BABU SHI A ZUCIYATA

BABU SHI A ZUCIYATA

 

🇳🇬®
*_ABORIGINAL WRITER’S ASSOCIATION📚✍️._*
[❄Dance above the surface of the world,let your thoughts lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

 

*_STORY & WRITTEN_*
*By*

*AUNTY BABY*✍🏼

 

*_Da sunan Allah mai rahama nake fara wan’nan book din Allah yasa abin da zan fada a wan’nan littafin ya f’adakar da kuma nisha’dan’tarwa sai fa kunyi hkr dan sabon shiga ce_.*😄

 

*Dedicated to Sady baby*🥰🥰

*Wannan page din na kine my friend 😙😙 kiyi yanda kike so da shi.*

 

*_DONT 4GT TO VOTE,COMMENT AND ALSO FOLLOW US ON WATTPAD @ AboriginalWrtersAsso._*

 

“`Bismillahir rahmanir rahim“`

 

2019 publishe.
*Page* 1⃣

 

“Hameeda dan Allah ki tashi mu tapi kin san yaya Yazeed baya san jira ko, ”

“Kai keko fadila kin cika naci mutum be gama shi’ryawa bane zai fita shima Yaya Yazeed din da kike mgn ai sai da ya shirya san’nan ya fito to Allah sai na.”

“Gama hmmmm lallai hameeda kin raina yay Yazeed .”

“way kuko baza ku fito ba kowa ya shirya amma ku kuna Nan kuna wan’nan kwalliyar banza.”

” Yauwa momy gwara da kika zo ni na shirya hameeda ce bata gama ba .”

“Kai hameeda maza tashi ku tapi momy.”

” Sauran kadan fa”.

” Allah ranki zai baci.”

“to momy nagama.”

” To sai kun dawo.”

Mikewa tayi ta dau gyalan ta ta yafa suka fita .

suna fita sukaga duk Yan matan gidan nasu kowa yaci kwalliyya kaman Wanda za’aje kasan sarauniyar kyau.

Yaya Yazeed ne yace.

” ku sai yanxu kuka ga daman fitowa?”

Fadila tace ” yaya dan Allah kayi hakuri”.

yace .

“kowa ya huce ya hau mota”.

Hameeda kon ko kallo ma be isheta ba.

Yaya Yazeed yace.

” Ke”

kowa ya juyo ita ko tapiya ma tacigaba dayi .

saida ya qara cewa

“Ke”.

Sai Saudat tace .

“Aunty Hameeda da kefa Yaya Yazeed yake”.

Cikin fusata Hameeda tace .

“To ni ke ne sunana ko hameeda”.

Cikin b’acin rai yaya Yazeed yace .

“Wato kin San ma dake nake ko ,to wacce motan zaki hau ba wan’nan ba.”

Tace ” Lallai motan ma Sai an gaya min wace zan hau, naga dai mutum bashi ya siya ba.”

Ta fada tana mur guda baki.

Yaya Yazeed yace .

“Ni kike fadawa haka to baki isa ki hau ko wace mota ba sai wan’nan sai dai in ki fasa zuwa.”

Cikin masifa tace .

” Akwai wallahi bazan hau motan ka ba.”

Kowa ya huce ya shiga mota ban da Hameeda.

Fadila tace ” Hameeda dan Allah kije ki hau motan”.

“Fadila wallahi bazan hau motan shi ba”.

Fadila tace .

” hmmm ke dadi na dake saurin fushi indai Yaya Yazeed ne ai kon saba ta fada tana dry,

mtswww Allah ya kyauta muku.”

” Nusaiba kenan ke kuma wayasa bakin ki ban sani ba hmmm wallahi yanzun zan basa ma yariya baki”

inji Nusaiba

“haba dan Allah ke kulum in ba’ayi rigima ba baki Jin dadi Ina ruwanki da mgn mu.”

“Da ruwa na fadila barta wallahi ta min ne yanxu zata gayama jikin ta dan ta sanni sarai”.

” wai me kuke jira ne?”

cewar Aunty talatu

Bakomi Aunty yanxu zamu wuce”.

“To a dawo lfy “.

Kowa ya shiga mota Amma Hameeda take shiga ta Kai wajan motar su Yaya Areef, taji yay Yazeed na cewa

” Allah hameeda kika shiga sai kin sani waye.”

Hameeda tace .

” Ina ruwan mutum na ne da ni.”

ta fada a zuciyar ta

” kizo ki huce to “.

Yaya Yazeed ya fada.

“naji”.

hakan nan dai ta hau suka dau hanya daman motan daga ita sai Nusaiba to ba shiri suke ba shiyasa ba Wanda yayi mgn har suka kai wani hall din party.

daman bikin abokin Yaya Yazeed din ake to shine yace dik Y’an matan gidan da samari su shirya su tapi.

suna zuwa kuwa kowa ya fito aka fara shiga Amma yay Yazeed ko Alamar fitowa baiyi ba, kuma bai bude musu ba.

Nusaiba tace “Yaya Yazeed kowa ya tapi fa”.

yace

“To rike ke nayi ne”.

Tace ” A’a naga baka bude bane “.

Tsaki kawai yayi ya bude mata ita kon Hameeda ko kala Bata ce mai ba ta fita .

Suna fita fadila tazo suka wuce tare.

Suna shiga gurin kallo ya koma kansu barin ma Hameeda.

Ai kam Nusaiba ta hada rai kamar bata taba dariya ba.

 

 

 

 

*in kuna so a cigaba ba to zanga comment*.

 

 

*Comment*
*Share*
*vote*

 

 

*Aunty Baby ce*✍🏼

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

 

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻

 

🇳🇬®
*_ABORIGINAL WRITER’S ASSOCIATION(ƳAN ASALI)📚✍️._*
[❄Dance above the surface of the world,let your thoughts lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

 

*STORY & WRITTEN*
*BY*
*AUNTY BABY*✍🏼

 

*Dedicated to my family*😘😘😘

*_DONT 4GT TO VOTECOMMENT AND ALSO FOLLOW US ON OUR WATTAPD @AboriginalWrtersAsso._*

 

 

“`Bismillahir rahmanir rahim“`

2019
*Page* 2⃣

Nusaiba ta hada rai.
Ita kuwa Hameeda ma Bata San tanayi ba.

Hameeda tace , ” Fadila nifa ban San kallo wallahi , jiba sai kace sunga wani abu.”

Fadila dai murmurshi kawai tayi har suka qarasa wajan ango da amarya.

Angon yace,

” ai nayi fushi sai yanxu zaku zo.”

Fadila tace, “Kai Yaya Safwan ai munzo da wuri ma”.

Yace “Ina shi my friend din”?

Fadila tace, “gashin zuwa”.

Hameeda tace, ” Amarya ya kike?.”

Sadiya amarya tace,

“lfy lau sai yanxu zaku zo ko”.

Hameeda tace, ” hmmm da kika samu ma muka zo, bari muje mu zauna”.

samun wani gurin da ba maza suka zauna.

Fadila ta fito da wayan ta tace,

“sis bari in mana pic”.

Suna cikin pic kawai sai ga wani guy ya zauna gujeran dake kallon Hameeda.

ita kuwa Bata ma san da zaman shi ba hoton su kawai suke.

sai can Saurayin yace,

” haba ‘yan mata ba mgn ya kuke”?

Fadila ce kawai tace,

“lfy”

Yace, “wai baki mgn ne”?

ya nuna Hameeda.

duk da haka ko kallo shi din batayi ba .

Yaya Yazeed ne sai da yagama cin maganin shi sai gashi ya shigo.

y’an Mata gurin kon suka rude kowa sai gyara fuska da gyale ake shiko ya qara hada fuska har ya qara sa gun angon.

Angon yace ” yeah my friend nayi fushi ace biki na San yanxu zaka zo?”

Yaya Yazeeda yace .

“oh sorry abokina”.

Angon yace ” hmmm to ya”.

Mc ne ya fara sanarwa ga babban abokin ango nan nafa aka fara sakin kida yan’mata da samari aka fara chashewa ana zuba liqi.

Mc yace Amarya da Ango su fito, Nanfa aka fara liqi .

Yaya Yazeed ma ya fito ya fara liqi har Ango da Amarya suka koma aka sa wakar Wizkid ta fever .

Daman Hameeda nasan wakar, nan kowa ta fito tana rawa.

kamar ance Yazeed dago ya ganta ana ta zuba Mata kudi, ita kuwa sai rawa take.

Daman Hameeda da rawa hmmmm ba’a mgn.

Baisan lkc da yaje ya figeta ba tana kwa’cewa ya dalla Mata mari.

Aikuwa taji Marin nan.

Cikin b’acin rai ya yace .

” Wato ke iskanci da kike yi ne yau zaki mana ko, wacce yariya kikaga tana rawa a gidan mu? banza Yar iska”.

Cikin tsiwa Hameeda tace .

” Ni wallahi ba yar iska bace, kuma sai na qara yin rawan dan baka isa ka hanani abun da nayi niya ba”.

Wani marin ya qara mata .

yaya Areef da yaga fitowan su yace.

” Haba Yaya Yazeed yau daya dan tayi rawa ai ba wani abun bane….”

Wani kallo da yayi masa ya Hana sa qarasawa .

Wuce ki shiga mota .

“Ba inda zani tunda dai ba kafan ka bane, ka takura min ka tsaneni mai na tare ma.”

tana fada tana kuka😭

janta yayi da karfi Wanda har sai da ta yarda jakarta, yasa ta a mota .

shiko Yaya Areef kallon ikon Allah kawai yake .

ya figi motan da gudu be tsaya ku Ina ba sai bakin gate din gidan.

horn yayi mai gate man din yayi saurin budewa ana bude mai ya huce ko gaisawan da suke da get man din bai tsaya ba.

ya bude ya fito yace.

” fitar min a mota”.

Hameeda kuwa tana fitowa tace.

” motar banza motar wofi ai daman Kai ka sani ba Ni na shiga ba mtswwww “.

tayi hucewar ta.

galala Yaya Yazeed ke kallonta yace .

“Lailai yarinyar nan ta manta koni waye”.

Hameeda tana barin wajan part din su ta wuce, tana shiga parlour momy tace.

” Hameeda har kun dawo ne’?

” Eh momy”.

kawai tace ta huce dakinta.

Magana take tana fadin.

” Wai Ni Hameeda Yaya Yazeed zai yiwa haka, hmmmm wallahi sai yayi daya sani kuma rawa yanxu na fara tana cire kaya tana fada.

(niko nace mai yasa bakiyi a gaban shi ba 🤣)

tana gamawa ta fito parlour momy tace.

” Hameeda yanxu yayan ku Yazeed ya zo wai kije ki kaimai abincin shi .”

Hameeda tace “Kai momy daga dawowar mu , shifa wannan yaya Yazeed din ya cika sa mutum aiki .”

“Hameeda yanxu Kai abincin ne aiki”?

cewar momy

” Wallahi ke da shi ba ruwana”

“To momy yanxu fa muka dawo ko hutawa ba muyi ba .”

Momy tace ” Hameeda baza ki wuce ba”.

” To momy “.

kitchen ta huce ta fara hadamai tana masifa.

” wai shi mutum saikace ni daya ce a gidan yabi ya takura min .

tana cikin hadawa ne taji Fadila na mgn da momy saiga ma .

Fadila tace ” hehehe 😈 qanwar Yaya Yazeed ya aka riga mu dawowa tana fada tana dryn shaqiyanci”.

Hameeda tace ” oho ban sani ba banza kawai Ni ki daina hadani da wannan mutumin.”

fadila tace ” wai wa kike hadama abincin ne?”

Hameeda tace “wannan yayan naku mana”.

Fadila tace ” wanne kenan kinsan suna da yawa “?

Hameeda tace “Yaya Yazeed mana wai in hadamai abincin kinji gulma fa.”

Fadila tace” hmmm kije ki kaimai kafin ya fara masifar shi”.

Hameeda daukan tire din tayi ta nufi part din Yaya Yazeed din .

tana zuwa ko salama ta shigewar ta d’akin.

Yana zaune akan kujera ya daura kafan shi zaman tebir din dakin laptop dinshi yake dannawa.

Abincin kawai ta ajiye zata fita yace

“Ke”

tsayawa kawai tayi Bata juyo ba.

yace “baki iya sallama bane”.
Cikin rainin hankali tace .

“oh namanta”.

Cikin fusata yace .

“dan ubanki sallama ce kika manta yau zaki gane bana wasa dake”.

 

Cikin b’acin rai ya Mike ya nufi inda take.

 

 

 

 

To komai Yaya Yazeed zaima Hameeda 🤔🤔🤔🤔🤔

 

 

*Mu hadu a next page*🤝

 

*Aunty baby*✍🏼

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻

 

🇳🇬®
*_ABORIGINAL WRITER’S ASSOCIATION(YAN ASALI)_*📚✍🏼.

[❄ Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

_*DON’T 4GET TO VOTE, COMMENT AND FOLLOW US ON WATTPAD @*_
*_AboriginalWrtersaAsso._*

 

*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏼

*Dedicated to SAUDALA fan’s group*😊

*gaskiya naji dad’in comment din ku Allah yabar kauna ina yinku irin over din na*. 😘😘😘😘😘😘

*Bismillahir rahmanir rahim*

2019 Published.
*page* 3⃣

 

 

Cikin ‘bacin rai ya Mi’ke ya nufi inda take Yace ,

“Ke Hameeda dan kan uwarki Ni sa’an ki ne? dik gidan nan wa kika ga Ina wasa da shi”?

Hameeda tace, ” oho tambaya ta kake ko mai, nifa gaskiya ka takura min haka kawai…. ”

Yaya Yazeed kallonta kawai yake, shi besan mai yasa yanxu baya ma Hameeda hukunci ba ko yayi niyar zaneta sai yaji ya kasa Amma in be Zane yariyar nan ba baza ta saitu ba.

juyawa yayi bayan shi kawai yaga wata wayan canji, d’auka yayi ya nufo ta.

Hameeda kuwa tana gani ya d’au abin duka ta fara zare ido dan tasan bashi da wasa wajan duka .

tace, ” Yaya Yazeed dan Allah kayi hakuri wallahi bazan qara ba”.

Yaya Yazeed yace,

“lallai kin Raina min wayo ai yau sai kinji a jikin ki .”

yayo kanta kuwa ta fasa ihu tana fad’in,

“wayyo Allah jama’a Yaya Yazeed zai kashe ni”

“Ke dalla ki rufe min baki ubanki na miki”.

Aunty Talatu dake wajan window d’akin taji ihun Hameeda tace,

” Hameeda! Hameeda! Lpy? ”

Hameeda taji kaman ana magana hakan yasa tako q’ara ihun.

Aunty Talatu ta sake cewa, “wai lfy kuwa kina tama mutane ihu Hameeda”?

Tace, “ba Yaya Yazeed bane zai dakeni”

Aunty Talatu tace, “Haba Yazeed mai tamaka kai kuwa”?

ko kallo Aunty Talatu baiyi ba ya wuce bedroom Yana ‘kwafa.

Hameeda kuwa da tasamu bai ta’ba lafiyan jikin ta ba ta fito d’akin tana Allah ya isa.

Aunty Talatu tace, “wai mai kike mai ne, kinsan Yazeed ba ha’kuri gare shi ba.”

” ba fa komai na masa ba”

Hameeda tace ta wuce, tana zuwa d’aki
Momy tace mata,

“ke kuma daga Kai abinci saiki nemi wuri ki zauna?”

” Momy sani yayi na gyara masa d’aki”

“OK”

kawai momy tace da ita.

Nusaiba ce ta shigo d’akin tana wani bata rai .

Tace ,

“ke Hameeda Haj Jadda na Kiran ki”

Hameeda tace, “naji”

“Momy bari inje wai Jadda na kira na”

“to Hameeda in zaki dawo kije gun Auntyn ku Amarya kice ta baki kayan dan jiya na siyan muka less ke da Fadila da Nusaiba”

“yeeeee Momyna kenan Allah ya amfana, Amma Momy mai yasa kika siya da Nusaiba kinsan dai Mamanta ba so take ba ko”

“Haba Hameeda ke har yanxu baki hankali ba, yanxu kawai sai in siyan miki abu inki siyan ma Yan uwanki”

” to Momy mai yasa baki siyan ma Saudat ba naga dai ita ce ma ‘yarki, Amma ki ba mutum abu ba godi bare nagode.. ”

“to Hameeda maiye rayuwan in shi be gode ma ba ai Allah nagani ko “?

“hmmmmmm Momyna kenan Allah ya barmun ke ” ,

“maza kije K’iran da ake miki kinsan halin Jadda dai”

” to Momy ”

fita tayi a d’akin taje Kiran Jadda, daman ba nisa gare su ba.

part biyu ne tsakanin su daga na Aunty Amarya sai na Maman su Nusaiba.

tana shiga Jadda tace,

“sai yanxu kikaga daman zuwa gimbiya..”

Hameeda batace Mata komai ba kawai tace,

” Ina wuni”

“lfy” kawai Jadda ta amsa.

” daman na kiraki ne in fad’a miki gobe ubanku zai dawo sai ki fad’awa uwarki dan asiri ya karye sai abi wani bokan.”

sororo Kawai Hameeda tayi tana jinta _asiri_ ta ‘ƙara maimaitawa _lallai ma Jadda nan.._

“hmmm Jadda kenan ai asirin ma matsayi ne wata dik abinta Bata isa tayi asirin ba kuma yaci……. ”

“Laaa Haj Jadda kike fad’awa magana, lallai Hameeda kin riƙa”

cewar Maman Nusaiba da zuwan ta kenan tayi maganar .

 

To fa wan’nan gida nasu Hameeda ya yake ne?🤔🤔🤔🤔

*Sai mun had’u a page nagaba muji yadda wan’nan cakwakiyar zata kasance*.

 

 

 

*comment*
*vote*
*share*

 

 

Aunty Baby✍🏼
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻

 

®🇳🇬
*_ABORIGINAL WRITER’S ASSOCIATION(YAN ASALI)_*📚✍🏼

[❄Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

 

_*DON’T 4GET TO VOTE, & COMMENT FOLLOW US ON WATTPAD @*_
_*AboriginalWrtersAsso.*_

 

*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏼

 

*Dedicated to BABU SHI A ZUCIYATA FANS GRP*.💃🏻💃🏻🥰🥰

 

*Bismillahir rahmanir rahim*

 

2019 published.
*page* 4⃣

 

“Barta-barta Hajara ai tasha a nono”

cewar Haj Jadda.

Ita kuwa Hameeda tana tsaye ko motsi takasa dan halin Haj Jadda inda sabo tasa ba dashi kaman ba ita ta haifi ubanta ba.

kwata-kwata Bata sonta sabda kawai da aka haifi Hameeda ba’a sa mata sunan taba shine ta ɗau Karan tsana ta d’aura mata.

duk abinda Hameeda zatayi bata birgeta shiyasa itama bata wani shiga harkarta.abinda ke gabanta uwarta, bata son rashin mutuncin da take mata sam duk kuwa da irin abinda Mommy ke mata bata gani.

