BATUUL CHAPTER 3

BATUUL




CHAPTER 3











        Suna zaune suna jiran jin announcement ďin departure su, Mahir yacewa Aunty zai sha smoothie, sauran yaran naji yace zai sha suma duka sukace zasu sha, Aunty ganin dukkansu na son sha kuma ba wai suna son bane dagaske kawai dan sunji ďaya daga cikinsu yace zai sha ne dan kawai suje yawo yasa ta faďin cewa Batuul, “Batuul jeki da Fa’iza ku kawo musu , bazan iya da yawon yaran nan a cikin airport ďinnan ba , yanxu sai in nemi wani in rasa”, Murmushi Batuul tayi sannan ta mik’e ita da Fa’iza suka karb’i kuďin a hannun Aunty suka tafi, suna tafiya yaran na ihun faďan shi ice cream yake so wani kuma yace milk shake yakeso, bata kula kowanne daga cikinsu ba tayi tafiyar  ta, mutanen dake zazzaune sai kallonsu sukeyi ,suna tafiya suna ďan hira da Fa’iza har suk’a k’arasa eatery ďin dake airport ďin, order ďin smoothie ta bayar ta zauna jiran a gama packaging su tafi, ana gamawa aka mik’o musu Fa’iza ta karb’a, suna juyowa zasu tafi taji bugun zuciyanta ya sake k’aruwa, saurin tafiyanta ta rage tana ta ambaton “Hasbunallahu wa ni’imal Wakeel”, juyowa Fa’iza tayi ta dubi Batuul tace “Yaa Batuul lafiya ,naga kina tafiya a hankali”, Ce mata tayi “Lafiya Fa’iza, muyi sauri mu k’arasa” Suna cikin tafiya daga gefe ta hango Abui da wani mutum a tsaye, bata ga fuskanshi ba dan ya juya bayanshi, Abui ke facing ďinsu sai bayan mutumin kawai take gani, “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel” ta sake ambata sabida yadda bugun zuciyanta ya k’aru, da sauri ta k’arasa inda ake zaman jiran , a ranta tana cewa in sun koma gida zata faďawa Aunty dagaske bugun zuciyan nata ya k’aru, suna zuwa suk’a mimmik’awa kowa abinda yace yana so suka koma wajensu suka zauna, basu fi minti biyar da zama ba akayi announcing passengers ďin Maiduguri to Abuja su fara boarding yanxu jirgi zai tashi, mik’ewa sukayi suka isa inda jirgin Med View ke tsaye suka hau matakalar suka shiga ciki, a first class suka sami waje suka zazzauna, Batuul ce k’arshen shigowa, duk seats ďin sun cika sai last two seats ďin k’arshe ne da daga shi sai economy class babu kowa a wajen ta k’arasa ta zauna, tana zama ta cire wayarta daga cikin jaka da ear piece sannan ta saka jakar daga sama inda ake ajiye luggages,  wayarta tasa a flight mode ta jona ear piece ďin da wayan ta mak’ala a kunnenta, a hankali ta jinginar da kanta a kujerar tare da lumshe idanuwanta, heart beat ďinta ne ya k’ara k’aruwa kamar zai fito daga ciki, seat belt din jikinta tayi unfasten snn ta shiga karanto addu’a a hnkli a xuciyarta tana dan jujjuya kanta, ji tayi kmr mutum na tsaye kanta don wani dad’da’dan kamshi ne ya bugi hancinta, duk da hka ba ta buďe idonta ba sai da ta gama addu’ar da take snn ta bude idonta a hnkli, wani mugun faduwa gabanta yyi ganin Wanda ke tsaye kanta idonsa a kanta ko kiftawa baya yi, dauke kai yyi da sauri fuskar nn tasa a daure yace “Excuse me” sae a snn ta lura da phone dinta da ke ajiye kan seat din dake gefenta, daukewa tayi ta mayar cinyarta snn ya xauna, mamaki ne ya cika ta ba kadan ba, mikewa tayi ta ajiye phone dinta xata fita duk da bbu takamaiman abinda xata je yi amma ya ki bata hanya, ita kuma taki cewa ya matsa mata, komawa tayi ta xauna ranta yyi mugun baci, “to wae shi wnn guy din me yake daukan kansa, me ma yasa zai zo kusa dani ya zauna at d first place, ko ina ne sae mun hadu, su Farida ma basu dawo ba shine shi zai tafi ya barsu, ko mey zaije yi shi kaďai oho” ďan k’aramin tsaki taja ta kawar da kanta tana kallon waje ta window, tsakin da taja ne ya sashi kallonta, lokaci ďaya yyi kwafa ya dauke kansa da yaga hankalinta baya wajen, announcement aka shiga yi nacewa ” passengers on board should pls fasten their seat belts, Med view flight is about to take off” fastening din seat belt dinsa yyi ganin bata da niyar yin hkn ita yasa ya juya yana kallonta, a lumshe ya ga idonta snn ga earpiece a kunnenta, da farko dan tsaki ya ja ya kawar da kansa, amma ganin few minute ya rage flight yyi take off yasa ya dan buga hannun seat dinta, ko kadan batuul bata ma san yana yi ba don kure Karatun da take saurara tayi, ya kuma buga handle din seat dinta da karfi nn ma bae ga alamar tasan yana yi ba, jin announcement din da ake yasa yyi saurin jawo seat belt din ya shiga kkrin fasten din mata, Batuul kam kawae jin hannun mutum tayi jikinta, ta bude ido da sauri tare da cire earpiece din kunnenta tace “What….” Shiru tayi ganin har ya gama sa mata ya dauke kai, lkci daya ya lumshe ido kamar mai bacci, takaici ne ya isheta bata san lkcn da ta furta “Hw dare yhu!” Bude ido yyi da sauri ya xuba mata manyan idonsa yana kallonta, murya can kasa yace “damn those  words of urs!” hawaye ne ya cika idonta, lkci daya ta rufe fuskarta da mayafin jikinta,  dauke kai yyi ba tare da ko dar ba, bayan yan mintuna Batuul ta bude fuskarta suka hada ido, hawaye ya gani fuskarta, lkci daya jikinsa ya dan yi sanyi don ya tsani kukan mace, a hnkli ya furta “Damn her, ita kenan kullum hawaye, ko meh nayi mata oho,” kusan a zuciyanshi ya faďi haka, handkerchief ďinshi dake aljihun jeans ďinshi ya ďauko ya mik’a mata ba tare da ya kalleta ba fuska daure, k’in karb’a tayi, haushi ne ya kamashi ya maida handkerchief ďinshi ya ruk’o kafaďanta da k’arfi, “clean that face, bana son sake ganin hawayen nan, don bbu abinda nayi maki I only helped yhu, ko kuma you leave this seat immediately” saketa yayi dan k’aruwa hawayen sukayi, ya ja dogon tsaki ya ďauke idonshi daga wajenta, sake juyowa yayi bayan y’an mintuna yaga har lkcn hawayen take, da kanshi ya ďauki handkerchief ďin ya fixgota ya shiga goge mata hawayen , ture hannunshi tayi daga fuskanta tace mishi “malam ka rabu dani da hawaye na, ai fuskana ne kuma hawayena ne, let me be plss” ta juyar da kanta tana kallon gajimare da sauri , magana zaiyi mata kenan hostess ďin jirgin ta tsaya a daidai kujeran da suke, plate holder ďin seats ďin nasu ta jawo ta ďora musu ruwa akai a ďan k’aramin disposable cup, hak’oranta ta washe ta gyara murya tana yiwa Abutturab magana, “Sir what would you like to have”, bai ďago kanshi ba yace mata “Get me coffee”, okay tace sannan ta dubi Batuul tace mata “Ma’am what would you like to have”, k’in juyowa Batuul tayi, sake tambayanta matar tayi sannan ta juyo tace mata, “am okay, i need nothing” murmushi matar tayi sannan ta wuce” wayanta ta ďauko dake mak’ale a pocket ďin seat ďin gabansu ta sake mak’ala ear piece ďin a kunnenta taci gaba da jin karatun qur’anin da takeji ďazu, hostess ďince ta dawo da coffee ta ajiye mishi ta juya.





     k’arfe 12:10 daidai jirginsu yayi landing a filin jirgin Nnamdi azikiwe international airport dake Abuja, jirgi na tsayawa Batuul ta tashi zata fita daga seat ďin da sauri fuskar nn tata a daure, k’in matsawa yayi ta fita har saida mutanen dake can economy class suka gama fita na first class ďin ma sun k’are, ita dae bata ce mishi komai ba har ya gama zaman mulkinshi ya mik’e cikin isa, ko gama barin wajen be yi ba ta bangajesa ta fice ta ďauko jakanta, sae da ya gama bari ta dauki jakarta snn ya fixgo ta yace “Are yhu blind” buge hannunsa tayi ta fita da gudu, tana fita taga y’an gidansu a waje ďaya, Aunty ce tace mata “mey kika tsaya yi ke baki fito ba sai yanxu”, cewa Aunty tayi “bana so inzo fita ina jiran mutane shiyasa na jira kowa ya gama fita”, Abutturab ne ya k’araso inda suke fuskarshi a sake kamar ba shi ke ďaure fuska ba ďaxu a cikin jirgi, Hannu ya mik’awa Baba tare da ce mishi “Baba ya gajiyan jirgi”, murmushi Baba yayi yace mishi “Alhamdulillah Aliyu, mun godewa Allah mun iso lafiya” juyawa yayi ya dubi Aunty ya ďan sunkuyar da kanshi tare da gaisheta, itama amsa mishi tayi cikin sakin fuska, hannu ya mik’awa duka k’annen Batuul suka gaggaisa, Aabid ne kawai bai gaisa dashi ba sai kanshi da ya shafa tare da murmushin da ya bayyana dimple ďinshi yace mishi  “Hello champ” dariya sosai Aabid ya saka kamar yasan abinda aka faďa mishi, tsayawa Batuul tayi tana kallonshi da mmki a ranta take cewa “Yaushe yasan su Baba kuma” shi kam ko kallon inda take bae yi ba,  tab’e baki tayi ta juyar da kanta, suna tsaye motoci suka k’araso inda suke, Baba ne yacewa Abutturab “toh Aliyu sai kaje ka huta ko gobe za a fara aiki” da murmushi ya amsawa Baba da “In sha Allah”, sai da ya jira sun shiga motocinsu sannan ya shiga nashi shima da aka zo ďaukanshi dashi, hanyan Gwarimpa su Batuul sukayi, motar su Abutturab kuma tabi hanyar Asokoro.


      A hanya Baba ke tambayan Batuul abubuwan da take buk’ata na graduation ďinta, ce mishi tayi “Baa dama kayan graduation ne ,prom da zamuyi a ranan da yamma sai walima shi kuma inada kayanshi”, kallonta Baba yakeyi har ta gama sannan yace mata “Sai kuje ko Dubai ne ku duba tunda babu time kuma shi kaďai kuke da visanshi, sai ki siyosu a can”, murmushi tayi tace “Baa ai nayi magana ma da designer ďita har na gama faďa mata yadda nakeson kayana ya zama, next wek ma tace zata gama”, tambayanta Baba ya sakeyi “are you sure babu matsala Mamana zaki samu yadda kikeso”, kai ta gyaďa tace ehh Baa In sha Allah”, murmushi yayi ya shafa kanta yace, “Allah ya miki albarka” daďin addu’an ne ya sata saurin cewa  “Amin”, hira suketayi suna tafia, k’arfe biyu daidai suka isa gaban wani gate saboda nisan tafiyar dake tsakanin airport ďin da cikin gari ga hold ups,  horn sukayi, gidan exactly irin gidan da suka baro ne a Maiduguri, sai dai wannan cream paint ne da brown gate wancan kuma farin paint ne da black gate, masu gadi ne guda biyo suka taso suka buďe musu, a lokaci ďaya suka ce musu sannu da zuwa tare da yi musu ya hanya, cikin sakin fuska suka amsa musu da Alhamdulillah Friday da Jonathan driver ya k’arasa ciki dasu wajen parking, firfitowa sukayi daga motocin suka nufi cikin gida, shima cikin iri ďaya ne da wancan abinda kawai ya banbantashi da wancan shi cream and brown live wallpapers ne manne a bangon, sai wani large human size family picture daga gefe manne da bango, k’arasawa kowa yayi cikin gidan ya samu waje ya zauna a falon, Baba ne kaďai ya haura sama,khalil ne yace “Home sweet Home” Ahmad ne yace mishi “ai nan ba home bane, dole zamu koma maiduguri saboda Abuja ba garinmu bane”, “but still this is where we live” inji kalil, tsakaninsu suke ta hiransu abunsu, Mus’ab ne ya tashi zaije ya kunna Tv, Aunty tayi maza tace mishi “koma ka kashe TVn nan ku wuce kuje kuyi alwala kuzo muyi salla” komawa yayi ya kashe TVn duk suka tashi suka tafi sama yin alwala, basu fi minti biyar ba suka sake sauk’owa bayan sunyi alwalan, Baba ne yajasu Sallah dukkansu kasancewar an idar a masallacin gidan, suna idarwa sukayi y’an addu’oinsu suka shafa, hannu suka mimmik’awa junansu har Baba da Aunty suna cewa  *Baa nda dubdo, Auntu nda dubdo*, (Baba ina wuni Aunty ina wuni), “Wassalatu wassalamu ala Rasulillah” Al’adan gidan kenan indai sukayi sallah sai sun gaida junansu , suna gamawa wata mata siririya da baza ta wuce 25 yrs ba ta shigo falon ta k’ofan kicin , sanye take da kayan kuku tana rik’e da wani food flask mai kyau zatayi hanyan dinning su Yusra ne suka  hangota suka ruga wajenta da gudu suna faďin “Aunty Esther mun dawo, ashe kina nan shine baki fito ba, mey kike dafawa, jawosu tayi jikinta tace muje kuga abinda na dafa in baiyi muku ba sai ku faďa min wanda kukeso, murna suka sa suna jin daďi, sai da tazo ta gaida Baba da Aunty sannan taja yaran suka tafi, Baba ma mik’ewa yayi yace yana da aiki gobe sosai yanxu zai fita, tare suka ce mishi “Baa adawo lafiya, Allah ya bada sa’a” , Amin ya amsa musu da sannan ya fita, Mik’ewa Batuul tayi ta k’ira janet tace ta hawo mata da jakanta, ana kawo jakan ta ciro Macbook ďinta ta kunna, skype ta shiga ta duba ko Farida na online, da taga bata nan ne ta ďau waya ta k’irata, tana amsa tace kixo skype sannan ta katse wayan dan tasan in Farida ta fara magana ba yanxu zata gama ba, connecting tayi da Farida, tana ganin Batuul ta mik’e cikin sauri ta zauna, cewa tayi “babe i missed you soo much, ji nakeyi kamar Nigeria gaba ďaya kuka bari ba Maiduguri ba, i just cant wait to be back”, katseta Batuul tayi tana dariya tace “Riri you can talk for Africa, tun ďazu fa kike magana , har na tausayawa Affan”, dariya Farida ma tayi tace ” He loves me, babu yadda zaiyi, infact he enjoys surutuna and not only Africa, the whole planet”, dariya suka sa dukkansu biyun a tare sannan Farida tace “Ya hanya, what time kuka isa”, “Hanya Alhamdulillah , tun 12 but sai 2:00 muka isa gida” sunanta ta k’ira tace “Farida Yaa Abun ku yau ya dawo Abuja ko” dan ita gani take ba shi bane, da sauri Farida ta amsa da “Ehh, kinji yadda gidan yayi daďi, dama so nake ya tafi, naji ance ma country ďin gaba ďaya zai bari, ni daďi nakeji, kinga ko yau da ya tafi har na samu na fita” Batuul ce tace “nifa babu ruwana kullum kiyi ta gulmanshi, nidai babu ruwa”, tsaki Farida taja tace “ai idan ka nuna kana tsoronshi ya fi baka wahala, ni yazo yayi aure ma ya tafi” dariya Batuul tayi tace “zaki sani, nifa about grads na k’iraki, gown zan saka , kefa” ta tambayi Farida , “Ni wando zan saka” inji Farida, “wane wando kuma sai kace su Hamra, its either gown or skirt, am not wearing any trouser” dariya maganan ya bawa Farida tace “woh calm down lady , am just kidding, yadda kikace haka zamuyi, but a ina zamuyi ordering”, “dont worry about that, just send me irin wanda kikeso zan bayar ayi mana” inji Batuul, “aii zan tura miki details ďin duka ” da haka sukayi sallama, suna gama wayan Batuul ta cire kayanta ta shige toilet ta watsa ruwa ta fito, wani doguwan riga ta saka mara nauyi bayan ta shafa mai, ta ďan fesa turare




     Abutturab na isa gida ya shige ciki yasa key ya buďe dan babu kowa, ďakinshi ya nufa yana shiga ya zauna akan  gado, tunanin aikin dake gabanshi yayi, mik’ewa yayi ya shiga toilet ya watsa ruwa yayi alwala ya fito, kaya ya canja amma basu kai waďanda ya cire nauyi ba, sallah ya tada, yana idarwa bayan addu’oin da yayi ya mik’e ya sauk’a k’asa, kitchen ya nufa ya fara neman abinda zaici dan ko breakfast baiyi ba, coffeee ya haďa ya zauna a kujerun island ďin kitchen ďin ya fara sha, sai da ya gama juye saurin a wani ďan madaidaicin flask ya koma sama dashi, wani ďaki daban ya nufa na glass, komai na ďakin farine da glass, sanyi ke fitowa daga ciki, yana shiga ya isa wajen wani drawing board ya zauna a kan kujeran dake gaban board ďin, kayan aikin architects ne a ďakin irinsu irregular curves, french curves, desktop ďin apple, daga gefe akwai wani table akai an ďaura su set squares, CAD,pencils da sauransu, wayanshi ya ciro ya k’ira layin Amma, tana ďauka yace mata “Ammah ina wuni” da lafiya ta amsa sannan ta tambayeshi ya hanya, “Alhamdulillah ya amsa mata da sannan yace sun isa lafiya” tambaya yayi ko Abui na gida tace ehh, mik’awa Abui wayan tayi sannan shima suka gaisa, addu’a yayi mishi akan aikin da zai fara sannan Ammah ta karb’i wayan, cewa Ammah yayi “Ammah ki faďawa su Bawa na dawo suzo su dafa min wani abu am hungry”, cike da damuwa tace “Abu saida nace kayi breakfast kace ba yanxu ba, kai baka jin yunwa, gashi 2:30 yanxu,  kuma kasan condition ďinka,zance suyi maza su shigo suyi maka ” sannan ya katse wayan bayan yayi godiya, gaban desktop ďin ya koma ya fara danne danne, wayanshi ne yayi k’ara, ganin mai k’iran ya ďan saki tsaki sannan yayi recieving tare da sawa a kunnenshi, daga ďaya bangaren aka fara magana “Hello baby, ranan i called you kace min in ka koma gida you will call me amma baka k’ira ba”, shiru yayi baice komai ba har saida ta gama sannan yace mata “ya kk”, cikin yanga da karairaya murya tace mishi “lafiya inata missing ďinka amma kai babu ruwanka dani, ko da kace zaka k’irani inata jira naji shiru”, ce mata yayi “yeah i was busy shiyasa, Yasu Mum” bata ji daďin amsan da ya bata ba amma ya ta iya tunda tana sonshi haka zata hak’ura , ce mishi tayi “su mum lafiyansu rannan ma tace in gaida ka”, “ina amsawa, in kun dawo zamuyi discussing wani issue, i dont it want to take long, so in kun dawo sai muyi magana”, tunanin maganan da zasuyi ďin ta tsaya yi a ranta, tana ta addu’an Allah yasa maganan aurensu ne dan ta daďe tana son nuna mishi ya fito ya ncewa ba yanxu ba, shirun da yaji yayi yawa ne ya sashi tambayanta “kina jina” da sauri ta katse tunanin tace mishi “Eh ina ji, amma baby wane magana ne baza muyi ba sai na dawo, ai waya ma ya isa” katseta yayi da cewa “nace sai kin dawo ba awaya zanyi maganar ba” jiki a sanyaye tace “okay sai mun dawo” ta katse wayan, sai da ya gama wayan ya koma wajen CAD  ďin yana daddanawa






    Batuul na saukowa ta nufi palo inda Aunty ke zaune, kusa da Aunty taje ta zauna sannan tace mata “Aunty sannu da hutawa”, “yawwa sannu Batuul”, magana ta gani a bakin Batuul dan taga yadda take ta fidgeting da zoben dake hannun ta, tace mata “Menene Kinxo kin sani gaba kin kasa mgana”, a hankali Batuul ta buďe bakinta zatayi magana sai kuma ta fasa, da Aunty taga Batuul ďin tak’i magana ne tace “toh Allah ya kyauta” ta juyar da kanta taci gaba da kallon Tv, can da Batuul taga shirun bazai fissheta ba tace “Aunty dama inason ki faďawa Baba in munyi grads bayan result ďinmu ya fito ya kaini LONDON UNIVERSITY OF ECONOMICS, dagaske i promise zanyi karatu har in fito da first class” da mamaki Aunty ta waigo ta dubeta, tasan dai Batuul da Baba tare suke komai sai dai taji daga baya amma ya akayi yau take tambayanta, ce mata Aunty tayi “ban gane inyiwa Baba magana ba, kinyi magana ne yace bazai kaiki ba”, cikin marairaicewar fuska Batuul tace tun ina school yace min wai inyi hak’uri da wajen nan duk inda nakeso a Nigeria zai kaini amma banda abroad”, kallonta Aunty tayi sannan tace “toh tunda yace baya son waje ai sai ki hak’ura, meye sai nayi mishi magana, its his decision i cant change” hawaye ne ya fara gangarowa idon Batuul tace “Aunty in kinyi magana zai yadda ni nafison wannan university”, mamakine ya sake lullub’e Aunty, tasan Batuul bata yiwa maganan Baba musu amma yau harda hawaye, hawayen ne yasa ta ce mata “tashi kije, zamuyi magana”, da murna Batuul ta tashi tana addu’a Allah yasa ya yadda, kitchen ta nufa taje tayi waffles da syrup ďin vanilla ta dawo dinning ta ci




     Masu aikin gidan ne wata dattijuwa daga cikinsu ta hawo sama ďakinda yake taje , knocking tayi daga bakin k’ofa, baice ta shigo ba dan baya yadda kowa ya shigar mishi wannan ďakin, tashi yayi da kanshi ya duba yaga ko waye ke nemanshi, yana buďewa yaga tsohuwar, da sauri yace mata “Bawa ashe kece ai da kin shigo baki tsaya knocking ba” ce mishi tayi a ah babana ai nasan aiki kake shiyasa na k’wank’wansa, dama zance maka na gama yi maka abincin ne”, sai da ya gaidata sannan ya amsa da toh,  sannan yace ai ban san kina gida ba da na k’ira na ce miki ina dawowa”, ce mishi tayi “ai babu komai , yanxu ma Hajiyace ta k’irani take ce min ka dawo kana neman abinci shine na shigo na samo maka wani abun, a kawo nan ne ko a bari a dinning”,” a ah Bawa ba sai an kawoshi nan ba zan sauk’a inci” godiya yayi mata, toh tace sannan ta sauk’a ta koma k’asa 
