta dago hannu zata mareta, Zara tayi saurin riqe hannunta tace “don’t you dare try that nonsense” Ruqayya ta kalli Farouq tace “Honey, aren’t you going to say anything?” Farouq wanda yake kallon su yace “Me kike so in ce? for crying out loud gidanta fa kika zo kuma kina zaginta” Ruqayya cikin mamaki tace “meyasa tunda ka tura mu gidan Hajjaju baka zo ba? Na kira wayarka baka…” Kafin ta qarasa maganarta ne Zara tayi dariya tace “isn’t it obvious? He doesn’t want you anymore” Ruqayya wadda al’amarin yayi mata kamar a mafarki tace “shegiya mayya Allah ya isa tsakani na da ke, kin yi ma mijina asiri” Zara wadda take ta dariya ta juyo ta kalli Farouq wanda yake qoqarin boye dariyar shi tace “Ya Farouq please do something” Farouq ya miqe ya nufi wurin su ya janyo Zara jikin shi sannan ya kalli Ruqayya yace “okay you need to leave now” Ruqayya wadda ta fashe da kuka tace “yanzu Honey shine ka sa wannan yarinyar a gidan nan ni ka bar ni a can?” Farouq ya girgiza kai yace “like seriously?” Yayi murmushi yace “lokacin da muke Germany da na fada miki maganar gidan nan me kika ce?” Shiru Ruqayya ta dan yi sannan tace “you didn’t tell me wannan gidan ne ai” yace “kin bani space ne? Besides ko hoton gidan ma fa baki kalla ba, you had a dream house remember?? There you have it even though its mine” Ya bata rai sannan yace “Please leave, I am not ready for this” Ruqayya wadda take ta kuka tace “wai me nayi maka ne Honey?” yace “you tell me” Tana sheshekar kuka tace “Please ko ma menene lets sort it out..” Kafin ta qarasa yace “okay na ji toh zan zo muyi magana, you can go” Ruqayya dai juyawa tayi a guje ta fita tana kuka domin kuwa ji take yi kamar zata mutu don baqin ciki. Zara ce ta Harare shi tace “ban gane Okay ba, wai zuwa zaka yi? Ni fa gaskiya..” Murmushi yayi yace “hey relax, I needed to make her go, Ba abinda kike so kenan ba?” Yayi mata kiss tare da fadin “get ready, we will be leaving tomorrow” Zara tace “Yeeey” tare da rungume shi. Yana murmushi yace “you know what?” tace “tell me” yace “da na ga kuna fada a kai na I felt like a king, I won’t lie to you I enjoyed watching” Zara tana dariya ta ja kumatun shi tace “bad boy” sai kuma ta dan bata rai tace “toh wai Ya Farouq sai yaushe zaka rabu da ita??” Yana murmushi yace “not yet”2 ********** ALHAJI ABUBAKAR BULAMA MANSION Hajjaju ce ta shigo dakinta inda ta tarar da ita tayi tagumi yayinda tayi nisa a tunani.+ A yau wata daya kenan da su Farouq suka yi tafiya. Ita ma Hajjaju jiya ta dawo daga Dubai domin kuwa a kwanakin nan bata samu zama ba. Hajjaju ce tace “wai ni kuwa in tambaye ki, har yanzu ba’a gama gyaran gidan naki bane ko kuwa wani gidan zai canza miki?” Ruqayya tayi ajiyar zuciya tace “wallahi hajjaju ban sani ba, rabo na da Farouq yau kusan wata daya kenan, ko a waya baya kirana” Cikin mamaki Hajjaju tace “shine baki taba fada mun ba?” Tace “toh Hajjau kullum ba kya nan” Hajjaju tayi tsaki tace “dauki waya ki kira mun shi muyi Magana, wannan ai wulaqanci ne” Ruqayya wadda ta fashe da kuka ne tace “ai baya qasar” Hajjaju tace “what? Tare da matar tashi ya tafi kenan? Amma dai kin bani kunya wallahi, ya za’a yi ace ‘yar qaramar yarinya ta qwace miki miji? Aikin banza” Ruqayya tana kuka tace “na shiga uku” Haka dai Hajjaju ta cigaba da masifanta ta tashi ta bar dakin. Ruqayya ta dade zaune a dakinta tana ta kuka. Gani nayi ta janyo wayar ta tana qoqarin kiran Musty ko ta samu sauqi. Musty dai yau sati daya kenan da aka daura auren shi. A yanzu haka tun ranar da aka daura auren nashi bai sake bi ta kan Ruqayya ba. Sai da ta kira wayar Musty sau uku sannan aka amsa. Ga mamakinta kuwa ba muryar Musty din ta ji ba. Muryar Zaheera matar Musty ce ta daki kunnen ta. Ruqayya ce tace “ina mai wayar?” Zaheera tace “baya kusa, da wa nake Magana?” Cikin mamaki Ruqayya ta bi wayarta da ido sannan ta mayar a kunnen ta cikin fada tace “nace ki ba mai wayar, kina da hankali kuwa?” Zaheera ma cikin fada tace “what? A matsayin ki na wa? Who the hell are you?” Ruqayya tayi tsaki cikin bacin rai tace “uwar dan shi” Zaheera wadda take kwance a jikin Musty tayi murmushi tace “done” Dayake wayar tana a speaker phone sai na ga Musty yayi dariya sannan yayi gyaran murya yace “finally kin fada mun gaskiya My Ruqy, dama na dade da sanin cewa Junior yarona ne” Ruqayya tayi tsaki tare da fadin “na fadi hakan ne don in bata haushi, you know he is not yours” Muryar Zaheera ta ji tana fadin “you don’t have to do that Madam, My G-man ya fadi mun komai and I will be glad to have Junior as a member of my family” STORY CONTINUES BELOW Ruqayya cikin mamaki tace “What?” Musty yana dariya yace “abinda ta fada haka ne Ruqayya. Now listen to me carefully, zamu je Honeymoon dinmu gobe, idan mun dawo I will come and take custody of my son. My regards to Farouq” Bai tsaya sauraronta ba ya kashe. Ruqayya dai bin wayar tayi da kallo yayinda ta fashe da wani irin kuka. Gani nayi tana ta birgima a qasa tana ta rusa kuka yayinda take fadin “na shiga uku, what is happening to me??”2 (Toh masoyan Ruqy… ku bata ansa😜) ************* Zara da Farouq kuwa suna can qasashen turai suna ta yawon su abinsu. Farouq dukda baya son yawo hakanan ya haqura domin kuwa Zarar tashi akwai son adventure. Watan su kusan uku kenan suna zagaye qasashe. Soyayya dai an sha ta kala kala. Hotuna kuwa an dauka babu adadi. Farouq dai har gajiya yayi da hoto (kun san Zara da son hotuna) lokutta da dama ma baya sanin ta dauka sai idan yana duba wayar ta ne yake gani yayi ta mamaki. Duk wannan bidirin da ake yi Ruqayya tana can Nigeria tana kallo. Social media pages kamar jira ake yi Zara tayi posting hoto sai ayi ta reposting. A yanzu dai rayuwa tayi ma Ruqayya zafi, ga Farouq yayi abandoning dinta sannan ga Musty din ma ya kufce mata. Saboda tsananin tashin hankali da Ruqayya ta shiga har kwanciya tayi a asibiti. Ko da aka sanar ma farouq rashin lafiyar Ruqayya wasu excuses marar sa kai ya dinga badawa har aka sallame ta kuwa bai waiwaye ta ba. AL-HASSAN MANSION FRANCE Kwance yake a kan cinyar Zara yayinda suke hira a falon su Safa. Yau kwanan su biyu kenan da zuwa France din wanda daga nan zasu koma Nigeria. Zara wadda take ba su Saima labarin zuwan su india ne tace “wai fa har qofar gidan Salman Khan muka je amma Ya Farouq ya hana ni ganin shi” Su Safa suna ta kwasar dariya yayinda Saima tace “ai wallahi kana da gaskiyar ka Ya Farouq, ance fa idan mace tayi tozali da shi shikenan” Farouq wanda yake kallon hotunan Zara a wayarta ne ya zaro idanuwa yace “what? Dagaske?” Zara ta harari Saima tace “wa ya fada miki haka?” Farouq yace “gaskiya yakamata kuwa a kama shi” Su Saima suka fashe da dariya. Marwa ce tace “Ya Farouq duk India fa babu mai kyan shi” Farouq ya bata rai tare da dago kai ya kalli Zara yace “oooh, saboda yana da kyau shiyasa kike son shi??” Fashewa da dariya suka yi yayinda Zara tayi saurin duqowa tayi mishi kiss tace “ko kadan, a duniyar nan babu wanda ya kai ka kyau Handsome” Ya Harare ta yace “liar” tace “dagaske Ya Farouq” ya girgiza kai yana murmushi yayinda su Safa suka cigaba da kwasar dariya. Wayar Zara wadda take hannun shi tayi ringing. Sunan da ya gani ne ya sa ran shi yayi masifar baci. Gani nayi ya tashi zaune fuskar shi a murtuke yayinda ya miqa mata wayar ya miqe. STORY CONTINUES BELOW Zara wadda ta ga ‘My Luv’ a fuskar wayarta ne tayi saurin miqewa ta riqo hannun shi ta tsaya a gaban shi ta amsa wayar tare da sakawa a speaker phone tace “hello My luv” harda kashe mishi ido daya. Farouq wanda yake kallonta cike da mamaki ne ya ji muryar Sadiq a dayan bangaren inda yake fadin “Huh Princess, ina ta kiran ki bana samu. Wanted to remind you please kar ki manta ki siyo mun turaren nan” Gani nayi Farouq ya saki wata muguwar ajiyar zuciya wadda ta sa su Safa suka fashe da dariya yayinda Zara tace “insha Allah Ya Sadiq bazan manta ba, Ya Farouq yana gaishe ka” Farouq ne ya Harare ta yayinda take murmushi. Cikin mamaki Sadiq yace “dagsake??” Zara tana dariya tace “baka yarda bane?” yace “ba haka bane, kawai dai na ga its unusual ne, anyways my regards to him please” Tana dariya tace “insha Allah My luv” yayinda ta qara kashe ma Farouq ido daya. Bayan sunyi sallama ne ta kashe wayar tare da hugging dinshi tace “what were you thinking? That I am cheating on you?” Ajiyar zuciya ya sake yi sannan yace “I almost had a heart attack” Su Saima dai suna ta kwasar dariya. Ya Harare ta yace “wato Sadiq ya samu ana kiran shi My Luv sai ni da aka raina ne ake kira da wani Ya Farouq ko?”2 Marwa ce tace “gaskiya Anty Zara hakan ba daidai bane” Saima tace “kawai kaima ka daina kiranta Baby angel din” Zara ce ta harari Saima tace “dama ke ‘yar adawa ta ce, toh bazai daina ba” Saima kuwa dariya ta cigaba da yi yayinda tayi mata gwalo. Zara ta kama hannun shi tace “Zo mu je daki in nuna maka wani abu” daga nan kuwa ta janye shi yayinda su Saima suka cigaba da yi musu dariya. ********* Wasa wasa dai sai da suka yi sati uku a France. Sunyi yawo sossai tare da su Safa. Su Abba ne suka matsa ma Farouq akan lallai ya dawo a dalilin maganar Ruqayya domin kuwa Alhaji Bulama ya zo musu da maganganu wadanda ake buqatar a zauna. (Hehehe🤨)2 ************* ALHAJI ABUBAKAR BULAMA MANSION Zaune suke a babban falon Alhaji Abubakar Bulama inda ake jiran isowar Farouq da Zara. Tuni su Abba sun iso gidan inda ake ta hira yayinda Ruqayya take zaune a gefe cikin fargaba. A yau kusan satin su biyu kenan da dawowa wanda ake ta qoqarin a zauna don ayi Magana da Farouq amma kullum sai yace he is busy. Toh a yau dai an samu ya amince a zauna din domin kuwa shima ya gaji da auren Ruqayya maqale a wuyan shi sannan a yadda ya kula an matsa mishi ya tabbatar lallai ta shiga wani hali ne wanda ta kasa jurewa. Sallamar Farouq ce ta sa Ruqayya tayi saurin dago fuskar ta yayinda ta zuba musu ido. Gaba daya sun canza kamar ba su ba musamman Zara wadda ta koma tamkar baturiya don tsananin hutu da ta samu. STORY CONTINUES BELOW Nan da nan kuwa baqin kishi ya rufe ta. Bayan Farouq da Zara sun gaida kowa a falon ne suka samu wuri a qasa kusa da kujerar da Mamy take zaune suka zauna. Farouq ne ya kalli fuskar Ruqayya wadda itama shi take kallo, gani yayi duk ta rame ta lalace har a ranshi yana fadin “good job Farouq” Abba ne yayi gyaran murya yace “toh Farouq ga matan ka nan, ga mu iyayen ka sannan kuma ga iyayen Ruqayya, Ruqayya ta kawo qorafi akan cewa baka bata haqqinta kamar da sannan alamu ya nuna hakan tunda a cikin watanni uku da kuka yi tafiya Ruqayya ta kwanta ciwo har sau biyu amma kayi watsi da ita. Menene dalilin ka na yin hakan? Wane laifi Ruqayya tayi maka to deserve so much resentment from you?” Farouq yayi gyaran murya yace “Alhamdulillah, dama I have wanted this to go down this way” Ruqayya wadda take kallon Farouq ji tayi zuciyarta ta buga yayinda ta cigaba da sauraron shi. Farouq ya cigaba da fadin “Ruqayya is cheating on me with someone else kuma I found out Junior is not my son” Gaba daya falon suka ce “what?” yayinda suke ta salati. Mamy ce tace “this is a serious accusation Farouq, ka kuwa san me hakan yake nufi?” Ruqayya dai tuni jikinta ya fara rawa yayinda Alhaji Abubakar Bulama yayi gyaran murya yace “shin ko kana da proof?” Farouq yace “ina da shi” Hannu ya sa a aljihun shi ya fiddo wasu takardu ya miqa ma Abba sannan yace “reports ne guda biyu, daya yana nuna cewa Junior is a sickler, my Genotype is AA kuma nata AS, it got me confused” Ya kalli Ruqayya wadda take dafe da qirjinta yayinda hawaye ke bin fuskar ta ya cigaba da fadin “I went ahead to confirm by carrying out a Paternity DNA test which came out negative” Ji nayi gaba daya falon an dauki salati yayinda ake ta passing din report din. Hajjaju kuwa ji tayi kamar ta bace daga falon don tsananin kunya, bata taba tunanin Ruqayya zata yi sakarci irin wannan ba. Zara wadda komai dadi yake yi mata kallon Ruqayya kawai take yi tana murmushi. Gaba dayan su Jikin su yayi sanyi yayinda suka kasa yin Magana. Alhaji Abubakar Bulama ne ya kalli Ruqayya wadda ta riga ta fita daga hayyacinta yace “me zaki ce a game da wannan?” Cikin kuka tace “wallahi Dad sharrin shaidan ne, bazan…” Kafin ta qarasa ne Farouq yayi saurin kallon Abba yace “if you will permit me sir, nayi deciding zan saki Ruqayya saboda bazan iya zama da ita ba” Jin haka ya sa Ruqayya ta miqe a guje ta nufi wurin Farouq tare da yin kneel down a gaban shi tace “don Allah Honey kayi haquri, wallahi bazan qara ba” Ta harari Zara wadda take zaune a gefen shi tace “duk laifinta ne..” ji suka yi Farouq yace “shiyasa kika jefo ta daga steps har ta kusa rasa ranta?” Gaba daya falon suka ce “what?” Mamy tayi salati sannan tace “tir da halinki Ruqayya, Yanzu dama ke kika aikata wannan?” STORY CONTINUES BELOW Abba ya girgiza kai cikin bacin rai yace “that’s attempted murder” Zara dai cikin tsananin mamaki take kallon Farouq tace “babylove dagaske ba mafarki bane?”2 Ya girgiza kai tare da fadin “No Baby angel, ba mafarki bane” Zara ta kalli Ruqayya cikin tsananin bacin rai tace “Allah ya isa tsakani na da ke, muguwa kawai” Anan dai Farouq ya basu labarin komai da komai da ya sani. Hajjaju dai saboda kunya da baqin ciki banda kuka babu abinda take yi. Gani suka yi Ruqayya ta tafi wurin Zara da sauri zata shaqe yayinda take fadin “wallahi baki isa ba..” Farouq ne ya janye ta sannan ya gaura mata wani wawan mari wanda yasa ta zame ta fadi a qasa. Nuna ta yayi da yatsa yace “kar ki qara zuwa kusa da mata ta, Na sake ki saki uku”4 Zaro idanuwa Ruqayya tayi tare da sakin ihu tace “na shiga uku please Honey don’t do this to me” Farouq wanda yake rungume da Zara ne ya kalli Alhaji Abubakar Bulama da Hajjaju yace “kuyi haquri” Alhaji Abubakar Bulama yayi murmushin takaici yace “kar ka damu Farouq, this is the right punishment for Ruqayya. Asali ma mu yakamata mu baka haquri” Farouq wanda ya kalli Iyayen shi yace “kuyi haquri Abba we will just be on our way” Ya janyo Zara suka miqe suka fita abinsu yayinda Ruqayya ta dinga birgima a falon tana ta sabbatu. Abba ne ya kalli Alhaji Abubakar Bulama yace “toh Alhaji, Allah yasa hakan shi ya fi zama alkhairi, Allah ya qara shirya zuri’ar mu” Alhaji Abubakar Bulama cikin takaicin abinda Ruqayya tayi yace “Kuyi haquri akan dukkan abinda ya faru. Hakan ma ya zame mata ishara a rayuwarta” Abba ya kalli Mamy yace “tashi mu tafi” Mamy dai haka ta tashi ko sallama bata yi ma su hajjaju ba ta wuce suka fita yayinda suke ta mamakin abinda ya faru. Alhaji Abubakar Bulama dai har wurin Motar Abba ya raka su inda yake ta qara basu haqurin abinda ya faru. Bayan Alhaji Abubakar Bulama ya shigo ne ya kalli Hajjaju wadda take zaune tana ta share hawayen ta yace “duk laifin ki ne Hajjaju, ke kika bata yarinyar nan. Babu dama a tsawata mata sai ki ce anyi miki ba daidai ba, yanzu wa gari ya waya?” Ya kalli Ruqayya wadda duk ta bi ta fita hayyacin ta yace “idan kin ga dama sai ki dora daga inda kika tsaya, marar mutunci kawai” Ya wuce ya haura sashen shi. Ruqayya wadda ta dago ta kalli Hajjaju ce tace “Hajjaju…” Hajjaju ta daga mata hannu tare da fadin “rufe mun baki, shashasha kawai. Banda rashin hankali ya ma za’a yi ki aikata irin wannan babban kuskuren?” Ta miqe tare da fadin “you are on your own” tayi tsaki sannan ta bi bayan Alhaji don bashi haquri.2 Gani nayi Ruqayya ta sa hannu a kai yayinda ta dinga rusa kuka na fitar hankali. STORY CONTINUES BELOW Ni dai ji nayi cikin kuka tana fadin “this doesn’t end here, I swear” (Whoa🙄🙄🙄) FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) A yau wata daya kenan da Farouq ya saki Ruqayya. Kwance yake a kan gadon shi yana kallonta yayinda take tsaye a gaban madubi tana fesa turare. Juyowa tayi tana murmushi ta qarasa kan gadon tayi hugging dinshi tare da fadin “Good morning Babylove, yi haquri na tada ka kana bacci”2 Murmushi yayi yace “Not at all my Baby angel, I enjoy watching you everyday. Har kin shirya ne?” Tace “yes” yace “if not because I am tired da na kai ki” Murmushi tayi tare da jan gemun shi tace “its okay Babylove, kai da ka dawo da asuba, you need some rest. Nima da na duba jikin nata zan dawo. I wanna spend the rest of today with you” Murmushi yayi sannan yace “I love you my Zara, I cant imagine my life without you” tace “I love you too my Ruqu”. Farouq ya raka ta har parking lot inda ya bude mata qofar mota, tana shirin shiga ne ya riqo hannun ta tare da hugging dinta ta baya ya shafa cikinta yace “I have a feeling like I have something in here” Cikin farin ciki tace “dagaske??” yayi murmushi yace “ofcourse Baby Angel, je ki dawo mu je mu tabbatar”6 Ji nayi tace “Oh my God, Allah yasa hakan Babylove, I really want to have a baby” daga nan kuwa tayi locking din bakin shi da nata.2 Ganin ma’aikatan gidan suna kai da komowa a harabar gidan ne yasa Farouq yayi saurin zare bakin shi daga nata yace “hey your workers are staring at us” hararar shi tayi tace “who cares right?” suka fashe da dariya. Zara tana kallon shi tace “I am going to miss you My babylove” Farouq ya dan bata rai yace “hey you are just going away for a few hours” ajiyar zuciya tayi tace “haka ne but a moment without you is like hell” dariya yayi yace “same here my dearest, ki gaida mun Hafsat din and please drive safe” tace “okay Sir” Farouq yana nan tsaye har Zara ta fita daga gidan. Bayan ya dan yi Magana da Habibu ne a nan harabar gidan ya koma ciki don yin bacci domin kuwa wasu surgery yayi jiya cikin dare wanda bai dawo gida ba sai da asuba. ********** Tafe take a kan hanyar ta na zuwa gidan Hafsat. Addu’a take yi akan Allah yasa dagaske tana dauke da ciki domin kuwa babu abinda take so illa ta ganta da baby. Murmushi tayi yayinda take ta fadin “I hope so.. I hope so..” Bata ankara ba sai gani tayi wata mota qirar toyota Hilux ta danno kai da gudu.3 Dukda kuwa Zara ta matsa ma motar don ta wuce sai gani tayi motar ta doso ta. Ni kuwa gani nayi Zara ta zaro idanuwa yayinda hankalin ta ya tashi. Babu abinda take fadi sai “innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” Ba tare da bata lokaci ba kuwa Hilux din ta ture motar Zara da qarfin gaske. Gani nayi motar Zara tana ta rolling akan hanya yayinda Hilux din ta wuce a guje. Motar Zara wadda take ta juyawa a kan titi sai gani nayi ta fara hayaqi. Nan da nan mutane suka rugo don kawo agaji wanda kuwa kafin su qarasa sai gani suka yi motar ta kama da wuta…4 ***********