Tsaye yake gaban durowan da yike adana neck ties ɗinsa ,gasunan jere akwaku akwaku sunfi kala ɗari,cikin zafin nama ya miƙa hannu ya zaro wanda yafi dacewa da kayansa ,ya ɗaure wuyarsa ya tsaya yina kallon kansa a madubi yina ma kansa wanka da turare designers ,Ni kuwa ba wankuwan da yayi ya tafi dani ba A’ah tsayinsa da kyawunsa su suka fi tsoratani ,zabgegen gaskene ƙiran samudawa ,wanda ba’a saba ganin irinsu a jinsin Hausa / Fulani ba ,kana kallon gaɓɓansa dukda hankali kwance yake ,zaka tabbatarwa zuciyarka ɗan atilaye ne,saboda ya horar da jikinsa da tirenin kamar ɗan dambe,cikinsa a shafe yake tamkar loman tuwo baya shiga ,amma yina da manya manyan damatsa, duk da kasancewarsa ba mai ƙiba ba amma sadaukin gaskene very very tall gentle man,kyawunsa kuwa mai gusar da hankali ne yafi dacewa da ka kirasa Balarabe ba bahaushe ba.
Ɗaukar brief case ɗin sa yayi na zuwa aiki ya gangaro ta matakalan benen gidan sai ga wata kyakyawar budurwa cikin crazy kayan barci da basu ɓoye komai na suran jikinta ba,da gudu tazo ta runfacesa ta fashe da kuka “Na tuba Karka horani da rashinka bazan jureba” kallon ta yayi fuskarsa a tanke kamar na boss “Bazan iya having sex dake ba for life,now gargaɗi ɗaya zan maki kar in dawo inga tsinke mallakinki a gidan nan…bana fatar zaluntar ki don niɗin mai gaskiya ne ,don haka in na fita kije ɗaki na uku bene hawa na Tara , securityn ɗakin zai kasance a buɗe,akwai akwatin dololi ki ɗebi duk yanda kike jin zai isheki and go plz” yina rufe baki ya wuce ta bai damu da gunjin kukan da takeyi ba kuma,sake biyosa tayi da gudu saidai nunata kawai yayi da yatsa taja cakk ta tsaya,har ya wuce bata iya motsawa ba.
Yina fitowa ƙofar falon jirgine ke tsaye an Rubuta ADNAN 3.
Pilot ɗin jirgin ,sojan samane riƙe da bindiga ,yina ganin ya fito yayi maza ya karɓi brief case ɗin hannunsa yina gaishesa ,bai magana ba ya miƙa masa hannu sukayi musabiha ya shige jirgin ,filfilan helicopter ta waina ta lula cikin gajimare.🚁
Mohammadul_Adnan kenan,Shahararren matuƙin jirgi na ƙasa da ƙasa ,sa’annan kuma shugaban kamfanin ƙera motoci da ƙananun helicopter na A&D.
Matashin billoniya mai kimanin darajar kuɗi Dala tiriliyon bakwai .
Uni lag.
Female hostel
Room 4
“Ifty 8 on dot” matashiyar da ke zaune gaban Laptop a falon ta ƙwalla kiran iftyn tana kallon wani ƙofa dake hagu da inda take zaune .
“Wayyo gani nan sisto…” zazzaƙar murya ta bata amsa daga ciki.kafin ta falfalo da gudu rungume da file ɗin takardu mai tsananin kyau sai wayoyin hannunta guda biyu duk kamfanin iPhone Wanda kowani ɗaya zai kai kuɗi 700k
Zuwa gefen kujeran da Aalima take tayi ta ɗan haɗe gefe da gefen kumatunsu ta sakin mata sautin kiss
“Umuhhh…I’m going…”(Na tafi) Ta ƙare maganar tana fashewa da dariya har saida kyawawan dimple dinta suka lolloɓa a gefen kuncinta .
Subhanallh! tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya ƙera kyakyawar halitta kamar Iftihal_khair.
Kyakyawar dirarriyar bafullatana ce mai ɗauke da kala mai tsada wato chocolate colour , sai ƙyalƙyali fatar takeyi irin na hutu da jin daɗi ,saye cikin doguwar riga Maroon mai azaban kyau yasha adon duwatsu baƙaƙe don haka cover ɗin takalminta ,agogon iWatch ɗin ta suka kasance baƙaƙe.
Aalima jinjina mata kai tayi “Ok ga car key ɗina ki je a ciki”
Ƙara daka tsalle tayi ta rungumeta “awwwwn kina sona fa da yawa li_li… Bye”
Ta ɗauki makullin motar a kan table ɗin karatunsu ta fice da sauri .
A gaban premises ɗin Hostel ɗin motocin ɗalibai ne reras kyawawan mata masu lekcan safe sai wucewa suke a kafa wanda ajujuwansu ke nesa da Hostel suna zaro motarsu a inda suka saba adanawa suna ficewa .
Iftihal ma haka tabi sahun sauran ɗaliban ta je ƙarƙashin wata bishiyar dalbejiya ta fiddo motar Aalima ɗin Marcedes C320 baƙa wuluk tayi masa key ta fice da gudun gaske saboda har 8.15 am tayi
Tazo giftawa ta wajen department ɗin su wasu rukunin ƴan mata su hudu na tsaye da lekcaransu Sir Dauda ,suna ganin ta dumfarosu suka bushe da dariya suna nuna motar da take ciki
“Malam gafa mutuniyarka ko ina zata je oho ” zarrr yabi motar da ido har saida yayi nasarar lalubo ganinta ta saukakken glass ɗin motar .
Sosai Iftihal ta tsargu don tasan gang ɗin su Fari’at basu da Alkhairi ,bare taji labarin jiya malam Dauda yazo kiranta a aji bataje ba,don haka da sauri ta ƙara ma motar wuta fuuuu ta wuce.
Wani sassanyar Ajiyar zuciyar sir. Dauda ya ajiye “Gaskiya yau tafi ko yaushe haɗuwa “
“Mtseww malam duk kayan Aro ne fa ,wallahi daidai da wayoyin da kake ganin tana fafa dasu na Aalima ce ka ganta ƴar matsiyata ne na gaske don inajin ana binta bashin kudin makaranta na shekaru uku kenan…yawwa misali baka ganta baƙa ba ? Ka na ganin ƴaƴan masu kudi bakake ? Sai ƴaƴan wahalalu masu dambe da kwanon tuwo”
Aikuwa suka doka shewa suka ƙyaƙyace da dariya
Dafe baki malam Dauda yayi “Aihooo ai na aza ƴar masu dashi ne ,ina binta tana Gara Ni ,Kinga da ta kwantar da hankali da ko kudin makarantar ne ban biya mata ba…”?
Tsaki Salma tayi “Mtseww baka dandanƙara mata carry over bane,Dama naga kanta na fizga ana kiranta da brain box tana yinma mutane kallon hadarin kaji …amma tana ganin ruwan carry over zata daina bin ta rich kids I bet u”
Tunda Ifty ta isa mahaɗan Victoria Island ba abunda kake iya hange sai Dogon ginin gilas da gilas ɗin A&D group of companies ,shi kaɗai kake hangowa wanda tsayinsa ya shiga har cikin jido, benene mai nisan gaske an lulluɓeshi gabaɗaya da gilasai masu ruwan sararin samaniya.
A gaban kamfanin ta faka motarta da taga ya zama tsohon yayi cikin lafta laftan motocin da suke wajen. Fitowa tayi hannunta riƙe da file tana ƙarewa dogon ginin kallo amma ta kasa ƙirga benen hawa nawane ma,sosai ta zama ƴar ƙauye makuwa yina neman kamata,aro mazantaka tayi ta daidaita natsuwarta sannan ta iya shiga Companyn ,tasha tambayoyi da bincike kafin a barta ta isa floor ɗin da ofishin ADNAN yake saida aka amshe komai na hannunta daga ita sai jotter da waya guda ɗaya,sannan ta sadu da secrataries ɗin sa su biyu
“Kince shine ya Baki verbal appointment yace kizo yau ko?” jinjina masu kai tayi saboda tasan tana buɗe baki za’a gane ƙarya tayi,rubutu sukayi a jikin computocin gabansu suka tura masa saƙon zuwan Ifty,da cewan da tayi shi yace tazo
Mamakine ya kamasa don shi bai baiwa kowacce mace appointment din ganawa dashi yau ba. Da har zaice a koreta Kuma sai yace a barta ta shigo
Na’uran tantance mutum aka ɗauko aka kara mata a jiki ,da sauri ta daga hannunta sama baiyi ƙara ba wannan ya tabbatar masu da bata ƙunso komai na sharri ba don haka ,PA ɗinsa wacce ta kasance baturiya ta tasa ta har gaban office ɗin sa.
Office ne sunan office ne amma ba’a yi shi da bulo koda guda ɗaya ba,zallan frame work ne na gilasai a ɓangarorin ginin guda huɗu wanda na ciki yake ganin komai dake gudana amma shi ba’a ganinsa .
Ifty ana bata izinin shiga kawai ta sa ƙarfi ma ƙofar da nufin ta tura ta shiga,saidai naurane yayi magana da turanci wanda ya sata firgita ,kawai ƙofar ya buɗe siyyyy .kamar wanda aka hankaɗo sai gata kif ta kife a ƙasa.
Adnan dake tsaye jikin window yina kallon yanda gajimare ke gudu a sararin samaniya har yana ɗan dakan gilas ɗin windown sa wani zubin ,hannunsa riƙe da cup ɗin coffee ,bazato yaji faɗin wani abu mai nauyi gamida ƙarar mace
Cikin karsashi ya waigo ganin ta watse a ƙasa yasa yayi saurin zuwa ya kamo hannunta ya miƙar da ita tsaye ,da wani kalar murya na kamilallun maza mai kama da raɗa yace mata
“Easy”
Kamar zata nitse don kunya haka tace
“Thank you”
Cak ya tsaida idonsa a kanta,hannunta riƙe a hannunsa ,yina mamakin ƙaryan da ta masa ,shidai tunda yake bai taɓa ganin mai kama da ita ba
“Lafiya? Wacece ke?” yayi magana a dake kamar boss
Ruɗewa tayi kwarjininsa ya cika mata ido baza ta iya masa ƙarya ba kuma,don haka muryarta a take ya fara rawa kamar za tayi kuka
“Ni ɗalibar jarida ce mai sanin makamar aiki nazo ne In maka wasu tambayoyi ”
Kallonta yayi da lumsassun idonsa kamar na mai jin barci,sai kuma ya maza ya sakar mata hannu ,cikin karsashi yace “Sure?” jinjina masa kai tayi ,kawai sai ya juya yayi taku biyu kafin yace “Plz have a seat”
Saurin cin masa tayi gamida daidaita tsawonta dashi cikin hikima tayi,wacce duk tsawonta komawa tayi gajera can ƙasa dashi da kaɗan ta gota cikinsa. Mamaki fal ranta ta samu kujera ta zauna “Nagode yallaɓai”
Kafeta da ido ya sake yi wanda ya sata tsarguwa tayi maza ta sunkuyar dakai tana wasa da ƴan yatsun hannunta da ya gama gauraya da ƙamshinsa
“Ehem”
Ya bata alama da ta soma maganarta .
A ɗarare ta buɗe jottern hannun ta da ta shirya tambayoyin ta ,sannan ta kunna wayarta domin naɗan rahotanni ,sai kuma ta tsaya tana dawara tunda babu biro.
Cak ya miƙe ya dawo gabanta ya manna bayansa da teburinsa ya ciro biro guda daya daga cikin tarin birukan da aka rubuta sunan kamfanin a jiki ya mika mata.
Jikinta ya sake mutuwa ya akayi yasan biro take nema?
Amsa tayi gamida yin masa godiya sannan ta rubuta kwanan wata (Date)
Gyaran murya tayi gamida washe baki
“Ready?” (Ka shirya?”
“what ever you want”(Duk abunda kike so) ya bata amsa hannunsa dogare akan table ɗin yina tsaye a gabanta
“Wannan hiran zanyi da kaine a matsayina na ɗalibar jarida mai sanin makamar aiki dake ƙoƙarin kammala project na degree ɗina daga nan jami'ar uni lag. Ina fatan ...” katseta yayi
“Shiyasa kuka hada baki da ƙawayenki don kece me livern tunkarata amma ba don makaranta ta saki ba ko?” ɗauke wuta tayi ,ya akayi ya sani? Ta tambayi kanta,share maganarsa tayi don Batada amsa sannan taje tambaya na farko
“you’re very young wasu ma suna cewa shekaranka 31 amma ka shiga sahun masu kuɗin duniya...”
Katseta yayi ta hanyar ƙarasa mata abunda takeson faɗi
“Ta yaya nayi nasaran zama multi billoniya?😎”
Buɗe idanuwa tayi cikin mamaki ,sannan ta basa amsa da
“Yes😳”
“Kin tabbata haka kike nufi?”
Jinjina masa kai tayi ,kawai sai ya tashi daga inda yake tsaye ya fara tafiya ,taku uku sannan ya tsaya gamida juya mata baya
“Wannan ya danganta da yanda mutum yayi aiki tuƙurune ”
“Hum kodai kana da sa’a yallaɓai”
Juyowa yayi ya kalleta
“Ban ƙaryata ki ba ,amma ki sani the more you work the more you luck,so karki yaudari kanki da tunanin masu kudi a huce suke samun kudinsu sun fiki jajaircewa ne sai Allah ya taimakesu……..So work hard and be honest that’s my key to success”
“Ok sir, kai ɗin matuƙin jirgi ne abunda ka karanta kenan ,ya akayi kuma ka buɗe kamfanin ƙera motoci ,helikwafta da airplane gadgets? ”
“Ventures”(kasada ce)
Girgiza kai tayi “Ban gane ba”
“Duk wani business da kikaga an farar dashi da kasada,ake farawa to hakan ne ma anan,ko har yanzu baki yarda ba?”
Ɗan Tsurewa tayi ganin kamar yayi fushi “Naga kamar ranka ya ɓaci kayi haƙuri”
“Mutanen da suka Sanni suna kirana mutum mai tsananin kirki da hakuri ”
“me yasa?”
”saboda sun Sanni sosai. To karki expecting dariya a wajena bazaki samu ba I’m very serious man”
“I’m sorry sir….ammmm mutane suna tuhumar ka da rashin aure ko budurwa bakada meye gaskiyar maganar ?are you a GAY?”
Ware Ido yai da sauri “A gay? gay fa kikace? But wow”
Jikinta rawa ya farayi “Don Allah kayi hakuri ba nufina inci fuskarka bane ba kawai tambaya ne”
“Bana luɗu”
“To amma me yasa …”
“Tambayoyin sun fara ginsana ”
“I apologize”
Tsam ya taso har inda take ya jawo kujera gabanta ya zauna har sunajin tashi da saukar numfashin juna
“Ke fa?”
Ware ido tayi “Now time to ask you ,wacece ke?” ta kusa ƙwarewa da miyaun bakinta ,saboda yanda tambayarsa yayi shocking nata. don haka ta fara tari ƙwal ƙwal! Bai ko motsaba ,bare ya nuna ƙosawarsa ,har ta gama. kana yace “Careful”
Gyaran murya tayi “Thank You…”
“Wacece ke?”
“Sorry sir ba wani labari da zakaji me daɗi game dani ,bayan abunda na fada maka a farko ”
“Me yasa Ni kikazo ki ka tambaye ni?”
“Saboda kai ɗin namijin duniya ne ,kowa zai nishadantu da tattaunawarmu dakai in ya saurara,amma nikuwa babu wani abu na cigaba da zaka samu in kaji labarina sai tarin haushi”
Buɗe baki yayi zai magana sai ga D.A ɗin sa ta turo ƙofa
“Excuse me miss ,lokacinki ya ƙare wani zai shigo”
Ɗagowa yayi ya kalli DA ɗin sa,cikin ƙosawa “Ki dakatar da ko wanene sai mun gama”
Ƙanƙan da kai tayi cikin ladabi “Ohk sir”
Da mamaki a fuskar Ifty tace “Me yasa?”
“kin kunna mun fitilar son sanin ko ke wacece,ki saki jiki dani kamar abokai ,ki bani labarin rayuwar ki ta yanda zan fahimta”
“friends? Look at me” (kalleni )
“Yes I am…sunanki ,iyayenki komai na rayuwarki”
Rumtse Ido tayi kawai sai ga hawaye na gudu daga jijiyoyin idonta da gudu taja hanci ta soma ƙoƙarin maida hawayen
“Iftihal_khair Mohammed ,Na fito daga garin Gombe, makaranta ya kawo Ni Lagos da na gama zan koma wajen sick mother ena…” shesheƙa ta soma yi hakan ya dakatar da ita ga ƙara sa maganar ta .
“Sorry ok ? Take heart”
Jan majina tayi kawai ta mike da sauri ta ɗauki jotter ɗin ta zata fita
Bin bayanta yayi da sauri amma ina har ta kai ƙofa ,kuma ƙofar ya buɗe,har ,ta taka ta fita gilass ɗin ya fara ziyyy zai rufe
“Me yaja ra’ayinki wajen interview dani ?Baki bukatar tallafi a harkar karatun ki?”
“Tambaya kayi na baka amsa amma bana buƙatar taimakon kowa sai Allah”
“Ina da ƙarin tambayoyi da zan maki”
“Tambayoyi kuma?” kafin ya bata amsa ƙofar ya rufe da ita a waje don haka ta wuce ta fita kamfanin da sauri .
Akwai murɗaɗɗiyar cakwakiya a kwance ,keep following💃