“Au tsayawa kike akan mutane shegiya mai halin dagin uwa,toko dukanmu zaki ne”

“Ai wallahi gwara da halin dagin uwata nayi banyi naki ba”

Hameeda na fad’ar haka tayi tapiyar ta .

 

“Haj wallahi yariyar nan Bata da kunya yanxu harke zata dinga gayawa mgn”

cewar Naman Nusaiba.

“Ai barta Yusuf d’in ya dawo, zata san dawa tayi “.

Hameeda kuwa tana fita part d’insu ta wuce ,kota kayan da Momy tace ta amso banta biba.

 

*WACECE HAMEEDA ?*

Hameeda dai ‘yace ga Alh Yusuf, Alh Yusuf su uku ne a d’akin su, Alh Ahmad shine babba sai Alh Yusuf sai kuma autan su Alh Abubakar dika Haj Jadda ce ta haife su.

 

Mahaifinsu ya daɗe da rasuwa tin Abubakar Yana shekara 5, daga nan Haj Jadda ta d’au nauyin karatun su har suka gama Allah yasa suka samu wani abu a duniya dan Alh Ahmad babban d’an kasuwa ne shiko Alh Yusuf ma’akacin Gomnati ne .

 

Alh Abubakar ma dai d’an kasuwa ne,Alh Ahmad ne ya fara yin aure ya auri yariyar mai gidan shi bayan shekara 5 Allah be basu haihuwa ba Nan fa Haj Jadda ta fara masifa saidai yayi aure ba’afi wata ba da zance Allah ya bata ciki nan fa ake ta murna har Allah ya sauke ta lfy ta samu namiji mai suna Yazeed tin daga Nan Bata qara haihuwa ba har Alh Yusuf yayi aure ya Sami mata mai suna Hajara.

 

Hajara na shekara ta haihu itama namiji ta samu aka samai Areef tin daga nan Haj Jadda ta ‘Kulla da Hajara Bata da abokin shawara sai ita daga Areef sai shamsiya sai kuma Nafisat shima Alh Abubakar Allah ya had’a shi da wata Ameena.

 

Aunty amarya a shekaran kuma Alh Yusuf yace zai ƙara aure lokacin Hajara tana da cikin Nusaiba haba Nan fa Hajara tace Bata San zance ba shikuma yace sai yayi da da farko Haj jadda ta Hana sai daga baya kuma tace yayi ba komai ai kon rana d’aya aka d’aura musu aure shi da Abubakar amare sun tare lfy .

Shekaran su d’aya suka haihu Ameena ta haifi ƴarta Fadila, ita kuma Zainab Momy ta haifi ƴarta Hameeda.

 

Haj Jadda taso asa sunan ta ne sai kuma aka sa sunan yayan Momyn data rasu hakan yasa Haj Jadda ta tsani Momy kenan.

 

*Cigaban labari.*

 

Pls in nayi kuskure ku min afuwa kunsan Ni din sabon shiga ce kuma Dan adam 9 yake bai cika goma ba barin mu sabon shiga . Allah ya barmun tare 😘😘😘😘😘😘

 

 

*Comment*
*vote*
*share*

 

 

Aunty Baby✍🏼
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻

 

🇳🇬®
*_ABORIGINAL WRITER’S ASSOCIATION_*📚✍🏼

[❄Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

_*DON’T 4GET TO VOTE, COMMENT & ALSO FOLLOW US ON WATTPAD @*_
*_AboriginalWrtersAsso._*

 

 

*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏼

 

 

_A gaskiya zan daina rubutun litafin nan sbd ba’a comment ko litafin ne be muku dadi to ban sani ba in be muku dadi ne gwara tin wuri in sani in daina Bata lkc Ina yi kunsan dai yanda typing yake kuma muna da abinyi pls in baku so to in sani in daina bata lkc na_ 🙂🤨

 

*Bismillahir rahmanir rahim*

 

*page* 5⃣

 

Hameeda ce sanye da uniform din makaranta riga da wando sai karamin hijab kayan son Mata kyau sosai dan Hameeda fara ce tana da dan tsawo kadan Bata da Kiba sosai .

“Momy Ni na tafi kin San yau zamu fara test”.
cewar Hameeda kenan

Momy tace “to Hameeda Allah ya taimaka, san’nan ki fara zuwa part din Haj jadda ki gaisheta sannan sai ki huce kin San yau daddyn ku zai dawo “.

Hameeda tace “Kai Momy kin San fa nayi lati kuma su fadila na jirana Kar in Bata musu lkc ki bari in na dawo pls Momy “.

“To shikenan A dawo lfy “.

“To Ameen Momyn na “.

 

Tana fita kuwa taci karo da Fadila ta biyo Mata su wuce .

“A Fadila da yanxu zanje part dinku ashe kin taho “.

Fadila tace “Eh wallahi Hameeda kin San yau zamu fara test Kar ya hanamu shiga Sir haidar “.

 

Hameeda tace” hhhhh wallahi bai isa ya Hana mu shiga ba tinda dai my uncle Hamed na nan “.

Suna fitowa bakin Gate din gidan sai ga Yaya Areef Nan yace to su shiga ya Kai ku.

Hameeda tace ” Yaya Areef Kai da zaka tapi office kawai ka bari mu tapi karmu saka lati “.

Yay Areef ” yace ku wuce ku shiga kun tsaya min surutun ku “.

To kawai suka ce suka shiga

Minti 10 ne ya kaisu dan basu da wani nisa da school din
Yana sauke su suka wuce .

Hameeda sai zabga murmushi take .

Fadila ce ta zungureta tana f’adin,

” ke Hameeda Allah ya shirye ki yanxu zaki je ki hadu da uncle Hamed ko kuma kin San test zamu shiga Allah yasa ma bai zo ba”.

ta fada tana dariya

Hameeda tace ” aniyarki ta biki kin san da in banga uncle Hamed ba Allah bazan iya rubuta komai ba…….”.

Muryar da tajine ya hanata qarasawa . k’yakyawan saurayine ajin farkon dan gayu fari tas da shi .

” sarauniyata “.

ya qara fada a qaro na biyu

Wani murmushi Hameeda ta sakin mai tana cewa ,

“my uncle Hamed “.

Yace “Na’am sarauniyar kyawawa kin tashi lfy? da fatan dai kina cikin koshin lfy dan wallahi jiya kadai da banganki ba Ina cikin tashin hankali, Hameeda kece farin cikin Hamed Allah ya rasaki zai iya rasa ransa gabaki daya Yana fada hannun shi dafe da zuciyar shi “.

Habawa Hameeda ai sai taji ta kaman a sama gajemare

“My Hamed Ni da Kai mutu ka raba takalmin kaza wallahi duk randa aka rabani da Kai an rabani da Raina ina sonka kaman Raina……

 

 

“Hameeda! Hameeda!! kizo mu shiga class fa ko so kike a hanamu yin test din ku da soyayya Bata isar ku”

Fadila ce mai mgn .

 

Uncle Hamed yace “oh sister mu kiyi hkr yanxu zata zo “.

Hameeda tace “my Hamed na tapi sai mun fito daga test “.

Uncle Hamed yace “to my sarauniya sai na shigo dan yanxu zan shigo class din ku in muku English da fatan dai kinyi karatu sosai duk da dai nasan my Hameeda akwai kwakwalwa”.

Hameeda tace “hmmmm my Hamed kenan “.

Har bakin class din su ya rakata sannan ya huce office dinsa yana tinanin shi fa wallahi gwara ya je gidan su Hameeda yayi mgn tun wuri Kar ya tsaya kallon ruwa kwado ya mai kafa dan in ya biyewa Hameeda sai wani ma ya riga shi dan kullum sai in yayi Mata mgn sai tace wai sai ta gama secondary to Allah shi ya gaji haka dai yayi ta surutun shi shi kadai .

******

Yay Yazeed ne yayi Shirin shi na zuwa aiki suit ne fari ajikin shi gashi nan nashi kaman na larabawa yasha gyara yay Yazeed dai fari ne sosai, Yana da tsawon Kashi, Yana da dan fadi daga saman, in ba kaji Yana hausa ba sai kace ba bahaushe bane fuska nan tashi murtik dan kafin kaga Yana dry da aiki sai in yna tare da iyayan shi maza Amma in ba hka ba ka dade baka ga dryn shi ba fitowa yayi daga part din shi hannun shi dauke da jakan aikin shi ,dayan kuma rike da faran riga ta likitoci kenan motan shi ya nufa an wanke mai ita sannan yasa kayan aikin shi a ciki ya nufi part din Haj jadda .

Salama yayi Haj jadda tace ,

zaune a daya daga cikin kujeran parlour ta zubama tv ido Kai kace tana jin abinda ake fada ,

“A’a gaka miskili daga Ina kuma “.

Yay Yazeed yace haba matas sallama nayi Amma baki amsa ba kin fara wani waye miskili… ?”

Haj jadda tace ” yo ni Ina ruwana da sallaman “.

Yay Yazeed yace ” au haka zakice to in kuma in da na fito “.

 

“To ka koma mana “.

 

“Hmmmm haba matas wai waya tabokine?”

” Ni tashi ka ban guri ace yanxu duk iyayan ka ba mai ma f’ada “.

“F’ada kuma Haj jadda mai nayi “.

cewan yay Yazeed yana dan murmushi .

 

Haj jadda tace ” kayi aure kaki yin aure kafi so har sai kanin ka Erif yake ko an anreef yayi ya barka “.

“Hhh Haj jadda ke har yanxu baki iya Areef ba “?

Haj jadda tace “hmmmm to suna ne kaman na aljanu baza a sama yara sunan mu nada ba sai wa’in Nan sunan banzan “.

 

 

 

*Gaskiya yau na muku typing da yawa qila ma har da na gobe*😄

 

 

 

 

*Comment*
*vote*
*share*

 

 

Aunty Baby ce ✍🏼
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻

 

🇳🇬®
*_ABORIGINAL WRITER’S ASSOCIATION(YAN ASALI)_*📚✍🏼

[❄Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

*_DON’T 4GET TO VOTE, COMMENT & ALSO FOLLOW US ON WATTPAD @_*
_*AboriginalWrtersAsso.*_

 

 

*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏼

 

*Dedicated to my only son Areef*🥰🥰

 

*Bismillahir rahmanir rahim*

*page* 6⃣to7⃣

Ko da su Hameeda suka tashi a school sai suka fito Gate din mkrt su uku da Fadila da Hameeda sai kuma wata class mate din su zarah suna tafiya suna fira .

Sai ga motan uncle Hamed nan yayi parking kusa da su ya fito Yana kallon Hameeda Yana Mata wani shu’umin murmurshi yace,

” Hameeda shine ko ki jirani ko”…..

 

“Hmmmmmm my Hamed kasan ba Ni daya bace shiyasa “.

 

Yace ” to naji yanxu dai kuzo in qarasa da ku gida”.

 

“A’a wallahi Karmu baka wahala “.

cewar Fadila tana kallon Hameeda taga ta yarda ko Bata yarda ba sai taga Hameeda ko a jinkin ta ma .

 

Yace “my sarauniya dan Allah Kar kice min Aa nasan haka zaki ce “.

Hameeda tayi murmurshi kawai Bata ce komai ba.

Ya bude Mata gaba yayi Mata alama da hannun shi ta shiga su kuma su Fadila suka shiga baya .

Motan tayi tsit ba mai mgn sai can yace “my sister ya test”?

Fadila tace “alhmdllh”.

yace ” yayi sauki ko”?

Fadila tace “ummmmm ba wani sauki ka zuba mana questions dik naka ma yafi zafi “.

uncle Hamed yace “haba dai my sister “.

Hameeda dai tana jinsu Bata ce komai ba har suka qaraso gidan su dan gidan su zarah na bayan gidan su ne
Su Fadila suka bude suka fita suna mai godiya .

yace “ba komai”.

Hameeda zata fita yace yana son mgn da ita tace to tana gyara jakan ta na mkrt a jikin ta.

 

Yaya Hamed yace “Hameeda”.

Yanda ya Kira sunan sai da tsigan jikin ta ta tashi .

Hameeda tace ” Na’am “.

 

Yace “wai ya kike so inyi ne kullum na miki mgn akan in Toro iyayan na ayi mgn auran na a huce gun Hameeda wallahi ban San in rasa ki Dan in na rasaki kaman na rasa Raina ne kuma jiki na na bani za’a kwace min ke pls rabin Raina ki taimakawa masoyin ki”.

ya qarasa zancan muryan shi na rawa

 

Tinda ya fara mgn Hameeda take kallon shi har ya gama sannan tace ,

“my Hamed Ina sonka Amma bana son inyi aure ban gama secondary School ba kuma in Sha Allah ni matar kace ba mai rabamu har mutuwa sai dai ta dauke mu tare……. ”

Yace “to Allah yasa “.

Hameeda tace ” my Hamed bari in huce Kar momy ta jini shuru su Fadila har sun shiga gida “.

Yace ” to sai munyi waya ki kula min da kanki kinji”.

kai kawai ta daga mai.

yace “bye my dear I love you Hameeda”.

Tace “love you too my Hamed “.

Ta bude murfin motan ta fito .

Fitowan da tayi yayi dai dai da zuwan yay Yazeed wajan.

Yaya Yazeed na cikin mota ya hango Hameeda tana fitowa a mota kuma har ta tsaya ta gilas din mota tana daga mai hannun haba ai be San lkc da ya fito a motan ba.

yace”Ke”

 

Hameeda dake tsaye bayan ta gama dagawa uncle Hamed hannun taji ance “Ke” ai sai da hantar cikin ta ta kada .

Yac”e daga gidan uban wa kike sannan wani shegine ya sauke ki a mota “.

Dik wannan tambayan da yake Mata ta kasa amsa ko daya

Yace “ba mgn nake miki ba “?

Bakin ta na rawa tace “daga mkrt “.

“Mkrt shine ke daya ko Daman ke daya ce ke zuwa mkrt ?”

Hameeda tace ” A’a ai tare muka dawo “.

 

“Zaki ci ubanki ne in baki gayamin gaskiya ba , wuce muje gida.”

jikin ta na rawa suka fara tafiya ai da sauri sauri take tafiyan Dan ta wuce part din su suna shiga Gate din gidan yace ,

“part dina zaki huce ba naku ba “.

ai gaban Hameeda ya rasss

Yace “way ba mgn nake miki ba shigiya mai fuskan aljanu wato maza kike bi ko “.

“Maza cewan Hameeda”.

Yace “in ba maza ba mai bazaki tahu tare da Yan uwanki ba sai ke daya to yau Allah ya tona asirin ki Daman wannan rawan ka naki ai ba’a banza ba “.

 

Hameeda tace ” wallahi sai Allah ya min sakaiya kuma ka tambaya Fadila in ba tare muka dawo ba…….”

Yaya Yazeed yace ” zaki rufe min baki ko sai nayi kwallo da ke banza yar isaka “.

 

“Kuma yau sai kin gane kuran ki dan har big Daddy Alh Ahmad sai yaji tinda aure kike so ba gwara su miki ba kuma ki huce muje kafin jikin ki yayi tsami”.

Hameeda na hawaye 😭 ta huce part din Yaya Yazeed a zuciyar ta kuma tana tsine mai suna shiga ya rufe kwanfan harda sa key ya zauna a gujera ya daura kafa da kan daya yace,

” zo ki zauna a nan”.

ya nuna Mata kasa zaunawa tayi ,

sannan yace “uban mai ya shigar dake motan wani namiji da ba dan gidan nan ba”.

Hameeda tace ” wallahi Yaya Yazeed uncle din mune na mkrt kuma ba Ni daya bace harda Zarah da Fadila “.

 

“Wallahi in baki fada min gaskiya ba sai na Zane ki “.

Hameeda ta qara fashewa da kuka tace “wallahi kuwa gaskiya na fada ma kuma ka Kira Fadila ma……. ”

 

Marin da taji ne ya hana ta qarasawa.

” dan ubanki baza ki bada min gaskiya ba sai na balla ki…..

.Kiran wayan da akayi ne yasa shi tsayawa daga Marin da zai Kara Mata wayan ya ciro a aljihun wandon shi Yana dubawa yaga abbu Daddyn su Hameeda ya dauka cikin ladabi yace ,

“abbu barka da rana”

” eh abbu to ok Allah ya dawo da kai lfy shikenan to a huta lfy “.

 

 

Yace ” wallahi Hameeda in baki fada min maye tsakaninki da Wanda ya ajeki a mota ba yau sai na balla ki “.

 

Muryarta ta dashi sabida kuka tace,

” wallahi uncle dinmu ne kawai “.

Yaya Yazeed yace “Allah ya kaimu gobe zanje mkrt inji wani dalili malami zai dauki daliban a motan shi har ya kaita gida”.

Hameeda tace “Allah ya kaimu “.

Yace ” tashi ki ban guri kafin in basa miki Kai “.

 

Tashi tayi tana Allah ya saka Mata kuma wallahi gobe ko ya zo mkrt zata nuna Bata San shi ba .

 

Har takai bakin kofa yace “ke” juyowa tayi batare da ta amsa ba .

Yace ” zo ki gyara min d’aki sannan ki wanke min bedroom wallahi in d’akin Nan be gyaru yanda nake so ba hmmmmmmmm Allah kadai yasa dukan da zan miki”.

 

Hameeda tace “yay Yazeed banci abincin ba kuma Wallahi yenwa nake ji dan Allah ka bari zan gyara ma daka baya “.

 

“Dalla malama ki huce ki fara abinda na saki “.

Hucewa tayi tana yi tana kuka har ta gama tace mai ta gama. Hannun kawai ya daga Mata alaman ta tafi ta bashi guri .

 

 

Momy kon taji Hameeda shuru sai ta Kira Fadila tace ko Hameeda na part din sune dan Bata shugo ba kuma taga kowa ya dawo daga makaranta Fadila tace Bata Nan kuma tare suka shigo gida Bata fadawa Momy a motan uncle Hamed ta barta ba ok tace shikenan qila tana part din Haj jadda dan dama tace Mata ta je ta gaisheta

 

 

Fadila na fitowa daga part din su Hameeda Gate din gidan ta nufa ta bude ko zataga Hameeda Amma shuru sai ta dawo tana tinanin Ina to Hameeda taje………….

 

 

 

 

 

*Wallahi naso muku mai yawa Amma waya ta sai hawan chaji ya kamata sai Allah ya kaimu gobe I love you all my fan’s*
💋💋💋💋

 

 

 

*comment*
*vote*
*share*

 

 

Aunty baby✍🏼
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻

 

🇳🇬®
_*ABORIGINAL WRITER’S ASSOCIATION(YAN ASALI)*_📚✍🏼

[❄Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

_*DON’T 4GET TO VOTE, COMMENT & FOLLOW US ON WATTPAD @*_
*_AboriginalWrtersAsso._*

 

 

*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏼

 

 

*Dedicated to Ummu Irfaan, maman khady, and ummu Sadeeq.*😍

*wannan page naku ne kuyi yanda kuke so da shi naji dadin comment din ku na jiya Allah ya bar kauna*🥰🥰🥰🥰🥰

 

_Musu min mgn ta private Ina godiya Allah ya bar zumunci kuma Ina mai basu hkr da jiya ban samu Daman amsa su ba_.

 

*Bismillahir rahmanir rahim*

 

*page* 8⃣to9⃣

 

 

Fadila tace Ina to Hameeda taje………….

 

 

Hameeda kuwa tana fitowa daga part d’in Yaya Yazeed part d’in su ta wuce.

 

Sallama tayi Momy da ke fitowa daga bedroom d’in ta ta amsa sallama tana kallon Hameeda da jikin ta asanyaye .

Momy tace “Hameeda daga Ina tinda kuka dawo daga makaranta baki shugo ba?”.

 

Hameeda tace.

“Ba Yaya Yazeed bane ya sani wai in gyara mai D’aki Wallahi kuma yunwa nake ji “.

 

Momy tace ” To ga abincin can kan daning”.

” To”.

kawai hameeda tace ta wuce .

 

Maman Nusaiba ce zaune a parlour ta tana waya da qawarta Haj zuwaira .

tace.

“Wallahi haj nima haka nake son ayi dan yaron yanxu kudi na shigo mai sosai”.

Haj zuwaira tace.

” To ita Nusaiba na so”?.

“Yo Haj Ni Ina ruwa na da wata so mu dai kawai ta yarda ta aure shi mu zamu kudi.”

Haj Zuwaira tace .” Ai in ma Bata yarda ba gurin bokan nan zamu je shi zai sa ta yarda “.

maman Nusaiba tace “Allah Yar gari “?

Haj zuwaira tace ” Allah kuwa “.

maman Nusaiba ” Tace haka za’a yi zan Kira ki dik yanda mukayi da ita”.

Haj zuwaira tace ” To shikenan “.

 

Big Daddy ne da abbu suka dawo D’aki Haj jadda zuka huce .

 

Tana zaune a parlour kaman kullum tana basgar goron ta su Daddy suka shigo.

Haj jadda tace ” A’a kaga mutanan Abuja”.

abbu ne ya zauna gujeran da Haj jadda take yace,

” Haj kina lfy ya muka samai ku “.

Haj jadda tace ” lafiya lau Yusuf ya aikin”.

abbu yace . “Alhamdulillah”.

Haj jadda tace ” Madalla “.

Daddy yace ” Haj Ina huni “.

tace “Lafiya lau”….

 

Haj jadda ta gyara zama ta fara mgn.

” Daman akan yaron nan Yazeed ne “.

Abbu yace “Badai laifi yayi ba ko Haj “?

Haj jadda tace. “A lallai mai d’a baza ka tsaya in fada ma abinda ake ciki ba zaka fara wani ba laifi yayi ba to ku dai kuka sani aure nake son yayi yaro ya zaman mana gardi a gida to Wallahi ko mai aure”……

Ba Abbu ba har Daddy sai da yayi dry way ya zaman musu gardi a gida Kai Haj jadda da rigima take.

Abbu yace “Karki damu Haj in Sha Allah za’a mai”.

Haj jadda tace “Da dai yafin muku sauran kuma yaran Nan su Nusaiba su ma dik ku musu auran aca gida dik yara ba aure Kai Allah ya shirye ku”.

ta fada tana tashi a guri Ni bari inje in kwanta. Daddy da abbu suka Mata sallama Suma kowa ya huce part din shi .

 

Abbu ya shiga part din maman Nusaiba tana zaune ko alaman tashi batayi ba sai da ya shigo parlour sannan tace ,

“Alhaji sannu da hanya”.

yauwa kawai yace yana zama kan kujeran parlour.

 

Abbu yace ” Ina yaran Nan ne banji su ba “?

Maman Nusaiba tace Duk suna D’aki su”.

yace “Kira min su”.

tashi tayi tana cewa ai ka dawo kenan kuma mutum bashi da hutu mtswwww tayi tsaki .

In baku manta ba Daman nace muku yaran Hajara hudu ne Shamsiya da Nafisat sunyi aure sai kuma Areef da Nusaiba .

 

D’akin Nusaiba ta nufa ta fara kwankwasawa Nusaiba na waya da wani class mate din ta Imran taji ana buga Mata kofa tace waye?

Maman Nusaiba tace “Uwarki ce Nusaiba”.

tace “Kai mama menene kuma”?

” Ki bude mana wai”.

cewar maman Nusaiba tashi tayi tana wai ko mai tazo yi min D’aki oho Mata budu D’akin tayi maman Nusaiba tace ,

“Abbun ku ke Kiran ki kinsan shi da naci in baki zo yanxu ba ya dinga Kiran ki kenan.”

Nusaiba tace “Kai shi abbun na daga dawowar shi har zai fara ta kurawa mutane”.

(gaskiya iyaye Mata muna da sakaci wajan nuna ma yaran mu matsayin uba a gare su yin zancen uba Mara kyau a gaban yaro nasa yara su Raina mahaifin su Dan Allah mu kiyaye )

 

D’akin Areef ta nufa Amma be dawo ba

Nusaiba na zuwa ba ladabi balle biyeya tace “Abba gani “.

Abbu yace “Yaushe ne zaku fara zana jarabawar ku Nusaiba”?

tace “Ni dai ban sani ba amma dazu mukayi test. ”

Abbu yace ” Allah ya taimaka “.

tace ameen tana tashi a gurin .

Abbu ya kalla agogon hannun shi yace Hajara Ni na tafi in kwanta ko kala Bata ce mai ba ya qara cewa way ba mgn nake miki bane ?

Hajara tace “To mai zance “?

Alh yace “Wai Hajara yaushe zakiyi hankali ke kwata kwata baki girma to Allah ya shirye ki”.

Yana gama fadan haka ya huce abinshi Daman a D’akin Momy ya ke .

 

10:30 Yaya Yazeed ne ya fito daga motan shi daga gani daga gun aiki yake part din memen shi ya tafi Yana shiga ya tarai da Daddy ma Yana Nan suna zaune a kasan dadduma Daddy na cin abincin sallama yayi gabaki daya suka dago suna kallon tilon d’an nasu Wanda suke so da kauna cikin ladabi ya karason in da Daddy ke zaune shima ya zauna kusa da kafan shi yace,

” My daddy Ina huni ya kasuwan da fatan kana cikin kushin lfy”?

Daddy yayi murmurshin su na manya yace “My son lfy lau alhmdllh ya naka gun aikin”.

yace.

“Alhamdulillah Daddy “.

Meme tace” Wato Kun matan da Niko lallai my son ta Daddyn ka kawai kake “.

Yaya Yazeed yace “Haba memena ya zan manta da ke ya matso in da meme take ya Dan kwantar da kan shi jikin ta ya memena na gaji da yawa Wallahi”.

Daddy yace” My son wai yaushe zakai aure ne haba my son.”…

Yaya Yazeed yace “Daddy kwata kwata shekarata nawa kuke min zancan aure 28 fa ne haba my Daddy”.

 

Daddy yace.
“Hmmmmmm my son kenan zo muci abincin nan nasan baka ci komai ba”.

Yaya Yazeed yace” To”.

tare suka gama ci Yaya Yazeed ya musu sai da safe sannan ya tafi Yana tinanin mgn Daddyn shi wai aure haba sai kace wani babban mutum………

Ko da abbu tafi part din su Momy ta gama hada mai komai na abincin Yana shiga ta tashi ta tare shi cikin murna da farin cikin shima haka.

 

Momy tace “Sannu da hanya abbun Hameeda da fatan ka dawo lfy”.

abbu yace ” Lafiya lau alhmdllh”.

tace ” To haka ake so ga abincin ka can Yana jiran ka “.

abbu yace. ” Allah ya miki albarka Zainab”.

Momy tace ameen

Hameeda tana D’akin ta taji kaman muryan abbun ai da sauri ta fito tana murna abbu da da hanya yace,

” yauwa my daughter kina lfy”?

tace ” Lafiya lau abbu”.

yace ” To ya makarantar na tambaya Nusaiba tace kun fara test ko”?

Hameeda tace ” Eh abbu “.

yace ” To Allah ya bada sa’a”.

tace “Ameen”.

Saudat ma ta fito da gudun ta ta hau kan cinyar shi tana mai shagwaban da ta saba Hameeda ke Saudat baki girma Wallahi jiki fa a kan cinya sai kace wata qaraman yariya Abbu yace ai auta ce ki barmin auta ta ta huta Momy tace Saudat sauka Abbun ki yaci abincin ko Saudat tace to Momy Hameeda tace Abbu Momy good night Abbu yace night my darling daughter Momy ma tace sai da safe…

Washe gari

love you all my fan’s 💋 💋💋 💋💋 💋💋 💋💋 💋

 

 

 

*comment*
*vote*
*share*

 

 

 

Aunty baby✍🏼

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻

 

🇳🇬®
_*ABORIGINAL WRITER’S ASSOCIATION (YAN ASALI)*_📚✍🏻

[❄Dance above the surface of the world, let your thought lift you into creativity that is not hampered by opinion.]

_*DON’T 4GET TO VOTE, COMMENT & ALSO FOLLOW US ON WATTPAD*_
_*@AboriginalWrtersAsso.*_

 

 

 

 

*Story & Written*
*by*
*AUNTY BABY*✍🏻

_posting day:_
_Monday & Tuesday only👌_

 

Bismillahir rahmanir rahim

 

 

*page* 1⃣0⃣ to 1⃣1⃣

 

 

Washe gari.

Yay Yazeed ne yayi Shirin shi na zuwa asbitin yayi kyau sosai.

wayan shi ne yayi ringing dubawa yayi ya ga sunan abbu, yace to abbu kuma da safen nan.

dauka yayi da sallama yace,

” Abbu Ina kwana.”

Abbu yace ” lfy lau my son ka tashi lfy”.

yay Yazeed yace “lfy Abbu, ”

Abbu yace “kafin ka fita asbiti ina son ganin ka.”

yay Yazeed yace ” to Abbu insha Allah “.

yana gama Shirin shi ya dau mukullin motan shi ya fito….

Part din su Hameeda ya shiga dan ansa kiran Abbu

yana shiga ya Sami Saudat a parlour.

yace “Saudat”

Saudat dake zaune tana home work tace,

” Na’am yay Yazeed Good morning”.

yace “Morning ya kk Ina momy.. ?”

Saudat tace ” tana kitchen tana hada breakfast.”

yace ” ok Abbu be tashi ba?

Saudat tace *eh be tashi ba.”

yace ok… Gujera ya Samu ya zauna Yana duba waya…

Hameeda tace “Momy bari in fara shirya breakfast din tinda an gama hadawa…”

Momy tace ” to shikenan daga Nan ki huce ki shirya Kar kiyi Letty.”

Tace “to Momy.. ”

dining ta nufa ta hada komai sannan ta fito parlour tana kiran Saudat.

Saudat ! Saudat !! way mutum yayi ta Kiran ki kina ji.

Saudat tace ” haba Aunty Hameeda home work fa nakeyi.. ”

tace “to dan kina home work shine baza ki amsa ba , to kije ki shirya dan ba jiranki zanyi ba.”

Saudat tace ” to Aunty.. ”

yay Yazeed na zaune yana jin su ko kallo bata isheshi ba.

Abbu ya fito daga bedroom din shi yace,

” A’a Hameeda baku shirya makaranta ba?”

tace “Good morning Abbu , yanzu zamu shirya na taya Momy hada breakfast ne.”

Abbu yace “to shikenan”.

 

Yay Yazeed yace “Ina kwana Abbu. ”

Abbu dake zama a doguwar kujera yace,

” lfy lau my son har anyi Shirin aikin? ”

Yay Yazeed yace “eh Abbu.. ”

 

Momy dake fitowa a kitchen tace,

” A’a Yazeed Kaine ?”

Yay Yazeed yace “nine my Momy kin tashi lfy”.

 

Momy ta fadada murmushin ta tace,

” to ku taso muyi break dan nasan baka ci komai ba “.

 

Yace “to my Momy kaman kinsan kon banyi break ba…”

Hameeda dake tsaye haushi ya kamata wai da wannan dan rainin wayo za suyi break mtswww .

Momy tace “ke kuma lfy ki kike ma mutane tsaki…. ”

Hameeda tace “wani Abu na tina Wallahi.. ”

Momy tace “zo kiyi serving din mu mana ,”

Hameeda tace to.

Ta fara serving din su tana zuwa na yay Yazeed tace,

” mai zan zuba maka”.

a daqile tayi mgn shima sai yayi kaman bai ji ta ba .

ta qara cewa mai zan hadama. Sannan yace kisa min tea kawai…

Abbu yace ” haba my son Ina tea zai isheka.”

Yay Yazeed yace “Abbu bansan abu mai nauyi ne da safe. ”

Abbu yace ” ok Amma kana dinga cin abincin.”

To kawai yay Yazeed yace…..

Suna gamawa su Hameeda suka tashi dan shiryawa makaranta Momy ma ta mike dan kwashe abun da suka bata .

 

Abbu ya gyara zama Yana fuskantar yay Yazeed sannan ya fara mgn kaman haka.

“Yazeed” yaya Yazeed Na’am Abbu

Abbu yace “Ina so ka fito da matar aure nan da 3week sbd Haj jadda ta fara mgn dan haka Nan da sati uku Ina so ka fitar da Mata Suma sauran Yan uwanka Mata zan musu mgn Amma sai Allah yasa sun gama jarabawar su Dan daga Nusaiba har Fadila da Hameeda aure dasu zanyi… ”

 

Ji yayi abin duniya yayi mai yawa har yaushe ya Samu matar aure nan da sati uku shi da ko budurwa bashi da ita kai wannan tsohuwa da rigima take ko Ina ruwanta da shi kwatakwata shekaran shi nawa da zata damu yayi aure…….

Yana cikin wannan tinanin ne yaji Abbu yana cewa,

” zaka iya tafiya Amma ka tabbatar sati uku na baka in ba haka ba dik Wanda muka zaba ma to Kai kaja. ”

Yace ” to shikenan Abbu Ni na tafi “.

Abbu yace Allah ya bada sa’a..

Yana fitowa daga part din su Hameeda part dinsu ya huce tinani fal. ranshi ya rasa yanda zaiyi gashi wai in be fito da Mata ba za’a bashi dik Wanda ake so Kai shi yaga ta kanshi…

 

Ya shiga da sallama Daddy Yana kan 3str Yana kallon labaran safe Meme kuma na hada mai shaye suka amsa sallaman suna kallon shi fuskan shi ba walwalla.

Daddy yace “my son ya naganka haka ko baka da lfy ne? ”

yaya Yazeed yace ” A’a Daddy lfy na kalau Ina kwana. ”

Daddy ya amsa ya gaisher da meme ma.

 

tace “ga abincin shi can kan dining.”

 

yay Yazeed yace ” shi ya koshi Dan Sai da ya fara zuwa part din Abbu tukun na”.

Meme tace ” to badamuwa.”

Dan ta San Momy nasan yay Yazeed sosai tin yana yaron shi…

 

Yace “Ni zan huce asbiti dan Ina da patient da yawa.”

Duk suka mai Allah ya tsare ya kare..

Ya tashi ya tafi.

 

 

 

 

 

 

*comment*
*vote*
*share*

 

 

*Aunty baby ✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce,daga ƙinta sai barinta,burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

 

*Story & Written*
*by*
*AUNTY BABY*✍🏻

 

*Dedicated to my besty Maryam Ahmad😍😍😍 qawar amana*

 

 

*page* 1⃣2⃣to1⃣3⃣

 

*Bismillahir rahmair rahim*

 

 

Ya tashi ya tafi

 

Yana zuwa asbiti, office ɗin shi ya wuce dan yau kanshi a kulle ya ke, Ina zai samo matar aure nan da sati uku?

Wayan shi ne yayi ringing banza yayi da ita sai da aka yi 3miss call sannan ya ɗauka ko duba wake Kira beyi ba yace.

“hello,”

Safwan yace , “haba abokina kwana biyu shuru tindaka biki fa Ina ka shige ne.”

 

Yaya Yazeed yace , “lfy lau na barka ne ka gama cin amarci sai yau ma zaka tina da ni”.

 

Safwan yace, ” haba abokina Wallahi ba haka bane, Wai ya naji muryanka kaman kana cikin damuwa lfy dai ko ?”.

Yaya Yazeed ya nisa sannan yace,

” Wallahi Safwan Ina cikin tashin hankali Abbu yace in fito da matar aure nan da sati uku sanin kai ka ne ko budurwa Banda ita, Wallahi Kaina ya kulle bansan yanda zanyi ba.”

Safwan yace , “tab abokina matar aure nan da sati uku lallai kana cikin tsaka mai wuya. Amma ga shawara.”

Yaya Yazeed yace, ” Ina jinka “.

 

Safwan yace , ” Ina Ameera class mate dinmu daman tana sanka kawai kaje ku sa santa dan Wallahi Ameera ba karamin so take maka ba “.

“Lallai Safwan baka da hankali wannan yariyar zan aura tab to ai gwara in jira su aura min duk wacce tai musu da dai in aura Ameera.”

 

Safwan yace, ” to ga Yasmeen wace kullum sai tamin mgn ka tana sanka sosai Wallahi har biki na fa ta zo dan ku hadu Amma bata ganka ba, ”

Yaya Yazeed yace, ” to ai gwara in aura Ameera da Yasmeen, kai baka da anfani Wallahi Ni fa yariya mai hankali nake so bawai irin Yan matan da kake mgn ba.”

 

Safwan yace, ” to shikenan ka zauna kawai su Abbu su zaɓa ma Mata dan Ni na gaji duk wacce na faɗama kace Bata maka ba sai ka jira a baka ƴar qauye dan naga hakan kake so.” Yana gama fadan haka ya kashe wayan shi

 

Yaya Yazeed yace, ” oho ma ni ina son mace mai Adini kana faɗa min wa’inda sallah ma bata damai su ba ”

ya daura kanshi a gujeran office ɗin ya cigaba da tinanin shi…

Maman Nusaiba ce zaune a kan bed ɗin ta tana tinanin yanda za’a yi ta jawo hankalin Nusaiba ta so yay Yazeed dan Wallahi baza ta ga samu taga rashi ba ai dole ma Nusaiba ta yarda ta aura Yazeed tana cikin wannan tinanin ne Abbu ya shigo.

“Wai tinanin mai kike ne ina ta sallama hankalin ki na wani waje?”.

cewan Abbu kenan yana zama bakin gadon da take .

Maman Nusaiba tace,

” Ah, Alh yaushe ka shigo banji sallaman ka ba? “.

Abbu yace , “Ina zaki ji sallama na kuwa kina can kina tinani “.

Maman Nusaiba tace,

” hmmmm Alh daman Wallahi Ina son mgn da Kai… ”

Abbu yace Ina jinki

Maman Nusaiba tace,

” hmmmm ban San dai yanda zaka duba mgn ba Amma dai nasan kowa zaiji dadin wannan hadin daman Nusaiba ce da Yazeed naga ya dace a hada su aure .”

tana fada tana satar kallon shi taga yanda fuskan shi ko ya canja ko kuma Amma taga be canja ba sai kawai ta cigaba da mgn ,

“Alh ya naji kayi shuru…….”

 

 

_Allah ba dan halin ku ba yasa nake muka typing shiyasa nima yanxu ba kullum zaku dinga jina ba_

 

 

 

 

*comment*
*vote*
*share*

 

 

 

Aunty Baby✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce,daga ƙinta sai ɓata,burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

 

 

*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏻

 

 

*Dedicated to my family ❤️❤️❤️ and my brother hamoudi🥰*

 

*page* 1⃣4⃣to1⃣5⃣

 

*Bismillahir rahmair rahim*

 

 

Tace Alh ya naji kayi shuru.

Abbu yace, ‘” Ina jinki. Lallai Hajara baki da tinani yanxu Yazeed ne zaki ce zai aura Nusaiba ko to ban yarda ba ke daman kin iya San kan ki”,

Yana cikin mgn ne yaji wayan shi na ƙara ɗauka yayi yace “hello.”

Abba ne baban su Fadila yace “Yaya Haj Jadda ce take neman mu ga big Daddy shima ya zo shine nace ai baka fita ba ko.?”

Abbu yace “eh ban fita ba gani Nan zuwa.”

Abbu ya kalli Maman Nusaiba wacce ta hada rai ta cika fam kaman zata fashe yace,

” Wallahi daga yau na ƙara Jin mgn Nan a bakin ki sai kin sani tinda ke baki da tinani … ”

Yana gama fadar haka yayi huce war shi.

Maman Nusaiba tace” Wallahi ko ta boka 👹 sai Yazeed ya aura Nusaiba dayake ba Sona yake ba shiyasa baya san ƙaruwar mu to aure ne kaman anyi shi”,

tana ta fadan ta dai ita ɗaya…

Abbu kon Yana zuwa part ɗin Haj Jadda ya samai su duk a zaune ya gaisher da Haj Jadda sannan ya zauna shima yace “Abubakar Ina batan dai lfy. ?”

 

Abba yace , “lfy lau daman kan mgn yaran nan ne shine big Daddy ya yanke hukunci .”

Abbu yace , “to Allah yasa alkairi ina ji “.

Big Daddy yace, ” na yanke hukunci Areef zai aure Fadila sannan kuma Yazeed zai aure Hameeda sai Nusaiba kuma yaron abokina Nabil,Ba Wanda ya isa ya fasa wannan abu da nasa “.

Haj Jadda tace, ” A lallai ka nuna min Kai ka haifa yaran nan shiyasa bakayi shawara Dani ba to alkur’an ban yarda ba sai dai in Nusaiba ta auri Yazeed ka haɗa aure da irin tsiya to Wallahi ban yarda ba ko kuma a fasa auran gaba ɗaya.. ”

 

Big Daddy yace, ” haba Haj mai yasa kike haka ne yaran nan gaba daya jikokin ki ne yanxu zaki hada faɗa tsakanin su kina nuna kinfi San wannan da wannan. ”

Abbu ya katse shi da ai Yazeed ma Yana da matar da yake so dan ɗazo da safe nayi mai mgn ya nemo matar da yake so Nan da sati uku to ai sai a bari ya kawo tukun na ko Dan ba a mai shigan hanci ba .

Abba yace , “Aa Ni Ina ganin abin da big Daddy ya fada shine dai dai ai basu suka haife muba mu muka haife su dan haka dole su bi abin da muke so….”

 

Haj Jadda tace, ” oho muku dai tinda Kun nuna min ba Ni na haifa yaran ku ba ai shikenan Allah ya sanya alkairi/”

Big Daddy yayi murmurshin su na manya yace , “Haj Jadda kenan Ameen ai daman haka muke San kice yanxu sai a fara shirye shiryan biki ko dan auran yara shida ba wasa ba. ”

Abbu yace , “saurin mai kake ai sai a bari my son ya zo dan shine babba aji ta bakin shi ko “.

Abba yace, ” ai kawai a hada family meeting tinda jibi Saturday “.

Big Daddy yace, ” eh haka za’a yi sai a faɗawa Shamsiya da Nafisat dan su tambaya mazajan su. ”

Haj Jadda tace , “wannan kuma ai iyayan su Mata zaka gawa. ”

Abbu yace , “to shikenan Allah ya kaimu Saturday ɗin Ina San zuwa Abuja yau amma gobe zan dawo insh Allah “.

Big Daddy yace, ” Allah ya kiyaye hanya. ”

Abba ma yace Allah ya kaishi lfy…

Haj Jadda tace “Kai Amma Yusuf baka jin tafiya Abuja ka maida shi kaman Zaria da kaduna”.

Abbu yace, ” ai dole ne Haj ku dai kuyi tamana addu’a “.

Tace “to Allah ya Kai ka lfy ya kuma dawo mana dakai lfy “.

Abbu yace ameen

 

Hameeda ce zaune a class yau kwatakwata Bata jin daɗi tama kasa fita break bare su hadu da uncle Hameed ɗin nata. Sallaman shi kawai taji sanye yake da farar shedda am Mata dinkin hannu yayi kyau sosai kallon shi kawai take ta kasa ɗauke ido a kanshi.

Yace “kallon fa
Sai kace baki taba gani na ba” Yana faɗa yana zama saman tabir din da take.

Tace “Wallahi kamin kyau ne sosai Ni baka taba min kyau bama kaman na yau Wallahi dik haushi ya kamani yanxu haka ka shiga class Mata na ta kalle min kai? ”

Yace “haba my only kin san dai ba wacce takai matsayin da zan sota kin mamaye ko Ina Allah son da nake miki daga ummi sai papa pls ki yarda gobe su papa su je gidan ku Wallahi kullum jikina na bani in banyi sauri ba to gaf nake da rasa ki pls kinji my Hameeda”.

 

Hameeda tace “hmmmm my Hamed kenan ai in gayama Hameeda ta kace ba Wanda ya isa ya mallake Ni sai Kai inshallah Ni matar kace kuma na yarda su papa suje gidan mu”.

Hamed yace “Hameeda kin yarda su papa su je gidan ku..?”

” Hameeda dan Allah da gaske kike kai Allah na gode ma hameeda ke tawa ce inshallah Allah na gode ma da ka bani Mata kaman ki Hameeda mai kike so in miki Hameeda sbd wannan kyautar da kika min .

Hameeda kawai tsayawa tayi tana kallon shi wannan murna haka sai kace an daura auran gabaki daya.

 

 

Tofa ana wata ga wata 🤔

 

 

 

*comment*
*vote*
*share*

 

 

 

 

Aunty Baby✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*

 

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce,daga ƙinta sai barinta,burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

 

*Story & Written*
*by*
*AUNTY BABY*✍🏻

 

*Dedicated to my talala family ❤️ Allah ya qara hada kanmu yan uwa rabin jiki*😘😘😘

 

*Bismillahir rahmair rahim*

 

*page* 1⃣6⃣to1⃣7⃣

 

Hameeda tace “Haba my Hamed sai kace an daura auran gaba daya?”

Yace. “Hmmmmmm Hameeda kenan baki san irin son da nake miki ba ko,Wallahi Hameeda dik ranar da na rasa ki zan rasa Raina, Ina mai rokon Allah yasa ki zama mallakina matata uwar yarana..”

Tace “Ameen my Hamed ai ka kwantar da hankalin ka Ni ta kace har abada”.

Yayi murmurshi yace ” To Ni bari in koma office Kinga an kusa komawa break”.

Tace “To my Hamed bye sai an tashi kuma”.

Yace “Shikenan ki kula min da kanki kinje “.

Tace “To” 😘😘😘

Yace “Kai Hameeda zaki sa in kasa aiki fa Wallahi wannan 😘 haka “.

Tace “Ba wani nan in ban maka ba waye zai ma “.

Yace “Babu fa my only”.

Ko da aka tashi sai da suka Sha soyayyar su sannan Fadila ta zo suka tafi gida.

A gida kuwa su big Daddy ba Wanda suka gayawa a Mata sunce sai ranar Saturday tukun na kowa yaji shiyasa ko da Hameeda ta dawo gida hankalin ta kwance sai ma murna da takiya iyayan uncle hameed zasu zo Amma Bata gayawa kowa ba dan nunawa zatayi ba ita tace ya turo ba sai dai kawai in an tambayeta tana son shi tace eh.

(Ni kon nace Hameeda ai an bar shiri tin rana bakin san an bawa yay Yazeed ke ba)😂

 

Uncle Hamed kuwa cikin farin cikin ya shiga gida ko gate man sai da yasa Yana cikin farin cikin a parlour ya samu Umma na zaune Hanifa ta daura kanta a kafan Umman suna fira.

Sallama yayi Umma da Hanifa suka amsa.

yace “Ke Hanifa Wallahi baki girma ni daga min uwa karki karya min ita”.

Ya fad’a yana murmurshi.

Hanifa ” Tace haba yay Hamed har wani girma nayi ,wai yau ya naganka sai farin cikin kake Allah yasa alkairi.”

Umma tace ” Wallahi kuwa abun da zance kenan keka riga ni”.

Yace “Hmmmmmm Ummana abunda kike so inshallah an kusa dan Hameeda tace in tura gidan su”.

Yana fada yana wani shafa Kai alaman ya ji kunya. 😏

Umma tace “Alhamdulillah inshallah yau zan gayawa papa ku sai su tsada ranan zuwa ko?”.

Uncle Hamed yace “Yarda kika ce umma “.

Ita kuwa Hanifa tinda Hamed ya fara mgn gabanta ke faduwa dan ba qaramin so take mai ba wasu hawaye ne suka fara zubo Mata dan Wallahi tana bala’in son shi.

“Hanifa tashi ki kawo ma yayanki abincin”.

cewar Umma dake duban Hanifa
Saurin tashi tayi dan Kar su gane yanayin da take ciki kitchen ta shiga tana hada mai abincin tana aikin kuka wai Allah na ya zanyi da rayuwata ya Allah ka cire min son Hamed a zuciyata Allah ka zaba min Mafi alkari sai da ta wanke fuskarta sannan ta hada mai komai ta huce part din shi dan yace can zata Kai mai .

*Wanene Hamed*

Hamed d’a ne gun Alh Mustapha Wanda yake cewa papa sai Mahaifiyar sa Murjanatu Umma ya taso cikin gata da so irin na iyaye shi kade Allah ya basu shiyasa soke son shi kaman rainsu.
Hanifa yar qanwar Umma ce tin tana Yarinya Umma ta dauke ta har ta girma Allah yasa Mata soyayyar Hamed Amma .

Cigaban labari.

Yau ta kama Saturday daman big Daddy ya gayawa kowa yau akwai meeting karfe 11:00 shi yasa kowa na gida har su Shamsiya sun zo

Kwance take kan bed din ta tana waya da Hamed, tace. ” My Hamed bari in je in shirya yau muna da family meeting kuma har damu aka ce ban San maiyasa ba “.

Hamed yace ” To shikenan my dear anjima su papa za su zo “.

Tace ‘ To Allah ya kawo su lfy”.

Sai da suka dan taba hira sannan suka sallama

10:00 dai dai kowa ya halarci babban parlour gidan Haj jadda na zaune kan babban kujeran parlour meme da momy suna kujera daya maman Nusaiba tana zaune kan 1st haka ma ummi maman Fadila su big Daddy ma suna tasu da ban.

Yaran kuwa dik suna kasan kafet kama daga kan Yaya Yazeed, yay Areef, shamsiya, da yaran ta biyu suna ta wasan su Nafisat kuwa yaronta daya Bata ma yaye shi ba

Hameeda da Fadila suna gu daya Nusaiba tana kusa da uwarta haka dai dik kowa yayi shuru yana jiran a fara mgn .

big Daddy ne ya fara mgn yace ayi Addu’a kowa yayi sannan ya fara mgn kaman haka ,

“Ba komai yasa na hada wannan meeting ba sai dan ku Yazeed, Areef , da kuma su Fadila , da Hameeda, da Nusaiba. Sannan Ina so dik abinda na fada ya zama zaima kowa dad’i a Nan gun nasan zakuyi alfahari da wannan hadin da nayi ko ba yau ba.”

Babu abunda kirjin yay Yazeed ke yi sai bugawa.

Big Daddy ya cigaba da cewa “Nasan ku yara ne masu biyaya Allah ya muku albarka ”

Dik aka amsa da Ameen dan kowa burin shi big Daddy ya fada abin da yake san fada .

Yazeed big Daddy yace Yana duban shi.
Yaya Yazeed ya amsa da Na’am Daddy ,

Big Daddy yace.

Inshallah Kaine mijin Hameeda “.

Ai ba yay Yazeed ba kowa a parlour sai da ya kirjin shi ya buga Hameeda kowa sai da numfashin ta ya dauke na hucen gadi .

Big Daddy yace ” Kai kuma Areef Fadila, sai kuma Nusaiba Nabil, Allah yasa alkairi a cikin wannan abu da na hada sannan kuma ko bayan Raina Kar Wanda ya sauya wannan hadi. ”

Big Daddy yace “Haj jadda baki ce komai ba. ”

Haj jadda tace “To Ni mai zance Allah dai ya bada zaman lfy yasa alkairi”.

Kowa yace ameen .

Ita kam Hameeda ma Bata san mai ake cewa ba dan gaba daya Bata fahimtar komai .

Maman Nusaiba ce ta fara mgn “Haba dan Allah dan ba’a sona shi yasa Yar tawa ma ba’a so ya zaayi a hada ta da wani wai Nabil to Wallahi ban yarda ba sai da…..”

Bata qara saba Abbu yace ” Hajara mai kike Shirin yi yayan nawa yace Abu ke kece ba haka ba to Wallahi baki isa ba kika qara mgn a bakin auran ki dan Wallahi bazan dauka rainin ki ba yanxu “.

Haj jadda tace ” Haba Hajara ai hakuri zakiyi tinda aikin gama ya gama ki taya su da Addu’a kawai “.

Abbu yace “Kowa ya tashi ya basu guri dan Abbu yana da fushi sosai yafi su big Daddy fushi shiyasa kowa ya tashi ya tafi”.

Hameeda kuwa sai Fadila ce ta taimaka Mata ta tashi dan kwatakwata bata Jin abinda ake cewa

Yay Areef sai washe baki yake dan shi Yana son zabin iyayan nashi fatan shi Allah yasa ita Fadilan ta so shi…..😁

 

 

*To Ina team din Yaya Yazeed sai kuYace o muyi tawaye😎 dan gaskiya baza mu yarda ba*😂

 

 

 

 

 

*comment*
*vote*
*Share*

 

 

Aunty Baby✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻

 

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce,daga ƙinta sai barinta,burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

 

 

*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏻

 

 

_*Dedicated to my only Mr Aliyu rabin Raina🥰🥰🥰😍 Allah ya barmu tare soldier na*_❤ 👨🏼‍✈

 

 

_Wato baka gane masoyan ka sai wani Abu ya samai ka gaskiya Ina godiya my fan’s Allah ya bar kauna ina tare da ku Yan babu shi a zuciyata fan’s_💃💃💃💃💃💃💃💃💃🥰🥰🥰

 

*Bismillahir rahmanir rahim*

 

*page* 1⃣8⃣to1⃣9⃣

 

Kuka Hameeda take sosai Fadila har ta gaji da lallashi ta qara fasa ihun da har momy sai da ta shigo d’akin.

” wayyo Ni Hameeda na shiga uku ya zanyi da Raina Wallahi bana son shi, *BABU SHI A ZUCIYATA* .

Momy tace ” Hameeda bazaki ma kanki fada ba kiyi shuru ke daya aka bawa Wanda bake so yanxu wa kika ji yayi wani mgn sai ke ko Hameeda shikenan kija min zagi “.

Tace “Momy Wallahi in kuka aura min yay Yazeed mutuwa zanyi Wallahi Momy baya Sona nima bana son shi kuma nayiwa Hamed alkawari pls Momy ke uwa ce ta gari baza ki so in shiga wani hali ba dan Allah Momy ki taimaka min”. tana mgn tana kuka

Momy ta tausawa Y’ar tata Amma baza iya Hana wannan abu ba tunda big Daddy ne yasa.

Zaunawa tayi a bakin gadon da Hameeda take ta maso da kanta kan cinyarta tace ,

” Hameeda kiyi hakuri da kaddaran da ta samai ki nasan abin son Yazeed Amma kiyiwa iyayan ki biyaya inshallah zaki ci rabar abun gaba.”

Hameeda ta qara fashewa da kuka tace “Momy ya zanyi da Raina Momy na shiga uku Momy yay Yazeed baya Sona Wallahi kashe Ni zaiyi “.

Momy tace “A’a Hameeda Yazeed bazai kashe kiba ke Y’ar uwarsa ce Ni dai ki cire damuwa a ranki kinji Hameeda”.

Kai kawai Hameeda ta daga .
Momy tace “bari inje D’akin na.” Fadila ce kawai ta amsa da cewa to Momy .

Fadila ” haba Hameeda mai yasa haka dik kin dagawa Momy hankali kiyi hakuri mana ai ba ke daya aka zabawa miji ba harda Ni Amma mai kika ga nayi pls Hameeda dan Allah ki daina wannan kukan”.

Tace” Fadila qila ke kina son yay Areef ne shiyasa baki damu ba Amma Ni Wallahi bana son yay Yazeed *BABU SHI A ZUCIYATA* kuma Wallahi ya yarda aka daura auran na Wallahi ya shiga uku da Ni dan bazan taba zaman aure da wannan mutumin ba .”

Dry sosai Fadila keyi tace “A lallai Hameeda yay Yazeed din to Allah ya kaimu muka ana Shan love❤”

Duka Hameeda ta d’aka mata tace ” dawo za’a Sha love din sai dai my Hamed kuwa.”

haka dai suke ta firan su rabi dik fada ne dan Fadila akwai ta da tsokana.

 

Shi kuwa yay Yazeed Yana D’aki ya rufe kanshi yama rasa mai ke mai dadi a duniya shi dai da a hada shi da Hameeda gwara an hada shi da mai aikin gidan su dan Wallahi baya son ko ganin tane balle kuma wai aure .Kai da sake gaskiya hakadai yake ta mgn shi daya .

Maman Nusaiba sai faman safa da marwa take dan Wallahi baza ta taba barin ayi auran Nan ba yanda yarta Bata aure shi ba haka ita ma Hameeda baza ta aure shi ba dan an Raina Mata wayo shine za’a hada yarta da wani Nabil wayar tace tayi Kara tana dauka tace, “Haj zuwaira dan Allah kizo gidana yanxu akwai mgn da zamuyi “.

Haj zuwaira tace “lfy ko Haj “?
Maman Nusaiba tace “lfy ba lfy ba dan yau wan can yayan nasu ya yanke auran yaran nan shine dan rashin mutunci ya ba Nusaiba Nabil yaron abokin shi.”

Haj zuwaira tace ” iyeeee lallai ne mu da muke son ta aura Yazeed.”
Maman Nusaiba tace ‘to ai ba wannan ba Hameeda yasa “.

Haj zuwaira tace ” tab Wallahi sunyi karya dan Wallahi Yazeed mijin Nusaiba ne kota boka kota malam sai Nusaiba ta aure shi .”

Naman Nusaiba tace ” Ni dai kizo sai musan abinyi “.

Haj zuwaira tace to gani nan.

Hameeda sosai ta shiga cikin damuwa bata ci Bata Sha wuni daya kawai ta ramai sai kace mai ciwo Bata da aiki sai kuka da anyi mgn tace babu shi a zuciyatar har Momy ta fara fusata da ita ta daina ko kallon ta dan haushi take bata sai kace an hada ta da mutuwar ta .

ko Hamed ya Kira ta ma Bata dauka Dan Bata San mai zata ce mai ba .

Tana kwance a kan gadon ta tana aikin nata kuka. Zarah ta shigo
Zarah tace ” Hameeda mai yasa mai ke baki da lfy ne”.
Hameeda tace “A’a zarah mai kika gani “?

Zarah tace “Hameeda dik kin rame”.

Tace “lfy na kalau kawai dai “.

Zarah tace “kawai mai ?”

Hameeda tace “Zarah auran dole za’a min dan Wallahi bana son shi *babu shi a zuciyata*”.

Zarah ta maimaita auran dole Hameeda ki fada min kin sani a duhu

Hameeda ta fashe da kuka tace “yay Yazeed wai za’a aura min “.

Zarah tace ” yay Yazeed Hameeda yay Yazeed fa lallai dole kiyi kuka, Amma kiyi hakuri kiyi biyaya.”

Hameeda ta qara goge hawaye tace ” shikenan ”
Zarah tace ” tashi ki rakani zan tafi daman na Kira kine naji wayan a kashe shine nace bari in zo ko lfy “.

Tashi tayi tana gyara Dan kwalin tace mu tafi .

Fitowa sukayi zarah tace “mu fara shiga part din su Fadila”.

Hameeda tace ” to”.

a parlour suka hadu da Fadilan ma zata fito .

Hameeda tace “shikenan ma kin hutashe mu daman D’aki ki zamu “.

Fadila tace “nima kam gunki Zane kinsan yau zamuje amsa dinkin na”.

Hameeda ta dafa Kai tace Kinga na manta Wallahi .

Fadila tace “ai nasan haka zaki ce “.

Zarah tace “Ni ku rakani Kun tsaya surutun ku”.

Fadila tace “hmmmm yariya mun kosa zama manya ko Hameeda ta fada da tsokana “.

Hameeda tace “au daman yara ne mu “?”

Fadila tace ” yara ne mana 18yrs fa Kinga lkc da zaki haifan ma yay Yazeed d’a kina 19yr”.

wani wawan tseki mtswww Hameeda ta ja Allah ya rabani haihuwa da wannan .

Dry Zarah tayi tace “Wallahi Ni zan tafi ai ke daman Fadila in bakiyi tsokana ba baki Jin dadi.’

Fadila tace “naji mu tafi dai “.

suna tafiya suna hira har suka kawo Gate.

Hameeda tace “Ni dai anan zan tsaya Kinga bani da hijab “.

Zarah tace ” to shikenan sai munyi waya “.

Fadila tace “Ni bari in rakata in dawo “.

Hameeda tace ” to sai kin dawo ki samai ni kitchen Wallahi yinwa nake ji “.

Fadila tace ok

Tana juyowa sukai ido hudu da yay Yazeed fuskan nan nashi kaman kullum d’aure. yau kam harda gyalass .😎

*nace to fa harda gyelashi bari inyi Nan* 🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀🏃🏿‍♀

 

 

 

 

 

*comment*
*vote*
*share*

 

 

 

 

Mr’s Aliyu ce ✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

🎐 “`G•W•A“`🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

 

 

*Story & Written*
*by*
*AUNTY BABY*✍🏻

 

 

 

_*gaskiya Ina jin dadin comment din ku musanma mardiyyah Ina yinki irin over dinnan 🥰🥰🥰💃*_

 

*Bismillahir rahmanir rahim*

 

 

*page* 2⃣0⃣to2⃣1⃣

 

 

Tana juyowa sukai ido huɗu da shi .

Ya ƙara tamke fuska yace “ke! daga Ina kike dan wulakanci ma ba hijab?. “.

Wani kallon wulaƙanci tamai sannan tace ” Ina ruwan ka in bansa hijab ɗin ba ?”.

Yace ” Hameeda rashin kunya taki har takai Ina miki mgn kina mayar min to Wallahi ki kiyaye Ni in ba haka ba wataran sai na karya ki idiot kawai “.

“Hmmmmm yay Yazeed kenan ai Wallahi baka ga ranin ba ma Sai ka yarda an daura auran nan dan Wallahi ka aura masifa da bala’i kuma Wallahi bana son ka bazan taɓa sonka ba mutum Yana da Wanda yake so Amma za’a haɗa shi da wani.”
ta ƙarashe zance tana barin wajan

Shiko binta kawai yake da kallon , kaman ba Hameeda ba ita ce zata tsaya tana gaya mai wannan magana lallai yayi sake to shiko sai ya bari anyi auran yaga abin da ta isa ta mai .

 

komawa yayi part ɗin shi ya kwanta cike da tinanin mgn Hameeda wai Bata son shi to waya gaya Mata shi zai ma taɓa sonta a duniya ai Wllh never ya san wannan yariyar da ko budurwa Bata gama zama ba.. Yana wannan tinanin har bacci yayi nasaran daukan shi .

 

Hamed ne kwance a d’akin shi tinanin duniya ya isheshi Yana ta Kiran Hameeda take dauka daga karshe ma kashe wayan akayi to shi mai yasa maita da har Bata daukan wayan shi .

Wani tinanin ne ya zo mai kawai ya tashi ya fada toilet yana fitowa yayi Shirin shi cikin bakin yadi mai sharashara Wanda har faran singlet din shi ana gani yayi kyau sosai abin ka da farin mutum daukan key din motar shi yayi ya fito daga part din nashi part din Umma ya nufa dan yau kwata kwata be fito ba sai yanxu.. ba kowa a parlour bedroom din ta ya nufa ya samai ta tana ninke kayan ta.

yace “sannu Umma “.

d’a guwa tayi tana kallon shi dik ya fada gashi fuskan shi kaman da damuwa.

 

tace “baka da lfy ne naga dik ka fada kuma yau baka fito breakfast ba “.

Zaunawa yayi a gefanta sannan yace wllh umma banjin dadin jiki na ne kawai.

Tace to “mai yake damun ka bari Hanifa ta kawo ma break ɗinka in kaci sai kasha magani ”

Yace no” Umma bana shaawar komai yanxu ma fita zanyi,”

tace” Kai da baka da lfy Ina kuma zaka? ”

Yace” zanje gun abokina Fahad ne.”

Tace “to a dawo lfy.”

Fita yayi ya shiga motan shi be tsaya ko Ina ba sai gidan su abokin shi Fahad Yana zuwa ya Kira shi yace ga shinan a bakin Gat.

Fahad yace to ga shinan zuwa be daɗe ba kon ya fito Yana shima ya fito daga motan shi gaisawa sukai irin na aboka sannan Fahad yace Hamed mu shiga ciki ko

Hamed yace “no abokina ba dadewa xanyi ba kawai muyi mgn a mota ”

Fahad ya kalle abokin nashi da fuskan shi da a laman damuwa sannan yace “haba Hamed wani irin baza ka shiga ba ”

Hamed yace “ok muje bana son surutu da yawa ”

Fahad yace “to muje ”

D’akin Fahad din suka wace suna shiga ya Sami kujera ya zauna Yana sauke ajiyan xuciya. Fahad ya yace “wai Hamed maike damun ka ne kwatakwata ba walwala tare da Kai ?”

Hamed yace “Hameeda kullum Ina Kiran ta Bata daukan waya na gashi papa yau zai dawo Ina so suje gidan su kafin ya tapi Wallahi Ina cikin damuwa sbd ban San maike damunta ba “.

Fahad ya nisa kafi yace “ai wannan mai sauki ne kawai muje gidan su muji ko lfy.”

Hamed yace “to shirya mu tafi”

Fahad yace “ok bani 30min kawai”

Hamed yace “ok ”

 

 

Maman Nusaiba ce ita da qawarta Haj zuwaira suna Shirin fita. Haj zuwaira tace

“haba Haj kiyi sauri mana kin San dai boka Dan dunkulu baya san jira kuma nace mai da wuri zamu zo.”

Maman Nusaiba tace “to Haj ko break banyi ba Amma tinda kin matsa mu tafi kawai ”

Haj zuwaira tace” Ina wani zance break ai kawai In mun dawo mayi dan ko Ni banyi break din ba ”

Maman Nusaiba tace to tashi mu tapi na gama. Haka suka fito maman Nusaiba ce mai jan motan suka kama hanyan wani kauye da ke can cikin Zaria tafiya suke har saka bar kwalta suka shiga D’aji tafiyan awa daya ce ta kaisu inda suke San zuwa.

Haj zuwaira tace “muyi fakin anan dan mota baza ta shiga gurin ba ”

To kawai maman Nusaiba tace dan gabanta sai faɗuwa ya ke ta rasa dalili

Fitowa sukayi a motan Haj zuwaira ta rike hannun maman Nusaiba da jikin ta ke rawa wata buka Haj zuwaira ta nuna ma maman Nusaiba tace” yauwa Kinga bukan can mu qarasa ko “ta faɗa tana Jan hannun ta.

 

gurin bukan suka nufa suna zuwa Haj zuwaira ta saki hannun ta tace “bari in je in mai mgn ”
To kawai maman Nusaiba ta iya cewa
Haj zuwaira kuwa bukan ta shiga wani katon mushiriki ne zaune kan wani jan buxu fuskan nan tashi ba ken gani ga rantamaiman Kai bashi da wani tsawu sosai. Washe jajayan hakurin shi yayi Wanda basu wuce goma ba Amma sun cikin bakin sabida girma.

Haj zuwaira tace” a lfy dai boka Dan dunkulu ifiritu ya baka lfy ya qarama sawan kwanan” kirari dai kala kala

Wata uwar ashar ya mulmulo yace” sarki Dan tsamake na miki barka da zuwa kice wa Wanda kuka zo ta shigo da kafar hagu ”

Haj zuwaira tace “an gama Dan dunkulu” fita tayi tacema maman Nusaiba ta shiga Amma da kafar hagu haka kon maman Nusaiba tayi ta shiga tana zuwa ta xube gaban shi.

Tace “Ina gaisuwa Dan dunkulu ifiritu ya baka abin da kake so. ”

Ya hadiye wani miyu mukun kake ji a zuciyar yace ai dole na huta da wannan. Sannan yace dik abinda ke tafe dake na sani yanxu mai kike son ayi musu

gaban maman Nusaiba ne ya fadi tace “kasan mai ke tafe da Ni? ”
Wani ashar din ya qara sannan yace “qarya zan miki ne ?”

Bakin maman Nusaiba har rawa yake gurin cewa Aa

Sannan yace” to mai kike son ayi musu ?”

Haj zuwaira ta kalla sannan tayi mgn a hankali tace” mai za’a yi musu ”

Haj zuwaira tace “ki faɗi abun da kike son ayi musu mana ”

 

Sai sannan ta kalle shi tace” a lalata auran tinda dai yariya ta Bata aure shi ba to ita ma baza ta aure shi ba”

Wani ruwa ya dauko sannan yayi dan dube duben shi yace “wannan aure bazai taba lalatuwa ba dan naga kaman da yara a ciki ”

Duban shi maman Nusaiba ta qara yi sannan tace” haba boka Dan dunkulu ya zaka ce bazai lalatu ba ?”

Yace “eh abinda na gani kenan Amma yanxu mai kike son ai musu a kashe su ko kuma ai musu kurciya ko kuma a sa musu kiyanyar juna ?”

Zuba ce ta rubata sharaf dan dik makircinta baza ta iya kisa ba.
Haj zuwaira ce ta tabota tace mai kike son ai musu?
Maman Nusaiba tace” kawai a sa musu kiyanyar juna da ko anyi auran baza suyi zaman lfy ba ”

Yayi wata shegiyar dariya sannan yace “aikin gama ya gama sai dai da sharadin zaki bamu kanki dan ifiritu ya yaba ”

Ras Ras gaban ta yace” tace na shiga uku da auran nawa ?”

Dafa ka fadar ta Haj zuwaira tayi sannan tace” haba Haj sai kace wani ya San abinda kikayi waye ana daga Ni fa sai ke haba karki bada Mata mana ”

Wani gumi maman Nusaiba ta sharce sannan tace “Wallahi Ina Jin tsoro ”
Haj zuwaira tace” dan Allah ki cire tsoro qawata badai bukata zata biya ba ai ba matsala “ta fada tana Mata murmushi

Maman Nusaiba ta qara kallon shi gaba dayan shi wari yake ga wani uban daud’a a jikin shi wani irin take ji a jikin ta

Kallon ta yayi yace” shikenan In baki yarda ba amma ki San da sani dik abinda ya samai ki ke kika ja ”

Bakin ta na rawa tace “na yarda ”

Washe jajayan hakurin shi yayi sannan yace” yauwa Yar gari ”

Ya dube Haj zuwaira yace” sai ki bamu wuri ko”

Murmushi Haj zuwaira ta sakin mai kafin “tace a gama Dan dunkulu”

Ita kam maman Nusaiba ba abinda tayi sai kolla Amma in ta tina ai dik kan Nusaiba tayi sai taga ai ba komai bane in dai ‘yarta zata dauwama cikin farin ciki

Ta sowa yayi ya matso gareta. Wani irin wari ya dushi hancinta Bata San sanda ta tofar da miyu ba
a zuciyar shi kuwa cewa yake zaki gane kuren ki tinda kin zo hannu. gyalanta ya fara cirewa sannan ya cire Mata komai nata shima ya cire ya haye kanta haba ya fara aiki……..

 

 

 

Hamed ne da abokin shi Fahad cikin mota sun zo dai dai Gate din su Hameeda
Fahad yace” to yanxu waye zai Kira mana ita.?”

Hamed yace” bari in ma getman din su mgn” fitowa yayi daga cikin motar sannan ya fara noking din Gate din yayi
getman ne ya leko sannan yace waye

Hamed yace “dan Allah hameeda na Nan ?”
getman din yace” eh tanan nan ”
Yace” Dan Allah dan yi min sallama da ita ”
Yace “to wa za’a ce Mata
Hamed yace kace Mata Hamed ne ”

 

getman din yace to sannan ya huce part din su Hameeda konkwasa kofan D’akin yake.
Saudat na zaune tana kallo ta ji anan noking tashi tayi taga ko waye tana bude kofan taga getman tace Aa baba Kaine
Yace eh “Saudat Hameeda na ciki ne ?”
Saudat tace” eh tana nan lfy ?’
Yace :eh wai Hamed ne ke kiranta ”
To Saudat tace sannan yace bari in fada Mata
Yace to tare da barin gun

Kwance take kan bed dinta tana aikin nata wato tinani ta ramai sai dai ta kara fari Saudat ta shigo tace aunty Hameeda wai kizo in ji uncle Hamed
Mikewa tayi daga kan gadon tace wani Uncle Hamed din Dan bayi tinanin zuwan shi yanxu ba

Saudat tace uncle Hamed din ki mana

Hameeda tace to gani nan daman sanye take da daguwar riga atamfa sai kawai ta gyara fuskan ta ta yafa gyalan ta ta fito dan Momy Bata Nan ta tapi gaishe da mara lfy a asbiti shiyasa kawai fitowa tayi..

Jingine yake da jikin motar shi ta fito tinda ta fito yake binta da kallon har ta iso gare shi tayi mai kyau sosai sai dai kaman ta ramai ya fada Yana sakin Mata murmushin shi yace my Hameeda
Tace naam my Hamed Ina yini
Ya amsa sannan yace baki da lfy ne hameeda in na Kira wayanki baki dauka sannan kuma yau sai kika kashe wayan?

Ta shagwabe fuska tace haba to wani tambaya kake son In amsa
Yace dika mana
Tace to bani da lfy ne shiyasa Ni wayan ma kwana biyu ban dauke ta ba

Yace ayya my love shiyasa nima asha Banda lfy
Hey guys ka manta dani ko cewar Fahad da yake fitowa daga mota
Ina yini Hameeda ta fada tana sanya kanta kasa

Fahad yace lfy lau amaryan mu ya kk ya hutu

Tace alhmdllh
Yace to haka ake so

Soyayyar su suke sha Dan ita Hameeda har ta manta da wani aure da aka ce za’a Mata tinda taga sanyin ranta

 

 

Be sararamata ba sai da ya kwashi awa biyu sannan ya d’akata wani wahalan kuka ta saki ji take kaman ta mutu Dan azaba ko kallan ta beyi ba yace ta tashi ta bashi guri dan Yana da baki yace ta tapi zata ga aiki da cikawa sannan kudin aikin ta dubu hamsin hakan Nan tana kuka ta ciro kudin shi ta bashi sannan ta maida kayan ta ta fito a bukan
Haj zuwaira ta tare ta da Haj ya naga kin dade
Wani mugun kallo ta watsa Mata sannan ta shige mota jikin ta dik ciwo yake Haj zuwaira na ganin haka ita ma ta ciga Bata ce Mata komai ba har suka kawo gida ta fitowarta ba tare da ta kula ta ba
Haj zuwaira yace kajin min Mata waye ce kike da zaki dinga min fushi mtsww ta ja tsaki tana fitowa daga motar Bata bi bayan ta ba sai ma hucewar ta gidan ta da tayi cike da haushin fushin da maman Nusaiba keyi da ita……

 

 

Haka suka gama Shan hiran su ta soyayya sannan ya Mata sallama ya tafi ita ma ta koma gida sai sannan ma Hameeda ta tina da auren yay Yazeed din da za’a Mata wani haushi ne ya kamata tace Wallahi bazan taba auran ka ba yay Yazeed na tsane ka….

Washe gari…..

 

 

 

 

 

*comment*
*vote*
*share*

 

 

 

 

 

Aunty baby✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

 

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA* 💅🏻

 

 

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

🎐 “`G•W•A“`🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

 

 

*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏻

 

 

*Bismillahir rahmanir rahim*

 

 

 

*page* 2⃣2⃣to2⃣3⃣

 

Washe gari.

Hameeda ta tashi da wani irin ciwon ciki da duk wata takeyi, kuka sosai takiyi dan dama bai Mata da wasa kuma duk wata takeyi.

Mamy ce ta shigo dakin hannun ta rike da kofi tace “Hameeda tashi ki Sha wannan maganin kafin yayan ki Yazeed ya fito sai ya miki allura”.

Tashi Hameeda tayi tana matsa kwala tace, “Momy dan Allah karki Kira shi Wallahi bana son allora” .

“A dole kuwa a miki kin San da ita d’aya ce ke saukan miki da wannan ciwon,”

Maganin ta amsa tasha sannan ta koma ta kwanta ita kuma Momy ta fita Kiran yay Yazeed.

 

Maman Nusaiba kam tana shiga D’aki toilet ta wuce tayi kwanka sannan ta gargasa jikin ta dan ba karamin ciwo yake Mata ba.

a zuciyarta kuwa in banda tsine ma Haj zuwaira ba abinda takiyi dan Bata gaya Mata sai ya kwanta da mutu ba aiki keyi da baza ta ba sai dai ta nemi wani bokan. Haka dai take ta zancen zucinta har ta fito daga toilet din .

Nusaiba ta Tarar a kwance kan bed dinta tana chatting kallon ta tayi taga chatting dinta take hankalin ta kwance
tace Nusaiba” wai bakin San na dawo bane” ?

Kallon ta Nusaiba tayi sannan tace “au ashe fita kikayi ai ban sani ba , yauwa mama dan ban dubu goma wata kawata ce zatayi birthday shine zan siyan Mata gift”.

Wani kallo maman Nusaiba ta zubama Y’ar tata sannan tace “da kin San inda naje da baki camin in baki kudi ba”. ta fad’a ranta bace

Nusaiba tace “to mama Ni Ina ruwa na da inda kika je, Ke daman in dai mutum zaice ki bashi kudi sai kin mai masifa”. ta fad’a tana k’ok’ari tashi a gurin .

Maman Nusaiba tace “haba Nusaiba Dan ke fa naje in da naje Amma kike k’ok’arin fata min rai”.

Nusaiba dai fitan ta tayi bata tsaya taji mai take cema Mata ba.

Yaya Yazeed na kwance a D’aki shi yaji a na knocking,
yace “waye”?

Momy tace “nice Yazeed bude min”

Tashi yayi yaje ya bud’e k’ofan sannan yace “au Momy”

Momy tace “Yazeed Hameeda ce ciwan ta ya tashi kasan dai yanda take Shan wahala ga ta can sai kuka take”. ta qarashe zance muryarta a sanyaye .

Yace “to Momy muje in duba ta” .

Tana kwance sai faman kuka take tana kiran Abbu zata mutu sai gashi ya shigo, kallon ta yayi a zuciyar shi yace “jibeta ciwan ciki take ma wannan kuka” .

Momy tace”Hameeda tashi ga yayan ki yazo duba ki”.

“Hmmmm Ni Wallahi momy bana son allora kuma kin San ita zai min pls Momy ya tapi kawai” .

 

Dan k’aramin tsaki yaja sannan yace “kin tashi ko sai jikin ki ya gaya miki”.

“Wayyo Abbu ka zo ga wannan mugun zaimin allora wayyo Meme wayyo Allah na,” haka Hameeda ke ta fad’i sai kace taga alloran ma a hannun shi

Momy tace “Allah hameeda ranki zai baci”.

Yay Yazeed yace “barta Momy ta tashi ta biyo Ni D’aki Dan ban fito da kayan da zan duba ta ba” .

Hameeda tana jin haka ta gane akwai muguntar da zai hada Mata, tace “Aa ka bani magani kawai” .

Ko kallon ta beyi ba yayi fitar shi, dole yasa ta tashi tana mai zubar da k’wallah…

 

Ko da suka je allura taka ya dauko Yana sanya maganin a cikin ta sannan
yace “ki matso dan Ina da abinyi in kuma baki so shikenan ya daga kafad’in🤷‍♂ sa”.

hawaye ta share sannan ta matsa kusa da shi ta tsaya
tace “to gani”.

Alluran ya saita sannan ya janye rigar ta ya fara Mata bako tausayin Dan in ya tina mgn da ta gaya mai sai yaji wani mugun haushin ta.

ita kuwa kankame jikin ta tayi hawaye wani na bin wani…..

 

Yana gama Mata ko mgn be Mata ba ya huce abin shi.

Tana bin bango har ta fita daka part din taje nasu Dan ciwan ya fara Mata sauki. Nan kuma jinin ya fara zuwa shiyasa take saurin ta koma D’akin ta gyara jikin ta……..

 

 

Yaya Areef ne zaune a parlour su yana aiki a laptop dinshi, sai Fadila ta fad’u mai a rai yace ya gamata fa yayi mgn da yariya da tin randa akai mgn Nan be qara sata a ido ba. tashi yayi ya fito ya nufi part din su Fadila Yana zuwa dai dai kofan ya hadu da su Mubeen suna ball,
Yace “Mubeen zonan” .
Mubeen “yace to yaya”
Yay Areef yace “Fadila na nan”?.
Mubeen yace “eh tananan”.
Yace “Kira min ita kace ta samaini a D’aki na”.

Mubeen”yace to yaya”.

D’akin Fadila Mubeen ya shiga Daman ta fito wanka kenan,
yace “Aunty wai yaya yace ki zo yanxu”.

Fadila tace “wani yayan”?.

Yace “Yaya Areef, yace kuma ki samai shi a D’akin shi”.

Fadila tace”to naji”.

Shiryawa tayi cikin atamfa riga da siket sun Mata kyau sosai, ta fito ta nufi D’akin nashi .

Tana zuwa ta fara knocking.
yace “yes come in”.

Shiga tayi da sallama a bakin ta,
ya amsa Yana Wani watsa Mata wani shu’umin murmurshi….

Ita sai taji duk ta tsargu, kallon ta yake kaman yau ya fara ganin ta
Tace “Ina yini”.

Yay Areef yace “lfy lau, Fadila kin tashi lfy”?

Tace “alhmdllh” .kanta na k’asa “tace kace in zo” .

Yace “eh Fadila dama tambayanki nake San inyi” .

 

Tace “Allah yasa na sani”.

 

Yace “Fadila kinji yanda big Daddy yace ko, to ke mai kika ce Ina Sona ko baki Sona ki bada min tsakanin ki da Allah” ya qarashe mgn Yana kallon fuskan ta.

Tace “yay Areef Ni……..

 

 

To fa Fadila ko mai zatace 🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀🤷🏻‍♀

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

 

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻

 

 

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

🎐 “`G•W•A“`🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

 

*Story & Written*
*by*
*AUNTY BABY*✍🏻

 

*Dedicated to babu shi a zuciyata fan’s 2*

Wannan shafin nakune kuyi yanda kuke so dashi Ina Jin dadin comment din ku💃💃💃💃💃💃 Allah ya barmu tare🥰😍😍

 

*Bismillahir rahmanir rahim*

 

 

*page* 2⃣4⃣ to2⃣5⃣

 

Tace “yay Areef Ni na yarda da zaɓin da big Daddy ya min Allah yasa hakan ne Mafi Alkairi”

Wani irin sanyi yaji a zuciyar shi, Dan be taba tinanin Fadila zata amince da wuri ba…

Yace “gaskiya Fadila naji daɗin amincewar ki Allah ya miki albarka”

tace”ameen yay Areef Ni bari in tafi”

Tashi yayi yace “to muje in raka ki”

Tace “la, yay Areef da kayi zaman ka”

Yace “Aa ni dai muje”

Tafiya suke cikin farin ciki da annashuwa dan ba qaramin daɗi yake ji ba yau dinnan, suna zuwa kofan D’akin su.
Yace “Fadila Ni na huce sai na Kira ki”

Kanta a kasa tace “to yay Areef” sannan ta shiga dikin su….

 

Big Daddy ne zaune a D’akin Haj jadda suna magana akan yanda bikin zai kasance Dan yace Mata ya tsayar da rana wata hudu, lkc su Hameeda sun gama exam,

Haj jadda tace “to Allah ya kaimu lkc yasa kuma ayi da mu”

Big Daddy yace “ameen”

 

Hameeda da uncle Hamed kuwa suna Shan soyayyar su dan har yanxu baban Hamed be samu lkc zuwa gidan su Hameeda ba, ita kuma Hameeda Bata gayamai an Mata miji ba

Yanxu kowa na gidan yasan an tsayar da biki wata hudu, har yanxu kuma ba wata jituwa tsakanin yay Yazeed da Hameeda sai ma tsanar juna da sukayi duk abinda zai hada ta da shi bayi take ba shima haka, shiko yay Areef da Fadila kaman zasu had’iye juna Dan so

Fannin Nusaiba da Nabil ma dai sai a hankali dan be taba zuwa ba sai dai ya Kira ta a waya wayan ma ba wani firan arziƙi suke ba ita tayi shuru shima yayi shuru har ya gaji ya kashe dan shi baya daukan raini

 

Bayan sati uku

 

Yay Yazeed ne zaune a office ɗin shi Yana duba marasa lfy, sai ga wata yarinya ta shigo fara ce sosai Amma daga gani tana qarawa da mai,

Tace “Dr Yazeed Ahmad, ashe daman zan ƙara ganin ka Kai Amma yau sai na tasa a cikin tarihin rayuwata”

D’aguwa yayi ya ga kaman yasan mai muryan ai kon yana ganin ta,
yace “Yusura?”

Tace “naam Yazeed ai Wallahi ba haka alkawari yace ba tinda muka dawo shikenan baka k’ara nema na ba kuma dai kasan yanda nake sonka Yazeed Wallahi har yanxu sanka be fita a zuciyata ba I love you I love you so much my Yazeed”

Tinda ta fara mgn yake kallon ta yace “lallai Yusura har yanxu kina Nan da shirmanki ko”?

Tace “wai Yazeed yaushe zaka gane Ni masoyiyar ka ce ta asali kullum Ina kawo ma Kaina kana yar fa Ni Amma bazan gaji da nuna maka ina sonka ba”

Yace “duk ba wannan ba yanxu dai ga guri ki zauna”

Zaunawa tayi a gujeran da ya nuna Mata sannan, tace

“Yazeed da fatan dai bakai aure ba dan Wallahi duk mace da tayi kuskuran auran ka to wallahi…..”

Bai bari ta k’arasa ba yace “haba yusura wani irin mgn kike haka Ni tin muna makaranta na gaya miki ki cire Ni a ranki Ni bana sonki kuma iyaye na baza su bari in aure ki ba pls ki cire ni a rayuwan ki kinji yusura pls” ya qarashe zance da alaman lallashi

 

Wani uban ashar tayi sannan tace “Wallahi Yazeed qarya kake dole ka soni Wallahi sai ka aure Ni Yazeed mai kake so inyi ma Wanda zaka aure Ni Allah Ina sonka Ina sonka Yazeed in ban aure ka ba zan iya mutuwa” tana magana ne tana kuka

Wani irin mugun tausayinta ne ya kama shi yasan yusura tana son shi Amma shi halayanta ne baya so kuma Yana tinanin ma da wuya iyayan shi su yarda ya aure ta, Dan yusura wayaryiyace ta karshe tun suna Landon take son shi tasha fada da mutane sabida shi Amma shi ko kadan be Jin sonta a zuciyar shi..
“Yazeed”
Firgiget ya dawo daga tinanin da ya lula,
ta qara cewa “Yazeed”

Yace “naam yusura yanxu Ina da mutane ke je zan Kira ki”

Tace “Aa Yazeed baza ka Kira Ni ba nasan halin ka”

Yace “bani nace zan Kira ki ba ki tapi mana”

Jakan ta ta dauka sannan tace “zan tafi Yazeed Amma zan dawo gobe har sai ka yarda ka soni Yazeed Ina sonka I love you Yazeed”

Da kallon kawai ya bita har ta fice sanye take da wani riga da wando sun matseta sosai kayan sai Dan qaramin gyale da ta sa, kadan kenan daga halayan yusura da baya so,

Tinda ta fita ya fada duniyar tunani Yana tina maganganun yusura, wata zuciyar tace Yazeed kawai ka aure ta tinda dai ba son Hameeda kake ba, wata kuma tace Aa Yazeed gida ma baza a yarda ka qara aure ba bayan ga Hameeda, da yaji bazai iya aikin ba tashi yayi kawai ya dau key din motar shi ya fita ya Kira safwan yace ya kula da sauran patient din

 

 

Yawan comment yawan typing 🤷‍♀

 

 

 

Aunty Baby ✍🏻
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

 

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻

®☄
*GASKIYA WRITER’S ASSOCIATION*✍🏻
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

🎐 “`G•W•A“`🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

 

*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏻

 

 

 

*Bismillahir rahmanir rahim*

 

 

*page* 2⃣6⃣to2⃣7⃣

 

 

 

Ko da yay Yazeed ya tafi gida part din su ya huce, mgn yusura ce kawai ke mai yawo a kwakwalwa, Yana shiga D’akin ya Sami Meme na waya da qarwata suna mgn ne akan bikin, zaunawa yayi a kusa da ita ya Dan kwantar da kanshi a cinyar ta sannan yace,

“Meme na” yayi mgn ne cikin shagwaba.

Meme tace “Naam my only son menene naga fuskan ka ta chaja kuma ai yanxu ma ba lkc dawowar ka aikin bane”

Yace “hmmmmm Meme hakan kurun naji bana son zaman asbiti shine na dawo gida na dan huta”

Meme tace “to my son dama akwai mgn da nake son inyi da Kai”

D’a guwa yayi Yana kallon ta yaji wace mgn ce,

Yace “to Meme Ina jinki”

Sai da ta shafa kan shi sannan, tace

“Ina cikin farin ciki Yazeed”

Mik’iwa yayi a jikin ta dan kafin yaji Meme ta Kira sunan shi da wuya Amma to wani irin farin ciki take haka….

Sannan ta cigaba da mgn, “Wallahi ba qaramin dadi nake ciba way Kai zaka aure Hameeda Ina son Hameeda kaman yanda nake sonka Yazeed Dan Allah ka daure ka faranta wa Hameeda na San Bata sonka Amma ka daure ka chusa Mata sonka”

Wani irin bugawa girjin shi yayi, daman mgn wannan banzar yariyar zatayi mai to shi gaskiya yanxu yake jin zai iya auran yusura shi ya gyara Mata halayanta dan ita tana son shi ba abinda baza ta iya ba sbd shi,

Taba shi Meme tayi dan taga ya tafi wata duniyar
tace “Yazeed baka ji abinda nace bane”?

Yace “naji Meme Amma nima Ina son in gaya miki wata mgn”

Tace “Ina jinka”

 

“Hmm daman hmmm”

Sai kuma ya kasa mgn dan yasan Meme da wuya ta yarda,

Meme ta qara cewa “ina jinka”

Yace “Meme akwai wata yariya da take Sona tun muna Landon kuma na Mata alkawarin zan aure ta shine” hmmmmmm
Sai kuma ya kasa qarasa wa

Meme tace “shine mai, badai so kake kace min zaka aure ta ba to Wallahi Yazeed karka kuskura in qara Jin wannan mgn” ta karashe zancen da fada, tace “Wallahi karka yarda ma Daddy ka yasan mgn nan, to ita Hameeda kayi Yaya da ita “?

Shi Yama kasa mgn sbd wani irin tsanar Hameeda yaji ya qara ji a zuciyar shi akan ta za’a Hana shi abinda yayi niyar yi to Wallahi sai dai ita ya fasa auranta,

Meme tace “wai ba mgn nake maka ba”

Yace “Meme ai itama zan aure ta Amma a fara yin na”…… Bata bari ya qarasa ba ta gwabe mai baki tace

“Shashasha Wanda basan abinda yake mai ciwo ba tin yaushe ake ma mgn aure kace Kai baka da budurwa sai yanxu da aka baka yar uwarka shine zaka fara ma mutane maganan banza tashi ka bani guri kuma Bari Daddyn naka ya dawo in fada mai shashanci da kake tinanin yi”

Tashi yayi ya fita rashin b’ace akan wannan yariyar Memen shi ta gwabe mai baki to Wallahi akan ta zai rama Allah ya kaimu ayi bikin, part din shi ya huce kwantawa kawai yayi Yana tinanin yusura ga wacce take son shi har kuka take sbd shi Amma za’a hada shi da wacce qaramar yariyar da ko 18yr bata rofa ba…

*************
Maman Nusaiba ce zaune abin duniya duk sun ishe ta Dan ita har yanxu bata ga aikin ya fara ci ba, wayan ta ta dauka da danna ma qawarta Haj zuwaira kira ringing biyu ta dauka, tace

“Sai yau aka tina dani ai Haj kin ban mamaki sai kace Ni ne miki laifin”

Maman Nusaiba tace ” haj kenan ai kece kin ban haushi kin San fa Ina da aure na mai yasa zaki kaini gun wannan bokan, duk cin amanata ban taba zina ba shiyasa na damu sosai”

“Hhhhh Haj kenan ai Wallahi Ni zuwaira naci dubu sai ceto maiye a ciki Dan kayi zina abunda ba wani ne ya ganka ba ai ba wani Abu”

Maman Nusaiba tace “duk ba wannan ba nifa har yanxu ban fara jin fadan su ba, shine nace ko zamu koma ne Amma fa gaskiya bazan qara aikata kuskuran da na aka ta ba”

Haj zuwaira tace “Ni in qara rakake kizo kina Jin haushi na ba inda zani”

Maman Nusaiba tace “haba qawata ai ko wancen ma Dan ban saba bane Amma kiyi hakuri”

Haj zuwaira tace”to shikenan Allah ya kaimu gobe zan zo”

Maman Nusaiba “tace yauwa qawata na gode sai goben ”

Wata dry ta sak’i hhhhh sai Ni Haj zuwaira tace “zaki ci ubanki ne ai gabaki daya kudin ki sai na cinye”

Hameeda ce zaune a parlour su suna kallon tarkon kauna a tashar arewa24, sai ga zarah nan ta shigo.

Tace “Kai Hameeda ke kina son wannan film din nikon banga abin kallo a ciki ba”

Hameeda tace “Zarah kenan in kika fara kallo baza ki Bari ba sbd Yana da kyau Ni Wallahi omar din nan haushi ya ke bani ace mutum bashi dry sai kace wani yay Yazeed”

Dry Zarah tayi sannan tace “au nagane abin da yasa kike kallon wannan film din Yasin sbd Omar na kama da yay Yazeed ne”

Hararan ta Hameeda tayi sannan tace “Wallahi zaki sa ma na daina kallon film din”

Fadila dake shigowa yanxu tace “yo ki daina kallo mana ai mundai San baza ki daina kallon mai kama da mijin ki ba”

Dry suka kwashe da ita duka Hameeda kon ta qara ciki ta fam..

