BATUUL CHAPTER 15

BATUUL 
CHAPTER 15

Kan gadon ya koma bayan ya ajiye wayan hannunshi, kallon Batuul dake bacci kawai yakeyi yana lumshe ido tare da bud’esu, ya dad’e sai kallonta yakeyi, tausayinta yakeji har cikin ran shi, bai san lokacin da wani murmushi yayi escaping lips d’inshi ba tunawa da yayi da ranan da ya fara had’uwa da Batuul har kawo jiya da daddare, murmushi kawae yake yana girgixa kansa ya kwanta gefenta ya jawota jikinshi ya rungumeta, a tsorace ta saka y’ar k’ara tana k’ok’arin tashi, rungumota ya dad’ayi jikinshi kamar wacce za a k’waceta a hannunshi, a kunne ya rad’a mata “shhhh sleep, babu abinda zan miki”, maida kanta tayi kan faffad’an k’irjinshi a sanyaye tana maida ajiyan zuciya, har lokacin heart beat d’inta bai koma normal ba dan gani take zai mata wani abin, ta dad’e idonta biyu har sai da taga ya jima bai yi mata komai ba ta samu bacci ya d’auketa.
+
         *TWO MONTHS LEAP*
           A hankali Batuul ke sauk’owa kan staircase, sanye take da doguwar riga ta atampa, riqe da jakarta sai waya a d’aya hannun, ta k’ara kyau abinta sai shek’i takeyi don ko kadan bata da damuwa sai na Ajiddeh, a dinning ta tarar da Ajiddeh ta zauna tana kwasar girkin da ita d’in tayi, har saida ta k’arso sannan ta dubi inda Ajiddeh ke zaune tace “ina kwana”, ba yabo ba fallasa Ajiddeh ta amsa mata gaisuwarta, k’arasawa tayi parlour zata fita waje, gabanta ne ya fad’i jin cikin husky voice d’inshi yace mata “Hey, wait, I will b dropping you off today”, sai da taji yayi shiru sannan ta juyo ta dubi inda akayi maganan, kamar bashi ya gama magana yanzu ba, remote ne a hannunshi yana kwance yana kallon Tv, har lokacin gabanta fad’uwa yakeyi dan tasan abinda tafiya dashi ke nufi, rolling eyes d’inta tayi tace “David will drop me off, zanyi latti”, kamar ba dashi tayi maganan ba ko motsi baiyi ba bare ya nuna alamun yaji mey tace, ranta ne ya b’aci ganin yaqi kulata hawaye ya fara taruwa idonta, Ajiddeh dake dinning kamar da ita ake magana ta ture plate d’in dake gabanta ta mike ta dawo parlour ta tsaya daidai kanshi tace “Babe wane irin you will drop her, kai da ko breakfast bakayi ba, wankan ma naga ba yinshi kayi ba amma kake wani cewa zaka kaita, mey amfanin driver in bashi zai na kaitan ba?”, itama d’in kamar yadda bai cewa Batuul komai ba haka ita ma babu abinda yace mata, juyawa Batuul tayi zata fita ganin ya lumshe idonsa tajishi da wani irin voice yace “Don’t you dare go out”, ta kai seconds goma tsaye kamin ta juyo jiki a sanyaye idonta duk ya cicciko, sama ta koma ta fad’a d’akinta tareda banko k’ofar d’akin ta fad’a gado tana hawaye, a hankali ya bud’e lumsassun idanuwanshi ya sauk’esu kan Ajiddeh dake tsaye ta zuba mishi na mujiya sai huci take, mik’ewa yayi ba tareda yace mata komai ba zaibi ta gefenta tasha gabanshi tace “wato kaifa na lura dakai kwana biyun nan y’an wulak’ancin naka sun fara dawowa akan yarinyar nan ko?, akan mene ga driver zaka wani ce kai zaka kaita, kuma ma ai ta iya tuk’in in ba dai wata manufar ce dakai ba”, kallonta ya tsaya yanayi da lumsassun idanunshi dake rikitata har saida tayi shiru, fixgota yayi ya d’aura hannunshi mai d’umi a wuyanta yana yi mata tafiyar tsutsa sannan ya rank’wafo daidai kunnenta yace “mesa ke abin fad’a baya miki kad’an, yanzu meye na tada hankalinki kina stressing kanki, stress na sa tsufa da wuri and I don’t want that to happen to you, inba kinason inje in samo new babe ba”, ya k’arashe maganan tareda d’ago kanshi ya kashe mata ido d’aya, turashi tayi daga jikinta jin ya ambaci tsufa, cikeda bala’i tace “ai kuwa wlhy ……”, bai bari ta k’arasa ba ya had’e bakinshi da nata, tun tana kokawa har ta hak’ura ta biye mishi, sai da suka gaji tukunna ya sake ta suna maida numfashi, hannu yasa cikin gashinta data gyara ya bajesu yace “You are just getting yourself worked up, inada abinyi a can school d’in nasu shiyasa nace I will go with her”, kallonshi take amma bata jin ta yadda da abinda yake fad’a mata, “toh kai wulak’ancin naka ai dayawa, kana ganifa nan na tsaya ina maka magana amma kayi kamar bakaji ni ba kuma sai gaban yarinyar nan zaka rik’a yimin irin wad’annan abubuwan bayan kasan banson raini”, murmushi yayi tareda sa hannu waist d’inta yace ” Let’s help me change, in na dawo sai muyi magana dan nima banso ta rainaki”, a shek’e take ta kalleshi sannan ta cire hannunshi dake waist d’inta tace “na yaushe kuma bayan ta gama raina ni, ni abinci nakeci kaje abinka ka shirya”, smirking yayi ya haura sama ita kuma ta koma dinning taci gaba da cin abincinta, d’akin Batuul ya wuce kai tsaye yana hawa sama, kwance ya tarar da ita kan gado, zama yayi daga bakin gadon yana kallon yadda idonta ya canja kala, sam baya son kukan mace, he always considers them weak and naive, bare in Batuul keyi har cikin ranshi yake jin kukan, he don’t know but yarinyar nada wani irin effect akanshi that makes him feel vulnerable, so yake ya rungumota ya rarrasheta amma bazai iya ba dan wannan kukan nata sai anyi dagaske, abinda yake na kuka da ba na kuka ba duk yi takeyi, its getting out of control, dakewa yayi yana kallonta yace “da akayi miki mey kika zauna kina kuka?”, shiru tayi mishi tareda d’auke kanta ganin yadda ya tsareta da ido, hannu yasa ya juyo da kan nata yace “I will slap you kika sake d’auke min kai ina miki magna, tambayanki nakeyi what happened to you?”, hawayen ne ya shiga gangarowa daga idonta, rintse ido yayi tareda fad’in “shit”, ciki ciki, sai da yaje tsakiyan d’akin yace mata “tashi ki tafi”, kamar munafika haka ta mik’e jiki a sanyaye tayi maza ta fad’a toilet ta d’aurayo fuskanta ta fito har lokacin yana d’akin, kallonshi ta tsaya yi ganin bai fita ba shima, juyawa yayi ya fara tafiya sannan ta biyoshi a baya, a dinning suka tadda Ajiddeh har lokacin ana d’a’amun, wani irin kallo ta bisu dashi, Batuul kam d’auke kanta tayi kamar batasan da ita gun ba ta fice waje, a minute after shima ya fito, tundaga sama Ajiddeh ke kallonshi, ita kad’ai tasan irin son da takeyiwa Aliyu, har cikin ranta takejin shi, har wani lumshe ido takeyi tana kallonsa batasan ma lokacin da ya k’arasota ba, saida yasa hannu yayi waving gaban fuskarta snnan ta sauk’e ajiyar xuciya ta k’irk’iro murmushi, murmushin shima yayi mata yace “thinking of me?”, kai ta gyad’a mishi, gefen fuskanta ya shafa yace “Ikr, I will b back right away”, take murmushin dake fuskanta ya gushe ta zumb’uro baki tace “kofa wanka ma bakayi ba yau, bazaka office bane?, these days kamar ma aikin dena zuwanshi kayi”, bai juyoba yaci gaba da tafiya yace “kinki shiryani shine zanje inda za a shiryani ko ban tambaya ba, and you know am my own boss”, tab’e baki tayi a ranta tace “ko ba boss ba, mutum sai son jikin jaraba, k’ato dashi wani wai in shiryashi, ai danma kar inyi aikin wahala nak’i yadda in haihu yanzu”, da haka ta koma kan kujeran dining taci gaba da abinda takeyi, a parking area ya tadda Batuul tana tsaye, k’arasawa yayi ya bud’e ya shiga ya tada motar, har lokacin tana tsaye bata shiga ba, ya kai five minutes zaune cikin motan baice mata ba itama bata shiga ba, sai da ta gaji dan kanta ganin zatayi latti ta bud’e ta shiga, murmushi yayi ya tada sukatafi, saida yayi nisa sannan ya had’e rai yace  “kin fara rainani ko, dan kinga ina kulaki kuma matata ta dena damunki ko, I will leave you to her”, har yayi shiru batace mishi komai ba sai ma d’auke kanta da tayi daga dubanshi ta tsuke baki, saida taga ya d’auki hanyan d’ayan gidan sannan ta wara ido ta juyo da sauri tana kallonshi tace ” Yaa Abu ina zaka kaini?, Yaa Abu school fa zanje am almost late”, kamar baiji mey tace mishi yaci gaba da tuk’inshi, idonta ne ya cicciko taci gaba da yarfe hannu tana girgiza kai, ganin har lokacin baice komai ba tace “Yaa Abu dan Allah ka kaini sch, I will b missing my class kaji?”, ta rok’eshi tareda juyo kanta tana kallon shi da idonta da ya cicciko, har lokacin kuma ko juyowa baiyi ya kalleta ba, sai da yayi parking a compound d’in gidan glass sannan ya kalleta, sai a snn yace mata “You can come out”, d’auke idonta tayi daga kanshi  ta kifa kai kan cinyarta taci gaba da kuka, murmushi yyi yasa hannu cak ya d’auketa, “ihu zata fasa yayi maza ya matseta jikinshi, k’ok’arin sauk’a ta shiga yi daga jikinshi sai harba k’afa takeyi, daidai wuyanta ya sunkuyo ya manna mata lips, jin lips d’inshi masu d’umi jikinta yasa ta jin wani irin shock yabi spine d’inta dama ga sanyin da takeji, lamo tayi ta sake shigewa jikinshi, murmushi yayi ya d’ago ya kalleta yace “hakkina zaki bani”, da sauri ta sinne kanta jikinshi, ciki ciki tace “Wane hakkinka wai Yaa Abu, ni bansan mey kake……” , bata k’arasa maganan da zatayi ba yayi murmushi ya sake rungumota har ya isa bakin k’ofa, kamar kullum yau ma da hannunta ya bud’e gidan, bai ajiyeta ba sai da yaje har d’akinshi sannan ya direta k’asa ya fad’a gado, tana ganin ya kwanta ta mike zata fita, da hanzari ya mik’e ya fizgota ta fad’a kanshi, ihu tasa mishi yayi saurin had’e bakinsu, abinda take gudu ya shiga yi mata, tun tana nonnoke masa tana kukan shagwaba wai bata so, har dai ta bada kai bori ya hau, ta fara mayar masa da martani ba tare da ta shirya ba, Abuturrab ba dai iya sarrafa mace yasa ta mance hanyar garinsu ba Lol, don kam Batuul ta mance hanyar garinsu.
2
STORY CONTINUES BELOW
        K’ank’ameta yayi tsam jikinshi bayan kura ya lafa, yasa hannunshi d’aya cikin gashin kanta yana wasa dashi lkci daya yana kissing wuyarta, Batuul kam lumshe ido kawai tayi tana jin abinda yake mata dake aika mata electric shock, gaba d’aya jikinta yayi sanyi, a kunnenta ya rad’a mata “You are just different, so sweet, warm and tight!” K’in bude ido tayi as usual, as he expected kuma, don in dai ya kusance bata bari su hada ido duk nacin sa, dariya yayi yana shafa cikinta ganin yanda take boye fuskarta a kirjinsa yace “Farida will
be coming gobe, I don’t….”, bai Karasa ba ta dago kanta da sauri tana rufe kirjinta da bargo ta kalli fuskanshi cike da farin ciki tace “Don Allah Yaa Abu dagaske?, and shine bata fad’amin ba, lemme call her right away”, ta k’arashe maganan tana k’ok’arin tashi daga jikinshi, hannayenshi duka biyu yasa a waist d’inta ya zagayesu ya maidata jikinshi yace “Yeah, nasan halin Farida, ban yadda kuyi duk abinda zaiyi stressing min mata ba, sannan wannan yawan kukan naki…..” jin ya ambaci matarshi wani k’arfi yazo mata tayi maza ta k’wace kanta daga rik’on da yayi mata, idonta duk ya cicciko ta matsa can edge d’in gadon tana rufe jikinta, ita dama tasan ba sonta yakeyi ba, jikinta kawai yake bid’a, inma yana son matarsa ai ba sai ya dinga fad’a mata ba kullum, shiyasa duk ranan da buk’atarsa ta tashi yake kawota gidan nan in ya gama ya maidata batare da sanin matar tasa ba wataran tana class haka zaije ya d’aukota ya haramta mata lecture duk don biyan bukatarsa, batasan sanda kuka ya kufce mata ba, Su Aunty sunyi kuskure da suke tunanin zai sota har yayi keeping d’inta happy, ta tashi zata fita daga d’akin, wani jiri ya kwasheta tayi taga taga zata fad’i da sauri ya tarota k’irjinshi, kan gadon ya maidasu suka zauna, kallonta yake da mamaki dan bai san mey ke damunta ba, kuka ta fashe mishi da ta shiga tutturashi tana dukan k’irjinshi ya saketa, “keh kinada hankali kuwa, mey ke damunki”, batace komai ba taci gaba da kukanta, firmly yayi gripping kafad’unta yana mata wani mugun kallo yace “tell me mey aka miki kike kuka ko yanzu I slap you”, itakam babu abinda take in banda hawaye, shi sam hawayenta is one of his greatest weakness, yanzun nan sai ya zama vulnerable jikinshi yayi sanyi, d’an siririn tsaki yaja ya rungumota jikinshi, kanta ne taji yana juyawa ga zuciyan ta da ya fara tashi jin k’anshin turarenshi da ya cikata kamar daxu, da k’yar ta iya d’agowa idonta yayi ja ta shiga turashi zata sauk’a, ganin yaqi saketa saima tsareta da yayi da ido ta bud’e baki da k’yar tace “I need to throw u….”, bata gama maganan ba taji tana yunk’urin amai, da kanshi yayi maza ya sunkuceta sukayi toilet, a gaban sink d’in ya tsayar da ita, ganin baza ta iya tsayuwa ba ya jinginar da ita jikinshi ya rungumota ta baya, sunfi five minutes cikin toilet d’in amma babu abinda ya fito sai k’ak’arin amai takeyi gaba d’aya ta galabaita, d’agota yayi ya wanke mata face tare da kuskure mata baki snn ya dawo da ita d’aki, sai numfashi take maidawa, a kan gado ya kwantar da ita tareda rufa mata duvet, tsareta da ido yayi yace “ban hanaki fita ba tare da kinyi breakfast ba?”, hawayen dake idonta ne ya shiga silalowa, tsaki yayi ya tashi ya fita daga d’akin, bai jima ba ya shigo riqe da cup d’in tea a hannunshi da pack d’in Cookie, har ta d’an fara bacci sanda ya shigo, a kan bedside drawer ya ajiye abinda ke hannunshi snn ya hau kan gadon tareda d’agota jikinshi da k’yar ta Iya bud’e lumsassun idanunta ta sauk’esu kanshi, cup d’in tea d’in ya kawo daidai bakinta, d’auke kanta tayi tana girgiza mishi kai, d’ayan hannunshi yasa ya juyo da kanta yace mata 
“C’mon take it before I slap you”, haka ta dinga sha yana had’a mata da cookies d’in, sai da tasha da d’an yawa sannan ya kwantar da ita ya fad’a toilet yayi wanka, da ya fito har tayi bacci, zama yayi kan bedside drawer ya zuba mata lumsassun idanunshi, har cikin ranshi yake jin Batuul, baisan yanda zai fara fad’awa Ajiddeh Batuul matarsa bace, she ought to know tun ba yanxu, gashi wannan sarkin y’an rawan kan na tafe, yasan dole tayi abinda Ajiddeh zatasan Batuul matarshi ce, d’an tsaki yayi ya tashi yaje yayi shafe  shafenshi yasa kaya mara nauyi ya hawo kan gadon ya kwantar da ita jikinshi, baisan lokacin da bacci shima ya d’aukeshi ba, 1:30 Adhan d’in wayanshi ya tadasu, a hankali ta bud’e idonta da sukayi mata nauyi, ganinta kwance jikinshi ya sata yin lamo, a hankali yace mata “muje kiyi wanka”, da sauri ta girgiza mishi kai tace “zan iya”, ta k’arashe maganan tana zumb’uro baki,  baibi ta kanta ba ya d’agata cak yayi toilet da ita, k’ok’arin cire mata kayan jikinta ya shiga yi, da sauri ta riqe rigan tace “Yaa Abu zan iya, zanyi da kaina”, baiyi mata musu ba ganin ta samu d’an k’arfi ya saketa ya juya ya fice daga toilet d’in, wani toilet d’in ya shiga ya d’auro alwala ya dawo d’akin yayi nafila yana jiranta ta fito suyi a tare, sai da tayi wankan tsarki sannan ta d’aura da normal wanka tayi alwala ta fito d’aure da towel, idonshi kyar akanta, da sauri ta bud’e closet d’inshi ta ciro wata doguwar rigarta dake ciki ta saka, sai da sukayi sallah tukunna ta shafa mai, tsareta yayi da ido yace “mey ke damunki d’azu kike kokarin amai’, tsuke baki tayi tace “nima ban sani ba, kawai shine yaxo”, yace “I have warned you, next time kika fita school bakiyi breakfast ba, you won’t like an encounter with me”, tab’e baki tayi a ranta tace “as if he really cares”, dan har yanzu bata manta maganar matanshi da yake mata ba, sai da ya sake maimaitawa yace “You heard me right?”, kai ta gyad’a mishi tareda ce mishi “Toh”, da haka ya mik’e yace mata “I will be right back”, baifi minti 20 da fita ba ya dawo da ledoji a hannunshi, har ta gyara d’akin ta saka turaren wuta cikin nata dake d’akin daban, kan gado ta koma tayi zamanta dan yau kam tasan zancen makaranta babushi, ajiyar zuciya ya sauk’e tareda lumshe ido jin daddad’an kamshin da gidan keyi,  zubewa yayi kan coffee chair d’in d’akin yayi wa Batuul dake zaune kan gado alama da hannu tazo, ba musu ta tashi ta isa inda yake, fizgota yayi ta fad’a kanshi, bata ankara ba taji ya shiga yi mata wani passionate kiss, sai da ya gaji ya saketa ya rik’o hab’arta yana kallon idanuwanta masu haske yace “Fatima I just lyk everything about you, I can’t  get enough of you, lyk duk inda kike that place is always conducive, kullum wajen da k’anshi and its serene”, kasa ci gaba tayi da kallonshi ta sunkuyar da kanta k’asa, tasan kawai ya fad’a ne to get what he wants, janye jikinta tayi ta sauk’a k’asa, murmushi yayi shima ya sauk’o ya jawo ledan da ya shigo dashi yace mata “get us plate, am so famished, you are the only thing dake sani in manta da inajin yunwa”, batace mishi komai ba dai ta fice ta dawo riqe da plates, spoons, forks da serving spoon, shi ya amshe ya shiga bubbud’ewa, yana bud’e d’ayan ledan tayi maza ta toshe bakinta, girarshi d’aya ya d’age yana kallonta yace “Ya akayi”, kai ta girgiza mishi tace “Banason k’anshin cheese din”, da mamaki ya kalleta yace “saboda mey?”, da k’yar tana komawa baya tace “nima ban sani ba”, maidawa yayi ya rufe ledan ya janyo wani, ya kalleta yace “wannan is just pasta with tomato sauce, babu cheese a ciki”, dawowa tayi a hankali gabansa, tare suka gama cin abincin a plate d’aya, tana yi tana kurb’an fresh lemonade dan yana rage mata tashin zuciyan da takeji a lokacin, sai da suka gama ta tattare wajen, bayan kamar awa d’aya bayan ya gama danne dannenshi a system yace “Let’s get going, I know matata na nan tana missing d’ina by now”, ko kallon inda yake batayi ba ta tashi ta d’auki jakanta ta fita daga d’akin, a bakin mota ya tarar da ita ta tsuke baki idonta duk ya cicciko, yana bud’ewa ta fad’a motar cike da fushi, shiga yayi yana murmushi ya xauna shima sannan ya tada motar, hannunta ya kamo cikin nashi ya kai bakinshi zai d’an yi kissing ta warce hannunta a fusace, hannu yasa ya juyo face d’inta yana kallo, hawaye ne taf ciki saura k’iris su zubo, da mamaki yace “yarinyar nan kinada hankali kuwa, you are okay just now and in a minute kin fara kuka, ko dai kukan is your hobby?”, batace mishi komai ba har ya gama surutunshi, kafad’a ya d’aga yaci gaba da driving, yana parking ta bud’e mota ta fito ko rufewa batayi ba ta shige gida abinta
1
          Babu kowa a parlourn sanda ya shiga d’aki, yanda ya fita ya bar dining d’in haka ya sameshi, kai ya girgiza ya haura sama dan yasan Ajiddeh will never change, ko abinda taci abinci bata iya d’aukewa ba, a gaban mirror ya tadda ta tana shafa lipstick, bata amsa sallamanshi ba saima binshi tayi da wani irin kallo tace “Aliyu ba da wannan kayan ka fita ba”, murmushi yayi yace “You thought I was joking ko when I said zanje inda za a shiryani?”, idonta ne ya k’ank’ance da bala’i, har zata fara masifa sai kuma ta fasa tace “ga alama na gani ae”, daga gefenshi ta zauna tace “Babe yanzu Aunty Jainaba ke ce min ta iso tana airport, har na tura David yaje ya taho da ita”, tunda ta fara magana yake kallonta, shi ya rasa wace irin mace ce Ajiddeh, yana kallonta yace “keh bansan lokacin da zakiyi tunani irin na mutane ba, is it proper for you sai da ta iso har kin tura a d’aukota kike fad’amin, tunda keh ke iko da gidan meye na fad’amin?”, a fusace ta mik’e kamar wata iska tace “Kai ai kullum tunani na ba irin na mutane bane, kai lokacin da kazo da wancan yarinyar wayace maka wani abin, ko kuma da wa kayi shawara, sai ni da kawai zatazo yin yan kwanaki, in tazo kace ta fita ta bar maka gidanka Aliyu”, da haka ta banko mishi k’ofa tayi d’akinta
Lumshe ido yayi bayan ta fita daga d’akin, tunani kawai yakeyi na yadda zai sanar da Ajiddeh Batuul matarsa ce, sai yanzu yake ganin rashin kyautuwar fad’a mata da bai yi ba tun farko, yasan da ya fad’a tun lokacin da duk wani rikici ya kau by now, amma gaba d’aya kanshi a k’ulle yake as of then, yana ce komai zaizo da sauk’i amma yadda yake jin Batuul a ranshi, bazai iya yin nisa da ita ba, not for a second, d’an siririn tsaki yaja ya mik’e ya koma gaban desktop d’inshi yana duba ayyukan da baiyi ba yau a office, kamar wanda aka tsikara ya mik’e ya fita daga d’akin ya shiga d’akin Batuul, har ta canja doguwar rigar dake jikinta ta saka wani d’an bingel d’in gown pink ta baje gashinta kan pillow dan yasha iska, tana kwance ta d’aura Laptop d’inta saman cikinta tana danne danne, wani irin ajiyar zuciya ya sauk’e ganin she is fine, a hankali ta juyo da kanta ganin shine ta maida kallonta ga abinda takeyi, tura k’ofan d’akin yayi ya shigo ya maida ya rufe, daga bakin gadon ya zauna yana kallonta, ya kai wajen 3mins amma ko sau d’aya bata juyo ta kalleshi ba, hannu yasa ya d’auke laptop d’in, sai a lokacin ta d’aga ido ta kalleshi, idanunsu na locking cikin na juna tayi maza ta sadda kanta k’asa ta juya mishi baya, hannu yasa cak ya d’agota yana kallonta yace “are you okay?”, kai ta gyad’a mishi ta sulale zata koma ta kwanta ya rik’ota yace “then why are you like this, aman ne har yanzu?”, har lokacin batace mishi komai ba sai gyad’a mishi kai da tayi, hannu yasa ya d’ago hab’arta yace “talk to me and stop nodding, wani abun ke damunki?”, ganin idonta ya fara ciccikowa yasa yace “stop that, don’t you dare drop a tear,  tell me mey ke damunki”, kamar cewa yayi ta fara kuka ta fashe mishi da wani matsanancin kuka, har cikin ranshi yakejin kukan nata, rintse ido yayi ya janyota jikinshi ya rungumeta, patting bayanta ya shiga yi har saida ya samu tayi shiru, sai ajiyar zuciya take sauk’ewa, a hankali ya d’agota yasa hannu ya share mata d’an guntun hawayen dake fuskanta ya had’e rai yace “Look at me”, bata d’ago ba sai da ya sake maimaitawa jin yayi maganar in a serious tone ya sata d’agowa tana ajiyar zuciya yace “Fatima kinada hankali kuwa, keh abin kuka baya miki kad’an, ko don kinga ina k’yaleki kullum sai kinyi kuka, gari baya wayewa ya wuce bakiyi kuka ba, tell me what your exact problem is”, ajiyar zuciya ta sauk’e ta zumb’uro mishi baki tace “ni ai ba kullum nakeyi ba sai in kaine ka…..”, tsareta yayi da ido yace “ehhn, sai in nine nayi mey?”, sadda kanta tayi k’asa tace “You always talk abt your wife, kullum sai kace min your wife your wife, I know she is your wife, but ai ba sai ka dinga tunamin ba”, baisan lokacin da dariya ya k’wace mishi ba, dariya ya dinga har sai da abin ya bata haushi, haushin kanta ma taji da ta fad’a mishi hakan, takaicin dariyan da yake yasa taja bargo tayi kwanciyarta, sai da yayi mai isarshi sannan ya d’agota har lokacin yana murmushi, kwace jikinta ta shiga yi zata kwanta amma yaqi saketa, fuskarta ya kamo da duka hannayenshi yana kallon idonta da duk ya cicciko yace “Toh ni yau duk yaushe na ambaci my wife”, baki ta zumb’uro mishi tace “ko d’azu ma ba ka….”, sai kuma tayi shiru, saketa yayi sannan yace “indai wannan ke saki kuka baza ki sake ji ba, you won’t hear that from me okay?, ya hade rai ya ci gaba “but promise me kema baki sake yin kukan, kinga Farida will b coming so banso tazo taga kina wannan koke koken tayi tunanin wani abun ake maki”, kamar wata y’ar yarinya ta gyad’a mishi Kai, ajiyar zuciya ya sauk’e ganin yayi convincing d’inta kan kukan nata, yanzu saura Farida, itama sai yayiwa tufkar hanci tun wuri, hannunta ya kamo yace “inason shan kunu, can you make some now?”, kai ta gyad’a mishi yayi d’an murmurshi yace “Thank you”, tsuke baki tayi zata tashi daga kan gadon yayi saurin janyota yace “Did you just pout?”, da sauri ta kad’a mishi kai tace “baka ganiba, ni ba pouting nayi ba”, murmushi yayi ya janyota jikinshi sosai ya d’anyi brushing lips d’inshi kan nata yayi mata light kiss, lips d’inta na d’aya daga cikin abinda bazai Iya resisting ba akan Batuul, suke tempting d’inshi yayi abubuwan da ma bai shirya yinsu ba,  mik’ewa yayi  itama ya mik’ar da ita, kallonta yayi yace “muje?”, a hankali tace mishi “Ehh”, Hijab d’inta ta d’auka zata saka ya riqe yace “Do you really need to put on this?”, kai ta gyad’a mishi kawai taci gaba da saka Hijabinta, ita tayi gaba ya biyota a baya, turus ta tsaya bakin k’ofa ganin mutanen da suka hauro wa sama, kallon mamaki suka tsaya yi mata, wani irin bugawa Ajiddeh taji k’irjinta nayi ganin ya fito daga d’akin Batuul, tun bayan dawowanta bata tab’a tunanin har lokacin yana shiga d’akin ba, baki ta bud’e zatayi magana Jainaba tayi saurin rik’o mata hannu, murmushi ta k’irk’iro tace “Aliyu ashe ana ganinku a gari”, shima d’in murmushi yayi yace “ai sai in ba a nemi ganinmu ba Aunty, Ya hanya?” Ya tambaya yana k’arasa fitowa daga d’akin, murmushin nan dai taci gaba dayi tace “Alhamdulillah, hanya mun baroshi, mun sameku lafiya?”, kai ya gyad’a yace “Alhamdulillah, ya jikin Mummy, kwanaki bata ji dad’i ba, I wanted going with her”, ya nuna Ajiddeh da zuciyarta ke tafasa “but abubuwa held me hear”, dariya tasa tace “Ai ba komai ma, ai zuwan Ajiddeh ma yayi,taji sauk’i yanzu sai dai Allah ya kiyaye gaba”, “Amin” yace sannan ya juya yana kallon Batuul da ta tsaya daga bayanshi kamar wata munafika yace “baki iya gaisuwa bane kika tsaya kallon mutane?”, ido ta d’aga ta kalleshi sannan ta kalli Aunty Jainaba da ta bita da wani shu’umin kallo tana jira ta gaida ta, juyawa tayi ta shige d’aki ta banko musu k’ofa, gaba d’ayansu freezing sukayi ganin abinda Batuul d’in tayi, tsabar mamaki kasa magana Abu yayi, Ajiddeh ce a fusace tayi k’ofar d’akin zata bankad’a Jainaba ta rik’ota, “shegiya karamar matsiyaciya har kin isa ki wulak’anta min y’an uwa, toh koma uban wa ya d’aure miki gindi, ko kuma aka zugoki kizo ki min iskanci ko, toh dama hak’uri nakeyi nake k’yaleki, yau sai kin bar min gida y’ar abu kazan uba”, Aunty Jainaba ce ta janyota da k’arfi ta d’an kanne mata ido sannan tace “Haba Ajiddeh, bakya ganin yarinya ce, kema ai kinsan hankali ba isanta yayi ba, yarinta ne ke damunta”, wani irin kallo ta jefawa Aliyu da ya kasa cewa komai sai kallonsu yakeyi, a masifance tace “ai dama nasan kai ke d’aure mata tana min abinda taga dama, gashi ka janyo min raini da bai tsaya iya kaina ba, har kan y’an uwana ya koma, toh Allah zamanta ya k’are gidan nan ko kuma ni in bar muku gidan sai kuyi xaman auren da ita”, Aunty Jainaba ce ta d’anyi magana a tsawace tace “keh wai wace irin yarinyace Jiddah, haka ake yiwa miji magana dama, wuce mu shige tunda bakida hankali wawiya kawae”, taja ta sukayi gaba, wani irin iska mai d’umi ya furzar daga bakinshi yasa yatsunshi cikin gashin kanshi ya bajesu, juyawa yayi ya bud’e d’akin Batuul tana tsaye tana waya da alama da Farida suke wayan, a hankali ta juyo ta dubeshi, sai da y’an hanjin cikinta suka kad’a ganin irin kallon da yake tunkarota dashi, dakewa tayi da k’yar ta bud’e baki tace “Hey hold on, I will call you ltr”, bata cire wayan a kunnenta ba taji ya fizge ya jefar kan gado tareda fizgota gabanshi, yana mata wani irin kallo yace “What’s d meaning of what you just did, kinada hankali ma kuwa?”, babu abinda k’irjinta keyi sai heaving kamar zai fito amma ta dake tace “ni kuma mey nayi?”, fizgota ya sakeyi jikinshi yana mata wani irin kallo yace “you are asking, i will slap you yanzun nan in baki min magana ba, meye dalilinki na tafiya ba tareda kin gaidata ba, are you stupid?”, k’wace kanta daga rik’on da yayi mata tayi zata matsa daga gabanshi ya kuma fizgota a tsawace yace “kehh! na fara wasa da ke koh, I will right away slap you, bakida hankali ne”, hannunshi tacire daga rik’on da yayi mata tace “wai ni mey nayi ne na rashin hankali, dan ban gaishesu ba?, dole ne sai na gaishesu? Naga ai dama ba dole bane gaida kishiya, ita yaushe ta tab’a gaidani? Let me be plss”, ta k’arashe maganan tana rolling eyes d’inta cike da masifa, kafeta da ido yayi cike da mamaki, baisan lokacin da gasp yayi escaping lips d’inshi ba jin abinda take ce masa, ci gaba tayi da cewa “kuma ni daga yau na dena gaisheta tunda itama bata gaishenin take ba”, daga haka ta juya fuu zata tafi ya fizgota, kankamesa tayi jikinta na rawa tana kiran Anty, murmushi ne ya subce masa jin yadda k’irjinta ke heaving, kana ganinta kasan a tsorace take, yace “Huh kishiya?, waye kishiyar taki, ko kuma kinji nayi declaring d’inki matata ne da har kike fad’in baki gaida kishiyarki?”, hawaye ya cika idonta tace “Ai ko bakayi declaring d’ina ba nidai bazan sake gaishesu ba, period”, jefata kan gado yayi yace “Fine, duk ranan da ta koreki daga gidanta sai kisan inda kika nufa”, da haka ya fita ya barta a d’akin, mikewa tayi a fusace ta sa key a kofarta, k’ofar d’akinshi ya tura ya shiga, nan ya tarar da Ajiddeh da Aunty nata zaune tana mata magana can kasa, d’an tsaki yaja ya koma da baya dan baisan ranar hankalin Ajiddeh ba, duk d’akunan dake gidan nan ta rasa wanda zata shigo da bak’i sai nashi, key d’in mota kawai ya d’auka ya fice daga gidan, bai dawo sai bayan Sallah Isha, direct d’akinshi ya wuce amma har lokacin suna ciki, sai ma dad’a littering d’in d’akin da sukayi da kayayyakinsu, ganin shi ne yasa Aunty Jainaba jin kunya tace “Laah Aliyu ashe har ka dawo, gashi mun b’ata maka d’aki”, Ajiddeh kam ko kallonshi batayi ba, Murmushi yayi wa Aunty Jainaba yace “Nah its okay, ba komai, I will use another room”, da haka ya fice ya jawo musu k’ofa, d’akin Batuul ya koma ya murda kofar yaji a rufe, komawa yayi ya dauko spare key sannan ya dawo ya bude ya tura kofan a hankali, as usual yana k’anshin da ya saba, kayanta ya tarar da ita tana gyarawa, kallo d’aya ta mishi ta d’auke kanta taci gaba da abinda takeyi fuskarta daure, k’arsawa yayi ciki ya kamo hannunta ya jata, tirjewa tayi a waje d’aya tana kallonshi tace  “Lafiya, ko ka mance hanyar dakin matar taka ne?”, ita kanta mamakin sabon halin nan nata takeyi, shi ma haka ya tsaya kallonta cike da mamaki, ta juya ta ci gaba da abinda take yi, ganin zata b’ata mishi lokaci yasa ya d’agata cak  “baki ta bud’e zata sa mishi ihu ya sa yatsa ya bige mata d’an baki yace “shout and I will drop you down d stairs, dare me ki ga”, gaba d’aya kanta ne taji yana juyawa kamar d’azu ga tashin zuciya, wani k’arfi ne yazo mata ta sauk’a daga hannunshi tace “zan tafi da kaina, ba sai ka d’auke ni ba”, ta fad’a tana murgud’a mishi baki, shi mamakin sabon halin nan nata kawai yakeyi har ta fito daga cikin d’akin shima ya biyota rik’eda hijab d’inta, ganin Hijab a hannunshi yasa ta ce mishi “wai ina zamu?”, baice mata koma ya rik’ota ya sa mata Hijab d’in ya jata sukayi waje, mota ya bude ya saka ta ciki sannan ya xaga shi ma ya shiga ya tada motar suka bar compound din, eatry ya nufa da ita ya siyo masu abinci suka dawo gida, yana gama parking ta fice daga motar ya bi ta da kallo yana murmushi, fitowa yayi shi ma ya kwashi ledojin abincin ya rufe motar ya bi bayanta, dakinta ta shige ta fada kan gado jin yanda xuciyarta ke tashi, ya hauro sama shi ma, yayi knocking dakinsa da su Ajiddeh suke, Ajiddeh ta leko fuskarta daure ya mika mata leda daya, wani matsiyacin kallo tayi masa tace “Ae nayi xaton da yunwa xaka bar ‘yar uwar tawa” daga haka ta maida kofa ta rufe ta bar sa nan tsaye, girgixa kai yayi cike da takaici ya juya ya nufi dakin Batuul, ajiye ledan hannunsa yayi ya karasa kusa da gado ganinta kwance ya xauna daga gefenta yana kallonta yace “Tashi ki ci abinci” ba tare da ta kallesa ba tace “Am OK ka kai ma matar ka” dariya ta basa ba kadan ba yace “Uhnn! Ae sai da na fara kai mata kafin in kawo maki” tace “Nawan ma ka hada mata ta cinye” dariya yayi ya dago ta yace “Ashe kema haka kika iya masifa, wannan ba halin Anty bane” kwace kanta tayi tace “Ni ka kyaleni” yace “Sakko ki ci abinci toh” tace “Ban ci” sakko da ita yayi kasa ya jawo ledan yace “Look am not joking fah” bude kofa aka yi daga waje, yyi saurin mikewa yana kallonta yace “Kafin in dawo ki tabbata kin cinye” daga haka ya juya ya nufi kofa ya fita, mikewa tayi da kyar ta koma ta kwanta don duk ta rasa me ke mata dadi ga tashin xuciyar da yasa ta gaba, tana kwanciya bacci ya dauketa. Shi kam Abuturrab duk ya kagu Ajiddeh ta koma gun ‘yar uwarta ya je yaga ko Batuul ta ci abincin don xuwa tayi ta sa shi gaba a palo, har sha biyu bai ga alaman xata tafi ba yace “Kin bar Anty ita kadae” tace “Ehh ita tace in tafi gun mijina bacci xata yi” bai kuma ce mata komai ba, har dai ya mike daga karshe yace “Am going to bed yanxu” ta mike tana mitsika ido, ya kashe kayan kallon parlour’n da wuta ya nufi sama ya bar ta, ta bi bayansa,  kwanciyarsa yayi a bedroom ya juya mata baya ta shige jikinsa, ko ta kanta bae bi ba ya lumshe ido kamar me bacci, yana jin alaman tayi bacci ya xame jikinsa daga nata ya mike daga gadon ya fita daga dakin, dakin Batuul ya shiga, ya karasa yana kallonta, kwata kwata bai ji dadin rashin cin abincin da bata yi ba, ya xauna gefenta ya cire duvet din da ta lulluba da a hankali, ya ji jikinta da d’an xafi, ya jima yana kallonta sannan ya lumshe ido yayi pecking lips dinta ya mayar mata duvet din jikinta ya mike ya dauke ledan abinci yasa a fridge ya fita daga dakin ya koma nasa.Washe gari da safe kamar yadda ta saba tashi haka ta tashi, sai da tayi Sallah tukunna tayi wanka ta gyara d’aki, ta koma toilet ta wanke sannan ta fito tayi kwanciyarta kan gado saboda jirin da take ji, jin jikinta ya d’anyi dama dama yasa ta mike ta fita daga dakin ta sauk’o k’asa yin breakfast kamar yadda ta saba, a gurguje ta shiga gyaran parlour dan bata son yin latti, lecture 11 ne da ita, gashi jiya ma bata samu taje ba, kitchen ta shiga ta harhad’a kayan abincin da zata dafa grilled fish da salad ta shiga had’awa, tana jin saukowan sa parlor da Ajiddeh ta tabe baki ta ci gaba da aikinta, kunun gyad’a ta dama sannan ta shiga baking musu chicken pie, Oven d’in da kifin ke ciki ta bud’e zata duba ko yayi, tiririn dake fitowa ciki yasa taji kanta ya fara juyawa ga tashin da zuciyarta ya fara, ba shiri ta yadda hand napkin dake hannunta jin amai na yunk’urin zuwa mata ta fito daga kitchen din da sauri, yana kwance a parlour ya lumshe ido, Ajiddeh na kwance jikinshi duk ta wani kanainayeshi, abubuwane kawai suke mishi yawo akai, duk he was just confuse, Ajiddeh kuma ba hankali ta cika ba da komai zaizo mishi da sauk’i, dan ko jiya shirmen da ta dinga mishi darajar Auntyn ta dake gidan taci da yayi maganinta, gaba d’aya bayajin zai iya yin nesa da Batuul, she has become part of him, duk da shi dai yasan ba wai sonta yake ba amma har cikin ransa yake jin ta, dole ne ma yasan yadda zai sanar da Ajiddeh dan bazai iya cigaba da b’oyewa ba, inma ya b’oyen to dole attitude da movements d’inshi su nuna, lumsassun idanunshi ya bud’e jin motsi kamar an fito a guje, inda yaji motsin nan yabi da ido, Batuul ya gani bakin staircase ta durkushe wajen tana kwarara amai, baisan lokacin da ya ture Ajiddeh dake jikinshi ba ya mik’e a rud’e ya iso inda take, rik’ota yayi ya jawota jikinshi yana rik’e da ita har saida yaga ta gama aman, Ajiddeh ce ta k’araso wajen ta rik’e k’ugu sai karkad’a jiki take taja wani dogon tsaki tace “iskancin banza, ke iskancin naki har ya kai da yi min k’azanta a parlour, jibi yadda kika b’ata min gida da amai, toh wlhy sai kin gyarashi tsaf, nan yayi maki kama da toilet”, ko ta kanta Abu baibi ba ya d’aga Batuul da ta gama galabaita cak yayi sama da ita, bai ajiyeta ba sai da ya shiga toilet d’in d’akinta sannan ya taimaka mata ta wanke bakinta, tana rik’e jikinshi har lokacin, suna fitowa ya kalleta with care yace “mey ki kaci ya saki amai?”, ko kulashi batayi ba saima k’ok’arin k’wace jikinta da ta shiga yi daga hannunshi, suna zuwa bakin gado ya saketa, kamar jira takeyi yana saketa ta sulale tayi kwanciyarta kan gadon ta lumshe ido tana maida numfashi, ganin ta lumshe ido yasa kawai ya k’yaleta ya gyara mata kwanciyarta yayi waje, k’asa ya sauk’o ya tarar Ajiddeh bata nan, kitchen ya shiga ganin stoves a kunne duk ya kashesu sannan ya d’auko Vacuum cleaner ya shiga gyara gun da tayi aman, d’akin ya koma yaga alamun tayi bacci, ya sauke ajiyar xuciya yaja k’ofan ya rufe, toilet d’in d’akin da ya kwana ya shiga yayi wanka ya canja wasu kayan, key d’in motarshi ya d’auka ya fita daga gidan yaje eatery siyo musu breakfast, har lokacin baiga Ajiddeh ba, d’akinshi da yasan zai samesu yayi knocking, ita ta taso ta bud’e mishi k’ofa, tana ganin shine cike da masifa tace “inji dai ta fito ta gyara min parlourn dan ni I can’t withstand wannan K’azantar,” wani mugun kallo ya sakar mata sannan ya dungure mata ledan ya juya ya barta nan tsaye baki a sake, kwafa tayi ta  d’auki ledan ta juya ciki, d’akin Batuul ya koma da sauran ledojin dake hannunshi yaga tana bacci har lkcn, bakin gadon ya zauna ya zuba mata lumsassun idanunshi, tausayinta ne gaba d’aya yaji yana ratsashi, har ta d’an fad’a, to wai ma me ke damunta haka, deciding yayi idan ta tashi still not ok su tafi hospital kawai, hannu yasa ya gyara mata gashin da ya zubo mata fuska sannan ya d’an shafi fuskan nata ya miqe ya fita waje, yunwa yakeji amma baijin cin abincin waje at all, kitchen ya shiga yaga kunun data fara, k’arasawa yayi ya ciro kifi da meat pie d’in da tayi baking, ya nufi dining ya zauna yaci, sai lumshe ido yakeyi yana cin abincin, a ranshi kuwa cewa yakeyi “She is angel, always different”, addu’a samun sauk’i ya dinga yi mata har ya gama cin abincin shi, parlour ya koma ya kwanta dan bai tunanin yau zai iya fita ya bar Batuul, duk bayan 30mins sai ya shiga ya dubata, Sallah azahar ma yau a gida yayi baije masallaci ba, baiso ta tashi baya nan, mamaki ne ya kamshi ganin har la’asar tayi amma bata farka ba, kuma baccin nata normal, yasan bata irin wannan baccin haka, ita kuwa da ta tashi wani baccin ke dauketa, bayan yayi sallahn magrib a gurguje ya fita ya siyo musu abinci, sai da ya fara kaiwa Ajiddeh nata sannan ya shiga d’akin Batuul har lokacin tana bacci, deciding kawai yayi ya tasheta sabida baccin yayi yawa, a hankali ya shiga tashinta bayan ya hau kan gadon, da k’yar take iya bud’e ido tana maidasu ta lumshe, d’agota yayi ya jinginar da ita jikinshi yace “Hey wake up, wannan wani irin bacci ne, tashi kici abinci, its already late, bacci tun safe”, a hankali ta bud’e lumsassun idanunta ta k’arewa d’akin kallo, a kanshi ta tsaida kallonta tace “Farida bata iso ba?”, tana sake lafewa a jikinshi, d’agota yayi yace “tashi kici abinci”, had’e rai tayi ta zumb’uro mishi baki tace “Ina Farida nace?”, tana magana tana dad’a sulalewa jikinshi, ganin baza ta tashi ba yace “Farida anyi delaying flight d’insu sabida bad weather baza su iso yau ba sai gobe da safe”, daga haka ya d’agata ta zauna, hannu yasa ya janyo pack d’in abincin yace “C’mon zo kici abinci”, ya bud’e pack d’in, da sauri ta matsa baya tace “mey wannan d’in?, ni banaso”, da mamaki yake kallonta yace “ba kya so kuma, duk yau baki ci komae ba fa, c’mon have it, ya d’ebo daga cikin spoon d’in ya kawo mata baki, da sauri ta toshe bakinta da d’ayan hannunta d’ayan kuma ta ture hannunshi da ya mik’o mata gabanta tace “Nace banaso, banason k’anshin abinci bazan ci ba, ka fita dashi”, kallon mamaki kawai yake mata, rai b’ace cike da masifa tace “ka matsar mana, nace fa bazanci ba”, abincin ya matsar gefe kamar yanda tace ya rik’ota da damuwa yace “toh mey zakici”,  kamar jira takeyi da sauri tace “Ni ice cream zansha”, baki ya bude yace “kina ma da hankali kuwa, ina tambayanki mey zakici kina ce min ice cream, I will slap you right away in baki bar wannan shirmen naki kin fad’amin abinda zakici ba, duk yau mey kikaci da zakice min wani ice cream zakisha, you were sleeping all day kamar wata jaririya”, tutturashi ta shiga yi daga jikinta tana murgud’a baki tace “Ni dama bance dole sai ka samomin ba ai, kuma ma ni da kaina zan iya zuwa inyi, bana ma so na fasa, ko ka kawoma bazan sha ba, ka tafi min daga d’akina ni”, ta d’an ja tsaki tayi kwanciyarta ta juya masa baya, ya kai minti biyu zaune yana kallonta da mamaki, can dai ya mik’e daga karshe ya nufi kofar d’akin, jin motsin kofa ta juyo da sauri tace “ice cream d’in zakaje kawo min?”, wani irin kallo ya watsa mata, bata damu da kallon da yakeyi mata ba tace “Ni kar kaje Cold stone fa, ko na lick ko scoop, ba na can nakeso ba, na gelatorino nakeso, sai flavour Kuma pistachio, strawberry, Madagascan vanilla, kuma banason na corn, su min scooping a cup, yawwa with a couple of some more exotic options kamar su coconut lemon grass, pepper mi…..”, bai jira ta gama surutun nata ba ya kad’a kai ya fice ya rufo k’ofan, baya ya jefa key d’in aljihunsa, gaba d’aya ya kasa gane what came over this girl, mota ya shiga sannan ya kunna map navigator yayi searching wajen da ta fad’a mishin, dan shi baisan ma inda gun yake ba, tafiyan 15mins ya isa wajen, duk abubuwan da ta lissafo mishi sai da ya siya harda k’ari, da snacks, bai jima ya dawo gidan, har lokacin bai ga Ajiddeh ba, d’akin Batuul ya wuce kai tsaye da ledojin hannunshi, tana jin motsinshi ta mik’e da sauri, daga bakin gado ya zauna ya mik’o mata ledan hannunshi, da sauri ta anshe, na snacks d’in ta fara ansa, rai b’ace ganin abinda ke ciki tace “nifa ba abinda nace inaso ba kenan”, ta tura mishi gabanshi, jin d’ayan ledan da sanyi yasa tayi hanzarin jawoshi ta shiga bubbud’ewa, ba tareda b’ata lokaci ba ta shiga shan ice cream d’in, kallonta kawai yakeyi ganin yanda takesha d’agowa tayi suka had’a ido, murmushi ta mishi tace “Thank you, you can have some”, tayi mishi nuni da ledan dake ajiye, kai kawai ya iya girgiza mata, tab’e baki tayi taci gaba da shan abinta, ko rabin na cup d’in batasha ba ta ajiye tace “Alhamdulillah, am full”, ta ajiye zata juya ta kwanta yayi maza ya rik’ota yace “meye hakan?, wai kina nufin har kin gama sha? kai ta gyad’a mishi tareda d’age mishi girarta d’aya tace “Ehh”, yace “abincin kuma fa?”, d’an had’e rai tayi jin ya ambaci abinci tace “Nifa bana jin yunwa, am okay”, ya d’an yu shiru sannan yace “toh brush d’in kuma fa da kike k’ok’arin kwanciya, and baki yi sallah ba, tace “nifa bacci nakeji, xan yi anjima wllh”, “Bacci?”, ya tambayeta dan yau wuni yaga tayi tana bacci kuma its just 8:08 yanxu, bata bashi amsa ba ta kwanta abinta, tana kwanciya kuwa bacci ya d’auketa, ya dad’e zaune yana kallonta daga baya ya tashi ya ciro mata kayan baccinta cikin closet ya cire mata na jikinta ya saka mata wanda ya ciro?, mamakin irin baccin nata kawai ya dinga yi dan har ya canja mata kayan bata tashi ba ita da bata da nauyin bacci,  addu’ar bacci ya tofa daga baya ya kashe mata wutan ya tafi d’akin da ya kwana jiya, wanka yayi sannan ya d’auro alwala yayi sllhn Isha ya koma gado, kamar jiya yau ma a waya ya dudduba ayyukan office da baiyi ba snn ya kwanta, sai wajen sha biyu snn Ajiddeh ta shigo  d’akin, yana jinta sai wani shige mishi jiki takeyi, ganin yayi bacci ta k’yaleshi  itama ta kwanta.
+
Washe gari da asuba bayan yayi Sallah direct airport ya wuce d’aukan Farida, arrivals ya wuce kai tsaye bayan ya gama parking, dai dai lokacin da Farida ta fito daga terminal janye da akwatinta, ita ta fara hangoshi, da gudu ta k’araso ta rungumeshi, shima d’in rungumeta yayi, cike da farin cikin ganinsa tace “Yaa Abu ina kwana, thought tare xa ku xo da Anty Batuul” da xolaya ta kare maganan da wide smile d’inta mai kyau shimfid’e fuskarta, murmushin shima yayi yace “Lafiya Alhamdulillah, Ya hanya?”, zumb’uro mishi baki tayi jin yace ya hanya tace “hmmmm ai ni shiyasa bana son bin wani flight inba B.A ba ko Emirates, kasan transit kawai muka tsaya amma suka fake da wani wai bad weather, baza mu taso ba sai bayan nan da 14hrs , ni ai da so nayi in koma Nigeria, amma sabida ina son ganin my other half”, ta wani lumshe ido tana d’aura duka hannayenta biyu a k’irji tace “Allah dan ita kad’ai na yadda na k’araso, kuma kasan wani abu……”, bai barta ta k’arasa ba yace “Let’s get going, d’an wannan surutun naki zamu kwana nan baki gama ba”, suna tafiya yake tambayanta Yasu Ammah da kowa a gida, kamar jira takeyi ta dinga mishi zuba, wasu abubuwanma ba ji yakeyi ba har suka isa inda yayi parking mota, butt ya bud’e mata ta saka jakarta a ciki, sannan ta xagayo ta zauna, sai da ya tada motar suna tafiya sannan ya juyo ya dubeta yace “kina jina?”, gaba d’aya hankalinta ta tattaro ta kalleshi jin yana mata magana, yaci gaba da cewa “Babu ruwanki da duk wani abu da zaki gani in mun je, Ajiddeh isn’t aware Batuul is my wife”, a firgice ta kalleshi tace “What?”, kallonta yayi ya wani hade rai yace “Yeah you heard me right, dan haka babu ruwanki da duk abinda ke faruwa cikin gidan, am repeating it, don’t try anything stupid like you did last time, babu ruwanki da Ajiddeh”, tabe baki tayi ta kauda kai, yace ” Baki da hankali ina mako magana kina dauke min kai” xumburo baki tayi ta gyad’a mishi kai alamar ta ji, ya hade rai sosai yace “bakida bakine?”, ta dan murguda baki tace “Toh naji mana”, kwafa yayi ya ci gaba da driving dinsa, ta d’auke kai ta juya tana kallon window, ranta ne taji ya baci ba k’adan ba wai Ajiddeh batasan Batuul matarsa bace, toh does that mean they weren’t intimate ko me, shine har Ammah ta fara lissafin jikoki, “Chabdi” ta fad’a a ranta ba tare da tasan ya fito fili ba, juyowa yayi yana kallonta yace “kikace meye?”, maza tayi ta kad’a mishi kai tace “No ni bance komai ba”, ya harareta ya maida hankalinsa kan driving din da yake,farida taci gaba da sak’e sak’enta, a ranta tace masifaffe wai wani I shouldn’t try anything stupid, tabdi ai kuwa wlhy sai dai in wannan matar tasa mai kama da bishiyar gwanda sai tsawo babu shape tayi hankali itama, dan indai ta tab’ani ba yadda za ayi in k’yaleta wlhy sai na rama, kuma sai nasan ynda nayi tasan wacece Batuul, “kutt, ai wlhy bama zai yiwu ba”, batasan a fili  tayi maganar ba saida taga yayi parking yana mata wani irin kallo yace “meye d’in ne bazai yiwu ba?”, da sauri ta shiga girgiza mishi kai a rikice tace “I wasn’t talking to you fa”, ya jima yana kallonta fuskarsa daure kafin yayi k’wafa ya ci gaba da driving, bata kuma gigin wani tunanin ba bare har ya fito fili, kamin su isa har gari ya washe, bayan yayi parking kamin ta fito in a serious tone yace mata “hope you heard all I said clear?”, kai kawai take girgiza mishi dan ita ta matsu taga Batuul, yana bud’ewa ta fita guje ta shige gidan, tun daga bakin k’ofa ta fara ihun “His beloved, His First Lady, kina ina na iso”, A guje Batuul dake kitchen ta d’an samu karfi tana gyare gyaren kitchen din ta fito jin muryar Farida, Ajiddeh da Aunty dake d’aki ma fitowa sukayi lokaci d’aya ganin wake ihun, Abu kam mamakin Farida ne ya cikashi jin abinda take fad’i, ya k’asa karasawa parlorn, ita ko ta tafi da gudu suka rungume juna da Batuul cike da murnan ganin juna, farida ta tura Batuul daga jikinta tana kare mata kallo ta wara ido har da d’an tsallanta tace “Waoww waow, yayana ya iya kiwo wllh, kinga yanda kika yi wani fresh kika yi kyau kuwa love, OMG” wani tsawa da ya rikita ta daga ita har Batuul din Abuturrab ya daka mata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *