BATUUL
CHAPTER 9
Kanta a k’asa ta kasa ďagowa, bata tab’a jinta takure a gidansu Farida ba irin yau, hawaye ne ya fara taruwa idonta tana k’ok’arin maidawa, Ammah ce tace “Bitti ya haka, kici abinci mana”, Murmushi Sadiq yayi yace “Toh ai Yaa Abun ne bai bata ba shi ya zauna abinshi sai ci yake kuma ba haka akeyi ba”, gaba ďaya kunya ya kamata su Farida sai dariya sukeyi, shikam Abu sau ďaya ya kalleta ya ďauke kanshi yaci gaba da shan shayin shi, Aunty Amna ce tace “Batuul ďauki spoon ďinki kici a cikin nashi plate ďin da ya ďiba kinji, rabu dashi inyaso shi ya ďebi wani”, kallon Aunty Amna yayi da tayi kamar batasan yana kallonta ba, Ammah tace “Farida zuba mata tunda ita kunya takeji taqi sakin jikinta”,tashi Farida tayi tazo daga gefen Battul ta ďauki serving spoon tace wa Batuul “Bestfrnd what would you like to have, i will be at your service”, tana murmushi ta kare maganan, juyawa tayi suka haďa ido da Abutturab dake shan tea yana kallonta, harara ya watsa mata tayi saurin ďauke kanta tana zumb’uro baki a ranta tace masifaffe, ta juya ta sake lek’a fuskan Batuul dake k’asa, kaman yadda waitresses sukeyi tace “Ma’am just say anything and i will serve you”, Sadiq ne ya harareta yace “Kin tsaya surutu yaushe zata faďa miki abinda zataci, kawai ki zuba mata komai”, shima zumb’uro mishi bakin tayi ta ďauke kanta ta janyo plate ta shiga zubawa Batuul abinci, sai da ta zuba mata duk abincin dake kan dinning ďinnan, plate ďin soup ďin kayan cikin kawai ta iya jawowa gabanta ta saka spoon a ciki, a hankali take ďiba tana kaiwa baki, kanta ta ďago shima a lokacin zai ajiye cup ďin hannunshi, wani irin kallo yayi mata ya mik’e ya bar wajen, hanyan stair case yabi ya haura sama, da ido su Aunty Amnah suka bishi ganin bai ci wani abin kirki ba ya mik’e yayi tafiyarsa, Ammah kam ko ta kansa bata bi ba, yana barin wajen ta sauk’e ajiyan zuciya, abincinta ta shiga ci tana haďa soup ďin da soyayyen dankali a hnkli, kaďan taci ta janye hannunta daga ciki, sai da kowa ya gama tukunna suka koma sama.
+
Wajen sha ďaya Ammah ta shigo ta gansu a ďakin Faridah suna kwance kan gadon Farida suna kallon wani abu a system sai dariya sukeyi, ta daďe tsaye tana kallon yadda Batuul ta sake, sosai hakan yayi mata daďi, basu lura da tana ďakin ba sai da sukaji ta k’ira sunan Farida, da sauri Batuul ta mik’e tana gyara ďankwalin kanta kamar ita aka k’ira, murmushi Ammah tayi tacewa Farida “Ki shirya kije Baa Liman na jiranki zakije gidan Yaa Mera ku kai mata sak’o”, kai ta gyaďa tace “Toh Ammah”, ta juya ta kalli Batuul da tayi shiru tace “Ki shirya mu tafi”, Ammah da har ta juya zata tafi ta juyo tace “A ah, ke nace kije, bance zaki tafi da ita ba, banda ita a yawo yanxu, duk fitan da zatayi yanxu sai da sanin mijinta”, da sauri Batuul ta ďago idanunta da suka fara kawo ruwa jin abinda Ammah tace, taci gaba da cewa “Bitti tashi muje kamin ta dawo, muje in k’arasa harhaďa miki abubuwan da nasan zaki buk’ata kamin anjima ku tashi tafiya kuma babu time”, zuciyantane ya shiga bugawa jin abunda Ammah tace, yau kuma zasu tafi, ina ďin wai zasu tafi da har za ayi mata shirin abinda zata buk’ata, gaba ďaya kanta ya gama ďaurewa, gabanta ya shiga faduwa, Allah yasa ba can kasar Ammah ke nufi ba, jiki a sanyaye ta tashi tabi bayan Ammah sukayi waje Farida kuma ta sa mayafinta tayi waje, har suka isa ďakin Ammah Batuul sak’e sak’e takeyi a ranta, sai da Ammah tace mata ta zauna tukunna ta samu guri ta zauna k’asan carpet ďin, ďagota Ammah tayi ta zaunar kan gadon, sai sissinne kai take wai ita kunya, wasu manyan kwalaye Ammah ta nufa tacewa Batuul “Bitti kinga wannan ma nakine, ďazu Aunty tasa aka kawo miki shi, turarrukan wutanki ne da na shafawa, in kinje kullum ki riqa amfani dasu, ya zama kullum ďakinki akwai shi, kinga dai yadda Mamanki takeyi ko, ko gidanku aka shiga sai an fito ana k’anshi, toh haka zaki rik’ayi kema kin ji, zakije inda bakisan kowa ba Bitti, ki dage da addu’a, duk abinda Abu zai yi miki kar kice zaki faďawa su Aunty, nima matsayin Aunty nake in har yayi miki abunda ba daďi kar kiji komai ki k’irani ki faďamin, ni da kaina zan sab’a mishi”, take idon Batuul ya fara zubda hawaye hankalinta ya tashi ba kadan ba, Ammah taci gaba “Kinga in kun koma bake kaďai bace, ki bata girmanta a matsayinta na wacce ta girmeki, babu ruwanki da shiga harkarta, babu ruwanki da duk wani abu da zakiga tanayi indai ba ta haďa dake bane, ki zauna da ita tsakani da Allah, kinga zaman aure ne yasaki barin gaban iyayenki har wata k’asa, kiyi hak’uri ki zauna sannan ki kula da ibadunki, ki kula da kanki sosai kinji, Allah yayi miki albarka” sosai Batuul ta shiga kuka kamar anyi mata wani abun, da k’yar Ammah ta rarrasheta ta bata baki tayi shiru, Ammah dake cicciro kwalaban turaren cikin kwali tana yiwa Batuul bayanin duk yadda suke, ta dubi Batuul tace “Bitti tashi je ki k’iramin Yayanku yazo ayi packaging kwalayen nan”, jiki a sanyaye take kallon Ammah tace “Ammah bansan ina yake ba”, Ammah tace ai bazai wuce ďakinshi ba, kije can yana ďakin kice yazo ina nemanshi yanxu”, kamar bata son mik’ewa a hankali ta tashi jiki ba kwari ta dauki mayafinta, har ta fara tafiya ta juyo tace “Ammah inane ďakin nashi yake?”, Ammah tace “ďakin k’arshe by your left”, jiki a sanyaye ta juya ta fita daga dakin, tafi minti biyar bakin k’ofar ďakin tukunna ta shiga knocking a hankali kamar bata so aji gabanta na faduwa, bayan ‘yan mintuna taji ya murda kofar ta koma baya da sauri, shi kam tsayawa kallonta yyi da mamaki don yyi tunanin farida ce hkn yasa ya taso ya ji dalilin knocking maimakon sallama, hade rai yyi ya juya ya koma cikin dakin, a hnkli ta bi bayansa ta shiga dakin ta tsaya daga bakin kofar kanta a kasa tace ” Ammah na kiran ka” mikewa taga yyi, tana ganin hka ta juya da sauri xata fita daga dakin yyi hanxarin rikota ya juyar da ita yana mata wani irin kallo, kin bari su hada ido tayi, yyi wani murmushin yace “Tunda kika yrda aka hada mu dama akwae sharadodin da xan lissafo maki kafin mu bar kasar nn, nd yhu have to abide to them ol idan kina son kwanciyar hankalin ki da xaman lfyan ki, it’s vry well knwn to yhu dat ni bana son ki, yea bana sonki sure, we 2 were neva on gud terms ryt frm d start! Duk da hkn baki yi making any effort ba wajen preventing parent dinmu frm hooking us up, rather yhu encouraged them ta hanyar amince masu dari bisa dari, So….” Wani matsanancin kuka ta fashe da ta durkushe wajen ta shiga rerawa, komawa baya yyi yana kallonta, lkci daya hankalinsa ya tashi, kofan da ke bude ya kalla ya karasa da sauri ya rufe, snn ta dawo ya durkushe gabanta shi ma yana kallonta yace “Na maki wani abun ne?” Kuka take ssae, kukan bakin ciki da kukan tausayin kanta, ji take kmr Allah ya dauki ranta ta huta kawae, ko bae fada ba tasan karshen farin cikinta ne a duniya ya xo, a dan rikice yace “Talk to me mana, me na maki kike kuka, why kike son hada ni da mahaifiyata ne wae, daga magana sae kuka,” kin dagowa tayi bare yasa ran amsa, sae kukan da take har da sheshsheka, ji yyi an bude kofar dakin Ammah, ae bae san lkcin da ya jawota jikinsa ya rungumeta ba, wani dad’da’dan sanyin kamshin da ya bugi hancinsa ya sa shi runtse ido da sauri, ita kanta sae da ta tsorata ta kasa ci gaba da kukan da take gabanta na faduwa, sun kusa minti biyar a hka, cikin sanyin murya idonsa lumshe har lkcn kmr me rada yace “Am… am.. I mean am srry!” A hnkli ya kuma cewa “Am srry” sae kuma ya bude idanuwansa ya daura kan gashin kanta dake fitar da wani fitinannen kamshi don gyalenta ya xame, d’ago kai tayi suna hada ido ya saketa ya mike da sauri, da kyar ita ma ta mike kanta a kasa xata fita ya fixgota ya wani hade rae kmr ba shi ba yace “clean those tearz” sunkuyar da kai tayi, ya ciro handki a aljihunsa ya dago kanta ya shiga goge hawayen fuskarta, yana mayar da handki din aljihunsa ta juya ta fice ya bi bayanta, ko da suka koma dakin Ammah bata ciki, Batuul taje can karshen gado ta xauna bayan ta daura mayafinta a kai, stool ya ja ya xauna shi ma ya fiddo wayarsa yana dannawa, lkci lkci yake satan kallonta ita ma hka, da sun hada ido kuma ya jefa mata harara, a hka Ammah ta shigo ta samesu, xama Ammah tayi yace “Gani Ammah” Ammah tace “Eh dama wa en can kwalayen xa ayi packaging kadda lkci ya kure ko ya kaga” kansa a kasa yace “Toh Ammah bari in kira sadiq,” ya mike ya fita daga dakin, Ammah ta juya ta kalli Batuul, da sauri ta sunkuyar da kai cike da kunya don gani take kmr Ammah xata ji kamshin turarensa a jikinta.
Da yamma Ammah tasa Batuul ta sake shiryawa cikin wani kayan, atampa exclusive ta saka mai kyau, kayan yayi mata kyau sosai har ta gaji, k’asa suka sauk’o lokacin Abutturab shima yana k’asa yana jiranta, shima yayi kyau sosai cikin kaftan ďinshi fari da hularshi Rawaram, tunda take sauk’owa yake kallonta har sai da ta k’araso tazo kusa dashi tukunna ya ďauke idonshi daga kanta, Ammah ce tace “ku fara zuwa gidan Yaa Mera daga nan ku wuce gidansu”, “Toh kawai yace ya juya yana jira ta fara fita, ganin batada niyyan motsi yayi ďan siririn tsaki ya fita, a hankali take ďaga k’afa tabi bayanshi, sai da ya buďe motar ya shiga ya zauna tukunna itama ta buďe ta shiga, babu wanda yace da wani uffan har suka isa gidan Yaa Mera, sosai taji daďin ganinsu, Nasiha tayi musu sosai tasa aka cika musu gabansu da abinci iri iri, suna zaune Massa ya shigo shima yayi ta tsokanan Batuul da ta kasa cewa komai, basu wuce awa ďaya ba suka yiwa su Yaa Mera sallama, itama tayi musu addu’a suka wuce, sai da ya ďau hanyan gidansu tukunna ya fara magana ba tare da ya kalleta ba “ki dena yiwa mutane wannan shirun naki, sai anyi miki magana kiyi kamar bakya jin abinda ake faďi idan aka tambayi dalili ki saka ma mutane kukan munafurci” kamar batasan mey yake cewa ba taci gaba da kallon window ta waje, jin tak’i cewa komai yayi k’wafa yaci gaba da tuk’inshi, suna zuwa gaban gate ďin gidansu, hannu tasa zata buďe k’ofan ta fita kamin masu gadi su buďesu musu gate, kamar yasan abinda take shirin yi ya danna lock ďin motar, murďawa tayi taji yaqi buďuwa, rau rau tayi da ido tana kallonshi, har idonta ya fara hawaye , mamakinta ya tsayayi yace “da akayi miki mey ďin zaki fara hawaye kuma”, ďauke kanta tayi tare da ďan murguďa bakinta ta ďanyi murmuring wani abu sae dae fa duk ganinsu da tayi a kofar gidansu ne yasa ta samu wnn livern, kallonta yayi yace “Did you say anything”, daidai lokacin aka buďe gate ďin yayi k’wafa ya ďauke kanshi daga dubanta ya sa kai cikin gidan, kin buďewa yayi bayan yayi parking har saida ta juyo ta kalleshi, yace “clean those tears , baza ki shiga gidannan da hawaye ba”, ba shiri ta shiga share hawayen dake idonta, sai da ta goge ta juyo tana dubanshi ganin yaki budewa har lkcn a hnkli tace ” na goge”, daga gefenshi ya danna lock ďin, da sauri ta buďe motar ta fita a guje, murmushi yayi ya fito daga cikin motar, da gudu ta shigo palon gidansu tana k’walawa y’an gidansu k’ira a jere, Aunty Hafsat da ta fito daga kitchen ta fara haďuwa da, da mamaki Aunty Hafsat tace “A ah Batuul daga ina haka kika shigo kina ihu haka”, tafiya taji kan stairs, juyawa tayi taga Aunty ke sauk’owa, da gudu tayi wajen Aunty ta rungumeta, tana jinta da tayi jikin Aunty ta fashe kuka, murmushin k’arfin hali itama Aunty tayi dan itama kwana ďaya da tayi bata gidan tayi kewarta sosai, ďagota tayi tana kallon fuskanta tace “Kukan na meye kuma Batuul”, sake komawa tayi ta kwanta jikin Aunty taci gaba da kukan da takeyi, da sallama ya shigo , ďagowa tayi daga jikin Aunty tana kallon Aunty tace “Aunty su Mahir fa”, Aunty tace “Ai yau babu wanda yaje Islamiyya cikinsu, Hafiz kam kuka ya dingayi wai sai an kaishi inda kike”, hawayen dake idonta ne ya k’arasa gangarowa jin abinda Aunty tace, da gudu ta k’arasa hawa sama tayi ďakinsu, buďewa tayi tagansu kamar kullum ďakin yadda yake suna kallon ball, da gudu ta shige ta rungumosu, sai da suka sake juna Yusra tace “Yaa Batuul wai inji Baba zaki tafi Uk yau zamu daďe bamu ganki ba dagaskene?”, ji tayi kamar zata fasa ihu tayi murmushi tace “a ah bazan daďe ba, ai zaku rakani airport ko”, da sauri suka shiga gyaďa kai, ta kalli manyan da sukayi kamar basu san tana ďakin ba tace “y’an rainin wayo dama nasan jira kuke in bar gidan shiyasa kun ganni yanxu ma baku damu ba”, dariya sukayi suka juyo sukace “penalty za a buga shiyasa”, duk suka taso suka dawo kan gadon da take, zama tayi suna ta hira da k’annenta har saida Aunty ta tura a k’irata, kitchen suka shige da Aunty Aunty ta dubeta tace “Batuul wa yace miki haka akeyi, ya zaki tafi ki barshi shi kaďai ko ruwa baki bashi ba”, baki ta zumb’uro tace “Aunty toh ba su Janet zasu bashi ba”, Kai Aunty ta girgiza tasan akwai aiki sosai gaban Batuul dan ba wayone ya gama isanta ba gashi lokacinsu is limited, amma ba komai ko ta wayane zatayi mata magana, kai ta girgiza ta juya ta ďauko tray ta jera abubuwa tace “ďauki ki kai mishi”, baki ta zumb’uro ta kinkimi trayn tayi palo dashi, sai magrib lokacin suna shirin tafiya Baba ya dawo, shima ganinshi ta shiga sabon kuka, da k’yar ya samu tayi shiru, Abu kam suna haďa ido yake sakar mata harara, cewa Baba tayi sam sai k’annenta sun rakata airport, da farko da yaqi dan sai sun koma gidan Ammah zasu wuce, amma ganin yadda take kuka yasa driver ya kaisu, sai a lokacin Aunty taji baza ta iya jurewa ba itama taja Batuul sukayi ďaki, sunfi minti talatin har saida Baba ya shigo yace ya isa haka ta fito su tafi, kuka takeyi sosai har ta shiga cikin motar, bai ce mata komai ba shima ya shiga, motar su Ahmad na daga gaba nasu na bya sukayi gidan Ammah Kanta ta kifa tsakanin cinyoyinta ta dinga rusa kuka, shi dai bai ce mata komai ba sai kallonta da yake ta gefen ido yaga if she’s fine, sai da suka shiga cikin gida bayan yayi parking ya juyo ya dubeta ganin batada niyyan tashi ya sa ya bude motar ya fito ya wuce gun motar k’annenta, sai da k’annenta suka fito suka nufi motar Abuturrab tukunna ta shiga goge hawayen dake fuskanta, dan murmushi tayi masu ta sauk’o daga cikin motar tana kallonsu tace “mu shiga mana”, ba musu sukayi gaba, yana daga gefe yana kallonsu, yaran masu kyau duk sun fita haske, juyawa tayi ta dubi inda yake tsaye yasa hannu ďaya cikin aljihu, wani kallo ya shiga yi mata, ďauke kanta tayi daga dubanshi tabi bayansu, ita ta buďe musu k’ofa sai da suka gama shiga itama ta shiga da sallama, da murna Farida dake zaune tare da Ammah ta mik’e tana k’ok’arin ďaukan Hafiz, waje suka samu suka zazzauna daga k’asan rug ďin palon, da fara’a Ammah ta shiga ce musu “Ahmad ku tashi ku zauna kan kujera mana”, babu abinda sukeyi sai murmushi, ta dubi Batuul tace “Bitti ce musu su hau kujera mana su tashi daga k’asan nan”, kallonsu kawai Batuul tayi ta kasa musu magana, ganin sunqi tashi Ammah ta mik’awa Yusra, Mahir da Hafiz hannu alamun suzo wajenta, Yusrace kaďai taje dan ita tana da saurin sabo, Janet Farida tashiga k’walawa k’ira, babu b’ata lokaci ta fito tace “Aunty gani nazo”, ta dubeta tace “kawo musu ruwa”, ba b’ata lokaci ta juya ta tafi kawo musu ruwa, Ammah zatayi magana kenan ya turo k’ofa ya shigo yana tafiyarshi ta k’asaita, palon ya k’araso ya zauna, Ammah ta dubeshi tace ” tare da su xa ku airport knn”, Batuul da kanta ke k’asa taqi ďagowa yake kallo kamin ya kalli Ammah yace “Ehhh kuka tayi ta musu kamar yarinya wai tanaso su rakata”, Ammah tayi dariya tace “Babu wani yarinta, ai gaskiyanta da tace su rakota su yi bankwana”, baice komai ba sae tab’e baki da yyi ya mik’e yana kallon Ammah yace “Ammah Sadiq ďin ya fito ne, saura thirty minutes tafiyan namu”, Ammah tace “Ai yanxun nan ya shiga wanka”, daga jin haka ya wuce, Ammah ma tashi tayi tace “Bitti muje ki shirya kar lokaci ya k’ure kinji”, ba musu ta mik’e amma har lokacin ta kasa yadda wai itace za a rakata airport zata bar garinsu dan tayi aure zataje zama da wani, take idonta ya fara kawo ruwa, jiki a sanyaye ta bi bayan Ammah, tana shiga bath tub ta dinga kuka dan kanta ta mik’e ta fito bayan ta kusa minti goma a ciki, wasu kaya ta gani Ammah ta ajiye mata kan gado, Lace maroon ne mai green designs da jewellery ďinsu na gwal, ba b’ata lokaci ta ďauka ta sakasu cikin rashin kuxari, riga da skirt ne, kayan sun mata kyau sosai, a bakin gado ta zauna bayan ta gama y’an shafe shafenta ta shiga tunanin irin rayuwar da xata yi ynxu.
+
D’akin Abuu Ammah ta shiga bayan Batuul ta shige toilet, har ya canja kaya lokacin yana zipping wani akwati, ganin Ammah da yayi ďakinshi ne ya sashi barin abinda yake cikin hanzari ya k’araso inda take, bata ce mishi komai ba har ta k’arasa shigowa tukunna ta zauna daga bakin gadon, rabon da Ammah ta shiga ďakinshi har ya manta, jiki a sanyaye ya bita ya zauna daga k’asa, ce mata yayi “Ammah ai da kin k’irani nazo ba sai kinzo da kanki ba” har ta buďe baki zata fara mishi magana ta fasa tace “in ka gama ka sameni a ďaki toh”, daga haka ta mik’e tayi waje, ajiyar zuciya ya sauk’e dan yasan da magana bakin Ammah, koh minti biyu batayi ba da fita shima ya fita yabi bayanta, zaune ta tadda Batuul bakin gado har lkcn, ganin Ammah ta shigo yasa ta sauk’e kanta k’asa zata sauk’a k’an rug ďin Ammah tace mata tayi zamanta, kin zama tayi kan gadon ta sauk’o k’asa, da sallama ya shigo ďakin shima ya zauna kan stool ďin mirror, Ammah na kallonshi ta fara magana “Abuu ga amanan Batuul nan na baka da hannuna”, da sauri Batuul ta ďago jin abunda Ammah tace, jiki a sanyaye ta sauk’e kanta dan har idonta ya fara tara ruwa, Ammah taci gaba tana kallon yadda ya sauk’e idonshi k’asa tace “tunda kayi aure kasa k’afa ka fita daga garin nan hankalina bai kwanta ba, ni bansan tsakaninka da matarka ba amma mu dai kam babu abin alheri da tayi mana, ni da kaina na sa aka nemo maka auren Batuul dan tun kamin aurenka da Ajiddeh Batuul naso ka aura amma Allah bai yi ba sai yanxu, ko sau ďaya ban yadda kasa hawaye zuba daga idon Batuul ba, ban yadda ko da wasa matarka ta wulak’anta min ita ba, yadda take zab’inka haka nima Batuul take zab’ina sannan amana na baka ita kamar yadda iyayenta suka aminta dakai suka baka y’arsu, ka kula da ita fiyeda yadda xa ka kula da kanka, sannan makarantarta ba denawa zatayi ba, an sama mata admission a can, ka taimaka mata da dukkan k’arfinka har sai ta kamalla dan tana karatunta muka nema maka aurenta, Allah ya tayaka rik’o ya baka ikon yin adalci tsakaninsu”, ta juya tana kallon da Batuul da ta jik’a gyalenta da hawaye a lokacin tace “Bitti ga yayanki nan xa ku tafi, na faďa miki duk abinda zaiyi miki mara daďi, don’t hesitate in zama ta farko da zaki faďawa, ki zama mai respecting ďinshi kinji, he will be your guide In sha Allah, tsakanin ki da matarsa girmamawa, ki goge hawayenki kinji, kuma duk lokacin da kike son dawowa ki faďa mishi zai dawo dake kina yin kwana biyu kinji”, Sadiq ne ya turo k’ofan tareda sallama, da murmushi a fuskanshi ya dubi Abu yace “ba dai kun fasa tafiya ba yau”, Abuu ya dubeshi fuskanshi babu walwala yace “We are coming”, Ammah ta dubi Batuul ta ďagota tace “Bitti share hawayenki ki tashi kuje, Allah yayi muku albarka, ya baku xuri’a dayyaba”, da k’yar Batuul ta iya mik’ewa tana gyara gyalen dake kanta har wani shidewa take don kuka, Sadiq sai tsokananta yake sae dae shi ma xuciyarsa fal yake da tausayinta, suna sauk’a k’asa suka tarar da Massa shima yazo, gaba ďayansu suna zaune palon sun gama shanye drinks ďin da aka kawo musu, Ammah tace “jeka Abui ya shigo yanxu kuje kuyi sallama dashi, tare sukaje sukayiwa Abui sallama yana gaba tana biye da shi a baya, Abui ya sake musu Nasiha tareda yi musu Allah ya kiyaye hanya, mota uku suka yi suka nufi airport.
STORY CONTINUES BELOW
Tunda suka ďau hanyan airport take kuka ba k’akk’autawa dan tasan farin cikinta ragagge ne tunda har ta yadda tabi Abu wani garin da babu kowa nata, tausayin kanta take sosai tana kuka, sai da tabi y’an uwanta ďaya bayan ďaya tayi hugging ďinsu tana kuka su din ma kukan suke, har ta iso kan Farida dake kukan itama ta rungumeta, da k’yar suka sake juna don itama kukan da take ya hanata yin magana, ta kasa yin komai sai gyaďa kanta da takeyi, cikin hanzari ta sake Farida xata bi Sadiq da ya kasa ci gaba da kallon emotional scene din ya juya xae bar wajen, Abuturrab ya fixgota jikinshi, sosai ta shiga yin kukan kmr ana tunxura ta, dai dai saitin kunnenta ya sunkuyo a hnkli yace “control, its a public place baza mu tafi kina kuka kamar wacce na sato ba”, kwanciya tayi jikinshi tayi lamo tana ajiyar xuciya, yana jin yadda heartbeat ďinta ke up and down, hannunshi ďaya ya ďaura bayanta, ďayan kuma yayiwa su Sadiq alamun suja su Ahmad su tafi, hakan kuwa akayi, takai minti biyar kwance jikinshi, can da ta tsagaita kukan ta fara dawowa normal ta ďago kanta, jinta jikinshi yasa ta kallon fuskanshi taga shima ita yake kallo, da sauri ta matsa baya ta juya bayanta ganin ko su Farida na nan, taga wayam babu kowa wajen, kallonshi tayi da idonta da yacicciko tace “Yaa Abu dan Allah mu koma kar mu tafi plss”, wani irin kallo ya bita dashi yaja akwatin dake gabanshi yace “When you are done ina ciki”, babu yadda ta iya haka tabi bayanshi a sanyaye tana share hawayen dake sakko mata, a departures waiting room ya xauna yana jiran jin announcement din departure’n su sanin few minutes ya rage, ya juya yana kallonta ganin a tsaye take, a hnkli ta xauna nesa da shi kanta a kasa, tabe baki yyi ya kauda kai, bayan kusan minti takwas akayi announcing cewar passengers din Abuja to UK su fara boarding ynxu jirgi xae tashi, mikewa yyi yana kallonta, wasu sabbin hawayen ne ke sauko mata duk jikinta yyi sanyi ta kasa tashi, har ya fara tafiya yana jan trolley dinsa ya tsaya, juyawa yyi yana kallonta ganinta xaune yasa ya dawo yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace ” Ko in daga ki ne” a hnkli ta mike tana rufe bakinta da mayafi kar ta saki ihun da taji na shirin fitowa, sauke idonsa yyi daga kallonta ta kama hannunta ya shiga tafiya tana binsa har suka isa inda jirgin British Airline (B.A) yake tsaye, yana rike da hannunta suka shiga jirgin, a first class ya samar masu empty seats, a hnkli ta xauna ta jinginar da kanta jikin kujerar tare da lumshe ido, ya saka trolleyn hannunsa daga sama inda ake ajiye luggages, snn shi ma ya xauna, announcement aka shiga yi na cewa “Passengers on board shud pls fasten their seat belts, British Airline flight is about taking off” Abuturrab yyi fasten din seat belt dinsa yana kallonta, gani yyi ko motsi bata yi ba, ranan da suka yi boarding same plane daga Maiduguri xuwa Abuja ya tuna, yyi shiru yana kallonta, a hnkli ya kai hannunsa ya mata fasten din belt din da kansa, ta bude rinannun idonta tana kallonsa, lkci daya ya hade rai, da sauri ta sunkuyar da kanta, wayarsa ya fiddo ya maida shi flight mode ya jona earpiece ya sa a kunne ya lumshe ido, jirginsu na tashi ta fashe da wani kukan tausayin rayuwarta, bude ido yyi yana kallonta sae dae bae ce komae ba, tayi mai isarta bayan wani lkci tayi shiru ta kwantar da kai jikin kujeranta lkci daya bacci ya dauketa, sae a snn ya cire earpiece din kunnensa ya rike kansa dake sara masa xuciyarsa a dagule, from Where is he going to start this long explanation to his Ajiddeh, just ta ina xae fara ce mata iyayensa ne suka makala masa Batuul, ya xata dauki xancen, will shi even believe him, tunanin hkn ya sa ciwon kansa ya tsananta, jinginar da Batuul tayi jikinsa tana bacci ya dawo da shi duniyar tunanin da ya tafi, juyawa yyi yana kallonta ya ga bacci ssae take, ya fuzar da iska tare da lumshe ido ya jawota jikinsa don gyara mata kwanciya, muryar wata hostess din jirgin ya sa shi bude idonsa, tana tsaye dai dai kujeran da suke plate holder din seats dinsu ta jawo ta dora ruwa a kai a karamin disposable cup, murmushi dauke fuskarta tace “Sir what would yhu like to have?” Yace “Just coffee” kallon Batuul tayi xata yi magana yace “She’s OK” juyawa tayi ba a dau lkci ba ta dawo da cup din coffee ya karba yace “Thank you” d’an bow din masa tayi tana murmushi tace “Yhu are welcome Sir” daga hka ta juya ta bar wajen. Karfe sha biyu saura na dare Batuul ta bude idonta ganinta jikinsa yasa ta kallesa, idonsa lumshe yake alamar ya fara bacci, a hnkli ta xame jikinta ta xauna da kyau, ta shiga rera kuka tunawa da tayi shknn fa ta rabu da Anty, bude ido yyi yana kallonta, ya gyara xamansa a fusace yace “God! What again? Ke wae baki gajiya da kuka ne, am tired of this pls, aiki kawae su Ammah suka hada ni da I knw” jin ta kara sautin kukan yasa ba tare da yyi wani tunani ba ya jawo ta jikinsa murya can kasa yace “are yhu hungry” kin cewa komae tayi, ya watsa mata wani kallo yace “Kina jina dae koh?” Girgixa masa kai tayi, ya hade rai yace “Gud! Go back to sleep ynxun nn” rufe idonta tayi, tayi lamo jikinsa sae dae yana jin ynda xuciyarta ke bugawa. Har asuba daga ita har shi basu rintsa ba, da ta bude ido xae tambayeta ko tana jin yunwa ta girgixa kai ta kuma rufe idon, Karfe bakwae na safiyar washegari jirgin British Airline ya sauka airport a UK, nn fa Abuturrab ya ji duniyar gaba daya tayi masa xafi, da ya tuna Ajiddeh sae gabansa ya fadi ba kadan ba, da kyar ya mike yana kallon Batuul da idanuwanta suka rine ssae, hade rae yyi lkci daya ta mike kanta a kasa, ya fiddo trolley dinsa ya shiga tafiya, bin bayansa tayi hawaye cike idonta har suka sauko daga jirgin, duk da ta sha xuwa kasashen turawa da Baba har ma da Anty Hafsat yau komawa tayi kmr bakauyiya a haraban airport din, don sae shishshige masa take, ba komae kuma ya janyo hkn ba sae don duk a tsorace take, ba kuma wae turawan suka bata tsoro ba sae don tunawa da tayi da Ajiddeh Amma na ganin tafiyarsu ta koma cikin gida itama tana jimamin rashin Batuul da zatayi, ďakin Abui ta wuce ta sameshi zaune yana kallo da glass idonshi, daga gefenshi ta zauna tace “Barka da zama Abui”, yace “Yawwa Ammah, naga har kin fara missing yaran naki”, murmushi tayi mishi tace “Ai ni tausayin yarinyar nan ke cikani, sosai nake tausayinta danma dai tana da nutsuwa”, juyawa tayi ta kalli Abui with full attention tace “Abui amma hankalina gaba ďaya yaqi kwanciya, matar Abu nake jiyewa Batuul dashi kanshi Abun, ko wancan karan ni nasan Abu ba yin kanshi bane zaman da yayi ba tareda dawowa gida ba har na shekara ďaya”, with full concentration Abui yake kallonta har saida tayi shiru yace “Ehhh shiyasa this time da mukaje Maiduguri kamin a ďaura aurenshi sosai nasa aka mishi addu’a, sauk’an Alqur’ani kuma kullum sai anyi har yau ďinnan Allah ya rabasu da sharrin masharranta”, wani ajiyar zuciya Ammah ta sauk’e tace “Alhamdulillah”, ta gyara zamanta tana fuskanta Abui tace “Nima tun lokacin da Ashiekh yace a dage da addu’a ban daina ba, yanxu naga komai ya fara daidaita, dan banga alamun abinda akayi mishin har yanxu yana jikinshi ba, sai dai mu sake dagewa Allah ya sake rufa asiri, wannan karan har Batuul ďin sai da na sa ana yiwa sauk’an Qur’ani da addu’a, daga baya ma zan sake tura mata maganin kariya dan yanxu lokaci ya k’ure shiyasa ban basu ba” Abui yace “Allah ya sake karewa, tare suka amsa da “Amin”, mik’ewa tayi tana kallon Abui tace “Abui abincin fa baka ci ba gashi har takwas ya wuce”, murmushi ďauke fuskanshi yayi mata alama da tazo ta zauna gefenshi, ba musu ta dawo ta zauna gefenshi tana kallonshi yace “naga kina ta hidiman yaranki bakizo bani abinci ba shiyasa nima banci ba”, murmushi tayi dan tasan tsokanarta yake ta ďan kalleshi tace “Toh su ba yara bane, kai ai kullum inayi maka kuma daga yau su tafiya zasuyi”, k’ok’arin tashi take daga wajen tana cewa “Abui bari in kawo maka tea toh tunda baza kaci abincin ba”, jawota yayi jikinshi yace “No am okay, kiyi zamanki nima bana jin yunwa, i ate late in d evening shiyasa banci abincin ba, kuma tea ďinma i dont feel like taking it”, batace komai ba ta sake shigewa jikinshi daga nan sukaci gaba da hiransu,
1
Har suka fito daga terminal ďin bata dena kuka ba, shidai bai ce mata komai ba dan kukanta ya ishesa, tafiya yake tana biye dashi sai shishige mishi take har lkcn abun har yaso bashi dariya, Taxi ya tarar bayan sun fito yace mishi “GEORGE’S street”, driver da kanshi ya fito zai buďe musu k’ofa yace “No its okay you can sit back”, gidan baya ya buďe mata ta shiga sannan ya zagaya ya buďe ya shiga shima, babu abinda zuciyan Batuul yake sai faďuwa, hawayen da take ta k’ok’arin mayarwa yaqi tsayawa sai ma daďa zubowa yake, sau ďaya ya kalleta ya ďauke kanshi, har sukayi nisa bata dena kukan ba, ranshi ya gama b’aci sosai, juyowa yayi yana kallon yadda take ta sheshek’a kuka, hannu yasa ya kama kafaďunta yace “Behave! Kinaji na ko, tun farko i gave you option, da kin buďi baki kince bakyaso am sure babu mai miki dole, but kikayi kunnen k’ashi shine yanxu zaki dameni da kuka”, jajayen idanunta da suka rine ta ďago ta kalleshi taga shima idonshi akanta yake, hannunshi dake kafaďunta ta ture taja da baya tana goge hawayen fuskarta, kallonta ya tsaya yi da mamaki daga baya yayi k’wafa ya juya jin wayarshi na k’ara, iska ya ďan furzar daga bakinshi ganin mai k’iranshi, recieving yayi tare da sawa a kunnenshi a hnkli yace “Babe am back”, wani irin k’ara tasa da har ya sashi cirewa daga kunnenshi tukunna ya mayar yace “Hae chill ba sai kinzo ba ina hanyan dawowa ko David ban faďawa muna hanya ba”, da mamaki a ranta tace suna hanya kuma, shi da waye? oho ko ma dai waye shi ya sani, abunda ta shirya mishin in yaso duk munafikin da ya biyoshi shi ya sani ya faďa musu, da sauri ta kawar da tunanin tace “Baby ai da ka faďamin da ko breakfast nayi maka, but ban tashi ba ina bacci har yanxu, babe kazo min da Domino’s pepperoni Pizza da Cold stone Ice cream tunda akwai a hanya dashi nakeson yin breakfast”, kai ya girgiza yana mamakin halin Ajiddeh, ko yaushe ma ta iya girkin da har zata ce wai da ya faďa mata tayi mishi breakfast, ya sauke ajiyar xuciya yace “Fine naji, mun kusa isowa gida you should get up from your slumber and get ready”, yana iya jiyo murnar da takeyi tace “Right away baby”, da haka ya katse k’iran, suna gama wayan ta dirk’o daga kan gadon, straight away garden ta wuce da ďan bingel ďin rigar bacci dake jikinta taje duba kuttun data ajiye, ganin yana nan very safe ta dawo bakin palo dan tun ranan da ta dawo zuba abin ba ayi shara a gidan ba sai bayan ta aiwatar da abinda tayi niyya, sai da tabbata komai daidai ta koma cikin gida tayi wanka ta sako wata y’ar crop top da bum short, sosai ta gyara dogon gashinta ta baďe jikinta da turare ta koma ta kwanta, Batuul kam banda bugu babu abinda zuciyarta keyi, haďuwarta da Ajiddeh ba wani mai yawa bane tasan babu abin arzikin da ya taba haďata da ita in banda hararta da takeyi kullum in sun hadu, maganganun da Ammah tayi mata ne suka dinga dawo mata kai, Ammah tace mata kar ta yadda su rainata, yes hakane baza ta yadda su rainata ba, toh ita inama ruwanta da ita ne, ba sai ta kulata bane bama zata rainata, ďan tsaki taja ba tare da ta san tayi hkn ba, juyowa yayi yana kallonta jin tsakin da tayi, ganin za a wuce Domino’s yasa shi cewa driver ya tsaya, parking driver yayi ya fita ya shiga Domino’s bayan 10 mins ya fito rik’e da kwalaye a hannunshi na pizza da ledan Ice cream, kanta na daga jikin window tana ta kalle kallenta ta ďago tana kallonshi, wani irin relief yaji ganin idonta ba hawaye, shiga yayi ya zauna driver ya tada motar suka tafi, tafiyar 8mins suka isa anguwansu, gini ne uniformly masu kyau duk iri ďaya da red bricks, bambancin wani da wani kawai motocin dake pake ko kuma yadda flowers ďin ke jere, bin ko ina da kallo ta rik’ayi zuciyanta na ci gaba da bugawa, har compound ďin driver yayi parking, tsayawa yayi yana kallonta bayan ya fito daga motan ganin taqi fitowa yace “you can come out, ba motata bace”, ďauke kanta tayi a sanyaye ta fito, ta bi bayan shi, murďa k’ofan palon yayi ya shiga da sallama yana kalle kalle, kan vanity table ďin palon ya ajiye boxes ďin hannunshi, Batuul ta kasa Karasowa cikin falon, Ajiddeh ce ta sauk’o a guje daga kan bene tazo rungume shi da murna tare da lumshe ido, shima ya rungume ta ssae, sam bata lura da Batuul dake bakin kofa ba, cikin muryar shagwaba tace “Babe shine ka daďe a Nigeria ina ta jiranka, ka kawomin pizzan?”, idonta ne ya faďa kan vanity table ďin ta juya zata ďauko kwalin cike da murna, cak ta tsaya ganin Batuul a bakin kofa, lkci daya komai ya tsaya mata, zuciyanta ne ya shiga bugawa da sauri da sauri tana kallon Batuul da itama ke kallonta duk a mugun tsorace take hkn bae nuna a fuskarta ba, dawowa tayi da baya tana kallon Abu, idonta ya cicciko ruwa tana kallon idonshi ta fara mishi magana da kyar, “Aliyu who is she?”, this d time he dreaded dama, runtse ido yyi ya kamo hannunta zai jawota jikinshi ganin yadda jikinta ke b’ari, ta wani warce hannunta da karfi daga rik’on da yayi mata cikin rawan murya tace “wannan wane irin jaraba ne Aliyu, watan ka ďaya can kana tare dasu shine zaka dawo ma baza a bari ka dawo kai kaďai ba sai an haďaka da wata, watanma a rasa da wacce za a haďaka sai wannan mai kama da y’an ethopian ragowar yunwa”, sosai ran Batuul ya sosu jin abinda Ajiddeh ke kiranta da, lkci daya hawaye ya kawo idonta ta sunkuyar da kanta, shima Abu ranshi ya b’aci jin maganganunta amma baison nunawa gaban Batuul dan ya gama cika mata bakin yana son matarsa, kuma bai son ta rainata, iska ya fitar daga bakinshi ya birkita lallausan gashin kansa yace “calm down babe, kinsan she is my cousin, and.. and… Babe karatu fa tazo yi nothin else, babanta ne baison tayi zaman hostel shiyasa yakeso ta zauna gun mu”, da mamaki Batuul ta ďago kanta jin abinda yace, shi kansa bai san lkcn da yyi formulatin karyan ba lkci daya kmr da can ya tsara, ajiyar zuciya ta sauk’e ba tare da ta shirya ba, sae dae duk da hka xuciyarta bae bar tafasa ba don ita har ga Allah ta tsani Batuul with passion, ita kanta bata san dalilin k’in ta da take ba, janyewa tayi daga jikinshi tana k’arewa Batuul kallo tana yamutse fuska ganin yadda jikin Batuul ke kyalli saboda gyaran da yasha, tasan hasken Batuul bai kai haka kyau ba, gashi sai wani kyalli takeyi kamar amarya, nn hankalinta ya kuma tashi tace “toh in suna son karatunta waje sai an kawota gidana ne xata yi, nasan duk salon sa ido ne aka haďoka da ita babu wani karatu, sai kace wanda nake yankan namanshi inaci baza a bar mutum ya huta ba, toh wlhy sai dai ko ni ko ita a gidannan dan bazan yadda da harkar munafikai ba”, ta fadi hkn tana masa wani matsiyacin kallo tana girgixa kafa, da mamaki ya tsaya yana kallonta, wai shi Ajiddeh ke yiwa shirmen nan a gaban yarinya don ta rainasa, kallon Batuul yayi da itama ta tsaya jin abunda Ajiddeh ke cewa, karasawa yyi fuskarsa daure ya kama hannunta yayi hanyan staircase da ita, mutuwan tsaye Ajiddeh tayi ganin abinda yyi, a tsorace take kallon Abutturab ko shi ďinne dan tasan ko da safe sai da ta sake duba magungunan da tayi mishi taga kuma komai daidai yake, toh ya akayi ya iya tsallake maganarta har yaja hannun wannan shegiyar da yake ikirarin k’anwarsa ce su bar ta tsaye, wasu hawayene masu ďumi shiga bin kuncinta ta bisu da kallo, Batuul kam ta kasa cewa komai sai binshi da takeyi a baya gabanta na faduwa, wani ďaki taga ya buďe suka shiga, kallonta yayi yace “Sit right here” ya juya yaja k’ofar ya fita, juyawa tayi tana k’arewa ďakin kallo, ďan madaidaicine mai kyau komai na ciki grey and white, ďaya daga cikin sofan ďakin taje ta zauna dan ita batasan ko ďakin waye nan ya kawota ba, yana fita daga ďakin k’asa ya dawo inda Ajiddeh ke tsaye ta kasa gaskata abinda take gani da idonta, ganinshi yana nufota ya sa zuciyarta yin sanyi dan tasan bokan nan yayi assuring ďinta komai zaiyi daidai, sae dae hkn bae hanata tsuke fuska tana hawaye ba, magana ya fara yi mata yace “Ajiddeh mey ke damunki wai kike abinda kika gama yi yanxu kamar wata yarinya”, murmushin takaici ta saki tasan dole ma ai asirin nan ya kamashi, idonta cike da bala’i tace “dole mana kace mey ke damuna, kaje an gama munafirce min kai shine zakazo kana tambayata mey ke damuna”, yasan ya fara losing control dan ranshi ya fara b’aci amma bayason biye mata suyi faďa after a long time, matsowa yayi gabanta yana kallon idonta yace “control and hear me out ki dena wannan haukan da kikeyi, its not what you are thinking uhhn?”, harzuk’a ta sakeyi dan yanxu ta fara tsorata maganin nan bai kamashi ba knn, rai b’ace tace “Lallai Aliyu, hauka ko” tayi ďan dariya mai sauti tace “ai kuwa yanxu zakaga hauka in baka fita da tsinanniyan nn ba daga gidana wllh”, ranshi yaji yayi mugun b’aci cikin tsawa yace mata “Keeeh”, idonta na zubar da hawaye tana kallonshi tace “meye zakayi min kuma bayan wanda ka riga da kayi, ni nasan munafikan dake gidane suka haďoka da wannan mai kama da karuw…..”, bata samu k’arasa maganan dake bakinta ba ya daka mata wani irin tsawa tareda da damk’ota ya shaketa yana huci, turata yyi lkci daya idonsa ya kada, Batuul dake ďaki tana ta kalle kallenta ta zauna a takure sosai ta tsorata jin k’aran a falo, jiki na b’ari ta buďe k’ofa don ganin ihun mey taji, sauk’owa tayi tana kallonsu, bnda rusa kuka bbu abinda Ajiddeh ke yi, juyawa yyi yana kallon Batuul a tsawace yace “C’mon get back before i get there ynxu”, sosai Batuul ta tsorata ganin yanayinshi, sae dae bata nuna ba ta juya a hnkli ta koma sama tana share hawayen dake son xubowa daga idonta ta koma ďakin ta rufoshi.Juyawa Abuturrab yyi ya haura sama a fusace ya shige bedroom dinsa, tsaki yyi ganin hw untidy the room is, wae kuma mace ce ke rayuwa ciki, toilet ya nufa ya wanke baki ya dauro alwala ya fito ya tada sllh, ya jima xaune kan darduma yana mamakin hali na Ajiddeh, hw wil she b insulting his family into his face kuma ya dinga tolerating hka, tsaki yyi a xuciyarsa yace na san maganin ki, mikewa yyi ya shiga toilet don yin wanka, cikin kananun kaya ya shirya bayan ya fito, ya cire bedsheet din kan gadon, ya shimfida sabo, bae tsaya gyarawa ba yyi kwanciyarsa tare da lumshe ido, lkci daya ya bude ido ya mike xaune tuno Batuul da yyi, sauka yyi daga kan gadon ya fita daga dakin ya nufi wanda ya kai ta, tura kofar yyi ya shiga, xaune ya sameta can karshen gadon dakin, ta jingina jikin gadon, kana ganin idonta kasan kuka ta gama, ya wani hade rae yace “Wato ni kike jira in xo in maki sllhn in maki wanka koh, are yhu okay?” A d’an tsawace ya kare maganan yana mata mugun kallo, mikewa tayi da sauri gabanta na faduwa ta fara waige waigen inda xata ga kofar toilet, taji yace “Over there” juyawa tayi tana kallon inda ya nuna mata snn ta karasa ta bude kofar ta shiga, vry neat toilet din me hade da bathroom, sae dae da gani kasan ba a amfani da shi, ba laifi yana da girma ssae, ta dde tsaye toilet din ganin bbu toothpaste bbu toothbrush, bbu sabulu da sponge, a hnkli ta juya a sanyaye ta tura kofan ta fito, dai dai lkcn da shima ya shigo dakin, kallo daya yyi mata ya dauke kai, sabon brush, da toothpaste ya ajiye mata gefen gado, da sabulai da shower gel, sae wani sponge me laushi, da brand new white towel duk lkci daya ya dire su snn ya juya ya fice, karasawa gadon tayi ta dauki wanda xata yi amfani da ta koma bayin, wanka tayi gaba daya bayan ta wanke baki, snn ta dauro alwala ta fito, ta dde xaune kan darduma hawaye na bin kuncinta tana rokon Allah ya yyi mata katanga tsakanin ta da Ajiddeh don har ga Allah tsoronta take ita dae, ko kadan bata ji haushin matsayin da Abuturrab ya bata a gidan ba gaban matar tasa na cewa ita cousin dinsa ce da ta xo karatu kawae, share hawayen idonta tayi tayi murmushi don ita ma ya saman mata saukin bala’in matar tasa, bude kofar dakin taji anyi ta d’aga kai da sauri tana kallonsa, fuska daure yace “ki sakko ki sama ma kanki abun kari” ganin yana tsaye har lkcn yasa ta Mike da sauri ta nufi kofar da dogon farin hijab din jikinta, juyawa yyi ta bi bayansa, a tare suka sauko downstairs sae dae duk a tsorace take, gabanta yyi mugun faduwa ganin Ajiddeh xaune har lkcn a falon idon nan nata duk ya kumbura alaman ba karamin kuka ta ci ba, ko kallon inda take bae yi ba ya nufi kitchen, Batuul kam kanta a kasa take bin bayansa kmr munafuka, Ajiddeh ta bi ta da wani mugun kallo cike da tsana, suna shiga kitchen din duk ya nuna mata food stuffs ba tare da ya kalleta ba yace “Sae kiyi duk abinda kike so,” daga hka ya dauki mug ya hada Coffee don akwae ruwan xafi a E.kettle ya fice daga kitchen din, bin sa tayi da kallo a tsorace, kaddae tafiya xae yi ya bar ta daga ita sae Ajiddeh a falon ta xo ta risketa, tunanin hkn ya daga mata hnkli ssae, ta kasa motsi inda take, shi kam yana haurawa sama Ajiddeh ta bi sa da kallo hawaye na bin kuncinta, ita tasan tana son Aliyu tsakaninta da Allah ta rasa ynda xata yi ya xama sae abinda tace masa, ynxu duk kudin da ta kashe asirin nn bae yi tasiri kansa ba lallai da sake dole ta kira mummy ynxu ba da dde wa ba, kallon kofar kitchen din tayi xuciyarta na tafarfasa sae dae tana tsoron shiga ta riske Batuul don tasan Abuturrab xae iya yi mata komae ynda ransa ya baci, mikewa tayi rai bbu ddi ta haura sama tana tunanin mafita don ita kam wllh shegiyar baxata xauna mata a gida ba da sunan karatu ta dinga mata leken asiri, kofar dakinsa ta tura a hnkli ta shiga, kwance ta samesa idonsa lumshe, ta karasa kan gadon ta kwanta faffadan kirjinsa ta saki kukan kissa tace “Don ka ga ina son ka Aliyu shi yasa kke walakantani hka koh, ni bni na daura ma kai na sonka ba Allah ne ya daura min, kuma da xan iya da tuni na cire na huta….” Ta fashe da wani matsanancin kuka, d’ago kanta yyi yana kallon fuskarta da ya wanke da hawaye, ya sauke ajiyar xuciya ya rungume ta yace “Y xa ki dinga fadin bad things about my relative Ajiddeh, ni kuma ba hka nake ma naki ba, yhu are the cause of every fight btwn us, bakya daraja family na Jiddah,” shiru tayi tana sauke ajiyar xuciya, a hnkli ya shiga shafa dogon gashin kanta dake ta kamshi, cikin sanyin murya yace “Yhu knw I love yhu babe, yhu are d cause of everything, Batuul will only b here for sometime, snn yarinyar bata da damuwa, nd of course she wil b of help to yhu ke da ba kya son aiki, idan kika sake mata xa ki ji ddin xama da ita, she’s a Nyc gal” jin Ajiddeh bata ce komae ba yasa ya d’ago kanta yana kallonta, cikin shagwababbiyar murya tace “Toh shekara nawa ne karatun nata?” Yace “Ban sani ba babe, ni ban ma san me take karanta ba, dad dinta yace yana son ta xauna gun mu tayi karatunta kin ga baxan iya ce masa A’a ba, ni ma kuma burden aka daura min ynxu don dole wani abun na makaranta ni xan mata, don hka ba ke kadae abun nn ya shafa ba har ni babe” shagwabewa ta kuma yi ta shige jikinsa tace “Toh shine xaka nemi tijara ni gabanta babe, har kana…..” Bae bari ta kai karshe ba ya hade bakinsa da nata, nn fa suka lula wata duniyar, ya shiga gwada ma Ajiddehn ynda yyi kewarta ita ma hka duk ta rikita shi. Karfe sha biyu saura ta farka daga bacci, ta xame jikinta a hnkli daga nasa don bata son ta tada shi ta nufi bathroom, wanka tayi ta fito ta shirya cikin wasu sheggun kaya irin wanda ta saba sa wa, ta fito dakin ta sauko falo, pizzan dake ajiye har lkcn ta nufa.
+
STORY CONTINUES BELOW
Batuul kam tsayawa tayi tana k’arewa kitchen ďin kallo, kitchen ne mai girman gaske da yasha kayayyakin aiki sai dai da gani babu maintenance, tafi minti goma tsaye kitchen ďin ko xata ji Ajiddeh ta shigo amma shiru, hkn yasa hnklinta ya kwanta sae dae kuma ta rasa mey zata dafa, ga kitchen ďin duk yayi k’ura, batayi gigin gyarawa ba ta ďauko noodle k’waya ďaya ta buďe fridge nanma taga sausage,babu b’ata lokaci ta ďauko dafa haďaďďen noodles, standing fridge ďin dake kitchen ta buďe ta ďauko ruwa ta fito, ajiyar zuciya ta sauk’e ganin Ajiddehn ta bar falon, da sauri ta haura sama, duk ďakuna a jere suke iri ďaya ta rasa wanne ne ma ta fito daga ciki, hannu tasa zata buďe wanda ke baya ta tuna ai da zai sata bata ga an wuce ko wane ďakin ba, that means na farkon ne, a hankali ta murďa ta shiga turawa, takai seconds uku kamin tasa kai cikin ďakin, ajiya zuciya ta sauk’e ganin batayi mistake ďin ďaki ba, shiga tayi ta zauna ta fara cin abincinta, rabonta da abinci tun kamin su bar gida sai yanxu da take ci, ko a jirgi ma k’in ci tayi, sai a lokacin idonta ya kai kan ďan medium fridge a ďakin, frame ta gani daga samanshi mai kyau manne a jikin bango, hoton Abutturab ta gani da uniform ďin aviation a jikinshi tsaye gaban wani jet yana dariya, yayi kyau a hoton duk da tasan ya ďan jima dan taga girmanshi bai kai yanxu ba, hoton ta k’urawa ido dan bata saba ganin dariyanshi ba, d only time she could rememeber ranan da ya dawo da ita gida ranan da zasuyi prom yaga su Ahmad na tennis, that was d only day taga murmushinshi dan ko ran aurenshi bata ga yana dariya, ďan tsaki taja, toh ita meye nata ma da dariyanshi ynxu matsalarta Ajiddeh, juyawa tayi tana duba ko da wani frame ďin, ganin babu wani ta jawo abincinta da ya ďan huce ta faraci dan dama ba mai cin abinci mai zafi bace, a hankali take ci har ta gama tasha ruwa ta ďau plate ďin ta ajiye kan fridge ďin dan ita tsoron fita take kar taje ta haďu da Ajiddeh, dawowa tayi kan gadon ta kwanta, sai yanxu take jin gajiyar dake jikinta, tunanin rayuwarta ta shiga yi a gidan, da haka har bacci ya ďauketa nan kan gadon.
Daukan Pizzan Ajiddeh tayi ta dawo palon ta zauna tareda ciro wayanta dake aljihun wandon dake jikinta, ranta gaba ďaya a dagule yake dan tsakaninta da Allah batason Batuul da gaba ďaya zamanta kusa da mijinta, sai da ta ďauki slice ďin pizza ďaya ta faraci tukunna ta fara neman layin mummy dan a san yadda za ayi, wannan aikin nasu bai ci ba, ringing biyu mummy ta ďaga, mummy ce ta fara magana da “ya dawon?”, cikin b’acin rai Ajiddeh tace “Mummy ya dawo, babu abinda ya faru yadda muka tsara, sai ma wani masifan dake son bibiyata yanxu”, cikin hanzari mummy ta katseta da cewa “ban ganeba, kina nufin asirin bai yi tasiri ba kome?, kuma masifar mey naji kina k’irawa kanki”, kuka ne ya sub’ucewa Ajiddeh tace “Mummy babu wani aiki da bokan nan na Jainaba ya iya, duk k’arya yayi mana ya karb’e mana kuďi dan yanxu haka wata matsalar ce kan ta da”, Mummy tace “kece dai kikaje kikayi shirme bakibi abinda malamin yace ba, ko ba munyi dake in ya dawo ke da kanki zakije tarbarsa ba dan ki tabbata yabi takan abun”, cikin sheshek’a tace “Mummy ni nace miki nasan zai dawo nema, ina kwance ya k’irani wai sun dawo kuma sai na tabbata duk komai dai”, Mummy tace “toh naji, yanxu kuma matsalar mey naji kina cewa na bibiyarki, tace “Mummy sun haďoshi da wannan y’ar iskar mai kama da refugees ďin Ethopia, ni tun farko ai sai da nace muku bana sonta, gashi yanxu wai a gidana zata zauna”, Mummy tace “ban gane ba, wai wace yarinyace kike surutu haka akanta”, tace “Mum ko ba yarinyar nan ba Batuul, dan munafirci irin nasu da baya k’arewa shine suka haďoshi da ita wai karatu zatayi, kuma a rasa inda zata zauna sai a gida na”, Katseta tayi da cewa “nifa ban gane wa kike magana ba akai har yanxu Ajiddeh, wacece ita”, tace “Mum wannan yarinyar da yazo da ita a motar da zamu dinner, bayan nan a wajen dinner ta kusa faďi har ya rikota, toh ita fa”, mummy tace “ohhh jaraba, toh wannan duk ba matsala bane, su suka sani, mu yanxu tashi muke, indai muka samu mukayi tasiri akanshi ai mun gama da kowa da kowa, wulak’anci kaďai ya isheta har sai ta nemi hostel ko kuma ta koma gidan ubanta karatun, kuma ai suma da nasu gidan a can da sun sata zama ai”, Ajiddeh tace “Toh mummy ni yanxu ya zanyi dashi, ni bazan iya da bak’in halin nan nashi ba, ko ďazu inace abu yayi na kama mishi hauka ashe babu abinda yayi toh da naga a hankalinshi yake shine fa na sauk’o, wlhy bakin rai nashi daban yake, i cant take it”, Mummy tayi ajiyar zuciya tace “zai bari kizo Nigeria?”, kai ta girgiza kamar Mum ďin na gabanta tace “Mummy wlhy ko giyar wake yake sha bazai barni ba, dan ni da kaina nasha faďa mishi ban son zuwa, ko wancan bikin da mukazo nasan da abinda na shuka shiyasa, amma da cikin nutsuwarshi yake da babu inda zamu tunda da bakina na nuna mishi bana son zuwa”, Mum tace toh shikenan yanzu zamuyi magana da Jainaba sai muji yadda za ayi, duk yadda akayi zakiji a waya”, tace “toh Mummy ki gaida Dad”, da haka suka katse k’iran
D’aya saura ya buďe idonshi, ganin Ajiddeh bata nan yasan tana ďakinta, tashi yayi ya dafa kanshi tare da sauke ajiyar xuciya at last dae ya shawo kanta ya kuma san ta hakura, mikewa yyi ya faďa toilet ya sakarwa kanshi shower yayi wanka yayi alwala, sai da ya fito ya canja kaya zuwa English wears, k’arfe 1:15 ya gani lokacin, yasan by now ya fara jin yunwa, ďan tsaki yaja tunawa da yayi Ajiddeh ba iya abinci tayi ba, yanxu dole yadawo gidan da xae riqa fita yana nemawa kanshi abinci, tunawa ya sakeyi Batuul na gidan, wani xuciyar yace mishi ai sai ta riqa dafa muku, wani kuma yace mishi yarinyar nan ce zatayi maka girki, baka shirya cin abinci ba knn, ďan tsaki yaja dan itama yanxu wata liability ce, fitowa yayi ya buďe ďakin Ajiddeh don sata tayi sallah dan in ba faďa mata akayi ba toh ba yi zatayi ba akan kari, ganin bata nan ya fito yayi hanyan ďakin da ya ajiye Batuul, kan gado ya sameta kwance tana bacci ta k’udundune waje ďaya a cikin bargo.K’arasawa yayi bakin gadon yasa hannu zai yaye bargon yaga small figure ďinta na bacci peacefully a ďan takure, kitson da aka yi mata ya rufe rabin fuskanta, d’an tabe baki yyi ya bugi gefen gadon da nufin t’ada ta amma ko motsi bata yi ba, cire bargon yyi lkci daya ta mike xaune da sauri ta shiga komawa baya ganinsa, tsaki yyi yace “Kin ma yi breakfast din kusa?” Kai ta gyada ba tare da ta kallesa ba, yace “Gud, sae ki tashi kiyi sllh ki kara komawa kitchen ki sama ma kanki lunch, don matata bata girki!” Jin bata ce komae ba ya duka kusa da ita har tana iya jiyo numfashin sa da kamshin turarensa da ya cika ta, cikin kaushin murya yace “Hope am clear?” Kai ta gyada masa tana kkrin mayar da hawayen idonta, ya juya ya fice daga dakin.
+
Kwance ya tadda Ajiddeh parlour, kwalin pizza duka uku a buďe an ďan tab’a kowanne, sai apple a hannunta yana kallon Tv, daga gefenta ya zauna ya kamo hannunta yana kallonta yace “shine kika gudo kika barni koh babe”, ba tareda ta kalleshi ba don ita kam Batuul ta tsaya mata a rai tace “ai bacci ka keyi shi yasa na dawo nn” murmushi yyi ganin ynda ta basa amsan ya mik’e yace “tashi kiyi sallah toh”, dauke kai tayi kawae, kwalin da tayi littering yabi da ido ya kaďa kai ya koma sama, yana idar da sallah ya koma gaban desktop ďin dake ďakinshi, buďewa yayi yana dudduba sak’onnin da aka turo mishi, yawanci daga office ne sai na k’arshen ne ya gani daga Sadiq, sai da ya gama buďe na office ďin tukunna ya buďe wanda Sadiq ďin ya turo mishi, tsayawa yayi ya gama karanta abinda yake ciki tukunna yayiwa sauran reply sannan ya kashe ya ďauki wayanshi ya shiga neman layin Sadiq, Sadiq na ďauka yace “Yo bro, kun isa lafiya”, Abu yace “Sallama kenan”, kai Sadiq ya sosa kamar yana gabanshi yayi sallama, Abu ya amsa yace “Yeah naga ka turomin abu ta email, Sadiq yace “Ehh Abui ne yace in turo maka, acceptance letter Batuul into London University of Economics ba?”, Abu yace “tun yaushe aka nema mata admission ďin, like everything is so fast kuma tana da wannan k’ok’arin ne na karatu a can ne ma?”, dariya Sadiq yasa yace “Yaa Abu dont estimate Batuul, yarinyar nada kok’ari sosai, ai sai da akayi issuing transcript ďinta suka bata admission toh kaga they are satisfied with her perfomance”, yace “Fine naji, sai anjima ka gaida gida”, Sadiq yace “Okay bro, a gaidamin Batuul da sis Ajiddeh”, yace “zasuji”, daga nan ya katse k’iran, duk da yana son jin muryar Ammah bae kirata ba don bae son ta d’aga masa hankali da xancen Batuul.
Kan abin sallah ta zauna tayi jigum bayan ta idar da sallah, akwatinta da wayarta ke ciki ta hango daga gefe, bata san ma ko yaushe aka shigo dashi ba, da murna ta tashi ta isa ta buďe akwatin, wayarta dake ciki ta ciro ta kunna, ganin layin dake ciki yasa jikinta yin sanyi ta koma bakin gadon ta zauna, yanxu sai ta sayi sabon layi kenan, ďan tsaki tayi ta jefa wayan kan gado, tana missing gida, tana son tayi magana da Aunty da kowa ma, hawaye ne ya fara gangarowa daga idonta, tunanin roaming ne ya faďo mata, da hanzari ta mik’e tana dariya ta ďauko wayar daga kan gado, babu b’ata lokaci tayi roaming, da murmushi a fuskanta ta shiga dialing Aunty, kamar jira akeyi aka ďauki wayan, da murna tace “Hello Aunty ina kwana”, ajiyar zuciya Aunty ta sauk’e daga ďaya b’angaren har Batuul na jiyowa tace “Lafiya Batuul, halan yanxu kika tashi daga bacci naji kina kwana”, dariya Batuul tayi tana goge hawayen idonta tace “A ah Aunty, garin ne kamar safiya shiyasa nace kwana, yanxu nayi azahar ma”, Aunty tace, “yayi kyau Batuul, tun ďazu ma muke trying number ki baya shiga, Su Mahir sai damuna suke a k’ira musu ke”, kukan dake shirin fitowa ta maida jin abinda Aunty ta faďa mata tace “Allah sarki Aunty suna ina, a basu mu gaisa”, Aunty tace “sunyi bacci Batuul tun ďazu, sai dai gobe in basu ku gaisa”, kai ta kaďa kamar Aunty na ganinta, Aunty tace mata “Batuul kun isa lafiya babu matsala ko, ina y’ar uwar taki”, wani iri taji maganan Aunty, wai har itama cewa take Ajiddeh y’ar uwartace, dan batasan mey ya gama faruwa bane bama yau da safe, sai da Aunty ta sake maimaita tambayan jin tayi shiru, a hankali tace “Aunty tana lafiya, ai tana ďakinta”, Aunty tace “yayi kyau Batuul, in kin huta zamuyi waya kinji, inason muyi magana”, Batuul tace “Toh Aunty, Baba fa, yana gida?”, Aunty tace gashi nan Batuul, tayi rau rau da ido tace “Aunty shine baice zaiyi magana dani ba”, Aunty tayi dariya tace “ai gashi nan faďa mishi da kanki”, kamar zatayi kuka bayan Aunty ta mik’awa Baba wayan tace “HellO Baa, nda dubdo”, da murmushin shi na manya yace “Mamana nda dubdo, ya sabon waje”, a hankali tace “Baa Alhamdulillah”, yace “Masha Allah Batuul, Allah yayi miki albarka, ki kula da ibadunki, ki girmama na gaba dake kinji, babu ruwanki da tsokana ko tadawa mijinki hankali, ki zama mai biyayya kuma kiyi ta hkuri kinji, Allah ya taimaka”, tana kuka da k’yar ta iya buďe baki tace “In sha Allah Baa, nagode”, da haka suka katse k’iran, kuka sosai ta sa bayan sun gama wayan, shikenan rayuwanta ya canja kenan, ta dde xaune ganin yunwa ya dameta don har uku na rana yyi yasa ta mike a hnkli da Hijab jikinta ta tura kofan dakin ta fito, downstairs ta nufa a xuciyarta tana addu’an Allah yasa Ajiddeh bata nn, xaune ta sameta falon tana kallo tana cin sauran pizzan ta, duk irin faduwar da gabanta yyi hkn bae sa ta koma ba, cikin natsuwa ta tako har cikin falon ta kalleta a hnkli tana ci gaba da tafiya tace “Ina yini Anty?” Wani matsiyacin kallo Ajiddeh ta bi ta da shi har ta shiga kitchen din, snn ta mike, sae da ta fara kallon stairs snn ta bi ta cikin kitchen dib, Batuul na tsaye tsoro ya cikata don xuciyarta ya bata sae ta biyota, lallai tayi gangancin sakkowa Ajiddeh na falo, daga bakin kofa ta tsaya tana kallonta tana murmushin rainin hankali tace “Ke a tunanin ki kin samu gun xama a gidana koh? To yhu are mistaken yarinya, don sae kin gwammace da baki shigo gidana da sunan xama kiyi karatu ba, banda kinibibi, gulma, da munafurci irin na iyayen ki sun san basu da halin kama maki hostel me xae kai su karambanin turo ki UK karatu, shine xa a wani xo a daura ma miji na nauyi da wahala to wllh kun yi kadan, duk uban da ma ya kawo wnn shawarar zae saketa ne, don sae sai kin gwammace da titi kike kwana kan gidana, makwadaita kawae” Ae Batuul bata san lkcn da ta fashe da kuka jin xagi da cin fuskar da Ajiddeh ke ma iyayenta, ita din ba mai son fada bace bare ta mayar mata da martani, durkushewa gurin tayi ta dinga kukan takaici da tausayin rayuwarta, ran Ajiddeh yyi fari don har da murmushinta, ta cigaba daga inda ta tsaya.
STORY CONTINUES BELOW
Abuturrab kam na daki kan system wayarsa ta hau kara, dauka yyi ganin Ammah yasa shi saurin d’agawa da sallama, Ammah tace “Abu kun isa lafiya, shine ba kira?” Yyi k’asa da kai yace “Kiyi hkuri Amnah ynxu nake da niyar kiran ki, gajiya ne yasa hka”, Ammah tace “Shknn Babana, ina Ajiddehn, kun sameta lafiya”, yace “Alhamdulillah Ammah she is doing good”, tace “toh Abu, bazan gaji da yi maka Nasiha ba, ka kula dasu ka zauna tsakaninka da Allah dasu, Allah zai tayaka rik’on indai niyyanka is pure, sannan Fatima yarinyace k’arama, hankali bai gama game ta ba, in ka cuceta akan matarka, toh Allah sai yayi mata sakayya, kaji tsoron Allah Abu, kuma makaranta Abui yasa Sadiq ya turo maka, in ka duba kaje kayi mata necessary abubuwan da duk ya kamata” sai da yaji tayi shiru tukunna yace “In sha Allah Ammah nagode, Allah ya k’ara nisan kwana”, ta amsa da “Amin, Allah yayi muku albarka, bata wayan inyi magana da ita”, yace “Ammah tana ďakinta, sai dai in kai mata”, tace kai mata ina jira”, yace ” Toh xan kira ki” daga hka ya katse wayar ya fita yayi hanyan ďakinta, ganin bata ciki yasa ya sakko falo, tsayawa yyi daga stairs hango Ajiddeh da yyi tsaye kofar kitchen din don yasan ba arxiki ya kai ta ba, Karasowa yyi Ajiddeh na hango sa tayi tsit daga cin fuskar da take ma Batuul cike da faduwar gaba, shiga kitchen din yyi yana kallon Batuul dake durkushe har lkcn a kitchen din tana kuka, Ajiddeh ta juya ta bar bakin kofar da sauri ya bi ta da kallo, murmushi yyi yana kallon Batuul dake kuka kmr xata shide yace “Yhu see! Kinga abinda nake guje maki knn, kika rufe ido kika ce sae ni, don hka yhu have to endure duk me xa ki fuskanta daga matata tunda kika ce kin ji kin gani….” kallonshi tayi da idonta da yyi jajir ta mike da kyar ta fice daga kitchen din hawaye na bin kuncinta, murmushi ya shiga yi yana jujjuya wayar hannunsa, wayar ya fara ring, sae a snn ya tuna abinda ya sakko da shi, xaro ido yyi ya bar kitchen din da sayri ya hau sama ya nufi dakinta, kwance ya sameta tana kuka ssae, ya karasa gadon ya xauna yana kallonta yace “Wae kukan me kike ma mutane hka daga an gaya maki gskya” kin cewa komae tayi, ya kalli wayar hannunsa jin ya katse, yasan Ammah ba hakura xata yi ba, sake bugowa tayi, ya ajiye wayar ya dago Batuul ya daura hannu kan kafadarta ya runtse ido yace “Alryt! Kiyi hkuri” ko kallonsa bata yi ba kuma bata daina kukan da take ba, a tsawace yace “Nace kiyi hkuri” ae sae ta kuma fashewa da kuka, rungumeta yyi ba tare da yyi wani tunani ba, yana patting bayanta a hnkli kmr me rada yace “Am.. am srry” ita kanta ta rasa dalilin da yasa ta tsaida kukan nata sae ajiyar xuciya da take saukewa, tana jikinsa ya jawo wayar da har ya katse, sae ga shi Ammah ta kuma kira, d’agawa Ammah tayi cikin fada tace “Walakanci ne hka Abuu?” Yace “Kiyi hkuri Ammah tana bayi ne, gata” kara wayar yyi a kunnenta yana rungume da ita, jin muryan Ammah yasa hawaye sake gangarowa a hnkli cikin sanyin murya tace “Ammah ina wuni”, Ammah tace “Lafiya lau Bitti, ya gajiya, duk gajiyan ne naji muryar ki hka”, kallon fuskarta Abuturrab ke yi kawae, tana sharen hawayenta tace “Alhamdulillah Ammah, babu gajiya ya su Abui da Farida”, Ammah tace “suna lafiya Bitti, babu dai matsala ko”, kai ta ďaga tana kallon Abu da suna haďa ido ya kuma mannata jikinsa, jiki a sanyaye tace “Ehh Ammah babu komai”, Ammah tace “haka nake son ji dama, kiyi hak’uri sosai kinji Bitti, sai kiga komai yazo miki da sauk’i, makarantarki ma soon zaki fara zuwa kinji, ki manta da komai kiyi abunda ya kaiki, as i told you, don’t hesitate in telling me your problems kinji, koh na meye”, kai ta gyaďa kamar Ammahn na ganinta hawaye na xubo mata tace “Toh Ammah zanyi nagode”, tace “Yawwa Bitti”, daga haka ta mik’awa Abu wayan, ji tayi yace “Yeah gobe Monday zamuje a gama processing komai, sai Anjima Ammah mun gode”, ita kam Batuul bata ďago ta kalleshi ba sae kkrin janye jikinta daga nasa da ta shiga yi amma ya ki saketa, cikin kakkausar murya yace “Wae ma kukan mey kike yi ma mutane daga an fada maki gskya,”, sake fashe mishi tayi da sabon kukan takaici, lumshe ido yyi yana murmushi, lkci daya ya bude ido ya dafa kafaďunta yace “okay naga alamar kina son hada ni da Ammah ne, today shud b the last time da xa ki min kuka a gidana, its not going to b good for you idan na sake ganin kin yi hka, ba gidan ku bne nn, tunda kika zab’i aurena yhu have to endure everything yhu will come across” Shiru Batuul tayi tana saurarensa, duk taji yace ita ta xabi aurensa sae ranta ya baci, ido yabi fuskanta dake jik’e da hawaye, ďan k’aramin lips ďinta ya koma ja, yace “clean your face and hear me out”, a hankali tasa hannnu tana goge hawayen, sai da ta gama yace “nasan dai kinsan zancen komawanki makaranta, gobe zakije a fara komai, it doesnt mean komawanki makaranta zaisa kiyi min yawo a gida ba, am not tolerating that, sannan babu ruwanki da matata inba girmamawa ba i cant take duk wani raini da zakiyi mata, ban yadda ki rainata ba, sannan ban yadda da tarkacen k’awaye ba, not in my house, abinda ya kaiki shi zakiyi ki dawo, inma zakiyi toh ya tsaya daga can makaranta, in kuma baki yadda da all i said ba, try me and see what will happen”, har sai da taji yayi shiru tukunna ta janye daga rikon da yyi ma kafadunta tace “ai dama nasan you are always against my happiness, you snatched it all away from me, kuma da kake cewa kar in raina matarka ai nima duk sunanmu ďaya da ita, am also your wife kammar yadda kace an lik’a maka ni, and as it is, zan ďauki komai daga wajenka but not from her ka ja mata kunne bbu ruwanta da ni, kar ta kuma involving iyayena a abunta yawo kuma ba halina bane, k’awaye kuma, nobody can live in isolation, ba kowa na sani ba,”, cikin k’arfin hali tayi duka wannan maganganun dan idonta rufe tayi duka wannan maganan, chest ďinta sai heaving yake, tsaf ya gama kalleta yana kallon yadda zuciyanta ke bugawa, dariya ta kusa bashi, a hankali ta buďe idonta, cikin hanzari ta tashi zata gudu dan sai yanzu maganganun da tayi suke dawo mata, hannu yasa ya fincikota jikinshi, a tsorace tace “Ni ja kyaleni xan hada ja da Ammah” sake janyota yayi jikinshi daidai kunnenta ya sunkuyo yace “fine if thats what you actually said, just try me and see”, jin sauk’ar numfashinshi a wuyanta yasa duk tsigar jikinta tashi, kan gadon ya jefata ya juya xae fita daga ďakin, daidai bakin k’ofa yana fitowa suka ci karo da Ajiddeh ta shiga masa wani kallo, bai ce mata komai ba yayi tafiyarshi, da ido tabi k’ofan ďakin sannan tabi bayanshi da ido, hankali tashe tayi hanyan ďakinshi itama, ae ko baxa ta yi tolerating wnn ba.