Zarah tace “Yan Mata biki na ta k’aratowa mai kuke ganin zamu shirya ne dan bikin Yan Mata uka ba wasa ba”

Fadila tace “haka ne Amma ki bare mu kammala exam, sai a San abinyi”

Ita dai Hameeda Bata ce k’ala ba, sai ma wayan ta da ta fito tana game….

 

Lakaci na ta tafiya

Yanxu haka bikin su Hameeda sauran wata biyu, shirye shirye ake yi ba kama hannun yaro Dan kowa Yana so ya fito da d’iyar shi, ita dai auntyn amaryar maman Fadila kenan tare suke abin su da Momyn Hameeda, maman Nusaiba ba kon ita daya ke abinta Daman ba son yaron take fa kawai dai tana yi ne Dan ta yarta tafi kowa fice a gidan

Yanxu haka kuma exam din su Hameeda sauran paper uku su gama

Yau kuma iyayan uncle Hamed sukai Shirin zuwa, sun gama komai nasu papan Hamed da kanin shi sai kuma abokin shi, Hamed ne ke ta Kiran Hameeda wayan be shiga ba sai kawai kawun shi yace ba matsala bari su tafi tinda ita yariyar tana son shi ai ba matsala, hakan kon aka yi shi ya kaisu har bakin Gaten din gidan su Hameeda sannan sannan ya je neman musu iso gun getman din yaje ..

Yace “baba Dan Allah baban su Hameeda na Nan”?

Getman din yace “eh suna Nan duk mazan gidan”

Yace “to dan Allah kace musu suna da baki”

Getman din yace “to”

sannan ya tafi part din big Daddy ya nufa Yana xuwa kon ya Samu big Daddy ya fito zai fita yace sai da suka gaisa sannan yace mai suna da baki,

Big Daddy yace “baki kuma daga Ina”

Getman din yace “eh baki ne Amma bansan daga Ina suke ba”

Big Daddy yace “to kace musu su shigo ka Kai su D’akin baki”

Getman din yace “to alh sannan ya huce”

Yana zuwa yace ma Hamed ance su shiga sai Hamed ya je ya gawa papan shi sannan shi kuma ya shiga motan, fita sukai a motan suka shiga gidan D’akin bakin getman ya kaisu.

Big Daddy ne ya shigo da sallama sai da suka gaigaisa sannan..

Yace “ban waye ku ba”

Kawun Hamed ne yace “sannu alh sunana alh sagiru shi kuma wannan sunan shi alh mustapha papan Hamed kenan sai kuma wannan sunan shi alh Abbas” abokin papa kenan

Big Daddy yayi murmurshin yace “to sannun ku da zuwa”

Alh Abbas “yace wato alh dalilin zuwan mu gidan ka shine d’ana yaga yarku yace Yana so shine muka zo in Allah yasa ba ayi Mata miji ba”

Saudat ce ta shigo da babban faranti a hannun ta sannan ta gaishesu ta fita ruwa ne da kayan motsa baki….

 

Big Daddy yace “ga ruwa ku Sha alh”

Duk suka ce sun gode sannan alh Abbas ya cigaba da mgn

Big Daddy yace “to duk da dai bansan wacce kuke mgn ba Amma dai yaran uku Mata an musu mijin dan yanxu haka ma sauran wata biyu bikin su”

Kawun Hamed yace “to Ina ga dai wannan ba a Mata miji ba gaskiya”

Big Daddy yace “ko ya gaya muku sunan ta”

Kawun Hamed yace “eh sunan ta Hameeda”

Big Daddy yace “kash Hameeda bikin ta sauran wata biyu ko dai Saudat yake mgn”

Alh Abbas yace “Aa alh Hameeda ce”

Big Daddy yace “Ina mai baku hakuri Hameeda an riga da an Mata miji yayan ta zata aura”

Sai yanxu papan Hamed yayi mgn yace “to alh mun gode da karamcin da ka mana, ita kuma Allah ya basu zaman lfy”

Duk suka amsa da ameen sannan big Daddy yace

“Shima Allah ya bashi mace ta gari”

Nan ma suka ca ameen sannan suka mik’i zasu tafi,

big Daddy yace “baku ci komai ba”

Suka ce ba komai daga gida suke..

Hakanan suka fito gidan jiki a sanyaye, Hamed na ganin su ya fito daga mota ya tare su da murnar shi, yace
“Kawu sannan ku”

“Yauwa” kawai kawun Hamed yace

Motan suka shiga suka fara tafiya har suka kai gida ba Wanda yayi mgn, sai da suka fito a motan Hamed yayi haryar part din shi papan shi yace Aa ya biyo su, parlour suka shiga gabaki dayan su umman Hamed tana ganin su ta tare su da murnar ta, gabaki daya zauna wa suka Hamed Yana kan cerpat, papa ya gyara murya yace

“Hamed duk Dan adam an San shi da yarda da qaddara mai kyau ko Mara kyau……….

 

_In naga comment in cigaba in ban gani ba kuma Ina muku fatan alheri dan bazan dinga muku typing ba baku comment😊_

I love you 😘 all my fan’s💃💃💃💃

 

 

*comment*
*share*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

 

*💅BABU SHI A ZUCIYATA💅*

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

🎐 “`G•W•A“`🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

 

 

*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏻

 

 

*Bismillahir rahmanir rahim*

 

 

*page* 2⃣8⃣to2⃣9⃣

 

 

 

Hamed dai baice k’ala ba, dan tinda yaji ana mai wannan maganar yasan to ya rasa Hameeda har abada.

Papa ya cigaba da cewa, “Hameed an riga da an sawa Hameeda Ranar bikinta sauran wata biyu kayi haƙuri ka daure Allah ya baka wacce tafi Hameeda, sannan yanxu na yanke shawaran haɗaka da ƴar’uwarka Hanifa”

Umma kallon dan nata kawai take yi Dan tasan ba ƙaramin so yake wa Hameeda ba Amma ba rabon shi bace, Daman (hausawa sunce matar mutum ƙabarin sa)

Kawun Hameed yace,

“Masha Allah wannan haɗin yayi Allah ya kaimu lokacin”

Duk suka amsa da “ameen” shiko Hameed ma ai ya kasa magana, ɗakin shi ya tashi ya tafi.

Abokin Papa yace,

“Allah sarki Allah ya cire mishi sonta a zuciyar shi”

Papa yace, “in banda yaran zamani ma maiye dan kana son budurwa baka samu ba, ba sai ka koma kan wata ba”

Umma tace, “to Allah yasa dai ita Hanifa Bata da Wanda take so”

Papa yace, “wannan kuma ai ke ya kamata ki tambaye ta, Amma nasan dai ba Wanda take kulawa kin San Hanifa akwai nutsuwa”

Haka dai sukai ta tautaunawa…………

*************

Big Daddy kon suna fita shima ya wuce part ɗin Haj Jadda, ya Kira Abbu da Abba yace su samai shi a part ɗin Haj Jadda, Nan da Nan kon suka haɗu.

Haj Jadda tace, “ince dai lfy?”

Big Daddy yace, “lfy lau fitan nan da nayi sai aka ce min nayi baki Ina zuwa na samai su, sun zo tambayan auren Hameeda”

Haj Jadda tace, “wace Hameeda kuma ita da aka mata miji ko basu San bikinta ya matso bane”

Big Daddy yace, “basu sani ba Amma na gaya musu”

Abba yace, “to ai gwara da ka gaya musu”

Haj Jadda tace, “halin ma ƴar banzan yariyar nan ta San da zuwan su dan ta kunyata mutane yasa ta turu su”

Big Daddy yace “haba Haj Jadda tasan an Mata miji Ina zata ce wasu su zo kuma”

 

tashi yayi ya kalla agogon hannun shi yace, “Bari in wuce daman baƙin nan ne suka tsayar Dani”

Sai yanxu Abbu yayi magana yace, “to Allah ya dawo da kai lafiya nima Ina ga yanzu zan fita”

Haj Jadda tace, “a dawo lafiya”

******
Hameed tinda ya shiga ɗaki ya dafe ƙirjin shi, wani irin nauyi yaji yana mai sannan kanshi na sarawa, wasu hawaye ne suka zubo mai masu zafi yace,

“Wallahi nasan mutuwa zanyi bazan iya rayuwa Babu ke ba Hameeda nasan kema dole akai miki, shikenan yanzu na ƙara rasaki Hameeda wayyo Allah Daman ɗaukan Raina akayi da ganin wannan ranar”

 

ji yayi an dafa shi ya d’ago yaga ko waye,
Umman shi ce ƙwalla ta cika Mata ido tace,

“Hameed ka zamo namiji mana kayi haƙuri da ƙaddaran da tazo ma Dan Allah karka sa kanka cikin damuwa kasan halin ciwan ka”

hannunta ya rik’e sannan yace,

” Umma Wallahi Ina son Hameeda bazan iya rayuwa Babu ita ba, kina gab da rasa Ni Wallahi Ina ma Hameeda son mutuwa ya zanyi da rayuwa….”

 

Tari ne ya sarƙe shi ya kasa ƙarasa abinda zaice , tari yake kaman na ɗaukan rai idon shi ya firfito, ya saki hannunta ya rik’e ƙirjin shi.

Kuka Umma ta fashe da shi sannan tace,

“haba Hameed mai yasa zaka min haka dan Allah karka tafi ka barni”

 

shiko ko jinta baya yi, da taga abin bana ƙare bane ta fita ɗakin da gudu, parlour ta shiga tana,

“Alhj ka taimake ni Hameed, Hameed kar ya mutu ya barni”

Papa yace, “Hameed kuma mai yasa mai shi”?

Kawun Hameed yace, “ai ba tambaya zamu tsaya yi ba muje mu gani”

Fita sukaiyi dukan su, ɗakin Hameed ɗin suka nufa, yanda yake haka yake hannun shi dafe da ƙirjin shi.

 

cikin hanzari Alhji Abbas yace, “Alhji kama shi mu sashi a mota”

kama shi sukaiyi suka Kai shi mota sannan suka shiga, Umma hijab ɗinta kawai ta ɗauko a ɗaki sannan suka wuce hospital……….

****

Yana bacci yaji wayan shi na ringing, baƙuwar number ce shiyasa ya mayar da wayan ya ajiye, Kiran aka ƙara yi nan ma be ɗauka ba sai da akai Kira uku sannan ya ɗauka cikin Jin haushi yace, “waye”

Daga can tace, “haba Yazeed yanzu number nawa ma baka da ita ai Daman nasan ba Kira na zakayi ba shiyasa na Kira ka”

Sai yanzu ya gane ashe Yusura ce yace “oh sorry Yusura ya kike”

 

Tace, “hmmmm my Yazeed sonka ya hanani bacci ko da yaushe fuskanka ita ce farin ciki na pls my Yazeed ka yarda ka aure Ni daga baya ka soni”

ta ƙarashe magana cikin wani irin Kashe murya.

Ji yayi duk Yanayin shi ya sauya sannan yace, “uhhmmn to zanyi shawara”

Tace, “kaman yaushe zan ƙara Kiran ka inji”

Yace, “ki bari in nayi zan Kira ki”

Sai da ta ƙara Kashe murya sannan tace, “to my Yazeed sai ka Kira Ni din Ina nan Ina jiran ka I love you”

 

“Hmmmmmmmm” kawai yace Mata dan duk ta gama canja mai Yanayin shi.

 

yanzu dai ya gama yanke wa kanshi shawaran zai auri Yusura tunda ta riga ta nace mai.

hakan Nan zai aure ta, murmushi yayi yace, “hmmmmm daman Ina son macen da zan aura ta zamo babba saboda itace zata iya ɗaukan nauyi na ba ƙananan yara ba irin su Hameeda……”

 

Suna isa hospital ɗin aka amshe su da sauri, Daman Alhjj Abbas ɗan shi likita ne ya Kira shi yace suna hanya suna zuwa kuwa aka amshi shi da sauri aka Kai shi wani D’aki.

 

sosai suke bashi taimakon gaggawa sakamakon ciwan zuciyar shi dake niyar tashi, Allah ya taimaka an kawo shi da wuri da sai dai wani ba shi ba..

Umma ba abinda take sai kuka Dan shi kaɗe Allah ya Bata gashi yanzu tana niyyar rasa shi, papa yace haba,

“Hajiya addu’a zaki mai ba wannan kukan naki ba”

Hawaye ta share sannan tace, “haba Alhji ka banni nayi kuka na baka ganin halin da Hameed ke ciki ne”

Yace, “to addu’a ki ya ke buƙata ba kuka ba”

Dr ne ya fito, da sauri kawun Hamed ya tare shi yace ,

“Dr baku ce mana komai ba”

Yace “ku biyo ni office”

Office ɗin suka shiga, kujera ya nuna musu su zauna sannan yace,

“wato Alhji Allah ya taimaka kunyi gaggawan kawo shi sannan kuma ciwan shi Yana ne man tashi to yanxu dai Allah yasa munyi maganin abun sannan kuma a kiyaye ɓata mai rai dalilin wannan ciwan nasu nasan farin ciki da walwala da fatan za’a kiyaye”

Papa yace, “insha’Allah za’a kiyaye za’a iya ganin shi yanzu?”

Dr yace, “gaskiya ba yanzu ba, saboda ya Samu bacci yanzu sai zuwa anjima zaku ganshi”

Kawun Hameed yace, “to shikenan mun gode Dr Bari mu je waje kafin ya tashi”

 

Dr yace, “to Allah ya bashi lfy”

suka amsa da ameen sannan suka fito daga office ɗin……

****

Zaune take a kan kujeran parlour su abin duniya ya isheta, musamman in ta tuna auran nan sai taji gaban ta ya faɗi, tinanin irin zaman da zasuyi da Ya Yazeed kawai take, wasu hawayen baƙin ciki ne ya zubo mata, duk son da take ma Hameed ya tashi a banza kenan.

 

innalillahi ya zatayi da ranta, dafa ta taji anyi, dubawa tayi taga Momy ce zaune a kujeran ta dafa kafad’ar ta tace,

“Hameeda mai yasa baza ki ma kanki faɗa ba, kinsan dai auran nan dole ne to mai nasa kanki damuwa, to tun wuri kima kanki fad’a Dan Wallahi Ni ba irin iyayan nan bane musu goyawa y’ayan su bayan rashin gaskiya, dube ki yanda kika ramai kaman bake ba, baki cin abincin baki komai Wallahi zan Bata miki rai”

Kuka Hameeda ta ƙara fashewa da shi sannan tace, ” haba Momy da wanne zanji da wannan auran ko da faɗan da kike min, Ni Wallahi ma gwara na mutu na huta”

ta ƙarashe zance cikin matsanacin kuka.

Dariya Momy tayi sannan tace, “to Hameeda ki mutu mana ai lokacin ki ne yayi in kin mutun”

Tace, “Wallahi Momy na mutu sai kinfi kowa kuka”

Momy tace, “Ni ba kukan da zanyi, tashi ki wuce kitchen kiyi abinda zaki ci jibi duk yanda kika ramai”

Hameeda tace “to” tare da Mik’ewa…….

***
Karfe 7:30 dai dai Hameed ya farka cikin wani matsanencin kuka Yana cewa, ” Hameeda Allah yasa mafarki nakeyi ba da gaske rasa ki zanyi ba”

Umma dake zaune a kujeran ɗakin tayi saurin tashi ta matso inda yake tace
Hamed, “ka tashi”?

Yace, “Umma dan Allah kice min mafarki nakeyi na rasa Hameeda Wallahi nima zaki rasa Ni”

Umma ta share hawaye sannan tace,

“Hameed kayi haƙuri ka rasa Hameeda Allah ya cire maka soyayyar ta a zuciyar ka, kasa ma ranka haƙuri kasan ba lfy gare ka ba”

riƙe hannunta yayi sannan yace, “Umma baki San zafin da zuciyata take bane, Amma insha Allah zan cire ta a zuciyata nasan da wuya hakan Amma zan kok’arta”

Dr ne ya shigo D’aki sannan ya ƙara duba shi yace , “bawata matsala zuwa gobe ma zai iya sallamar shi”

tea Umma ta haɗa mai sannan ta zauna tana bashi har ya shanye, Hanifa ce ta shigo D’aki hannun ta rik’e da basket ɗin abinci fuskan ta ba walwala sosai…

Tace,”Sannu Umma ya mai jiki”?

Umma tace, “Hanifa kece sai da nace miki karki zo gobe zamu dawo Amma kika zo”

 

muryanta a sanyaye tace, ” Umma abinci fa nayi muku kuma nasan bakici komai ba”

Umma tace,”to Allah ya miki albarka”

Hanifa tace, “Ya Hameed ya jiki”?

“da sauƙi” kawai yace ya juya da kanshi,
Tace, “Allah ya ƙara sauƙi”

haka sukai ta firan su da Umma shidai bece musu ƙala ba, har 10:00pm tayi Umma tace Hanifa ta tashi ta tafi gida gobe ma ba sai ta zo ba tinda goben zasu dawo, Hanifa tayi musu sallama sannan ta tafi…….

Washe gari Ya Yazeed ne cikin Shirin shi na asibiti ya fito part ɗin su Meme ya shiga dan yin breakfast, yana shiga Dining ya wuce anan ya Samu Big Daddy da Meme Suma suna break ɗin.

 

gaishe su yayi sannan ya zauna ita dai Meme ciki ciki ta amsa.

Big Daddy yace, “lfy dai ke da ɗan gidan naki”

Sai da ta ƙara haɗa rai sannan tace, “bar wannan shashashan yaron”

Big Daddy yace, “a dai mai haƙuri” Yana faɗa ne Yana dariya dan yasan bata fushi da ɗan nata.

Shidai Ya Yazeed break ɗinshi kawai yake dan sai da ya gama tukun yace,

“Meme na a min afuwa Ni zan huce”

Tace, “a dawo lfy”

Big Daddy ma yace, “sai ka dawo my son”

yace, ” Allah yasa”

sannan ya fito cikin sauri Dan yayi Lette..

Yana zuwa asbitin office ɗin shi ya wuce Yana buɗe ƙofan kenan yaji an rungumo shi ta baya…………

 

 

 

 

 

*comment*
*share*

 

 

 

 

*AUNTY* *BABY* *ce*✍ 🥰
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺
🌺

 

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA*💅🏻

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

🎐 “`G•W•A“`🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

 

 

*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏻

 

 

_Wayyo dadi 💃💃💃💃💃💃 a gaskiya naji dadin comment din ku na kwana kin nan, comment din ku na qara zuga Ni Ina qara suburbud’a muku typing🥰🥰🥰🥰_

 

 

*Dedicated to my mother ❤️ Allah ya bar min ke uwata*😍😍😍

 

*Bismillahir rahmanir rahim*

 

*page* 3⃣0⃣to3⃣1⃣

 

 

Juyowa yayi a fusace yaga wacece tamai wannan rungumar, yusura ce sanye cikin wani riga da wando pink da blue tayi kyau sosai, sai murmushi take zuba mai

Finciketa jikin shi yayi sannan ya ture ta, “wai baki da hankali ne yusura mai zaki wani rungumai Ni”

Tace “haba Yazeed menene dan na rungumai ka Kai fa mijina ne to ai ba wani Abu”. Ta fad’a tana wani k’ara shige mai jiki.

Janye ta yayi sannan yace .”A ganin ki ba, wai mai ma ya kawo ki office d’ina da safen nan”?

“Hmmmmm my Yazeed da tinanin ka na k’wana shiyasa kawai nace Bari in zo in ganka”.

Wucewa yayi daga in da take, ya zauna a kujeran shi sannan yace “ki zauna mana dan Ina da abinyi yanxu magana kad’an zamuyi ki tafi”.

Zaunawa tayi a gujeran da ke kallon shi tace “Ina Jin ka Amma kasan dai nima ina da abinda zanyi na zo wurin ka ko”? .

Yace “to Ni nace Yusura ki zo ko kuma ki kikai niyar zuwa”.

“Ummmmmmm Wallahi my Yazeed kana burgeni shiyasa kullum sonka ma yake k’ara shiga Raina”.

 

Yace “hunnmmm Yusura Ina son ki San wani Abu bazan tab’a auran ki kina irin wannan shigan ba dube ki fa dan Allah”.

Kallon jikin ta tayi sama da kasa ita dai Bata ga wani abun kushewa a jikin ta ba saima kyau da take ganin tayi, tace “haba my Yazeed Dan Kai fa nayi wannan kwailiyan Amma baka yaba ba Amma kace wai in daina gaskiya Ni Aa”

Daure fuska yayi sannan yace “to shikenan taki iya tafiya dan Ina da patient a gaba na”

“To my Yazeed yaushe zan dawo kasan dai kace min zakayi shawara kuma baka ce min komai ba”?

Dafe kan shi yayi a zuciyar shi yace wannan yarinyar ta iya naci. Yace “duk sanda kike da lkc Amma karki qara zuwan min office da safe dan lkc nake duba patient”.

“To my Yazeed na tafi”.

“To ” kawai yace Mata ya cigaba da abinda yake yi Dan ta damai shi da surutun ta shi kuma ba jure magana yake ba…..

 

Hamed kon ya tashi jikin alhmdllh shiyasa da safe aka sallamai su suka wuce gida, Amma in ya tina wai Hameeda aure za’a Mata bada shi ba sai yaji k’irjin shi ya buga,

Yanxu ma Yana k’wance ne a doguwar kujeran parlour su yana tunanin k’arshen maganar papa da yace Hanifa zai aura mai, hmmmm yanxu shi zaiyi rayuwar aure da Hanifa, yasan dai Hanifa akwai nutsuwa da kamun Kai kuma kyau dinma dai tana da shi Amma shi a ganin shi ba macen da takai Hameeda, haka dai yake ta tinani har lokacin sallahr Azahar yayi ya tashi ya fita, Yana dawowa daga masallaci yaji wayan shi na ringing duba wa yayi yaga waye, Hameeda dum dum dum k’irjin shi yace da kaman bazai d’auka ba sai kuma ya d’auka.

Hameeda muryan ta na rawa tace “hello”

Sai da ya Dan ciza labb’an shi sannan yace “hello”

Hameeda ta fashe da kuka, tama kasa magana sai kukan kawai da take yi

Yace “ayya Hameeda kiyi hak’uri ki daina kuka Ni nasan ba da San ranki bane hakan ya faru Amma Dan Allah kiyi shuru Allah na tare damu pls Hameedan Hamed”

“Cikin shashek’ar kuka tace my Hamed yanxu kana nufin kaji ance za’a min aure my Hamed mutuwa zanyi”

“Haba Hameeda kiyiwa iyayan ki biy’aya haka k’addarar mu take Amma Allah yasa muci wannan jarabawar pls karki sa kanki a damuwa kinji Hameedan Hamed” ya k’ara she zance cikin zulaya Dan dai karta gane Yana cikin damuwa

“To my Hamed insha Allah zan daina damuwa Amma kuma na maka alkawari Ni taka ce, ba wani namijin da ya isa ya mallake Ni in ba Kai ba, Kai d’aya namawa ta najin jiki na”

“Hmmmmmmmmm” kawai Hamed yace dan yasan wannan magana Bata bazai tab’a yiwuwa ba Dan ba namijin da zai aura Hameeda yace ya tsaya yana kallon.

“My Hamed ya naji kayi shuru”

Yace “Aa Hameeda ba shuru nayi ba sai anjima Dan zan shiga gida yanxu”

Tace “to sai anjima” wani irin dadi taji dan Bata Sha Hamed zai fahince ta ba wani irin son shi na qara shaga Mata zuciya…

 

****************

Bayan wata d’aya

 

 

_Kuyi hkr yau ban samu Daman yi muku typing da yawa ba kunsan ance jiki da jini_🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀

 

I love you all my fan’s😍😍😍🥰

 

 

 

*comment*
*share*

 

 

 

Aunty Baby✍🏻

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺🌺🌺🌺
🌺

 

💅🏻 *BABU SHI A ZUCIYATA* 💅🏻

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
{ _Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira._ }

🎐 “`G•W•A“`🎐
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

 

 

*Story & Written*
*By*
*AUNTY BABY*✍🏻

 

 

*Bismillahir rahmanir rahim*

 

 

*page* 3⃣2⃣to3⃣3⃣

 

Shirye- shiryan biki ake sosai an fito da anko kala-kala sai Wanda ka zab’a, gyara kuwa su Hameeda nashan shi duk da dai ita Hameeda ba wani tsayawa take ba sai Momy ta Mata Jan ido tukun na, aunty amarya ummin Fadila kenan ta d’auko musu wata mai gyaran jiki ‘Yar maiduguri sosai take gyara su, Nusaiba kon uwarta ta Hana ta zuwa, Fadila da Hameeda kawai ake ma wa, Hameeda ta qara kyau sosai tayi fari Amma ta rame sosai bata cin abincin in ba an titseyeta ba….

 

Yanxu haka suna d’akin da ake gyara su Fadila ake shafawa wani had’in magana na fata Hameeda kon na zaune tana karanta wani novel mai suna *SAUDALA* na Neat Lady dariya take sosai, Fadila tace

“Wai Hameeda mai kike wa dariya ni raban da in ga kina dariya kaman haka har na manta”

Dariya Hameeda ta k’ara yi sannan tace “Wallahi buk din nan namin dadi saudala tana wulakanci ta”.

Fadila tace “tab Ni karatun novel bawai ya damai ni bane Amma zan fara ko dan kula da my yaya Areef”.

Murmushi mai musu gyara tayi sannan tace.
“Ai kuwa kin burgeni Wallahi gwara ki kula da mijin ki kafin k’adangarun barike su kwace miki shi, Yan matan yanxu basu san kula da miji ba su dai burin su kawai a Sha magani su burge miji da dare Amma basu San yanda za su kula da tsafta girki kwailiya iya daukan wanka iya magana iya tafiya ke abubuwa da yawa Wanda ba sai kasha maganin Mata, ba baka San daga Ina aka yi shi ba kai dai kawai ka dauka kasha wai da duk ka burge miji kuma hakan bazai hana ya wulakanta ka ba, Ina mai baku shawara Kar ku biye wa Yan matan yanxu na shaye- shayan maganin Mata, ko Kai da kanka zaka iya had’a abinda zai amfane ki Wanda bazai cutar da Kai ba irin su, dabino, aya, ko kayan fruit suna gyara jiki da duk abinda kike so”.

Kallon ta Hameeda tayi sannan “tace hmmmmmm aunty Rawan kenan ke yanxu duk Ina kika San wa’innan abubuwan Naga dai baki dad’e da aure ba”? .

Tace “ummmmh Hameeda zauna ganin ruwa kwado ya miki k’afa ai yanxu dole ka kula da kanka saboda ‘yan Mata yanxu bin maza suke ba maza ne ke binsu ba, dan haka ku dage wajan gyara jikin ku d’akunan ku girki shine adon mace duk mace da Bata iya girki da kwaliya ba to Wallahi sunan ta sorry”.

Murmushi Fadila tayi sannan tace “Wallahi aunty Rawan mijin ki yayi dace gashi kin iya gyaran jiki kin iya kwalliya kin iya girki to ai kin more” .

Tace “keko ba dole in iya ba ko so kike ai min abunda Mata suka tsana”?.

 

Dariya sukai dukan su, haka dai ta cigaba da koya musu abubuwa kala-kala ita dai Hameeda ba d’auka take ba dan tace ba Wanda zata je tana ma gyara, dan ita Hamed kawai ta tana darwa kan ta………

******************

Maman Nusaiba ce zaune gidan Haj zuwaira suna magana yanda zasu tsara bikin su dan a cewar su Nusaiba sai tafi kowa had’uwa a gurin bikin, Haj zuwaira tace

“Haba Haj yanxu shi Nabil din yake Bata kud’in to Wallahi tun wuri gwara mu datse mai baki sai yanda tayi dashi in ba haka ba nan gama mun shiga uku, dan zamu siyar da akuya ne da dawo tana ci mana danga”

Tace “Hmmmmmm ke dai bari Haj zuwaira wannan yaro daga ganin shi bashi da kirki, wai cewa nayi tace ya bata ko dubu d’ari biyu ne a k’ara a cikin shagalin bikin na Amma ya k’i to Wallahi ta bakin nake dole mu d’aure mai baki in ba haka ba zafi karfin mu wata ran”

 

Haj zuwaira tace “haba Haj ai qarki damu nice ba Haj zuwaira, dole ma ya sakin Mata hannu”

Haka dai suke ta kule kuken su……..

***********

Yanxu baki sauran sati biyu,kuma yau ne suka gama exam din su gaba daya, yaya Areef ya had’a musu party a cikin gida suke abin su k’awayan su gaba d’aya sun zo ana ta cashewa, fadila duk ta gaya musu bikin su sauran sati biyu, akwai suna ta murna zasu Sha biki haka aka tashi cikin farin ciki…….

Washe gari

Big Daddy duk ya tara su yace Areef zai zauna a gidan shi dake malali kaduna, shi kuma Yaya Yazeed Abbu ya siyan mai wani gida a GRA, sosai sukai murna sanna sukayi godiya, yaya Areef ya mik’awa yaya Yazeed IV yace gashi Nan ya d’ibar wa Hameeda, shikuma zai ba Nusaiba da Fadila, yaya Yazeed yace ai da biyi bama yasa ayi, yay Areef yace kawai yace a barshi tinda yayi, iyayan su suka sa musu albarka sannan yay Yazeed yace abokanan shi sun had’a dinner, kuma harda iyaye za’a je, suka ce to ba matsala Allah ya kaimu……..

 

 

***********

 

Kaya sosai a haka had’a na amare, kuma duk big Daddy ne yayi Hameeda akwatuna goma Sha biyu ita ma Fadila haka sai dai kayan cikin da ya banbanta dan Meme ba qaramin kudi ta narka a kayan Hameeda ba, ita ma Nusaiba yau za’a kawo nata shiyasa gidan ya tashi da shirye- shirye…….

 

Karfe 4:23 motan iyayan Nabil suka zo kawo kaya, part din haj jadda suka Kai Dan nasu Hameeda ma duk Yana can, akwatuna ne gwada takwas sai kit daya kayan sunyi ba qarya, Amma ita uwar amarya sai ta buge da zage-zage wai anyi San Kai su, su Hameeda an musu goma Sha biyu ita kuma yarta an kawo Mata takwas, haka dai tayi ta fad’an ta…….

 

*************
Yanxu an shiga satin biki, in gaka su Hameeda baza ka iya gane su ba sunyi kyau, barin ma hameeda kaman ka sace ta ka gudu, su Fadila duk sau shirya abun da za’a yi, ranar laraba za’a fara shakali za’a fara da walima ne sai ranar alhamis ayi Arab night sai ranar juma’at ayi kamu ranar asabar kuma daurin aure da dinner,

 

Hameeda ce kwance tana tinanin yanxu fa auran nan za’a yi da gaske, Fadila da Zarah ne suka katse Mata tinanin da d’aka Mata duka Zarah tace.

“Waya gaya miki amarya na bacci ki tashi yanxu aunty Rawan zata xo ta miki dilka”

Mtswwwwww taja tsaki sannan tace “haka kurin Ina bacci ba mai dadi Kun xo Kun tashe ni”

Fadila tace “lallai ma yariyar Nan ana miki gyara kina fushi Wallahi wata ran zaki ga amfanin shi”

“Wallahi bazan taba ganin amfanin shi ba tinda ba Hamed nayiwa ba”

Zarah tace”oho miki dai”

Nusaiba kon ba abunda uwarta ke Bata sai maganin Mata Dan tace shine gyara mai kyau ba irin Wanda ake wa su Hameeda ba, akwai tayi wani himmm da ita ta qara ciki kaman ba ita ba……

 

 

Hamed kon har yanxu Yana son cire Hameeda a rain shi Amma ya qasa, Amma dai yanxu Yana Dan sakewa da Hanifa dan umma ta Mata bayani komai kuma ita hanifan tace ta yarda zata aure shi murna kam sosai umma tayi Dan Bata Sha zata yarda ba (Ni kon nace Daman tana son abunta🤣) shiyasa yanxu tana kula da shi sosai, yanxu bikin su ma sauran 1month haka daman kawun Hamed wata daya da rabi yasa………

 

 

Yau ta kama laraba kuma yau ake musu lalle, karfe 4 za’a yi waliman shiyasa aka fara musu da wuri, an gamawa Fadila da Nusaiba sauran Hameeda ita ma an kusa gama mata, bakin lalle ne da ja aka musu yayi masifar kyau da yake sun iya masu yin,

 

Su Momy kam ana cikin jama’a Dan Yan uwanta sun zo su aunty Hiba aunty Yasmeen aunty Sakinat duk sun zo…

Ita ma Meme part dinna nata ba masaka sinke Yan uwanta kowa ya zo tinda Bata tab’a auran wa ba sai akan Yazeed kuma shi daya Ni ba wani shiyasa mutane…..

 

Maman Nusaiba ma dai hakan take yaran ta duk sun zo su aunty Nafisat da aunty shamsiya…

 

Aunty Amarya ma haka take, gida dai ya cika tam,
part din Haj jadda ma dai shima mutanan ne Yan Zaria duka……

 

Ana gamawa Hameeda aunty Rawan ta zo ta tafi da su D’aki ta qara turare musu k’unshin sai kamshi suke zubawa, ko ruwan wankan da za suyi ita ke hada musu da turarukan kamshi, yanxu ma haka ita da hada musu dan karfe 4 ta kusa an fara cewa suyi sauri, suna fitowa dakan wanka sai da ta qara musu wani turaran sannan ta musu kwaliya, wasu dugayan riguna ne da Aunty amarya ta siyo musu suka sa rigan Hameeda pink ce sai dan ratsin blue daga sama ta matse sai kuma kasa aka sake ta ta zauna daram a jikin ta sai dan qaramin gyalen rigan da shi aka yafa mata, ita kuma Fadila fari ne sai ratsin black iri daya ce dai da ta Hameeda kala ne kawai suka banbanta, sunyi matukar kyau Dan sun Sha make-up, aunty amarya ce ta shigo D’aki sannan tace.

“Wai ku har yanxu baku gama Shirin bane kunsan fa karfe 4 aka ce za’a waliman Nan Amma Kun tsaya sai faman nuku-nuku kuke”

“Aunty amarya mun gama fa cewar” Hameeda

“To ku fito mu tafi”

Takalman su suka sa shima dai irin rigan ne haka suka fito, a cikin gidan za’a yi waliman Dan anyi decoration din gidan yayi kyau sai fararan kujeru da aka shirya……

 

K’wance yake abin shi zakace na angon kwana biyu da zasu su ba, wayan shine yayi ringing Yana cikin bacci ya d’auka ba tare da sani waye ba, yace “hello”

Daga can yace “Amma Kai dan i’ska ne daga ji ma bacci kake sai kace ba ango ba wani irin bacci kuma yanxu”

Yaya Yazeed yace “safwan yane Wallahi bacci ne a ido na kasan jiya banyi ba ina asbiti duba patient”

Safwan yace “lallai ne ango to Wallahi d’azun nan Yusura ta zo baka nan naso na gaya Mata bikin ka Amma na fasa”

Yace “Ni Dan Allah bar wannan mgn yanxu dai menene ka kira ni”?

Safwan yace “daman kan mgn abokan mu ne an manta ba’a sa karfe nawa za’a yi dinner Nan ba a iv”

Mtswwwwww yaja tsaki sannan yace “Daman akan mgn Nan zaka tashe ni to ka Bari sai na fito anjima mayi mgn” ya fada tare da Kashe wayan ko tsayan amsan shi beyi ba.

Safwan yace “Allah ya shirye ka Yazeed”

 

An fara walima sosai malaman ke wa’azi aka aure, jikin su duk yayi sanyi a haka har aka tashi a gun sannan suka koma part din Aunty amarya, ita Daman Nusaiba Bata je ba tana can tare da k’awayan ta suna party.

Washe gari suka tapi salon aka musu gyaran Kai karfe biyu suka dawo, aka fara Shirin kamu kuma gashi harda angwaye za’a yi. Amaran gaba daya lifaya za su sa su kuma angwaye suit zasu sa, shima kamun ana cikin gida za’a yi Amma an canja Yana yin decoration din.

Su Nabil ma sun shirya zasu tahu, yay Areef shima yay Yazeed ne kawai sai yanxu da su safwan suka zo ya shirya.

Anyi wajan zaman amarya da ango duka su ukun sannan na mutane, su Hameeda an musu kwaliyan su an yafa musu lifaya ga gyaran kan da aka musu sai qara feshe su da turarukan ake , Kai fadab kywun da sukayi Bata lkc ne bazan iya musarta muku ba kawai ku aiyana a xuciyan ku, Nusaiba ma irin ta aka Mata tayi kyau ita ma.

Motar su Nabil na qarasowa Suma su yay Areef suka zo yay Yazeed ma shima suka fito, gaskiya angwaye sunyi kyau iya kyau.

Aunty Yasmeen qarwan Momy tace a Bari amaran su zo sai su huce gun zaman su tare, haka kon aka yi su Fadila na fito yay Areef yace ya reko hannun ta Yana takar Mata murmushin.

Shima Nabil hakan nan ya je ya riko tashi Nusaiba.

Yay Yazeed kuwa……………

 

 

To fa ko mai yay Yazeed zaiyi 🤷‍♀

 

 

*comment*
*share*

 

 

*Aunty* *baby* ✍🏻

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *