BATUUL
CHAPTER 5
K’iran Ajiddeh ne ya fara shigowa wayanshi, kin dagawa yyi da farko don ya rasa gne haushinta yake ji ko akasin hka, ansawa yayi daga karshe tare da yi mata sallama can kasa “salamu alaiki zawjati”, wani irin murna takeji kamar ta ganta a gabanshi, ta saki wani murmushi cikin muryarta me ddin sauraro tace “baby an ďaura, am officially yours now”, murmushi kawae yayi hade da girgiza kai yana mamakin Ajiddeh ko kaďan bata jin nauyinshi ko kunya, cikin sanyin murya yace”In sha Allah forever” zata sake magana kenan wasu mutane suka zo yi mishi murna, ce mata yayi “hold on wife, zamuyi magana anjima, am busy over here”, da murnan sunayen da ya k’irata yau ta katse wayan, daman mum ta faďa mata in ya aureta sai ya sota fiye da komai, gashi nan tun yau ta fara gani, gaisawa yayi da mutanen dake gabanshi, jama’a sai k’aruwa sukeyi suna mishi murna tare da yi mishi fatan alheri a rayuwan aurenshi, walima suka wuce daga wajen ďaurin auren a state hotel, k’arfe ďaya suka gama walimarsu suka wuce airport daga nan, a airport sukayi azahar gaba ďayannsu, 1:45 sukayi boarding plane, k’arfe uku dai dai sukayi landing a Nnamdi azikiwe international airport dake Abuja, basu isa gida ba sai biyar saura, a gajiye ya shiga bayan an gama kai mutane masaukinsu,
Bayan su Batuul sun gama cin abinci, wajen k’arfe uku Aunty ta ce su shirya suje gidan Ammah, ita yau baza ta samu zuwa ba, in sunje gaisheta, sai sun haďu a dinner, dan gudun magana Batuul ko attempting saka abaya ma batayi ba, wani peplum blouse da skirt na atamfa ta saka, ta samu k’aramin pearl pendant ďinta da stud masu kyau suma ta saka, ta ďauki k’aramin mayafi ta yana a kanta, Addua take a gama bikin nan ko zata huta da yawon nn ita kam, Baa Liman suka sa ya kaisu, k’arfe huďu suka isa gidan, gidan a cike yake da mutane kowa nata hidima, gaishesu suka rik’a yu har suka isa ďakin Ammah, basu sameta ba a ďakin ba, ďakin Farida sukaje , da sauri Farida ta janyo k’ofar dan kamar ba ďakinta ba, side ďin Abui ta jawo hannun Batuul sukayi tana cewa Batuul “ni in zanyi aure baza a zauna a gida ba, dubi fa gidan kamar ba shi ba kuma fa masu aiki na ta gyara amma kamar basayi”, “dama haka taro yake, sai an kwana biyu zakiga gidan ya koma daidai”, suna isa side ďin Abui Farida ta murďa k’ofan ta shiga, Ammah ta tarar ita da Aunty Amna suna zaune a ďakin bak’i na side ďin Abui tana yi mata bayanin wani abu, ga robobi nan manya manya a gabansu cike da kaji da snacks, k’arasawa sukayi daga ciki, Farida ce ta fara gaida Ammah da Aunty Amna, sai Batuul, bayan ta amsa gaisuwan ne tacewa Batuul “Bitti sai yau na ganki tunda aka fara bikin nan, lafiya bakya zuwa”, kai ta sunkuyar sannan tace mata “Ammah ina zuwa, shekaran jiya ma naje wushe wushe”, ” toh yayi , madallah, ďazu tela ma ya kawo kayanku na dinner na sa a ďinka muku, sai kuyi shiri anjima kuje kunji”, toh kawai Batuul tace amma ba wai dan ta saka zuwan a ranta ba, suna zaune su Ammah kuma nata bayanin yadda za a kai kayan nan gidan amarya, mik’ewa Farida tayi ta fita, shigowa tayi ita da wata yarinya ďauke da plates a hannayensu na abinci, ajiyewa tayi ta zauna yarinyar kuma ta fita, cewa Batuul tayi ta taso suci abinci, mik’ewa Batuul tayi tazo kusa da ita ta zauna, ďan kwalin dake kanta ta cire ta ajiye daga gefen gadon sannan suka fara cin abinci, sallama akayi a k’ofa, Sadiq ne ya shigo ďakin , sai da ya gaida Ammah da Aunty Amna sannan ya zauna, Ammah ce ta dubeshi tace “kun dawo Sadiq, ya hanya, anyi lafiya babu matsala dai ko”, kai ya girgiza tare da cewa “Alhamdulillah Ammah kunyi k’ok’ari mutane kamar turo su akayi a wajen ďaurin auren nan, komai ya tafi lafiya”, cewa tayi “Alhamdulillah , dama haka nake son ji, Allah ya sanya Alheri, Allah ya basu zaman lafiya” dukkansu suka amsa da Amin, Farida ce tace “Yaa Sadiq shikenan yanxu Yaa Abu zai bar zama a gidanmu, shikenan daga shi sai kai, gidanmu zai zama daga Abui sai Ammah sai ni, zanyi abinda nakeso”, dariya ma ta bashi yace mata “zama gadin gidan zakiyi ashe, ai nima sai kin rigani barin gidan nan, waye ma zai barki ki zauna, next year kema by now munje maiduguri har mun dawo”, b’ata rai tayi tare da zumb’uro baki tace “Ammah kin ga Yaa Sadiq ko”, kamar ba ita ta fara hiran ba, “Sadiq ka dena damun ta tana cin abinci”, dariya yayi ya mike yace “Ammah bari inje in dawo”, tace “okay sai ka dawo”, Batuul ji tayi sun birgeta, inama tana da yaya itama, amma irin Sadiq ba irin Yaa Abu ba dashi bama a ganin dariyanshi, Sadiq na fita yayi hanyan su ya haďu da ango, tsaidashi yayi yace “Abui ya shigo gidane naganka a side ďinshi, ce mishi yayi “No Ammah na ciki, daga wajenta nake, yace “okay let me get to her”, k’ofan falon Abui ya buďe, yana saka k’afa Batuul dake ciki taji gaba ďaya ta zama restless, bugun zuciyan ta ya fara, a hankali ta rik’a tauna abincin dake bakinta, k’ofar ďakin da suke ya tura ya shigo, cak komai ya tsayawa Batuul dan batayi expecting ďinshi ba at this time, k’anshin turarenshi ya cika ko ina na ďakin, da sallama ya k’araso ďakin yana kare ma mutanan ciki kallo snn ya zauna a gefen gado, Gaisheda Ammah dake ta binsa da kallo yayi ta amsa tana masa sannu da xuwa, sannan ya gaida Aunty Amna da ta dage sae tsokananshi take, Farida ce ta gaisheshi ba tare da ta kallesa ba, ba yabo ba fallasa ya amsa mata, sau ďaya ya kalli inda Batuul take ya ďauke kanshi, ita dai bata ce mishi komai ba gashi nan dab da ita ya zauna, xame hannunta tayi daga plate ďin ta cewa Farida ta k’oshi, Abuturrab na kallon Ammah yace “Ammah béri manyin, (Ammah inason abinci) banyi breakfast ba yau throughout bare inci lunch ga yamma tayi”, Aunty Amna ce tace “wannan duk ďokin zama angon ne ya hanaka cin abinci” tana dariya tayi maganar, bai ce mata komai ba sae murmushin da yyi dan ya saba da tsokanar Aunty Amna, shi bai tab’a haďuwa da Aunty ďinshi mai tsokana kamar ita ba, Ammah ce ta dubi inda su Farida ke cin abinci ta lura da Batuul bata cin abincin, tambayanta tayi “bitti ya akayine bakya cin abincin”, murmushi Batuul ta k’irk’ira tace “Na k’oshi Ammah”, ce mata tayi “Bitti ďauko wa Abu abincinshi a palo, yana nan na shirya akan tray xa ki gani”, a sanyaye ta mik’e tare da cewa toh, inda ta ajiye ďankwalinta ta duba zata ďauka taga akai ya zauna, bata ce mishi komai ba tayi hanyan palo, binta yayi da kallo har ta b’ace sannan ya ďauke idonshi tare da tabe baki a ranshi yace batason rufe kanta, dan yasha ganin gashinta on several occasion, mik’ewa Ammah da Aunty Amna sukayi suka fita dan sun gama abinda zasuyi, turowa kawai zasuyi a zo a ďauki kayan, inda Farida take zaune ya duba yaga tana ta faman dambe da k’ashi, ďauke kanshi yyi daga kallonta tare da jan tsaki, can ya sake dubanta gnin bata ma san yana yi ba sae fama da k’ashin take bayan ga nama me yawa a plate din yasa ya xabga mata harara yace “ke in baza ki ci abinci nan ba tashi ki fita, kin zauna kina ta kokuwa da k’ashi ko ina zaki kai na cikin plate ďin” zumb’uro baki tayi tareda kinkiman plate ďin abincinta tayi waje a ranta tana faďin “ohh masifaffe, mutum ran aurenshi ma sai yayi masifa ko ina ruwanshi da k’ashin da nake ci oho”, ta fice abinta ya bi ta da harara.
Story continues below
Bayan few minutes Batuul ta shigo ďakin kinkime da babban tray, saura kaďan ta sake tray ďin don wani irin faďuwa gabanta yayi ganin shi kaďai ne a ďakin, kanshi ya ďago ya ganta tsaye, ďauke kai yayi yaci gaba da abinda yakeyi a wayarsa, ganin ta fara gajiya da tsayuwan ne ya sata k’arasawa jiki a sanyaye ta shigo, a gabanshi ta sunkuya ta ajiye tray ďin , shi kuma gashin kanta da tayi parking in a messy bun yake kallo, yadda sukayi curls wasu na lilo ya zubawa ido, ďagowa tayi daga tsugunnen ta mik’e tsaye, tsayawa tayi a kanshi tana so tace yana zaune a kan ďankwalinta zata ďauka amma ta kasa bude baki, binta yayi da kallo yace “wa zai zuba min abincin kin wani ajiye kin nemi waje kin tsaya kina kallona, C’mon sense din ki bae baki cewar ba dungure min abincin xaki yi ki mike ba”, bata kulashi ba sae wani hade rae da tayi ta tsuguna ta ďauki plate da serving spoon kanta a kasa tace mishi “mey zan zuba maka”, ba tare da ya kalleta ba a takaice yace “anything”, gima ta zuba mishi a plate ďin, daga gefe ta saka mishi scrambled potato mai cheese sai kémoniye a wani saucer, kallonta kawae yake har ta dago kai tana kallonsa tace ” Ya isa?” Bae tanka ta ba sae sunkuyawa da yayi ya ďauki abincin ya fara ci a hnkli, ďagowa yayi da kanshi ya ganta tsaye tana fidgeting yatsunta kamar zatayi magana, kallonta shima ya tsaya yi sae dae fuskarsa a daure, sunkuyar da kanta tayi da sauri, shi kam bae fasa kallonta ba sae a nn ya kuma lura da yarintar ta, k’aramace ssae ya faďa a ranshi, a fili kuma cikin dakewar murya yace mata “get me a bottle of water”, ba musu taje ďauko mishi ya bita da kallo har ta bude fridge ta dauko ruwan, kan ta juyo ya maxa ya sunkuyar da kansa, ta karaso ta mik’a mishi, hannu yasa zai karb’a taji hannunshi cikin nata, maza tayi ta sake ruwan ya faďi a k’asa, kallonta yayi tare da jan ďan k’aramin tsaki ya ďauki ruwanshi, ganin ta kasa mishi maganan ďankwalinta ne ya sata kawai ta fita haka, juyawan da tayi zata bar wajen kawai ta bige tumbler dake wajen , a take suka tarwatse a wajen, ba karamin rikicewa tayi ba ta daga k’afa da sauri zata matsa daga wajen ta tak’a ďaya daga cikin broken glass ďin, wani k’ara ta saki ta tsuguna a wajen, wani mugun kallo yake jefa mata kmr xae maketa, ita ko duk ta tsorata ta saka kuka, ganin jini a kafar ne ya sashi ajiye abincin hannunsa a gefe da sauri ya mike, tunawa da yayi lokacin da yake k’arami suna London, Aunty na koya mishi homework ďinshi ya ďauki blade ya yanke hannunshi dashi, rudewa tayi sosai har idonta sai da yacika da hawaye tayi mishi treating hannun, har sai da ya warke tukunna ta fara barinshi yana yin abu da kanshi, karasawa yyi inda take ya tsugunna dab da ita har tana iya jiyo numfashinshi a fuskanta, ga k’anshin turarenshi ita yayi mata yawa, hannunshi yasa zai janyo k’afarta tayi maza ta janye, tsaki yayi tare da janyo k’afan yana dubawa, glass ďin da ya mak’ale a k’afan ya sa hannu ya cire, wani ihu tasa tare da k’ank’ame shi, shiru yayi yaji yadda heartbeat ďinta ke bugawa da k’arfe, idonta ta buďe da taji zafin ya ďanyin sauk’i, da sauri ta sakeshi ta matsa baya ganinta kwance a jikinshi, tashi yayi ya koma gefen gadon ya zauna, yunk’urin tashi tayi itama zata tafi ta kasa, wani k’ara ta sake sawa, tasowa yayi ya dawo gabanta ya mik’a mata hannun alamun ta rik’e ya mik’ar da ita, nok’e hannayenta tayi, haushi ne ya sashi sunkuyowa ya ďauketa cak sae jin ta tayi jikinsa, ta wara ido ganin abinda yayi, k’ok’arin sauk’a ta farayi daga hannunshi, hade rae yyi ssae ya xuba mata idonshi masu kama da na masu jin bacci, hawaye ne makale idonta suna shirin zubowa, ce mata yayi “stay still, ciwo kikaji bazaki iya tafiya ba, am helping, ki tsaya in gama or ki sha mari ynxun nn, ina wasa da ke ne” yana hararanta ya kare mgnr, shiru tayi ta dena k’ok’arin sauk’an da take sae dae ba karamin faduwa gabanta yake ba, toilet ďin ďakin ya shiga da ita ya ajiyeta a bakin bathtub, shower ya janyo ya kunna ruwa yana zubawa a wajen tare da sa hannu yana wanke jinin da ya fara bushewa a wajen, rintse ido tayi ta dafa sa sabida zafin da wajen keyi, sai da ya gama ya sake ďaukanta cak ya fito da ita ďakin, a kan kujera ya kwantar da ita , ďakin Abui ya shiga ya ďauko first aid kit, dab da k’afanta ya zauna ya kamo k’afan ya shiga gogewa da spirit da cotton wool, ido ta rintse tsabar azaba ta rik’e hannunshi da sauri, sae kuma ta sake kuka, hannunta da ta rik’eshi dashi yabi da ido, ďauke hannun yayi daga jikinshi yaci gaba da abinda yakeyi, zafin ne yayi yawa tace mishi “Yaa Abu dan Allah ya isa haka, akwai zafi”, dubanta yayi yaga hawaye take ssae ,ce mata yayi “clean your face and close your eyes, it wont hurt, beside raki ne yyi maki yawa”, hakan tayi ta rik’e mishi riga har sai da ya gama dressing ciwon , tashi yayi daga wajen ya gyara mata k’afan ta kwanta comfortably, juyawa yayi zai fita tace mishi “Yaa Abu don Allah ka kira min farida”, tsayawa yayi cak ba tare da ya juyo ba jin ta k’ira sunanshi sai da yaji abinda take buk’ata, ba tare da ya juyo ba yace “Anki” fita zaiyi daga ďakin kenan Farida ta shigo tana ihun “Batuul mey kika tsaya yi tun ďazu ina jiranki kizo kiga kayan da akayi mana, its f**ki…..” bata k’arasa ba tayi maza ta rik’e baki ganin Yaa Abu a tsaye, dariya ne kawae Batuul bata yi ba ganin yadda ta haďiye maganan, a sanyaye ta k’arasa wajen Batuul tace “mey ya sameki, ya akayi kika ji ciwo har haka daga fitana” “Shut ur filthy mouth nd clean up this mess kafin in dawo” yana kai wa nn ya sa kai ya fita, da harara ta bisa snn ta dube Batuul tace “shi ya ji miki ciwon ko, ai nasani, kuma in yaga mutum yaji ciwo yafi kowa damuwa, garin yaya”, kai Batuhl ta girgiza tace mata “Ba shine fa ya ji min ciwo ba, nice na fasa tumbler da na ajiye, dama ance everybody will b d first victim of his own corruption, gashi nan ni ya fara ji wa ciwo”, tausaya mata Farida tayi tace “sannu”, tambayanta Batuul tayi “mey kike faďa ne da kika shigo har da su f**king” ta k’arashe maganan tana mata dariya, “kayanmu ne na dinner, yayi kyau sosai, both d material and d style sunyi kyau sosai, sai ma mun saka tukunna”, ce mata tayi “Dinner sai ku, ni yanxu ina naga k’afan zuwa dinner” a ranta kuwa hamdala tayi ta samu rusheshen excuse da xata bada dan dama bata son zuwa, a hnkli Farida tace “toh nima bazanje ba tunda bazaki ba”, ido Batuul ta wara ta buďe baki tace “kinsan mey kike faďa , dan bazanje ba kema bazaki ba, ai sai in sa Ammah ta turaki dole, bare da ita ma za a ai dole kije”, dariya Farida tasa tace “I wont miss it for the world wasa ma nakeyi, zanje kema kuma zakije yarinya”, kamin ta bata amsa Ammah ta shigo ďakin, ganin Batuul a kwance yasata hanzarin k’arasowa inda suke, tambayanta ta shiga yi yadda akayi taji ciwo, faďa mata gaba ďaya, sai da ta gama tace mata “Toh yanxu ina Abutturab ďin, shine dan bak’in hali ya fita ya barki ke kaďai Kuma bai zo ya sanar dani kinji ciwo ba”, “yanxun nan ya fita Ammah”, Batuul ta faďa mata, taimaka mata sukayi ta tashi, har toilet sukaje da Farida tayi alwala ta fito, kaďan kaďan take ďingisawa, side ďin Ammah suka koma sukayi sallah suka fara shirin zuwa dinner dan Ammah tace babu abinda zai hanata zuwa, har da dan hawayenta don ba hka ta so ba.
Shiri suka hau yi bayan sunyi isha da magariba, ďakin Ammah suka zauna suna dudduba kayan, lace ne purple mai ďan ratsi ratsin grey mai kyau, ďinkin ya amshsu soaai, iri ďaya akayi musu, sai da suka gama Ammah ta dubi Batuul “Bitti kunyi kyau, amma babu sark’a da ďan kunnefa, ke Farida ya baki bata ba, sai ki saka keh kaďai”, hararan Batuul Farida tayi sannan tacewa Ammah “Ammah kiga jewellery box ďin mafa a gabanta yake, nace ta zab’i wanda zata saka tak’i wai baza ta saka ba”, Ammah cewa tayi “A ah Batuul bazai yiwu ba, ina aka tab’a gaye babu ďankunne”, mik’ewa tayi ta buďe closet ďinta ta fiddo wani ďan akwati k’arami mai kyau kmar chest box na katako, sai da ta zauna ta buďeshi ta fiddo wasu set ďin y’an kunne da sark’a masu kyau da abun hannu da zobe na azurfa harda agogonshi ta mik’awa Batuul, “ungo maza saka wannan”, a kunyace Batuul ta karb’a ta saka, kamar wasu diamond ta saka haka ya dinga haske sabida tsabar kyan da yayi, sai da ta saka Ammah ta dubeta tace “Masha Allah ko kefa”, wasu matane suka shigo dukkansu sunyi shiga ta alfarma cikin kayansu masu kyau, harda Aunty Amna a cikinsu, zuwa tayi kusa da Ammah sannan tace mata “Ammah motocin sunxo sunce a shirya a fito, tace toh sai kije ku fara tafiya, ni Sadiq ne zai kaini ku tafi tukunna”, Farida ce ta fara fita, motan farko tabi, Batuul dake ďingisawa kamin taje motocin sun k’are, dawowa tayi tacewa Ammah babu motocin suntafi, a ranta tana murna Allah yasa babu wanda zai dawo, “ba damuwa, bari in Sadiq yazo sai mu tafi tare”, tace “toh”, ta hau gado ta kwanta, Takwas da kwata Sadiq ya k’ira Ammah uace mata ya iso, yana jiranta, wasu y’an matane sunsha kyau suma zasu wajen dinner suka ce mishi, tafiya zaiyi yace ehh amma Ammah yazo ďauka, suka ce mishi tunda ita kaďai ce bari su shiga dan har yanxu motocin suke jira su dawo, gaba ďaya bayan sunyi occupying saura seat ďin gaba kawai, tare da Batuul Ammah suka sauk’o, rik’e da hannunta a hankali suka taho sabida ciwon da taji, sai da suka zo Ammah taga mota a cike, ce mishi tayi “Sadiq ya akayi haka, ina Batuul ďin zata zauna”, “Ammah bansan da Batuul ba shiyasa na ďaukesu”, “Shikenan kuje da Batuul ďin , bari in k’ira Alai yazo in ya sauk’e mutanen da ya kai ya dawo ya ďaukeni, Bitti shiga kuje”, Batuul dai na tsaye tana ta addu’an Allah yasa ma kar a samu space ďin, cewa Ammah tayi “a ah Amma, ke ki fara tafita ni sai a sa driver ya kaini ko Ahmad ne sai in k’ira ya kaini”, bata rufe bakinta ba Ammah ta hango Abutturab yana tahowa, cikin tafiyarsa ta kasaita ya nufo inda suke yana gyara hulan kanshi, k’amshin turarenshi gaba ďaya ya baza wajen, baima lura dasu a wajen ba, sai da ya k’araso yaji muryan Ammah ya ďago ya dubi inda suke, ce mishi tayi “yawwa Abu ka shiryako”, yace “ehh Ammah yanxu zan wuce sunata jirana” ce mishi tayi “toh ga Batuul nan ka tafi da ita, bana son barinta ita kaďai a gida ni zamu tafi tare da sadiq”, Batuul da kanta ke sunkuye a k’asa tana wasa da abin hannun da Ammah ta bata ďazu tayi saurin ďagowa ta dubeshi jin abinda Ammah tace, ido huďu sukayi ya daka mata harara tare da ďauke idonshi daga dubanta, marairaicewa yyi yace “Ammah sai fa naje hotel mun haďu dasu Massa da sauran friends ďina tukunna mu biya in ďauka Ajiddeh, tabi Sadiq kawae, ke sai mu tafi tare”, Ammah tace “ka ji ka. ina ni ina wannan yawon da ka lissafa, gara dai itan, kuje da ita kawae, kuma ai Ajiddeh ba duka motar zata cinye ba da kake cewa zaka ďauko ta, iyaka ta zauna a gaba, Batuul ďin ta zauna a baya”, wani irin b’acin rai yaji gaba ďaya ranshi, wai mesa Ammah ke son haďa shine da yarinyar nan ko da yaushe, a tak’aice yace “muje”, snn ya juya ya nufi wajen motarsa, Ammah ta cewa Batuul dake tsaye a wajen ta rasa mey ke mata daďi “Bitti kuje kinji”, a hankali ta fara ďingisa k’afarta ta isa wajen motar, wani tsaki yaja ganin yadda take tafiya kamar mai tausayin k’asa, sabuwar lambo ce bak’a k’irin mai tint glass, buďe gidan gaba tayi ta zauna , yadda ya fizgi motan ne ya tsorata ta tayi saurin sa hannunta ďaya a jikin k’ofa ďaya a wajen hand brake tana neman wani abinda zata rik’e, jin hannunta tayi kan nashi, da sauri ta janye nata hannun ta dafa gaban motar, sai da suka fita tukunna Ammah ma ta shiga na Sadiq suka fita
Gudu yakeyi akan titi kamar shi ya shimfiďa, tsabar tsoro har wani zazzabi ne taji yana son kamata, sanyi takeji sosai, hannu ta saka ta rage Ac dake aiki a motar, ganin ta rage Ac ne ya sashi juyowa ya dubeta yace “hw dare yhu! inamiki wasa ne zaki tab’a min mota, ko dan kin ganki a ciki” wayanshi ne yayi ringing ya duba yaga mai k’iranshi, bai ďauka ba har ya tsinke, haka ya dinga ringing wayan baya ďauka , daga k’arshe ma ya sata a silent, ita dai bata ce mishi komai ba, tunda abunda ke daminta ma ya isheta, ganin ya juyar da kanshi bai k’ara magana ba ta ďan kwantar da seat ďin motar ta ďanyi relaxing tare da lumshe ido dan kanta ya ďan fara ciwo , a hankali ya juyo ya dubeta yaga yadda ta jingina amma a takure, fuskanta ya kalla, idonshi ya sauk’a kan ďan k’aramin bakinta da aka sa mata purple ombre lipstick, kyabe baki yyi tare da ďauke idonshi daga kallonta yaci gaba da tuk’in shi, can ya sake juyowa ya dubeta, lashes ďinta da suka kwanto fuskarta ya kalla this time around, kamar zatayi magana ta ďan motsa bakinta, bin bakin yayi da ido, buďe idonta tayi taga idonshi akanta, da sauri ta mik’e ta gyara zamanta, shi kuma yyi saurin ďauke idonshi yayi ya mayar kan titi tare da jan tsaki, haushin kanshi yaji da ya tsaya kallonta har ta buďe ido ta ganshi, kuma fa ba wae tayi masa kyau bne, gyara zamanta tayi ta janyo kujeran, ta jingina kanta a glass ďin window tana kallon waje, a k’ofan hotel ďin yaja yayi horn aka buďe mishi ya sa kai ciki, motoci dayawa ya tarar na abokanshi suna jiranshi, duk sun shirya sunyi kyau, sauk’e glass ďin motar yayi tareda fitowa waje, inda suke ya isa, Massa ne ya fara tareshi “Kai fa wulak’ancinka dayawa Aliyu, ya zayi kazo ka bar mutane suna ta jiranka, kainefa da kanka kace babu african time 8 dot muna wajen , ana ta k’iran wayanka ma baka ďauka, har matar taka ma baka ďaukan wayanta tana ta damuna, har na rasa k’aryar da zan shirya mata ma ta yadda daga k’arshe”, duk maganan nan da yakeyi Abutturab baice mishi komai ba, idon Massa ne ya faďa kan motar da Abutturab yayi parking , ce mishi yayi “Man ba cutie bace a motan can, mey takeyi a motan ka kuma”, ba tare da ya kalleshi ba yace satota nayi zanje in saida ta, ya k’arasa wajen sauran abokan yana mik’a musu hannu, sai da suka gama gaisawa yace musu “kuyi hak’uri na b’ata muku lokaci, something came up, muje ko”, kowa motarshi yaje ya buďe ya shiga, photographers na ta ďaukansu hotuna da video, bin Abutturab Massa yayi wajen motanshi yace “na tambayeka ya akayi ka taho da cutie kai da zakaje ďauko matarka ku wuce, ina zaka da ita, a hasale Abuturrab yace “bakaji bane, nace maka saidata zanyi” ya k’arasa wajen motansa, massa yace “Man i aint joking, am damn serious”, yaje ya tsaya dab da widown da Batuul ke zaune yace “cutie”, da hanzari ta ďago ta dubeshi, ce mata yayi “fito in kaiki a motana, tare zamu tafi”, juyawa tayi ta kalli Abu, wani mugun harara da ya kada hanjin cikinta ya sakar mata, lkci daya ya dauke kanshi kamar bai san abinda suke faďa ba, da kyar ta iya bude baki tace ” yaa Abu Bari in bi Yaa Massa tunda kaima zakaje…..” tana k’ok’arin buďe k’ofa, cikin dakewa yace “come on get back, da kinsan da Massan kika tsaya sai da kika biyoni, kai kuma ka bari in na maidata kaje ka ďaukota ka kaita koma ina zaku, just follown Ammah’s instruction” yana kai wa nn ya tada motarshi yaja ya bar sa wajen, tsayawa Massa yayi yabi motar da ido, toh mey Abutturab ďinnan ke nufine akan Batuul, haka rannan a wajen wushe wushe ya hanashi sakat, yau kuma ya hanata binshi, yasan kuma ba sonta yake ba, ina! dama ai babu batun so, kafaďa ya ďaga yayi hanyar motanshi, koma dai menene zaiji bayan bikin, shima convoy ďin motocin da akayi yabi a baya
Allah Allah ta rik’ayi su isa inda zasu ta rabu dashi, gashi ya wani hade rae wane hadarin kaji, ko kwakkwaran motsi ta kasa a motar, mistakenly idan ta kallesa kuma ya xabga mata harara, gate ďin gidansu Ajiddeh ya shiga dan a buďe yake kasancewar ana biki, wasu motocin sun samu sun shigo, wasu kuma na daga waje, parking yayi, y’an mata ne dayawa duk sunsha kwalliya sunyi kyau, wata ce daga cikinsu ta iso inda motan Abu yake, tace “ango muna ta jira har amarya ta gaji da jira”, a takaice yace “Ae gashi nazo ďaukanta, kuyi mata magana, ko kuma bari in k’irata ta fito”, harara tabi Batuul da ganinta a gaban Motan Abutturab, sae kuma tayi dariya tace “No bari inje in fito da ita dan nima yanxun daga wajenta nake”, ta juya ta tafi, Massa ne ya fito yacewa sauran y’an matan suzo su shiga motocin kamin amaryar ta fito, a hankali take takowa, tun daga nesa ake ganin kyan da tayi, kayanta sai walwali suke saboda hasken dake wajen, tana k’arasowa wajen motan ta tsaya tabi abinda take kallo cikin motan da ido, buďewa yayi ya fito tare da cewa Batuul “get back” a hnkli ta buďe k’ofan motar tayi ta fito, wani irin Kallo Ajiddeh tabi Batuul dashi baki bude, Batuul bata ma san tanayi ba ta buďe gidan baya ta shige, zagayowa yayi ta gabanta yace “wifey” yana kallonta tare da buďe mata k’ofan, wani irin kallo ta sakar mishi tace “Aliyu mey haka?, wane sabon wulak’anci ne kuma wannan, ya zaka zo ďaukana zamu tafi dinner sai kazo da wata, motan nan fa musamman mukayi order saboda in shiga ranan nan shine ka ďauko wata a ciki”, shiru yyi yana kallonta sanin gskya ta fada, hannunta ya kamo ya wara mata manyan idonsa yace “c’mon its your happy day, meye dan wata ta shiga, Batuul cefa ba kowa ba, my cousin sis bbu motar da xata shiga ne shi sa Ammah tace in daukota nima ba a son raina ba coz ke naso ki fara shiga motar”, a fusace tace “ai nasha faďa maka ni bana son yarinyar nan, wlhy hankalina baya kwanciya duk inda na ganta, kuma ya xaka yrda ta biyoka bayan ga motoci da drivers a gida”, Iska ya furzar daga bakinshi a fusace yace mata “get in, in kuma baxa ki shiga ba ki koma gida” yana kai wa nn ya zaga mazauninshi ya zauna, sai da taga dama tana cika tana batsewa sannan ta shige motan, yana fita sauran motocin suka bi bayanshi , a conference hall akayi dinner, suna shiga mutane duk sun hallara, shi da kanshi ya fito ya buďe mata k’ofa ta fito tana ta b’ata rai tana cin magani, Aunty Amna ta fito ta samesu tace k’annen ango ne zasu shigo da amarya, tsayawa Ajiddeh tayi tana jiran taga su waye k’annen Aliyun da zasu shigo da ita, a hankali Batuul ta fara ďingisa k’afarta zata shiga hall ďin, Aunty Amna ce ta tsaida ita, Batuul tsaya ku shiga da amarya, Farida na fitowa, tana gama rufe bakinta Farida ta fito, su suka tsaya a gaban amarya kaďan , Batuul a hannun hagu, Farida daga hannun dama, sai Abutturab daga gefen Farida, kiďa ne ke tashi a hall ďin kowa yy kyau ssae, sae da suka shigo hall din Batuul tayi tuntub’e don dama ďingisa kafan takeyi, kan ta kai kasa Abutturab yayi maza ya rik’ota, shiru hall ďin yayi kowa idonshi da hankalinshi yayi kansu duk da basu karaso ciki ba gaba daya don da yawa sunyi xaton amaryar ce ya rike, xame jikinta tayi daga rikon da yyi mata ta karashe durkusawa wajen tana runtse ido hade da yarfe hannu, yana gnin hka shi ma ya bita ya durkusa da sauri yana kallon kafar yace “What?” Hawaye cike idonta tace “Na buge ciwona” Anty Amna ce ta taho da sauri don gnin abinda ya faru, Farida ta xaro ido tana kallon ikon Allah, Ajiddeh kam still tayi a wajen xuciyarta na bugawa da karfi.Tunda ya rik’eta masu hotuna ke ta ďaukansu hotuna dan sun zata amaryarce, Ammah dake zaune can gaba tana hango lokacin da suka shigo har lokacin da Batuul ta bige ciwonta, a ranta taji inama Batuul ďanta ya aura, dan tana son yarinyar, tunanin cewa matar mutum kabarinsa da tayi ne ya sata kawar da zancen tayi musu addua zaman lafiya, Aunty amna ce ta k’araso da sauri ta rik’e k’afan Batuul ďin, babu abinda Batuul ke yi sai yarfe hannu, hawaye na ta zubowa ďaya na bin ďaya, ďagowa Abuturrab yayi ya dubeta yaga yadda hawayen ke zuba, ya hade rae yace “cmon shut up, mey aka yi miki kike ta wani kuka kamar yanxu kikaji ciwon, clean those tears ynxun nn”, ya faďa yana kallon idonta, sauri tayi ta kawar da nata idon daga dubanshi, Aunty Amna ba tare da ďago ta dubeshi ba tana rik’e da k’afan tace “kai fa mugune Abuu, yarinyar tazo yi muku abin kirki taji ciwo shine zaka fara mata faďa, akan wane dalili, ka rabu da ita ka kama matar ka ku shiga ciki”, Farida ce tace “Aunty Amna mu maidata gida mana in baza ta iya tafiya ba”, shi dai bai tafi ba kuma bai ce komai ba yana tsaye a kansu, Sai da Aunty Amna ta ďago ta dubeshi sannan ta sake ce mishi “Abu kama matarka ku shiga ciki mana, zan kula da Batuul,” sai da ya sake kallon fuskanta dake ta ambaliyan hawaye tukunna ya ja ďan k’aramin tsaki ya juya ya dubi Ajiddeh, tana nan a tsaye kamar ta kurma ihu dan takaici sae wani xufa take, hannunta ya rik’e sannan yace mata “wife muje ko”, wani k’ululun bak’in ciki ne ya sake kamata, duk b’ata mata lokacin da yayi bai gani ba bare ya bata hak’uri shine ya wani rik’e mata hannu wai suje, ji tayi a wajen kamar tace ta fasa dinner amma sanin halinshi zai iya cewa ta tafi kawai ya sa ta bishi kmr Wanda aka xare ma laka, tana tunanin yadda zatayi da wannan yarinyar da yake ikirarin cousin ďinshi ce, dan tana sonshi kuma bata son ganin kowace mace ta rab’eshi ko da y’ar uwarshi ce, kae da ba dan in ta kasheta dole sae an hukuntata da gwara kawae ta daba mata wuka ta huta, da tunanin nn a ranta suka k’arasa MC na ta koďa su a wajen nan, sae dae Sam fuskarta bbu annuri xufa kawae take yi, Ammah ce ta k’ira wayan Farida dan duk hankalinta na kansu tace mata su shigo da Batuul ďin ciki, haka kuwa akayi , Aunty Amna da Farida su suka taimaka mata ta mik’e suka shiga hall, daga gaba wajen su Ammah ta zauna, Aunty na daga gefenta, tunda ta amsa gaisuwanta bata sake ce mata komai ba , bare ta tambayeta yadda akayi taji ciwon, MC ne ya fara magana da k’iran mai buďe taron addua, Aunty ya k’ira, she wasnt expecting it amma tunda aka k’ira ta tasan girmamata sukayi, tashi tayi taje tayi musu addu’a tare da fatan samun zaman lafiya da xuri’a dayyaba, data gama aka bi ta addua, daga nan aka k’ira abokin ango da k’awar amarya suzo su faďi biography ďin couple ďin, Massa ne ya fitowa Abutturab, ita kuma Ajiddeh k’awarta da taje k’iranta da Abutturab yazo ďaukanta ce ta fito, suna gamawa aka fara sauran events ďin, sai da akazo yanka cake ne aka k’ira iyayen amarya da ango, Ammah cewa tayi baza taje ba , Aunty da Yaa Mera suje kawai, haka kuwa akayi, daga nan aka fara rawa, ita dai Batuul tana nn inda take zaune, sai dai in daga ido taga idon Abutturab a kanta, da sun haďa ido kuma ya zabga mata harara, haka ma Ajiddeh da in ta maka mata wani hararan sae ka rantse kace idanuwanta xasu zaxxago, Batuul kam sae dae ta tabe baki a xuciyarta tace kwa ji da shi daga ke har mijin naki, daga yau ma ba lallai ku kuma ganina ba bare ku harare ni” ko lik’in ma kin tashi tayi ta musu, a haka dai har a gama dinner lafiya aka tashi komawa gida,
+
Inda su Aunty sukayi parking nan Batuul ta ďingisa k’afarta taje ba tare da kowa ya ganta ba tun kamin mutane su fara fitowa a hall ďin, jiran Fitowan Aunty tayi daga hall ďin, sai da mutane suka fara watsewa tukunna Aunty ta fito, ganin Batuul zaune ita kaďai da mamaki ta k’araso tace mata “Batuul mey kikeyi a nan?”mik’ewa tayi tare da k’arasowa inda Aunty ke tsaye tace “gida zan bi ki muje”, sai da Aunty tabita da kallo sannan tace mata “ban gane gida zaki bini ba, da ni kika zo dama ko kuma can ďin da kika baro ba gida bane”, kmr xata yi kuma tace “Aunty ni kawai….”, bata bari ta k’arasa ba ta katseta da cewa “kije ciki motoci na tafiya yanxu, na faďawa Baba ma can zaki kwana, tunda ke ba a abun arxiki dake sae na tsiya”, jiki a sanyaye idonta duk ya cika da k’walla ta juya zata tafi, Aunty ce ta dakatar da ita da cewa “Batuul”, tsayawa tayi for some seconds tukunna ta juyi tana k’ok’arin maida hawayen dake shirin zubo mata a fuska, juyowa tayi ta dubi Aunty tana jiran jin mey zata ce mata, cewa tayi “Batuul mey ke damunki, ya akayi kika ji ciwo”, hawayen da ta ke ta k’ok’arin dannewa ne ya zubo , takowa Aunty tayi tazo gabanta ta rik’e ta tareda tambayanta “Batuul lafiya kike kuka, meye ya sameki, kinyi shiru ki faďa min, ciwon da kikaji ne?”, kai ta girgiza, “toh meye” Aunty ta sake tambayanta, a hankali ta amsa da “babu”, “Ban yadda babu ba, babu ne ya saki zuwa da cemin zaki gida ko kuma babu ne ya saki yin kuka”, ita dai Batuul ta kasa cewa komai dan batasan ma mey ke sata kukan ba, cewa tayi “kawai inason komawa gida ne dan gidan da hayaniya ba zan iya bacci ba”, ta k’arashe maganan tana share hawayen fuskanta, ba dan Aunty ta yadda da maganan ta ba tace mata “toh yanxu idan na koma da ke mey zaki cewa Ammah ya maida ki gida, ki bari tunda bikin ma ya k’are gobe sai ki dawo gida kinji” ta faďa mata tare da ďan dafa kanta, kai kawai ta gyaďa a sanyaye , “keh da wa kika zo ne ma”, ajiyar zuciya tayi tace tare da Yaa Abu mukazo”, Aunty batace komai ba tace mata “toh yanxu ki koma ciki, su Ammah ma yanxu zasu tafi, kiyi maza ku tafi, gobe sai Ki dawo gida ki huta abun ki”, toh kawai tace, Baa Liman ne yazo inda motar ke pake yace “Hajiya zamu jira wani ne”, tace mishi “a ah Baa Liman, yanxu zamu tafi”, sai da safe Batuul tayiwa Aunty a sanyaye ta yi hanyan hall ďin, sai da ta jira taga Batuul ta shiga snn ta shiga mota suka tafi
STORY CONTINUES BELOW
Ammah ta hango ita dasu Aunty Amna sai y’an tsirarun k’awayen amarya da y’an uwanta, inda Ammah take ta k’arasa , Ammah na ganinta ta mik’e tace “Batuul ina kikaje, inace kun tafi da Farida , yanxu na k’irata a waya tace baku tafi tare ba, daga ina kike”, cewa tayi “Ammah hayaniya ne yayi yawa a hall ďin shine na ďan fita waje”, ajiyar zuciya ta sauk’e tace “toh, da har munji tsoro kowa aka tambaya sai yace bakwa tare, sae Amnah tace kila kin bi mamanku, ga Abun ma can na tsai dashi nace sai ya maidaki ko kuma in an ji kina gida su wuce, mu sai munyi ensuring everyone is safe home zamu tafi”, gyaďa kai kawai tayi dan yanxu ta yadda shiga motar Abutturab ďinnan qaddarar tace, Ammah ce tayi mishi alama da yazo, k’arasowa yayi giranshi na sama da k’asa a haďe, harara yabita dashi sannan yace wa Ammah gashi nan, “ku tafi toh tunda tazo, kayi maza kaje ka sauk’e y’ar mutane ta gaji”, a tak’aice yace toh ya juya, ko ba a faďa mata ba tasan binshi ya kamata tayi, a baya ta bishi shi da matar tashi dake wani yatsine yatsine har wajen mota, shi ya buďewa Ajiddeh front seat ta zauna, shi kuma ya zagaya ya shiga side ďinshi, itako back seat ta zauna kanta a kasa, a nutse yake tuk’in hannunshi cikin na Ajiddeh yana yi mata magana k’asa k’asa tana ta shan k’anshi, da suka isa gidansu Ajiddeh ma fita sukayi suka barta a motan sai da sukayi wajen minti talatin a waje tukunna ya rungumeta kmr baxa su rabu ba daga k’arshe ya shigo dan da alama aikin lallashi yake ta yi, yana shiga motan sae da ya bari ya fita daga compound din gidan snn ya juya yana kallon Batuul fuskarsa daure yace “waye driver ki, c’mon kin dawo gaba ko sae na sauke ki a titi”, ita dai bata ce mishi komai ba ta buďe k’ofa ta dawo gaba, sai da ya kama hanya ssae tukunna ya fara magana ba tare da ya kalleta ba “keh wato ni na zama driver ďinki ynxu ko, duk yadda za ayi sai kin samu yadda kika yi Ammah ta haďani dake koh, kin wuce kin tafi yawon ki kin ďagawa mutane hankali ana ta nemanki, inama kika fita kika tafi in d first place?” kinsa matan aure zama a waje duk da sunan jiranki, tunda ya fara magana bata ko kalli inda yake ba, shiru tayi bata kulashi ba, tsawa ya daka mata tare da cewa “ba tambayanki nayi ba, ina kikaje?” hawayen da tayi ta mayarwa ne ya zubo mata, kuka ta saka da karfi kamar wacce aka daka ta kifa kanta akan gwiwanta tana rerawa, sosai take kukan kamar ran ta zai fita, juyawa yyi yana kallonta, a fusace yace “wato ba a isa yi miki faďa ba shine zaki fashe min da kuka kmr wata yarinya, shut that mouth ynxu”, kamar k’ara mata kukan akeyi taci gaba da kukanta kamar bata ji shi ba har da shessheka, tsaida motar yayi xuciyarsa na tafasa yace “fita min a motata”, ko kallonsa bata yi ba tana ta aikin kukanta, da tsawa ya sake ce mata “i said get out,”, ďago kanta tayi tareda share hawayenta ta dubi cikin idonshi tace “babu inda zanje, ka mayar dani wajen Ammah kace mata baza ka kaini ba mana”, mamaki ne ya sashi sakin baki yana kallonta, dama tana magana haka, ranshi ne yaji b’aci, buďe k’ofa yayi ya fita ya zagaya ta inda kofarta take, buďe nata k’ofan yayi ya ce mata “out”, tana zaune kamar bata jin abinda yake faďa, fixgota yayi ya fitar da ita daga motan da karfi ya juya ya koma nashi side ďin ya tada motan ya tafi, tana ganin tafiyarshi ta nemi waje ta zauna tana kuka ssae, iska ne ya fara kaďawa mai k’arfi tare sa walk’iya, ďankwalin dake kanta ta warware ta yafa a kanta tana hawaye, tana nn zaune aka fara yayyafi, duk’unk’une wa tayi waje daya dan sanyi yayi mata yawa ga tsoro don bbu alamar mutum wajen, ruwane sosai ya sauk’o kamar da bakin k’warya amma ko niyyan tashi ba tayi ba sae hade kanta da tayi da gwiwa tana kuka a hnkli, ruwan da ya ganine ya sashi parkin, snn juyar da kan motan a hnkli, cikin ‘yan mintuna dawo wajen da take sbda gudun da yyi, fitowa yayi daga cikin motar ya isa inda take har lkcn yace “tashi mu tafi”, kamr bataji shi ba ta ďauke kanta, sai rawar sanyi take, da taji zai isheta ne ta tashi tayi hanya daban da sauri jin ya biyota yasa ta saka gudu, binta yayi da hanxari ya fixgota, jiri ne taji yana ďibanta dan sanyin ya mata yawa, tangaďi ta fara zata faďi yayi sauri ya tarota jikinshi, mutsu mutsu ta shiga yi xata kwace kanta bugun xuciyanta ya tsananta, kin saketa yyi ruwa na dukansu, cak ya ďauketa daga karshe ya kaita cikin motan yayi mata baya da seat ďin ya kwantar da ita fuskarsa dab da nata har tana iya jiyo numfashinsa cikin kaushin murya yace ” Idan kika kuskura kika fito xaki sha mamaki na” kasa motsi tayi daga gurin xuciyarta kmr xae fito don tsoro kamshin turarensa duk yabi ya isheta ga fuskarsa dake dab da nata har lkcn, da kyar take jan numfashi tsabar wani rawan sanyi da take, yafi minti uku yaki daga kallonta duk da ynda yaga jikinta ke rawa ssae, daga karshe ya mike ya rufe motar.
Xagawa yyi maxauninsa ya Shiga, maimakon ya ja motar sae ya kasa, ya fi minti uku daga karshe ya juya yana kallonta yace “Batuul!”,ya ji shiru bbu amsa, sau uku yana k’iranta yaga bata ko motsi, kafaďanta ya kama tare da jijjigata yana k’iran sunanta amma ko motsi bata yi, janyota yayi jikinshi da sauri ya kwantar tare da bubbuga mata baya, ko ba a gaya masa ba yasan she is unconscious ne, hnklinsa ya tashi ba kadan ba, all possible ways da yasan xae yi ta farfaďo yyi amma shiru, kawai yayi deciding da ya bata mouth to mouth respiratory aid, ďan kwalin da ta yafa a kanta ya cire, gashinta da ya kwanta lufluf yabi da ido, sunkuyo da kanshi yayi dai dai fuskanta tare da rintse ido yana k’ok’onton yayi ne ko kar yayi, but dats the only alternative, sai da ya kawo bakinshi daidai da nata idonsa na kan lips dinta hannunsa daya na kanta ta jawo wani dogon numfashi amma bata buďe ido ba, wani irin ajiyar zuciya ya sauk’e tare da komawa baya seat ďinshi ya zauna yana kallonta, sai da yaga ta fara motsa hannun tukunna ya lullubeta da dankwalin kanta bayan ya kashe Acn motar ya tayar ya jasu sukayi gida, suna isa gida yyi pakin ya fito ya ďauko ta a hannunshi kamar wata y’ar baby yana kallon fuskarta, mutanen gidan da sukazo biki waďanda basuyi bacci ba duk suka bishi da ido, bai bi ta kallon da suke mishi ba ya haura sama ya shiga da ita ďakin Ammah tare da sallama, Ammah na ganinshi ďauke da Batuul ta mik’e tsaye a rude tace “Aliyu mey hka, mey ya sami y’ar mutane ni Bilkisu, daga ina ku ke”, bai ce komai ba sai da yaje ya shimfiďar da ita kan gado , ya kashe AC ďakin tukunna ya juyo wajen Ammah da damuwa a fuskarsa.Wai ba magana nake maka bane Abu, mey ya sami Batuul ďin”, Ammah ta fada tare da k’arasawa gadon da ya shimfiďar da Batuul ďin, jikinta ta tab’a taji yayi zafi rau, ďankwalin dake kanta ta cire mata shima taji shi a jik’e, a fusace ta juyo ta dubeshi tace “tun kamin raina ya gama b’aci ka faďa min abinda ya sami Batuul Aliyu”, da damuwa a fuskanshi ya ďan dubi Batuul ďin da Ammah ke k’ok’arin cire mata jik’ak’k’en kayan dake jikinta tana kuma sauraran amsarsa, da kmr baxae ce komae ba don yasan ko ya buda baki gskya xae gaya ma Ammah don shi baya karya, gnin kallon da take jifansa da shi yasa yace “Ammah nifa banyi mata komai ba, muna tafiyane a mota ta rik’a min kuka ba gaira ba dalili, ni kuma i couldn’t endure it nace mata ta fita min a mota, taki fita kawae na kamata na fitar da ita, nayi tafiyata, gnin ruwa yasa na koma na ďaukota muka dawo”, baki sake Ammah ta tsaya tana kallonshi da mmki, rae a 6ace tace “hankalinka ďaya kuwa Abuturrab?, ka ma san mey kake faďa min? tsakiyar dare ka cewa y’ar mutane ta fita maka a mota, don rashin kunya kuma ka bude baki kke min tsari? mesa baka dawomin da ita kace baza ka ďauketa ba Aliyu, yanxu da wani abun ya sameta mey kakeso in cewa Maryam?, wato baza ka dena wannan bakin halin naka bako Abu, a haka mukayi maka auren aka baka amanar y’ar mutane da wnn halin xaka rike masu ‘ya, maimakon da kaga tana kukan ka tambayeta kaji mey key damunta shine zaka koreta tsakar daren nn don rashin imani, Allah ya rufa maka asiri da wannan mugun hali naka, ni y’ar mutane da aka aura maka ma nake tausayawa”, jikinsa yyi sanyi ssae don ko kadan bae son 6acin ran Ammartasa, har kasa ya durkusa kansa a kasa cikin sanyin murya yace “kiyi hkuri don Allah Ammah, ba mugun hali bane, kullum haka naga take kuka babu dalili kmr wata yarinya karama, plss ki yafe”, katseshi Ammah tayi a fusace “rufe min baki, waye baisan Batuul yarinyar arziki bace, magana ma bata isheta ba kukan mey zatayi maka, ko a ina kke ganinta, in ma tayi kukan ina ruwanka da ita, nace ina ruwanka? Toh wlhy ka fita idona in rufe, wannan halin naka tun wuri kayi watsi dashi dan ba na arziki bane”, ganin ran Ammah ba karamin bacewa yyi ba yasa ya marairaice mata kmr wani karamin yaro yace “Ammah nace fa kiyi hak’uri, don Allah kar kiyi fushi da ji, wllh hkn bazai sake faruwa ba in sha Allah, plss Ammah na” bnxa tayi masa na wajen minti biyu, shi dae har lkcn yana durkushe inda yake, juyowa tayi tace “nidai na faďa maka kuma ka tabbata gobe da sassafe ka shigo kunje asibiti , bazanyi taking risk ďinnan ba , zakaje ka halaka y’ar mutane sbda wani banxan hujja taka, in kai baka da hankali ni ina dashi”, atishawan da Batuul tayi ne ya maida hankalinsu kanta, Da sauri Ammah ta zauna ta dagota ta zaunar da ita tare da ce mata “sannu bitti, ina ke maki ciwo”, a hankali ta buďe idanuwanta tayi scanning ďakin, akan Abutturab ta sauk’e idonta, shima ita ya zubawa manyan idanuwanshi kamar mai shirin bacci har lkcn bae mike daga durkushen da yyi ba, baka tantance fushi yake ko akasin sa, maza tayi ta kawar da idonta daga kanshi ta cewa Ammah “sanyi nakeji”, cikin hanzari Ammah ta mik’e tare da cemata “tashi bitti ki cire kayan nan jik’ak’k’u, ki canjasu kinji”, k’ok’arin cire mata rigan jikinta ta fara, cikin jin kunya ta rike rigan tace “Ammah tulukin”(Ammah zan cire da kaina), sake mata tayi tana jiran ta cire taga kuma bata da alamun cirewa, ďagowa tayi ta dubeta tace “bitti cire mana, sanyin kar yayi miki yawa”, ďago kai Batuul tayi ta dubi inda Abuturrab yake, idonshi kyam a kanta, sunkuyar da kai tayi, Ammah ce ta dubi inda Batuul ďin tabi da ido ta ganshi a durkushe ta hade rae tace “Mey kuma ka tsaya ka sata a gaba kana kallo, kaje kuma da sassafe kazo kai kaita asibiti”, murmushin da bae shirya ba yyi a sanyaye ya mike yace “Sai da safe Ammah” snn ya juya , da yaje bakin k’ofa sai da ya kuma juyowa sukayi ido huďu da Batuul ta ďauke idonta da sauri ya juya ya fice, yana fita Ammah ta dubeta tace “Bitti, tashi muje kiyi wanka ki canja kaya, ni bansanma ina yarinyar nan ta karkaďa ba, ita taimaka mata ta cire kayan jikinta da sarkan da komai ta kaita toilet, ta haďa mata ruwan wanka mai zafi tukunna ta fito, Ammah na fita ta tub’e kayan dake jikinta ta shiga bathtub ta zauna a ciki, ta kai minti ashirin a ciki sai da taji ruwan ya fara hucewa tukunna ta fitodaga ciki, da bathrobe ďin da yayi mata yawa ajikinta ta fito, Ammah ta tarar ita da Farida har ta canza zuwa kayan baccinta zaune suna hira, Farida na ganinta ta mik’e cikin sauri ta isa wajen Batuul, rik’eta tayi tareda da zaunar da ita akan gadon a hankali tana kallonta kamar wacce aka ce mata Batuul zata karye in tayi k’wak’waran motsi, sai da ta tabbatar Batuul ta zauna tukunna tace “yanxu Ammah ke faďa min abinda ya faru, ni bansan baki tafi ba ai, na nemi ki a hall ďin ban ganki ba, daga baya Yaa Massa yazo yana tambayana ina kike, wai tare zaku tafi shi zai maidaki, toh i thought ma har ya dawo dake gida sai daga baya Ammah ke tambayana wai muna tare, sorry Sweetheart, bs nasha faďa miki Yaa Abun nan mugu bane kina k’in yadda gashi nan ai yana so ya illata mana keh, yanxu ai kya yarda, ni matarshi ma nafi tausayawa, ko da shike ma bana tausayinta tunda ita ta gani zata ita, tayi ta yiwa mutane kallon….”, Ammah ce ta tareta da cewa “toh meye na maganan y’ar mutane zaki sa gabanta yayi ta faďuwa babu gaira babu dalili, bana son hiran mutane, ki dai yi na yayan naki tunda shi ya jawowa kansa da bak’in halin nan nashi”, a marairaice Farida ta juyo ta dubi Ammah tace “Ammah dagaske nefa, sai waďanda taga dama take kulawa, a gidan nan daga Yaa Abu sai Sadiq take kulawa kamar su kaďai ne mutane”, “toh keh meye naki a ciki, dama Abun ne dolenta a gidan ai, tunda shi tana kulashi ai an wuce komai, ke dai ina faďa miki babu ruwanki da ita”, baki Farida ta zumb’uro tare da cewa “toh Ammah in sha Allah”, Batuul dai bata ce musu komai ba, tana nan zaune tana ta tunanin abinda ya sameta yau, tunani tayi da yanxu wani abun ya sameta mey zai dawo yace ya sameta, wata zuciyar tace mayb yayi k’aryan shi bai ganki ba mana, ai gaskiyan Farida ne da take ce mishi mugu, Ammah ce ta katse mata tunaninta da cewa “Bitti shafa mai ki saka kaya ki kwanta kinji”, ta mik’a mata mai da wasu rigunan bacci masu kyau riga da wando milk da brown masu kauri, sai da ta shafa man ta saka kaya tukunna tasa aka kawo mata abinci da magani tasha bayan taci abincin, Ammah ce tace su tafi wajen Abui su kwana dan nan ďin zaiyi musu hayaniya, hakan kuwa akayi, Farida ce ta taimakawa Batuul suka isa har side ďinshi, ko ina duhu an kashe wuta sai ďan hasken tv dake haskawa da alama Abui na ciki bai yi bacci ba, wani ďaki Farida ta shigar da Batuul tace mata ta kwanta zataje dubo Abui taga ko bai yi bacci ba, in yayi bacci zata kaso mishi tv ta dawo, tana fita Batuul ta jawo bargo ta rufe jikkinta dashi tayi kwanciyarta,
+
STORY CONTINUES BELOW
Yana isa ďakinshi ya zauna a coffee chair ďin ďakin, kanshi ya dafa ya kai wajen minti 5 a haka tukunna ya mik’e daga k’arshe tare da jan tsaki ya cire jik’ak’k’en kayan jikinshi ya ďaura towel ya shige toilet, sai da yayi wanka tukunna ya ďaura da alwala yazo ya sa kaya tukunna yayi sallah, bayan ya gama addu’o’inshi ya hau ya kwanta, kasa baccin yayi, tunanin yakeyi daga gobe fah Shida Ajiddeh har sai mutuwa ce zata rabasu coz shi saki baya daga tsarinsa, ya rasa gane farin ciki yake ko bakin ciki, toh ya ma akayi na aureta ko tun can dama ina sontane, mik’ewa yayi cak daga kan gadon kamar wanda aka tsikara, kasa bawa kanshi ansa yayi kuma yasan babu mai bashi wannan ansa, yanxu komai nashi sai da Ajiddeh hatta gadon da zai kwana, shine komai nata yanxu a rayuwa, responsibility ďinta gaba ďaya ya dawo kanshi, he has to protect her with all his life kamar yadda zai yi protecting nashi, zuwa ya farayi yana kaiwa da komowa a tsakar ďakin, idonshi ne ya sauk’a akan hannunshi, glitters ďin jikin kayan Batuul ya gani da suka mak’ale mishi a jiki, duk da yayi wanka amma baisa sun bar jikinshi ba, zama yayi daga bakin gado yana bin duk inda glitters ďin yabi, tunowa yayi da ranar da ya fara ganinta har ixuwa yau ďinnan da yazo ya kwantar da ita kan gado, ranshi ne yaji yana mishi duk babu daďi, duk sanda ya ganta sai yaji zuciyarshi na yi mishi double flip, gashi Ammah kullum sai ta haďashi da ita har ya kai ga yau Ammah tayi fushi dashi duk a kanta, iska ya furzar daga bakinshi tare da cea damn it ya daki gadon da yake zaune a kai da k’arfi, yanxu gobe ma tace sai na kaita asibiti, da damu wa fuskarshi yace Allah ya kaimu.
Abui da kanshi ya shigo ya tada su Batuul suyi sallah asuba tukunna ya wuce masallaci, a can ya haďu da Abutturab suka gaisa bayan an idar da sallah, ce mishi yayi ya sameshi idan gari ya waye ya amsa da toh kowa yayi side ďinshi, Su Batuul kuwa na yin sallah suka koma bacci, k’arfe 8 yayi side ďin Ammah dan ta shaida mishi yazo da safe ya kai Batuul asibiti a duba ta, yana shiga ya tarar da Ammah zaune itada wata y’ar uwar Abui, sai ya samu waje ya zauna tukunna ya gaishesu, babu yabo babu fallasa ta amsa mishi , sai kuma yayi shiru jikinsa yyi sanyi kalau, da dae yaga shirun yayi yawa yace “Ammah nazo muje asibitin”, sai da ta gama abunda takeyi ta juyo ta dubeshi bbu yabo ba fallasa still tace kaje tana side ďin Abui, ka turota ta shirya ku tafi”, “toh” kawai yace ya mik’e ya fita, yana fita matar ta dubi Ammah tace mata ” Yaa Bilki ya naga kamar kina fushi da angon namu ne”, ta tambayi Ammah, sanin halin matar Ammah tace mata “babu wani fushi, ai safiyace, bawai an gama watsakewa ba”, kai matar ta gyaďa tace “gaskiyane, amma jiya kamar naga ya shigo da yarinyar nan da taji ciwo wajen dinner ďauke a hannunshi yana kallon fuskarta”, surutun ne ya ishi Ammah tace mata “ni ban ganshi ba”, sanin sarai Ammah tasan abinda take son sani ya sata ce mata “yanxu ki ďan jira Sadiq ya na shigowa zan tura shi ya karb’o” yana tafiya yana zancen zuci , mamakin irin yadda Ammah ta ďaukaka yarinyar yakeyi, toh wai meye ma da yarinyar da har xa ayi fushi sbda ita, wani dogon tsaki ya ja rae a bace ya isa side ďin Abui, ďakin da yasan zasu kwana ciki ya nufa ya tsaya daga bakin k’ofa, knocking yayi da farko yaji shiru, sake knocking yayi tare da tura k’ofan ďakin, a hankali Batuul ta mik’e tare da atishawa, idonshi ne ya faďa a kanta, hulan dake kanta ne ya faďi, sai gashinta da ya barbaje yabi bayanta, idonta ta kai bakin k’ofa dan ganin mai knocking ďin, da sauri ta mik’e ta wara idonta ganinshi a tsaye a bakin k’ofa, tada Farida ta shiga yi, a fusace Farida ta mik’e tana gungunin “yanxu kuma meye zaki tada ni”, k’ofan ta nuna mata amma ta kasa cewa komai, yana tsaye sanye da farar jallabiya, tashi tayi da sauri itama ta zauna, tace “lahh” saukowa tayi daga gadon ta k’araso gabanshi da ladabi tace mishi “Ina kwana Yaa Abu”, a takaice ya amsa mata da “lafiya”, tsayawa tayi tana kallonshi taji mey zai ce ya kawosa, ce mata yayi “kice waccan ta fito mu tafi asibitin ina jiranta”, juyawa tayi ta dubi Batuul sannan ta dubeshi tace “Yaa Abu da sassa….”harara ya bita dashi har bata samu k’arasa maganan ba tace “toh” ta rufe k’ofan ta koma ciki, a kan gadon ta tarar da Batuul tana zaune abinta, tana hangosu amma bata jin mey suke cewa, ce mata tayi “wai ki shirya ku tafi asibitin”, “ni mey aka ce mishi yana damuna toh, ni lafiyata k’alau”, Farida ce ta koma cikin bargo tace “kije ki faďa mishi mana, faďa min bazai yi miki wani amfani ba” ta juya ta kwanta abinta, Mikewa Batuul tayi tare da tsaki ta fice daga ďakin, yana daga parlour sama a zaune yaga tazo ta wuce tayi hanyar ďakin Ammah da kayan baccin da yayi mata yawa, sai yawo takeyi a ciki, shiga ďakin tayi ta gaida Ammah da matar dake zaune bata san ko wacece ba, “Bitti ya jikinki inji Ammah”, da ďan murmushi ta amsa da “naji sauk’i Alhamdulillah”, “Masha Allah ki shiga kiyi wanka ki fito ya kaiki a dubaki kinji, kar da akwai wani abun bamu sani ba”, ba dan bata son musu da Ammah ba da tace mata batason zuwa, amma babu yadda ta iya, matar dake zaune duba sukayi ido huďu, ďauke idonta tayi dan wani harara ta sakar mata, ita bata ma santa ba, mik’ewa tayi ta shige toilet tayi wanka ta fito, ta saka babban hijab zata fita Ammah ta dakatar da ita tace mata “ina zuwa bitti”, tace “ďakin Farida zanje in ďauko kayanta ďaya in saka mutafi”, buďe wardrobe ďina akwai wasu kayan nata a ciki har da sabbi ki ďau ďaya ki saka”, ta amsa da toh, matar nan sai bin Batuul take da ido, duk inda tayi akan idonta, duk tasa Batuul ďin tsarguwa, sai da ta ciro kayan ta koma toilet ta sakasu dan baza ta iya sawa ba a gabansu, abaya ce ta saka very simple, sai dai tsayin ya ďanyi mata yawa kasancewar Farida ta fita tsayi, ko mai bata shafa ba bare a samu ta taje kanta, chappette kawai ta shafa a lips ďinta da body spray da ta fesa tacewa Ammah ta shirya, ce mata tayi “toh kuje bitti Allah ya kara lafiya, yana jiranki”, tayi mata sallama ta fita, a parlour ta tarar dashi yana zaune yana rik’e da remote, tsayawa tayi ba tare da cewa komai ba, ďagowa yayi ya dubeta yaga ta tsaya mishi a kai, tsaki yaja tare da mik’ewa a ranshi yana faďin shikenan yarinyar nan ta gama rainashi, dan ko gaisheshi ma batayi ba, kuma duk Ammah ce ta ja masa, a baya ta bishi har suka isa inda motar ke pake, wata infinity brown mai tint taga ya nufa, itama shi ďin tayi, sai da ya buďe tukunna itama ta buďe ta shiga, sai da ta zauna tukunna ya kunna yaja suka tafi, suna cikin tafiya turarenshi yayi mata yawa ta fara atishawa, tunda ta fara bai juyo ya kalleta ba sai da tayi na uku, juyowa yayi ya dubeta with irritation, ďauke kanshi yayi daga dubanta, yana juyawa ta sake jero biyu, rae a bace yace “kiyi using handkerchief mana, you cant b spreading it anywhere”, bata ko kalleshi ba ta sake jero biyu, k’wafa yayi tare da kashe Ac motar yasan ko ba komai shi yayi contributing wa atishawan, yana kashewa kuwa ta rage yi continously sai dai jefi jefi, a gate ďin Nizamiye hospital dake Life camp yayi horn aka buďe mishi ya shiga, reception ya tsaya zai yi mata folder, ce mishi tayi “inada folder na anan”, juyowa yayi ya dubeta a yatsine yace “sai ki faďa mana number”, number ta faďawa matar dake tsaye gun, a cikin computer ta binciko tace mata “Fatima Kashim Goni ko”, kai ra gyaďa mata, matar ce ta fito tayi directing ďinsu har office ďin wani consultant farar fata, ko turancin kirki baya ji dan yanda ya amsa musu ba da turanci mai kyau ya amsa musu ba, k’arasa sukayi ciki matar kuma ta koma, kujera Abutturab ya jawo ya zauna itako Batuul tsayawa tayi bata zauna ba, likitan ne ya dubeta yace “beautiful lady come and seat down, relax and dont stress yourself” ya faďa cikin turancinshi da babu daďi yana nuna mata kujera, Abutturab ne ya juya ya dubeta tare da watsa mata harara, ďauke kanta tayi ta jawo kujera ta zauna, tana zama ya juya ga Abu yace mishi “couple?”, ko kadan bae xaci tambayar, yaji tambayar wani iri, ya ďaga kanshi ya sace kallonta, itako kanta a k’asa kamar bataji mey yace ba, samun kansa yyi da gyada masa kai kawae snn ya mik’a mishi hannu suka gaisa sannan ya fara mishi bayanin abinda ya kawosu, sai da ya gama mutumin yace musu pneumonia ke son kamata, ta guji duk wani abu mai sanyi sanyi sannan yayi musu prescribing drugs, mik’ewa yayi suka sake gaisawa da likitan sannan suka fita sukayi hanyan pharmacy dake asibitin, da pos yayi amfani ya biya duka kuďin magana sannan sukayi mota dan su koma gida, a hanya wayarsa ya fara ruri, ya dauki wayar hnklinsa na kan tukin da yake ya duba me kiran nasa ya ga Ajiddeh ce, tsaki yyi ya mayar da wayar ya ajiye, gnin tana ta kira yasa ya kuma jan wani tsakin ya daga tare da yin shiru, daga can bangaren cikin tsiririyar murya tace “Gud morning hubbyna baka tashi bane” a takaice yace “Na tashi, hw was ur nyt” cike da shagwaba tace “Au ka tashi Shine ka ki kirana sweetheart” kamar baxae ce komae ba can yace “Kinga driving nake Wife, we will tok later” ta dan wara ido cike da jin ddin sunan da ya kirata da tace “Driving kuma da sassafe angona ina ka tafi” kaguwan da yyi ta kyalesa yasa yace “Na kai sister hospital bata da lfya” dan yatsine fuska tayi tace “Sistern ka? Yhu mean farida or Who?” Xae yi magana Batuul ta fara tari tana covering bakinta da hannunta lkci daya ta daura fuskarta kan kafarta tana ci gaba da tarin ba kakkautawa, juyawa yyi yana kallonta, gnin sosae take tarin yasa ya gangara gefen titi ya tsaya, ko kadan bae lura har lkcn waya na kare kunnansa ba kuma Ajiddeh bata fasa Hello din da take yi ba jin shiru, sosae Batuul ke tarin har da kkrin amae, bae san lkcn da ya ajiye wayar hannunsa ya dagota yana kallon idonta da yyi ja ssae har lkcn ta toshe bakinta da hannunta, da kyar ya bude baki yace “Sorry” ta kauda kanta tana kkrin bude motar, ya jawota yace “Ina xaki C’mon” bakinta take nuna masa, hkn yasa ya gne me zata yi ya bude lock din motar ya fita ya xaga ya bude mata, fitowa tayi daga motar tana layi ta nufi wani gutter ta tofar da mucus din bakinta snn ta juyo tana rike da kanta dake mugun tsara mata, tana shiga motar ya rufe snn ya xaga ya shiga motar ya xauna dai dai lkcn da wayarsa ke katsewa dubawa yyi yaga miscals din Ajiddeh har uku, ya ja tsaki xae ajiye sae ga kiran ya kuma shigowa, dagawa yyi tace “Wani wlknci ne wnn Aliyu, y will b treating me like this for God sake, don ka ga na damu da kai” Cikin tsawa yace “Hold it plss kar ki bata min rae da sassafen nn, baki ji me nace maki bane, or are yhu deaf can’t yhu hear her coughing” Shiru tayi xuciyarta na tafarfasa, amma gnin ransa ya baci yasa ta marairace murya tace “To Wacce kanwartaka? Baka gaya min wacece ba” a takaice yace “Batuul, we will tok ltr” yana kai wa nn ya katse wayar ya ajiye, snn ya tada motar tare da juyawa yana kallon Batuul da ta jinginar da kanta jikin kujera idonta a lumshe.Tsayawa yayi ya zubawa fuskanta lumshashen idonshi, babu komai fuskanta daga dogon hanci sai lashes ďinta da suka kwanto a fuskan da ďan k’aramin baki, ya kai minti biyu yana kallon fuskanta ya ma rasa me yake kallo a fuskar, daga k’arshe ya dan ja tsaki ya tada motar sukayi gida, Batuul kam tunda ta kwantar da kanta bata ďago ba, parking yayi da suka isa gida ya kashe motar, jin an tsaida motan ya sata buďe idonta a hankali ta dubi side ďin da yake, maza tayi ta ďauke idonta don kallonta yake, buďe k’ofa tayi zata fita yace mata “wa zai ďaukar miki maganin”, bata kulashi ba ta dawo ta ďauki ledan magani tayi gaba abinta, ďakin Ammah ta nufa, a hankali ta tura k’ofan ďakin tasa kai, babu kowa a ďakin sai k’anshi dake tasowa ta kowane angle, shiga tayi ta zauna kan gado tare da jinginar da kanta a jikin gado ta lumshe idonta, numfashi take sauk’ewa kamar wacce tayi wani babban aikin, buďe k’ofan ďakin yayi shima ya shigo, babu kowa sai Batuul jingine a gado, k’irjinta na heaving, a zuciyanshi yace “she is lazy, kamar wacce ta ďauko gari” tabe baki yyi yaja k’ofan ya rufe, falon sama ya tsaya zai k’ira Sadiq ya tambaye shi inda Ammah take, yana ciro wayan ya hango Ammah ita da ďaya daga cikin masu aikin gidan ďauke da babban tray suna hawowa sama, sai da suka hawo tukunna ya k’arasa wajen ta yace “Ammah mun dawo”, ba tare da kalleshi ba tace “mey suka duba sukace ya sameta”, ta faďa tare da tura k’ofar ďakin, sam shi baya jin daďin yadda Ammah ke yi mishi akan yarinyar nn, binta yayi shima jiki a sanyaye ya shiga ďakin, trayn hannunta yarinyar ta ajiye ta juya ta fita, sai da ta fita tukunna ya zauna ďan nesa da Ammah yace “pneumonia ne sukace yana son kamata, sunce ta guji anything cold sai ta rage yawan wasa da ruwa da shan abun sanyu”, katseshi tayi da “wane irin ta rage wasa da ruwa, ai dama ba yi takeyi ba, kuma da k’yar aka samu ta rabu da wannan pneumonia tun tana k’arama yake wahalar da ita, sai da aka samu yarinya ta huta zaka sa ya dawo mata, ai da baka sata shiga ruwa ba da babu abinda zai sameta”, a hankali yace “Ammah nace kiyi hak’uri fa, bazai sake faruwa in sha Allah, kiyi hak’uri”, tana kwance bata buďe ido ba tana jiyo duk abinda yake faďa, wani ďan k’aramin murmushi tayi dan taji daďin yadda yake yiwa Ammah, ashe akwai waďanda yake jin maganarsu, “ai dama aikin kenan , da kayi abu ka fara bani hak’uri, k’arfe nawa zakuje gaisuwan iyayen?”, sakin murmushi yayi dan ya gano cewa ta hak’ura tunda ta fara wani zancen, ce mata yayi “bayan azahar zamu je, sai dare kuma aje a ďaukota”, “Allah ya kaimu , Su Aunty Amna sai suje su ďaukota, ba sai kun shiga gidan naka ba ai tunda kwana huďu kawai zakuyi ku wuce, tayi zamanta kawai a nan a side ďinka, kar a bata mata gida, duk ranan da kuka tashi dawowa gidanku ya zamana sabo”, yace “hakan ma yayi Ammah, inaso inci abinci” ya faďa mata kamar wani k’aramin yaro, tray ďin ta nuna mishi tace “dama Batuul na sa akawowa, amma yana da yawa zaka iya ci a ciki, Ammah ce ta mik’e ta isa inda Batuul take ta tasheta taci abinci, har kan gadon ta bita da abincin, ta ansa, kasa cin abincin tayi da hankalinta sam yaki kwanciya, shiko ko kallon inda take ma bai yi ba sai abincin shi yake ci suna ta hira da Ammah, a hankali ta ďan tsatsakuri abincin ta tace ta k’oshi, mik’ewa yayi ya yiwa Ammah sallama akan zaije ya shirya suje gidansu Ajiddeh.
+
Wayan hannunta ta k’urawa ido xuciyarta na bugawa da karfi ga wani mugun bacin rw da ya baibayeta, gumi yana ta tsatsafo mata, mesa takejin faďuwan gaba ne duk lokacin da taji sunan Batuul ko ta ganta, yanxu akan yarinyar nan Aliyu ya katse min waya harda yi min tsawa, danshi taji a fuskanta tana kai hannun taga hawaye a fuskanta, rai a b’ace ta mik’e ba tare da tasan mey zatayi ba, ďakin Mum ta nufa hawayen wani na bin wani, mata ne sun kai takwas a ďakin wasu kwance wasu kuma na cin abinci suna hira, ba sallama ta shiga ďakin tafaďa jikin Mum, kuka ta saka kamar wacce aka daka, a firgice Mum ta ďagota tana kallon jikinta taga ko da akwai abinda ya sameta, da taga jikinta lafiya ta tambayeta “meye ya faru haka, mey ya sameki, ko Aliyun ne wani abu ya sameshi”, kasa magana tayi sai ci gaba da kukanta takeyi, Yaa zee sake gefe taja tsaki tace “waye kuwa in bashi ba, ai ďan wulakancin nan nema ko baku tambaya ba”, tambayanta kowa ya shiga yi amma ta kasa basu amsa, sai da ta gaji dan kanta Mum na rik’e da ita ta ďago tace “Mum kefa kikace idan mukayi aure zai soni fiyeda koma…” bata k’arasa ba Mum ta tareta da cewa “toh meye ya faru yanxu”, cikin sheshek’a tace “Mum katse min waya yayi harda min tsawa wai ya kai k’anwar shi asibiti, kuma ba k’anwarshi bace, ni bana son yarinyar nan, duk randa na ganta sai zuciyana ya rik’a faďi, har gumi nakeyi, ko a wajen dinner kuna ganin yanda ya rikice wai dan ta ji ciwo, mum na tsaneta wllh”, sai da ta gama tukunna Mum ta mik’ar da ita tace mata “mey na yin kuka toh, ba wannan bak’ar yarinyar bace dai y’ar Maryam, mey zaiyi da ita yana da farar mata kamar ki, ko kuma kin tab’a ganin wanda aka yiwa kishiya duk zuri’armu, ai mun fi k’arfin kishiya, duk jarabar mutum sai dai ya rabu damu rabuwar kuma sai ya ďanďani kuďarsa amma ba dai yace zai shigo da wata matar muna ciki ba, kuma ke ďinnan da kike gani auren mutu ka raba, bare azo zancen kishiya, ki share hawayenki babu abinda zai faru dake”, Yaa zee ce ta turo baki tace “Ammah nifa yaron nan bai kwanta min ba, ya rik’a wani huhhura hanci yana kallon mutane ďai ďaya, ni mugun haushinsa ma nake ji”, juyowa Ajiddeh tayi cikin rashin kunya tace “ai ni dama bance mijina ya birgeki ba, kinje kin kaso aurenki kin kasa zama a ďakin miji shine zaki dameni da mijina bai birgeki ba, toh ni a haka nake sonshi kuma babu ruwanki dashi, a fusace Yaa zee ta mik’e tayo kan Ajiddeh kamar zata daketa tana faďin “da wa kike, maimaita abinda kika faďa yanxu inji in baki da hankali”, Mum ce tareta da cewa “Mey kukeyi hakan wai, kuda zaku haďu ku rufawa kanku asiri kunkama kuna faďa, keh zainab babu ruwanki da mijinta, kema Ajiddeh babu ruwanki da ita” taja tsaki, Jainaba dake gefe itace ta taso ta ďago Ajiddeh tace “ke yanxu kukan na meye kikeyi haka, akan dan ya ďauki yarinyar ya kaita asibiti koko dan taji ciwo ne ya taimka mata kike kuka, share hawayenta tayi tace “Jainaba tun randa na fara ganin yarinyar kawai naji bana sonta, gashi mamarshi sai tayi ta haďashi da ita, haka ranan graduation ďinsu tace wani wai su biyu su tsaya ayi musu hoto, wlhy da na gansu tare sai da zuciyana ya kusa harbawa ga wani gumi da nakeyi kamar nayiwa sarki k’arya duk da sanyin da akeyi, ko jiya da zamuje dinner da ita yazo wai babu motoci a gidan sun k’are duk yawan motocin gidansu amma sai da ta haďoshi da ita, haka ma da aka tashi ta tafi yawonta sai da akayi ta nemanta duk sunbi sun ďagawa kansu hankali, ni wlhy bana sonta”, sai da tayi shiru Janaba tace “toh meye alak’arshi da ita?”, “ni ban sani ba, kullum ce min yakeyi wai cousin ďinshi ce, ban san ta ina ta zama cousin ďin tashi ba, ko a wajen wannan wushe wushen nasu kunga yadda abokanshi suka tsaya yi mata liki kamar itace amaryar, ni in bata dena shiga harkata ba Allah illatata ma zanyi”, Mum ce tace “Ai ba wani alak’a na jini bane a tsakaninsu, abotace kawai a tsaksninsu na iyaye tun suna yara”, kai Janaba ta girgiza tace “toh ita mamartasa mesa take son haďashi da ita kullum, ko tana son shi ne ya aureta”, ďagowa tayi ta dubi Janaiba da idonta suka rine tace “babu wani, mey zaiyi da ita, kawai dai iko take nuna mishi na ita ta haifeshi dole yayi abinda takeso, kuma ni bata tab’a nuna bata sona ba”, “toh ki kwantar da hankalinki, babu abinda zai sami aurenki indai muna raye, ku da zaku bar k’asar ma gaba ďaya, ki kwantar da hnklin ki kinji”, kai ta gyaďa kawai ba tare da tace komai ba, haka suka ci gaba da hiran babu namijin da ya isa yi musu kishiya ko da ta wasa ce, da yadda za ayi da duk wani wanda yayi gigin cewa zai yi dashi da wacce zai auran.
STORY CONTINUES BELOW
Convoy ďin motoci sukayi shida abokanshi bayan sallar azahar har gidansu Ajiddeh, daga waje suka tsaya ya k’ira wayanta, shi yama manta da ďazu ya b’ata mata rai, a dak’ile ta amsa wayan har yanxu ranta a b’ace, ce mata yayi “ki faďawa su Mum gamu nan mun iso, zamu shigo yanxu”, tsaki taja tace “meye toh sai ka k’irani ne, ko gidan bak’onka ne”, cire wayar yayi daga kunnenshi ya duba ya tabbatar da wacce yake magana, mayarwa yayi ya k’ara wayar a kunnenshi yace “Ajiddeh kinsan da wanda kike waya kuwa”, “na sani mana , wanda ya daka min tsawa ya katse min waya akan wata Batuul….”, ji tayi an warce wayan daga bayanta anyi sallama cikin natsuwa, Janaiba ce ta anshe wayan tace mishi “Aliyu har kun iso ne”, bai nuna mata kamar sunyi komai da Ajiddeh ba yace “ehh muna bakin gate”, tace “toh bari a zo a shigo daku”, k’wafa yayi bayan sun gama wayan a ranshi yana zanyi maganin ki, bakinki bazai sake min tsaki ba, shi ba dan Ammah ma tasa shi zuwa ba wlhy da bazai zo ba, dan ya gaji da bikinma gaba ďaya, bayan y’an mintuna aka zo aka yi musu jagora, a guest room aka sauk’esu , duk matan suna parlourn lokacin, cikin girmamawa suka gama gaishesu sannan suka sa aka shigo musu da akwatuna dozen , suka ajiye musu bandir ďin dubu d’ai d’ai sabbi guda biyar, sannan suka yi musu sallama suka tafi akan anjima zasu zo ďaukan amarya, daga nan sukayi hanyan gidansu Abutturab ďin zasu gaida su Ammah, kai tsaye side ďin Ammah yayi dasu har sama, Batuul na kwance a palon sama tana kallon e tv, bata zata ba taji sallama, gashinta a buďe, da hanzari tamik’e daga kan kujerar, kamin ta tashi ta rufe kanta har sun shigo, idonshi ne ya faďa akanta , ido huďu sukayi, lumshesu yayi kamar mai jin bacci tare da galla mats hararara, juyawa tayi zata bar falon Massa ya tareta “haba cutie, sai kiyi ta wani b’uya, inata nemanki ina kika shiga ne”, a tak’aice tace mishi “ina nan mana, kaine baka ganni ba”, taci gaba da tafiya Massa na biye da ita, waje Abutturab ya bawa sauran abokan nashi suka zauna shi kuma yaje ya cewa su Ammah sun iso, a bakin k’ofar ďakin ya tarar da Massa ya juya zai dawo, bai kulashi ba ya buďe ďakin ya shiga, a gaban madubi ya tarar da ita, cikin dakewa yace “ki dena zamawa mutane a gida kai a buďe kina k’ira musu aljanu, kullum za a ganki kai babu ďan kwali”, idanunta ta juya dan tasan masiface kawai yakeji da ita tak’i kulashi, ai ko juya idanun da tayi yasashi fixgota har ta kusa faďawa jikinshi tukunna tayi maintaining balance ďinta ta tsaya, duk da haka tana jiyo numfashinshi a fuskanta, “did you just roll your eyes, I mean ni kika harara?”, yana tambayanta fuskarsa daure, tsoro ne ya sa ta kasa ansa mishi, kiciniyar k’wace kanta ta farayi daga rik’on da yayi mata idonta taf da hawaye, janyota yayi jikinshi ta faďa k’irjinshi, shiru tayi a jikinshi tana jiyo bugun zuciyanshi, sun kai kusan minti biyu a haka babu wanda ya motsa daga k’arshe ta samu ta k’wace kanta ta gudu ta shige toilet ta rufe, binta yayi da ido ya kai minti uku tsaye daga baya ya juya yyi kwafa ya fice daga ďakin, a palo ya tarar da su Yaa Mera, Aunty, Ammah, Aunty Amna da sauran Aunties ďinsu a zaune suna gaggaisawa, bayan sun gama gaisawa sukayi musu sallama suka tafi, su Ammah sukayi musu fatan komawa gidajensu lafiya, suka haďa musu guzuri dayawa.
Da daddare akaje ďauko amarya, kuka sosai tayi kamin su fito kamar ba ita ke ďaukin ayi auren ba, sosai babanta ya zaunar da ita yayi mata faďa, wa’azi da Nasiha sannan suka tafi, a side ďin Ammah aka sauk’eta ita da y’an uwanta bayan su Ammah sun gama masu fatan alheri sukace akaita side ďin Abutturab, can dare wajen k’arfe goma ya raka abokanshi ya shigo ya tarar da Batuul da Affan zaune sun rakoshi yazo yi musu sallama dan yaje gida wajen Aunty tace mishi ai tana gidansu Farida, shima faďa Aunty tayi mishi kan in yaje school yayi abinda ya kaishi ya maida hankali ya kula da ibadunshi don gobe zai wuce, sunsha kuka sosai, bear hug tayi mishi tace zata koma ciki dan baza ta iya ganin tafiyanshi ba, Farida taje ďauko mishi wani abu, Abutturab ne ya shigo ganin su tare ya bisu da harara, komawa tayi daga ciki zata wuce ta corridor taji an fixgota, baki ta buďe zata saka ihu ya toshe mata baki da ďayan hannunshi, jikinta a sake yake dan bata da k’arfin yin kokawa dashi, dab da ita yake numfashinshi na bugun fuskarta, idonta da ya cika da hawaye yayi ja yake gani, lumshe idon tayi ba tare da ta buďe ba hawayen dake tare suka zubo, jikinshine yaji yayi sanyi , baya son ganin hawayen mace, sassauta rik’on da yayi mata yayi yace “wane moron ďinne ya biyoki har cikin gida kike hugging ďinshi, kasa yi mishi magana tayi dan tasan in ta buďe bakinta to kukane, janyota ya sakeyi yace “ba tambayanki nake ba, waye shi nace”,a hankali ta buďe baki zata yi mishi magana ta kasa, sulalewa tayi a k’asa ta shiga rusa kuka, binta yayi ya kamota jikinshi, “mey aka miki kike kuka kuma yanxu, salon ki kuma hada ni da Ammah koh”, ya faďa tareda ďagota yana hararanta, cikin sark’ewar murya tace “Affan , he is going”, kallonta yayi sannan yace “who is he nace?”, a hankali tace “my bestfriend, cousin, everything”, dubanta ya sakeyi sannan ya saketa daga rik’on, jin ya sake ta ta ruga ciki a guje tana share hawaye, kusan kwana sukayi itada Farida suna jin tafiyar Affan, kamar ance musu bazai dawo ba.
Ana gobe Abutturab da matarshi zasu tafi Batuul ta koma gida dan Ammah tace sai ta warke zata tafi, ko sau ďaya basu tab’a magana da Batuul ba, in ta shigo wajen Ammah iyakanta tabi Batuul da harara, itakam Batuul ďauke idonta takeyi tace kya ji dashi, ranan da ta koma gida Aunty take faďa mata Baba ya samo mata admission a Nile, tayi hak’uri da London university of economics ďin, bata faďa mata dalili ba, ranta baiso ba amma tayi addu’an Allah yasa hakan ne yafi alkhairi, a ranan da daddare yazo yiwa su Aunty sallama shida matarshi, sai da suka fara zuwa gidansu Ajiddeh tukunna sukayi gidan su Massa, haka sukayi ta yawo, wajen sha ďaya sukaje gidansu Batuul, tana kwance a parlour ita kaďai tana kallo taji bell na ringing, da mamakin waye mai buga k’ofa war haka ta tashi taje ta buďe, manyan idanunshi na masu kama da mai bacci ya watso mata, da sauri ta ďauke nata idon dan wani iri takeji ganin idonshi, matsawa tayi ta basu hanya suka shiga ciki, Ajiddeh bata sanma nan bane gidansu Batuul sai da taga Abutturab ďin ya matsa ta hango Batuul, tsaki taja itama ta shigo, hanyan sama tayi zata hau taji ya biyota a baya, sai da ta hau sama yana biye da ita tukunna ta tsaya, a dake ya ce mata “Aunty fa, i want to meet her”, bata ce komai ba tayi hanyan ďakin Aunty, tafiyan a hankali yake kallo daga baya har ta shige ďakin, ya sauk’o k’asa, ďakinta ta wuce bayan Aunty ta sauk’a, samun kanta tayi da tsayuwa a bakin window tana jiran taga tafiyansu, ta daďe sosai tukunna taga sun fito, sai da taga tafiyan nasu tukunna ta faďa kan gadonta, bata murna kuma bata farin ciki, ta rasa gane meke damunta, washegari karfe tara jirginsu ya ďaga suka tafi UK.