      Sai da ya gama aikin da yakeyi ya sauk’o yaci abincin, bai wani ci dayawa ba ya tashi ya shiga toilet ďin dake k’asa yayi alwala ya fita masallaci dan lokacin 3:50,  da ya idar ya dawo gida, tunda ya shiga yaci gaba da aikinshi sai kuma sallah ke tadashi, bai kwanta ba sai after 12, yana kwanciya bacci ya kwashe shi, washegari 6 ya tashi bayan yayi sallah asuba yayi wanka, jeans blue  ya saka da farar rigar max n spencer sannan ya ďaura blue Tuxedo ta giorgio Armani daga sama, kayan ba k’aramin kyau suka mishi ba kasancewanshi dogo, agogon ciélo ya mak’ala sannan ya fesa turaren karenbkelly da versace eros, k’arfe bakwai daidai ya gama shirinshi ya fita, CLS rose gold ya buďe ya shiga ya fita daga gidan, office ya wuce, a nan yaci gaba da aiki har sai da minister yayi mishi waya suka tafi sighting area da zasu yi constructing, shi ya bada shawaran contractors ďin da ya kamata ayi aiki dasu, shi kuma yayi musu designing plan ďin yadda wajen ya kamata ya zama, satinshi ďaya yana aiki babu hutu, a ranar satin ne su Ajiddeh suka dawo, yana office  12:00 yaga k’iranta da number ta ta Nigeria, gaba ďaya ma ya manta da yau zasu dawo kuma yace mata zai ďaukota in sun dawo, tsaki ya ďan ja kamin yayi recieving call, kamin yayi magana ta riga shi da murna tayi mishi magana “Hello Baby mun dawo, we just landed, yanxu ma kai nake jira, bazan bi su Mum ba ni”, sai da ta gama yace “olryt gani nan zuwa”, key ya ďauka yayi magana da PA ďinsa akan duk wanda yazo neman shi ya tashi for d day sai gobe, cikin girmamawa ta amsa da “Okay sir, sai ka dawo”, yana fita yayi hanyan airport, awa ďaya da rabi ya isa, side ďin international arrivals yabi, waya ya ďauko zai k’irata kenan yaji an sa ihu daga bayanshi “Baby am here” ko bai juyo ba yasan Ajiddeh ce, da gudu ta taho ta rungumeshi kamar za a k’wace mata shi, “i missed you soo so much baby” peck tayi mishi a kumatu sannan ta ďan sassauta rik’on da ta mishi ta ďan kwanta a kafaďanshi, shi mamakin halin Ajiddeh ne ya hanashi magana, duk y’an gidansu na wajen har Dad da Mum ďinta amma babu ruwanta haka tazo ta mak’aleshi, janyeta yayi daga jikinshi yayi mata magana a hankali “sweetheart baki ganin akwai jama’a a nan infact gasu Mum nan ” zumb’uro baki tayi tace “ai dama nasan bakayi missing ďina ba,  komai nayi is not right to you, wata ďaya  we didnt meet, i was just happy, kuma su Mum ai sun san ina sonka ne” bai sake ce mata komai ba dan yasan she wont understand, k’arasawa yayi inda suke ya ďan risina ya mik’awa Dad hannu, gaisawa sukayi ya juya ya gaida Mum, da murmushi ta amsa sannan , juyawa yayi ya gaida Yaa xee, a dak’ile ta amsa mishi, bai bi ta kanta ba ya cewa Dad muje, Mum ce tayi saurin ce mishi “No ai drivers sunzo da su zamu tafi, sai dai kai ku tafi da Ajiddeh”, cewa yayi okay, sai da ya bari suka isa inda driver yake sannan sukayi inda motanshi ke pake, unlock button ďin jikin key ya danna ya buďe, k’ofar ta buďe ta shiga shima ya shiga ta ďaya bangaren ya tada suka tafi, hanyar Wuse II yabi da ita, kalonshi tayi tace “baby kace zamuyi discussing wani issue in muka  dawo”, ta tsaya tana duban shi tana jira taji amsa da zai bata, sai da ya ďebi wajen 30 seconds tukunna yace mata “Yeah , inaso ne in turo gidanku batun aurenmu, i dont want to take long so ki faďawa su Mum”, har ya gama magana ita dai ji take kamar a mafarki take, shirun da yaji yayi yawa yasa ya dubeta ya ga kallonshi take yace mata “you there”, da sauri ta girgiza kanta tayi hugging ďinshi a cikin motar, sai da ta sake shi tace, “Aliyu i cant believe my ears, you just said zaka tura gidanmu though bamuyi grand proposal ďinmu ba but its okay, am super excited, I love you soo much baby, ai yau ma zan faďawa Mum, sai ta faďawa Dad” peck ta k’ara mishi sannan ta zauna da kyau tana ta jero mishi abubuwan da zasuyi na bikin



     Batuul kam tana can gida tana shirin grads ďinsu, da kuma murnan yau Farida zata dawo, dukkansu biyun kaya iri ďaya tayi musu ďinki ne kawai ya bambantasu, har takalma iri ďaya sukayi, taso taga Farida yau amma babu time, kawai driver ta tura ya kaiwa Farida nata kayan, a washegarin graduation ďin taje saloon aka wanke mata gashinta, sai da ta gama ta k’ira driver yazo ya ďauketa, tana shigowa gida taga kowa a palo, k’arasawa tayi ciki ta cire gyalen abayar jikinta ta zauna a kan kujera, su Ahmad ne suka fara cemata” inyeh su graduate, shikenan daga gobe kin tashi daga pupil”, dariya tayi musu tace “as in, yanxu sai university, ku ku tsaya ma tukunna, ticket tara aka bani a school that means mutanen gidan nan tara ne zasu” ihun kowa shi zaije suka farayi, dariya tayi musu tace “ai sai dai kawai wasu su hak’ura dan bazai ishe mu ba, we are eleven and nine tickets ake badawa, so excluding Aabid still mutum ďaya bashida ticket, and i want you all there”, da taga babu wani da is willing to hak’urane ta ciro wayarta tayi dialling Farida, tana ďauka tace ” Riri kinsan meye, i have only 9 tickets mu kuma we are ten, kuma i didnt invite kowa ma, so if akwai extra inaso for one of us”, cewa Farida tayi “dama ni am not inviting kowa, zan bawa Yaa Abu 3, sai Abui, Ammah da Sadiq, kinga inama da extra 2, “Yawwa babe, na aika Baa liman da kayanki sunyi daidai ko” inji Batuul, “sosai ma wlhy , thank you soo much”, katse ta Batuul tayi tace ” I hear you, who are you thanking”, dariya Farida tayi tace sorry i gat to go Ammah na k’irana we will talk later, bye” da haka suka katse wayan, cewa y’an gidan Batuul tayi ai ta samu ticket ďin mutum ďaya duk daďi sukaji suka ci gaba da hiransu, k’arfe tara ta tashi ta hau sama 




       Da murmushi a fuskanta ta buďe ido, k’iran asuban fari ne ya sata tunawa da yau wace rana ce, a hankali ta tashi daga kan gadonta ta shiga toilet, wanka tayi da brush sannan  tayi alwala ra fito, nafilfili tayi, ta godewa Allah da ya nuna mata ranar gama makarantan ta lafiya, Addu’a sosai tayiwa iyayenta da al’ummar musulmai, da ta gama tayi karatun k’urani, tana gamawa aka tada sallah ta tashi tayi, komawa tayi kan gado bayan ta idar da sallah amma ba bacci take ba, itama bata san tak’amaimai abunda zatayi ba dan murna, wayanta ta jawo ta k’ira Affan, yana ďauka tace “cousin of life” a hankali ya amsa mata kamar mai jin bacci, “Hello best friend what is it kika tadani da sassafe haka”, ido ta wara tace “Affan dont tell me you are still on bed sleeping , its our day fa yau, our graduation day”, ce mata ya sakeyi “Batuul saifa 9 o’clock and its still 7, i have two more hours to do everything”, ce mishi tayi “ai yanzu zan k’ira Maa ince mata ko tashi sallah bakayi ba, Affan get out of that bed and get ready”, katse wayan tayi batajira mey zai ce ba, haka ta k’ira Farida ma, ita ma hira sukayi tayi dan ta kasa bacci itama, sai da takwas yayi suka katse sukaje shiryawa, ďakin su Ahmad taje ta tashesu tace kowa ya shirya kar su b’ata mata lokaci, Janet ce tazo tace mata wata mata tazo nemanta, cewa janet tayi ta hawo da matar ďakinta, ita kuma ta juya ta tafi, tana ďaki sukayi knocking tace su shigo, wata mata ce fara siririya da murmushi a fuskanta suka shigo, wani ďan madaidaicin akwati a hannunta ta ajiye, sai da ta zauna sannan suka gaisa da Batuul, matar ce tacewa Batuul “yanxu zamu fara ko dan kince 9 ne event ďin naku ko”, da ehh Batuul da amsa mata sannan tace “Light nude make up zakiyi min, ko foundation bana so a sa min, just my brows then eyeliner, i just want everything nude” murmushi matar tayi tace mata “Na gane but brows ďinki are full, ko za a ďanyi carving”, a ah Batuul tace sannan suka fara, takwas da ashirin da bakwai suka gama, ba k’aramin kyau Batuul tayi ba, matar ce ta ciro mata kayanta a closet ďinta da takalmi da duk abinda zata buk’ata, da kanta matar  ta taimaka mata ta saka kayan, dogon gown ne bak’i, mai buďaďďan k’asa, wani gold plated pendant da chain ďinshi matar ta saka mata a wuya na montinè da agogonshi sai pin earing da matching bracelet ďin sarkan, cashmere scarf bak’i mai golden crystals ta ďaura mata akai kamar turban, ga front hair ďinta da ya fito ya kwanta lub lub sai ya k’ara mata kyau, wani murmushi ta saka da taga kanta a mirror, ba k’aramin kyau tayi ba , takalmin karen kelly heel bak’i ta saka, a hankali take takawa har ta fito daga ďakin ta sauk’a k’asa, sai da Aunty tace “Masha Allah” da ta ganta , duk da Batuul bak’a ce bata kai sauran y’an gidan haske ba amma ta fisu kyau, Baba ne yace “Mamana kinyi kyau” da murmushinta mai kyau tace “nagode Baa”, break fast sukayi dukkansu sunsa kaya sunyi kyau, matar da tayi mata makeup ďince ta sauk’o ta mik’o mata clutch bag ďinta shima golden shima na karen sannan tayi musu sallama, k’arfe tara da rabi suka isa international conference center inda venue graduation ďin yake, tun daga waje manyan motoci ke a pake, k’arasawa sukayi ciki, decoration ďin wajen yayi kyau kalan graduation gown ďinsu ne purple and blue, sai da suka shiga ta saka graduation gown ďinta da hula, side ďin da aka tanadawa graduants ďin tabi, kujeranta ta nufa seat number twelve, Affan ne daga hagunta sai na Farida daga gefen Affan, tambaynshi tayi Farida  bata k’araso ba, bai bata ansa ba ,Affan ne ya dubeta bayan ta zauna, mitsitsika idonshi yayi sannan yace “sorry this is my best friend’s seat, can you kindly move to the next seat”, dariya tayi ta ďan dungure mishi kai tace “Allah ya shiryaka Affan, in best friend ďin taka tazo sai in tashi”, dariya shima ya saka yace “Besty you look gorgeous, i mean i cant say how much beautiful you look, am gonna miss you”, ya fara share hawayen k’arya, dariya ma ya bata tace mishi “Farida fa, she isnt here…..”bata k’arasa maganan ba ta ciro wayanta kenan zata k’irata taji bugun zuciyanta ya k’aru, a zuciyanta tace “No no, not today, let me be happy its my day” sannan ta fara ambaton “Innalillahi wa inna illaihi rajiun”, tana cikin addu’a taga Farida tazo kusa da Affan ta zauna, da harara tabi Farida da ido, Affan ne ya kare Farida da hannunshi yacewa Batuul “wannan kallo haka ai sai ta ji tsoro, Hayati ya akayi kikayi latti, i was waiting for you here all alone”, ajiyan zuciya Farida tayi tace “baza ku gane waye Yaa Abu ba, wai fa girlfriend ďinshi ce mukaje ďauka shine take b’ata mana lokaci tana ta wani abu kamar yarinya,ni shima nake tausayi ansa aurensu nan da three weeks, ya mayi ya bar mana gida mu samu mu huta”, dariya Affan yasa yace mata “babe you are too much, lets concentrate on what we are here for”, suka maida hankali kan speech ďin da VP ďinsu keyi, ita dai Batuul kawai tayi shiru ne amma bugun zuciyanta k’aruwa yayi dan har hawaye ya fara taruwa a idonta 


             Shiru hall d’in yayi ana sauraron speech d’in da VP keyi, da ta gama ne sauran members d’in high table suma suka karb’i mic suna yiwa graduants d’in Nasiha da tunatarwa rayuwansu da kuma wanda zasu fara a gaba (university), sai da aka gama speech aka fara k’iran graduants d’in d’aya bayan d’aya su karb’i Certificate da Testimonials d’insu, Batuul ce number Twelve cikin wad’anda ake k’ira, Hall d’in ne ya cika da ihu bayan Batuul ta mik’e, Juniors d’inta sai hailing d’inta suke, malamanta da sauran mutane na tafa mata, she have been their most outstanding student, kind, generous, neat and obedient, Ihun da aka sane yasa Abutturab mamaki, surnames d’in da yaji an ambata are familiar, not even familiar ya san sunan sosai, tab’e baki yaci gaba da abinda yakeyi, a hankali ta sauk’a daga kan kujeranta ta k’arasa a nutse inda vice president yake, da hannunshi ya mik’o mata certificate d’inta, a hankali tace mishi “Thank you”, tare da d’an duk’awa sannan ta ansa akayi musu hotuna dashi tukunna ta koma inda sauran ke tsaye itama tabi layinsu ta tsaya, har saida aka k’ira 67 students sannan akayi musu standing ovation tareda tafa musu, a kan stage ďin kowannensu ya cire graduation cap ďinshi suka sa ihu sannan suka watsa su tare da faďin ” Mommah we made it”, a hankali Batuul tace “Alhamdulillah”, hawaye murna taf idonta, kowa kujeranshi ya koma bayan ovation ďin da akayi musu, lokacin ne aka fara presenting prizes, Best in further Physics goes to Affan Abba gana, tafi aka sa mishi, bai dawo ya zauna ba ya sakeji ance shine best in TD, haka ya sake karb’an building and construction sai chemistry, Farida Ahmad Kyari aka k’ira best in Mathematics da Further Maths, sai Hamra Imam Imam best in biology, Maryam Ibrahim Tsoho best in Agric, Abdul Azeez Abidemi ne best in Accounting and commerce, Sai da aka gama k’iran sunayensu aka ce best in Economics goes to Fatima Kashim Goni, tashi tayi taje ta karb’a da smile a fuskanta, bata k’arasa wajen zamanta ba aka sake cewa itace best in IRS, Government,Geography, English sai Arabic , marketing da Food and Nutrition, tasowa akayi ana tayata kwasan prizes d’in dan baza ta iya ďauka ba duka sunyi yawa, haka aka ci gaba da bata prizes har na neatest, punctual da most obedient, Dj ne ya kunna mata wakan stand up for the champion dan tafi k’owa karb’an prizes a wajen, Abutturab na daga zaune tunani ya fara wacece Fatiman nan, koma wacece Masha Allah tayi k’ok’ari, sai da ya sake ambaton sunan ne ya tuna da Kashim Goni ai Minister ne, lokacin ya tuna da ai Batuul ce, kwata kwata bai ganeta ba dan wani kyau tayi da tsawo saboda heel ďin dake k’afanta, Sadiq dake zaune gefenshine ya tab’a shi yace “Yaa Abu yarinyar nan is a Genius, ga wani kyau da tayi bari mu fita sai na tambayeta yadda akayi tayi tsawo” ya faďa yana dariya, Abutturab bai kulashi ba illa wayarshi da ya ci gaba da dannawa, haka aka ci gaba da occasion d’in daga k’arshe aka rufe da addu’a, tun suna ciki suka fara selfie har suka fito waje, Kowa wajen family members ďinshi ya wuce, Baba Batuul ta fara rungumewa shi kuma yace mata “Mamana Allah yasa Albarka, Allah ya taimaka yasa kufi haka”, daďi ya sata cewa Amin da sauri, wajen Aunty ta koma, da murmushin murna a fuskanta ta shafa kan Batuul tace “Sannu Batuul, Allah yayi miki albarka, Allah yasa afi haka”, Hotuna sukayi tayi dama sunxo da photographers ďinsu , duk y’an gidan sai da tabisu sukayi hotuna ďaya bayan ďaya sannan sukayi na Family, Affan ma sai da yazo dasu Maa sukayi hotuna, Farida ce tazo a guje tana k’iran sunan Batuul, ganin su Aunty yasa ta gaishesu, sukayi congratulating ďinta, cewa Batuul tayi “kixo Ammah nata jiranki tun ďazu muyi pictures, taqi ayi wai sai kinxo, a jiraki wait”, murmushi Batuul tayi tace “toh muje nima yanxu nake tunanin zuwa” , tacewa Aunty zataje ta dawo, Aunty ce tace suma gasu nan zuwa wajen su Ammah ďin bari su gama gaisawa da mutane, suna juyawa zasu tafi ta rik’e hannun Farida da k’arfi, kallonta Farida tayi tace “lafiya?”,  “I dont know y, but these days i use to feel restless kuma heart beat ďina na increasing”, Farida da damuwa a fuskanta tace “Dont worry kiyi addu’a, we will talk about it later, let’s move now”, k’arasawa wajen su Ammah sukayi, y’an gidansu Farida ne a wajen duk tasansu sai wata farar yarinya daga gefen Abu, sai wani da bata sani ba, bata kalli gefen da Abu yake ba ta je wajen Ammah ta rungemta,janyeta Ammah tayi tareda da d’ago kanta ta dubeta tace “useki Bitti, Masha Allah, Allah bariki”, murmushi tayi ta tace “Amin Ammah”, juya wajen Abui tayi shima ya shafa kanta yayi mata addu’a, Juyawa tayi ta dubi Sadiq da Massa da suke a tare tace Yaa Sadiq “ina wuni”, smirking yayi yace “Batuul wannan tsayi da kika k’ara ai har nima kin fini, ban ma ganeki ba, ni kai har yanxu banma yadda ke bace”, da murmushinta mai kyau tace “Yaa Sadiq u are just too much, kome na saka ai bazan fika tsayi ba”, yace mata “gashinan kin kamo hanya”, dariya tasa sannan yace mata “congrats Batuul, we are proud of you, keep it up”, murmushi tasa sannan tace “Thank you Yaa Sadiq”, mutumin dake tsaye da Sadiq tacewa “ina wuni”, da murmushi yace “Lafiya kalau, congratulations, kinyi k’ok’ari sosai, Allah ya bada sa’a”, duk da bata san ko waye shima amma addu’an da yayi mata yasa ya burgeta, da murmushi tace “Nagode In sha Allah”, Abutturab na daga gefe shida Ajiddeh sai zuba take mishi, Ammah ce tace bakayi congratulating Batuul ba, Idonshi ya sauk’e k’asa yace “ai mun haďu nayi congratulating ďinta” dan shi har yanxu ya kasa yadda Batuul ce, da mamaki Batuul ta ďago ta dubeshi duk da yadda zuciyanta ke bugawa dan tasan bai yi congratulating ďinta ba amma yacewa Ammah wai yayi, tana ďaga kanta suka haďa ido, sauri tayi ta ďauke nata dan brown hazel eyes ďinshi na sata taji wani iri, matar dake gefenshi fara siririya tacewa “ina wuni”, kamar baza ta amsa ba har saida suka haďa ido da Ammah ne tace “lafiya” a dak’ile, duk da bata san Batuul ba, bata tab’a ganinta ba amma sai da taji bata sonta, Ammah ce tace “toh tunda kun gaisa sai ayi pictures”, photo grapher ne yazo ya fara arranging yadda zasu tsaya, da Batuul na daga gefen Abui ita da Farida, cewa Batuul yayi ta dawo gefen Abutturab, Ajiddeh kuma ta koma daga gefen su Sadiq, ba dan taso akayi wannan canjin ba haka ta koma daga gefen su Sadiq, itako Batuul kamar bata ji shiba ta tsaya a inda take har sai da ya sake cewa “young madam ki dawo nan”, ya nuna mata gefen Abutturab, a hankali take tafiya har tazo inda yake nuna mata ďin , rigarta ta kama daga k’asa tana cikwikuyewa, tsayawa tayi amma gaba ďayanta ji take kamar a kan k’aya take tsaye, tsayawan da tayi gefenshi ne ya sashi jin wani iri, so yake a gama hoton nan gaba ďaya ya bar wajen dan gaba ďayanshi wani iri yakeji, sai da mai hoto yayi clicking wajen talatin sannan ya tsaya, Ammah ce tace Abutturab ya tsaya suyi daga shi sai Batuul, ďago kanta tayi ta dubeshi taga shima ita yake kallo, maza tayi ta ďauke kanta ta k’ara damke riganta da k’arfi har hannunta na gumi, hawaye ne ke shirin fitowa daga idonta dan gaba ďaya a tsorace take, tsayuwa sukayi dukkansu biyun dan babu yadda suka iya, mai hoton ne yace Abutturab ya ďan matsa kusa da Batuul, matsawa yayi dan so yake a gama wannan photo session ďin da Ammah ta sasu yi, tana ganin ya matso itama ta mata da baya, tsayawa yayi ranshi a b’ace yana kallonta, hannunta ya kama ya jawota har saida ta kusa faďawa jikinshi, ido ta wara ta bishi dashi taga bama ya kallonta, su Ammah ta juya ta gani taga hankalinsu ma baya kansu, wannan farar matar ce kawai taga ta k’ura musu ido tana kallonsu, da Batuul ta kalleta ne ta bita da harara, kanta ta ďauke daga duban matar ta tsaya har pg ya gama snapping ďinsu, yana gamawa su Aunty da Maa suka iso, bayan sun gaggaisa aka sake sabon photo session, Ajiddeh kam k’in shiga tayi wai flash ďin na reflecting idonta yana sa mata ciwon kai, suna gamawa Batuul da Farida sukace zasuje suyi pictures da friends ďinsu, Affan suka fara haďuwa da a garden ďin school ďin yana ganinsu ya cewa Batuul “Best friend i will miss, i dont know how i will start over without you, you have been there for me through good and bad times all these six years…” bai k’arasa maganan ba kukan da take ta mak’alewa tun safe ya fito, da gudu taje tayi mishi bear hug tace “Affan i will miss you more, how you always make me laugh, how you make me waffles every week end night, kuma har yanxu ban koya ba, Affan muje Uk tare kaji sai kaci gaba da koyamin,i will miss everything about you”, tana buďe idonta dake rufe zata janye daga rik’on da yayi mata taga Abutturab a tsaye daga gefe ya zubo mata hazel like eyes ďinshi yana hararanta, kamar ma waya yakeyi amma ya kasa ci gaba da wayan sai tsayawa da yayi yana kallon inda suke, idonta ta ďauke taci gaba da magananta tace “zan faďawa Maa ma kar a kaika cyprus a bari muje Uk tare” Farida da ta tsaya daga gefe tana share hawaye dan sun bata tausayi duk da itama tana tausayin kanta na rabuwa da masoyinta amma tasan shak’uwan Affan da Batuul daban ne, ce musu tayi “you guyz there, kun tsaya kuna ta kuka and you are making me an emotional fool here, wont anyone give me a hug”, hannayensu suka buďe mata taje itama ta rungumesu, Affan ne yayi k’arfin hali dan shima sun kusa sashi kukan yace musu “its okay, am always the man, just give a call and i will be there right away”, murmushi sukayi a tare suka ce mishi “The man”, haka sukaci gaba da hiransu sannan suka gyara fuskokinsu suka je inda sauran abokanensu suke sukayi hotuna,
K’arfe 1:30 kowa yayi shirin watsewa, Farida ce tacewa Batuul “muje gidanmu sai daga nan mu tafi prom ďin daga nan it will be easier ko”, Shiru Batuul tayi sannan tace ” okay muje mu faďawa su Aunty sai su turomin kayana gidanku”, wajen Aunty Batuul taje ta faďa mata komai sannan tace “okay kuje sai Baa Liman yazo miki da kayanki”, mota su Aunty suka shiga suka tafi , wajen dasu Ammah suke suka k’arasa taga su Ammah ma basa nan daga Abutturab sai wannan farar matar ta zauna daga gaban mota tana ta kumbure kumbure, hango su yayi yabi Farida da harara yace “ina kika tsaya inata k’iran wayanki bakya recieving”, ce mishi tayi “Yaa Abu a silent wayan yake, banji bane” Batuul ce a ranta addu’a take Allah yasa ba dashi zasu tafi ba, da ta sani da kawai su Aunty tabi in yaso daga baya a kawota, da taga Farida ta buďe k’ofan baya ta shiga ne yasa itama ta buďe ta shiga, tana zama ďaga kan da zatayi suka haďa ido da Abutturab, harara ya sakar mata tayi saurin ďauke kanta sannan yaja mota suka fita daga wajen 
     Sau biyu idonsu na haďuwa ta rear mirror da Batuul tana saurin ďaukewa, daga k’arshe  ma komawa tayi daga gefe owners corner yadda baza ta na kallonshi ba,  ita da tasan shi zata bi ma baza ta bari y’an gidansu su tafi ba, ga wannan heart beat ďin da yaqi barinta kamar heart d’in na shirin fitowa, gaba ďaya ma ita she is not comfortable, Ajiddeh ya duba yaga tana ta fushi, rage volume ďin music d’in yayi sannan ya kallota a hankali yace “Babe meye ne kike ta b’ata rai”, zumb’uro bakinta ta sakeyi ta juyar da kanta ga kallon window, bai sake bi ta kanta ba yaci gaba da tuk’in shi cikin kwanciyar hankali har suka isa wuse II, gaban wani tangamemen gate ya tsaya yayi horn, mai gadi ne ya buďe mishi ya sa kai ya shiga, yana shiga ya nemi waje yayi parking, Ajiddeh ce ta fito daga motan shima ya bita suka fita a tare, zagayawa yayi ta b’angarenta yayi mata magana, “wai fushin mey kike yi ne haka, tun a wajen event ďin naga kina ta b’ata rai bayan kuma lafiya muka fito”, ce mishi tayi yarinyar nan wacece, meye haďinka da ita da har za a ce kuyi  snapping picture daga kai har ita sannan taqi bin motar gidansu sai naku”, juyawa yayi ya dubi motar ya kalli Batuul dake danna waya kanta sunkuye, side view ďinta ake gani da lashes ďinta da suka kwanta, kallon da taga yana yiwa Batuul ne ya sata cewa “Aliyu da kai fa nake magana”, juyowa yayi yace mata “she is my cousin”, kallon mamaki ta bishi dashi dan tasan almost duka cousins ďinshi, beside ai taga yarinyar y’ar minister ce kuma bai tab’a ce mata minister ďan uwansu bane, cikin rashin yadda tace “Aliyu baka tab’a ce min a cousins ďinka akwai yarinyar nan ba, ni gaba ďaya naji bana sonta” ce mata yayi “well there is a first time for everything, yau kin santa”, shi da kanshi mamakin kanshi yayi, why did he lie, mey sa yace Batuul cousin ďinshi ce bayan ba haka abun yake ba, ce mishi ta sake “Fine naji, but duk cousins ďinka i like her least, infact i dislike her”, da mamaki ya dubet yace “control, ki tuna da wanda kike magana, i told you she is my family and you are telling it to my face that you dont like her, kar ki manta we are getting married in the next three weeks, you cant just disregard duk wanda kika ga dama”, ranshi da ta gani ya b’aci ne sosai  yasa tace “Baby am sorry, i dunno, am just pessimistic about her, i have this negative feeling….”, haushi ta bashi yace mata “naji am going, we will talk later”, tunda ya shiga mota take tsaye a wajen, tasan halinshi baya son wasa, bare in ranshi ya b’aci, yanxun ma haka tasan sai tayi dagaske zata shawo kanshi, yadda ya figi motan ne kamar mai shirin tashi sama ya fita daga gate ďin gidan, ya tsorata su Batuul ba kaďan ba, maza maza ta jawo seat belt zata saka kenan suka haďa ido, wani kallo ya sakar mata tayi saurin sauk’e kanta a sanyaye, a ranta faďi tayi “kai ka sani, haka kawai kayi ta b’ata rai kana b’atawa kanka rai, ai matar ma da zata aureka ina tausayamata”, Farida ce ta matso kusa da Batuul tace cikin raďa “yaje ta b’ata mishi rai shine zaizo ya sauk’e a kanmu, ai kaďan ma ya gani sai ya aureta, dan da gani wannan babu abinda ta iya sai kwalliya, mu dai kar yaje ya zubar da mu”, murmushi Batuul tayi tace “kai Farida ke dai , nikam babu ruwana in ya jiki”, wani brake sukaji yaja a gefen titi, a tare suka ďago suka dubeshi dan suga abinda ya faru dan su suna ma ce hatsari akayi, ganin da sukayi lafiya yasa su ajiyar zuciya, cikin dakewar murya yace “ďaya ta dawo gaba”, a tare suka ďago suka dubi junansu, Farida ce tayi saurin cewa “Batuul kije gaba”, a razane Batuul ta kalli Farida, a ranta cewa tayi “Farida are you sick, ya za ayi kice inje gba”,a fili kuma ce mata tayi ” No am okay here ke kije”, cewa Farida tayi “kinga ni am by d road, kuma highway ne its risky in buďe k’ofa…..”, bai bari ta k’arasa magana ba yayi magana cikin tsawa yace “kuna b’ata min lokaci, ďaya ta dawo gaba, ba driver ďinku bane ni”, buďe k’ofan Batuul tayi ta koma front seat dan ta tsani ihu, tana shiga ya figi motar da k’arfi, sauk’e kanta tayi ta sa a tsakanin cinyoyinta dan k’amshin turarenshi ya isheta ga bugun da zuciyarta keyi, kallon ta yayi ta gefen ido yaga ko she is fine sannan ya k’arasa dasu gida






       K’arfe uku saura suka isa gida , Suna shiga gida bayan yayi parking suka buďe k’ofofin suka fita, har sunje bakin corridor taji yana cewa “keh”, tsayawa tayi taqi juyowa dan tasan sunanta ba keh ba kuma tasan yasan sunanta, saida taji yace “waye zai rufe miki k’ofa” sannan ta tuna ashe bata rufe mishi k’ofa ba, komawa tayi taje ta tura k’ofan sannan ta dawo ta shiga, A falo ta tarar da  Ammah da Sadiq, Ammah ce tace “Batuul kuda zakuyi shirin fita mey kuka tsaya yi, ai da kunyi sauri kun dawo tunda kuna da abun yi”, Farida ce tayi maza tace “Ai Yaa Abu ne ya tsayar damu sai da muka kai Ajiddeh gidansu ya tsaya suna ta hir…..”, bata k’arasa ba ya shigo da sallama, Ammah kawai yacewa sannu da hutawa yabi Farida da harara ya wuce ďakinshi, basu zauna a falo ba suka haura sama dan basuyi azahar ba, Farida ce ta fara shiga toilet bayan ta cire kayan jikinta tayi wanka tayi alwala ta fito, tunani Batuul ta zauna yi na mesa ma ta yadda da idea Farida na zuwa gidansu bayan akwai wannan masifaffen, bata san lokacin da Farida ta fito ba sai ji tayi ta tab’ata, a ďan tsorace ta juyo tace “hell you scared me”, dariya Farida tayi tace “sarkin tsoro, tunanin mey kikeyi”, mik’ewa tayi daga kan gado ta fara cire kayanta itama zata shiga toilet da murmushinta na tsokana tacewa Farida “My charming prince”, da gudu Farida ta janyota suka zauna a kan gadon a tare tace “Omg, i have been waiting for this moment, bari in k’ira Affan in faďa mishi, tell me about him dan Allah, dogone, fari ne, is he handsome, shekarunshi nawa, ďan inane”, dariya Batuul tasa bata barta ta k’atasa tambayoyinta ba tace “I live for you Riri”, mik’ewa tayi zata tafi , tayi sauri ta sake janyota tace “Batuul dagaske nake ki faďamin waye shi, finally mun same shi”, ce mata Batuul tayi “wasa fa nake miki Farida, ai in zai zo you will b first to know tun ban zauna tunaninshi ba”, tsaki Farida taja ta saketa tace “ke dai positive vibe killer ce Allah, ni ban sani ba ko 18 birthday ďinki kike jira kiyi legalizing boyfriend ba”, “You still love me” inji Batuul  sannan ta shige toilet da murmushi a fuskanta, tana fitowa ta tarar da Farida tana Sallah, itama doguwar riga mara nauyi tasa ta saka hijab ta tada sallah, basu fito ba sai da suka jira aka k’ira la’asar sukayi suka fito, ďan kwali kawai ta ďaura, shima bai rufe duka gashinta ba, irin square scarf ďinnan tayi triangle dashi , dinning suka nufa zasu ci abinci dan rabonsu da abinci tun breakfast, tafiya kawai Batuul takeyi amma ta gaji da bugun zuciyan nan nata dake k’aruwa all the time, addu’a kawai tayi ta ci gaba da tafiya, suna isa dinning suka ga Yaa Abu a kan kujera yana cin abinci hankalinshi kwance, wani irin kallo ya bita dashi ganin gashinta da ya kwanta a kafaďunta har sai da taji wani iri ,kujera Farida ta ja ta zauna, Batuul juyawa tayi zata koma sama dan baza ta iya zama inda yake taci abinci ba ga gashinta da yake a buďe, Ammah ce ta fito daga kitchen ta ganta a tsaye, ce mata tayi “Zauna mana bitti kici abinci”, kujeran dake facing Abutturab ta nuna mata, jiki a sanyaye taja kujeran ta zauna, kasa tab’a komai tayi sai da Ammah ta sake mata magana, plate ďaya ta ďauka ta jawo food flask ďaya taga pasta ne a ciki, mayarwa tayi ta ďauko wani, duk abin nan da takeyi in ta ďaga idonta sai sunyi ido huďu dashi, ďayan ne da ta ďauka taga shinkafa a ciki, kaďanta ďiba ta zuba a plate ta janyo bowl ďin salad shima ta ďan saka kaďan, a hankali take ci dan a takure take, hannunta na hagu ta ďago zata mayar da gashinta dake buďe, tana ďaga ido idanunsu suka sake locking, bugun zuciyantane ya k’aru da k’arfi har saida hawaye ya taru a idonta, hawayen da ya gani yana shirin zubowa ya sashi yin tsaki ya mik’e, ido Farida ta bishi dashi tana tab’e baki a ranta tace “masifaffe ko mey aka mishi kuma yanxu yana cin abinci ma sai yayi faďa”, Batuul ta duba taga kanta a sunkuye, bata yi tunanin komai ba dan tasan haka cin abinci Batuul yake a hankali, k’ok’artawa Batuul tayi ta mayar da hawayen sannan tayi ajiyan zuciya ta fara cin abincinta





    K’arfe 6:30 mai shiryasu for prom tazo, sama suka hau da ita ďakin Farida, tunawa sukayi da ba a kawo kayan Batuul ba, ďakin Ammah taje ta faďa mata ta sameta tana waya, sai da ta jira ta gama waya sannan tace mata “Ammah har yanxu fa ba a kawo kayan Batuul ba kuma tana ta k’iran wayan Aunty not reachable”, da damuwa a fuskanta ta tashi tace “toh muje in duba in Sadiq na nan ya kaita ta ďauko ke kuma sai ayi miki kamin su dawo ko” wayan Sadiq ta k’ira yace mata baya gida, driver kuma sun fita da Abui, k’asa suka sauk’o , Abutturab ta gani a palo da remote a hannunshi yana kallon Fast8 a MNET, wajenshi ta k’araso tace “Abu, zaka kai Batuul gida ta ďauko abu, tayi mantuwa ne”, tsayawa processing wacece Batuul yayi dan yasan babu Batuul a gidan, sai da tace mishi “kana jina”, ce mata Yayi “k’awar Farida ko, Ammah babu wanda zai kaita ne, ina drivers ďin gidannan, ni yanxu ma nake shirin fita”, ce mishi tayi “ai sai ka kaita ka dawo sai ka wuce inda zaka ďin”, ba dan ranshi yaso ba yace a ce mata ta fito, Farida ce ta koma sama a guje tace mata ta fito za a kaita su ďauko, cikin hanzari ta tashi ta ďauki hijab ta saka suka sauk’o k’asa a tare, Ammah ce tace mata “Bitti maza kije ku dawo da sauri”, da toh ta amsa mata ba tare da tasan waye mai kaitan ba, parking space taje taga babu alamun motan da akwai mutum, horn taji daga gefe, anyi wining glass ďin ďayan side ďin k’asa, wajen wannan motan ta k’arasa , tana ganin Abutturab ne a ciki tace  “innalillahi wa inna illaihi rajiun” a fili, “Yaa Abu da kai zamu tafi”, mamakin salatin da tayi ya tsaya yi kamar na taga wani mugun abu, bai ce mata komai ba ya sa hannu ya buďe mata k’ofa , jiki a sanyaye ta shiga ta zauna, tun kamin ya tada motan yace mata “inane gidan”, ce mishi tayi Gwarinpa, Tai Solarin crescent”, bai ce komai ba ya tada suka fita daga gidan suka ďau hanyan Gwarinpa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *