BATUUL CHAPTER 13

BATUUL






CHAPTER 13




Hade rai Abuturrab yayi yana mata wani mugun kallo yace “if I shud slap yhu! Na maki wani abun ne kike min kuka, waye ya sauke ki a mota nace” share fuskar ta tayi ba tare da ta d’ago ba tace “A frnd!” Yana mata wani irin kallo yace “A frnd? Male or female” a takaice tace “Male” wani xaro ido yayi cikin tsawa yace “What, Male? Da aure nawa kanki kika hau motar wani kato, are yhu insane?” Wani takaici ne ya rufe ta wasu hawayen suka dinga xubo mata, bata san lkcn da ta mayar masa da amsa ba tace “Ohh ashe kasan da auren ka kaina, toh ai ni ban san da haka ba, nayi xaton wanda ka raka airport kadae auren ka ke kanta” tana kai wa nan ta nufi stairs ta bar sa wajen tsaye, bin ta yayi da kallo baki bude, har ta haura sama, sae kuma ya shafa kai yana murmushi ya koma cikin Palo ya xauna, ba dai kishin sa Batuul take ba, No! Ya ma san it’s impossible tunda ba son shi take ba. Batuul kam tana shiga daki ta jefar da jakar hannunta tayi xamanta gefen gado, sae dae banda tukuki babu abinda xuciyarta yake, ta fi minti goma xaune kafin ta mike ta rage kayan jikinta ta shiga toilet, warm shower ta sakar ma kanta, ta kusa minti sha biyar a bayin sannan ta fito daure da towel, gaban mirror ta nufa tayi shafe shafenta, xata dauki kaya a closet dinta ta ji wayarta na ring, juyawa tayi ta koma gaban mirrorn ta dauki wayar, ganin me kiran yasa tayi murmushi ta daga tare da sallama “Tace Ammah ina yini?” Maimakon ta ji muryar Ammah sae taji kmr muryar Anty Amnah, daga daya bangaren Anty Amnah tace “Kina ji na Batuul?” A d’an kunyace Batuul tace “Ina ji Anty ina yini” don kunyar matar ita dai take, Anty Amnah tace “Lfya lau Batuul, ya ku ke gaba daya” Batuul tace “Lfya muke Anty” Anty Amnah tace “Toh madalla, cikin kayan da aka kawo maki kinga wani parcel da aka yi wrap kuwa” Batuul ta d’an yi shiru tana tunani, Anty Amnah tace “shi kadae ne karami cikin kayan” Batuul tace “Eh na gan shi Anty” Anty Amnah tace “Yauwa! Kin bude kuwa” girgixa kai Batuul tayi kamar tana ganinta tace “A’a Anty, ina ce turare ne ae” Anty Amnah tace “A’a ba turare bane, maxa dauko yanxu ki bude in maki bayani” xaro ido Batuul tayi tunawa da tayi ae duk kayan na can gidan, tace “Toh Anty bari in dauko” ajiye wayar tayi ta fita da sauri ta sauka Palo, Abuturrab na xaune har lkcn ya jinginar da kai jikin kujera idonsa lumshe, ta wani hade rae ta tsaya gabansa tace “Ya Abu, Anty Amnah ta kira wae xata min bayanin wasu daga kayan da aka kawo kuma basa nan ai” a hankali ya bude ido yana kallonta, gyara xama yayi da sauri yana ci gaba da kallonta, jin yaki cewa komae tace “Kaji, she’s still on the line fa, ni ban san me xan ce mata ba” ko kadan bae san ma abinda take cewa ba, ganin haka yasa tayi saurin kallon kanta ta ga me yake kallo, wani kara ta saki ganin ashe towel ne jikinta har lkcn, ta juya da sauri xata bar wajen yayi saurin fixgota ta fado kansa, tsorata tayi ta shiga turasa xata mike yaki sakinta, tace “plss ya Abu, she’s still on the line….” Bata rufe baki ba taji bakinsa cikin nata, still tayi na wasu yan dakiku kafin ta fara kokuwa da shi, duk ta rude, shi kam bae ma san tana yi ba, kan kace me sae ga su a kasa, nan jikinta ya dau rawa tana hawaye, danna bell da aka yi yasa ya saketa da sauri, ita ma ta mike a gigice ta koma baya don Ajiddeh ce kawae ta fado mata, a tare suka mike ita ta nufi sama da sauri shi koma yayi gun kofa, murda kofar yayi ya ga drivernsa ne David, ya sauke ajiyar xuciya yace “It’s ok david, she’s back minutes ago” Batuul kam daki ta shige ta fashe da kukan da bata san dalilinsa ba, wayarta ta dauka ta ga Anty Amnah ta kira ya fi a kirga, wani kiran nata ne ya kuma shigowa ta dauka da sauri, ta fara kame kame “Anty kiyi hakuri, dama naje ina dubawa ne, ga gashi na gani” Anty Amnah tace “Yauwa toh kin bude” xaro ido tayi sae kuma tace “Eh na bude” da sauri ta juya jin an murda kofar dakin, Abuturrab ya shigo, sunkuyar da kai tayi ta ci gaba da sauraran Anty Amnah, ganin ya nufota ta bar wajen da sauri ta koma can karshen dakin, bin ta yayi, ta kuma barin wajen da sauri ta ga ya kuma biyo ta, kamar xata yi kuka take kallonsa gashi ko kadan bata ma gane bayanin Anty Amnah, shi kam murmushi kawae yake yana kallonta, ta haye kan gado shi ma ya bi ta, rudewa tayi jin Anty Amnah na cewa “Hello Batuul are yhu there” kai ta shiga gyadawa tana koma wa baya tace “Eh eh Anty!” fixgota yayi ta fado kansa, bata san lkcn da tace “Wayyo ya Abu kayi hakuri pls” Anty Amnah da ta saki baki tace “Meye haka?” Kamar xata yi kuka tace “Anty ya Abu ne ya ki ya bar ni in ji me kike cewa” Anty Amnah tace “Ji min fitsararre da’alla ka fita ka ba mu waje” Abuturrab ya danne dariyarsa don ya ji ta sarai ya rungumo Batuul jikinsa yace “Toh Anty sorry na tafi” lamo Batuul tayi gabanta na faduwa, Anty Amnah tace “Ya tafi?” A hankali ta dago kai tana kallonsa ya mayar da kanta kirjinsa, tace “Uhm Anty” kunnensa ya kai dai dai nata don jin me Anty Amnah ke ce mata, Anty Amnah tace “Yauwa, wannan garin da kika gani me yawa da milk xaki kada ki dinga sha, shi kuma dayan da honey, you make sure you do that frequently,” Batuul tace “Anty na Meye?” Anty Amnah tayi dariya tace “It will make yhu fresh kiyi kyau abun ki, sannan akwae tiger nut da date da aka hado maki cikin kayan sae ki sa ya siyo maki coconut kin dae san yanda xa ki sarrafa ba sae na gaya maki ba ki maida shi drink din ki, sannan ki xama me yawaita shan kayan itatuwa kin ji” daga nan Batuul ta fara gane inda xancen Anty Amnah ya nufa ta ji wani mugun kunya ya rufe ta ga Abuturrab na sauraren Anty Amnah shi ma, a hankali ta dago kai tana kallonsa ta ga kallonta yake yana murmushi turasa tayi ta mayar da wayar daya kunnenta, ya kuma kankameta yana dariya ciki ciki ya kai kunnensa inda ta maida wayar, bbu yanda ta iya haka ta tsaya tana sauraren Anty Amnah, kunya duk ya isheta, ita kanta Anty Amnah tana yi ne tana jin nauyin wasu abubuwan, can dae tace “Bari dae xan maki text kin ji” da sauri Batuul tace “Toh!” Anty Amnah tace “bari in kai ma Ammah wayar ku gaisa koh” Batuul bata iya cewa komae ba har bayan wasu ‘yan mintuna ta ji muryar Ammah, suka gaisa Ammah na tambayarta gida tace “Lfya Ammah ina farida” Ammah tace “Tana lfya bitti, ina yayar ta ki” Shiru Batuul tayi sae kuma tace “Ae ta taho Nigeria daxu” saketa Abuturrab yayi da sauri yana kallonta, irin kallon me yasa xata fadi din nan, Ammah tace “Haba lfya dae koh?” Batuul bata damu da kallon da Abuturrab ke mata ba tace “Wae mumynta bata da lfya” Ammah tace “Ayya, ae ko ba mu sani ba nan ma, gobe xan je idan Allah ya yarda in dubo ta, Allah ya sauwake” Batuul tace “Ameen” Ammah tace “Ina Abun fa?” Batuul ta dan kallesa sannan tace “Yana Palo” Ammah tace “Toh ki dae maida hankali a karatu kin ji Bitti, ki kula da tsaftar jikin ki da na dakin ki, Allah maku Albarka” Batuul tace “Ameen Ammah na gode” nan suka yi sallama Batuul ta ajiye wayar, yana mata wani irin kallo yace “na aike ki kiyi announcing matata ta taho Nigeria” kokarin sauka Batuul ta shiga yi daga kan gadon ya fixgota, ta fashe da kuka tace “Don Allah ya Abu ka bari in sa kaya plss” d’an murmushi yayi yana kallon cute lips dinta yace “Wae me Anty Amnah take maki bayani a kai?” Da sauri ta dauke kai ta fara kokarin kwace kanta tace “Oho!” Ya bude ido yace “Oho ma xaki ce? Meye amfanin fruits din da tigernut drink da ta ce ki dinga sha?” Kamar xata yi kuka tace “Wayyo ni ma ban sani ba fa” a hankali ya daura bakinsa kan wuyarta wanda hakan sae da yasa jikinta ya dau rawa, murya can kasa yace “Toh in fada maki na menene ni?” Rikicewa tayi tace “Noo” yace “Okk then, which means kin sani, oya fada min kar in nuna maki abinda take nufi” ta fashe da kuka tace “Allah ban sani ba ya Abu” +Jawota yayi ya d’aura ta kan cinyarsa yasa hannayenshi cikin towel d’in dake jikinta, numfashinta ne taji yana neman d’aukewa jin hannayenshi a k’ugunta, kuka ta saka sosai tace “Yaaa Abuuu dagaske ban sani ba, kayi hak’uri
ka barni”, dariya ta bashi ya sake janyota jikinshi ya d’aura bakinshi kunnenta, cikin rad’a yace mata “then, shine zan nuna miki abinda take nufi”, girgiza kai ta shiga yi tana hawaye, bata ankara ba sai ji tayi ya juyo da ita tana fuskantarsa, rintse ido tayi dan bata iya kallon idonshi, jikinta sae rawa yake, cikin wani irin murya da taji har cikin ranta yace “open your eyes”, sake rintse su tayi kamar abinda yace tayi kenan, a hankali ya sunkuyo yayi kissing idon nata d’aya, wani irin shock taji yabi jikinta, sake rintsewa tayi hawayen na dad’a silalowa, d’agowa yayi yana kallon yadda jikinta ke shivering, kirjinta sai heaving yake, murmushi yayi ya sunkuya ya sake kissing d’ayan, nan ma shivering jikinta ya dinga yi, d’agowa yayi ya sake kallon k’aramin pink lips d’inta da hawaye ya jik’a, har lokacin hannunshi bai bar cikin towel dinta ba, sunkuyawa ya kuma yi yayi brushing lips d’inshi kan nata, a tsorace ta bud’e ido tayi ‘yar kara dan ita yanzu Yaa Abu ya fara bata tsoro, murmushi yayi ganin ta bud’e ido don dama haka yake so, lips d’inshi ya maida kan nata ya shiga yi mata wani deep kiss, wani irin ajiyar zuciya ta sauk’e jin yadda yake kissing d’inta, a hankali ya kwantar da ita kan gadon har lkcn bakinsa na nata, ta rike towel dinta gam jin yana kkrin cire mata, kuka sosae take tana kokuwa da shi, da kyar ta kwace bakinta ta turasa da duk karfinta ta mike xaune tana kuka sosai ta shiga komawa baya tace “Am on my period ya Abuu” kallonta ya tsaya yi da idanuwansa da suka sauya kala ko kifta wa bae yi yana sauke numfashi a hankali, ta tsorata ba kadan ba, xata sauka daga gadon ya fixgota yana kallonta cikin husky voice dinsa yace “Na fiki sanin u are not clean, Laifi ne don nayi kiss din ki, ke baki ji dadi ba ma na hada baki na da naki?” Sunkuyar da kai tayi jikinta na rawa bata ce komae ba, murmushi yayi yana kallonta cikin sanyayyan muryarsa yace “xaki gaya min ma’anar tsoron nan nawa da kike, soon” mikewa yayi ya nufi kofa ya fice daga dakin, ta bisa da kallo xuciyarta na bugawa.


+

Bayan Ammah ta gama waya dasu Batuul, Ammah ta juyo ta dube ta tace “Amnah ashe mahaifiyar Hauwa bataji dad’i ba wae”, da mamaki Anty Amnah ta dubi Ammah tace “wacce Hauwa?”, Ammah tace “Ajiddeh ko, matar Abu”, baki Aunty Amna ta tab’e tace “Au! Allah ya bata lafiya”, taci gaba da abinda takeyi, Ammah tace “kaji min yarinya, toh fa har Hauwan ta taho wae yau, kin ga kenan jikin yayi tsanani, ai baza a daka ta halinta ba, auren d’an uwanku ne kanta, dan shi zakuyi ba dan ita ko halinta ba”, Aunty Amna tace “Ammah bance komai bafa, addu’a nayi mata”, Ammah tace “kin dai ji, tun wuri ku gyara halin nan naku”, da murmushi Aunty Amnah ta dubi Ammah tace “Allah ya k’ara nisan kwana Hajiya Ammah, yadda kikace haka za ayi”, hararanta Ammah tayi tace “tashi ki koma gidanki, nasan su Nawal da Babansu na can suna jiranki”, girgiza kai tayi tace “Ammah kullum sai kin korani in nazo gidan nan, can ma in Babansu na nan babu ruwansu dani shima haka, tare sukeyin komai nasu basa sani, in kuma a can ne baya nan har rasa yadda zanyi dasu nakeyi, shiyasa nake zuwa gidan nan, amma kullum sai an korani”, Ammah tace “da bakya barinsu ai da zasu na sakoki a abubuwan nasu, ni yanxu tashi ki tafi, nima yanzu zan shirya a kaini gidansu Hauwan inji ya jikin mahaifiyar tata” mik’ewa Aunty Amna tayi tareda ziran gyalenta tace “Ammah kinga sai muje a tare mu dubata, ko na koma babu abinda zanyi musu in banda wahala da zasu taramin”, Ammah tace “A ah ban yadda ba, kama hanya ki koma gidanki sun fi buk’atarki fiyeda zuwa gaisuwan da zakije yi, nima da driver zanje yanzu in dubota, daga baya sai mu koma da Abui”, kamin Ammah ta gama magana Aunty Amnah ta shiga dialing number a wayarta, ana d’auka tace “Hello honey, zamuje mu duba Maman matar Abutturab tareda Ammah bataji dad’i ba wllj, you guys should not miss me nasan zakuyi, I will b back shortly”, murmushi yayi yace “as though bamu saba ba, you know we are not going to do that, ki gaida Ammah, Allah ya bata lafiya ita kuma, ki gaishesu”, tafiyanta Ammah tayi dan tasan halin Amnah, sama ta haura daga nan, Aunty Amnah ma dariya tayi tabita a baya, basu jima da hawa ba suka sauk’o, Aunty Amnah na riqe da keyn mota, tare sukaje har gidansu Ajiddeh a WUSE II, a bakin gate suka tarar da masu gadin su Ajiddeh, da sauri d’aya daga cikinsu ya taso ya fara musu magana cikin Hausarshi da ba dai dai ba yace “Sannunka da zuwa Hajiya, kazo wajen dayan Hajiya na ciki ne”, kai Aunty Amnah ta gyad’a mishi tareda cewa “Ehhh”, Allahumma salli Ala, kamar jira yake ta gyad’a Kai ya fara zuba “Hajiya, ai Hajiyan ciki dinma baya nan, kwananshi biyu Kenan, dayan Aunty dinne ya fara tafiya tun ya dade sai kwana guda biyu sun wuce sai babban Hajiya din shima ya tafi, toh tun rana din har yanzu basu dawo ba, Alhaji ne kawai yana nan sai masu yin aiki din na gidan suma y’an iska tun Hajiya Babba da ya tafi basa bamu abinci mai dadi yirin na da, toh munason Hajiya ya dawo, Dan Allah kayi mishi waya sai kace mangal ne yace ya dawo Dan ……..”, hannu Aunty Amna ta d’aga mishi tace “Kai ka tabbata, Hajiyar gidannan fa nake nufi”, ta nuna mishi gidansu Ajiddeh, juyawa yayi ya dubi gidan sannan ya juyo yana kallonta yace “Ye shine gidanmu din ai, gida na Alhaji namu, sunanshi ya fada a TV munji ma lokacin Abba Ahmad Jidda”, kallon juna Aunty Amna da Ammah sukayi jin bayanin mai gadin, Ammah ce tayi magana wannan karon tace “Hajiyar gidan ba rashin lafiya tayi aka kaita asibiti ba?”, kai ya shiga girgizawa kamar zai yadda k’asa . “Hajiya baije asibiti ba, yapot ne Abor ya kaishi ya tafi gari nasu can”, da mamaki Ammah take dubanshi tace “Toh Hauwa kuma fa, ta dawo itama ko tare sukayi tafiyan”, kai ya d’aga alamar yana tunani sannan ya kallesu yace “Hauwa din ni ban sanshi ba, ba a gidan nan yake ba”, dariya Aunty Amnah tayi tace “Toh mangal ai Hauwan macece ba namiji ba, Ajiddeh fa muke nufi, wacce tayi aure”, yace “Owo, ai baka fadamin Aunty ne kana nema ba, ai shi din yayi auren tun ya dade, so daya ne naga ya dawo gida tun lokacin da yayi aurenshi ya tafi da miji mai kyau wannan, yana bamu kudi in yazo kullum, Kai wannan mutum da Aljanna ne nace”, Kai Aunty Amna ta gyad’a tace mishi “Toh Mangal mun gode, in sun dawo zamu dawo muma”, ta ciro kud’i daga jakarta ta mik’a mishi, godiya ya dingayi musu yana washe baki, suna barin k’ofar gidan Aunty Amnah ta dubi Ammah dake tunani tace “Ammah kinji wai basa nan, kuma Ajiddeh ma batazo ba, can kuma su Abu sunce miki ta dawowa mamarta ba lafiya, anya wannan abin da akwai kanshin gaskiya kuwa?”, Ajiyar Zuciya Ammah ta sauk’e tace “Amina koni abinda na kasa fahimta kenan, kuma kinji fa wai ita Ajiddeh ma bata nan, toh Allah dai ya tsare”, baki Aunty Amna ta tab’e tace “dama can ni Ammah hankalina bai kwanta ba, Allah dai ya rufa asiri”, “Amin”,basu sake yin maganan ba har suka isa gida, sai da ta sauk’e Ammah sannan tayi mata sallama ta wuce nata gidan, Ammah na isa gida ta buga waya Maiduguri, nan take ta bada order akan ayi addu’a da sauk’an Qur’ani ta tura musu kud’in sadaka, don ga dukkan alama ba abun kirki ya dawo da Ajiddeh gida ba.





Batuul ta kusa minti sha biyar xaune kan gadon bayan fitarsa ga yunwa da taji ta fara ji, mikewa tayi daga karshe tana share hawayen fuskarta ta nufi closet dinta, shiryawa tayi cikin y’ar gown mara hannu purple mai kyau, tana kkrin fiddo hijab da xata daura kan kayan ya shigo dakin, still tayi gabanta na faduwa, dad’da’dan kamshin turarensa ya cika dakin, a hankali ta juya tana kallonsa ta ga tsayawa yayi bakin kofar dakin yayi folding din hannunsa yana kallonta, maxa tayi ta dauke kai ta ciro hijab dinta xata sa yace ” Drop that!” zumb’uro baki tayi tace “Ni sanyi nake ji” murmushi yayi yace “Did you just pout?”, maza tayi ta maida bakin da ta zumb’uro ta girgiza Kai, karasawa yayi ya fizgo hannunta ta kusa fad’awa kanshi, bata ankara ba sae ji tayi ya hade bakinsu, sai da yayi kissing d’inta son ranshi sannan ya saketa, yana kallon idonta dake xub da hawaye yace “if you pout again, I will do more than this”, hannunta ya kama tana hawaye suka fita daga dakin suka sauka downstairs, makullin motarsa ya dauka a palon sannan suka fita, shi ya bud’e mata motar ta shiga sannan ya zaga nashi side d’in, sai da ya tada sannan ya rik’o hannunta ya fara driving, a hankali yace “kin ma ci abinci yau kuwa?” Kin cewa komae tayi, yayi murmushi yana driving dinsa, har suka isa babu wanda yace komai sai murza hannayenta da yake cikin nashi, ganin gaban gidan da yayi parking yasata yin murmushi don haka kawae take son gidan ita dae, juyowa yayi ya dubeta ganin yadda fuskanta yayi lighting da murmurshi, hannu yasa ya juyo fuskanta tana kallonshi, a hankali ta sauk’e idonta kasa, giranshi ya d’aga yace “My wife’s house, don’t be over joyed being here uhh?”, baki ta tab’e ta had’a rai ta janye fuskanta tareda bud’e motan ta fita, shima d’in murmushi yayi ya bud’e ya fita.Had’e rai tayi tareda zumb’uro d’an bakinta ta tsuke shi tayi gaba ta bar sa nan tsaye, sai da taje bakin k’ofa ganin k’ofar glass d’in rufe yasa ta tsayawa, rau rau tayi da ido ta juyo xata kallesa suka kusa cin karo, sadda kanta tayi k’asa zata juya ya saka hannunshi waist d’inta ya juyo da ita, fuskanshi dab da nata har tana jin numfashin sa na brushing jikinta da kamshin turarenshi mai dad’i, ya dan wara mata ido yace mata, “mey ya hanaki shiga, ai na fad’a miki its my wife’s house, ni kad’ai keda access to it, da kinace zaki iya bud’eshi ne”, bakinta ta zumb’uro mishi ta d’auke kai zata juya, hannu yasa ya juyo da kanta yana kallon fuskanta yace “Did you just pout again”, kai ta shiga girgizawa da sauri dan ita bata ma san tana yi ba cikin murya kamar zatayi kuka tace “Yaa Abu banyi ba, kayi hakuri”, murmushi yayi ya d’auke idonshi daga kanta sannan ya jawo hannunta sukayi k’ofar gidan, hannunta ya d’aura kan security lock d’in dake mannne jikin bangon, k’ofan ne ya bud’e da kanshi, da mamaki ta kalleshi, smirking yayi tareda d’age mata girarshi d’aya, kauda kanta tayi kamar bataga abinda yayi d”in ba, hannunta ya kamo cikin nashi su shiga, tur jewa tayi nan gun taqi motsi, da mamaki ya juyo don ganin mey ke damunta, dawowa yayi gabanta yana kallon fuskanta yace “Are you okay”, tsuke bakinta tayi ta juyar da kanta, hannunshi yasa ya juyo da fuskan nata tana fuskantar shi yace “Hey!, talk to me, what’s wrong with you”, raurau tayi da idonta taqi ce mishi komai, sassauta muryanshi yayi yace “mey ke damunki wai”, baki ta sunkuyar da kanta cikin sanyi tace “you just said I shouldn’t be overjoyed being here, its your wife’s house, so why asking me wats wrong?”, abinda ta fad’a da yadda tayi maganan ne ya bashi dariya amma ya dake, had’e rai yayi yace “and what does that have to do with entering in, in zaki shigo ki shiga, you are wasting my time”, hawaye ne ya shiga taruwa idonta, juyawa tayi zata bar wajen, yasa hannu ya fixgota, cak ya d’agata ya rungumota, ko’k’arin sauk’a ta shiga yi daga jikinshi tana wuntsila k’afafu, matsetata yayi k’irjinshi sannan ya sunkuyo daidai kunnenta yace “if I should slap you right away, ina miki wasa ne”, lamo tayi jikinshi ta rintse ido tana shak’ar k’anshin turarenshi mai dad’i, bata bud’e ido ba sai da taji ya direta kan lallausan gado, a hankali ta bud’e lumsassun idanuwanta ta sauk’e kansa, ya kwanta gefenta ya lumshe ido, kyakkyawan fuskanshi ta tsurawa ido, lumsassun hazel like idanunshi da lashes yabi ya kwanta, sai chiseled nose d’inshi, da d’an k’aramin plumpy pinks lips d’inshi, tab’e baki tayi ta d’auke Kai a ranta kuwa haushin kanta taji na kallonshi da ta tsaya yi bayan bama wani kyau bane dashi, a hankali ta sake juyowa bayan kamar 3mins, har lokacin yana kwance kuma bai bud’e ido ba, Idonta ne ya fad’a kan broad k’irjinshi da buttons d’inshi na sama guda biyu da suka bud’e, gabanta ya fadi ba kadan ba, a hankali ta dinga jin abu na yawo spines d’inta, rintse ido tayi dan batason cigaba da jin abinda take jin, samun kanta tayi da son jinta kwance jikinshi, ita kanta ta rasa gane dalilin hakan, ta kuma runtse ido xuciyarta na double flipping, dai dai lkcn da ya bude nasa ya juya yana kallonta, a hankali ya mirgina kusa da ita ya dagota ya mai da ita kan faffad’an k’irjinshi, kamar wacce akayi electrocuting a firgice ta bude ido ta yunk’ura xata sauka daga jikinsa, kamin ta sauka taji ya sako hannayenshi a waist d’inta ya dad’a rungumota jikinshi, ajiyar zuciya ta sauk’e tareda yin lamo tana jin yadda heartbeat d’insu ke gudu lokaci guda, hannu yasa
kan gashinta ya warware k’ullin da ta yiwa gashin, ya d’aura fuskanshi kan lallausan gashin nata yana shak’ar k’anshin da sukeyi mai dad’i.



+

    Ajiddeh kam tun a airport tayi magana da Mummy tace mata suna Ndjamena, tana sauk’a airport a Nigeria ta sake booking wani ticket d’in da zai kaita har can d’in, awanta shida tana zaune kamin jirgi yazo suka tafi ko cikin gari bata shiga ba, taxi ta tara ya kaita har hotel d’in da su Mummy sukace mata sunyi lodging, kai tsaye ta wuce d’akin da suke bayan ta sallami d’an taxi,  knocking k’ofar d’akin tayi  ta tsaya tana jiran a bud’e mata k’ofa, Yaa Zee ce ta bud’e mata k’ofan, babu yabo babu fallasa suka gaisa tun daga bakin k’ofa, Mummy da Aunty Jainaba ne zaune d’akin hotel d’in, k’arasawa tayi itama ta zube kan makeken gadon tana maida numfashi, takai minti biyu a haka sannan ta mik’e daga kwancen da take tana kallon Mummy tace “Mum sannunku”, sannan ta juya ta dubi Aunty Jainaba dake kallonta itama, murmushi tayi mata tareda mik’ewa tana k’ok’arin rage kayan jikinta tace “Mummy duk abinda zamuyi cikin kwana biyu zamu gama dan cewa zaiyi zai biyoni, dan da k’yar na samu ya hak’ura bai biyonin ba, jarababbe, dan haka yau da gobe ayi komai mu koma da wuri”, baki Aunty Jainaba ta tab’e tace “Dan shi sarkin k’wak’war mata ai sai ya biyo kin, kwana biyun da zakiyi shine harda wani kuzo tare, ai ko da yaxon ma kuma babu abinda zai hanamu tahowa”, Yaa zee ce ta taho riqe da can drink da ta d’auko fridge ta bayan ta rufe k’ofan, zama tayi tana kallon Mum tace “mummy kinsan mutumin nan appointment yake badawa, in bakazo ba time ya wuce sai dai a sake booking, Ku shirya mu wuce tun wuri kamin time d’inmu ya k’ure muyi asara, ba musu su Mum aka hau shirin tafiya, lokacin Ajiddeh ta fito cikin toilet d’aure da towel har ta watsa ruwa, itama shirin ta hau yi, suna gamawa suka fito waje, taxi suka tare sukayi mishi kwatancen inda suke son zuwa, babu b’ata lokaci ya fad’a musu amount d’in da zasu bashi sannan suka d’au hanya, tafiyar awa uku suka isa, driver ya tsaya dab inda suka mishi kwatance, gidane d’an madaidaici mai kyau, gabanshi da bayanshi kuma duk jeji ne,  da mamaki Ajiddeh ta juyo tana kallonsu tace “nan ne gun?”, kai suka kad’a mata a tare, cewa tayi “ca nake wajen wannan mutumin zamu koma na kwanaki”, Aunty Jainabace tace “wa?, wa zai koma wajen munafikin nan, ai kud’inmu kawai yacinye babu wani aiki da ya iya, macuci ne, bok’an k’arya”, (Lol boka ma harda na k’arya da gaskiya, Allah ya tabbatar damu kan shiriya), Ajiddeh ce ta ciro kud’in ta baiwa mai taxi kud’inshi, yana tafiya suka shiga knocking, mai gadine ya bud’e musu gate d’in gidan bayan ya gama yi musu tambayoyi sannan yayi musu jagora har palon gidan, palone babba, babu komai ciki sai carpet da aka shimfid’a su wasu throw pillows, wani farin dattijo ne zaune yana sanye da farin kaya da dogon farin gemunshi, gefenshi kuma littafai ne tuli guda, a tare sukayi sallama, saida ya amsa musu sannan suka shigo daga ciki suka samu waje suka zazzauna, shi ya fara yi musu magana kamar haka, “nasan abinda ke tafe daku baki d’ayanku, Keh!”, ya nuna Yaa Zee yace “senator Gamji ke son aurenki amma yana da mata ku kuma baku son mai mata, ita kuma wannan”, ya nuna Ajiddeh yace “tabbas akwai wani al’amari tattare da ita mai rikitarwa da ni kaina na kasa fahimta, abune babba da ya shige min duhu na kasa gano komai game dashi duk iyawata, kuma shi wannan abun na tare da ita dan har ya faru ya k’are sannan ba alheri bane gareta”, a tsorace suke jin bayanin malamin da abinda yake fad’a musun, a d’arere mummy ta kalli malamin tace “Allah gafarta malan, wane abune haka har zaifi k’arfinka, mu nan munyi maka alk’awari daga miliyan goma har zuwa hamsin zamu iya badawa in dai aikinmu zai yi yadda mukeso, Allah gafarta malan, a taimaka a dubo mana wannan abun dake shirin jawo mana matsala”, wani shu’umin murmushi yayi yace “ai ni d’in nan duk abinda kikaga banyi shi ba a fad’in garin nan toh tabbass babu mai iya yi dan ni keda iko ga kowanne aljani da muke amfani dasu, dan haka ku kwantar da hankulanku, anjima da yamma za a fara aiki, yanzu haka masauki za a kaiku kamin yamma tayi, su wad’anda za ayiwa aikin kowacce d’akinta daban, ku kuma za a had’eku d’aki d’aya ku da babu aikin da zaku buk’ata, Dan aikin nada son sirri”, hakan kuwa akayi, wani d’an saurayi ne ya kaisu d’akunan da aka umurceshi da ya kaisu, y’an madaidaitan d’akuna ne masu kyau ba laifi, Zainab da Ajiddeh aka basu d’ad’d’aya kowannesu sai mummy da Aunty Jainaba aka had’esu a guda d’aya.





        A hankali Abu ya d’aura plumpy lips d’inshi kan goshin Batuul yayi pecking, haka ya dinga yi har saida ya sauk’o wuyanta, babu abinda jikinta keyi in banda rawa, k’ok’arin barin jikinshi ta shiga yi amma bai saketa ba, a nutse ya kwantar da ita kan gadon ya d’an sunkuyo kanta, sai lokacin tayi regretting dadewan da tayi kwance kan gadon, hawaye ne ya shiga silalowa daga idonta, baki ta bud’e zatayi magana Abu ya had’e bakinshi da nata, sosai ya shiga kissing d’inta, numfashinta ne ya kusa d’aukewa jin irin abubuwan da yake mata, kuka ta fasheda tace “Yaa Abu dan Allah kayi hak’uri plss bana son irin haka”, baima san tana yi ba yaci gaba da abinda yakeyi, Batuul kam kuka takeyi sosai, saida taji ya fara wuce limit kuma duk magiyarta bai sarara mata ba tace “Yaa Abu am not pure wllh, kayi hak’uri ka barni bazan sake ba dagaske”, sai da ya jagwalgwalata son ranshi kamin ya saketa ya fad’a gefenta yana maida numfashi, hannu yasa ya jawota jikinshi ya rungumeta tsam jikinshi ta gefe tareda kwantar da ita kan faffad’an k’irjinshi, kuka kawae take idonta a rufe, a hankali yayi brushing lips d’inshi kan nata tareda mata light kiss, har lokacin idonshi lumshe suke shi ma, sunfi awa d’aya a haka sai ajiyar zuciya Batuul ke sauk’ewa da haka har bacci ya d’auketa, a hankali ya kwantar da ita daga jikinshi ya mik’e ya shige toilet, wanka yayi ya fito ya canja kaya, murmushi yayi yasa hannu cikin gashin kanshi ya bajesu ganin tiny figure d’inta na bacci peacefully,  karasawa yayi gadon yayi pecking d’inta, motsi tayi tare da gyara kwanciyarta, wani nutsuwan da bae taba sanin da shi ba yake samu gun Batuul, gown d’inta ya d’age har zuwa cinyoyinta, ya janyo duvet d’in gadon ya ninka biyu ya rufa mata, kanta kawai ya bari a bud’e, key d’in motanshi ya d’auka kan side drawer ya fita, if he can clearly remember yau babu abinda taci, driving yakeyi amma gaba d’aya hankalinshi na kan Batuul, murmushi kawai yakeyi ba tareda yasan dalili ba, but shi dai yasan being with Batuul na sashi jin exceptional feeling d’in da bai tab’a experiencing ba, a wani restaurant d’in kusa dasu ya shiga ya siyo musu abinci, baifi thirty minutes ba da fita ya dawo, har lokacin tana bacci, kan gadon ya hau ya d’agota jikinshi, daidai kunnenta ya rad’a mata “Wake up, sleepy head”, a hankali ta bud’e lumsassun idanunta ta sauk’e kanshi, komawa tayi zata kwanta ya d’agata cak ya zaunar da ita, a tsorace ta wara ido, abubuwan da suka farune ya dinga tariyo mata, rintse ido tayi bata son ganinshi ga wani kunyansa da take, a ranta ta godewa Allah da yasa tace mishi she is not pure, iska ya hura mata fuska yace “Hey tashi kici abinci”, sai lokacin ta bud’e ido ta kalli inda ya zuba ledojin, ce mata yayi “Brush first”, a hankali ta yaye bargon da ya rufa mata, ganin cinyoyinta waje yasa tayi maza ta rufesu, a hankali ta kalleshi ta gefen ido taga ita yake kallo yana murmushi, zumb’uro baki tayi ta sauk’o daga kan gadon ta nufi toilet da sauri, ya bi ta da kallo, brush d’aya kawai ta gani, fitowa tayi ta tsaya bakin k’ofan baki a tsuke, ya tsaya yana kallon yadda ta tsuke bakin, a ranshi yace “she is cute, Not beautiful”, ce mata yayi “fito mana, ko tsayuwan bakin toilet d’in ke miki dad’i?”, raurau tayi da ido tace “Ai ba brush ciki, guda d’aya na gani”, ba tareda ya kalleta ba yace “then you use that one, it’s mine”, wara ido tayi jin abinda yace, ta had’e rai tace “I can’t use it, its yours”, murmushi yayi ya tashi ya isa inda take ya fixgota ta fasa ihu, ya had’a bakinshi da nata, ya kai two minutes yana kissing d’inta sannan yace “you can now go and brush”, hawayen da ya zubo mata ta goge da bayan hannu ta koma cikin toilet d’in jiki a sanyaye, ruwan d’umi ta kunna zata wanke brush d’in sai kuma tayi tsaki ta shafa toothpaste d’in ta wanke bakinta a haka, a d’akin ya baje abincin da ya siyo musu, a hankali ta k’araso ta zauna bakin gadon, kallonta yayi yace get down and eat”, ba musu ta sauk’o dan yunwan da takeji, a hankali ta dinga cin abincin har saida taji ta k’oshi, shi kam babu abinda yakeyi banda kallonta, birgeshi tayi yadda takecin abincin, ganin ta dena ci ya harareta yace “me?”, a hankali tace mishi “am full”, had’e rai yayi yace c’mon finish dat before I meet you there”, baki ta zumb’uro ta matso taci gaba da ci a haka har suka gama, ita ta tattare packs d’in duka waje d’aya, hannunta ya kamo yana kallon fuskanta yace “kin manta ma mey ya kawoki ko, you were busy engrossed in being hugged by me and feeling the warmth of my body huhh?”, had’e rai tayi ta d’auke kai kamar bata ji shi ba, murmushin shi mai kyau yayi ya jata suka tafi d’akin da ya zuba kayanta, ce mata yayi “Get what you are here for” sannan ya sake mata hannu, k’arasawa tayi ta d’auko d’an kwalin da kayan ke ciki, hannu yasa ya amshesu daga gunta, kallon mamaki ta bishi dashi, wai wannan Yaa Abun da ta sani ne kuwa, har wani trying yake ya zama gentle, Lol, kallonta shima yayi tareda smirking yace ” Hey kina kallewa Ajiddeh miji ko, zata dawo ne, before then let’s get going”, ya kamo hannunta, kin tafiya tayi har saida ya juyo yana kallonta “What’s up”, ya fad’i tareda d’age mata girarshi d’aya, raurau tayi da ido kamar mai shirin kuka a shagwab’e tace  “Yaa Abu I don’t want to leave, ni nafi son xaman nan kai ka tafi”, sai da ya tsaya for some seconds yana kallonta bayan ta gama maganan sannan yayi murmushi yace “har kin manta, d house is my wife’s, my love, we have to leave”, had’e rai tayi ta tsuke baki jin abinda yace mata, warce hannunta tayi daga nashi tayi gaba abinta, dariya ta bashi shima ya biyota a baya, yana danna lock d’in motar ta bud’e ta fad’a ciki, shima baice mata komai ba ya bud’e ya shiga yana murmushi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *