BATUUL
CHAPTER 2
Tuki yake cike da nutsuwa da kwanciyar hankali kan titin Kashim Ibrahim Road, ba a jin komai sai karar AC dake busa iska mai kanshi da sanyi har suka karasa masallacin suna ta fadin (Allahu Akbar Allahu Akbar Laillaha illalah Allahu Akbar kabira wal hamdulillahi kasira wa subhanallahi bukratan wa asilaah wa sallalahu ala nabiyina Muhammad wa ala alihi wa sahbihi wa sallama tasliman kabira) Abinda suke ta maimaitawa har suka isa masallacin kenan suka samu waje suka yi parking, da kanshi ya fito ya budewa Abui kofa Farida ma ta bude ta fito, ta miko mishi Sallaya daga bayan mota sannan ta kalli Abui tace bari in karasa side na mata, Abui yace “okay mamana, Allah yasa amsa ibadunmu yasa munyi a sa’a”, tayi murmushinta mai kyau tace “Amin Abui”, ta juya ta tafi
Bayan idar da sallah ne Aunty ta dauko jakarta ta ciro rafar yan dari biyar sabbi fil ta mikawa Batuul tace “gashi ki bayar sadaka, ai baba ya baki naki ko?”, Batuul tace “ehh”, sannan Aunty ta sake cewa “Ni zamu Je mota dasu Yusra dan Aabid ya fara jin yunwa in kin gama ki samemu” tace “toh Aunty”, ta karbi kudin ta saka à jaka tace “I will soon be back” su kuma suka tafi
“….Hajiya Allah yasa anyi à sa’a Allah yasa muna da rabon ganin bad’i, Hajiya à taimaka Fisabilillahi”
Batuul ce ta karasa inda mutanen nan da Almajirai suke a zaune ta ciro kudi daga jakarta na bandir din dari biyar da na dari biyu ta fara rabawa bayin Allah dake wajen su kuma suna ta yi mata addua tana cikin rabawa ne wani iska mai hade da ruwa ya fara saukowa , take ba tare da shiri ba ta zube musu kudin dake hannunta ta juya zata bar wajen kenan taji tayi karo da mutum, ta dago kanta da iska ke kokarin cire gyalen da sauri take fadin “Hey am sorr…..”, bata samu karashe maganar ba sabida yadda taga mutumin ya tsaya yana kallonta dogo ne sosai dan sai da ta mikar da kanta sosai kamin ta karashe ganin tsawonsa , kyakyawa ne sannan ba fari bane baqi ne amma baqin shi mai haske ne, yana da side burns sannan yana da long chiselled hanci da mitstitsin baki dake zagaye da millionnaires belt duk da akwai hula akanshi sai da ta hango curly gashin kanshi kanannadadde cikin hulan, bai rufe ba haka ma gashin gira da lashes dinshi bakake ne, cikin seconds da basu fi uku ba ta gama kare mishi kallo tayi sauri ta saukar da kanta kasa dan hawaye taf ya cika idonta, bugun zuciyanta ya karu kamar zai fito, sosai irin kallon da mutumin ke mata ya sata jin wani iri, ga mugun buguwa da heart d’inta keyi
ya bude baki kenan zaiyi mata magana cikin sauri ta matsa baya daga wajen bata tsaya jin komai ba ta juya cikin sauri sauri da dan gudu ta karasa inda tayi parking Mota ta bude ta shiga ta jefa jakanta baya , tana zama ta sauk’e ajiyar zuciya tareda da lumshe ido, mutumin nan ta gani kamar yanzu yake kallonta, Aunty ta juyo ta dubeta tace “lafiya kike ajiyar zuciya ?”, Tayi maza ta bud’e ido tace “Aunty ruwan nan da nayi escaping bai jikani bane ya sani yin ajiyan zuciya”, Aunty tace “toh ni yanxu karbi key mu tafi gida Yusra ta Ce min yunwa takeji, ga Aabid ma na rigima”, Batuul ta juya bayan motar ta kalli wacce aka kira da Yusra tace “ba sai da nace kici abinci ba kamin mu fito ba kika ki wai ke sai kin dawo”, Batuul ta juyo ta dubi Aunty tace “Janet fa har binta ta riqayi da abincin kamin ta saka mata kaya taqi, shine yanxu zata cewa mutane wai tana jin yunwa” bata ce komai ba Yusran sai zumburo baki da tayi, Batuul din ta sake ce mata “ki bude jakana akwai TWIX da cookies, ki dauko kuci ke da Hafix (Babich) ki bawa Fa’iza ma”, sannan ta juya ta dauki tissue à gaban motar ta goge fuskanta da ya jike da ruwa, ta bude pidgin din motar ta dauko orbit mai flavor din pepper mint ta jefa à baki sannan ta gyara gyalen ta daura shi kamar dankwali sannan tayi igniting motar ta tada suka tafi
Tunda ta bar wajen yake tsaye yana kallonta har ta shiga motar suka tafi bai dena kallon wajen ba sai da yaji an taba shi ta baya ya juyo ya ga Wanda ya tabashi Ya kalli Wanda ya tabashin tare da Sakin Fuska yace “Massa ya akayi shehu ya bari ka bar wajen shi kuma ban ganka da shirin hawa ba”, Massan yace “Man bari kawai ai bazan iya zama ayi hawan Durba dani ba, yanxu haka ma gudowa nayi”, yace “kai mey kake yi anan kai kadai bayan naga Abui ma suna tare da Shehu”, yace “yeah abu nazo yi amma banyi bama sai nan gaba”, Massa yace “okay muje”, sai da ya sake juyawa tare da sauk’e ajiyar zuciya kamin yabi hanyan da Batuul tabi tukunna suka juya suka tafi
A gaban gate din wani mansion ta tsai da motar tare da yin horn, masu gadine su biyu suka fito cikin hanzari suka bude musu gate din suna yi musu sannu da zuwa, karasawa tayi cikin gidan har ta isa inda ake parking, kamin ta tsaida motan Yusra tayi sauri ta bude kofan ta fita Hafix ma ya bita a baya, cikin hadin baki Aunty da Batuul suka ambaci “Inna lillahi wa inna illaihi rajiun”Fa’iza ta fito itama a guje ta bi bayansu tana fadin “bakuji ciwo bako”,su kuma suna ta kyalkyala dariya Yusra tana fadin “ai na rigaka”, shima Hafix yana ya rigata, suna karasawa bakin wani sliding door mai girma suka tsaya dan baza su iya danna kararrawar ba yayi musu nisa sai Fa’iza ce da ta karaso ta danna musu kararrrawar suka tsaya jiran à bude musu kofar, à dannawa na biyu ne aka bude musu kofa daidai lokacin Aunty da Batuul suka karaso suka Shiga ciki, parlour ne mara tarkace amma yana da kyau, wallpaper ne fari mai flowers fari da grey zagaye da dakin , daga tsakiya akwai farin kujera mai L shape da throw pillows akai ,karamin round Table daga gaban kujeran, office chair daga gefe sai Babban TV da ya kusa cinye bango dan girmanshi à manne da bangon.
Kanshine mai dadi na sandal wood ke fitowa daga parlour hade da iskan Ac mai dadi da sanyi ,bayan sun karasa daga ciki sun wuce wani bene mai rails silver suka isa wani dinning area shima créam ne da Brown mai dauke da dogon dining Table da kwanuka na alfarma sai chandelier daga tsakiya
Bayan sun shiga sun zauna ne yarinyar da ta bude musu kofa tace “sannunku da zuwa Aunty ” cikin hausar ta da ba dai dai ba ” Aunty tace mata “sannu Janet, Su Ahmad Sun dawo ne naga motan da suka fita dashi à parke ”
Janet tace “Ehh ,Aunty sun dawo tun dazu Sun hau dakinsune, su da babane dukkansu Sun dawo shima ya tafi sama” , Batuul ce ta juyo bayan ta ajiye wayar da take dannawa tace “Tabawa fa ko har yanxu aiki take ba à samu tayi wanka ba, tunda dama dan wankan tace baza ta masallaci ba”Janet tace “à ah Aunty taje dakine zatayi wanka”, tace “okay”
Tafiya sukeyi suna ta gaisawa da dimbin jama’ar da suka halarci sallah Massa ya dubi Abutturab yace ”Man yaushe yaushe ne tafiyan naku wai? Yaushe zaku koma Abuja ne ?”,
Abutturab ya furzar da iska daga bakinshi sannan yace ” Yeah i will b leaving in the next four days dan inada appointment da FCT Minister amma nasan su Abui sai next week cuz su sai Sun gama sallah anan, I cant wait that long, I have to go back, ina da ayyuka”
Massa yace “okay nima sai next week din zan shigo “, suna tafiya har suka iso inda su Abui suke, Abui ne ya Juyo ya dubesu tare da cewa mutumin da suke tsaye tare, “ai gasu nan ma”, mutumin ne ya fadada murmushinshi tare da fadin “Masha Allah” ya miqa musu hannu suka gaisa, yacewa Abui “Its been long i met them , almost 19 yrs nasan bazasu tunani bama, anyway ya kuke ? Ana karatu ko kuma an gama ? Ko kuma aure za Ayine ya fadi maganar tare da dariya ? ” , take fuskan Abuturrab ya canza dan baya so ana mishi maganan aure in Abui na kusa , yanxun nan zai tada maganar har sai ya dinga magiya taré da bashi hakuri
Abui ne ya bawa mutumin ansa tare da fadin “ai aure kam sunqi shi, Shi Aliyu(Abutturab) architect ne dan yanxu ma yana da contract da FCT minister, Mustapha(Massa) kuma Doctor ne tunda yayi karatu à Germany sukayi retaining dinshi, but munaso ya dawo dan baza mu barshi cikin turawa ba”, mutumin yace “gaskiya kam, Allah ya taimaka. ” *Alai*(Alhaji) Ahmad Kyaree zan wuce yanxu dan nasan su Madam suna jira, tare mukazo dasu kuma ga ruwan da akeyi, zan kawosu before ku koma in sha Allah ” , Abui yace okay à gaidamin su, ace musu muma muna nan zuwa.
Tunda mutumin ya fara magana Abutturab bai dago kanshi ba har sai da mutumin ya fara maganan aure, a snn ne ya dago kanshi ya k’arewa mutumin kallo har yaso gano inda ya sanshi amma ya kasa, sai cewa Abutturab yayi bayan mutumin ya karasa barin wajen, ” Abui is he an old friend”?
“Yeah à good one too inji Abui “, tare da basu labarin abotarsu, sannan yace ce musu su tafi kamin ruwan ya kara yawa da karfi
Ta miqe kenan tana cewa Aunty zata haura dakinta tayi wanka ta canxa kaya dan Sun jike ta hango Babanta na saukowa daga bene, da gudu taje ta rungumeshi, “tace Baa yanxu nakeso inje wajenka, ya d’an janyeta daga jikinshi yana tambayarta
“Batuul ya kayanki à jike haka?” Tace Baa ai anyi ruwa à waje ku tun dazu kuka dawo ko, shiyasa baku jiqe ba”, Ya sake ce mata “Batuul yanxu sallahn Allah Kowa na murna da saka Sabbin kaya shine ke kika saka baqin kayan nan kikaje har masallaci dashi?”, Batuul ta danyi kasa da ido ta zumburo karamin bakinta kamin tace “Baa sabone fa kuma designer ne na Hauté Èlan kai ka siyomin mafa ” , yace mata “toh naji maza Je ki cire su kar kiyi mura, tayi murmushi tace “yanxu zan dawo ai”, ta haura sama shi kuma ya karasa saukowa kasa .
Har ta wuce wani daki à sama sai kuma ta dawo daga baya, cikin sand’a ta bude kofar dakin, a hankali take turawa, sai da ya fara karane ta bude shi gaba daya tana fadin “Taraaan”, yara ne maza a dakin su biyar, kowa da game controller a hannunshi suna ta ihu,typical dakine na maza da akayi littering gwangwanayen drinks, kayansu da suka cire daga k’asa, gadajen à hargitse sai plates din abinci da spoons. Yan manyan guda biyu da baza su wuce 13-15 yrs ba sanye suke da wandunan shadda sai fararen vest à jikinsu hannunsu kuma maqale da agogo, sai mai bi musu shi kuma sanye yake da complète kaftan dinshi brown harda hula akanshi ya tsaya akan sofa yana ihun ni zanyi winning, dayan kuma sanye yake da three quarter da T-shirt shima yana riqe da game controller, karamin cikinsu ne snn duk yafisu haske yana daga gefe riqe da Ipad à hannunshi yana ta aikin dannawa, Suna ganinta suka yadda abubuwan dake hannunsu, Manya ukun na ihun “Aunty ta dawo”, k’anana biyun kuma suna cewa *Mama ta dawo”, a guje suka fito kowa na rige rigen ya riga dan uwanshi fita daga dakin, Da sauri Baatul ta matsa daga bakin kofa dan kar su bigeta tana ta dariya ta juya ta bar kofar dakin ta karasa nata dakin ta murda kofan ta shiga.
Tana shiga daki ta nufi inda towels dinta ke rataye, ta janyo daya sannan ta cire kayan jikinta da suka jiqe, ta daura towel din a kirjinta, ta nufi toilet din dake dakin nata, bayan minti goma ta fito tana kanshin shower gel da sabulu,da towel a jikinta, daya kuma a daure a kanta kamar turban, gashin goshinta ya kwanta lub lub, fuskanta ya kara haske da kyau, ta karaso gaban mirror dake cike da turararruka da yan kayan kwalliya da na shafa , ta jawo stool din mirror ta zauna sannan ta dauko man Makari, a hankali ta riqa shafa man kamar baza ta gama ba, bayan ta gama ne ta karasa gaban closet din kayanta, ta bude ta dauko peplum blouse da skirt din atamfa baqi mai pattern din purple ta saka à jikinta, kayan ba karamin kyau yayiwa jikinta ba, komawa gaban madubin tayi ta shafa powder a fuskarta sannan ta saka kwalli a idonta, ta shafa nude lipstick a bakinta , ta bude costume box dinta dake kan madubin daga gefe ta dauko dankunne da sarka silver masu duwatsu a jiki, sai abun hannu da zobe shima silver, sannan ta fesa turare, ta kalli kanta a madubin tare da murmushi sannan ta koma ta zauna a kan gadonta tare da d’aukan wayanta,
bayan ta d’an daddana wayan ne ta kara à kunne tare da fadin “Hello Riri, shine kikace min a Ramat Square zakuyi sallah koh? kuma bakije ba”,
Daga daya bangare aka amsa ana dariya tare da fadin
“Yo babe nan naje mana, i wanted calling you inji inda kike sai da na duba wayana naga ban fito dashi ba, You know anytime Yaa Abu na gida toh komai nawa doesnt go ryt”
Batuul tace “babu wani Yaa Abu, anytime kika samu matsala sai kice shine, toh duk ranar da zan ganshi sai na fada mishi”
Riri tayi dariya tace mata “dan baki sanshi bane ai, koh face dinshi idan kika gani zakiga ko smiling bayayi, brows dinshi kullum a hade, bayayiwa mutane ma magana wai surutu na saka mishi ciwon kai, kuma ko bashi zaiyi ba wai baza ayi a kusa dashi ba”
Batuul tace “all these apart, ni zanzo yau dan Baa yace nan da kwana hudu zamu koma dan yana da aiki sosai kuma gobe da jibi zamuje wajen su Yayya da sauran Family”
Riri tace “yawwa bae of earth,daman ina ta tunanin yadda zan ganki, I missed you soo much wlhy, kizo yanxu i have have So many things for you alone”, Batuul tayi dariya tace
“You are not serious, ai sai na fadawa Baba tukunna, sai yayi approving zuwana”
Riri ce ta marairaice murya hade da cewa “nasan Baba zai barki sai dai in kece bakison zuwa, pls kizo, am bored over here, kuma kinsan Yaa Abun in yana nan ba a yawo “
“Batuul ce ta cemata ni ba ruwana and i told you zan fada mishi whenever i meet him”
“Ai bazaki iya ba nasanki, I wish zaki zo yana nan shima yaga wanda ya fishi rashin magana,ai mantawa ma nayi halinku daya nake fada miki”
“Ni dai yanxu a bar maganan, yanxu zanje in fadawa su Aunty zanzo wajenki” ,
“Aii sai kinxo”
sannan suka katse wayan, tashi tayi ta jona wayan a caji ta juya ta fito daga dakin har ta karaso kasa, ta sauka daga benen ta jiyo muryoyin yan gidan a dinning suna cin abinci, karasowa tayi wajensu, Mahir na ganinta yace “Yaa Batuul kinyi kyau”, Hafix ma yabishi yace “kinyi kyau”, tayi murmushi tace musu “nagode, kuyi shiru ku gama cin abinci, bad manners, talking while eating”
kujera itama taja ta zauna a gefen Baba daga hagu, Baba ne ya ce mata
“kinga kayan nan yayi miki kyau amma ba kiyi ta saka baqin kaya ba a kowane occasion”,
Aunty ce tace “ai Y’ar kauye ce,”
ta juyo ta dubi Baba tai raurau da ido, yana ganin haka ya yace
“À ah Mamana ba y’ar kauye bace, ai kayan nayi mata kyau ko ?” ya tambayeta ,murmushi tayi sannan ta dauki plate, ta janyo wani babban tray da aka rufe da foil paper ta bude,Danderu ne na kaza yana ta tiriri da kanshin kayan yaji, fork and knife ta d’auka ta yanko kadan ta saka à plate din sannan ta sake janyo wani food flask din ta dauki masa daya a ciki tare da miyar masa, a hankali ta riqa ci ba tare da cewa komai ba har suka gama
Sun gama cin abincin ne suka tashi suka koma palo, Fa’iza da Janet ne suka zo suka gyara dinning din tare da kara turaren wuta à duka electric burners din gidan
Sai da kowa ya zauna ya nutsu sannan ta dubi Baba tace
“Baa inason inje wajen Farida tunda gobe da jibi we Will ne busy”,
“Okay what time zakije ?” ya tambayeta
Cewa tayi “ko yanxu tunda naga its already after 12”
” Tunda su Baa Liman(Driver)suna hutu sai Ahmad ya kaiki dan ya fiki iya driving kuma bana Son kina driving ke kadai especially a Maiduguri da ba a bin régulations din driving “
“Okay Baa nagode, ” Aunty dai bata ce komai ba tunda Baba ya yadda shikenan. Tashi tayi ta k’ara haurawa sama ta dauko jakarta ta chanel purple shima irin kayan da karamin gyale shima purple amma light, ta kara duba fuskanta a mirror sannan ta sauko
Tana saukowa taga Ahmad riqe da key din mota a hannunshi yana jiranta, karasowa tayi ta ce wa su Baba zasu tafi,
yayi musu a dawo lafiya sannan yace mata idan ta gama sai ta kira a zo a dauketa, tace “toh”,
Tacewa Aunty sai Sun dawo, Aunty tace mata “ki gaishe da Ammah kice mata nima zanzo ko bayan mun koma Abuja ne”, Toh tace sannan suka fita suka nufi inda akayi parking motocin gidan suka shiga wata Audi fara sol, Ahmad ne ya tambayeta anguwan da zasu bayan yayiwa mai gadi horn kamin yazo ya bude mishi kofan, ce mishi tayi Old GRA ne in munje zan nuna maka hanya, Ya juyo yace mata
“Yaa Batuul Allah kwatancanki akwai wahala yanxu sai mu kai two hours muna neman wajen da baifi muje a 20 mins ba “
“Tace toh ka bani inyi driving”
baice mata komai ba yaja motan suka bar gidan bayan mai gadin yayi musu a dawo lafiya
Tafiyan minti goma sha biyar suka isa gidansu Farida a old GRA ,Horn yayi aka bude musu gate suka shiga, suna shiga gidan bugun zuciyanta ya karu, ambaton Allah ta riqa yi har sai da taji ya dan ragu sannan ta bude motan ta fito daga ciki tare da yiwa Ahmad sai anjima akan in ta gama zata kirashi
Farida na Jin tsayuwar mota ta fito daga cikin gida a guje tazo ta rungume Batuul ta na ihun i missed you so much babe,
“Batuul ce tace mata sakeni kar ki ballani Baba ya hanani zuwa nan gaba”
Dariya tayi sannan tace “nasan Baba bazai hanaki zuwa ba, sai dai in ke zaki min halin naki ki qi zuwa”, Batuul batace komai ba har suka karasa ciki ,tacewa Farida “Ammah da Abui da Sadiq fa ?”
“Ammah da Sadiq basu dawo ba inaga Sun tsaya wajen Ayyi, Abui yana Shehuri, Nida Yaa Abu ne a gida kawai shi kuma yana sama”,
Batuul tace “okay”,
sama suka haura suka isa dakin Faridan, suna shiga ta cire gyalenta ta ajiye a akan gadon ta juya inda fridge din dakin yake zata dauki Fanta, tana budewa taga babu Fanta à fridge din, “kinsan zanzo shine baki saka Fanta a Fridge dinki bako, sai tarin bakaken drinks da kika ajiyewa mutane(coke), Farida dake tidyn din Novels din ta dake baje kan gadon tayi dariya tace “kinsan ni bana shan Fanta, ki sauka downstairs ki bude fridge din falo xa ki samu fanta, lemme finish tidying this, I have a gist for you besty” Juyawa Batul tayi ta fita daga dakin tana sauka falo ta bude fridge taji ana saukowa a stairs ta dago da sauri kallo daya tayi masa ta ci gaba da abinda take, ya karaso falon yace “Get me bottle water, Waye ya shigo gidan nn da mota Farida?” Shiru Batul tayi bata ce komai ba kuma bata dago ba, hka kawae gabanta ya fadi, ta rufe fridge din bayan ta ciro fanta da bottle drink din da ya bukata, lkci daya ta juyo suka yi ido hudu da shi, ta dauke nata da sauri ta karaso cikin falon ba tare da ta kallesa ba ta ajiye masa ruwan kan center table snn ta haura sama da sauri, bin ta yyi da kallo lkci daya ya shiga kwada ma Farida kira, A bakin kofa Batul ta kusa cin karo da Farida, Farida tace “Kinga abinda nake gaya maki, I wonder y he is calling me ynxu” bata jira cewan Batul ba ta sauka kasa tace “Gani yaa Abu” a nutse yace “Who is she? I mean that girl that just left here, a gidansu ba a mata tarbiyan gaisuwa bne, is this the kind of frnds yhu are mingling with?”
tsayawa yayi ya na kallonta ita kuma kanta à kasa, ba a Jin komai sai bugun zuciyanta da ya kara tsananta, riqon da yayi mata ne da kuma bugun zuciyanta yasa hawaye taruwa à idonta, kiciniyar kwace kanta ta fara yi daga wajenshi amma yaki saketa, Dumi yaji a hannunshi ya juya yabi hannun nashi da kallo, hawayen da ya gani ne yasa shi sakinta a hankali ya juya mata baya, juyowa ya sakeyi zai yi mata magana yaga bata wajen,
Parlour ya koma zauna yabi stairs din da ta hau da kallo, lokaci daya ya shiga kwada ma Farida qira, A bakin kofa ta kusa cin karo da Farida, Farida tace “kinga abinda nake gaya maki, I Wonder why he is calling me yanxu” bata karashe maganan ba ta ta riqe Baatul tana tambayarta “Why are you sore ? Mey ya sameki kuma idonki ya canja” , kamin ta bata answer ta sukaji ya sake kwada ma Farida kira, bata jira cewan Batuul ba ta sauka kasa tace “Gani Yaa Abu” a nutse yace “Who is she ? I mean that lady, doesnt she talk ko kuma gaisuwa ne bata iya ba ?”, A zuciyanta cewa tayi “Innalillahi wa inna illaihi rajiun, Yaa Abun nan komai ba a yi mishi daidai, in nayi magana yace na cika surutu, yanxu kuma Batuul bata yi magana ba zaiyi fada” Tana cikin tunanin taji yace “am i not asking you ?”
“No Yaa Abu bata jin dadi ne shiyasa bata gaisheka ba”, Ce mata ya sakeyi “daga ina take”? “Batuul cefa, yarinyan Aunty, kawata tun muna Centagon wacce ka kaini gidansu a Maitama last year da ka dawo har kace bazan kwana ba”,
Hannu ya daga mata alaman ya isa,
“ki miqomin ruwa a fridge”, a kan center Table din gabanshi ta ajiye ta juya ta bar falon
D’aki ta nufa, tana shiga ta tarar da Batuul à tsaye tana riqe da jaka da gyalenta a hannu, “Zan tafi gida”
“Ban gane zaki tafi ba saboda mey” Farida ta tambaya , “Yaa Abu yayi miki fada ne dan nasanshi da yiwa mutane fada”, “Ni baiyi min komai ba kawai zan tafi ne”
“In kinje toh mey zaki cewa Aunty ya dawo dake bayan kince har dare zaki kai , kuma in Ammah ta dawo mey zan fada mata? That kinzo har kin koma ? If Yaa Abune baza mu sake bin hanyan da yake ba nima haka yake min”,
“Toh naji bazan tafi ba amma baza muje inda yake ba ” Farida ta kyalkyale da dariya tace,
“Keh da kika ce zaki fada mishi ina gulman shi yanxu kuma ke da kanki zaki qi bin hanyan da yake “
“Ni ki rabu dani, kuma ai ni babu abinda yayi min kuma zan fada mishi din ai”, haka suka ci gaba da hira har Batuul ta manta da Abutturab na gidan
Yana zaune a palo bayan ya kurbi ruwan da Farida ta miqo mishi, tunani yayi na lokacin da Baatul ta bigeshi a masallaci da yadda tace mishi sorry har yanxu da ta zo gidansu yaga hawaye a idonta, hawayen da ya tuna ne ya sashi ajiye ruwan yana fadin “Damn it” à hankali, “does she always cry?” Yana cikin tunanin yaji an bude kofan palon , Ammah ce tare da Sadiq a bayanta suka shigo suna hira, ciki suka karaso suka zauna a palon, Abu ne yayi musu sannu da zuwa, Ammah tace “baku tsaya anyi hawa bane da ku ?” “Ehh naso mu zauna sai kuma na fasa amma Abui yana can” , “Muma munje mun duba Ayyi ne” sannan ta kwalawa Fanne kira,cikin hanzari Fanne ta karaso tacewa Ammah “sannu da zuwa Ammah, Gani”
“kije ki duba min Farida kice mata mun dawo, sama Fanne ta haura ta fadawa Farida sakon da aka bata sannan ta fita, Farida tacewa Batuul “muje ki gaida Ammah nasan baza ta hawo palon sama ba shiyasa ta sa a fadamin”
“Ni sai kinje kin duba in Yaa Abu baya palo tukunna zanzo”
“Farida tace you are kidding me,taso mu tafi ai in Ammah tana nan bazai yi komai ba” Hannun ta Farida ta jawo suka sauko k’asa, lokaci daya ta d’ago kanta suka hada ido hudu dashi, ta dauke nata da sauri ta karaso cikin falon ba tare da ta kallesa ba suka iso gun Ammah, Farida da gudu ta karasa gun Ammah tana fadin “shine Ammah kuka qi dawowa da wuri inata jiran ku”, Ammah bata yi mata magana ba sai Batuul da ta cewa ” A ah Batuul ce a gidan? yaushe kikazo, ya gida dasu duk suna Aunty na lafiya ? Ashe kunxo, Aunty da mukayi waya tace mayb baza ku zo ba dan Baba na da aiki, anyi sallah lafiya ?”, Batuul da murmushi a fuskanta ta k’arasa wajen Ammah ta zauna daga k’asa sannan tace “Alhamdulillah”, ta tambayeta ta karfin jiki, “Alhamdulillah Batuul, kun gama karatu lafiya ? Next two weeks zakuyi graduation dinku ko?”, Da “Eh” ta amsawa Ammah, Ammah tace “Allah yasa kuyi a sa’a, suka amsa da Amin dukkansu, Sadiq ne ya cewa Batuul “Wane school kikayi applying admission ne , ko har yanxu LUE din zakije?”, ya k’arasa maganan yana dariya, Batuul tace ” ban sani ba ko Baba nan yake nema min but if ban samu ba maybe nan zai kaini dan bayason inyi nisa”, Sadiq yace “ai dama LUE makarantan masu ilimine, ko da yake ai kema kina da ilimi you can do it”, tayi murmushi tace “kai Yaa sadiq”
Abutturab na zaune yana kallon TV amma duk hankalinshi yana kansu, tunani yake yaushe ma suka santa and everything about her,wai har Sadiq ma yasan makarantar da take son zuwa, tab’e baki yayi ya ci gaba da kallonshi, Ammah ce ta tashi ta hau sama, yan matan ma suka bita, da ido ya bi bayanta har saidai suka shige ciki
7:20 na dare duka y’an gidan na kan dinning suna dinner,Abutturab ne kadai baya nan Ammah tacewa Batuul “kwana zakiyi amma ko” Batuul tace “a ah Amma zan tafi yau, yanxu ma Ahmad nake kira baya picking, shi zaizo daukana”, Ammah tace , “No ai ba sai kin kirashi ba , gasu Sadiq sai su mayar dake bari a gama dinner”, Toh kawai tace dan batason yiwa Ammah musu, taci gaba da k’iran Ahmad a waya baya d’agawa
Abui ne yace “su tafi da Abutturab dan yanxu zamu fita da Sadiq”, mik’ewa yayi yacewa Batuul in taje gida ta gaida Baba, tace mishi yayi ta trying number dinshi its not going” Ta amsawa Abui da “Toh” sannan ya ciro rafar kud’i daga aljihunshi yace ga Barka da sallahn ta nan,tayi mishi godiya.
Saukowa yayi daga stairs sanye da grey sweats da farin shirt hannunshi rik’e da key din mota, Ammah ta tareshi tana tambayanshi inda zashi,yace mata shehuri zashi, Ammah tace mishi “zakayi droping Batuul a gida” , shi ya manta da yarinyar ma saida Ammah ta ambaci sunanta , cewa Ammah yayi “Sadiq fa baya nan ne”, “tace sun fita da Abui”, iska ya fitar daga bakin shi snn yacewa Ammah “a kirata mu tafi, am in a hurry”, Fanne Ammah ta kwadawa kira tace taje ta kira mata Batuul ace ta fito su tafi, fitowa tayi bayan Fanne ta fada musu sakon Ammah, wannan karon babu dankwalin daure a kanta sai gyalen kawai ta yafa,tana saukowa Ammah ta tambayeta ta shirya ? Tace “ehh” Toh ga Abu nan zai kaiki gida” Ido ta wara ta dubi inda Abun ke zaune yana jiranta, a sanyaye ta karaso falon tana kirkiran murmushi, Ammah ta mike tace dan jira bari in sakko, sama ta haura, Batul ta shiga Satan kallonsa, mikewa yyi lkci daya fuskar nn tasa bbu yabo bbu fallasa yace “mu je” Farida da bata ji ddin shi xae mai da bestyn ta gida ba tace “Ya Abuu Ammah tace ta jira ta sakko,” wani mugun kallo ya watsa mata snn ya nufi kofa cikin tafiyarsa ta isa, Farida ta dan tabe baki tana kallon Batul dake ji kmr ta saki kuka, danne dariyarta tayi tace “kema dae wllh, ae ba nuna masa xakiyi kina tsoro ba dakewa xa kiyi ki daure fuska kema ki….” Shiru Farida tayi ganin Ammah ta sakko rike da wata katuwar leda ta mika ma Batul tace “ga Goran sallahnki Bitti” murmushi Batul tayi ta dan risina ta karba hade da mata godiya, horn suka ji ana dannawa, Ammah tace “Au har ya fita, maxa ki je kar a bata masa lkci ki gaida su Aunty da kowa da kowa”
A hankali take tafiya sabida yadda bugun zuciyanta ke k’aruwa, tana zuwa bakin k’ofa ta juyo ta kalli Farida da pleading eyes ko zata rakata amma sai taga tana d’aga mata hannu da wide smile a fuskanta, Ammah ta sake juyawa ta duba taga ko tana wajen, itama hannu ta d’aga mata tare da mata murmushi, horn dinshi ta sake ji da k’arfi , murda kofan tayi ta fita daga palon har ta k’arasa wajen da motocin gidan ke pake, rasa wanne motan yake ciki tayi sai da taga ya dallo hasken motan daidai inda take tsaye tukunna ta k’arasa amma bata bud’e ba, tsayawa ta sakeyi tana contemplating gaba zata shiga ko baya ? Tsayarwa da tayi tana b’ata mishi lokaci bata shiga ba ya b’ata mishi ya sake danno mata horn din da k’arfi, kofan dake gaba na gefen driver ta bud’e ta zauna ba tare da tace mishi uffan ba, tada motar yayi sai da sukaje gaban gate kamin mai gadi ya bud’e mishi gate bayan yayi mishi horn ne ya jeho mata tambaya ba tare da ya dubi inda take ba yace “wane anguwane”, a hankali cikin sanyin magana tace mishi “Lagos street”, tambayanta ya sakeyi “Which side of Lagos street?” , cikin muryar sanyi tace “In munje area din zan nuna maka” Baisan Lokacin da ya juyo ya watso mata wani irin kallo ba, a ranshi fadi yake “Is she kidding me? muje zata nunamin, bata san ma hanyan gidansu ba kenan” bai ce mata komai ba ya fita daga gate din gidan ya d’au hanyan anguwan da ta fada mishi, tafiya sukeyi babu wanda ke cewa kowa komai sai k’ira’ar Juhanny dake karanta suratul Qasas da k’arar air conditioner, gaba daya hankalinshi na kan tukin da yake , Batuul kam skirt din jikinta ta riqe da k’arfi har hannunta na yin gumi saboda kwata kwata she is not comfortable, Allah Allah take su k’arasa gida, wani hanyan Lagos street din yabi wanda bata tab’a bi ba har suka isa, suna zuwa ya sake tambayanta “Ta ina gidan yake” juyawa tayi tabi window motar da kallo taga bata san wajen ba, a hankali tace mishi “ba nan bane fa” , wani kallon ya sake watso mata wanda yasa ta saurin sata kai k’asa , tare da gangarawa gefen titi ya tsaida motan, dago kanta tayi taga ita yake kallo yana jira ta k’ara yi mishi bayanin ina ne idan ba nan ba, ce mishi tayi “Ni ban taba ganin nan ba a anguwanmu ba, mu koma gidanku sai in nuna maka daga farko inda hanyan gidanmu yake ko kuma in qira Ahmad sai ya d’aukeni a can” sai da ya bari ta gama magana bai ce mata komai ba sannan ya tada motan yaci gaba da tafiya, tsaki yayi tare da duba agogo yaga k’arfe takwas 8 daidai, Sun kusa minti talatin suna yawon neman hanyan gidan basu samu ba, ita dai babu abinda takeyi sai addu’a gashi tana ta k’iran number Ahmda baya d’auka, sai da ya gaji da yawon neman tukunna ya sake tambayanta “For God’s sake tell me where your house is” cikin kakkausar murya yayi mata maganan, take jikinta ya fara b’ari, hawayen dake mak’ale ya k’arasa gangarowa, shiru tayi ta kasa ce mishi komai, magana ya sake yi “Are you this dumb naji Sadiq na cewa kina da ilimi”, tsaki ya sake ja yace mata “okay tell me right now cuz you have wasted my time alot”, ce mishi tayi “Nifa ban gane hanyan nan da ka bi ba, ba ta hanyan nan muke bi ba mu in zamu…..”, bai bari ta karasa maganan da ta keyi ba yace mata “GET OUT” da k’arfi, kai ta d’ago ta kalleshi dan ta k’ara tabbatarwa da gaske yake, ce mata ya sake yi “I SAID GET OUT”, kasa yin komai tayi a lokacin saida ya mik’a hannunshi ya bud’e mata k’ofan sannan ya k’ara ce mata “OUT” ko ledan da Ammah ta bata bata tsaya dauka ba ta bud’e motan ta fita, tana fita ya fizgi motan kaman wanda zai tashi sama
A wajen Batuul ta tsaya ba tare da tasan abun yi ba, ga tsoro da ya cika ta, tsoro ma takeji tayi motsi dan gani take wani abun zai kama ta, kuka ta saka a hankali tana k’iran Baba, wayanta ta ciro ko xata ga missed call din Ahmad amma taga bbu, takaici yasa ta ki kiransa ta kuma mayar da wayar cikin jaka, tsugunawa tayi a wajen ta kifa kanta a cinya ta ci gaba da kuka dan ita bata ma san inane nan ya kawota ba, gashi anguwan babu commercial vehicles bare tace zata hau d’aya ya kaita gida, shirun da anguwan yayi ne yasa ta d’ago kanta ta sake dubawa ko zata samu mafita, da taga babu yadda zatayi ne ta yanke shawaran kawai ta tashi tayi ta tafiya ko zata samu yadda zatayi,
Tunda ya bar wajen hankalinshi yake kanta, tuk’i yake cike da damuwa, “yama za ayi mutum yace baisan hanyan gidansu ba idan ba rainin wayo ba?” Tambayar da ya yiwa kanshi kenan tare da jan tsaki, Tunawa da yayi da fuskanta da yadda hawayen ke gangarowa daga idonta ne yasashi saurin taka brake da k’arfi, mutane ne ke ta yi mishi horn amma bai kulasu ba, parkin gefen titi yyi, idanunta da ke Tara hawaye kawai yake gani,d’an siririn tsaki yaja, wayanshi ya d’auko ya lalubo number Farida ya k’ira, tana d’auka yace “ke inane anguwansu k’awarki”, ce mishi tayi “lah Yaa Abu har yanxu baku k’arasaba” a tsawace yace “Tell me what i asked you and dont question me” ce mishi tayi “Lagos street ne behind Leventis, Yaa Abu wani abune ya faru” bai jira ta k’ara magana ba ya katse wayan, yana ajiye wayan ya juya motan hanyan da ya bar Batuul a wajen, yana isa inda ya bar ta ya duba yaga bata nan sai d’an kwalinta da bata san ya fad’i ba a kasa gun, fitowa yyi ya dauka ya jefa bayan motanshi, a hankali ya dinga bin hanyan, daga can ya hango ta tana tafiya tana share hawayen dake zubowa a idonta, karasawa yayi inda take yayi mata horn, bata juyo ba sai ci gaba da tayi da tafiya da sauri, wani horn din ya sake mata amma bata juyo ba sai ma sauri da ta k’ara sabida tsoro, gabanta yaje ya tsaya da motan, bude mata k’ofa yayi yace mata “GET IN”, ko kallonshi bata yi ba taci gaba da tafiya, fitowa shima yayi daga motan yabi bayanta dan ranshi ya soma b’aci, yana isa wajenta ya kama hannunta ya jawota har wajen da yake, fixge hannunta tayi da karfi batasan lokacin da tace “dole ne sae na shiga motar ka malam” bata ankara ba sae ji tayi ya ka ta cikin motar, yyi banging kofar snn ya zaga ya shiga ya tada motan ya bar wajen, kuka ta dinga yi a motar uwa wata karamar yarinya, kara gudunsa yyi had’e da dukan steering wheel din motan yace “Damn it” sae kace warce ya sato, a ranshi fadi yake “Duk su Ammah ne suka jawo masa yana xaman xaman sa” gnin har lkcn bata fasa kukan da take ba yasa ya bude pidgin din motar ya dauko handkerchief ya miko mata, kin karb’a tayi, wani haushi ya kuma kama sa ya mayar da handki din, wani gida suka kusa wucewa tayi sauri tace mishi ga gidanmu nan, brake ya taka yayi horn a gate din yana jira a bud’e, bata jira an bud’e ba ta fita da sauri ta shige gidansu, bin ta da kallo yyi cike da bacin rae, yafi minti goma a k’ofar gidan ba tare da ya tafi ba, idonshi ya fad’a kan ledan dake ajiye, d’auka yayi ya fito yayi sallama da mai gadin ya mik’a mishi yace mishi na Batuul da ta shiga yanzu ne, k’iran sunanta da yayi ne ya sashi jin wani iri ya juya ya koma mota ya tada ya tafi.
Tana shiga gida hanyan garden tayi ta wanke fuskanta da kyau dan kar a ce tayi kuka, da sallama ta shigo palon, ba kowa sai Aunty da Aabid a hannunta tana bashi madara, karasawa tayi cikin palon zata hau bene bayan ta cewa Aunty ta dawo taji Aunty tace “Batuul zo nan, mey ya sami idonki ya canja kala, kuka kikayi” da sauri ta ce “a ah Aunty kaina ne yake ciwo tun da naje, nace zan dawo ma Ammah tace in bari sai da yamma a dawo dani”, tana gama maganan ta hau stairs da gudu, da ido Aunty ta bita ba wai dan ta yadda da abunda ta fada din ba, tana kaiwa last stair case din taji sallaman mai gadinsu ya shigo da leda, ya gaida Aunty sannan yace “wai a bawa Batuul inji mutumin da ya kawota”, Aunty ce tace ya ajiye, yana ajiyewa ya tafi abunshi, Batuul kam tsayawa tayi tana kallonshi har saida ya ajiye ya fita tukunna ta tab’e bakinta ta tafi , dan ita ta ma manta gaba daya da batun abunda Ammah ta bata, dakin k’annenta ta bud’e ta lek’a dan a cike take da Ahmad da yaqi picking calls dinta kuma bai k’irata ba bare yazo d’aukanta , tana budewa taga dak’in ba kowa, an tattarashi tsaf sai k’anshi da sanyi yake yi kamar ba shine a hargitse ba d’azu, rufewa tayi ranta a b’ace dan taso ta sameshi ya fad’a mata dalilinshi na qin d’aukan wayan, ďakinta ta k’arasa ta bude, tana shiga ta tarar dashi kamar yadda ta fita ta bari sai d’an gyara da aka sakeyi, kayan jikinta ta cire ta shiga toilet, bath tub ta cika da ruwan dumi sannan ta shiga, tana shiga ta dinga kukan da bata san dalilin yinshi ba, sai da tayi mai isanta sannan ta fito daga cikin bath tub din ta nufi sink tayi alwala,fitowa tayi daga toilet din, gaban mirror taje ta shafa mai, ta fesa turare masu sanyin k’anshi, da ta gama ta k’arasa gaban closet dinta ta bud’e ta dauko kayan bacci, gown ne na sponge bob iya gwiwa ta saka, ta saka hula blue sannan ta shimfid’a sallaya ta hau ta tada Sallah Isha, tana idarwa ta hau makeken gadonta ta kwanta, remote din AC ta d’auka ta k’ure to the lowest degree, nan da nan d’akin ya d’au sanyi, duvet dinta ta janyo ta rufe duka jikinta dashi, wayanta taji yana ringing, kamar baza ta d’auka ba ta janyo shi da k’afa ta k’ara a kunnenta , a hankali ta amsa da “Hello” daga d’aya bangaren aka amsa da “sweetheart i was worried about you, inata trying number ki it wasnt going, kun isa gida lafiya?”, a hankali Batuul tace “Farida mun isa Alhamdulillah ina ma kan gado”, jin muryan Batuul yayi k’asa ya sata tambayanta “Batuul are you okay”, a hankali Batuul ta ce ” yeah am okay, am fine, Ya Ammah, kice mata na gode….”, katseta Farida tayi ta ce mata “Yaa Abu ya k’irani wai in fada mishi inda gidanku yake” , Baatul tace mata ” eh ina ta yi mishi describing ne bai gane ba shine nace ya k’iraki ya tambayeki amma ai tun dazu mukaxo, har ma na kwanta”, ce mata ta sakeyi “bari in barki sai da safe tunda har kin kwanta” jikin ta sanyaye ta ajiye wayan dan tasan ba lafiya bestyn ta take ba saboda ko zatayiwa ko shiru bata yiwa Farida, tasan mayb wani abun ya haďa ta da Yaa Abu
Tuki yake yana tsaki kwata kwata fitar da yayi niyyan ma fasa ta yayi, wayanshi ne yayi ringing, duba mai kiran yayi sannan ya jona wayan da speaker motan kamin ya d’auka, yana ďauka yace ” sai yanxu kika ga daman k’irana kenan” , daga daya bangaren cewa akayi cikin siririyar murya da kanaji kasan an lank’washeta “Bae kaima kasan ba da gangan naqi kiranka ba, kasan muna ta ibada ne kuma muna tare da family so….” bai bari ta k’arashe maganan ba ya katseta da cewa ” Yasu Mummy, yaushe ne dawowanku” , “su Mum na lafiya, next week zamudawo ai zakazo d’aukana ko, i even have something for you, ďazu mun fita dasu Mum munje bin Dawood naga wani turare ance shi ne latest of d month,na siyamaka dan har su prince Hamdan ma shi ne nasu for this month…..”, bai bari ta karasa maganan ba ya ce mata ” okay yanxu ina driving ne , i will get back to you when i reach home”, a sanyaye tace “Aii bae take care” ta katse wayan, kullum sukayi waya sai yayi mata hali, amma babu komai ai Mum dinta tace mata indai ta aureshi komai zaiyi normal, said yadda tayi dashi, shima har yazo ya fita sonshi,ayyanawa tayi a ranta ai tunda tana da kyau zatayi anything possible ya sota fiye da komai, tunanin hakan ne ya sata wani daria mai sauti , y’an dakin hotel din ne suka juyo suna tambayanta mey take yiwa wannan dariyan, murmushi ta sakeyi ta ce musu “Tunanin yadda zanyi da Abutturab nakeyi da yadda zai so ni in munyi aure” ta tab’a matar dake gefenta tace “Yaa zee wlhy ina sonshi, baza ki gane bane, wacce aka k’ira da Yaa zee dince ta ture mata hannu daga jikinta tace “rabu dani dallah, anyi anyi ki rabu da yaron nan kink’i, ni banga ma wani abu da yake dashi ba in banda tsawo da ya ďebo kamar isha da girman kai kaman wani basarake, ga manyan mutane nan na sonki amma kin nacewa k’aramin yaro da ya baki y’an shekaru, in banda wulak’antaki babu abinda yakeyi, dubi fa ko yanxu da kika k’irashi ce miki yayi sai yanxu kika ga daman k’iranshi, shi mesa bazai kirakin ba ďan rainin wayo kawai” taja tsaki ta ci gaba da danna wayarta, yarinyar ta sake cewa “Yaa Zee baza ki gane bane, da kinsan wahalan da nasha kamin ya fara kulani ,ke da kanki zakice inci gaba da hak’uri saboda inyi fulfilling dream dina in aureshi , kuma ai ina sonshi, tun first day dina a school nake bin shi yana shunning dina har na samu yana kulani yanxu ai bazanyi missing wannan opportunity ba, yanxu kawai jira nake muyi aure komai zaiyi daidai yadda muke so” , Yaa Zee tace mata” ke kika sani, Ni ki rabani da labarin wannan sarkin tsawon naki,” taci gaba da abinda take, tashi yarinyar tayi ta fita daga ďakin tana dariya
Aunty ce ta tura Fa’iza ta duba mata ko Batuul idonta biyu, da taje sai da ta lek’a ,hasken da ta ganine ya sata shiga , a hankali tace mata, “Yaa Batuul Aunty tana qiranki”, bata tashi ba tacewa Fa’iza “gani nan zuwa” Fa’iza na fita ta tashi tabi bayanta after ta duba fuskanta a mirror taga ya ďan zama normal , tana sauk’a k’asa taga duka yan gidan a palo kowa ya baje ledoji a gabanshi sai hira sukeyi suna dariya, Baba ne ya fara hangota yayi mata alama da tazo wajenshi, kusa dashi taje ta zauna , Ahmad ne ya kalleta ta doka masa harara, dariya yayi ya ďauke kanshi yaci gaba da abinda yakeyi, Baba ne yace mata “Da zamuje mu ďaukeki da muka fita dan Ahmad ya ce min ya bar wayanshi a gida, sai da mukayi waya da Aunty ta ce mana kun dawo” , a hankali tace mishi “Ehh Baa, inata kiran shi baya picking shine kawai Ammah tace a dawo dani, tun dazu ma na dawo”, ta karashe maganan tana hararan Ahmad da yake ta murmushi, tashi tayi ta koma wajen Aunty tace mata “Aunty gani”, “kinci abinci ne da kika shiga kika kwanta, kuma da kikace kanki na ciwo wane maganin kikasha”, kamar zatayi kuka tacewa Aunty “Naci abinci har na sha panadol, bacci nakeson yi yanxu”, Aunty tace “sai kije ki meant a”, da ta tashi tafiya ne Aunty ta nuna mata ledan da mai gadi ya shigo dashi yace nata ne, Faiza tacewa ta hawo mata dashi ta k’arasa sama ta
kwanta, binta kawai Aunty tayi da kallo dan ta san duk bacin ranta baya nunawa amma yau wani abun ya sameta,
Yana xuwa gida, ta back door ya shiga dan baya son had’uwa da kowa saboda ranshi ya gama b’aci, ďakinshi ya nufa ya buďe ya shige, toilet ya shiga ya watsa ruwa yayi alwala ya fito, pjs dinsa ya saka sannan ya shimfiďa abun sallah ya hau ,dan yaso yayi a shehuri idan yaje amma saboda yarinyar nan bai samu yayi ba sai yanxu wajen after 9, tada sallahn yayi , bayan ya idar ya gama azkar ďinshi ya hau gadonshi tare da janyo Mac book dinshi yana duba aikin da zaiyi nan da kwana huďu, yana gamawa ya kashe wutan ďakin ya kwanta
K’arfe biyar 5:00 daidai adhan din sallah Asuba ya fara dai dai lokacin Abutturab ya farka daga bacci, addu’ar tashi daga bacci yayi, k’afafuwanshi ya sauk’ar daga kan gadon a hankali, tashi yayi ya isa inda comfy fararen towels dinsa ke rataye , guda ďaya ya janyo, kayan baccin dake jikinshi ya cire sannan ya ďaura towel din ya shiga toilet, brush yayi ya watsa ruwa sannnan ya haďa da alwala ya fito, closet ďinshi ya buďe ya ciro farar jallabiya ya saka bayan ya goge ruwan jikinshi da towel, gaban mirror ya koma ya fesa turaren jéan pául Gaultiér ya k’ara da Hugo sai Arabian oud ya shafa, abin sallah ya shimfiďa yayi nafilfili, bayan ya idar ya karanta suratul Mu’minun cikin murya mai daďi, tashi yayi ya fita masallacin dake manne a jikin gidan daga waje, yana k’arasa yayi raka’atul fajr sannan ya zauna jiran Ladan ya tada sallah su fara, k’arfe 5:40 ladan ya tayar suka fara sallah, suna idar da sallah bayan y’an azkar suka fito daga masallacin, Abui da Sadiq ya hango ya k’arasa inda suke, “Nda wattu” yacewa Abui tare da mik’a mishi hannu, Abui ne ya amsa mishi da kélewa sélai, Sadiq ne shima ya mik’o wa Abutturab hannu suka gaisa, suna tafiya Abui ya k’ira sunan Abutturab, “yaushe ne tafiyanka” Abutturab ya amsa da “Na so in tafi on monday but naga i have things to cover before meeting dina da minister on tuesday, so i have decided to leave tomorrow monday”, Abui yace “okay sai kayi rescheduling flight dinka to gobe, kuma ka fad’awa Ammah dan bata sani ba, mu sai next week dawwanmu inaga” yace “okay Abui” sannan suka k’arasa cikin gida kowa yayi ďakinshi
Hasken ranar da ya hudo window ďakinta ne ya sata buďe idonta a hankali, ranan da ta gani ne ya sa ta wara y’an madaidaitan idonta ta dubi agogon dake kan bed side drawer taga 6:30, da tsalle ta tashi daga kan gadon, gashinta mai tsayi da shek’i da ya baje tana bacci ta kama ta haďe su in a messy bun, toilet ta shiga ta kuskure bakinta da Listerine mouth wash tayi maza tayi alwala ta fito, sallah ta tada , bayan ta idar tayi azkar ta fito daga d’akinta ta bud’e ďakinsu Ahmad, fridge din ďakinsu ta buďe ta ďauko ruwan sanyi ta shiga kwara musu, a firgice kowannensu ya tashi suna mitsitsika ido, Sa’eed ne yace mata “haba Yaa Batuul yanxu kuma mey mukayi kika tashemu da ruwan sanyi”, dukkansu ransu a b’ace suna kallonta suna jiran suji mey sukayi da ta katse musu bacci, “Y’an rainin wayo kunga ban fito sallah ba shine babu wanda yayi knocking min k’ofa, ai tunda baku ganni nazo gaida Baa ba sai kuzo ku dubani, amma kowanne da yaje masallaci dawowa yayi yaci gaba da baccinshi, sai yanxu nayi sallah asuba, yan rainin wayo kawai, Khalil ne yace ” toh mu mun san baki tashi bane, kuma ai Aunty ma munsan zata tasheki” Harara ta watsa mishi, Ahmad kam ko uffan baice ba dan ya san harda haushin jiya yasa ta zuwa da watsa musu ruwan sanyi suna bacci, Mus’ab ma baice komai ba, tana faďan dalilinta na watsa musu ruwa yaja bargonshi ya kwanta dan inda sabo sun saba da masifanta, saida ta gama faďanta sannan ta juya tare da banko musu k’ofa ta fita, k’asa ta sauko taga babu kowa ta koma d’akinta
11:00 ta sauko cikin abayar Al layl tayi kyau sosai, fuskanta ba komai sai kwalli da ta saka, duk y’an gidan na parlour, Su Ahmad ne suka bita da kallo ransu a b’acen abinda tayi musu ďazu,itama palon taje bayan ta gaida Baba da Aunty ta sami waje ta zauna, Baba ne yace mata “Batuul tafiyanmu gobe ne dan haka yau zakuje ku gaida su Yayya da kowa da kowa, meeting dina tuesday ne so dole mu tafi gobe, kuma kinga graduation ďinki saura two weeks, sai ki fara shirye shirye ko” tace “yo Baa”, Aunty ce tace mata “kan naki ya dena ciwon”, ita ta manta ma gaba ďaya da tayi ciwon kan k’arya, tunowa tayi da abinda ya sata yin k’arya, ďan k’aramin tsaki tayi daga ciki, a ranta tace wannan mugu ne dagaske shiyasa Farida bata sonshi tafi son Sadiq, da sauri tacewa Aunty, ” eh da nayi bacci na tashi ya dena”, “sai kije kici abinci ki fito mu tafi dan muna da wajen zuwa dayawa a yau” toh tace sannan ta nufi dinning ta bubbuďe food flaskses da kwanunkan dake kan dinning ďin, plate ta ďauka ta saka pancake guda ďaya da strawberry syrup sannan ta ďauki Fanta ta zauna ta ci a hankali har ta gama ta dawo palon tace ta gama, Aunty ce tacewa yaran “toh ku tashi mu tafi Baa Liman na jiranmu shi zai kaimu”, dukkansu sukayiwa Baba sallama suka fita, wata range rover 2013 suka dosa dukkansu, Baa Liman ne ya buďe kofan driver ya shiga, motan duk ya hargitse da surutu kowa yana faďin ga wak’an da yakeso a sa, daga k’arshe ne Batuul tace a saka musu wak’okin Wael Jassar, ana sawa duk suka fara bin wak’okin shi na farko a album din 7aareg damohom, motar cike da hayaniya ba a jin abinda wani ke faďi har suka isa gaban wani gate sukayi horn, mai gadi ne ya buďe musu su ka shiga, basu bari an gama parking ba suka buďe k’ofofin motar suka fito, da gudu suka shiga gidan suna faďin *yayya ishena*, *yayya ishena* Yayya munzo, Yayya munzo)da kanuri, wani ďaki suka buďe suka shiga, ďan madaidacin parlour ne mai kyau sai k’anshi turaren wuta yake da sanyi, suna shiga suka nufi wajen wata tsohuwa fara sol, dukda ta tsufa amma kyanta na nan, anyi mata kitson gaba da ya zubo daga gefe, na bayan kuma ta tufke shi, murmushi tsohuwar tayi ta rungeme yaran, Batuul na shigowa taje wajenta ta ture yaran daga jikin tsohuwar tare da cewa “Ku ďaga min takwara kar ku ballamin ita, tunda kuma bana yiwa takwarorinku haka”, rungume tsohuwar tayi sannan tace mata Yayya *tussuna nya rukéi*, (na daďe ban ganki ba, nayi missing ďinki), Yayya tace mata ” *nda rui sha, jirem géi*(dubeta kamar dagaske ban yadda ba), Aunty ce ta k’araso ďakin ta zauna sannan suka gaisa da Yayya, cikin girmamawa suka gaisa sannan yayya ta k’ira daya daga cikin masu aikinta, “ki kawo musu abinci da kayan sha ki jera a kan dinning,cikin kanuri ta faďi maganan don bata jin Hausa, sunajin abinda yayya ta faďa kowa ya fara faďan choice dinshi na abinda zaici, duk saida aka kawo musu abinda sukace sunaso aka jera musu, a gidan suka wuni har dare
k’arfe goman dare Baba ya iso gidan yayya shima, bayan sun gaisa da yayya sun ďan tab’a hira yace su tashi su tafi dan gobe flight dinsu eleven ne,tsaraba dayawa yayya ta haďa musu ta saka masu aikinta su kai musu mota, bayan kowa ya gama shirinshi zasu fita daga ďakin yayya ta k’ira Baba ckin ďakinta, zama tayi a kan gado shi kuma ya zauna a k’asa kanshi a duke, magana ta fara kamar haka “Batuul tace min ta gama sashen karatun nan nata amma zataci gaba, kuma har waje naji tana cewa zata, toh ni bance kar taci gaba ba amma ban yadda har waje ba, in kuma har wajen zaka fita da ita toh lallai saida mijinta , haba wane karatu ne haka da tunda aka haifi mutum yakeyinshi bai k’are ba, yarinya shekara sha shida zata shiga na bakwai amma babu abinda takeyi sai boko, toh inma uwarta ke zugaku da kai da Batuul ďin ni bazan ďauka ba, bazan yadda yarinya tayi ta girma babu aure ba, ai uwartata ma abinda ya sa na k’i ta kenan lokacin aurenku wai tana boko, toh mutane da dama ma ai sunyi bokon a gidan mazajensu, dan haka Batuul baza ta ci gaba ba sai tayi aure”, duk maganan nan da tayi cikin kanuri tayishi, tunda ta fara magana Baba bai ďago ba sai da ta gama, a sanyaye ya ďago kanshi yace mata “In sha Allah yadda kikeso za ayi Yayya, nima ďin bana son fitanta waje karatu babu muharrami, dan haka zan duba yadda za ayi”, Yayya tace “yawwa gara a duba , Allah yayi muku albarka, toh yaushe ne tafiyan naku gobe” yace “11” tace Allah ya kaimu ya kiyaye hanya sannan ta fito yana biye da ita a baya har suka k’araso parking lot, yaran nata tsokananta har Babansu ya tayar da motan tana ďaga musu hannu har suka fita daga gate ďin
Sweat pant blue ke Jikinshi da riga bak’a yana dadanna Macbook dinshi, tea ne a flask daga gefenshi idan yayi aikin sai ya ďan sha kaďan, wayanshi ne yayi k’ara ya ďauka yaga Amma keh k’iranshi, rusuna yayi yace “Hello Ammah”, daga ďaya bangaren Ammah ce ta amsa da ” ina falon sama, kazo maza ina jiranka”, tunani ya fara yi akan dalilin wannan k’ira da take mishi dan tun daga muryanta ya san ba lafiya ba, maganan Ammah ya sakeji tana cewa “banji ka amsa ba”, da sauri yace “Ammah ina zuwa yanzu” ya katse wayar, matsar da Macbook ďin yayi gefe ya tashi ya fita daga ďakin, hanyar falon sama yabi har ya isa, yana zuwa yaga Abui da Ammah a zaune tare a kujera ďaya, k’arasawa yayi ya nemi waje ya zauna akan tattausan rug ďin dake shimfiďe , a kusa da Abui dab ya zauna daga k’asa, kanshi dake duk’e ya ďago ya gaida su a tare, Abui ne ya fara amsa mishi sannan Ammah, bayan y’an seconds Abui yayi gyaran murya tare da k’iran sunan shi, “Abutturab magana zamuyi dakai kamar kullum akan dai maganan kayi aure ne, mun gaji da zaman ka haka, you are getting younger anymore, girma kakeyi”, Ammah ce tayi sauri ta karashe maganan da cewa “bazan yadda da tafiyanka wajen nan babu mata ba, wane aiki ne zakaje ka k’ara banda wanda kayi musu ba, yanxu Abui ke cemin gobe zaka tafi ,kuma kana gama aikin ne zasu tura ka waje, toh ni bazan yadda ba, kayi aurenka in yaso kaje kayi shekara goma a can banida damuwa”, Abui ne ya tareta da cewa “a ah ba shekara goma ba dai, abi komai a hankali, yanxu kai Abutturab kamin ka gama contract dinnan har su turaku waje muna so ka fiddo da mata ayi muku aure, mutuncinka ma zaifi k’aruwa a idon mutane, within two weeks kayi mana introducing wacce kake so, inma babu wacce kuka daidaita zamu samo maka a family, ga cousins ďinka ko a cikinsu ka duba, in akwai wacce tayi maka fine, in kuma babu sai ka nemo da kanka”, Ammah ce tace “ai ni Nafison ma mu nemo mishin dan da alamun bashida niyya”, Abui yace “Aure is a life time journey, he should chose his own choice dan kada a samu matsala, Allah yayi maka albarka”, baice komai ba har saida su Ammah suka gama maganan da zasuyi sannan ya ďago kanshi yace musu “In sha Allah zainyi Ammah, but inaso a ďan k’aramin lokaci, two weeks ďinnan yayi min kaďan, a k’aramin ko da one month ne, in sha Allah by then i will be done with duk abunda zanyi, sai ayi introduction ďin” Ammah ce ta sake ce mishi “Aliyu ban yadda ba, two weeks ďinnan da na faďa shi kenan, tukunna ma y’ar gidan waye kake cewa za ayi introduction ďin da ita”, sunanshi da yaji ta k’ira ne yasashi saurin ďago kanshi, don ya daďe baiji ta k’irashi ko da Abutturab ba amma yau gaba ďaya Aliyu ta ambata, a hankali yace “y’ar gidan perm sect ce Engr Abba Muhammad Jidda”, Abui ne yace “Masha Allah, ai Engr abokina ne, mutumin kirki ne sosai, ba komai kaje in mun koma Abuja sai kuyi magana da yarinyar akan zaka turo, tashi kaje Allah ya maka albarka” Amin yace sannan yayi musu godiya ya tafi, Ammah dai bata so haďin nan da ďanta ya samo ba, dukda tana y’ar Tchad amma bata so ďanta ya auri shuwa, amma haka dai ta hak’ura ba dan tana so ba, gara yayi auren da ya zauna babu mata, ci gaba sukayi da hiran Abutturab ďin da sauran y’ay’ansu bayan ya tafi
Suna isa gida bayan sun shiga ciki dukkansu suka zube a palon, Baba ne da ya shigo daga k’arshe yace kowa ya shiga ya kwanta gobe flight ďinsu sha ďaya ne dan haka kowa ya shirya da wuri, mik’ewa kowa yayi ya tafi makwancinshi ya shirya yin bacci, Batuul na shiga ďaki ta cire kayan dake jikinta ta ďaura towel zata shiga toilet, fridge ďinta ta buďe zata sha Fanta taga ya k’are, wayanta dake ajiye gaban mirror ta ďauka ta nufi kan gado ta zauna sannan tayi dialing number Janet, tana ďauka tace “Janet ki kawo min fanta ďakina , na fridge ďina ya k’are, “Janet ta amsa da to anti za a kawo miki wani abu dinne bayan Fanta”, Batuul tace “No i dont need anything else, am okay” sannan ta katse wayan ta ajiye ta shiga toilet, warm shower bath tayi ta fito daga toilet ďin, tana fitowa akayi knocking k’ofar ďakinta karasawa tayi ta buďe, Janet ce ta shigo da square serving tray na ceramic ďauke da Fanta akai, akan table ďin ďakin ta ajiye ta juya zata fita Batuul ta k’ira sunanta “Janet ku shirya da wuri gobe zamu koma,ki faďawa Fa’iza da Aunty Tabawa, karku sake delaying ďinmu kamar lokacin da zamu zo”, “Toh anti zan fada musu”, “kuma ba sai kunyi breakfast dayawa ba,amma kije wajen Aunty ta faďa miki abinda za dafa goben”, da toh ta amsa sannan ta fita, tana fita Baatul ta shirya cikin kayan baccinta na Lulu kitty purple, ta haďe gashinta cikin hula dark purple ta gama shafe shafenta ta hau kan gado, Laptop dinta na Apple ta ďauko ta ďanyi danne dannenta sannan ta kashe ta mayar kan side drawer, wayanta ta ciro a caji, kamar dama jira ake ta ďauki wayan ya fara ringing, ganin mai k’iran ya sa wani wide smile shimfiďuwa a fuskanta, dimple ďinta sai da suka lob’a deeply, wayan ta saka a kunnenta tare da tsuke fuska kamar ba ita ke murmushi ba yanxu ta Kuma yi shiru taqi magana, daga ďaya bangaren aka ce “shikenan since you wont talk, i will end d call, da sauri tace “Affaaannn” da k’arfi ta k’ira sunan har tana jiyo dariyanshi daga ďaya b’angaren, “woh lady so kike ki min bursting ear drums ko ko ya”, sake k’iran shi tayi da Affanu, “ta yaya ma akayi kika zama friend ďita ya faďa yana dariya”, “I know you love me” Batuul ta faďa mishi, ce mata yayi “waya faďa miki i love you, ai d moment you left for airport na manta da momeries and friendship ďinmu”, face ďinta tayi kalan tausayi dashi ta zumb’uro baki kamar yana ganinta tace mishi “ka manta dani, nayi fushi ma tunda ka manta ni” murya ta fara yi kamar zatayi kuka, da sauri ya fara ce mata “No no no Lulu, kar kiyi kuka mana, i didnt mean to hurt, kema ai kinsan you are my potential treasure, ai nima sai ki sani kukan” ya faďa muryanshi na rawa, kyalkyalewa ta kuma yi da dariya, ce mata yayi “dariya ma na baki ko, am offended shikenan ma goodnight”, da sauri ta tare shi, “wait wait pls, dagaske dariya ka bani how you reacted, so you care, intersting”, dukkansu biyu a tare suka sa dariya, ce mata ya sakeyi “I misssed you bestfriend”, a hankali itama tace mishi “I missed you too”, “so when y’all coming back”, Affan ya tambaya, “Gobe ina Abuja by now”, da sauri Affan ya tambayeta “Dagske Lulu gobe zaku dawo, baby na fa”, dariya Batuul tasa sannan tace “masu baby, toh ba gobe zata dawo ba sai nextweek, hope kana kula min da ita da kyau, jiya ma i was with her”, ce mata Affan yayi “i got to call her now in roqeta su dawo before next week dan i cant wait that long, I want to see her”, Da dariya Batuul tace mishi “Aii best friend, good night”, da haka suka katse k’iran, suna gamawa tayi adduan bacci ta shafe jikinta dashi, taje ta shafe duka k’annenta har way’anda ke kwana a ďakin Aunty, sannan ta tofe duka angles ďin gidan , ta kashe bedside Lamp ďinta ta kwanta
Story continues below
Bayan ya koma ďakinshi ne yaji komai baya mishi daďi, key ďin mota ya ďauka ya fita shehuri ba tare da ya cewa kowa komai ba, kai tsaye dogarai suke buďe mishi k’ofa dan sanin matsayinshi da sukayi a fada, chamber Massa ya wuce kai tsaye ya shiga, Massa ya tadda kwance a makeken gadonshi na sarauta yana waya kuma da alama yana jin daďin wayan da yake, waje Abutturab ya nema ya zauna akan ďaya daga cikin royal chairs ďin ďakin, ganin wayan da Massa keyi bazai k’are bane ya sashi tashi ya fizge wayan ya katse, “dan wulak’anci na kai minti goma ina ďakin nan, amma kakeyi kamar ba kasan ina nan ba ka zauna kana ta waya kana k’yalkyala dariya, ni banga ma abin yiwa dariya ba a waya da budurwa,mtsewww”, tsayawa Massa yayi yana kallonshi har sai da ya gama yace mishi “mik’o min wayata in ka gama” mik’a mishi wayan yayi ya nemi waje akan gadon ya zauna ya dafe kanshi, ganin da Massa yayi abokinshi ba wasa yakeyi ba yasa shi zama kusa da shi dan ya san ba komai ke sashi damuwa ba, komai girman abu yana danne zuciyanshi, dafashi yayi yace “Man whats wrong, you dont look yourself, you seem to be upset, hope dai lafiya, tell me whats wrong am dead worried right now”, ajiyar zuciya yayi yace “Su Abui ne suka ce that sun bani two weeks i should introduce to them the girl i would marry , ko kuma su nema min da kansu, wai bazan tafi project ďina ba mata ba” kuma you know i have no one at hand da zance musu gata am ready to marry, cikin jimamin abinda ke shirin faruwa da abokinshi yace “Man toh baga Ajiddeh ba, you guys go along well dan naga babu wacce ke samun attention ďinka kamar ita kuma ma she is beautiful and everything” wani kallo Abutturab ya watsa wa Massa, “wa yace maka dan kyanta nake kulata, yeah i know there is this ounce of affection i have towards her but bai kai har ince zan aureta ba, su Abui should understand su k’aramin lokaci, i need time, bana son yin mata biyu, so kaga i should be given time dan in samu right choice ďina” k’arashe maganan yayi tare da nannauyan ajiyan zuciya” Massa ne yace mishi kawai kayi introducing Ajiddeh tunda tana sonka you can make her all you like, zatayi duk abinda kake so, Ko Shehu bazaiyi siding damu ba saboda shima damuwanshi kenan a kanmu, sai dai ma ya ce a k’ara dani, Man kawai muyi addu’an abinda yafi alheri”, cigaba sukayi da hirar neman mafita daga k’arshe kawai suka yanke shawaran ya auri Ajiddeh tunda ita kaďai ce option ďin dan basu san wacce su Abui ďin zasu zab’a mishin ba, k’arfe goman dare ya mik’e yace da Massa zai koma dan yana da flight gobe by 11:00, sun fito waje Massa na rakashi inda yayi parking mota Massa ke tambayanshi, “Man ya akayi ne baka zo ba jiya inata jiranka”, tambayan ne ya sashi tunawa da duk abinda ya faru tsakaninshi da Batuul, ďan k’aramin tsaki yayi daga ciki yacewa Massa “gajiya nayi”, dariya Massa yayi yana ďan tab’a kafadarshi yace “ango tun bakayi auren ba har ka fara gajiya, toh in kayi auren kuma bazamu na ganinka ba kenan”, Abutturab bai ce mishi komai ba ya buďe motarshi ya shige tare da ce mishi “sai munyi waya, ni zan wuce”, Allah ya tsare hanya Massa yaayiwa Abutturab sannan sukayi sallama
Bayan sallah asuba babu wanda ya koma bacci, kowa shirin tafiya ya farayi, sai hayaniya akeyi a gidan, kowa ya tashi a gidan banda k’ananan k’arshe, Janet ce tayi knocking k’ofan, bayan an mata izinin shigowa ta shigo ďakin, tarar da Aunty da Batuul a ďakin tayi,Batuul na shiryawa Aunty kayanta da zata tafi dasu a cikin jaka, Aunty ce tace mata yarannan fa har yanxu basu tashi ba Janet, maza je ki k’irawo Fa’iza kuzo kuyi musu wanka dan 8 ya wuce, da toh ta amsawa Aunty sannan ta fita k’irawo Fa’iza dan suyi aikin da aka sasu, ďaya nayin wankan ďaya kuma na shafa musu mai da sa musu kaya, Batuul na gamawa tacewa Aunty “zanje in shirya” sannan ta fita daga ďakin Aunty ta isa d’akinta, wanka tayi sannan ta fito ta shirya cikin atampa exclusive green da pattern ďin yellow da bak’i, ďinkin yayi mata kyau sosai, skirt ne da peplum blouse mai three quarter hannu, ba a sa komai a jikin rigar ba sai patterns ďin atamfar aka yi mata aiki dashi, ďan kunne kawai ta saka bata sa sark’a ba, agogon gucci ta ďauka ta mak’ala a hannunta, babu wani kwalliya da tayi sai kwalli kawai da ta saka a idonta, duk da ba tsayine da ita ba, bata saka takalmi mai tudu sai slippers din versace baqi da ta saka, luggage ďin kayanta ta jawo ta ajiye bakin k’ofa sannan ta ďauko k’aramin bak’in gyale ta ajiye a kafaďarta, fitowa tayi ta sauko k’asa taga kowa ya shirya cikin kayan alfarma suna breakfast, shiyasa ma bata fara saka abaya ba dan tasan Baba sai yayi mata maganan abayar, k’arasawa tayi itama ta janyo kujera ta zauna , Aunty da Baba ta gaida a tare suka amsa mata sannan duka k’annenta suka gaisheta suma, Bismillah tayi ta fara cin abincin itama, a nutse suka gama breakfast ,tara da rabi dai dai aka fara fita da kayansu, manyan mazan kowa da hand luggage ďinshi a hannu, na Aunty, Batuul dasu Hafix kuma yana hannun su Janet, Baba ne shima ya sauk’o daga bene rik’e da nashi, Batuul na hango shi da sauri taje ta karb’a ta k’arasa dashi k’asa ta bawa driver su fita dashi, Kanta ya shafa Yace ya gode , Baba na k’arasowa duk suka tashi suka fita suka nufi inda motocin gidan ke pake, Baa Liman ne da Sunday driver zasu kaisu airport, Batuul da Ahmad, Sa’eed, Khalil, Mus’ab, Janet da Tabawa mota ďaya suka shiga while Baba, Aunty, Yusra, Mahir, Hafix da Aabid da Fa’iza na mota ďaya, sai da sukayi addu’an fita daga gida da ayatul kursiyu kamin drivers ďin su fita daga gidan
Hanyan Maiduguri international airport suka bi, goma da rabi suka isa, ana shiga cikin airport ďin heartbeat ďin Batuul ya k’aru idonta ya fara tara hawaye, addu’a ta soma har taji ya ďan ragu, bayan sun shiga har ciki sun sauk’a ta isa wajen Aunty ta ce mata, “Aunty tunda muka zo Maiduguri heartbeat ďina baya running at a normal pace, yanxu ma muna shigowa airport naji ya k’aru sosai”, Aunty ce ta dube ta ta tuna da ranan da ta dawo idanunta sunyi ja, ce mata tayi “baki da gaskiya shi yasa yak’e karuwa”, dariya sosai Batuul tayi sannan tace “kai Aunty, wane rashin gaskiya zanyi har heartbeat ďina ya rik’a karuwa, ni dai babu abinda nayi”, ta juya ta tafi, binta Aunty tayi da ido dan itama ta tab’a shiga yanayi irin na Batuul na k’aruwan bugun zuciya, murmushi tayi ta girgiza kai sannan ta tattara kan yaran sukayi departures waiting room suna jira a k’ira su in jirgi ya shirya