BA SONTA NAKE BA CHAPTER 16 KARSHE
Mutane tsaye cirko cirko a gaban motar Zara wadda take ta ci da wuta yayinda suke ta juyayi.+ Fire service ne suka kashe wutar. Tuni jami’an tsaro da paramedics sun zagaye harabar wurin yayinda suka fara neman ba’asin abinda ya faru. Daya daga cikin Paramedics din ne ya hango alamun mutum kwance a kan ciyawa can nesa da inda hatsarin ya faru. Qarasawa yayi a guje ya ganta kwance, gaba daya jikinta jini ne yayinda take numfashi sama sama. Mutumin ne ya kira abokanen aikin shi inda aka dora Zara bisa stretcher aka sanya ta a ambulance sai asibiti. CENTRAL HOSPITAL Farouq ne ya shigo asibitin a cikin tsananin tashin hankali. Kiran shi aka yi a waya aka sanar mishi abinda ya faru. Hawaye ne ke bin fuskar shi yayinda ya shiga emergency room din da aka kwantar da ita. Likitoci ne tsaye a kanta yayinda suke ta yi mata taimakon gaggawa, Farouq wanda ya daskare a tsaye ganin jikin Zara duk jini sai gani nayi ya runtse idanuwan shi tare da fadin “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” Gani nayi ya jingina da bango yayinda ya cigaba da fadin “hasbunallahu wani’mal wakeel” haka ya dinga maimaitawa har sai da ya samu natsuwa. A hankali ya qarasa wurin gadon yana kallon ta. Muryar shi tana rawa yace “what’s her status? is she going to be okay?” Dr Ibrahim wanda yake cikin team din ne ya girgiza kai tare da ce mishi “its too early to tell Sir, but we are doing our best to save her” Runtse idanuwan shi kawai yayi ya juya ya fita daga dakin domin kuwa ji yake kamar zai mutu. Su Mamy ya tarar a waiting room wadanda isowar su kenan. Kuka kawai Mamy take yi yayinda Sadiq yake ta lallashin ta wanda shima idanuwan shi suka yi ja. Ga Hafsat itama wadda take fama da jikinta maqale da Mukhtar tana ta rusa kuka. Farouq kuwa rungume Abba yayi yana ta surutai. Ni dai ji nayi yace “Abba I don’t want to lose her, Zara is my life… I will die if..”2 Abba ya dan bugi bayan shi yace “have faith my Son, Zara is a fighter. She will be okay Insha Allah” ********** Tsawon awa biyar kenan da aka kawo Zara asibitin. Tuni labarin accident din Zara ya zagaya ko ina, wasu ma fadi suke yi ta mutu. Granny kuwa har ta iso a Private jet din marigayi Alhaji Umar Jimeta. Su Daddy ma tuni sun kamo hanya daga France. Dr. Ibrahim ne ya fito daga dakin Zara ya qarasa wurin su Farouq yace “she is out of danger Sir but still unconscious for now, insha Allah she will be fine”2 STORY CONTINUES BELOW Ajiyar zuciya Farouq ya saki yayinda gaba daya ake ta hamdala. Dr. Ibrahim ya cigaba da fadin “uhm a yanzu mun gano karaya a hannun ta, sai dislocation a qafar ta. Anyi mata stitches a wuraren da tayi sustaining injuries sannan zamu cigaba da running tests akanta don tabbatar da komai lafiya a jikinta” Farouq ne yace “thank you Doctor” yayinda ya nufi dakin Zara ya bar su Abba suna ta gode ma Allah. Washegari su Daddy suka iso, har a lokacin babu mai shiga dakin Zara banda likitoci sai kuma Farouq. Ta gilas kawai ake hangen ta. har yanzu kuwa bata farfado ba amma kuma da alama tana samun sauqi. Jami’an tsaro dai sunyi iya binciken su akan abinda ya janyo hatsarin amma basu gano komai ba. Daddy ne ya basu damar su janye binciken kawai, a cewar shi tunda Zara ta rayu sun gode ma Allah. (Anya kuwa Daddy a janye binciken??🤔)2 ********** A yau kwana biyu kenan da Zara tayi accident. Farouq ne zaune a gaban ta yana ta kallonta. Wayarshi ce tayi ringing yayinda ya tashi ya dan matsa nesa da gadonta sannan ya amsa. Secretary dinshi ce tace “Sir you have visitors kuma sunyi insisting cewa suna so su ganka” Farouq ya shafa kan shi yace “suna da appointment ne?” tace “No Sir amma sun ce ba zasu bata maka lokaci ba” cikin mamaki yace “well okay I will be right there” Su Mamy wadanda suke zaune a waiting room sai ganin Farouq suka yi ya fito har Granny tana fadin “lafiya dai ko?” Yace “ehm, ana nema na ne Mi lady, I am coming” Haka ya fita yayinda su Anty suke ta tausaya mishi yadda duk ya bi ya rame. Farouq wanda ya qaraso ofis dinshi ne ya gan su tare da wata yarinya wadda bazata wuce shekaru goma ba. Bayan sun gaisa ne Farouq ya shiga ofis dinshi yayinda suka bi bayan shi. Farouq ya nuna musu wuri suka zauna yayinda yarinyar ta tsaya a tsaye rungume da wani littafi tana ta kalle kalle. Farouq ne ya kula da yarinyar yace “hey cutie won’t you sit?” Matar ce tayi murmushi tace “Hanan kenan, the inquisitive one. Yanzu gobe idan muka duba littafinta zamu ga sketch na ofis dinka a ciki” Farouq yayi murmushi yace “whoa, really?” Suka yi dariya yayinda matar tace “shiyasa muke kiran ta ‘yar baiwa” Farouq ya girgiza kai yace “you must be proud of her then, Allah yayi mata albarka” suka amsa da “ameen” Mutumin ne yace “ya jikin madam kuma?” Farouq yace “Alhamdulillah” matar tace “Allah ya bata lafiya” suka amsa da “Ameen” Farouq ne yace “ehm, saidai kuma ban gane ku ba” Mutumin yace “haka ne, ni sunana Isma’il” Ya nuna matar yace “wannan kuma colleague dina ce, sunan ta Amina” Ya fiddo ID card dinshi ya miqa ma Farouq. Farouq ya karba yana dubawa yayinda Mutumin ya cigaba da fadin “Mu ma’aikata ne a The city of refuge ophanage da yake nan Maitama kuma mun zo ne a dalilin abinda ya faru ranar da matar ka tayi accident” STORY CONTINUES BELOW Cikin rashin fahimta Farouq yake kallon Isma’il yayinda yace “ban gane ba, shed more light please” Isma’il ya cigaba da fadin “a lokacin da abun ya faru muna dawowa daga park ne tare da yara a cikin bus, we had to stop a kusa da GTB inda na fita ciro kudi a ATM” Isma’il ya kalli Amina wadda ta cigaba da fadin “muna zaune muna jiran shi ne muka ji qarar accident din wanda ya tada hankulan yara a cikin motar. Gaba dayan su suka dinga ihu suna kuka except for her” Ta nuna Hanan sannan ta cigaba da fadin “hawaye kawai na gani yana gangarowa a fuskarta as she watched the whole incident while ni da sauran staff din muna qoqarin kwantar ma yaran da hankali” Farouq dai har yanzu bai fahimci inda labarin yake zuwa ba domin kuwa fuskar shi ta nuna alamun confusion. Isma’il ne ya cigaba da fadin “ko da na fito daga bankin na tarar motar tana ci da wuta yayinda aka sa Matar ka a ambulance” Yayi ajiyar zuciya sannan yace “Mun jajanta qwarai abinda ya faru, ganin hankulan yara ya tashi ne yasa muka bar scene din” Amina tace “the thing is jiya Hanan ta kawo mun littafin ta kamar kullum tana nuna mun sketches din da tayi, sai na ga wani abu da ya bani mamaki” Ta juyo ta kalli Hanan wadda itama a yanzu su take kallo. Isma’il ya karbi littafin da yake hannun Hanan ya miqa ma farouq yace “we thought you might want to see” Farouq wanda ya bude littafin gani nayi ya dan zaro idanuwa cike da mamaki yayinda ya cigaba da kallon sketch din. Farouq ya dago kai da sauri ya kalli Hanan yace “hey cutie come here” Da gudu ta qarasa wurin shi yayinda ya nuna Hilux din yace “wannan motar ce ta bige ta?” Hanan tace “yes, I am sorry I couldn’t do anything for her” Farouq ya shafa kan ta tare da fadin “you just did cutie, thank you very much” Farouq dai yayi ma su Isma’il godiya tare da karban contact dinshi. Nan da nan ya rubuta musu cheque na naira miliyan goma wanda ya bayar as donation zuwa ga gidan marayun sannan yayi warning din su akan lallai kar su yi leaking to the press saboda kuwa yayi ne don Allah. Farouq dai bai fada ma su Abba maganar su Hanan ba, ya qudurta a ranshi da taimakon sketch din Hanan sai ya gano ainihin abinda ya faru insha Allah. (Hmmm… Ni kuwa nace how is it possible??😏) NIGERIA POLICE DIVISIONAL HEADQUATERS ABUJA Farouq ne zaune a gaban Commissioner of Police, Bala Ciroma tare da ASP Yahaya wanda yake incharge of case na accident din Zara dukda kuwa an rufe case din. CP Bala Ciroma ne yake kallon sketch din Hanan yayinda ya girgiza kai. Gani nayi ya miqa ma ASP Yahaya yace “track this vehicle via the plate number and get back to me ASAP” ASP Yahaya ya buga qafa tare da yin salute yace “yes sir” sannan ya fita. CP Bala Ciroma ya kalli Farouq yace “kar ka damu, I assure you cewa this is a major lead, idan dai plate number din is legit we will track down the culprit” STORY CONTINUES BELOW Farouq wanda yake kallon CP Bala ne yace “thank you very much Sir, i will be on my way” Tare suka miqe inda Farouq ya bashi hannu suka yi musabaha yayinda CP Bala yace “my regards to your Dad please” Farouq ya girgiza kai yace “insha Allah” CENTRAL HOSPITAL A yau kwana biyar kenan da Zara tayi accident. Tuni ta farfado amma a dalilin kalolin magungunan da ake sa mata a drip ne take yawan yin bacci. Gashi dama tun da ta farka take complain akan zafin da hannunta yake yi wanda ake bata pain reliever domin ta rage jin radadi. (Allah sarki baiwar Allah😟)2 Dr. Nila ce ta shigo dakin. Bayan ta gaida su Mamy ne ta qarasa wurin Farouq wanda yake zaune daf da Zara riqe da hannun ta dukda kuwa bacci take yi. Tana murmushi tace “sir, I have something for you” Farouq ya kalle ta yace “what is it Dr. Nila?” Ta miqa mishi wani report yayinda ta tsaya tana kallon shi. Farouq wanda ya duba report din gani nayi ya zaro idanuwa tare da miqewa yace “what??” Cikin tsananin farin ciki ya juyo ya kalli Dr. Nila yace “are you sure? Uhm I mean is it for real??” Dr. Nila wadda take dariya ta girgiza kai alamar eh yayinda ya daga hannuwa sama yana fadin “Alhamdulillah, Allah nagode maka” Mamy ce tace “lafiya??” yayinda su Granny suka sa mishi ido suna sauraron abinda zai ce. Farouq yana murmushi yace “Zara is pregnant”6 Aikuwa nan da nan aka fara murna. Su Safa sai tsalle suke yi Yayinda qawarta Hafsat ma ta cika da farin ciki. Mamy cikin murna tace “Allah sarki my princess, dukda wahalar da ta sha she didn’t lose my grand child” Granny tace “lallai kam ashe takwara ta jaruma ce” Anty ce ta kali Dr Nila tace “hope the baby is in good condition of health?” Dr. Nila tace “the baby is fine Ma, I had to confirm before breaking the news” Farouq dai komawa yayi ya zauna a kan gadon Zara ya rungume ta tare da fadin “Baby angel, mafarkin mu ya tabbata” Ya shafa cikinta yace “kamar yadda na fada I really have something in here, its true Baby angel I do, you are pregnant” Muryar ta ya ji qasa qasa tace “babylove” Da sauri Farouq ya kalli fuskar ta yana murmushi. Gani nayi yana ta yi mata kisses yayinda Dr. Nila tayi murmushi ta fita. Su Mamy dai kauda kai suka yi suna ta yi ma Farouq dariya har Granny tana fadin “na shiga uku da rashin kunyar ka Farouq” Zara tana murmushi tace “is it true that I am..” cikin murna yace “its true my baby, we are pregnant” Su Mamy kuwa me zasu yi banda dariya har Granny tana fadin “lallai baka da kunya, wato sai ka gwada mana kai ne mai cikin” Haka dai aka dinga dariya. Ko da likitoci suka duba jikin Zara komai normal, yanzu dai cast din hannun ta ne kawai sai kuma stitches din da aka yi mata. STORY CONTINUES BELOW Sai da tayi sati biyu a asibiti sannan aka sallame ta. Gidan Mamy aka tafi da ita saboda samun kula sossai. AL-HUSSAIN MANSION Zaune take a kan gadon dakin ta na da inda take riqe da madubi tana kallon fuskar ta. Gani nayi tayi wurgi da madubin yayinda ta fara kuka. Farouq ne ya shigo dakin. Ganin tana kuka ne ya qarasa wurinta da sauri ya zauna a gefenta tare da hugging dinta yace “hey baby angel what is it? Hannun ne?” Ta girgiza kai alamar a’a sannan tace “my face” yace “what about it” cikin kuka tace “ni bana son wannan scars din, i am looking ugly with..” Murmushi yayi tare da yi mata kiss yace “ssshhhh, wa ya fada miki haka? On the contrary you look beautiful, you are the most beautiful woman in this whole wide world. I love you very much”2 Hafsat ce ta qwanqwaso qofar dakin ta shigo. Ganin su rungume da juna ne tayi murmushi tace “oops sorry bari in dawo anjima” Farouq wanda yake murmushi yace “please come in, I was about leaving dama” Yayi ma Zara kiss yace “you will be back to normal insha Allah kin ji? I love you” Ya shafa cikinta yace “take care of our triplets” Tayi murmushi tace “I love you too, bye” Hafsat wadda take tsaye tana kallon su sai murmushi take yi. Bayan Farouq ya fita ne ta zauna kan gadon tace “hmmm, this love nawawoo” Zara tayi murmushi tace “babylove is my life” Hafsat tana dariya tace “you are his life too bestie” Zara ta shafa cikinta tace “i can’t believe i am pregnant, Allah yasa triplets ne” Hafsat ta fashe da dariya tace “ke da obsession dinki na triplets” yayinda Zara take ta dariya. Suna cikin hira ne Sadiq tare da su Safa suka shigo dakin aka cigaba da hirar da su wanda kamar kullum Saima ta dinga tsokanar Zara ana ta yi musu dariya. NIGERIA POLICE DIVISIONAL HEADQUATERS ABUJA Zaune yake a ofis din ASP Yahaya wanda yake yi mishi bayani akan case din accident din Zara. ASP Yahaya yace “munyi nasarar gano Hilux din sannan mun kamo direban motar, a halin da ake ciki yanzu yana nan a hannun mu” Ya miqe tare da fadin “bayan horo mai tsanani da ya sha he has asked to speak with you” Farouq wanda ya miqe tsaye shima yace “ni kuma?? Why??” ASP Yahaya yace “i really don’t know, mu je ka gan shi” Bayan ASP Yahaya ya kai Farouq wurin Mutumin a interrogation room wanda ya sha dukan tsiya ne ya kalli Farouq yace “I will be right outside” Farouq ya zauna a wata kujera wadda take fuskantar mutumin sannan yace “ina sauraron ka” Mutumin ne ya tsugunna har qasa yace “Yallabai don Allah ka taimaka mun, wallahi ina da iyali. Nima talauci ne yasa na karbi wannan aikin” Farouq wanda ya qagara ya ji mastermind behind it all ne yace “kai ji mana, fada mun sunan wanda ya baka aikin daga baya zamuyi maganarka” Mutumin yace “wallahi wata hajiya Ruqayya ce, diyar gidan tsohon minister…” kafin ya qarasa maganar shi ne Farouq ya miqe ran shi a bace tare da fadin “what???!!!”2 ************ ALHAJI ABUBAKAR BULAMA MANSION Ruqayya ce zaune a falonta tare da qawarta Aliya suna hira.+ Aliya ce take fadin “qawata kin kuwa ji labari an ce Zara ta farfado? Kai yarinyar dai ta bani tausayi wallahi. Motar fa qonewa tayi Allah ya so ta fita ta window” Ruqayya ta bata rai tace “ai na so ace ta qone wallahi, she won’t escape next time” Aliya ta kalli qawarta cikin mamaki tace “ba dai da sa hannun ki a accident din ba qawata??” Ruqayya ta girgiza kai tana murmushi tace “nope”. Daya daga cikin masu aikin gidan ce ta shigo falon a firgice. Ruqayya ce ta dalla mata harara tace “lafiya kika shigo mun falo kamar mahaukaciya?” Mai aikin wadda take qoqarin saita numfashi ne tace “wasu jami’an tsaro ne suka zo.. wai suna neman ki” A firgice Ruqayya ta miqe tace “what? Jami’an tsaro? Ni suke nema?” Aliya ce tace “qawata me ya hada ki da jami’an tsaro kuma?” Ruqayya wadda jikinta ya fara rawa ne ta kalli mai aikin tace “ki ce musu bana nan” Mai aikin tace “wallahi sun ce idan baki fito ba zasu hauro nan..” Aikuwa kafin ta rufe bakinta ne ta ji hayaniyar su yayinda suke haurowa saman. Aliya dai tuni ta miqe ta dauki Jakarta sannan ta yafa gyalen ta. Ruqayya ce ta kalli qawarta tace “qawata ya haka? Ina zaki je?” Aliya dai ko Magana bata yi ma Ruqayya ba ta lallaba ta fice. Ko da ta hadu da jami’an tsaron dakatar da ita suka yi suna ta yi mata tambayoyi wanda basu qyale ta ba har sai da suka tabbatar ba ita ce Ruqayya ba. Aikuwa haka Aliya ta fice daga gidan cikin tashin hankali yayinda jami’an tsaron suka qarasa suka cafke Ruqayya wadda take ta fizgewa. ASP Yahaya ne yace “Hajiya Ruqayya you are under arrest for attempted murder, you have the right to remain silent because anything you say or do could be used against you in a court of law” Haka aka tafi da Ruqayya wadda take ta kuka yayinda masu aikin gidan suka cika da mamaki. A lokacin da wannan al’amari ya faru kuwa gidan babu kowa, Hajjaju da Alhaji Abubakar suna America sannan qannen ta su Zain suna Malaysia inda suke karatu. AL-HUSSAIN MANSION Gaba daya dangin Alhaji Umar Jimeta suna zaune a babban falon gidan suna hira yayinda suke kallon tashar NatGeoWild a TV amma fa banda Farouq wanda yake asibiti sai Sadiq wanda yake sashen shi. STORY CONTINUES BELOW Zara wadda take kwance a kan cinyar Mamy ce tace “wai ina babylove ne bai dawo ba har yanzu” Granny wadda take zaune kusa da su ne ta harare ta tace “ya dawo yayi miki me toh? Ai in fada miki gaskiya tare da shi zan tafi Adamawa” Zara cikin shagwaba tace “ni wallahi ban yarda ba, tsohuwa da ke amma duk kin bi kin maqale ma yaro” Su Daddy ne suka dinga dariya yayinda Granny tace “toh bari ya dawo ya fadi mana wadda ya fi so a cikin mu” Zara cikin shagwaba tace “ni ya fi so dagaske” Mamy tana dariya tace “mun shaida hakan Princess, kar ki bata ran ki” Sadiq ne ya shigo falon a guje yayinda yace “ina remote??” Cikin mamaki Abba yace “lafiyarka kuwa?” Sadiq wanda yake ta neman remote ne yace “Abba wani labari ake yi a news” Ya dauko remote ya canza yayinda gaba daya falon hankalin su ya koma kan TV. Hoton Ruqayya ne a jikin TV din inda ake sanarwar an kama ta da yunqurin kisan kai. Ko da suka saurara sai suka ji ashe ita tayi sanadiyar hatsarin Zara wanda da taimakon wani evidence da Farouq ya bayar ne aka gano gaskiya. Aikuwa gaba daya falon aka dinga salati yayinda Zara ta fashe da kuka. Mamy wadda take lallashin Zara ne tace “Yi hqauri My Princess, ai ga sakayya nan, tun ba’a je ko’ina ba ta fara gani” Granny tace “Amma dai Ruqayya bata ji dadin hali ba, tayi asara a rayuwarta” Abba ne yace “wato shine yaron nan bai fada mana komai ba ko? Bari zai dawo ya same ni” Daddy yayi murmushi yace “haba dan uwa, you shouldn’t scold him. He did the right thing” Farouq ne yayi sallama ya shigo falon yayinda kowa ya sa mishi ido. Idanuwan shi basu sauka akan kowa ba sai kan Zara. Ganin Zara tana kuka ne ya qarasa kusa da Mamy da sauri ya zauna yayinda ya janyo ta jikin shi yana fadin “hey my Baby Angel me ya faru? Cikin ne?” Zara dai qara maqalewa tayi a jikin shi tana kuka yayinda aka sa musu ido har su Daddy suna dariya. Farouq wanda hankalin shi yake a tashe bai ma damu da cewa sirikan shi da iyayen shi suna zaune a falon ba sai hugging dinta yayi tare da kai bakin shi saitin kunnen ta yace “hey please tell me what is it? Wa ya taba mun ke?” Mamy ce tace “kai zaka fadi mana abinda ya faru, yanzu muka ga sanarwar Ruqayya a TV” Farouq yace “ooh, that?” Abba ne yace “ooh, irin no big deal dinnan ko?? meyasa zaka yi dealing da case irin wannan baka sanar da mu ba? ya aka yi ma ka gano cewa Ruqayya ce?” Farouq dai haquri ya basu sannan ya basu labarin Hanan. Gaba daya dai falon an jinjina zancen. Anty ce tace “kar ku yarda ku bari a bada bail, yakamata a barta ta sha wahala sossai. mahaukaciya kawai” Farouq yana murmushi yace “kar ki damu Anty, Ruqayya bazata bar prison ba sai tayi serving jail time dinta, i made sure of that” STORY CONTINUES BELOW Yayi ma Zara kiss a goshi yace “baby angel dina ta taba and she will pay dearly” Saima ce tace “gaskiya Ya Farouq life imprisonment kawai ya kamace ta” yayinda Sadiq yace “ai dama hukuncin kenan” Daddy ne yace “ai ina ganin akwai sassauci idan dai no life lost” haka dai suka cigaba da maganar tare da yin tir da halin Ruqayya. Zara ce tace “Babylove ina son ganin yarinyar nan Hanan, please take me to her” Mamy ma tace “gaskiya yakamata, its thanks to her an gano gaskiya” Farouq yace “Insha Allah gobe zan kawo muku ita” ************* Washegari dai kamar yadda Farouq yayi ma Zara alqawari har The city of Refuge orphanage ya je ya dauko Hanan wadda suka zo tare da Amina. Sossai Zara ta ji dadin ganin Hanan. Hanan dai yarinya ce fara sol kyakyawa, idan ka kalle ta da kyau ma zaka ga kamar tana da hadi da larabawa. Asali iyayen ta sun rasu a sanadiyar hatsarin mota da suka yi wanda aka yi cigiyar dangin su amma aka rasa shiyasa ta tashi a gidan marayu. Yini daya kawai da aka yi da Hanan a gidan amma ta shiga ran kowa. Wasa wasa dai duk bayan kwana biyu sai Zara ta roqa akan a kawo mata Hanan, ita kanta Hanan tana bala’in son Zara. Dukda bata yawan Magana amma idan tana tare da Zara zaka ji muryar ta. Tuni su Daddy sun koma France yayinda Granny ma ta koma Adamawa. Zara ma ganin ta samu sauqi sossai ta koma gidanta. MUKHTAR ABUBAKAR MANSION Zaune suke a falon Hafsat suna shan fruits suna hira. A yau wata biyu kenan da Zara tayi accident. Yanzu haka jikinta ya warke sumul. Zara wadda take cin ayaba ne ta kalli qawarta tace “Bestie cikin ki yayi girma sossai, qila ma triplets ne” Hafsat wadda take kishingide a kan three seater tana cin apple ta fashe da dariya tace “rufa mun asiri bestie, triplets sai ke, ni ya zan qare da guda dayan ma” Zara tana dariya tace “Allah dai ya sauke mu lafiya” Hafsat tace “ameen” Zara ce ta kalli agogo tace “Bestie bari in tashi in koma gida, yau za’a kawo mun Hanan” Hafsat tayi murmushi tace “na ga alama Hanan dai ta shiga ranki bestie” Zara tayi murmushi tace “wallahi bala’in sonta nake yi, how I wish she is mine..” ta dan yi shiru kamar tana tunani sannan tace “but wait, she could actually be mine fa” Hafsat tace “ban gane ba” Zara ta girgiza kai ta miqe tare da fadin “bari in tafi babes, zan baki labari” yayinda ta janyo gyalen ta. Hafsat tana dariya tace “lallai kam bestie, the love you have for kids is something else” FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Ya fito daga bathroom dinshi riqe da ita yayinda take maqale a jikin shi kamar mage. Gaban dressing mirror ya zaunar da ita sannan ya fara shafa mata mai. Bayan ya gama ne yayi mata kiss a kumatu yace “you are my life, na taba fada miki hakan?” STORY CONTINUES BELOW Tana murmushi cikin shagwaba tace “baka taba fada mun ba Babylove but I know” ta kashe mishi ido daya yayinda ya girgiza kai yana dariya. Closet dinshi ya nufa don fitar mata da night wear dinta. A yanzu dai Zara ta dawo dakin Farouq gaba daya, ta kwaso kayanta dayawa ta zuba a closet dinshi. Idan ka shiga closet din ma zaka ce nata ne domin kuwa tayi mishi hijacking wadrobes din shi. Gaba daya ma yanzu dakin shi qamshin Zara yake yi wanda yake bala’in so. Wata sleeveless silk nighty ya dauko mata, bayan ta sanya ne ta haye kan gadon shi ta zauna cikin shagwaba tace “Babylove my smoothie” Yayi murmushi yace “bari in dauko miki My Angel”. Bayan ya fita ne na ga ta daga hannuwan ta sama tace “Allah yasa ya amince” Tana nan zaune ya dawo riqe da wani dogon glass cup na smoothie ya zauna kan gadon ya janyo ta jikinshi yayinda ya fara bata. Bayan ta shanye ne ya ajiye cup din sannan ya kalle ta yace “what again?” Gani nayi ta dan yi shiru kamar tana tunani sannan tayi murmushi tace “nothing” Girgiza kai yayi yana murmushi sannan ya kwanta ya janyo ta jikin shi tare da hugging dinta. Ji nayi tace “Babylove you love me right?” Yayi murmushi yayinda idanuwan shi suke a rufe yace “a lot my angel” Tace “you will do anything for me right?” yace “absolutely my angel” Tace “even if its against your wish right?” yace “I can lay my life for you my angel” Tace “I want us to adopt Hanan, you will do it for me right?” da sauri ya bude idanuwan shi yace “what??”7 Tashi tayi zaune tana kallon shi yayinda fuskar shi tayi displaying confusion. Hannun shi ta riqo tace “Babylove ina son Hanan sossai kuma ka ga marainiya ce, zan ji dadi sossai idan ta dawo hannu na. Zamu samu lada plus ka ga idan ta zauna da mu zamu inganta rayuwarta fiye da gidan marayu..” Farouq dai tunda ta fara Magana ya qura mata idanuwa yana murmushi. A koda yaushe idan Zara tana Magana haka yake tsayawa yana kallonta saboda birge shi take yi sossai. Bala’in son surutun Zara yake yi a yanzu domin kuwa muryar ta dadi take yi mishi. Ji yayi tana fadin “please don’t say no Babylove” Yana murmushi yace “I said i will do anything for you my angel, idan har abinda kike so kenan its done” Zara ta zaro idanuwa tace “dagaske??” yana murmushi ya girgiza mata kai alamar eh. Aikuwa sai tayi hugging dinshi tana fadin “yeeeey, thank you very much my love, you are the best” Ya girgiza kai yace “ki shirya gobe sai mu je mu fara processing adoption din, Allah yasa su bamu” STORY CONTINUES BELOW Tace “ai idan basu bamu ba zama zanyi inyi ta rusa musu kuka” Hakan kuwa ya ba Farouq dariya sossai. ************ Farouq ya sanar ma su Abba plan dinsu na son adopting Hanan wanda suka amince da hakan musamman ganin cewa abinda Zara take so ne. Aikuwa nan da nan suka fara processing wanda basu samu matsala ba. Sanin cewa Farouq Al-Hussain mutumin kirki ne sannan da aka yi la’akari da donations din da yake bayarwa a gidan marayun it’s the least they can do for him. Ranar da aka gama adoption process din kuwa Zara kamar ta zuba ruwa a qasa ta sha don murna. Hanan ma ta ji dadi qwarai domin kuwa tana bala’in son Zara. Cikin qanqanin lokaci kuwa suka saba da Hanan, idan ka gan ta sai kayi tunanin diyar su ce domin kuwa wani mugun shaquwa suka yi da juna. Tuni an sanya ta a makarantar Nigerian Turkish inda ta cigaba da karatun ta. PRISON- ABUJA Hajjaju ce ta zo prison din a yau don ganin Ruqayya wadda da qyar aka bari ta ganta. Ruqayya dai an yanke mata hukuncin zama a gidan yari har tsawon shekaru bakwai wanda babu bail. Alhaji Abubakar Bulama dai ko da ya ji abinda Ruqayya tayi fita harkar ta yayi domin kuwa ba qaramin bata mishi suna tayi a qasa ba. Hajjaju ita tayi ta kai da komowa tare da kashe kudade amma a banza. Da qyar ma lauyan ta yayi mata qoqari akan a dinga barin Hajjaju tana zuwa ganin ta. Ruqayya ce ta fito yayinda wata jami’ar tsaro take biye da ita a baya. Gaba daya ta bi ta lalace tayi baqi, duk kyan nan nata ya bace. (Ni kaina sai da na razana a yadda na ganta🤨)6 Cikin kuka ta qaraso wurin Hajjaju ta zauna. Hajjajun ma kuka take yi tana fadin “Baki kyauta ma kanki ba Ruqayya, nayi iya qoqari in ga na fitar da ke daga cikin wannan wahalar na kasa. Yanzu dai haquri kawai zakiyi har Allah ya fitar da ke nan da shekaru bakwai” Ruqayya wadda take kuka tace “nayi nadamar abinda nayi Hajjaju, son kai shi ya ja mun, how i wish I could turn back the hands of time”2 Hajjaju ta girgiza kai tace “the past is in the past already, just look forward to your future kuma ki cigaba da istigifari. Ni kaina na tuba akan biye biyen malaman banza da muka yi. Things would have been different but its too late to cry” Ruqayya tana kuka tace “how is Junior?” Hajjaju ta girgiza kai tace “mahaifin shi ya zo shekaran jiya ya tafi da shi, kotu ce ta bashi damar ya dauki yaron shi. duk yadda muka so mu hana shi ya fi mu gaskiya don haka ne muka haqura muka bar mishi”2 Ruqayya dai kasa Magana tayi, wasu zafafan hawaye ne suke ta gangarowa a fuskar ta. Ruqayya dai sai kyarma take yi yayinda ta dafe qirjinta, zuciyar ta ce take zafi. Hajjaju gani tayi Ruqayya ta sulale ta fadi a qasa sumamma. Da sauri jami’an tsaro suka zo suka dauke ta suka tafi da ita infirmary na prison din yayinda Hajjaju ta sa hannu a kai tana ta rusa kuka. *************** BAYAN SHEKARU UKU FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION Kwance yake akan makeken gadon dakin shi yana bacci.+ Ji yayi ana ta birkita mishi gashin kanshi yayinda ake ja mishi gemu. Gani nayi ya yamutse fuska, idanuwan shi a rufe yace “please Baby angel, let me sleep mana” ji yayi ance “Abbu..”2 Murmushi yayi tare da bude idanuwan shi ya gan ta zaune a gefen shi. Kumatun ta ya ja sannan ya janyo ta yayi hugging dinta yace “hello my Gorgeous Amna, how are you?” Ji nayi kamar tace “fine” yace “where is your Ammi?” tace “Ammi” girgiza kai na ga yayi yana dariya sannan yace “okay, I shouldn’t expect an answer from her, right??” (Ni kuwa ina daga gefe nace ah toh🤨) Zara ce ta shigo dakin riqe da Amal a hannun ta tace “hmmm, finally she has succeeded in waking you up” Farouq ya tashi zaune yana murmushi yace “ai na san da gangan kika kawo mun ita” Amal ce ta miqa hannu wurin shi ta fara kuka tana fadin “Abbu..” Zara ta miqa mishi ita tare da matsawa tayi mishi kiss tace “good morning babylove, how was your night?” Yana murmushi yace “thanks to you it was fantastic” tayi dariya tare da birkita gashin kanshi. Farouq wanda ‘yan biyun suka maqale a jikin shi kamar maguna ne ya girgiza kai tare da fadin “I am in trouble, yaran nan ke suka biyo wurin son jiki, na ga alama nan gaba kadan zaku qarasa ni”4 Zara wadda ta zauna a kan gadon ta fashe da dariya tace “son ka muke yi babylove” yana dariya yace “nima son ku nake yi ‘yan mata na, where is Hanan?”2 Tace “kasan Hanan ai, tana can tana directing masu aiki akan yadda zasu jera breakfast, yanzu ma we came to fetch you ne” Yayi murmushi sannan yace “okay, bari inyi wanka first” Yana tashi kuwa su Amal suka fashe da kuka, kamar kullum wayoyin shi ya basu suna ta wasa da su sannan ya lallaba ya gudu yayinda Zara take ta yi mishi dariya. Zara dai ‘yan biyu ta Haifa mata wadanda suka ci sunan Mahaifiyarta da Mamy wato Zainab da Labiba amma ana kiran su Amal da Amna. Yaran Zara farare ne tas sannan kyawawa gwanin ban sha’awa.3 *********** Su Farouq ne suka shigo dinning room din don yin breakfast. Yana riqe da Amal yayinda Zara take riqe da Amna. Hanan wadda ta gan su ne ta rugo a guje tayi hugging Farouq tace “Abbu good morning” Ya ja kumatun ta tare da fadin “good morning my chubby bubbly, how was your night?” tace “fine Abbu, how was yours?” yace “great” Bayan masu aikin sun gaishe shi ne suka fita. Ko da suka zauna kamar yadda suka saba Hanan ya fara ba ma abincin wanda bayan ta qoshi ne ta miqe tayi mishi kiss a kumatu tace “thank you Abbu, you are the best Abbu in the world” yana murmushi yace “thanks my love” ta janye su Amal suka wuce sashen ta. Bayan Farouq ya gama ba Zara abinci ne ya fara cin nashi. Zara kuwa qura mishi idanuwa tayi tana murmushi. STORY CONTINUES BELOW Ba tare da ya kalle ta ba yace “yeah yeah I know I am handsome, thanks for the complement” Fashewa tayi da dariya tace “I didn’t say..” Katse ta yayi tare da fadin “you were staring at me babes, i caught you” Tana dariya tace “I love you” yana murmushi yace “I love you too, I swear it” Lumshe idanuwa tayi tana murmushi sannan tace “I need a favour from you, please don’t refuse” Farouq ya girgiza kai yace “ooh, I thought as much” Tashi tayi ta koma bisa cinyar shi ta zauna cikin shagwaba tace “please can you make it back from the hospital zuwa yamma?” Cikin rashin fahimta yace “why? Wani wuri zamu je?” ta girgiza kai alamar a’a sannan tace “just promise me you will, akwai abinda zan nuna maka ne” Yayi murmushi sannan yayi mata kiss yace “anything for you my angel, na san ko ma meye its gonna be awesome” Tayi dariya tare da sagala hannuwan ta a wuyan shi tace “Insha Allah babylove” daga nan kuwa ta fara jefa mishi kisses irin wadanda yake so. Sunyi nisa ne wayar shi tayi ringing. Tsaki yayi yace “not again with the spoiler” Zara tana ta yi mishi dariya ya amsa, daga asibiti ne inda ake neman shi kamar kullum. Har parking lot ta raka shi sannan ta dawo. Farouq bai dade da fita bane Zara ta kira Alveena event planner don fara aikin ta. nan da nan kuwa na ga an fara decorating Garden din gidan. (Ni kuwa nace ko me za’a yi oho🤔) *********** Zaune suke a falonta ita da Hafsat wadda bata dade da zuwa gidan ba. Hafsat ce tace “babes hope you got something for him? Don na san halin ki” Zara tana dariya tace “babu abinda na siyo mishi bestie, he has everything” Hafsat ta girgiza kai tana dariya tace “Allah ya shirye ki qawata” Hanan ce ta shigo cikin sallama ta qaraso wurin Hafsat tace “Anty kin ga Aimana bata son mutane, she has been crying since” Hafsat tana dariya tace “ai wannan yarinyar kyuyan bala’i gare ta. Ga Al-ameen can yana wasan shi babu ruwan shi amma ita sai fitina” Zara tana dariya tace “Oya feed her sai ki bani ita mu gani, she definitely won’t refuse her second mum” Hafsat tace “na ma kusa bar miki ita ki hada da su Amna ai” Zara tace “wallahi ina so qawata” Hafsat dai a yanzu yaran ta biyu. Al-ameen sai Aimana wadda duka duka watan ta goma. ******** Wuraren qarfe biyar saura ne Farouq ya shigo gidan a gajiye. Dayake Garden din gidan yana ta gefe ne bai kula da wani abu yana faruwa a ciki ba. Ko da ya shiga gidan shiru babu kowa. Sashen shi ya nufa yayi wanka sannan ya shirya cikin wandon sweatpant da wata polo T-shirt. Yana gaban madubi yana brushing gashin shi ne wayar shi tayi ringing. Ko da ya duba sunan Zara ya gani. Gani nayi yayi murmushi sannan ya amsa yace “hey baby angel, where are you? Na dawo gidan na ji shiru” Tana murmushi tace “yi haquri babylove, ina Garden please come” STORY CONTINUES BELOW Cikin mamaki yace “me kike yi a nan? its not your favourite place” Dariya tayi tace “it is today, please come. Ga su Amal ma suna jiran ka” yace “okay okay, I am coming” Farouq yana shigowa garden din ya ji an fara waqar “happy birthday to you..” Cikin tsananin mamaki ya tsaya cak yayinda yake ta kallon su daya bayan daya. Gani nayi kawai ya rufe fuskar shi da hannuwan shi yana girgiza kai. Zara ce ta qaraso wurin shi tayi hugging dinshi tare da fadin “happy birthday my love” Yana murmushi yace “oh my God, I cant believe cewa I forgot my birthday”2 Zara tace “hmmm… dama fa baka taba tunawa ba” har yanzu rungume suke da juna yace “Okay, I am glad I have you to always remind me my Angel, thank you very much and I love you sooo very very much” Muryar Granny suka ji tana fadin “toh sarakan soyayya, sai kun gama soyewa sannan zaku waiwaye mu ko me??” Gaba daya aka fashe da dariya yayinda Zara tace “ke dai kawai kishi kike, fadi gaskiya” Granny ta harare ta tace “wannan karon dai tare da shi zan tafi ko kin so ko kin qi” Zara ta turo baki tare da fadin “dama na sani banyi inviting dinki ba” Granny tace “ai ko bakiyi inviting dina ba sai na zo” haka dai aka cigaba da yi musu dariya. Farouq yana rungume da Zara ne suka qarasa cikin Garden din inda ya ga Daddy harda su Safa. Cikin mamaki yace “Oh My God, Yanzu saboda birthday din kuka zo all the way from France Daddy?” Gaba daya suna dariya ne Daddy yace “toh tunda Princess ta matsa sai mun zo ai dole mu baro abinda muke yi mu zo” Farouq yayi murmushi yace “thank you very much for coming, this means alot to me” Ya kalli Mukhtar yace “Haba my friend you didn’t even give me a clue dazu da ka zo asibiti, not fair” Mukhtar yana dariya yace “ba laifi na bane abokina, I wouldn’t be the one to ruin the surprise” ya janyo shi tare da hugging dinshi yace “happy birthday to you” Farouq yana murmushi yace “thanks abokina” Haka dai aka dinga taya shi murna tare da yi mishi fatan alkhairi. BigH kuwa ya dinga kashe hotuna. Bayan Farouq ya yanka cake dinshi an ci an sha ne aka fara bashi birthday gift. Kowa ya ba Farouq birthday gift wanda yayi ta godiya amma fa banda Zara. Gani nayi ya juyo ya kalle ta tare da daga mata gira yace “baby angel where is my gift?” Kafin tayi Magana ne Granny ta kalli Farouq tace “wane gift zata baka bayan mashirmaciya ce, shiyasa nace maka na fi ta sonka” ta kalli Zara tace “an dai ji kunya” Aikuwa gaba daya aka fashe da dariya yayinda Zara ta turo baki tace “wallahi wannan tsohuwar ta takura mun, yanzu zan baki kunya don kuwa zan bashi gift wanda babu wanda ya bashi irin shi a cikin ku” Hankalin kowa ya koma kan Zara don ganin abinda zata ba Farouq yayinda ta kamo hannun shi ta dora akan cikin ta tace “I am expecting a baby my love, you are going to be a father again” Zaro idanuwa yayi cikin mamaki hade da murna yace “what??” Gani nayi ya daga Zara sama yana ta twirling dinta round yayinda ake ta yi musu dariya yace “Alhamdulillah my angel, we are pregnant again, kin bani babban kyauta my angel I love you so very much”2 Zara ta kalli qawarta Hafsat tare da kashe mata ido daya. Hafsat dai fashewa tayi da dariya. Tayi murna sossai domin kuwa ta san Zara da son yara. Su Mamy sunyi murna qwarai da jin wannan zancen. Haka aka dinga yi ma Zara fatan Allah ya sauke ta lafiya. Sadiq ne ya kalli Zara yace “Allah yasa ki haifo triplets duka mata” Saima tace “what??? It means Ya Farouq da mata bakwai kenan fa” Granny tace “takwas dai harda ni” haka kuwa aka dinga dariya. Abba ne yace “Allah yayi muku albarka gaba dayan ku” aka amsa da “ameen” Suna nan suna ta hira ne Farouq ya janye Zara suka bar wurin. Su mamy dai sai neman su suka yi suka rasa har Anty tana fadin “ikon Allah, sun tara mu a wuri sun bace” haka dai aka dinga dariya.2 ************ Ko da na biyo su ganin su nayi a babban falon shi a tsaye yayinda yayi hugging dinta tight yace “baby angel” tace “na’am” yace “you are the best thing that has ever happened to me, A yau kin qara bani wani special gift, I love you very much and will continue to love you till the end of time” Zara tana murmushi tace “abinda nake so kenan Babylove, ka cigaba da sona har abada” Yayi mata kiss yace “you got it babe” Tana murmushi tace “banda kishiya” bata rai yayi yace “uhmmm, i will have to think about that” Turo baki tayi ranta a bace ta ture shi zata tafi.2 Da sauri ya janyo ta yayi hugging dinta tare da fadin “hey come here, wasa nake yi. I have eyes for you alone my angel, kin riga kin bani komai da nake nema. You are my life and i love you like crazy my Zara” Tana dariya tace “i love you too big brother” ya bata rai tare da fadin “arggghhhh” Kumatun shi ta ja tana dariya sannan tace “i mean I love you too my babylove” Yana murmushi yace “better” Gani nayi ya janyo hannun ta yace “mu je dakina in nuna miki wani abu” Zaro idanuwa tayi tace “Ana jiran mu a garden, ka manta ne?” Ya dan bata rai yace “ba an gama celebration din ba?? Ki barsu su cigaba da hira tunda dama sun kwana biyu basu hadu ba” Yana riqe da hannun ta yace “mu je muyi tamu hirar” ya shafa cikin ta yace “i need to introduce myself to this little angel ASAP” Zara tana dariya tace “bad boy” ya girgiza kai yana murmushi yace “only for you my angel” Ko da suka shiga dakin kafin in qaraso sai gani nayi Farouq ya rufo qofar. (Wato ba’a buqatar 3rd party🤨) Juyawa nayi na koma garden don ganin abinda yake wakana a can.5 Tammat bi hamdulillah…