Koda wannan tsohuwar ta gaishe da hadiza se hadiza tai kicin kicin da fuska lokacin tana zaune tana bada wake da shinkafa.
Tabe baki tsohuwar tayi zata miƙe ta fita sega hassana ta fito daga bayi tana ta faman yamutsa fuska.
Ganin tsohuwar a zaune amman tana ƙoƙarin tashi ya sanya ta faɗaɗa far’a tare da zubewa da ƙyar tana gaishe ta.
Tsohuwar ta faɗaɗa far’a itama tana cewa.
“Dama nice maƙociyar ku dana tare a wannan gidan na jikin gidan ku, Sunana Hajiya Hauwa amman ana cemin hajja ni ƴar nan cikin gari ce wata unguwa sabon titi ƴata ɗaya aduniya hafsatu tana aure a katsina amman aiki yakai mijinta abuja tana zaune acan da mijinta da yaranta, ita ma ta saimin wannan gidan bayan mahaifinta ya rasu dafatan zamuyi zaman mutunci atsakanin mu”
Hajjo ta faɗa cikin murna dayake tana da son mutane.
Wani irin sanyi hassana taji atake taji tana son hajjo tun da daman bata saba da kowa ba domin duk wanda zatai hurɗa dashi tofa yasan hadiza seya zame kasancewar hadiza ita ƴar unguwa ce.
“Nikuma sunana hassana ni ƴar ƙiru ce hussainata tana aure acan da yaranta uku se mahaifana aure ya kawoni nan bani da kowa anan se Allah seku ma ke daya kawo min dafatan zaki ɗauke ni matsayin ƴarki”
Hassana ta faɗa cikin raha.
“Aikam ammi ta samu ƙanwa” hajja ta faɗa tare da miƙewa ta kama hanyar soro wanda har waje seda hassana ta kaita sannan ta dawo.
Koda ta dawo gidan Basira mai shekara tara da zainab mai shekara takwas ƴaƴan hadiza sune suka hau yada mata magana.
Murmushi tayi ta rabesu ta wuce ɗakinta.
Kwanci tashi babu wuya wajan Allah yau ta kama laraba ta bawa ranar samu tsakar dare hassana ta kamu da ciwon naƙuda iya tashin hankali malam habu( baba ) ya shiga yayi zarya wajan hadiza yafi sau goma akan tazo ta taimakawa hassana amman taki daga karshe ma seta kunna rediyo.
A ɗimauce ya fita gidan hajja ya shiga buga mata ƙofar gate ɗinta cikin nutsuwa ta fito tana waye.
Da karkarwa baba yace.
“Nine Habubakar baban basira”
Bata gane ba amman haka ta buɗe mai ganin fuskar shi yasa taɗan faɗaɗa far’a tana cewa.
“Au lafiya malam habu?”
A kiɗime yake shaida mata meke tafe dashi da zafin nama hajjo ta koma ta ɗauko mayafi suka fita.
Lokacin da suka shiga gidan naƙudar takai ƙololuwa wajan kankama haka hajja ta tsaya tana bata taimako domin koda ance atafi asibiti ma lokaci ya ƙure domin kan ɗa ya kawo kai domin fitowa.
Ana kiran asubahin farko.
Yarinya ta faɗo duniya takwa tsanyara ƙara.
Wadda nan da nan ta cika gida da kuka hajja ta ɗagata tana mata addu’a kana ta naɗeta a zani bayan ta yanke mata cibiya.
Sosai hajja ta gyara ɗakin tare da ɗora ruwan zafi ƙarfe shidda hassana tai wanka da taimakon hajja ta gyarata tsaf taima jaririya wanka.
Ɗaki se tayar da ƙamshi yake hajja ta haɗe kayan jini zata wanke Allah ya jefo habiba kanwar malam habu mai binsa wadda ya aika aka kirata ita ta amshi kayan ta wanke.
Hajja bata bar gidan ba seda ƙanwar hassana tazo hussaina.
Wannan karamcin da hajjo tai musu yasa malam habu yayita mata godiya kamar ze ari baki abin har kunya ya bawa hajja
wannan shine silar daya sa malam habu yaji kaf unguwar bashida kamar hajja domin abin da taiwa matarshi ko mahaifiyar shima haka zataiwa matar tashi.
Ranar gidan yayi ta ɗaukar maƙota da ƴan uwa ƴan barka amman hadiza ko leƙe sema da daddare data sanya kiɗa da fanteka na habaicin ya zama uban mata.
Mahaifan hassana sun so ɗauketa tayi wanka agida amman hajja tace su bari tunda tana kusa zata dinga zuwa tana mata haka kuwa akai hajjo kullum da kalar kayan arziƙin da zata kawowa hassana banda farfesun data ke yo mata ta kawo mata sosai hassana da baba kejin daɗin abin arzikin hajjo.
Ranar suna na zuwa yarinya taci suna ummul-khairi sunan mahaifiyar malam habu innah data rasu wadda aka mata laƙabi da ummi.
Anyi taron suna lafiya angama lafiya mai jego tana cikin ƙoshin lafiya domin koda yaushe hajja tana aiko mata da abin arziƙi shima kuma malam habu yana iya bakin ƙoƙarin sa ta ɓangaren hadiza kuwa ta saki ranta sosai ganin hassana ta haifi mace.
Ummul yarinya ce fara mai kyau da ita tun tana jinjira take da shiga zuƙatan mutane duk faɗan babansu wanda yaran sa ke mugun tsoron sa baya hana ya dauki ummul yana jefata yana furta.
“Uwata tafi ta kowa”
Ahaka sukai arba’in suka rankaya zuwa ƙiru seda tai sati biyu ta dawo gida lokacin data dawo kuma al’amura suka sauya domin baba ya cinye jarin shagonsa baya zuwa ko ina se zaman gida talauci na saka shi cin mutunci domin hatta ƴan cinikin hadiza ma wani bin aguje yake binsu.
Da ƙyar suke sha haka zalika makarantar boko ma yace su basira zu dawo gida shi bai da kudin biyan kuɗin wata.
Ganin haka yasa hadiza ta mayar dasu da kanta.
Rayuwar gidan ta koma se a hankali ɗan tuwon da ake samu ana yi ada yanzu yafi ƙarfin su,, ummul nada wata biyar hassana ta samu ciki wanda malam habu yayita surfa masifa shifa sedai a zubar bai da abin da ze ciyar dasu kuka hassana ta sanya domin itama tafi buƙatar zubar da cikin fiye da komai sabida a yanzu ma datake da ƴa ɗaya cin cikinta na gagararta bare kuma ta kuma samun wata ƴar.
Ahaka hajja tazo ta tarar da wannan masifa wanda nan ta rufe shi da faɗa akan cewar yayi haƙuri yawan haihuwa daga gareshi ne bada ga matan ba idan har baze kauda kai ba to suma bazasu dena ɗaukar ciki ba, sabida tsananin kunyar hajja yasa yabar maganar zubar da cikin amman dai kam cin mutunci kullum yana tsakar gida yana yinsa kuma dole hadiza ta zubo mai wake da shinkafar ta na saidawa yaci.
Ummul bata isa yaye ba hassana ta yayeta hajja ta ɗauketa yarinyar bata da wani kuzari sabida shan cikin datai amman yadda hajja ta zage tana bata kayan gina jiki yasa ummu ta ciko tai kyau.
Shekarar ummul ɗaya hassana ta haifi ɗiyarta mace sadiya.
Sabida jarabar baba ko kallon sadiya baiyi ba ko ranar suna ma mahaifin hassana shiyayi hakika.
Sadiya nada shekara guda hassana ta haifi kausar daga kausar ta haifi ihsan.
ko wanne ya bawa ɗan uwan sa shekara guda abubuwa sun ma hassana yawa wadda ummul ke ce mata.
(BAMU) ma’anar shi Babarmu.
Kaf ƴaƴan babu mai iya wanke wa ɗan uwan sa pant ga yara ƙananu basu san babu ba.
Cikin haka Allah ya kawo masu allurar riga kafi anan wata nurse ta bawa hassana shawarar akan taje asibiti ai mata allurar tsarin iyali domin ta sami ta zara acikin haihuwar data yawan yi.
Ranar litinin na zuwa hassana ta goya ihsan suka tafi asibiti anan aka yo mata allurar ta dawo gida.
Abu goma da ashirin sunwa hassana caa domin mahaifin ta dake taimakonta sunyi hatsari a hanyar zamfara shida mahaifiyarta sun rasu sosai rasuwar ta kaɗa hassana nan da nan ta rame acan ta zauna har akai kwana sha huɗu kafin ta dawo gida.
Hajjah ke taimakonta ganin abin na yawa yasa ta fara ɗaura kayan miya haka baba ze rance kuɗin kuma tai magana ya ci mata zarafi.
Rayuwar gidan ta kacame yanzu hadiza ta dena kishi da bamu sabida kowa ta kan shi yake kowa fafutukar abin da ze rufawa kansa asiri yake daman hadiza ita yarant uku kuma bata kara haihuwa ba sannan kuma manya ne saɓanin bamu data ke da ƙananun yara nan da nan girma ya soma saukar mata sabida wahala ga cin mutunci baba wanda idan ya dasa cin mutunci jikinsa har rawa yake sabida talauci babu abin da baya sakawa.
Shikenan kullum yana gida ba cass ba as yana tsakanin mata yana karɓe ƴan canjin su ahaka zuciyar sa ta mutu har yamo ma baya fita aikin koya samu sedai yaci yasha ya tafi majalissa yana buɗa hanci.
Sukuwa su hassana tsabar tsoron shi yasa basa iya yi masa musu ko gardama ga dik abin da ya san yasu.