BATUUL CHAPTER 21

BATUUL




CHAPTER 21




Cikeda masifarta take kallonshi, shiko karasowa yayi hannunshi cikin aljihun wandonshi yace “Sit!, magana zamuyi”, kallonshi ta tsaya yi a tsagere kamin ta zauna ganin duk ya canja mata kamar ba Idrees d’in dake shakkarta da gudun b’acin ranta ba, wanda in ta fad’i abu jiki na rawa zai d’auki maganan, had’e rai tayi ta dake tace “Wai kai yanzu sabida tsabar wulakanci kan wadannan tsinannun kayan naka kasa na taso na baro muhimman abubuwan da nakeyi a Abuja na taho Lagos?, toh wlhy yanzu maza maza ka kwashe tsiyarka kuma gyaran ma ni ba irin wannan nace maka inaso ba ai”, ba yabo ba fallasa ya fara magan yace “Tun baki san kayan mene ba kike wannan b’ab’atun, toh kaya dai nakine in baki sonsu ki zubar dan haka al’ada yace min kuma itama d’in haka nayi mata”, katseshi tayi da hannu tace “Kayi wa uwar wa irin wadannan kayan, dan cin mutunci irin naka ma ba ni kadai kayiwa wadannan kayan ba harda had’ani da banzaye, nasan bazai wuce wad’annan masu kafar sauron bane da ke yawo a cikin gari kayi mana tare dasu, nasha fada maka ka dena had’ani da wadannan matsiyatan kana mana kaya tare……”, bata rufe baki ba sai ji tayi yace “Aure zanyi next week, Kayan fad’ar kishiya ne gashinan snn wannan yawon naki daka yau kin barshi kenan, in har badaa izinina kika fita ba toh koma inane kikajeshi karki dawo min gida, kiyi zamanki a can”, brain d’inta ne ya dena functioning for a minute, kamar a planet Neptune take jinta sbd yadda taji tana yawo saman iska, komai na juya mata, ido kawai ta zuba tana kallonshi har saida hankalinta ya dawo snn ta miqe tana cire duk wani abu dake kanta dan ji takeyi sun mata nauyi, takowa tayi tazo gabanshi tana mishi wani mugun kallo tace “Kace meye?, Aure?, Idrees ashe ko lallai zaka tafka babban kuskure na rayuwanka da baka taba yi ba wlhy, tun wuri ka gyara maganarka, kai d’in banza har ka isa tozartani kayi min kishiya?, wlhy Allah baka isa ba, bamu gaji ayi mana kishiya ba, You had better take back your words tun muna mu biyu da kai kamin duniya ta jimu, kai ka ma isa kayi aure, toh duk munafikan da suka saka yi dan ganin bayana sunyi kad’an, Ka koma kace musu ta Allah ba tasu ba ni nafi karfinsu, ai babu mai yimin wannan tijarar ni nasani inba wannan tsohuwar da ka ajiye can gida ba”, Tasss ya d’auketa da mari da yasa hawayen dake idonta ya shiga zubowa, mik’ewaKame tayi cikin zafin rai ta cakumo rigarshi tana “Wlhy sai kasan ka mareni, munafiki kawai maci amana, azzalumi, wlhy ba ni ka wulakanta ba sai tsohuwar banzar da ko tafiya batayi daka ajiye a gida, kwace rigarsa da ta cukwuikuye yayi daga hannunta snn ya kara mata wasu lafiyayyun marin, cikeda fushi ya shiga bugunta ko ta ina, duka yakeyi tana ihu tana zage_zage, duka yayi mata sosai har saida yaga ta jikata snn ya jefar da ita yayi yace “Keh kinyi kad’an, nan gaba koda wasa kika kuma zagar min Family sai nasa kinyi regretting, keh d’in har wata matar kirki ce da baza ayiwa kishiya ba?, mey kika iya a auren da har zai hanani yi miki kishiya kullum in kika fice kika bar gari sai lokacin da kika ga dama kike dawowa, wane mijin ne zai yadda matarsa take irin wannan shashancin, Y’ay’an da kika haifa da kansu basu san dad’in uwarsu ba, basu taba samun time d’inki, I have finally made my decision, aure ne nan da sati biyu zanyi shi” ya tsallaketa yayi ficewarsa daga d’akin amma har lokacin bakinta bai mutu ba sai zazzaga rashin mutunci takeyi, da k’yar ta iya samu ta mik’e ta janyo jakarta ta ciro wayarta daga ciki, tana kuka ta shiga neman layin wayar Mummy, bugu d’aya ta d’aga daga d’aya b’angaren tace “Wai uwar mey ya miki da ya uzzura miki da dawowa, jarababbe”, Jainaba ta fashe da wani matsanancin kuka tace “Nikam na shiga uku, Yaya kasheni yakeson yi”, Mummy tace “Kasheki? Dan uwarsa shi ya haifake da zai kasheki, shege matsiyaci”, Jainaba na sheshek’a tace “Yaya wai aure zaiyi shine ya kirani harda kayan fad’ar kishiya”, Mummy ta buga k’irji ta miqe tsaye tace “Ni Zuwaira, Jainab Bakal Abuki, da hankalinki kike kiramin mijinki aure zaiyi?”, Jainaba na kuka ta gama fayyacewa Mummy gaskiya da karyar abinda ya faru, Mum tasa salati, nan ta rarrashi Jainaba akan zasu nemo maganin matsalar snn suyi maganinshi, daga nn sukaci gaba da zaginshi da yadda za aci uban nashi daga nan sukayi sallama




+

STORY CONTINUES BELOW


Tun da suka karb’eta sukayi emergency suka fara aiki akanta basu fito ba saida suka tabbatar she is fine, sai bayan awa uku suka fito suka barta ta huta bayan sun mata allura, Office d’inshi doctor ya dawo bayan ya sa an maidata Amenity, nan ya tarar da Dad zaune anyi mishi treating hannunshi da yaji ciwo, bayan ya zauna ne ya fara yiwa Dad bayanin abinda ya sameta “Sir she is fine, Yeah she had a minor cut on her at her back, some wounds on her head which made her lose a lot of blood, that’s what cause the fainting and a broken arm, but she will be awake in some hours time and then she can be taken home”, wani irin ajiyar zuciya Dad ya sauk’e jin tana raye snn zata samu sauk’i In sha Allah yace “Can we see her now?”, Doctor ya kada kai yace “Yeah sure Sir, lemme calk the Nurse to lead you there”, haka akayi yana danna bell Nurse ta shigo ya fada mata inda zata kai Dad da haka yayi mishi sallama tareda godiya yabi Nurse har d’akin da aka kwantar da matar, a hankali suka tura kofar d’akin suka shiga, kwance take abinta tana bacci amma da gani ba mai dad’i bane, sun canja mata kaya zuwa wani blue yard, tausayinta yaji a ranshi ganin duk an d’aura mata bandage, daga bakin gadon yace “Sannu Baiwar Allah, tsautsayi ya ritsa dake, Allah ya baki lafiya”,,, sosai yake jin tausayin nata har ya fara tunanin ko ina y’an uwanta suke, yanzu hankalinsu gaba d’aya ya gama tashi duk Inda suke, Allah ya basu hakuri, da ta warke zai maidata gida yayi musu bayanin komai snn ta basu hak’uri game da tsautsayin da ya samesu, daga haka yacewa Nurse d’in zai turo masu zama da ita, da haka ya fita lokacin Ado ma an gama duba shi lafiyarsa kalau, sukayi waje suka nufi gida




Tashi yayi ya zauna yana salati tareda fad’in “Innalillahi wa inna illaihi raji’un”, juyawa yayi gefenshi yaga Ajiddeh kwance daga d’aya side d’in tana baccinta hankali kwance, mafarkin da yayi keh mishi yawo akai, cikin hanzari ya sauka daga kan gadon ya fita daga d’akin, d’akin Ammah ya nufa kai tsaye ya bud’e k’ofan ya shiga, ko ina babu haske, karasa shiga yayi snn ya kunna wutan bedside lamp, Batuul ya gani kwance sai juyi takeyi a hankali kamar wani abin ke damunta, goshinta duk yayi zufa, Tashi yayi maza yayi switching Ac d’akin, a nan yaga Farida dake kwance kan Sofa, stool ya jawo ya zauna gaban gadon yana kallon Batuul dake kad’a kai, siririn hawaye na bin kuncinta, hannu ya d’aura kan goshin nata tareda k’iran Sunanta shima yana jin kamar yayi hawayen “Fatima”, a hankali, kamar taji kiran sunan ta bar yatsina fuskarta da takeyi, gumin ya soma share mata snn ya cire hular dake kanta ya fara tofa mata addu’a, tun tana motsi a hankali har ta dena alamun tayi bacci, nan ya zauna yana tofa mata addu’a har bacci ya d’auke sa zaune kan stool d’in, Ammah da ta shigo da asuba ta ganshi yana bacci zaune kan stool hannunshi cikin na Batuul sosai ta tausaya mishi, a hankali ta matso gabanshi ta d’an tab’ashi, a d’an firgice ya mik’e yana kallon Ammah, tausayin na fuskarta tace “Abu lokacin Sallah yayi kaji”, kallon Ammah yayi snn yace “Ammah Batuul ta tab’a zuwa Ndjamena ne?”, kallonshi tayi tana son gano wani abu snn tace “Menene?”, Kai ya kad’a snn yace “No its okay, am just asking”, bata matsa ba ta kyaleshi tace “Jeka masallaci kaji, lokacin zai wuce”, mikewa yayi yana
Kallon Batuul haka ya fita yayi nashi d’akin, Ajiddeh na nan kwance kamar kullum, wanka ya shiga yayi a toilet snn ya fito ya tadata yace tayi Sallah, har ya fita bata tashi ba, haka nan akaci gaba da yiwa Batuul magani, kullum doctor sai yazo ya dubata kuma, Ajiddeh sau d’aya in ta shigo ta dubata take komawa d’akin Abu, sai in an gama abinci ta sauk’o in taga dama, in kuma batayi niyya ba haka zata zauna, amma ko da wane lokaci gabanta fad”uwa yakeyi, ta rasa yadda zatayi da Mum har ta kashe wayarta gaba d’ayanshi, fargabanta d’aya kada Batuul ta farka asirinsu ya tonu, wata zuciyar nace mata ta fad’i gaskiya ko don son da take yiwa Abu amma sam d’ayar zuciyar ta haneta, bayan sati ranan da za a gama yiwa Batuul sauk’ar Al Qur’an ranan ta yanke shawaran fad’iwa Abu gaskiya koda zaiyi sanadiyyan rabuwarta dashi, daren ranan kasa bacci tayi sai juyi takeyi, har Abu ya fita ya barta idonta biyu, lokacin da ya dawo tashinta sallah ma zaune ya ganta tayi tagumi, kallonta yayi yace “Babe what’s wrong with you?”, ajiyar zuciya ta sauk’e tace “Ba komai”, bai sake ce mata komai ba yace “tashi kiyi Sallah, its time”, daga haka yayi hanyan waje “Har yaje bakin k’ofa yaji tace “Aliyu”, juyowa yayi yana kallonta , kasa fad’a mishi abinda tayi niyya tayi jiki a sanyaye tace “Naga ka rame ne, you should rest, ka rage stress d’in”, murmushi yayi mata kawai yace “I will babe, je kiyi Sallah” daga haka ya fita, fad’awa tayi kan gadon ta saki kuka mai cin rai, tasan ko Abu ya hakura ya barta iyayenshi baza su hakura ba, har ya dawo daga masallaci tana nan batayi Sallah ba, ganin ta kwance inda ya fita ya barta yasa ya shigo ya zauna bakin gadon tareda d’agota, jikinshi ne yayi sanyi ya rungumeta a jikinshi yana patting bayanta, kamar wacce aka dad’a tunzurawa ta fashe da wani sabon kukan, cikin rad’a a kunne yace “Shhhh baby, its alright, she will b fine okay?, pray for her”, hawaye na zuba idonta ta shiga girgiza kai ta d’ago tana kallonshi, cikin kuka tace “Aliyu pls forgive me, kaji Dan Allah ka yafemin, wlhh ban San mey ya kaini……..”, kallonta ya tsaya yi da kyau snn ya sake jawota jikinshi ya matse yace “She will be fine kinji, babu abinda kika mata, it wasn’t your fault, azzaluman da suka sata in this condition will pay for each pain they caused her, its okay ki dena kuka kinji, she needs your prayers more than your tears, your sister is gonna be alright kinji”, kuka sosai ta shigayi har saida ya tausaya mata, ya d’agota ya kama mata gashinta da suke a baje yayi making mata messy bun snn yace “kinyi Sallah ne?”, kasa bashi amsa tayi hakan ya tabbatar mishi da cewa batayin ba, kamo hannunta yayi ya kaita toilet ya jirata har tayi brush tayi alwalan snn suka fito ya shimfid’a mata abin sallah ta hau tayi, yana nan zaune har ta idar kuma har lokacin hawaye takeyi, gado ya maidata ya kwantar ya lulluba mata duvet yayi mata peck snn yace “Get some rest and pray for her, she is gonna be alright and back to us okay?”, kai ta kad’a mishi, murmushi yayi mata da ta kasa maida mishi snn ya juya ya fita tareda rage mata wutan d’aki
D’akin Ammah ya koma bayan ya fito d’akinshi, bai tadda kowa ba sai Batuul dake Lullub’e cikin comfy bargo tana bacci, d’akin ya shigo ya tura k’ofar ya karasa ya hau gadon ya zauna, bargon nata ya janye yaga gashinta da ya bud’e tun jiya na nan a bud’e, kallonta yakeyi with so much affection da tausayinta a idonshi, hannu yakai ya gyara mata gashinta ya maida shi baya, kallon face d’inta da ya kara haske ya tsaya yi kamar ba ciwo takeyi ba, dukda ta rame amma kyanta na nan, satinta d’aya kenan kwance anan batareda tasan ina kanta yake ba, d’an murmushi yayi tunawa da yayi yau za a gama yi mata magani in Allah ya yadda ta samu sauk’i ya kai hannu ya shafi gefen fuskarta tareda lumshe ido yace “Haya”, hannunta ya kamo cikin nashi cikin sanyin murya yace “Fatima you are more than life itself, nasan kina jina ko Fatima, you are worth everything good life can offer, GWS kinji, I need to tell you how much you mean to me, you’ve become part of me, you know I never thought I could love anyone, I never tot someone could mean this much to me until I met you, The first moment I saw you, I knew there was something great about you, some vibes I can’t explain, Mesa tun a da ban dawo gareki ba, I wish I had known you long ago, You have become a part of me, my Haya, I never knew I had life until I met you, in such a small period you have made me understood what love means, I never knew how it felt to b loved, at the beginning inace k’in ki nakeyi sabida effect da kike casting a kaina, but I was wrong, I was growing fond of you, you became an acquaintance, a friend and the very best person I could ever ask for”, d’agota yayi ya d’aura kanta kan cinyarshi ya kama fuskanta da duka hannayenshi, idonshi ya rine har ya fara hawaye yaci gaba “Fatima pls get up, get up and don’t leave me, I need to tell you how much you mean to me, I promise to keep you Happy all the time, Plssss Fatima, I really need you, just give me a second Chance to show you how much I love you, I really do”, bai damu da drip d’in dake hannunta ba, rungumeta yayi Idonshi duk ya kad’a, a haka Ammah ta shigo ta sameshi, tun daga bakin k’ofa take jiyo maganganun da yakeyi, sosai take tausaya mishi itama har idonta ya cicciko, jiki a sanyaye tazo ta zauna daga gefenshi ta dafa kafad’unshi tace “Babana I’ve told you times without number addu’a zakayi mata, zataji sauki yau d’innan In sha Allah”, kallon Ammah yayi da rinannun idanunshi ya kad’a kai yace “Ammah cewa fa yayi in har aka cikata na kwana bakwai ba a samu nasara saidai wadanda sukayi abin nan sun karya da kansu, su waye haka zasuyi mata irin haka, mey tayi musu Ammah?”, Ammah ta girgiza kai hawaye taf idonta tace “Abu be optimistic, Da izinin Allah ya fisu, kuma zata samu sauk’i, mu jira har anjiman a gama mata magani sai muga abinda zai faru, kaci gaba da yi mata addu’a”, shiru kawai yayi ya kasa cewa komai, tashi Ammah tayi tace “bari inje in sa a shirya shigowan Asheikh d’in sai inzo in shiryata”, da haka ta fita daga d’akin zuciyanta duk ba dad’i ga fargaban dake tattare da ita, bayan ta fitane ya gyarawa Batuul d’in gashinta snn ya saka mata hularta




+

K’arfe bakwai Ajiddeh taji wayarta na ringing, kin dagawa tayi ganin Mum keh kira, duk fargaba ya cikata har wani sanyi sanyi takeji, zata kashe wayar kenan taga text ya shigo, budewa tayi ganin daga Mum ne, ce mata tayi “In baki d’auki wayan nan ba toh wlhy yanzu zaki ganni gidan da kika maida yafi iyayenki”, jiki a Sanyaye ta gama karantawa kamin tayi wani abu aka sake Kira, saida ya kusa katsewa ta d’aga da k’yar tasa a kunneta, muryar Mum taji da daki dodon kunnenta tace “Don uwarki har kinyi girman da zan rika kiranki kina kashemin waya ko Ajiddeh, toh gani nan tafe gidan naku sai kin fad’amin dalilin da ya sa duk kika canja, kamin tayi magana taji kiit an kashe wayar, b’ari jikinta ya hau yi jin abinda Mum tace mata, hawayen ma kasa yinshi tayi tsabar tashin hankali, a ina zata samu mafita ita yanzu, tana yiwa Aliyu son da har in ya rabu da ita toh lallai itama zata rabu da tata rayuwar, d’aukar wayar tayi zata kira Mum tace mata zatazo ita gidan basai Mum d’in tazo ba amma har k’iran ya katse Mum bata d’auka ba, sau uku tana k’ira amma har lokacin bata d’aga ba, hannu tasa a ka ta saki wani razananna ihu ta tsuguna a wajen ta saki matsanancin kuka, shawara kawai ta yanke ta fadawa Abu ganin batada wata mafita, wayar ta jawo ta kirashi taji wayar na ringing a cikin d’akin, takaici duk ya isheta, mikewa tayi taje ta sameshi ta fad’a mishi komai, a ganinta hukunci da zai yanke mata ba zai zama mai tsauri ba snn yana sonta zata bashi hakuri tace duk sharrin shaidan ne, hakanan ta fito ko d’ankwali babu daga ita sai y’ar rigar baccinta, gashin da Abu ya tufke duk ta baje shi, Tana fitowa ta kusa cin karo da Ammah, kallonta Ammah tayi ganin duk ta rikice, da k’yar Ajiddeh ta iya had’a kalmomin daga bakinta tace “Ina kwana”, Ammah da ta tsaya kallon yanayinta tace “Kin tashi lafiya?”, kai kawai ta iya gyad’awa, Ammah ta tab’e baki tayi tafiyarta tana mamakin Abunda ya sami Ajiddeh yasa duk ta rikice da idonta ya kumbura ya rine kamar wacce tasha kuka, ganin Ammah da Ajiddeh tayi ya sake tsoratata, ji tayi jikinta duk yayi sanyi a haka take ganin baza ta iya tunkarar Abu da zancen ba don tun da suka xo gidan har yau bata ga fuskarta da na Farida ba, Sadiq kadai ke kulata gidan, shi kansa Abu ba wani lokacinta garesa ba, komawa d’akin tayi ta zube kan gadon ta rasa inda zata sa ranta taji dad’i



STORY CONTINUES BELOW


K’arfe bakwai daidai Abu ya sauk’o da Batuul rungume da ita bayan ya gama shiryata ya shafa mata su Zaitun da habbatus sauda ya gama mata duk abinda ya kamata kamar yayi side d’in Abui inda ake mata magani, sauk’ar Qur’ani aka fara mata kamar kullum, Kowa zama yayi kawai yana zuba mata ido ganin mey zai faru, Farida na jikin Abui har wani rawa jikinta yakeyi, Abu kam ko kusa da ita bai bari ba yana nan rik’e da hannun nata, anayi Abu na d’an d’iga mata ruwan Zamzam da Ma’ul Ward snn ya shafa nan fuskar tata, Kaskon turaren wuta Asheikh yace a mik’o mishi nn aka had’a komai aka bashi, daga cikin jaka ya ciro wani gari a cikin roba ya barbad’e cikin wutan, nan da nan hayaki ya gauraye ko ina na d’akin, wani dogon numfashi Batuul taja tareda tari, ihu tasa tana k’ok’arin tashi ta xauna, baka jin komai a d’akin sai Kabbara da Hamdala da su Ammah keyi ganin ta farfad’o, Abu kam ido ya zuba mata ya kasa motsi, rungumeta yayi hawayen da ya taru idonshi ya gangaro, fuskarta ya lalubo yana kallonta yace “Haya, bud’e idonki ki ganni kinji, dont leave me again pls, I promise to keep you safe In sha Allah but don’t try leaving”, kantane taji yana juya mata ga wani irin amai datakeji, cikinta jinshi take duk ya hautsine, gaba d’aya bata da karfi, so take ya saketa amma batasamu yayi hakan ba, duk da kakarin Aman da takeyin, kamin yayi yunk’urin taimaka mata ta fara kwararo amai, wani irin amai takeyi bak’i kirin da wasu irin tsaba, kwararo shi kawai take ba ji ba gani, har wani sama sama numfashinta yakeyi, Abu zaiyi magana Asheikh ya d’aga mishi hannu alamar yayi shiru babu komai, amai ta dinga yi sosai, wani razanannen ihu tasa saiga cikin aman wani abu ya fad’o kamar blood clot, abin na fad’owa ta lumshe ido ta sulale, har lokacin bai bari ta bar jikinshi ba, tana kwanciya bacci ya d’auketa.





Mum a can gida duk hankalinta a tashe ta rasa da wanne zata fara, mijin Jainaba dake shirin tozartasu ko kuma Ajiddeh dake kunsa mata bakin ciki tana son jawo mata attack, ga wata munafika da Dad ya dawo gida da wai accident sukayi amma yanzu ita duk ba ta tasu takeyi ba, so take ta fara magance Jainaba da Ajiddeh tukunna inyaso asan abin yi kan buzuwar da ya kawo mata gida, bayan sun gama waya da Ajiddeh ta jefa wayarta cikin Jaka ta fito ta sami driver ta fad’a mishi inda zai kaita, gidan su Abu tace mishi tanaso, umarni yabi har saida sukazo gidan ta fita tace ya jirata ba jimawa zatayi ba, baki ta sake tana karewa gidan kallo, duk kallonta da manyan gidaje hadaddu wannan daban yake, a ranta kuwa cewa tayi “Shine waccan sallamamiyar take son janyo mata asara, irin wannan daula sai sun kwashi rabonsu ai”, har ta shigo cikin gidan sake sake takeyi cikin ranta, Da Ammah suka fara cin karo, rikicewa tayi ganin Ammah amma ta dake ta kirkiro murmushi tace “Hajiya Bilki kin ganni da sammako ko, wlhy abubuwane nayi dayawa gashi Ajiddeh tace min satinsu d’aya yar uwarta bataji dad’i ba shine nazo dubata, in banyi sammakon bane bazan samu time ba”, Ammah tsabar mamaki kasa magana tayi, mamaki fal ranta kuma hankalinta sam bai kwanta da zuwan Mum ba, dakewa tayi tace “Alhamdulillah mai jikin ma ta fara jin sauki, Allah bada lada”, Mum ta tab’e baki tace “ko ba sauki ba, saukinta d’aya ai mutuwa”, amma a fili tayi murmushi tace “Allasarki baiwar Allah, tasha wuya Allah yasa kaffara ne”, Mum dai ce mata tayi “Amin”, snn tace “Hauwa na sama ko, kamin kiga mai jinyar”, Mum tace “Ahh toh shikenan, ba jimawa zanyi ba”, Mum ta kira d’aya daga cikin masu aikin gidan tace ta kaita d’akin da Abu yake snn tace a kai musu refreshments can sama, saida sukayi gaba tayi inda aka kwantar da Batuul take bacci, lokacin babu Sadiq da Farida da kuma masu yi mata sauk’an sun fita, Asheikh ta tarar yana magana yace” Hajiya keh muke jira dama, Alhamdulillah yarinya ta samu lafiya kuma kamar yanda muka fad’i sihiri akayi mata snn Allah cikin ikonshi ya bayyana mana wad’anda sukayishi”, dafe k’irji Ammah tayi tace “Innalillahi wa inna illaihi raji’un”, Abui ya kad’a yace “La hawla wala quwata illa billahi aliyul azim, Subhanallah”, Abu dai kai kawai ya d’ago yana jiran jin karashen bayani, Ammah tace “Allah ya kyauta, yarinyar nan bana tunanin tana da matsala da mutane”, Asheikh ya d’anyi murmushi yace “Ai yanzu ba sai kayiwa mutum komai ba zaiso ganin bayanka”, Ammah ta sauk’e ajiyar zuciya tace “Allah ya kyauta”, Abu duk ya k’osa yaji wad’anda suka sa Batuul cikin wahala, har wani zafi ranshi keyi dan shi kad’ai yasan abinda zaiyi musu, sai yasa sun d’and’ani azaba fiyeda yadda suka sa Batuul ko su din su wayene kuwa yace “Asheikh munaji, zamu iya sanin sunayensu?”, Asheikh yace “Ehh kaga wannan abinda ta amayo shi ya nuna mana ko su waye su, dama shi irin wannan sihiri mugune, sosai yake lahanta mutun dan bama sihirine na haka ba, yarbawa sunfi yinshi , ba kowa ke iya juresa ba, in har aka yiwa mutum shi toh indai maishi ya mutu, ko ba dade ko ba jima sai ya koma kan wanda yayi shi, inko bai mutu ba, a irin haka duk abinda ya fito jikinsu toh da sunayensu zai fito kamar yadda nata yayi”, Abu dake tsaye kai kawai ya dafe dan ya fara losing cool d’inshi, baya tunanin inyaji sunayensu zasu k’ara minti talatin ba a prison ba, cikin tunanishi kamar daga sama yaji ana ambaton, “Zuwaira, Jainaba da Ajiddeh”, da sauri ya d’ago dan gaskata abinda yakeji, wani irin nauyi yaji kanshi yayi mishi kamar an d’aura mishi dutse, bai ankara ba sai ji yayi hawaye na bin kuncinshi, kai ya shiga girgizawa yana matsawa da baya, if his memory still serves him right sunan matarsa Ajiddeh yaji daga bakin sheikh itada iyayenta, jirine yaji yana neman d’ibanshi da sauri ya samu bango ya dafa, Ammah da ta tsaya itama da mamaki tayi hanzarin rik’oshi ganin zai fad’i, banda ance Azzanu zambin, zato zunubine amma hankalinta Sam bai kwanta dasu Ajiddeh ba, ido ya lumshe ido ya bud’e hawayen na ci gaba da zubowa yace “Ammah kinji?, kinji wai Su Mum d’in Ajiddeh su sukeson kashe min Fatima, Ammah mey tayi musu zasu kasheta, mey tayi musu?”, rungumeshi Ammah tayi tace “Shhhh Babana, Allah yayi da sauran kwananta a duniya, babu abinda zai sameta”, kuka ya fasheda kamar wani karamin yana rungume da ita.Can a asibiti lokacin da Matan nan ta farfad’o, Daddy da nurse na d’akin, nurse d’ince ta taimakawa matar ta gyara kwanciyarta, sai a snn taji duk jikinta ya rirrike ga wani ciwo da takeji a ko ina na jikin nata, k’arewa d’akin kallo ta shigayi har saida taji muryar Dad yana cewa “Sannu baiwar Allah”, da sauri ta dubi inda yake snn ta d’ago kai tana k’arewa d’akin kallo, a hankali ta shiga rera kuka, Dad da hankalinshi ya fara tashi ganin tana kuka yasashi tunanin ko kad’eta da sukayi ne ya sata yace “Subhanallahi sannu kinji, Allah ya baki lafiya kiyi hak’uri ki bar kukan haka kar ya k’ara miki da ciwon”, yayi ma nurse alama da a kira doctor, har doctor ya shigo bata tsaida kukan da takeyi ba, yana zuwa bayan ya duddubata yayi mata allura, bata jima ba bacci yayi gama da ita, har aka cika kwana uku bata cewa komai, kullum Daddy yakan zo ya dubata safe da yamma, abinci ma sai nurse d’in tayi dagaske take daurewa taci kad’an, a ranan da ta cika kwana uku tun da safe da Dad yazo aka sallameta bayan magunguna da doctor ya bata, gida Dad ya kaita ya sa aka gyara mata snn ya zuba mata masu aiki, washegari bayan ta huta Dad ya shigo ya sameta bayan sun gaisa ya fara tambayarta inane gidansu, kamar jira takeyi ta fashe mishi da kuka, da kyar ya samu tayi shiru snn tace “Ba mu da gida”, Dad ya d’an wara ido ya gyara zama yace “ban gane ba ku da gida ba baiwar Allah, akwai wadanda basuda gidane?, kiyi hakuri ki sanar dani mu samu mu maidaki muyi musu bayanin tsautsayin da ya sameki”, cikin kuka ta fara “mu biyu iyayenmu suka haifa nida Yayata Sa’adah, ranan da aka haifeni Allah yayiwa mahaifiyarmu cikawa, ban girma nasan dad’in uwa ba saidai rashinta, Babana da Yayata sune suka hanani kewar rashin uwar da nayi, mu yan k’asar Niger ne, ina shekara bakwai lokacin yayata ta auri wani d’an Nigeria da suke kasuwanci tareda Mahaifinmu, bayan an gama biki za a tafi da ita tasa kuka tacewa Babanmu Dan Allah ya bata ni mu tafi tare, da kyar iyayenmu suka yadda akan cewa in nayi kwana biyu a dawo dani, niko da murnata na biyota dan inason Nigeria, gidane mai girman gaske a garin Kaduna yayata take zaune, part hudu ne a gidan, nashi d’aya, yayata d’aya, uwar gidanshi sai kuma na uwar mijin, tun bayan biki yayata tasa mijinta ya nemamin makarantar kud’i da Islamiyya ta sakani batareda Babanmu ya sani ba, sai bayan wata biyu yace ta dawo dani sbd makaranta tayi magiyar ya bar mata ni, badan yaso ba ya kyaleni a wajenta, har Yayata tayi shekara bata taba koda batan wata ba, daga nan tsangwama ya fara mata a gun dangin miji, numfashi kwakwara bata isa yi ba yanzun zasu fara mata habaici ana zaginta, duk da ina k’arama amma na fahimci bata cikin kwanciyar hankali, maigidanta kullum shike kwantar da hankali kasancewarshi mutumin kirki, Hutu hutu takan shiryani inje gida watarana kuma tare muke zuwa, shekara biyar da aurenta akayi mata waya Babanmu babu lafiya, gaba d’aya hankalinmu ya tashi tunba Yaya Sa’adah ba, mijinta Ishaq ne ya kwantar mana da hankali yayi mana shirin tafiya, washegarin ranar muka isa gida muka tarar Babanmu rai a hannu Allah kwana mukayi yana mana Nasiha kan zaman rayuwaa snn yacewa Yayata ya bata Ni ta riqeni amana, kwananmu uku ya cika, munsha kuka ba kad’an mana, a ranan Ishaq mijin ta yazo bayan bakwai muka koma Nigeria mukaci gaba da rayuwa, duk bayan shekara sai Yaya sa’a tayi b’ari, tun bata damuwa abun ya fara damunta, duk inda taji ana bada magani sai taje nema amma ba a samu sa’a ba, shekara biyar tana yin asarar ciki, a shekara na shida ta samu cikin ya zauna snn nima a shekaran aka min aure da wani d’an unguwarmu malamin university da mukayi soyayya, bayan wata shida da bikina Yaya ta ta sake samun wani cikin da ya bata wahala, ranan da zata haihu muna tare take ce min duk abinda ta haifa kada in barshi hannun kowa inyi mata alkwarin riqeshi, kamar tasan mutuwa zatayi tana haihuwa ta rasu, abinda ta Haifa ma bayan awa hudu ya bita, tashin hankali babu irin wanda ban gani ba, da kyar na samu na saba da rashinta, haka na koma rayuwa banida dangi, bayan shekara d’aya na haifi Yayana maza yan biyu daga nan ban sake wani ba sai bayan shekara bakwai na haifi mace”, tsananta kukanta tayi sosai, Dad da ya tausaya mata ya mik’a mata tissue paper ta ansa ta goge hawayenta taci gana da bashi lbr tace “Safeena na jinjira rannan da rana wata mata ta shigo mana gida wai gidantane, nidai ban kulata ba na tattara yarana muka shiga ciki dan yanayin matar ma abin tsoro ne, da daddare bayan Sulaiman ya dawo ya huta nake sanar dashi abinda ya faru, yaje ya dubo mata ya dawo yace min ai matarsa ce anma tun kamin muyi aure tabar gidanshi ta tafi makkah shine ta dawo yanzu, tunda matan nan tazo mukayi sallama da kwanciyar hankali, masifar yau daban ta gobe daban, bayan watanni da zuwanta rannan muka tashi da safe Sulaiman ya rasu, tashin hankali babu irin wanda bamu gani ba, Yaya Ishaq mijin Yayata babu yadda baiyi in dawo gida ba nace zan zauna tareda Yarana in kula dasu mungode, rannan Hussaini ya shigo min d’aki duk ya rikice nake tambayarsa mey ya faru yace min yaji Larai suna hira itada wasu mazan wai su suka kashe Daddy,  na jawoshi na rungume nace kada in kuma jin haka a bakinshi ba abinda ya jiyo ba kenan, tun daga lokacin na tsorata da lamarinta, na dena barin yarana a ko ina kusa da ita, wata d’aya kenan yanzu da na san rasa komai na rayuwa, nima lokaci nake jira in bar rayuwar, ranar ina kwance na jiyo kamar Hussaini keh ihu daga waje, na tashi na fita, ai kuwa wasu katti na gani riqe da Hussaini zasu kasheshi, da sauri na isa ina tambayarsu abinda ya musu su rabu dashi, wani irin maka da d’ayansu ya kaimin ban kuma sanin ina kaina yake ba, saidai tashi nayi naga d’akinsu Safeena na hayaki alamun ya k’one kurmus, kukan da kanshi ranan nemansa nayi na rasa, lokacin da na farfad’o naji muryar Larai tana wadanne irin banzaye ne ku da baku iya aikinku ba, ba ita nake gani tana motsi ba can, wani k’arfine da bansan da ina dashi  ba na ji yazo min dan naci alwashin d’aukar wa yarana fansa, gudu kawai na shiga yi batareda nasan inda zan jefa k’afa, ina cikin gudun ne na hau titi amma bansan mey ya faru ba bayan nan”, Wani irin tausayinta kawai Dad yaji yana ratsa shi, a hankali yace “Innalillahi wa inna illaihi rajiun”, sau uku yana maimaitawa snn yace “Haka kaddararki tazo, kiyi tawakkali ki rungumeta da ikon Allah zaki samu kyakyawan sakamo a wajen Allah, in bazaki damu ba zan tafi dake gidana kiyi zamanki a can, inada mata da yara mata biyu in har bazaki damu ba”,

STORY CONTINUES BELOW


       Lokacin da Mum ta haura sama, d’akin da Ajiddeh take mai aikin tayi mata jagora ta kaita snn ta juyo k’asa kawo mata ruwa, har Mum ta shiga d’akin Ajiddeh batan sani ba tana nan kife kan gado sai kuka takeyi, saida taji k’aran rufe k’ofar Mum snn ta d’ago ganin waye, dasauri ta mik’e har tana k’ok’arin fad’uwa ta k’araso gaban Mum tana leqen ko da wani bayan Mum d’in, cikin kuka Ajiddeh na girgiza kai tace “Na shiga uku Mummy,  mey kikazo yi kuma, shikenan in auren nawa kikeson kashemin sai ki nemi waje ki zauna, dama gab asirinmu yake da ya tonu, tun daga Maiduguri aka d’auko Malamin da zai duba yarinyar nan kuma yau za a gama, saida nace miki a lalata aikin nan kikaqi gashi yanzu asirinmu zai tonu, Mummy kiyiwa Allah kiyi min rai ki bar gidan nan” ta k’arasa maganan tana mai tsananta kukanta, Mum da ta gama sauraren Ajiddeh ta wara ido tace “Keh don uwarki wasa kike, wane malamin aka kawo mata, ni Zuwaira naga rayuwa, ka haifi d’a baka haifi halinshi ba, Ajiddeh wai mey ke damun kwakwalwarki ne anya kinason gamawa da duniyar nan lafiya kuwa, yanzu har ke da bakinki kike cemin an nema mata mai magani amma baki sanar dani ba sabida ga kanwar uwarki Jainaba ake wa magani ko” Ajiddeh ta d’ago tace “Mum nifa mutuwan ne banaso tayi, mey zamu cewa Allah idan munje gabanshi, mey rayuwarta ta tsaremana da zamu karar mata da kwanakinta, tunda wuri saida nace miki ba kasheta za ayi ba amma kika qi ji”, kuka Mum ta fasheda tana “Na shiga uku ni Zuwaira, Hauwa wlhy Allah ya isa haihuwarki da nayi, duk rayuwata ta k’are akan nema muku farin ciki keda y’ar uwarki amma yau bud’ar bakinki nayi abu kike cemin banyi daidai ba”, jikin Ajiddeh ne yayi sanyi ganin Mum na kuka tace “Mum nifa ba abinda nake nufi kenan ba, wlhy duk ranarda Aliyu da iyayenshi suka san inada sa hannu cikin ciwon nan nata wlhy sai ya rabu dani Mum, Mum ko bashi ba iyayenshi bazasu yadda ya zauna dani matsayin matarsa ba, Mummy kinfi kowa sanin irin son da nake mishi, rabuwa dashi na nufin rabuwa da farin ciki na kuma bani kad’ai ba har Ku ba bari zaiyi ba dan ko yau da safe saida ya dad’a jaddadamin cewa in ya samu wad’anda suka yi mata wannan aiki toh hukuma ce zata rabasu dashi”, Mum da ta fara tsurewa jin har su Abu sunsan asiri ne akayiwa Batuul yasa ta sake matsowa kusa da Ajiddeh tana wara ido tace “Shirman banza, waye yace musun asirine ke sata wannan ciwon”, Ajiddeh tace “Yanzu haka fa Mum magani ake mata kumafa na fad’a miki yau d’innan za a gamashi kinga kuma dole komai ya bayyana”, Tsaye Mum ta mik’e tana cire mayafin kanta dukda Acn dake aiki cikin d’akin amma gumi takeyi tace “Inaaa!, bazai yiwu ba, Wace irin masifa ce wannan da take shirin kunno min kai lokaci d’aya haka, karya sukeyi wlhy dukkansu sunyi kad’an, bokan nan saida yayi assuring d’ina mutuwa zatayi kuma babu wani wanda zaisan sukeda sa hannu”, cikin hanzari ta lalubo wayarta ta shiga k’iran layin Jainaba, bata d’aga ba har ya katse, tsaki taja gaba d’aya jikinta sai rawa yakeyi taci gaba da k’ira, sau uku yana katsewa kamin aka d’aga, Ajiddeh dai kallon Mum kawai takeyi tana fatan Allah yasa kada asirinsu ya tonu, gaba d’aya hankalinta ya gama yin inda akewa Batuul magani, so kawai take taji mey ke faruwa taji meye makomarsu, Mum najin an d’aga waya tace “Jainaba kome kikeyi ki biyo jirgi ki shigo Abuja yau, abin ya min yawa nikad’ai, komai dad’a lalacemin yakeyi”, sheshek’ar kuka taji daga d’aya b’angaren, Jainaban dake kuka tace “Yaya kizo ki fitar dani cikin wannan masifa, na gaji da zaman gidan Idrees”, Mum ta katseta tace “Mey kuma ya faru bayan wanda kika fad’amin”, Jainaba na kuka tace “Banda duka babu abinda nakesha gurinshi, yasa masu gadi sun hanani fita daga gidan, duk ma’aikatan gidan ya koresu babu kowa cikin gidan nan sai ni kad’ai sai kace mayya, yaran ma ya kwashesu bansan inda ya kaisu ba gashi babu kud’i wajena bare in siya kati in miki waya kiji halin da nake ciki, kwakwaran motsi ban isa inyi shiba yanzu zaki ya fara hantara yana tamin habaici kan matar da zai aura”, Mum da k’afafunta suka fara rawa jin bayanin Jainaba dawowa tayi kan gadon ta zauna taci gaba da cewa “Yaya ki taimaka kiyi koma menene cikin yau d’innan in samu in fito daga gidan nan, in yaso daga baya musan yadda zamuyi dashi”, Mum da abu suka fara cakude mata tace “Ki kwantar da hankali Jainab kina jina, yanzun nan zan fita in San abin yin akanshi, yanzu haka ina wajen shashar nan, daga nan zamu wuce tareda ita, kwantar da hankalinki komai ya kusa zuwa k’arshe”, Jainaba tace “Shikenan Yaya ina jira”, da haka suka katse waya ta dafa kanta tana tunanin yadda abubuwa sukayi mata yawa lokaci d’aya, can ta juyo ta dubi Ajiddeh dake ta hawaye tace “Ki tashi yanzun nan muje musan abinda za ayi tunda kince yau za a gama mata maganin, Ya Allah mey nayi nake cin karo da masifu iri iri a cikin kwanakin nan”, Ajiddeh tace “Mum bafa masifar da kike ciki, in ta tawa kike kije….”, Mum cike da fusata tace “Dan uwarki bakida hankali ko?, ganin ina binki a hankali yasa kika fitsare har kike ce min indan taki masifarce in rabu dake ko toh bari kiji, mijin Jainaba aure zai k’ara kullum narka mata duka yakeyi a gida, Wanda zai auri Zainab ya fasa , matarsa da mukayi sanadin fitanta daga gidan ya maidata, Babanku yazo da wata mata gida yasa an gyara mata part guda ya zube mata y’an aiki, bansan tsakaninshi da ita kullum hankalina a tashe na tambayeshi wacece ita yace wannan ba matsalata bace snn gaki, akan wata can banza kikeson b’ata min rai, komai dan ku nake yinshi dan Ku samu farin ciki mai d’orewa amma bakya ganin k’ok’arina, yanzu babbar matsalar da muke ciki duk akanki sbd kin fifita miji da danginsa akanmu, har a samo mai magani bakiyi tunanin sanar dani ba”, Mum ta fashe da kuka tace “In sha Allah na barwa Aliyu ke Hauwa, kafata ta bar d’akin nan toh ki manta kinada wata uwa”, ta miqe ta zari Jakarta tayi hanyar waje, tana kaiwa bakin k’ofa zata bud’e taji an turo k’ofar, Abutturab ne tareda da Ammah suka shigo d’akin a tare, Ajiddeh na ganin yanayin sa durk’ushe a wajen ta saki wani irin kuka, cikin d’akin ya k’arasa shigowa, Mum da duk yan hanjinta sun kad’a ta dake ta dubi Ammah tace “Yanzu nake shirin inje in duba mai jiki, yarinyar nan ce take ta kuka nace addu’a zatayi mata”, ko kallonta Mum batayi ba, Hannun Ajiddeh dake durk’ushe tana kuka ya kamo ya mik’ar da ita, cikeda kuka kamar ranta zai fita tace “Aliyu tsaya kaji Dan Allah, Let me explain kaji, wlhy Allah….”, wani irin fizga da yayi mata yasa ta toshe bakinta da d’aya hannun nata, Mum da ta tunkarosu tana “Kai banza ina zaka kaimin y’a kake fizgarta haka”, wani mugun kallo da ya jefeta dashi yasa tayi shiru ta matsa da baya, Har ya fita da Ajiddeh daga d’akin baice komai har saida ya kaita d’akinshi da yakeyin ayyukanshi kamin yayi aure, sake hannunta yayi yana kallonta da idanunshi da suka rine yace “Hauwa did you really hurt her? Kune behind suffering din Fatima all this while?”, shiru yayi yana jiran jin amsar da zata bashi, ganin tayi shiru tana kuka yasa shi daka mata wani mugun tsawa yace “Answer me” har saida yasa Ammah yiwowa wajen tareda Mum, a kid’ime Ajiddeh ta kalleshi tana kuka tace “Am sorry, am so sorry, I wanted telling you Dan Allah kayi hakuri wlhy sharrin shaid’an ne, forgive me pls Aliyu”, wasu hawaye ne masu d’umi ya shiga zirarowa daga idonshi, lumshe ido yayi ya bud’e ya kalleta snn yace “Get out of my sight, don’t you ever cross my way not now not ever”, tsananta kukanta tayi tana girgiza kai ta shiga matsowa kusa dashi tana “Aliyu you know I love you, karka horani da rashinka, I can’t endure ko wane irin punishment amma banda rashinka dan Allah kayi hak’u…..”, wani mugun kallo ya jefeta dashi da ya sata had’iye maganarta ya daka mata tsawa yace “I said get out”, ganin yanayinshi tasan komai zai iya faruwa a lokacin, toshe bakinta tayi ta juya ta ruga a guje ta fice daga d’akin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *