BARIKI NA FITO
CHAPTER 35
Dariya bariki tayi tare da fad’in, amma ina tsoran irin fushin da Yarima zaiyi, Wlh ban son inga ya shiga wani hali, bazan iyajura ba, ina sonshi da yawa …..
Habib yace Toh fah, yau Ina ganin bariki…. Toh yanzu dai Mai kika yanke….??
Bariki tace abunda kuka fad’amin dashi zanyi aiki, ranan da aka d’aura aurenmu aka kaini ranan zan fad‘ama yarima gaskiya…..
Habib shewa ya saki tare da fad’in Aiko ki tabbatar kin fad‘a mishi tun Kafin ya shiga yaji ya shige zirif kaman bakin gate …..
Bariki duka takai ma habib iya karflnta tare da fad’in rafi ne ba gate ba
Habibya ri’ke wajan da takai Mai duka yana fad’in na shiga uku zata kassarani ….. Amma dai kekam bariki baki da mutunci yanzu ki takarkare iya karflnki ki sakan min wannan uban dukan yanzu inda kin sameni a wajan nono Nafa? Bayan kin San sarai ance a nan rayuwar mace take, salan kije ki kasheni Banyi aure ba naji yanda ayabar nan take ba ……
Bariki tace andai yi Asara Habib yace ke kikaga Asara bani ba
Umman ban’ki tace kudai dingayi a hankali Kun San Gidan mutane, yanzu saisu kaimu gaba….
Habib yace gaskiyanki domin naga matar can d’akln ta kusa daku Tana min wani kallo wanda ban gane ba, inta karamin sai na mata rashin mutunci In cire kaya mu daku Dan ban son iskanci….
Suna cikin haka Yarlma ya kirata tare da fad’in baby come out Ina waje….. Tashi tayi tana fad’in bari inje inga Yarima na.
Habib yace oh kunga salo a gayas…. Fita tayi tana fad‘in kaji dashi …..
Motarshi ta nufa tunda ta fito idonshi ke kanta harta karaso ta bud’e motar ta shigo ciki tare dayin sallama….
Amsawa yayi tare da fad’in my princess na gaji, tunanin driving nakeyl in zan koma Gida ….. Kallonshi tayi tare da fad’in ko in tu’ka ka, in kaika gida?? Yace dakin taimaka min kuwa
Dariya tayi tare da fad’in kamandagaske….
Yace dagaske nake mana Kinga ldan kikaje can saiki zauna kin zama matata babu dawowa….
Hannu tasa tare da rufe fuskanta tana dariya Yari’ma kiran sunanta yayi da Zainab ….. Da sauri ta d’ago ta kalleshi dominjin ya kira sunanta daka gani magana zai Mata Mai muhimmanci…. Wanda yake bukatar natsuwanta
Yace d’azu kina son yimin magana lnajinki yanzu….
Murmushi tayi tare da fad’in Yarima a kullum Ina tsoran fad’a maka cewa ni dakai bamu dace ba, saboda kai ka flto gidan girma ni kuma ba y’ar kowa bace ina tsoran auranka domin gudun wulakanci irin na mas…… Da sauri yasa hannunshi a bakinta ya rufe Mata, tare da fad’in enough. dama dukwannan
nonsense din kike son fad‘amin shine kike d’agamin hankali? ….. Dan tsaki yayi alaman jin Haushi
Ganin ranshi ya baci yayi banza da ita,yasa ta d’ago tana mishi magana Yarima kayi hakuri, ban San zakai fushi ba …..
Katseta yayi da fad’in Zainab ban taba tunanin zaki dinga irin wannan tunanin ba…. And kina ma sona kuwa????…..
Da sauri ta kalleshi tare da fad’in yari’ma baki bazai iya fad’in irin sonda nake maka ba, how l wish in bud’e maka zuciyata Kaga irin sonda take maka ….. Yarima Ina Sonka yanda baka zato dukwanijini dake gudana ajikina yana gudana ne da Sonka I ….. Da sauri tayi shiru ganin yana kallonta….. Jin tayi shuru yasa ya ru’ko mata hannu tare da fad‘in Zainab are you sure akan abunda kika fad’a?? Kal ta d‘aga Mai alaman eh Wani irin murmushi ya saki cikin jin dad’i. tare da fad’ln nace zan baki albishir d’azu right?
Tace eh ‘ Hannunta ya saki tare da fad’in ina goran albishirdin??? Dariya tayi tare da fad’in zan baka in naji albishir din
Dariya yayi tare da fad’in promise? Tace yes I promise….
Yayi murmushi tare da fad’in mai martaba ya amince da maganan aurena dake…. But at first yace in Bari nan gaba tunda ban dad’e dayin aure ba…. Daka baya kuma ban San mai yasa ya canza ra‘ayi ba yace za’a turo gidanku ayi magana d’azu waziri yake fad’amin May be cikin week dinnan a turo ……
Bariki gaba d’aya komai nata ya tsaya ta rasa mai takeji murna take ko akasin haka??? Gaba d‘aya ta kasa ganewa gadai ta nan ne dai….
Ganin tayi shuru yasa Yarima ya kura mata ido tare da fad‘in lafiya kuwa my princess? Kodai you are not happy ne dan za’a turo
Da saurl tace a’a am so much happy tare da sakin murmushi….
Ganin ta saki jiki yasa Yarima jin dad’i sun dad’e suna fira sannan yarima yace Zai tafi tare da bata wani Leda Wanda bata san ko miye a cikl ba….
Amsa tayi tare da fad’in ngd Hancinta yaja tare da fad’in sai munyi magana…..
Tace 0K tare da fita tayi cikin gida,…. Tana shiga habib ya amsa ledan tare da fad‘in Allah yasa Abun ciye ciye ne dan Wlh yunwa nakeji tun safe babu abunda naci….
Su turare ne Arabian perfumes masu shegen kamshi da kud’i a clki…. Habib d’aukan kud’in yayi dubu d’aya d’aya bandir biyu, dubu d’ari biyu kenan ….. Yace Kai yarima akwai kyautar girma….
Uwar barikita Kuwa tace ai gidan sarauta ya flto dole ya dinga kyautar girma…. Domin da suji kunya gwara dukiyarsu ta k’are….
Bariki kallon uwarta ta bariki tayi tare da fad’in mai kuke cine nakeji? Ummanta tace abinci nake dafawa wani zubin kuma kowa ya siya…
Bariki tace toh yanzu tunda nazo inyi sati d’aya nan sai a fara girki kullum, kallon habib tayi tare da fad’in muje muyi cefane mu dawo……
Tsakanin haulat da farhan soyayya ta shiga Sosai tun Haulat na nuna bata so harta yarda domin tana sonshi kuma uwa uba farhan ya iya nuna ma mace kulawa tare da kalamai masu dad’i da kwantarda zuciya …… Sai dai abu d’aya haulat da yake damunta shine tasan dakyar
hjj habiba ta yarda d’anta ya aureta ….. Sai dai haulat din tana ganin in bata yarda ba kaman ta nuna mata rashin adalci, and inma ta yarda ta auri’ d’an nata ya zasu dinga yima juna kallo
Farhan ne zaune a falo shida mahaiflnshi domin yana kasan….
Farhan ya kalli dad dinshi yace dad I have someone dat I wanted to marry ……
Kallonshl mahaifin nashi yayi tare da fad’in farhan aure Bayan baka kammala karatu ba Yace dad Ina final year ne, Ina son a fara magana kafin in Gama….
Dad din nashi ya kalleshi cikin son gudan d’an nashi yace why are u so rush to marry?! Yace dad just
Dad din yace ok but wacece yarinyar and Waye mahaiflnta??
Farhan yace sunanta haulat mum tasan ta domin at tyrn Tana kwana gidan na ……
Muryan hjy habiba sukaji tana fad’in karyanka Wlh koda zaka mutu bazan bari ka aureta ba, gwara ma kabarwannan maganan…..
Mijin hjy habiba ya kura mata ido tare da fad’in akan wani dalilin Har kike kiran koda zai mutu bazaki Bari ya aureta ba?? Kln kuwa San abunda kike fad’a kuwa? D’an nawa kike ma fatan mutuwa??….. Toh let me tell you Wlh lndai Inada rai kuma yana Sonta dole In tsaya
Tace ni kuma ban amince ba domin bai dace da ita ba….
Mijin nata yace habiba akan wani dalill? Miye rashin dacewan? Kallon farhan yayi tare da fad’in naji kaman kace yarinyartana kwana a nan wani zubin…. Farhan yace eh dad
Kallon hjy habiba yayi tare da fad’in na tabbata inda yarinyar tana da aibu bazaki kawota gldan nan ta kwana ba, harki kasa fad’amin,domin naga Idan kikai ba’ki kina fad’amin but baki fad’amin wannan ba, ina son ki sani kaman farhan ya aureta ya Gama lndai Allah yasa matarshi ce babu yanda za kiyi …..
Hjj habiba tace ni kuma lndai har Ina numfashi kuma nina haifeshi ban yarda ya aureta ba, kuma bazan taba yarda ya aureta ba….
Dad din farhan yace habiba Ina son ki fad’amin dalilin da yasa bakya son ya aureta??
Tace hakanan kawai ban son ya auri yarinyar ‘
Dad din yace you are not serious…. Tare da kallon farhan yace inka kammala karatunka I promise zan tsaya maka har sai ka aureta…. Yana fad’In haka ya haura sama Fuuuuu tare da fad‘in rabo dai yana kisa …..
Kallon farhan hjy habiba tayi cikin bacin rai tace wato ni ban isa bako?? Ka kyauta amma ba laifinka bane…. Itama fuuuu tayi sama
Farhan d’aga kafad’a yayi tare da fad’in whatever nidai Ina Santa kuma tunda dad ya tsayamin banda damuwa ….. Fita yayi yabar gidan
Yarima Aliyu ya fara aiki a asibitin shl, sannan an fara gina Mai falin da Mai manaba ya bashi,
da yake filin k’ato ne ko wacce za’a Mata gefenta ginin gidan sama, da yake akwai kud‘i an d’Iba ma‘aikata da yawa suna alkin domin Yarima yace nan da wata biyu ko uku yake son a Gama duka ginin …..
Yarima ya dawo gida yau ko wajan Zamab bai samu ya biya ba, kaman yanda Ya sabayi kullum, domin ya gaji, yana shiga Clkin falo gimbiya zinatu ta taso Tana kuka tare da fad’in Yarima jita jltan da naji gaskiya ne???
Kallonta yayi sannan ya kauda kai gefe tare da fad’in fad’amin abunda kika Ji coz am tired,l need to rest….
Clkin kuka mai sauti tace yarima naji ance ginin mata biyu kakeyi zaka K’ara aure …… Yarima Aliyu murmushi yayi tare da lad’in gaskiya aka fad’a miki …..
Wani irin ihu ta saki mai kara tare da fad’inWlh bazanyarda ba, aiwannan cin fuska ne yaushe ka auroni saboda rashin adalci ka Fara maganan k’arin aure, ko wata d’aya Banyi ba amma kake fad’amin zaka K’ara aure Wlh baka isa ba …..
Yarima Aliyu kallonta yake cikin bacin rai, domin ya tabbata ihun da takeyi kuyangima suna ji…. Dan haka ya wuce ba tare daya kulata ba …..
Ganin haka tabi bayanshi Tana fad’in ai dole ka wuce wlh Yarima bazan yarda da rashin adalci ba har d’akinshi ta bishi tana surutai….
Yarima kam ko kallo bata isheshi ba, toilet ya fad’a Ya barta nan tana ta surutai kaman zararra ‘
Bayan yayi wanka ya fito daka shi sai towel yana gage kanshi, tashi tayi ‘a nufeshi tare da rungume shi tana kuka tana fad’in Yarima dan Allah ka tausaya mln bana son kishiya Yarima Ina kishin ka, maina rasa da kake kokarin K’ara aure, ko wata d’aya Banyi a gldan nan ba amma har kana maganan aure …… K’asa tayi tana kuka mai ban tausayl …..
Jlkin Yarima Aliyu yayi sanyi tare da tausayinta…. Gimbiya dake k’asa tana kuka ganin kaman jikinshi yayi sanyi taji dad’i dan dama tasan za‘ayi hakan …..
D’agota yayi tare da fad’in zinatu kiyi hakuri, ki d’auka komai kaddara ne, komai ya faru da bawa ki d’auka wannan auren da zan kara a matsayin kaddara ……
Tureshi tayi tare dayin baya tace babu wani kaddara… Karka kara cewa kaddara akwai abunda ba kaddara bane mutum shike sama kanshi ….. Duk namiji inya tashi aure saiya dinga amfani da wannan Kalman kaddara kaddara ban yarda da wannan kaddaran ba….
Yarima Aliyu yace baki da “ilmi baki san addlni ba, so banda time din in tsaya ina bata bakina wajan yi miki bayani…… Kaya ya fara kokarin sawa …..
Ta Fara zunduma ihu tare da fad’in Wlh baka isa ba ,ni nafi karfin wulakanci, sai dal ka zaba cikin biyu koni ko wacce zaka aura ….. Ni Wlh bama laiflnka bane na iyayenka ne da suka d’aure maka gindi kake son yin wannan rashin adalcin sune munafukai marasa tsoran Allah d ….. Tas ya sauke ma‘a Marin da sai da yasa ta dawo cikin hayyacinta …… Rl’ke wajan tayi domin Marin ya shigeta Sosai…
Yarima Aliyu yace you cross your limit kije na sakeki saki d’aya bazan zauna da macen da zata zagi iyayena ba koda da wasa ……
Gimbiya zinaku tace saki?? Yarima kasan Mai ka fad’a kuwa? Ka manta cewa babu saki tsakamn mu koda kuwa maina maka saika kamani da gardin ……
Yarima yace keep quiet, wannan ne dalilin daya baki daman kiyi min komai saboda bazan sake kiba harda raina iyayena? U are wrong, al’ada ba addini bace, you better leave this place tun Kafin in miki abunda za kiyi mamaki ……. Tashin hankali Yarima Aliyu ya karya dokan masarauta koya zeta kaya muje zuwa ……..
ldonta na kanshi ganin dagaske yake zai iyayi mata komai yasa tayi gaba tare da tsayawa wajan kofa tace Yarima nika saka? Auren dako wata d’aya baiyi ba amma ace harka sakeni? Lallai kayi babban kuskure a rayuwanka daka furta min wannan Kalman, sannan inaso ka jira Kaga Mai zai biyo baya tunda har ka karya wannan dokarta masarauta ….. Fuuuuuu ta fita
Yarima Aliyu yace mad girl tare da saka, saka jallabiya ya kwanta danya huta domin yayi matukar gajiya gashi wannan matartashi ta kara jagula Mai lissafi, yana kwanciya yaji Phone dinshi na ruri kallon wayar yayi tare dakai hannunshi kan wayar, Sunan Mai martaba ya
gani, d’auka yayi ban San mai mahaifin nashi yace mishi ba naga yace gani nan zuwa …..
Tashi yayi ya canza kaya sannan ya nufi gefen mahaifin nashi inda yaga mum dinshi damai martaba a cikin bedroom dinshi ….. Yana kokarin gaida mahaifin nashi Kafln ya karasa sai saukan Mari yaji tas tas har guda biyu abunda ba’a taba mishi ba tunda ya taso gashi yau
mahaifin nashi yayi mishi …..
Cikin fushi da bacin rai Mai martaba yace ka zubar min da k’ima, saki cikin wannan
masarautar?? Bayan kasan sai an Kama mutum ya aikata laifi biyu ake saki???? Yarima Aliyu yace Abba Ina Mai neman gafaran ka, Abba zagin iyay …….
Mai martaba ya daka Mai tsawa Wanda ba Yarima ba harta mum dinshi saida ta tsorata da irin tsawar damai martaba yayi ma Yarima Aliyu ……. Yace na baka umarnin Ka maida matarka, sannan daka yau Indai harka K’ara Karya wannan dokar ban yafe maka ba duniya da lahira ….. A haka kake kokarin K‘ara aure??? Mata d’aya ma ka kasa da ita ko wata d’aya bakayi da itaba amma har Kalman saki ya shiga?? Am really dissapointed with
you …… Ina son daga yau kaje ka zauna kaida matarka karka K’ara taso da maganan auranka dan banga alaman zakai adalci ba ko kad’an …… Sannan wannan al’adan daka karya saina hukunta ka, kaje kaida kanka kasa a rufeka sai kayi sati biyu Kafin ka flto
mutumin banza kawai ……
Lallai ran mai martaba ya baci fa
Naga alamun kunason mu dawo da yin posting sau daya a rana ko? Karku damu zan muku yaddah kukeso,,, don nidai nace bazan sake rokonku akan kumin comments ba