GIDAN SARAUTA
CHAPTER 11
Aisekacemin babban likita ne kezaune agabana Dr Yarima Almustapha Abdulrahman Sulaiman”, Saifullah yayi maganar cikin raha yana demonstrating da hannunshi dariya Almustapha yayi sannan yace”duk wannan sunan nikadai?”…..
“Lol,sabida kacancanta kakuma kai wannan matsayin ne ae”cewar Saifullah din kafin yakoma fuskar serious to masu kallon mu kundaiji takaitaccen tarihin Yarima Almustapha daga bakinshi inakuma fatan kun gamsu kafin yamaida kallonsa kan Almustapha din sannan yace…. “kafin muje ga tambaya tagaba inason inyi dan wata clerification in babu damuwa”…….
Dan murmushi Almustapha yayi sannan yace”to inajinka Saifullah”…..
Saifullah nadan wasa da hannunshi yace”I don’t know if it’s so personal hakanan bansan dalilin dayasa baka tabo wannan bangaren ba bayan muntambayeka tarihin rayuwarka sede inason kasani wannan Yana daya daga cikin abubuwan dayasa mutane da dama sukeson ayi hirarnan dakai”.
Gyadakai kawai Almustapha yayi yayinda Saifullah yacigaba da magana”ayanda muka sani muka Kuma ji labari kai Dan Mai Martaba ne kuma his illigitimate son probably donkuwa abun yazama kaman ana musu nema akai wasu suce hakane wasu suce bahaka ba hakanan munsan kataso cikin tsangwama dakuma tsana da jama’ar gari sukayi maka bakidaya,Kai basu kadaiba harta mahaifinka da ya haife ka dakanshi benuna yasanka ba but just recently everything is normal,we were told that you’ll be the crown prince inkayi achieving some goals in five months wanda mutane da dama sunyi tunanin bazaka iyaba harma Dani cikinsu but Allah da ikonsa seyaba ka wannan iko ka Kuma yi proving namu wrong sannnan kasaye zuciyoyin jaamaa tahanyar yimasu alkhairi cikin watanni kalilan it’s indeed a blessing Yarima dukdama muna son musan is there any secret behind those hardships,is there any hidden secret that we need to know that will help us clear all our doubts sabida I
Nidai ah iya sani na yaron da ba ah haifeshi tahanya maikyau ba bazai taba gadan ubansa ba so dukyanda akayi akwai wani labari damu bamusani ba wanda yau inda hali munason kafada mana Yarima…….
Tunda Saifullah yafara magana Almustapha yadingajin zuciyarshi na dukan uku uku hakanan dukwasu abubuwa dasuka faru dashi abaya suka fara dawomai filla fillah, Allah ne kadai yasan yanda yakeji hakanan Allah ne kadai yasan halin dayake ciki ayanzu lokaci guda idanunshi suka canza launi bayajin zai iya musu bayani hakanan bayajin zai iya fadamusu sirrin gidan su it’s their personal matter hakanan bayason Sulaiman yayi suffering for his Mom’s deed dukda Magajiya deserve to be punished sede koma Mai tayi he can forgive her and akwai ranar kin dillanci ae tunda shi yanzu he’s living a normal life……….
Saifullah Jin shirun Almustapha yayi yawa yasashi karayin magana ahankali Almustapha yadubi Saifullah din da rinannun idanunshi kafin dakyar ya’iya cewa”I’m sorry, that’s my family matter I cannot tell you about it”…….. +
Ba Asma’u kadai ba kowa was very stunned by his words tsabar kidima batasan sanda takaraso gabanshi ba ta tsuguna tareda dora hannunta daya kan cinyarshi batareda ta damu da cameran dake haskosuba sannan tasa dayan hannu ah habar shi tadan dago da fuskarshi yana kallonta cikin murya mai rauni tace”why are you doing this Yaya imam?”…….
Kallonta kawai yakeyi yayinda idanunta sunciko da kwallah harma suna shirin zubowa harga Allah yarasa abun cemata ma sede by looking at those precious eyes of hers yagane cewa rashin maganar tashi ma has to do with something about her ba tausayin Sulaiman kadai ba……
Cikin murya merauni tace”I’m here for you, Ummi is with you like wise Abba and most importantly your people Yaya Imam,don Allah kada kayi shiru yau, you’ve to let the people that know the truth to speak out today,you have to let them clear all the alligations that are against you, you’re a very clean and pure person why will you suffer for someone’s mistake?…….
You’ve done nothing then,why are you trying to cover up for her?……
Tayi maganar tana hawaye kafin taciro hannunta dake gefen fuskarta tahada da dayan tadora akan nashi tana kallon hannayennasu sannan tace”do you know what Yaya Imam?”……
Girgiza mata kai yayi dukda bata kallonshi hannunsu dake sarke dana juna take kallo kafin tacigaba da magana….
“bantaba ganin mutum kamarka ba,you’re so and innocent but yet people always accuse you of being a bad person,baka taba cutan wani ba but still you never deny what people accuse you of,you never want to fight for your right you stayed like this for more than 18years now”……
Dauke idanunta tayi daga hannunsu sannan tamaida kan fuskarshi”kanada hakuri gaskiya,if I were in your shoes bazan taba iyayin haka ba, you’ve been cheated and been deprived of your rights for the past 18years but not anymore,if not for your sake atleast talk for the sake of Ummi and your two little sisters because not only you suffered but they went through alot too”, takarashe maganar tana dan goge kwallarta mutane da dama dake kallon program din seda suka zubar da kwallar tsabar tausayi ciki kuwa harda Hajja dukdama ita kukan farin ciki takeyi wai kullum tana ganin jama’a ah talabijin amma yau sega jikarta dare dare gefen Dan sarkima guda…. …
Almustapha dake kallon Asma’u with so much emotions ahankali yace”do you really want me to speak?”……..
Make kafadanta tayi yayinda hawayen ta ke karuwa kamn wanda aka bude fanfo tace…”I want it Yaya,I want it so badly”……..
Gyada matakai yayi in a very calm voice kuma yace”okay then, stop crying”,yayi maganar tareda taimaka mata tatashi sannan yazaunar da ita gefenshi hakanan yasa thumb dinshi yashiga goge Mata kwallar ta”,don Allah yagani har ranshi bason kukan nata yakeyiba daga Asma’u har Almustapha da alama sunma mata program akeyi he’s busy trying to wipe all her tears away, murmushi Saifullah yayi ganin abun bana kare bane sannan yayi dan gyaran murya cikeda zolaya yace”To lovebirds asauraremu”,don yanada tabbacin dau wannan Matar Almustaphan ne dubada yanda suke kallon juna……
wara idanu tayi lokaci guda tanashirin tashi yayinda yarike hannunta gam wannan dalilin yasa tayi lumui agurin sannan yadubi Saifullah din yana”mucigaba ba”…………
Dariya Saifullah yayi sannan yace”to Yarima munajinka”……
Dan shafa kansa Almustapha yayi sannan yace
“I’ve a very horrible past with which banmasan ta’ina zanfara yimaku bayani ba gaskiya but believe me the cause of everything was only one person and that’s my Father’s wife Magajiya”,yayi maganar ranshi na kuna don ko sunanta dabadan yazamemai doleba bayajin zai iya fada yaudin………
Magajiya dake bangarenta tana zaune da Zaliha tadafe kirjinta cikin sauri tana”nashiga uku da yaronnan”,yayinda tatashi tsaye don wallahi xaman ma gagaranta yayi Zaliha ne tace”kingani ko Mama i told you ae”…… 4
STORY CONTINUES BELOW
Magajiya da zuciyarta ke dukan uku uku tace”yimishi shiru,kiyi shiru inji maizai fada”……..
Babu yanda Zaliha ta’iya haka tayi shiru tana kallon TVn ……
Almustapha kuwa cigaba da magana yayi ahankali don muryarshi kadai canza launi tayi”we’ve gone through alot because of her, I mean me and my family dama tunda nataso she never loved me koda taga my Brother Sulaiman yana matukar sona bakaramin kokarin rabamu tayiba awancan lokacin amma hakan baiyuyu ba because we shared a very special bond,we love each other so very much da bazan iya fassara muku irin son da mukema juna ba hakanan tahana mahaifiyata rawar gaban hantsi akullum batada wani buri daya wuce tabakanta mata hakanan batada burin daya wuce ta taraba kan iyayena sede duk wani moves dinta was not a successful one harsaida tayi abunda tayi wurin ganin ta gusar da hankalin mahaifina takuma yi anfani da makamanta tamuzanta mahaifiyata bama ah idon mahaifina kadai ba har ah idanun duniya baki dayanta wanda Ina iya fadamuku that was the beginning of my hardships, awannan lokacin ne aka koremu daga gidan daya kasance na ubana hakanan akayi treating namu kamar wasu dabbobi dukda kuwa mahaifiyata nadauke da karamin cikin kannena and it was a day that my Father denied the fact that I’m his very own Son I can still feel the pain”, Almustapha yayi maganar yana taba zuciyar shi ahankali kafin yacigaba dacewa”bayan ankoremu haka muka tafi Chad da Ummi na thinking that zatasamu sassauci ah gurin iyayenta but unfortunately her family members also suka koremu hakanan suka ki yarda da’ita because sunsamu labarin abunda yafaru awancan lokacin they were all thinking that niba dan sarki Abdulrahman baneba,naso munemi gida ah garin Chad muyi rayuwarmu yanda babu wanda zaisan maima yafaru damu but Ummi was insisting that mudawo gida she’s very sure Abba zaiyafemata, she’s very sure Abba ya yarda da’ita because Ummi tayarda da mahaifina sosai,she trust him way too much haka muka damu dawo still he broke her trust infact ko kallonmu bayason yi wannan dalilin yasa nayi nayi nayi convincing Ummi mubar masarautar but bata yarda ba,she never want to leave him hakanan batason rabamu da gidan mu nikuma I’ve no other choice than to obey her wannan dalilin yasa aka labara mu Magajiya ta bamu wani gida muka zauna wanda ko slaves muhaliinsu yafi namu kyun gani amma dukda haka Ummi batadamu, we’re always treated so badly,ba daga mutanen gidan kadaiba harta bayi ma tsangwamar mu sukeyi sede dukda haka akullum Ummi hakuri takebamu tareda bamu kwarin gwiwa nikuma as her first child I never want to create a problem for her,I was too young to bear all that that’s why I became like dumb nakoma komaima akayi mani hakuri nakeyi dukda zuciyata na Kuna,komai ma aka fada akaina karba nike hannu bibbiyu tunda konace bani nayi ba inada wanda zai tsayamin ne?…
Bani dashi, I’ve no one except my Mother and two young Sisters, Sulaiman danake samun sauki agurinshi ma ba abari muhadu because daga karshema sawa tayi aka fitar dashi karatu kasar waje….. sekuma Mallam Hudu wanda I most say he’s indeed a very honest person shi ne meyima Ummi bayi ah lambunta tun everything is normal sabida ita mutum ce meson harka da kayan shuke shuke sabida irin savonsu yasa shi yarda da’ita dukda sharri da akayi mata shi of all people trust her and he helped us alot don koda Ummi tafara rashin lafiya he was the one that stand by us hakanan yarike amanan da Ummi tabashi na dukiyanta baki daya wanda mukanmu bamusan dashi ba and to tell you the truth Mallam Hudu mutum ne dabazan iya manta alkhairi dayayi min ba and we can never repay him no matter how we try”……….
Hakadai rayuwa tacigaba kannenna basuyi wani karatun kirkiba sabida andauke su matsayin bayine kullum sunacikin yima yayinsu najini aiki ah matsayinsu na bayinsu ga rashin lafiyar Ummi da bashida ranar warkewa ahakadai nasamu nake zuwa makaranta and I overlooked all abubuwan da mutane keyimin dukda kowa kyama na yakeyi,koya bayason ganina ah guri andaukeni kaman wani annoba daya shigo gari,ansha cewa nayi sata wanda bnsan daga ina yafito ba,hakanan ansha cewa na lalata ya’yan mutane wanda ni bansan anyiba but I always take the blame sabida azauna lafiya but all of a sudden,alokacin daban tsanmaci samun farin ciki ba Sulaiman yadawo daga school,he stood by me even though his mother is against it,he even went to Indonesia sabida yadauko Dad my father’s Brother sabida yagyara komai and alhamdulillah with Allah’s help I’m able to smile again,don tunda Dad yadawo cikin rayuwarmu komai yafara tafiya daidai I cannot thank him enough but I just want him and Sulaiman to know that they’ve played a very important role in my life and bazan taba mantawa da hakan ba,Dan numfasawa yayi sannan yace then,finally I’ve to introduce you to Talatu wanda itace ta hannun daman Magajiya,she knows Magajiya better than anyone sannan duk wani abu dayafaru tana sane dashi kuma ita dakanta tabukaci xata tona asiri after long years now…………
Talatu dake can gefe tana hawayen tausayin Almustapha wanda ba’ita kadai tazubda kwallah ba da jin yanda yake fadan pains din dasukayi going through dukdama ita tafi kowa sanin abubuwan dayafaru din hakanan da hadin bakinta akayi komai……..
Saifullahi da jikinshi yayi sanyi hakanan yanajin tausayin Almustapha na ratsa shi yace”Talatun tana kusa?”…..
Asma’u ne tatashi ahankali tayi inda Talatun take kafin tace tazota jiki ah sanyaye takarasa gurin yayinda mai daukan rahoton yace”Bismillah kikaraso mana”…….
Karasawa tayi ahankali kafin akabata kujera tazauna…..
STORY CONTINUES BELOW
Kallonta Saifullah yayi sannan yace”to kozaki iya fada mana sunanki malama?’……
Gyada masa kai tayi sannan tace sunana Talatu kamar yanda Yarima yasanar dakai…..
Jinjina kai Saifullah yayi sannan yace”to Masha Allah malama Talatu kaman yanda Yarima yafada cewa kinsan dukwani sirri na munafurce munafurcen masarautar nan inba bu damuwa munason kifadi duk wani abu dakikasani da bakinki”…
Dan gyada Kai Talatu tayi kafin dakyar tayi karfin halin composing kanta sannan tafara magana, nidai nakansance ta hannun damar Magajiya hakanan nakasance baiwarta me kulada ita tun ma kafin ta auri Mai Martaba don ina iyacemaka babu wanda yakaini saninta sannan tsakanina da Allah nikeson don ko yau inajin sonta araina shiyasa nadauki wannan matakin,dan numfasawa tayi sannan tacigaba”Magajiya mutum ce meson kanta dayawa hakanan mutum ce da intanason abu tosai ta cinma shi koda kuwa tawani hanyane”……..
Saifullahi da mamaki yace”takowani hanya fa kikace malama Talatu?”….
Gyada masa kai tayi sannan takarada”tabbas tako wani hanya, wanda zai iya kashe mutum don ya cinma burinsa miye bazaiyi ba hakanan wanda sallah ma bata dameshiba ba bare kyautata addininsa miyene bazaiyiba sannan wanda beyarda da Allah ba yafi fifita aikin boka miyene bazaiyiba Mallam?”, Talatu tayima Saifullah tambayar murya ah raunane shikuwa jinjina kai yayi ahankali yayinda yadan gyara zama tareda cewa”tofa nidai malama Talatu maganarki gaskiyace amma dai kinsani ah duhu dukdama Ina kyautata zato bani kadai akasa ah duhun ba harda dumbin jama’an dasuke kallon wannan shiri namu”……….
Murmushin dayafi kuka ciwo Talatu tayi kafin tace”zan warware muku komai,abunda nike nufi anan shine dukwani munafurci ah masarautar nan itace silarshi hakanan duk abunda Yarima yafada gaskiyane sunsha wahala sannan Magajiya ce sila,itace ta cinna gobara agidan tsohon Galadima da har yau ba asan miye silar tashin wuta ah gidanshi ba lallai kuyarda daniba Amma wannan shine gaskiyar al’amari”……
Saifullahi da abun yafara fin karfinshi yace topha,wane Galadima kuma donnidai banmasan da labarinba Hajiya Muniba dake can gefe tace”I’m a witness Talatu,ni yar Galadima ce nikadaice wutan nan bekama da ba I was able to escape but still haryau inaganin sanda Magajiya takashe dangina ah idanuna”……..
Dukda Talatu tayi mamakin zancen Hajiya Muniban amma sebata ce komai ba ahankali Hajiya Muniba takaraso tafadi yanda abun yafaru wanda hakan yasake tabbatar ma Talatu Hajiya Munibance don ko alokacin Magajiya tafada mata yanda sukayi da Muniba din sannan tace mata zatadauki mataki daman hakan Hajiya Muniba takarada harda waziri wanda yadade yanasane da laifin da yarshi tayi amma yaboyema duniya baki daya……
Bakaramin mamakine yakama kowa ba na irin selfishness na Magajiya,harma wasu nafadin anya mutum ce nidai araina nace kadan ma kukaji.haka Talatu tacigaba da bayani,”itace silar rabuwar Mai Martaba da Aunty Khairiya sabida alokacin tayi tayi tarabasu takasa setayi anfani da bin boka yayi mata aiki sannan tanemo hayan kato tasashi yakwanta kusa da Khairiya tana bacci yanda in Mai Martaba yazo zece cutansa takeyi hakan kuwa akayi don tabbas tariga tagusar da hankalinshi ga tuna irin yardarda sukayi da juna daganan tasa aka koresu ah masarautar hakanma be ishetaba don itace silar sa Almustapha yafara shan giya,itace silar rashin gama karatun shi dawuri hakanan itace silar shanyewar jiki da Mahaifiyar sa tayi na tsawon shekaru masu dama,haka Talatu tadinga tone tone tanayin bayanin komai dallah dallah babu abunda jama’a keyi se salallami tareda mamakin abubuwan da Magajiya tayi hakanan aka kira Mallam Audu yabada shaidan kaji,tayi Maganar wahalar da bayima suka sha awurinta damakuma yanda in anbada kudin project take zuga Galadima su raba kudin ah tsakaninsu batareda sunyi aiki mekyau ba wanda hakan bakaramin wanke Mai Martaba yayi ba hakanan suka Kara ganin girman bawan Allahn kafin daga karshe Talatu tadago layoyi guda uku dataciro tanuna musu sannan tafada musu yanda sukayi da Asma’u dayanda tayi mata alkawarin ciro layoyin to alhamdulillahi yau Allah yabata iko dukdama batasani ba ko Asma’u tayi succeeding wurin cire layoyin da yake bangaren Mai Martaba dukdama bata tabo bangaren rapping bayi da akayi tayiba kamar yanda tayi ma Almustapha alkawari hakanan Asma’u na mamakin rashin ganin bayin datayi agurin …………
Kafin daga karshe tace,wayannan sune abubuwan danasani sannan takarada”uwargijiyata nasan kina kallona yanzu sannan kina iyatunanin abunda nayi nayaudareki ne kokuma naci amanarki amma dukda haka inason kisani cewa ni Talatu mai kaunar kice har kullum shiyasa nadauki wannan matakin,nariga nagane gaskiya hakanan nagane abubuwan damukayi tayi bashine hanya madaidai ciya ba,natuba uwargijiyata hakanan nakoma ga Allah shiyasa nake fatan kema bayan ganin abunda nayi yau Allah yasa kema kigane gaskiya kikuma karbi hukuncin ki kamar yanda nima zankarbi nawa”, takarashe maganar tana kuka me tsuma zuciya kafin tatashi takoma gefe………..
STORY CONTINUES BELOW
Dukwanda yake kallon shirin ayau din seda ya zubdama Almustapha da yan uwanshi kwallah, it’s a very heart touching story da duk Mai inani inyaji seyaji wani iri aransa, Saifullah da jikinshi yayi sanyi yadubi Almustapha dake zaune gefenshi cikeda tausayinshi dakyar yace”indeed!you people have gone through alot”…….
Murmushi kawai Almustapha yayi sannan yace”and yazama tarihi yanzu ba”…….
Dafa kafadanshi Saifullah yayi in a comforting manner”still,I must say you’re a very strong Man sannan maganar ka gaskiya ne mahakurci mawadaci and surely everything that has a begining most surely has an end kuma ina tabbatar maka dacewa wannan labarin naka zaizama darasi ga mutane da dama na cewa bawai komaine da mutane suka fada akan mutum zai iya zama gaskiya ba,we all have hidden secrets but our people nowadays are so judgemental basuga abuda idanunsuba amma they always seems to claim they know,Allah dai yasa mudace kawai………
Amin cewar Almustapha din kafin Saifullah yadubi Asma’u dake gefen Almustapha yace”I’ve one last question please”…….
Dariya Almustapha yayi sannan yace”go ahead please”…….
Murmushi Saifullah yayi sannan yace”dubada irin yanda mukaji labarin ka dake tattare da dunbin darusa dakuma abubuwan tausayi aciki se nake mamakin wani abu kwara daya”……
Gyada kai Almustapha yayi kafin Saifullah yacigaba da magana”daga yanayin labarinka dakuma abubuwan dasuka faru dakai abaya inada tabbacin it must be difficult for any parents sudauki diyar su subaka aurenta awancan lokacin,shiyasa I’m very curious now ganinka danayi da very innocent and sweet Charming wife dinka and despite all the circumstances she’s even bold enough to make you courageous today,to tell you the truth I’m amaized by that”……
Murmushi Almustapha yayi sannan yadubi Asma’u kafin yace”gaskiya ne kamar yanda kafada it was very difficult for her and her family,haduwarmu was merely a coincidence but it was unfortunate for her that she was dragged into my problems wanda har hakan yasa iyayenta suka juyamata baya even though she’s innocent hakanan kuma suke ganinta amatsayin yarinyar da ta zubar da mutuncinta sakamakon hada hanya dani datayi sabida halayena da ake fada,anhanata karatun ta adalilina hakanan anrabata da farin ciki agidansu for quite sometime dukda Magajiya was behind it kamar yanda Talatu tafada I still can’t deny the fact that nice silan komai because dabata hadu dani ba bazama taba going through all this ba,I still feel bad for her that she’s accused of something she has not done but believe me”Asma’u is like an angel that came from the sky infact tunda tashigo rayuwa na nake ganin changes, she’s the first person dabata kyamace ba dukdama farkon haduwarmu I was in a bad state, she’s the first person datafara jin tausayina,she’s the first person dabata kyamace niba hakanan she always stand by me no matter what,she gave me courage all the time,she make me believe that I can be the person I want to be and she always make sure that I and my family are alright”, yakarashe maganar yana kallonta so lovingly itadai Asma’u she’s so speechless and out of words se hawaye, murmushi yasakarmata sannan yakalli Saifullah yana”to tell you the truth after my family members banida kamarta,she’s a precious jewel,a very rare precious gem that i want to treasure forever if possible”,sannan yasake maida kan shi gareta yana kallon cikin idanunta yace…
“Asma’u”….
Dagowa tayi ahankali tana kallonshi Itama hakanan takasa amsa kiran sunanta dayayi se kallonshi data tsayayi kamar wata sokuwa,su Saifullahi kuma se kallon ikon Allah sukeyi…..
Riko hannunta Almustapha yayi sannan yace”i just want you to know that you’re one of the most important people in my life and you’ve played a very important role in my life to which is why I’m who I’m today”, yakarashe maganar ahankali sannan in a very cool voice yakuma cewa”thank you Miss Taciturn”…
Asma’u jitayi kaman mafarki takeyi hakanan take ganin kaman ba Almustaphan data sani bane ba cikin sauri take kokarin cire hannunta cikin nashi amma yaki saki sema tashi dayayi yana rikeda hannunta suka fice agurin Allah yagani ayanzukam shima yagaji da amsa wasu tambayoyinne and he has to face her too,suyi magana ta fahimtar juna….
Da murmushi Saifullah yabisu da kallo kafin yace “to masu kallon mu nanfa muka kawo karshen shirin namu da Yarima Almustapha wanda yabaku tarihin rayuwar sa dake dauke da dumbin al ajabi dadama hakanan inafatan kowanne dake cikin ku yau gamsu yakuma samu amsar duk wata tambaya dayajima yanason samun amsarta daga gareshi, sannan daga karshe inason inneme alfarma daga gareku na muyi addu’a Allah yarabu da mutane irin Magajiya arayuwanmu itakuma da Allah yatoni asirinta ayau Allah yasa karshenta kenan hakanan muna fatan kada Allah yabata daman sake cutar wani daga…..
karshe ni Saifullahi Ahmad nakecewa Allah ubangiji yabar kauna tsakanin Yarima Almustapha dakuma Asma’u hakanan inafatan Mai Martaba da Ummi will dissolve their differences sekuma Asma’u Itama inaso in ari bakinta inci mata albasa nabatun iyayenta,I hope she’ll be forgiven today tunda yaukam nasan kunsan gaskiyar komai,semun sake haduwa awani shirin kuma indarai da lafiya………….
Hajiya Hajja dake gaban Tvn Asiya tana sharban kuka tace”don uwarki meyace da turanci akan jikata?”…….
Asiya dake sharban kuka Itama batasan sanda tayi dariya ba,sakan baki Hajja tayi tana “kaji min shegiyar yarinya inatambayar ki kinamin dariya”……
“kiyi hakuri Hajja cewa yayi bayan duwannan labarin da aka bayar yanafatan suku dasu Abba zakuyafema Asma’u kumanta abunda yafaru abaya”, Asiya takarashe maganar tareda karacewa inaganin besan cewa komai normal tsakanin Asma’u dasu Abba ba tunda aiyajima da yacemata……..
Hararanta Hajja tayi tana”kaji Yar banza to ai da Irina yake,ni ai bance nayafemata bako”..
Asiya dae dariya nacinta amma seta daure tace”to yanzukam zaki yafemata ko Hajja?”…..
Hajja Jan kasan zaninta tayi ahankali tana sharar kwallah sannan tace”nayafemata ma wallahi,nikam nayafemata Allah yayimata albarka, mijinki nadawowa ma kisanardashi nikam gobe da sassafe zantafi Zaria gurin jikata yanzuma don dare yafarayine ba lallai insamu motaba”…… 1
STORY CONTINUES BELOW
“To Hajja Allah yakaimu goben nima inason inje inga Yar uwata daman inya bari basai mutafi tareba?”
Gyada mata Kai kawai Hajja tayi batareda takuma cewa komai ba yayinda zuciyarta ke daukeda dumbin nadama kala kala na abubuwan da tayima jikokinta wanda basuyi mata laifin tsayeba bare nazaune………….
Bangaren Mai Martaba kuwa tun ba agama shirin ba yasaki jiki yafadi tsabar abubuwan daya rinka ji suna fitowa daga bakin Talatun,he was so very shocked hakanan yakasa yarda cewa Magajiya stoop so low like this, Ya’yan sa nacikinsa tamaida bayi and treated them that way for so many ways without him knowing,lallai shidin mutum ne dakawai tafiya yakeyi batareda yasan meke wakana cikin rayuwarsa ba dakyar su Dad suka taimaka mishi wurin shigar dashi daki sannan aka shiga kiran number likita cikin gaggawa…….
Talatu kuwa tunda aka gama labaran take tsaye cikin parlourn seda Hajiya Muniba tadubeta da tausaya sannan tacemata su tafi ahankali tabi bayanta dukda tariga da tasadaukar she must be punished for all her deeds kuma ita hakanma takeso because only then she’ll feel at ease……..
Koda suka fito ah fadan arba sukayi da motocin sojoji da na polisawa sunfi goma yayinda dukansu ke sanye da kayan aikinsa……..
Bakaramin faduwa gaban Talatu yayi ba wani daga cikin polisawan ne yace”itace,ta bada labari and we’re asked to arrest her too”,daganan Mata biyu daga cikin polisawan suka zo suka sama Talatu sukayi cikin motar da’ita dukda Hajiya Muniba na kokarin cemasu subari amma sukaki sema cemata dasukayi aikinsu sukeyi………
Dede lokacin kuma Dad yafito sakamakon zuwa da akayi akasamoshi akasanar dashi isowan matakan tsaron….
Musabaha yayi da ogansu kafin yace”thanks for coming but,I think this’s a family issue we can address it as you can see we we’ve all the facilities that can help us gurin punishing culprit din”……..
Murmushi ogan yayi sannan yace”we were sent by the commissioner of police na kaduna state shiyasamu muzo muyi arresting matarnan and Magajiya kuma shikanshi yasan kuna guards ai but this’s a public issue not a family one,yayi affecting mutane da dama so she has to be punshment”…..
Babu yanda Dad ya’iya haka yabarsu donyin yanda akasakasu daman tunkan ma afara labaran Dad yasa ah tare duk wani possible hanyar escaping acikin masarautar sabida yasan Magajiya can is so cunning,she might think of escaping to segashi yanzuma sojoji sun karu gashi dare yafarayi…………
Gudu lantana takeyi kaman wanda ranta zaifita ba’ita ta tsaya ba seda ta’isa bangaren Magajiya din,batada wani buri dayawuce taje tafada ma Zaliha da Magajiya halin da ake ciki don kuwa carab ah kunnenta taji maganar da Dad din keyi da sojoji da polisawan…..
Hakin da takeyi ne yasaka Zaliha daketa faman jijjiga Magajiya tana rokonta da ta gudu juyowa tayi tadubi lantana din,cikin sauri lantana tace”Gimbiya sojoji,polisawa dakuma dogarayen masarautar nan baki daya neman Magajiya sukeson farayi ayanzu and inada tabbacin nan zasu fara zuwa……
Zaliha da take ah rude tadora hannu aka tana”na shiga uku na gashi Mama tunda taga fuskar Talatu ah Tvn nan takasa motsi ko magana”…….
Lantana data saki kuka lokaci guda tashiga jijjiga Magajiya dake tsaye kaman gunki tana”uwargijiyata ki yi magana don Allah,yanzu zasu zo neman ki gwanda kigudu don wallahi insuka barki daraima bazaki ganuba”……..
Wani kallo Magajiya tayima lantana wanda yasakata sakinta yayinda Zaliha takarbeta tana Mama, Mama kigudu don Allah koso kike su kashe ki?……
Wani irin dariya Magajiya ta saki da sannan tadaga hannunta tashake wuyar Zaliha tana”don ubanki babu wanda ya’isa yakashe koda kuwa shiwayene”…….
Zaliha batasan sanda tafara kuka ba tana kiyi hakuri don Allah Mama,wasa nakeyi babu wanda zai kasheki wallahi”,tayi maganar tana kokarin cire hannun Magajiya dake wuyarta amma takasa da magiya da rokon su Laure da lantana dakyar Magajiya tasaki Zaliha tana dariya kamar wata mahaukaciya……..
Numfashi ma dakyar Zaliha tadingayi kafin tasamu ya daidaita jin tafara jin footsteps din sojoji da dogarayen yasata saketasowa tana rokon Magajiyan data gudu still Magajiya na dariya tace”bazan guduba harsaina cinma burina”…..
Kuka Zaliha tasakar mata tana rokonta, it’s the matter of her life she cannot stand seeing her dying kafin tayarda dukdama seda tace…..
“sekinyimin alkawarin Zaki karasa abunda nakasa karasawa”……..
Zaliha da take ganin kamar Magajiya tafara samun tabin kwakwalwa tace”namiki alkawari mama amma yanzudai kigudu don Allah”……
Lantana ne tace to bari infara lekowa in akwai hanyar fita, gyada mata kai sukayi duka yayinda tafice batajima ba segata tadawo tana haki,wallahi bangaren nan azagaye yake matakan tsaro tako Ina”……
Dafe kirji Zaliha tayi haka Magajiyarma don seyanzu taji abun yafara damunta sosai, she really want escape bakaramin rudewa sukayiba dukansu Laure dake gefene tace”akwai tsohuwar hanyar dana sani kuma ta dakin zamu iya bi semu fice batareda kowa yasani ba”……..
Kallonta Magajiya tayi irin can she trust her dinnan?….
Gyada mata Kai kawai Laure tayi kafin takama hannun Magajiya din suka fara gudu gani tayi lauren ta kaita bandakin ta dake cikin dakin sannan tace tataimaka mata su daga wani katon akwati,haka suka daga shi dakyar da mamaki Magajiya ke ganin gurin kaman hole hakanan tana mamakin ya akayi Laure tasan gurin bayan ita da dakinta nema amma batasani ba…. …..
Laure ne tafara dirka ciki kafin tamikoma Magajiya hannunta alamar tashigo babu musu tashiga gurin kafin Lauren takunna torch din wayar hannunta tana”inmuka bi hanyar nan harwani kauye zekaimu batareda ankama muba”……….
Magajiya na shirin tambayar Laure ya akayi tasan gurin amma bata bata dama ba sema kama hannunta dasuka cigaba da gudu kamar ba gobe………
*aradu yau hannuna har ciwo yakeyi tsabar gajiyan typing,kusamin albarka please*
4
*Topha nimadai Laure taban mamaki yau,why is she helping Magajiya to escape?, kucigaba da bin Zeeneert don jin yazata kasance*……Sosai sojoji da dogaraye sukashiga bangaren Magajiya din batareda neman iziniba hakanan suka shiga dube dube harsuka iso kan Zaliha da Lantana dake tsaye jikinsu na bari wani irin harara daya daga cikin sojojin yayima Zaliha kafin yace”Ina Magajiya?”….. +
Bakinta narawa tace bansaniba wlhy……
Wani irin tsawa yadaka musu wanda yasa lantana sakin fitsari ah take batareda ta shiryaba Zaliha kuwa tsabar rudani batasan sanda tanuna musu hanyar dakin Magajiya ba sabida ganinsu da tayi da bindigogi gani take mistake kadan zatayi su rabata rayuwarta….
Haka wasu daga cikin rundunar tasu sukayi dakin Magajiya din sukuma sukasamu suka fice da gudu itada Lantana……….
Haka sojojin suka dinga dube dube basu samu wani trace dintaba seda waninsu yashiga bandaki seyaga anmatsar da wani abu gefe and akwae rami gurin dukdama anrufe dakarfi yayi calling attention din wasu daga cikinsu koda sukazo bude gurin sukayi, bakaramin mamaki bane yakamasu ganin yanda ramin yake daya sojan ne yashiga ciki yana karema gurin kallo kafin yace…
“kilan tanan ta gudu,we might be able to catch her inmukabi”……
Suna shirin amsa masa ne sukaji muryar mace tayi masu magana daga dakin Magajiya din….
Dasauri suka juya suna kallonta…..
****
Sunfi minti talatin suna wannan uban gudun gabadayansu sungaji jikinsu yayi laushi amma dayake neman tsira Magajiya keyi bata wani tsaya rakiba gani tayi Lauren ta tsaya ah dede wani spot sannan tadaga torchlight din dake hannunta tadan haska saman gurin ganin irin kofar da suka shiga suka gudo tayi wanda yake very round ahankali Laure tasa hannunta ta bude abun wanda hakan yasa sukaji wani irin fresh air yashigo musu dukda ma babu haske kasancewar dare be, dubanta Laure tayi sannan tace tanan zamu fita uwargijiyata…….
Magajiya daketa zufa haryanzu ta gyada mata don itakam dakyar ma take magana tsabar rudani kama abun Laure tayi sannan tafara fita seda tazama stable sannan tahaska inda Magajiyan take tamika mata hannu harta fito da’ita……
Haki take sosai tsabar gajiya sede atleast she feel safe right now tunda tayi nisa da masarautar kamar yanda Lauren tafada mata dazu,zama tayi tana ajiyar zuciya agurin har laure tarufe gurin da kwado sannan tadan ja da baya…….
Kankace Mai hasken powerful torchlights ne suka haske gurin baki daya cikeda rikida Magajiya ta dago don ganin wannan ubanhasken daya zagayeta daga ina yafito sede da mamakinta sojoji da polisawa ne suka zagayeta hakanan sunsata ah tsakiya arude tadago tana kallon Laure with a questioning look ………… 1
Sede da mamakin ta gani tayi Lauren na tsaye gefen wata Mata datake sanye cikin kaya na alfarma,matar da ayan kwanakin nan take mata kallon kishiryata,amaryar Mai Martaba dayake ikirarin ya aure hakanan matar da ayau din taji tanacewa ita ce Muniba,her long lost friend ko enemy ne ma zatace dan babu wanda Muniban batayi playing role dinsa ba acikin biyun……..
Murmushi Hajiya Muniba tayi tana”nagode Laure, you’re my loyal servant and you’ll always be”…….
Dan rusunawa Lauren tayi alamar godiya sannan tace…
“Karki damu Ranki shidade indai nine akullum banida burin daya wuce inzauna tareda mai gaskiya shiyasa bana tunanin zantaba danasanin kasancewata baiwarki,kamar yanda muka tsara ga Magajiya nan nakawo miki ita inda bazata iya guduwa ba hakanan inkinada wani aiki dazanyi miki ayanzu kisanar dani ni maiyi biki biyayya ne akowani lokaci”…….
Dan shafa kanta Hajiya Muniba tayi sannan tace…
“Allah yayi maki albarka,kije kihuta abangarena innashigo zamuyi magana”
Amin ya rabbi shine abunda Laure tafadi kafin tayi wucewarta batareda tasake duban inda Magajiyan ke zauneba……..
STORY CONTINUES BELOW
Magajiya dake zaune gurin tana kallon Hajiya Muniba dumbfounded tsabar betrayal dataga anyi mata,mehakan ke nufi?…
Kenan Laure yar dakin Muniba ne komi,dondai daga ganin yanda suke magana tana da tabbacin sunada deep connection sannan hakan yanuna sunjima da sanin juna itakam yazatayi da rayuwarta yau asirinta yatonu but she know that she’s very strong,she can never give up so easily cikin karfin nama tajuya don sake durkawa cikin ramin dasuka fito sede da mamakin gurin agarke yake da kwado mamakine yakamata don bata masan sanda Lauren ta rufeba tsabar hankalinta baya jikinta……
Hajiya Muniba ne tace”you cannot escape anymore Magajiya, it’s better you just surrender yourself”…….
Wani irin kallo Magajiyan tayi mata sannan tace…
“I’m not a coward like you dazanyi surrendering kaina, I’m not a coward like you dazanzo in disguise inazama tareda enemy na because I cannot call you a long lost friend but an enemy that came back to ruin my life dana jima da gyarashi, you’re a betrayer Muniba and you’ll always be”…….
Murmushin takaici Hajiya Muniba tayi sannan takaraso gaban Magajiya din tana”to you I’m a betrayer but in my eyes and to the world you’re the betrayer and I assure you,you’ll get punished for all your deeds”,cewar Hajiya Muniba din kafin tajuya tadubi sojojin tace”Arrest her,lock her up in the cell harzuwa lokacin da Mai Martaba zaisamu sauki only then za afara case dinta though you’ve to make sure she suffers every blessed day”,tayi maganar tareda barin gurin Magajiya ihu takeyi tana “you’ll never get away with what you just did, I’ll take revenge bazan taba bari kiyi winning ba Muniba I assure you that”……
Itadai Hajiya Muniba kojuyowa batayiba barema takalli Magajiya din abunda tasani shine she’ll be punished not only in the palace but har ah wurin hukuman Kaduna state ma hakanan tana jin tausayin Magajiya in Mai Martaba yasamu sauki donshi mutum ne mai zuciya hakanan bayason betrayal……
Haka sojojin suka sa mata handcuffs aka sakata ah motar su za’a tafi da’ita tanata surutai itakadai………
Koda motocin suka isa bakin katuwar gate din masarautar ah garkame take da mamaki driver din motar dake gaba yashiga danna horn rai bace don ah tunanin shi ai yakamata ace guards din sunga tahowar motocinsu to miya hanasu budewa?…
Yana cikin wannan tunanin ne ayayinda yake danna horn din daya daga cikin dogarayen yazo da gudu yana”bazai yuyu kufita bafa”…..
Sojan dayake driving ranshi abace besan sanda yafito ah motar ba tareda cewa….
“miyasa bazamu fitaba,will you open the damn gate my friend?”…….
Sunkuyar dakai dogarin yayi sannan yace”Dokane daga Yarima Almustapha Yayan Mai Martaba(dayawa daga cikin ma aikatan masarautar haryanzu sukan kira Dad da Yarima wanda daman sunan yajima da zama abakinsu tunkafin yabar gida Nigeria)….
Sabida yanda dumbin mutane da suke waje gashi sundage wai se afito musu da Magajiya,suna rike da sanduna da duwatsu kaga muddin kuka fita ba’ita kadai ba harkuma babu mai iya tsira darai inba wani ikon Allah ba”……….
Dan ajiyar zuciya sojan yayi sannan yajuya ga sojojin da suka sauko daga motar tsabar takaici suma,bayani yayi masu da turanci sabida wanda baswajin Hausan amma mi gabadayan su se suka fara korafin anraina matsayinsu inbahakaba miyasa Dad zaice bazasu fitaba in talakawa sundage saisun shigo ai dai basu isa su hanasu wucewaba tunda su matakan tsarone……
Wannan dalilin yasa Dogarin yace toshikenan tunda haka sukace amma su bazasu bude kofa ba harsai anbasu izini daga cikin masarauta don haka yace musu bariyaje yafada ma Dad in anbada izini zaizo yasanar dasu….
Babu yanda suka iya haka suka tsatsaya sunajiran amsa daga Dad din donsuma sunsan kowace masarauta da shegen tsari suke haka kuma baswa canza tsarinsu batareda sunyi la’akari da wani muhimmin abu ba…..
Sallama Dogarin yayi ah parlourn Mai Martaba,Dad daketasafa da marwa cikun parlourn hakanan yana kallon TVn yana ganin yanda dumbin jama’a suka taru ah waje wanda yanada tabbacin yawancin talakawan garine sukayi gungumi suka taho dukda kuwa darene donma akwai security light ah street din masarautar tako’ina Wanda hakan yaba da daman haska gurin baki daya yayinda wasunsu ke daukeda duwatsu dakuma sanduna suna ihun Kiran Magajiya,Magajiya,sudai saidai abasu Magajiya,they must seek for revenge wanda tundazu ake abu daya dasu anyi anyi akoresu amma ina harcemusu akayi huku zatadau mataki akanta amma still sunki hakura gashidai mutane ne da ko guards din masarautar baki daya bazasu iya korararsuba wannan dalilin yasa yace ah rufe gate din baki dayanta sannan kada abari kowa yashigo,shikam mamaki ma yakeyi tayaya har yan daukan rahoton suke iya video taping dinsu acikin wannan halin(Niko nace Dad bakasan jarabar aikin yan jarida,masu aiki ah gidan radio da dai sauransu bane shiyasa)……………
Jin sallamar da Dogarin ne yasashi juyowa cikin lumana sannan ya amsa, zubewa dogarin yayi akasa yana mika gaisuwa kafin yafada mishi yanda sukayi da sojojin….
Dan tsaki Dad yayi sannan yace”they’re being stubborn inaga basusan yanda wajen yake bane shiyasa,I don’t want to take risk ba Magajiya bane kadai acikin motar,ga Wazirin da akayi arresting dinshi for hidden the Truth about his Daughter and that slave too gakuma su sojojin they might get injured,don mutanen nan dakake gani baswa ji baswa gani ah yanzu”…….
Cikeda damuwa Dogarin yace…..
“namusu bayani nima ai amma saicewa sukayi anraina iyawarsu ne shiyasa,suda suke matakan tsaro waya isa yajadasu”……..
Da mamaki Dad yace”Oh hakama sukace?”…
Gyada kai Dogarin yayi sannan Dad yace”kuje kubude musu gate din kawai to”…..
“Mutanen fa na dabda bakin gate din”,cewar dogarin cikeda tsoro cikin tsawa Dad yace”Do as I say”,dan yasan sojojin nan inba ayi yanda suke soba suna iya creating musu wani problems din yanzu tahanyar tayar musu da hankali….
Jiki na bari Dogarin yafice don aikatar da abunda Dad din yace yana isa bakin gate din yace musu za abude musu gate din yanzu haka suka koma cikin motocin yayinda shikuma yakarasa yana fadama sauran abokan aikinshi sakon Dad wanda harma ayanzun sunajin yanda mutanen keta ihu awaje,haka suka cire gangamemiya sakatan da padlock din sannan suka wangale gate din tunkan sukarasa wangalewa har wasu sunfara shigowa hakanan wanda suke baya suka shiga jife jifen duwatsu bakaramin mamakin dumbin mutanen sojojin sukayiba because they’re even out of control,baza a iya controlling dinsuba jifa sukeyi sosae wanda har glasses na motan gaban sunfara fashewa hakanan gabaki dayansu suka maida attention dinsu kan motar gaban ganin akwai mutum abaya wanda andaure hannunshi da ankwa yasasu tunanin Magajiya ne dakyar sojojinma suka samu suka tsira suka fice ah motar don abun yafi karfinsu,mutanen kuwa seda sukayima motar daga daga sannan hankalinsu yakwanta ahakan ma suka dinga se anfito da ita sunganta sun tabbatar ta lillisu tukunnan,hakanan suka shiga kokarin fito dashi,abunda basu saniba shine Waziri ne awannan motar Magajiya na dayan motan tunda taga sunshigo din sunfara jefe jefe ta sunkuya taboye ah ta kasan seats dukda haka kuwa seda tasha dutsuna don wulli sukeyi tako’ina akeyi hakanan bakaramin raununnuka taji ba ajikinta amma dukda haka batayi giving up ba …………
STORY CONTINUES BELOW
***
Almustapha da tunda yakama hannun Asma’u suka fice ah fadan Mai martaba side dinsu yayi da’ita batareda suncema juna uffan ba harsuka iso parlourn su sede da mamaki samun Ummi sukayi zaune tana kuka yayinda Mom keta kokarin lallashin ta………
Cikeda damuwa suka karasa garesu don Asma’u lokaci guda tamanta da tata damuwar ganin situation din Ummi din,seyanzu takejin miyasa tatafi tabar side dinta bayan tasan something yana iya faruwa batasan sanda tarungumi Ummin ba tana tapping bayanta….
“Ummi stop crying please,inkina kuka mukuma wazai rarrashemu,inkika tada hankalinki ta’ina su Afiya zasu samu courage din manta abubuwan da suka faru abaya?”…
dakyar Ummi ta’iya tsagaita kukan nata tareda dagowa ta kalli Asma’u din,itakanta tasan Almustapha bazai tabayin dacen mata irin Asma’u ba, she’s a blessing to the family and nothing can change that,abunda batasaniba kukan da Ummi keyi harda na farin cikin sabon rayuwar da suka tsinci kansu acine dukdama tatuna baya,takuma tuna hardships din dasukayi going through hakanan kuma take gode ma Allah dayayi solving problems dinsu cikin lumana dakuma ikonsa,inbahaka ba waya tsanmacin zasu sakejin dadi ah rayuwarsu,waye ya tsanmaci Almustapha zai taba samun wannan damar daya samu ayanzu?….
Lallai babu abunda yafi Allah,for her,her family means everything to her and alhamdulillah her children are very Happy and most importantly her Son is blessed with the best wife she could ever ask for batada abuncewa sede alhamdulillahi bangaren Mai Martaba kuma tanayi mashi fatan alkhairi everyone has his own destiny,even though gaskiya tafiyo yau,may be they were never meant to be together forever tunda dai yayi aurenshi and tanada tabbacin Hajiya Muniba will try her very best to take very good care of him Itama kuma nata ya’yan sun isheta rayuwa so far as she’s around them………
Shafa kan Asma’u tayi ahankali sannan tace”thank you Daughter because of you my Imam is able to talk his heart out in public,we’re blessed to have you as a family member indeed, Allah yayiwa rayuwarki albarka”…….
Asma’u dake kallon Ummi cikeda sonta tasake fadawa jikinta sede wannan Karan itace tafashe da kukan dakyar Ummin ta rarrasheta Almustapha da Mom dai suna gefe suna kallon ikon Allah seda Asma’un tayi shiru sannan yakaraso ya tsuguna gaban Ummi tareda dan riko hanuna cikeda damuwa yace”Ummi are you okay?”…..
Murmushi Ummi tayi dukda idanunta akwae guntu guntun hawaye sannan tace”do you think I’ll never be okay if your wife is with me?”…….
Batareda yabata ansaba yadaga idanu yadubi Asma’un dake kwance jikin Ummin idanunta sunyi jage jage da hawaye gashi harsunwani kumbura tsabar kukan datasha……..
Turo mishi baki tayi gaba tana…
“Ummi baiyi ko sallan maghrib bafa”……
Zare idanu yayi yana mamakinta wai harma kararshi take kaiwa Ummi sekace itan tayi, ahankali yace”dakike kawo karar nawa ke kinyi ne?”…
Murkuda mai baki yayi batareda tabari Ummi tagani ba don gani take raina mata wayau ma yayi aiyasan bata sallah inba neman magana ba miyasa zaice batayiba Itama abunda batasani ba Almustapha gabadaya yama manta cewa bata sallah……
Ummi ne tace….
“tashi kaje kayi sallah joor don yafadi gaskiya shine kake neman kayi mata sharri ko?”
Murmushi yayi tareda tashi tsaye yayinda aranshi yake fadin….
“To antaba shalelen Ummi yaukuma seyanda akayi dani”……..
Haka yafice don zuwa masallaci yayinda Asma’u tabishi da kallo harya bace mata da gani,jitakeyi kamar kada ranar rabuwarsu tazo dukdama yanzu kam tasan its high time tunda komai yazama normal alhamdulillah ga wayartama se kira yan gidan su ketayi tun sunacan gurin amma taki dauka sabida bayanzu takejin zata iya magana dasuba……
Wuraren bakwai da rabi Almustapha yafito ah masallaci don har Isha seda yayi sannan yafito ah masjid din,jiyayi kaman ana hayaniya ga commotion tako ina wannan dalilin yasashi juyawa ya kalli wani dogari dake shirin fara alwala abakin pampunan dake harabar masallacin yace”ihun mena keji anayi?”……
Cikin sauri Dogarin yazo kusa dashi jin muryar Almustapha dinne don baima fara alwalan ba daman,cikeda ladabi yace”Yarima Allah yaja da tsawon rai mutanen garine suka shigo waisai sundauka muku fansa agurin Magajiya,so suke abasu ita”…
Cikeda damuwa yace”bangane ba,gate din masarautar ba’a rufe take ba daman miyasa aka barsu suka shigo to “……
“Bansani ba wallahi donnidai nasan Yarima Almustapha yace kada abude bansan ya akayi suka bude daga bayaba”,cewar dogarin donshima bawai yasan abunda yafaru bane daga baya cikeda damuwa Almustapha yabar gurin,gurin hayaniyar ya nufa cikin takunshi na kasaita sede cikin sauri wasu dogaraye suka bi bayanshi suna rokonshi kada yaje gurin sabida crowd din yayi yawa suna iya jimasa ciwoma batareda sukansu sun saniba so, it’s better yakoma cikin gida kawai su zasusan yanda zasuyi…..
Cikeda damuwa yace….
“kuje kusamomin loudspeaker”…….
To sukace kafin wasu daga cikin su suka juya don aiwatar da abunda yasaka su yidin yayinda sauran ke tsaye ah bayanshi don yimashi tsaro hakanan batareda ya dubesuba yacanza hanya tafiya yadinga yi har yakai kan wasu dakali wanda daganan yana iya kallon duk abubuwan da mutanen sukeyi ba ajima ba kuwa sega dogarayen sunzo da loudspeaker,karba yayi yana kallon jama’an dake zagayeda motocin sojojin cikin calm voice dinshi yasa loudspeaker din ah bakinshi tareda yin sallama amma ina basuma kulashiba dukda kuwa wasunsu sunji,yayi sallaman yafi saubiyar amma hakan baisa sundaina abunda sukeyiba…………
Cikeda bacin rai yace dakuma muryardabaisan yanada ita ba cikin tsawa yace”Stop,i said all of you should stop!”…….
Kankace mai gurin yayi tsit babu motsin ko mutum daya sema juyowa dasukayi suna ganin bangaren da Almustapha din yake,aikuwa sosai suke ganinshi sakamakon hasken wutan da aka zagaye masarautar dashi baki daya…..
Cikeda bacin rai yace”haka ake daukan fansa,koko ance muku abunda kukeyi din shine daidai?”……..
Adalilin hakan dakukeyi din kuna iya jima junanku ciwo batareda kunsani ba hakanan Kuna iya jima innocent sojoji ciwo suda suke matsayin masu taimakon mu dakuma tsaron aduk lokacin da muke cikin matsala,adalilin mutum daya seku bari mutum dari suji ciwo ah musali?….
Tsakaninku da Allah kunyi mana adalci?…
I’m very sure some of you were here since before maghrib hakanan inada tabbacin cewa most of you bakuyi sallar maghrib ba bare isha da akayita bada jimawaba,inwani yafadi ya mutu anan tawannan dalilin do you think I’ll be able to forgive myself kokuma dawani idanu zeje ya kalli ubangijinmu mahalliccin mu?…..
Nam numfasawa Almustapha yayi sannan yacigaba”indai kunayin hakane don ku burgeni to tell you the truth nibaku burgeni ba infact batamin raima kukayi,I don’t want a situation whereby my people will suffer because of me hakanan ni banason tashin hankali inkuka zauna ah inda kuke inada tabbacin zakuga hukuncin daza ayima mai laifi,dubansu yakumayi sannan yayi folding hands dinshi”in abunda nafada yabata ma wani daga cikin ku rai then, I’m very sorry nina fadi abunda yake raina ne hakanan banason ku cuci kanku tahanyar faranta min indon kunason kuyi repaying dina for accusations dakukayi tayimin ne ah baya to nikam tunba yauba nayafe muku hakanan banrike ku ah raina ba so,Allah ubangiji ya yafe mana baki daya and to tell you the truth I’m very grateful for all your love and support, Almustapha nasonku From the bottom of his heart shiyasa banason abunda zaicuce ku baki daya and finally I request you all to go back home safely insha Allah zamuyi handling komai dakanmu”, yakarashe maganar still both hands dinshi are folded…….
Bakaramin sanyi jikinsu yayi ba da kalaman Almustapha din hakanan sun tabbata gaskiya yake fada musu shiyasa ma suka juya suna fita ah gidan ahankali yayinda suke hailing sunanshi”Yarima Almustapha!”, “Yarima Almustapha!”….
Yana nan tsaye gurin har suka gama ficewa kafin yasa dogarayen da gudu sukayi gurin motocin sojojin inda wasu daga cikin dogarayen duk sunji ciwuwwuka ah jikinsu hakanan sojojin cikin sauri suka shiga taimaka musu yayinda dakyar akasamu aka fito da waziri dake motar farkon gabadaya yayi jina jina dashi don ba karamin duka yashaba,ko motsi bayayi jini ta baki tahanci se zuba yakeyi haka aka dibeshi akayi clinic din masarautar dasauri,haka Talatu da Magajiya ma duk sunji ciwowwuka gwanda Talatun ma ba sosaiba kaman na Magajiya din don ita abunda yahanata guduwa ma kenan cikin crowd dinnan don babu abunda zaisa tazauna tana ganin wahala…….
Daza akaita clinic Almustapha yace baza akaitaba sukaita gidan horo shi likitan yabita can yayi treating dinta he knows how cunning she’s,she might think of escaping and he’ll never let that happen……….
Dukda ciwo da radadin da jikinta keyi hakan behanata wurgama Almustapha harara ba sannan tace”Daman anfada maka I’ll accept any treatment from you ne,nagwammace na mutu da’in karbi taimako daga gurinka,kayi kadan wallahi Dan shegiya”…….
Murmushi kawai Almustapha yayi tareda shrugging shoulder dinshi in an I don’t care manner sannan yadubi dogarayen yace”Do as I say”,kafin yawuce batareda ya kalli ko bangaren da take ba…..
Haka suka kaita gidan horon sannan aka tsagaye gurin da matakan tsaro tako’ina dukdama wasu sojojin dabasuji ciwo ba suntafi da polisawa, wanda sukaji ciwon kuma anyi rushing nasu to clinic din cikin masarautar don basu taimakon gaggawa……
Magajiya se huci take itakadai,wai inda takesa ah hora mutane nan aka kawo ta yau lallai Almustapha yadebo ruwan dafa kanshi she’ll makesure she succeed no matter what,tana cikin tunanin nan ne taji anbude gurin likita ne da wani dogari suka shigo hannunshi dauke da first aid box,wani harara ta watsa musu sannan tace”bana bukatar treatment dinku”…….
Lallaba ta likitan yashigayi amma gabadaya taki seda kokarin bibbige likitan da ankwan hannunta datake shirin yi wannan dalilin yasa yace”shi bazai iyaba koda akaje aka fadama Almustapha cewa yayi subarta kawai,ita tasani”….
Bangaren Mai Martaba yafara zuwa yaduba shi sede haryanzu bai tashiba sakamakon drip da akasaka mishi dakuma allura da akayi mishi na bacci sabida tsoron kada Bp dinshi yakai stage din da ba aso,yajima azaaune gun Mai Martaba din kafin daga karshe yatashi yafice zuciyar shi fal da tunanin halin da Sulaiman yake ciki batareda yayi wata tunani ba yawuce bangarenshi ahankali yatura kofar parlourn bayan several knocks dayayi ba a amsa ba……….
Duhu yagani ah parlourn gawani irin shiru kaman wani graveyard wannan dalilin yasashi kunna hasken wayarshi yanemi switch din wutan ya kunna kan kace me haske ya haskaka koina na harabar parlourn arba yayi da figure din Sulaiman din dake kwance jikin wata kujera ah kasa gabadaya ya dukun kune kanshi kaman wani maraya hakanan Almustapha yadinga jin zuciyar shi na dukan uku uku lokaci guda dakyar ya’iya yakarasa gaban Dan uwannashi tareda zama ah gabanshi gani yayi hawaye nazuba daga idanun Sulaiman din non stop hakan yakara idanunshi yana kallon bangare daya da alama kukan zuci yakeyi don ko sautin kuka bakaji se hawaye daketa ambaliya………
Take Almustapha yaji shima hawayen suntaru ah nashi idanun in a very calm voice yace”I’m sorry Sulaiman”…………Sulaiman da tunda Zaliha tashigo bangaren tagama babatun duniyarnan amma be kulataba daga karshe Itama hakura tayi tawuce daki don ji da nata damuwar…….
Bayan tashiga dakin ne yatashi yakashe wutan parlourn sannan yadawo yakwanta guri daya, gabadaya duniyar tayi mashi zafi dukyanda yaso yadaure beji wani iriba yaka sa,shiwayene dabazaijima mahaifiyar shi takaicin abubuwan da tayiba,shiwayene dabazai ji zafin wahalar dazata shigaba acikin zuciyar shi, she’s his Mother no matter what hakanan tadauki cikin shi for 9months and the most annoying thing she’s doing all this to make him powerful dukdama yasan tanayine for her own interest and benefits,jiyake inama inama,inama ana iya canza identity,inama ana iya canza mahaifiya da wallahi babu abunda zai hanashi canza Magajiya tunda jimawa……..
Hakanan yananan kwance ah parlourn har Sumayya tayita kiran layin shi amma baidaukaba,takira times without number amma yaki dauka can yaji Afiya tashigo tana waya da Sumayya din,jiyayi tanacewa…
“bayanan bangaren su ma,kinga wutan ma ah kashe yake baki dayanta alamun bakowa ni inaganin yana Fada tareda su Yaya Almustapha”……
Besan me Sumayyan tace mataba seji yayi Afiyan nacewa”kada kidamu,I trust Yaya Sulaiman he’s a very strong Man and besides shikanshi yasan wacece Magajiya so bazai wani damu ba”, takarashe maganar tareda juyawa tafice tabarshi besan sanda hawaye sukafara running cheeks dinshi ba hakanan yana maimaita kalaman Afiya”he’s a very strong Man”,sekuma yatambayi kanshi”,”is he really that strong?”,kaman yanda Afiyan tafada,yasani he always hide his pain but today the situation is different,yau yaji abubuwan dabai taba tunanin wani dan Adam zaiyi bama balle kuma Uwar data haifeshi.. ……
Allah sarki Sumayya haka tacigaba da kiran layin nashi amma yakasa dauka daga karshe ma kashe wayar yayi gabadaya don yasan indai taji muryarshi her mind will never be at ease dama tananan gida ne yasani she’ll always be with him, she’ll hug him and comfort him hakanan she’ll makesure that she makes him feel better and she’ll tell him that”everything will be alright”,yana cikin wannan yanayin ne har Almustapha din yashigo yasameshi ahaka…….
Jin yace mishi “he’s sorry dinne”,yasashi dago da idanunshi yana kallonshi da mamaki donshi aganinshi he should be the one to say sorry,if not for anything but for his Mother’s sake……….. +
Almustapha dinne cikin raunanniyar murya yace…
“i can’t see you like this katashi kazauna please”…….
Ganin yanda Yayan nashi yadamu yasashi tashi yazauna din yana kallon Almustapha din muryarshi na cracking yace…
“I sh…o..u..ld be the one to say sor..r..y Yaya”Almustapha besan sanda yajanyo Sulaiman din zuwa jikinshiba hakanan yashiga rarrashinshi yana…
“why will you say sorry you fool?”……..
Cikin kuka Sulaiman din yace”on behalf of Mama,she did many things,she hurt you guys way too much”yakarashe maganar yana kuka harda shashsheka…
Tapping bayanshi Almustapha yashigayi yana”it’s okay,you’re not at fault,Mama ne tayi bakai ba then why are you punishing yourself for her deeds,tell me?”, Almustapha yayi maganar yana dagoshi daga jikinshi kallonshi Sulaiman yayi batareda yace komai ba…..
In a very calm voice Almustapha yace”if we punishing her is giving you a very hard time zanyiwa Abba magana,we should just forgive her,let her go and we can move on in our lives I promise zan iya yimaka haka Sulaiman kawai so nake Inga ka kwantar da hankalin ka,I want you to be the Sulaiman I used to know”…….
Murmushin dayafi kuka ciwo Sulaiman yayi sannan yace…
“you don’t have to do that,l’ll be okay”…….
Kallonshi Almustapha keyi kafin yace”Are you sure?”…..
Gyada masa kai kawai Sulaiman din yayi kafin Almustapha ya mikar da kafansa yace “kwanta to” musubabu Sulaiman din yakwantarda kansa akan kafafun Almustapha din tareda lumshe idanunsa ahankali yayinda Almustapha yashiga shafa kan Sulaiman din in a comforting manner tareda yimasa addu’o’i ahaka har Sulaiman din besan sanda bacci menauyi yadaukeshi ba……..
Shidai Almustapha idanunshi biyu se kallon tilon kanin nashi dayakeyi hakanan yana kissima yanda abubuwa suke tafiya acikin rayuwarsu baki daya.yana cikin haka yaji text yashigo mai awaya dubawa yayi as he expected Asma’u ce budewa yayi yashiga karantawa…… 1
STORY CONTINUES BELOW
” _Where are you Yaya Imam?_ “…..
Dan murmushi yasaki tareda farayimata reply…..
_”Ina ruwanki?_”
Asma’u dake kwance kan three seater ah parlour tareda su Afiya daketa maida yanda akayi tsakanin su takaranta reply din nashi……
Turo baki tayi aranta tana”oh hakama zaice”…..
Kafin tatura mai…
” _Ayya am Yaya Imam, it’s so late in the night shiyasa kuma Ummi ma nata tambayarka_ “…..
Yana ganin massage dinnata yashiga karantawa hakanan yana karantawa yana imagining yanda zatayi da fuskarta in agabansa zata fadi maganar,dan hargitsa gashin kansa yayi kawai sekuma ya shiga kiranta damamaki ta kalli screen din phone dinta ganin shike kira kafin ta saci jiki tawuce dakinta harya kusa tsinkewa sannan tadaga………
Batareda yajira tayi magana ba yace…
“I’m with Sulaiman so,you don’t have to worry zanshigo dasafe”…….
Gyada mishi kai tayi kamar wanda tana kallonshi,jin tayi shiru ne yasashi cewa…
“are you there?”
Cikin cool voice dinta tace”uhmmm,hope he’s alright?”,don hakanan taji ba dadi don seyan zunema Sulaiman din yafado mata kan cewa shi Dan Magajiya ne….
“Yea, he’s asleep now”, Almustapha yabata ansa sannan yace”seda safe kifadama Ummi”……
Gyada mishi kai kawai takumayi kafin ya katse call din……….
★★★…..
Hajja tunda ta’idar da sallar Isha tashiga hada kayanta ah akwati koda Asiya tashigo da cikinta dayafito sosai da mamaki tadubi Hajjan tana…
“Hajja da kaya Zaki tafi?”…….
Batareda Hajjan ta dubeta ba tace…
“eh daso kike inbarmiki kidinga sawa komi?”…..
Zama Asiya tayi abakin gadon sannan tace…
“a’a Hajja bahaka nike nufi ba nayi tunanin zamuje mudawo tarene fa kumadai naga akwai kayanki acan gida”…….
Budan bakin Hajja cewa tayi….
“cabdi aini daganan babu inda zaku saukeni se gidan Asma’u ko gida bazaniba kuma kimaji ba dawowa zanyi ba ainayi maki kokari Itama Asma’un wayasani ko tanada karamin cikin ma dole inje inkula da ita kekuma zancema Babanku ah dauko miki Jiddo tazauna dake harzuwa lokacin dazaki sauka”……..
Itadai Asiya dariya kawai tayi don daman sungaji da Hajja da shegen mitanta ga takura in ankunna generator tace kara yadameta ita dai akashe haka abinci ma tadinga sa Asiya tanacin tuwon dawa dana hatsi waishi zaisa Danta yataso da kwarin jikibawai tayita cin abincin turawan nan da basu da karko ajikiba and on the other hand she’s very Happy for her Sister atleast she’ll get along with Hajja don da alama tagama saukowa baki daya in anci sa’a ma tana iya daina fushi da Ummin ma tahakura hakanan…..
Haka ta taya Hajjan suka karasa gyara kayan kafin suka kwanta bacci washegari tun sassafe tadingayi masu jaraba se su tafi dakyar Asiya tasamu takora Aslam yatafi aiki tace yabari inya gama ayyukansa seyazo suwuce kaduna da Zaria aiba wani nisa banedashi dahar saisunyi sanmako donda shima Aslam biyema Hajjan yayi………… 1
****
Almustapha da Sulaiman tare suka fita sallar asuba wanda bayan an idar ne suka samu labarin rasuwan Waziri da Allah yayi masa cikawa cikin dare ah clinic din cikin masarautar sakamakon bugun dayasha jiyan don likitocin sunyi kokaro gurin ganin su ceto ranshi amma dake wa’adin yacika bbu yanda suka iya….
Babu abunda Almustapha ke furtawa se innalillahi wainna ilaihir rajiun yayinda Sulaiman dakyar ya’iya cewa Allah yayi masa rahama hakanan yana tuna irin kirkin Kakan nasu dakuma yanda yake nuna musu kauna akoda yaushe shida yayunshi Mata don koda jiya Hajiya Muniba tafadi cewa Waziri was there sanda mahaifiyar shi tayi setting fire agidan Galadima he couldn’t believe it sede dayayi la’akari da Wazirin yayi hakan ne don yayi protecting Magajiya sebeyi mamakiba don yasan irin son da Wazirin keyima Magajiya wanda hakan yajamusu soyayyarda yake musu amatsayinsu na Ya’yanta……….
Babu laifi an halarci jana’izar tasa sosai donkuwa dukda abunda yayi din Waziri mutumin kirki ne gashi dason jama’a dasanin yakamata shidai kawai laifinshi yaso ‘yarshi dayawa,ya lullube laifinta mafi muni ah mutanen duniya wanda aganinshi yayi hakan ne don irin sonda yake mata sede besani ba cutan ta yayi sannan yasake gurbata mata rayuwartane don dayafada tun lokacin za ahukuntata hakanan bazama tasamu chance din sake aikata laifuffukan data aikata bayan nan ba shiyasa wani sa’in iyayenmu suke babban kuskure wurin boye laifin Ya’yansu batareda sunbari an hukuntasu ba,su gani suke kaman taimakon mu sukeyi kokuma gani suke shine karshen so suke mana bayan bahakan shine daidai ba gaskiya,when your children are wrong show them the way if you can,mu ajiye batun so agefe don inson yayi yawa yana leading to gurbata rayuwar yara da dama because sonda zakayima danka baka iya tsawata mishi inyayi laifi ba so bane wallahi barema in the case of Magajiya it’s so horrible,she did a very wrong thing but yet mahaifinta yaboye without thinking twice…..
Allah ubangiji yasa mudace,Allah yakuma sa mufi karfin zukata mu hakanan Allah yabamu ikon tarbiyantar da ya’yan mu tahanyar data dace,Amin ya rabbi………..
Sulaiman baimanta sanar da Yayunshi rasuwar Wazirin ba dukdama seda akakai Waziri gidanshi na gaskiya sannan yasamu yakira su sede abunda baisaniba shine suma sunacan suna fama danasu gidan mazajensu sabida abubuwan dasukayi ta aikatawa hakanan sarai anji labarin abunda mahaifiyartasu tayi wannan dalilin yasa mazajen nasu suka hanasu izinin fita daga gida don mijin Humaira kam cewa yayi intabar masa gida abakin aurenta wayasan wani halin banzan zata sake zuwa tadebo gurin uwarta tamaci albarkacin ya’yan dake tsakaninsu ne da sallamarta zaiyi ya huta shima…..
Hakuri tadinga bashi don itadai Allah yagani ta tuba kuma taga ishara akan mahaifiyarta …..
Sulaiman koda yakira Hamida kuka tasakar mai awaya lokaci guda hankalinshi yatashi yana tambayar ta ko lafiya don baya tunanin labarin rasuwan Wazirin yakai kunnenta bare ace shine dalilin kukan nata …..
Batareda ta tsaida kukan ba tace”mijinta ne yasaketa yanzu sabida tadage setazo gida sakamakon abunda yafaru da Magajiya din kuma don wulakanci ma saki uku”…..
Innalillahi wainna ilaihir rajiun shine abunda Sulaiman yashiga maimaitawa tareda dafe kanshi hakanan yadinga jin kanshi nasarawa lokaci guda tsabar abubuwan damuwa sunyi mashi yawa ayau din dakyar ya’iya karfin halin consoling dinta hakanan yakasa fada mata rasuwar Wazirin don yasan it might affect her health in abun yamata yawa gashi tana dauke da karamin ciki kamar yanda tafada mishi last time dasukayi waya………
Cikeda damuwa yace”Zansa aturo mota yazo yadauke ki,Abba is sick now I can’t tell him anything sekinzo gida din kawai”….
Gyada Kai kawai tamashi kamar wanda tana gabanshi kafin tayi hanging up call din ji tayi zuciyarta nayimata wani irin kuna……..
Abangaren Sulaiman kuwa lumshe idanunshi yayi tareda jinginar da kanshi jikin gini tunsafe babu abunda yasama cikin shi hakanan yakasa tashi daga gun zaman makokin tun bayan da suka dawo daga jana’iza, addu’o’i kawai yakeyi Allah yakawo mashi sauki cikin lamuransu baki daya, Almustapha kuwa yayi yayi dashi yaje yaci abinci amma yaki shikuma bayason yakawo masa abinci cikin taron mutane ga Dad ma is somewhat busy bare ya hadashi dashi and Abba too haryanzu bai farfado ba dukdama likita yace su tsanmaci tashinshi zuwa dare ko safiyar gobe insha Allahu………….
STORY CONTINUES BELOW
****
Bangaren Magajiya kuwa tana can gidan horo gashi taki cin abinci tun safe, ciwuwwukanta ma sunyi wani iri dasu and taki yarda abata treatment dukda they’re just trying to be nice to her ne kafin atashi fadan hukuncinta wanda Almustapha ne yasa ayi hakan, hakanan ba’a fada mata rasuwar Wazirin ba tun safe,bangaren Talatu kuwa ankaita clinic tun ah jiyan sannan anyi treating wonds dinta kafin akasakata cikin gidan yarin masarautar kafin afara case dinsu wanda duk jiran Mai Martaba akeyi tukun………
****
Around 4:30pm motarsu Asiya tasauka acikin masarautar zazzau wanda yatafi da imaninta lokaci guda because dukyanda ake bata labarinta bata tsanmaci ganin har haka ba tunda bata taba zuwa ba don ko ah auren su ai ita kaduna aka wuce da’ita batareda tazo taga gidan Asma’un ba………
Hajja ma da aka fito daga mota sewani washare baki takeyi kamar anbata gonar auduga tana”oh ni Hajja ashedai darabon zanganni cikin irin gadajen danakejinsu ah tarihi kullum kokuma ingani ah TV, Allah gatan bawa”,tayi maganar kuma tana dan sharar kwallah……
Aslam ma saukowa yayi yana dan dariyan Hajja din kafin yashiga kiran layin Sulaiman don number shi kadai yakeda shima agurin daurin aurene sukayi exchanging sede unfortunately wayar ah kashe take….
“Dan rike kugu yayi sannan yace yanzu yaza ayi musan wannene bangaren Asma’u ah wannan makeken gidan kekuma kince kar ah kirata you want to surprise her”,yayi maganar yana maida kallonshi ga Asiya……
Yar dariya tayi tareda dan riko hannunshi tana….
“Kai Sweetheart sekace babu mutanen dazamu tambaya”……
Jan hancinta yayi yana smiling to wakike ganin zamu tambaya nibanason raini kinsani…….
Cire hannunta tayi daga nashi tana yar dariya”to bani in tambaya mana”,tayi maganar tareda nufan wani dogari dataga yana tafiya cikin sauri yarikota yana”dawo I’ll ask him myself”……
“Murmushi kawai tayi tareda dawowan daman tasan za’a rina Aslam da shegen kishin tsiya wani sa’in har mamakin ya akayi ya yarda ze aureta take even after yaji batunta da Abba Dj sede kuma datayi laakari da irin sonda yake mata se tadaina mamakin”…….
1
Ba ajima ba sega Aslam din yadawo tareda dogari nan dogarin yadauki kayan Hajja sannan yayi masu jagora har bangaren su Asma’u……
Asma’u dayanzu dawowansu daga bangaren waziri itada Mom, Ummi, Afiya da Amira sunje sunyima iyalansa ta’aziya sannan suka dawo don su Amira ko islamiya basujeba sakamakon rashin da akayin,ko cire hajabinta batayiba taji ana sallama kuma kamar muryar data sani,dogarin ne yafara shigowa da kayan bayan ta’ansa sallamar sannan Asiya tashigo yayinda Hajja ke bayanta Aslam kuwa tunda dogarin yasanar dashi anyi rasuwa sekawai yawuce gurin zaman makokin donyima su Sulaiman din ta’aziya……….
Wani irin ihu Asma’u tasaki sakamakon ganin Asiyan datayi yayinda taruga aguje tafada jikinta tana ihun murna Amira da Afiya dake parlourn seda suka tsorata haka Ummi ma dake daki tuni tafito tana tambayar lafiya,meya samu Asma’u din sede ganin bakin da tayi setaja bakinta tayi shiru….
Asma’u dake jikin Asiya tana murna tace”Aseey wannan zuwa babu sanarwa haka?”….
Murmushi Asiyan tayi tareda dago Asma’un daga jikinta sannan tace”bakiji dadin ganina bane inkoma,don’t you like my surprise?”……
Turo baki Asma’u tayi tana karema Asiya kallo dubada yanda tayi jiki abunta tazama matar aure sak ba Asiyar datasani ah da ba sannan tace..
“I like your surprise Sis,I’m so happy bazaki gane yanda nayi kewanki bane ba”……
Cikeda damuwa Asiyan ma tace “Nima nayi kewanki sosai Asma’u”…
Hajja dake can baya ganin ba’akasa da’ita ba seta saki kuka harda shesheka tana….
“ni Hajja nashigesu nayi laifin da Asma’u ko kallona batason yi yau”……
Cikeda mamaki Asma’u tature Asiya don tabbatar wa kanta muryar Hajjan taji aikuwa itance dasauri takarasa gareta tana”Hajja kukan me kikeyi?”…..
Hajja dake sharar kwallah tace”kiyi hakuri jikata nasan nayi maki laifin da ba lallai kiyafemin ba amma don Allah kiyafe min wayasanima kona kusa mutuwa,banason inmutu da alhakinku”, Asma’u batasan sanda tarungumi Hajja tana sharar kwallarba Itama tana fadin ahankali”it’s okay Hajja,kada ajimu akwai mutane ah parlourn”,aikuwa tuni Hajjan tayi shiru daman kukan gulma ne…….
Asma’u kasa sakin Hajja tayi ah jikinta hakanan jitake inama agaban Ummi ne hakan tafaru don tasan zatafi kowa farin ciki ma,ashedai akwai ranar da Hajja xata rungumeta kamar yanda takeyima su Asiya, Allah buwayi me iko kuma mai canza al amuransa aduk lokacin dayaga dama………
Ummi ne ganin oyoyon bana kare bane tace…
“Daughter bazaki shigo dasu kigaisa dakyau ba kuntsaya daga waje?”…..
Cikin sauri Asma’u tashare kwallarta kafin tajuyo ga Ummin tana yanzu zamu karaso sannan takama hannun Asiya da Hajja tashigo dasu parlourn tace su zauna Itama kuma seta zauna gefen Hajjan tareda kwanciya ajikinta kadan tana cewa…
“Ummi ga Hajja na gakuma twin sis dita Asiya”……
Murmushi Ummi tayi tareda karasowa parlourn tashiga gaida Hajja din kafin Asiya ma tagaidata haka su Amira ma kafin daga karshe Amira tace dagaske ku twins ne?….
Dariya sukayi dukansu biyu tareda gyada mata kai murmushi kawai Ummi tayi don tasan sudin ba twins bane ba tunda ranar bataji Ummi ta ambaci Asiya cikin Ya’yanta ba……. 4
STORY CONTINUES BELOW
Cikeda mamaki Afiya tace”But they’re not identical”……
Dan gwaliyo Asma’u tayi masu tana”ai twins badole se suna kama ba besides kune bakuga kamar ba amma mutane da dama ma suna fada”…..
Cikeda tuhuma Afiya tace”bawani banyarda ba,they’re not twins agreed akwai kaman jini amma ba twins baneku”….
Ummi ne tace”tomiye na binciken kosu ba twins bane what matters they’re sisters and they love each other”…….
Murmushi kawai Asiya da Asma’u sukayi yayinda Amira da jaraba tace zantambaya ah gidan ku duk randa najeni……….
Kan kacemi ancika gabansu da kayan ciye ciye, Ummi sejan Hajja takeyi da hira tareda tambayarta mutanen gida har aka kira sallar maghrib kafin tabarsu sukayi dakin Asma’u don yin sallan anan ne Asiya tasamu zama da Asma’u bayan sunyi sallah tana fada mata sunga program and taji dadin yanda everything turn out this way sannan tadinga bama Asma’un shawarar zaman aure tareda yanayin zama acikin *GIDAN SARAUTA*, Hajja kuwa se kalle kalle takeyi ah dakin donba karamin tafiya da imaninta kyaun dakin yayi ba har bayan sallar Isha kafin Aslam yakira Asiya kan ta fito su tafi gida Asma’u kaman zatayi kuka tace “nadauka kwana zakuyi fa”,dariya Asiya tayi sannan tace…
“bafa mukarasa ko gida bafa,kinga dole muje kadama Daddy yafara tambayana tunda ance mishi zamuzo”…..
“Ayya am Daddyn ma nasan bazai hanaba inkincemishi zaki kwana”,dariya Asiya tayi sannan tace babu ruwana sokike Yaya Musty yamin korada hali kenan besides nima bazan iya barin mijina shi kadaiba and Hajja nanan ai”…..
Babu yanda Asma’u ta’iya haka itadasu Amira suka fita raka Asiya bayan tayima Ummi sallama haka Ummi tacikata da turarraruka ah leda bayan tace tagaida mata su Ummi da Mommy…..
Abakin mota suka samu Aslam,Almustapha da Sulaiman suna dan hira sama sama tunda suka iso gurin Aslam yake baxa idanu acikinsu yana”ina Sister Gimbiya Ma’un ne wai?”…..
Turo baki tayi hakanan taki gaidashi sarai tasan yagane ta neman tsokana ne kawai itakuma haushi takeji don gani take kamar shine yahana Asiyan kwana……
Asiya datasan halin Asma’un ne tace”wai fushi takeyi”…..
Dafe kirji yayi playfully”ni Aslam mijin Asiya menayi?”……
Cikin raha Asiya tace”kahana Asiya kwana agidan kanwarta”……
Dariya yayi tareda duban Almustapha sannan yace”Matarkan nan shagwabar ta yayi yawa,yakakeyi da’ita newai!”…
Faking smile kawai yayi don seda yaji wani irin jin ance tanada shagwaba wato bama ashikadai takeyimawa ba harda wasu katti komi?….
Asiya ne tace…
“Ina wuni Yaya Almustapha”……
Dukda baiganeta ba amma seya amsa mata fuska daukeda fara’a yayinda Sulaiman yace “itace Asiya she’s her sister,matar Aslam”…….
Murmushi kawai yayi yayinda suka shige mota bayan sunyi masu sallama seda ta tabbatar dagaske tafiyar zasuyi Aslam din baida niyar barin Asiyan setayi saurin karasawa side din da yake idanu cikeda kwallah tace”Ina wuni Yaya Aslam”……
Dariya yayi yana”kin hakura kenan?”…..
Wannan karan hawayen seda suka zubo tana fadin…
“to ya na’iya”…..
Bashi kadaiba harda su Sulaiman seda suka kwashe da dariya at her expression except Almustapha…..
Dakyar Aslam ya’iya rike dariyartasa sannan yace”sorry Ma’un Yaya Mubaraq namiki alkawari zankawo miki Asiya wataran tayi maki kwana biyu amma dai banda yanzu”……
Share kwallarta tayi sannan tace”promise?”…..
Gyada mata kai yayi yana smiling sannan yace”I promise Sis”……
Haka sukayi sallama Asiya ma duk taji ba dadi kafin suka tafi,satan kallon Asma’u Almustapha yayi ganin haryanzu sharar kwallah takeyi kafin yaja hannun Sulaiman sukayi side dinsu badon yasoba,suna shiga parlourn yace da Asma’u da suka shigo abayansu takawo abincin Sulaiman din…. 1
Gyada mai kai tayi sannan taje tazubo takawo,duban tulin abincin Sulaiman yayi yana…
“badai kunason kuce nikadai zanci abincin nan ba?”….
Wani kallo Almustapha yayi ma Sulaiman din yana”mema kaci tunsafe tukun?”…..
Turo baki yayi kamar karamin yaro yana”ammadai wannan yamin yawa”……
“Kaci dai”,cewar Almustapha din…….
Hakanan yafara ci ahankali babu laifi yadan ci sosai donshima bakaramin yunwa yakejiba daman kafin daga karshe yadauki glass cup din ruwan da Asma’u ta ajiye mishi yashanye tareda cewa”alhamdulillah”
Murmushi Almustapha yayi cikeda jin dadin yanda Sulaiman din yaci abincin sosai sannan yace”kokaifa”….
Yar dariya kawai Sulaiman yayi wanda baikai zuci ba sannan yatashi tsaye yana”asuba tagari nikam bacci nikeji”……
Dan kallonshi Almustapha yayi sannan yace”where is your phone?”….
da mamaki yace yana aljihun wandona,halama Almustaphan yamashi da hannu nacewa ya miko masa babu musu yacirota ah aljihun yamika masa kunna wayar Almustapha yayi kafin yamayar masa tareda cewa”kada kasake kashe wayarka”…….
“To Big Bros”,cewer Sulaiman din tareda yimasu saida safe kafin yafice zuwa bangarensa……..
STORY CONTINUES BELOW
Almustapha dakinsa yawuce ganin Asma’u natareda su Afiya,bejima dashiga ba itama tabi bayanshi sede ita dakinta tayi inda tasamu Hajja na sallah da alama shafa’i da wuturi takeyi don yariga yazame mata sabo daman kullum setayi…….
Murmushi tasaki sannan tacire kayanta tashige wanka abunta………..
Bangaren Sulaiman kuwa bangarenshi yawuce direct sede tunda yashiga yakejin wani kamshin turare nadaban da alama ansaka turaren wuta ah sashin bakidayanta abunda zai iya cewa harya manta yaushe rabon dayaji anyishi dondai ah iyasaninshi tun farkon aurensu da Zaliha ahaka dai yana mamaki harya karasa dakin shi sede to his own surprise ganin Zaliha yayi sanye da wasu shegen kaya daya nuna gabadaya illahirin jikinta yayinda hannunta ke rikeda turaren wuta tana zagaya dakin ahankali gakuma sanyin AC daya hadu da special scent din Sulaiman ya gauraye dakin wannan dalilin yasashi lumshe idanunshi ahankali kafin dakyar ya iya daurewa yakarasa bakin bedside drawer tareda ajiye phone din dake hannunshi jiyayi tarungume shi ta baya wanda hakan yasashi jin wani iri lokaci guda,cikin sauri yake kokarin yakice ta daga jikin shi yana”banason irin haka Zaliha,do not try me this night I’m not ready for your stupidity” ……
Wani irin sake rungume shi tayi tareda zagayowa tagabanshi tana mishi kisisina…
“I’m sorry,I missed you so much”……
Tureta yayi da karfin hali sannan yazauna bakin gado yana ajiyar zuciya aranshi yana addu’ar kada Allah yabata ikon cin galaba akanshi don yasan bazai wuce tazo tatadamai sha’awarshi baneba bayan bakaramin kokarin fin karfin zuciyanshi yake ah kwanakinnan ba,kanya ankara harta fado jikin shi yana shirin magana tayi saurin hade bakinsu guri daya daganan tashiga yi mashi salo kan kacemai Sulaiman yabada kai haka suka cigaba da aikin lada itakanta Zaliha bakaramin kewar mijinta tayiba dukda ma yanzun tayi hakan ne sabida tasamu tanuna mishi ita ta tuba fa and she’s sorry for all she did kafin kuma tasamu tayima sauran yan gidan fake tubanta sabida tasani without his support bazata iya achieving wannan dinba dukda kafin tashawo kanshi da wahala yanzunma don tasan lagonshi ne amma tanada tabbacin dasafe akwai drama tsakaninta dashi…….
****
Around 11:30pm jirginsu Sumayya yasauka ah airport din kaduna,hakanan tafito daga airport din ta tsaya tana trying number din Matar Idriss abokin Sulaiman don fada musu isowarta because babu wanda yasan dazuwanta agida bare azo tarbanta itanma batayi tsanmanin zatazo dinba sede irin yanda tayita kiran Sulaiman batasamunsa yasa hankalinta yatashi lokaci guda gashi inta tambayi su Afiya sesuce mata lafiyansa Lau,tayi tayi sukaimasa nasu wayan sesuce mata baya kusa kosu bata wani excuse wannan dalilin yasa tun jiyan tashirya tahowa don jitake ah jikinta ba lafiya ba……..
Haka tadinga kiran layin Matar Idriss din akashe gashi batada number din Yaya Idriss din wannan dalilin yasata tunanin gwada sake trying number din Sulaiman may be yanzu ya kunna wayar inyaso seya turo mata na Idriss din dukdama she wanted to surprise him ne kawai sede yaganta agida…….
Kiran wayan tadingayi sede har sau biyu ba’a dauka hakanan tacigaba da kira Zaliha dake kwance jikin Sulaiman dayake bacci tayi tsaki tareda daukar wayan jin anata kira duban screen din tayi ganin Sumayya ne yasata dagawa cikin sauri kafin tatashi daga jikinshi ahankali tashige bandaki sannan cikeda bacin rai batareda ta amsa sallamar Sumayyan ba tace”waike wace irin mayyace,kokin manta cewa Yayannaki yanada da aurene haba”,Zaliha tayi maganar raibace kafin takarada”inbanda jaraba acikin salasainar daren da mutum yake kasancewa da iyalinshi ma baza’abarshi ya huta ba,to bari kiji infada miki inkika yarda kikasake kiran mijina ah irin wannan lokacin to gaskiya za ajimu”…….
Daganan Zaliha takatse call din tareda komawa dakin gurin Sulaiman daketa sharara bacci, Sumayya dai mutuwar tsaye tayi hakanan tarasa abunyi,wani irin kututun bakinciki ne taji ya ziyarceta lokaci guda hakanan batasan sanda hawaye sukafara bin kuncinta ba,she came all the way for him thinking that something bad is happening to him ashe yana tareda matarshi hakanan tamanta cewa yanada wanda suka fita kusanci dashi hakanan batasan ya akayi tamanta ah al amarinsu zatayi encountering rayuwa da kishiya ba indai tace zata auri Sulaiman, tamanta ma da existence din Zaliha because all she sees was Sulaiman,his love,his support and care and all she care for shidinne seyanzu da Zalihan ta tunatar da’ita babu abunda take furtawa se neman sauki azuciyarta ahaka dakyar takoma cikin airport din tasamu kan wani bench tazauna akai tareda lumshe idanunta zuciyarta nayi mata kuna hakanan hawayen basudaina gangarowa ah kuncinta ba……….
*****
Seda tagama sa kayan baccinta sannan tadubi Hajja dake kwance kan gado hartayi bacci don tunkafin tama fito ah wanka ta kwanta,sotake suyi hira if possible suma kwana sunayi amma Hajjan harta kwanta murmushi tasaki tareda gyarama Hajjan bargon sannan taje takashe wutan dakin kafin tadawo takwanta hakanan setaji tana son takwanta ajikin Hajja din shiyasa ma ta matsa kusa da ita tareda shigewa jikinta cikin sauri Hajja tatashi don daman ba nauyin bacci gareta ba tana”waye wannan?”…….
Murmushi Asma’u tayi sannan tace “nine Hajja daman baccin ki beyi nisaba?”…….
Hajja dake mitsike idanu tace….
“kedin badai anan kike nufin zaki kwana ba?”…..
Dan turo baki tayi tareda kunna hasken wayarta tana”Gadon bazai ishemi bane Hajja,inbazai ishemuba se in kwanta kan kujerar can”,tayi maganar tana pointing sofa din dake cikin dakinta………
Wani kallo Hajjan tayi mata kafin tace”waya gaya miki ana barin turakar miji ko waya fada miki anabarin miji irin Almustapha yakwanta shikadai to inma kinayi ne donni wallahi baki burgeniba don haka kawai bazanso mijinki yazo yanacewa na hanaki zuwa dakinshiba bayan bahaka kika saba ba kibarni da irin kunyar dazanji innahadu dashima sakamakon abubuwan danayi abaya sun isheni”………
Asma’u na shirin magana Hajja tace”karki damu indai nine,tashi maza kije ga mijinki kinji”…….
Gyada kai kawai Asma’u tayi amma gabadaya ranta ya jagule, tukunnan ma ta’ina zatafara kwana daki daya dashi fisabilillahi,haka tafice tana ta turobaki itakadai……
Itakadai,tafi mintuna biyar tsaye wurin dinning table din da ba’ama cika anfanidashi ba hakanan yazama kaman abun kwalliya ne kawae agurin wanda kuma yake daidai setin dakin Almustapha din kafin tajuya tana karema parlourn kallo,babu kowa cikinta hakanan duk wasu nau’in kallo ankashe shi sede ba’a kashe wutan parlourn ba da alama wanda yafita last ya manta ne kokuma yanada niyar dawowa se Allah be bashi iko ba…………
Dan furzar da iskan bakinta tayi aranta tana fadin da’inje dakinshi aigwanda inkwana anan inyaso da asussuba inkoma dakina batareda kowama yasaniba because I’m very sure kowa yayi bacci by now,dawannan tunanin ne takarasa gurin switch din wutan parlourn takashe sannan tahaska wayarta takarasa kan three seater tafi minti uku akwance akai amma she’s not feeling comfortable wannan dalilin yasa tadauki daya daga cikin cushions din tajefa kasa kafin takwanta akai hakanan tana jin dari kadan kadan sabida rashin bargo amma hakan baisa ta daddaraba kan kacemai bacci yadauke ta dukdama atakure takeyinshi………….
+
Almustapha nazaune kan makeken bed dinshi yayinda kafanshi ke mike hakanan yadaura labtop akansu yana research har wuraren shabiyu da rabi na dare kafin yakashe system din ya ajiyeta can gefe kafin yayi shirin kwanciya,har ya gama addu’an bacci seyaji yanajin kishin ruwa kuma wannan dalilin yasashi tashi yakarasa ga fridge dinshi dake cikin dakin sede gabadaya ruwan sun daskare babu wanda zai iya sha ayanzu hakan yasashi sakin tsaki ahankali batareda yashiiryaba kafin yafice ah dakin don daukowa ah fridge din dake parlour because Allah yagani bazai iya zuwa na kitchen ba tunda shiba ma’abocin zuwa gurin bane ba……..
Ganin parlourn da duhu gashi bai fito da wayarshi ba sekawai yasa hannunshi yana lalubar switch din wutan inda yake tsanmanin agurin yake don daman yana dab da kofar dakinshi and hasken wutan dakinshin ma yana haskowa kasancewar dakinnashi ah bude yake,bayan ya kunna wutan ne yayi inda fridge din yake sede da mamakin shi yayi arba da figure din Asma’u dake kwance kan carpet bakaramin mamaki yashaba don wallahi dabadan wuta akunne yakeba sema yatakata batareda yasani ba gashi baccin ma atakure takeyinshi kallo daya zakayi mata kagane cewa she’s not really comfortable,tabe baki yayi ahankali sannan yakarasa ga fridge din yana mamakin wani dalilin ne zaisa tabaro dakinta tazo takwanta anan seda yasha ruwan me isansa sannan yadawo inda take ahankali yatsuguna gabanta kafin yashiga tabata ahankali yana”Asma’u, Asma’u wake up”…
Amma shiru sema kara juyamai baya da tayi dan tsaki yayi ahankali kafin ya ajiye goran ruwan daya dauko sabida Incase inyasake jin kishir ruwa zuwa anjima hakanan yana tunanin yadauketa ne kawai donya lura batada niyar tashi,tana sanye da riga na bacci pink wanda tasha hotunan teddies agabanta hakanan rigan da kadan tawuce gwiwarta se pink safa dake kafarta Itama ankle socks ne hakan ya bayyana kyawawan sirarun kafafunta se hijan din dake kanta dabashi da wani girma hakanan cikin sakan hamsin ya gama analysing kayan dake jikinta kafin ahankali yasa hannunshi duka biyu yadagata in a bridal style as usual batada wani nauyi shalem shalem kaman tsinke…………
Asma’u da taji andagata sama ana tafiya da’ita wannan dalilin yasata saurin bude idanunta tana shirin sakin ihu tareda yin wuntsil wuntsil da jikinta,bude dazatayi taji bakinshi cikin nata wannan dalilin yasata yin tsit haka Almustapha yacigaba da kissing dinta passionately wanda cikin sakanni kadan tafara mayar mishi da martani batareda tasanma tanayiba,It’s just something pleasurable dabata taba experiencing ba dukdama bayaune rana tafarko dayayi kissing dinta ba but the other day she can’t even remember the feelings,she was shocked,confused and out of words that day unlike today………….
Ajiyeta yayi akan gadon still bakinsu na hade kafin dakyar ya’iya sakinta tareda lumshe idanunshi itakuwa saurin juyakanta tayi tacusa cikin pillow cikeda kunyarshi murmushi yasaki sannan yakoma yarufe kofar dakin tareda kaso wutan sannan yadawo kan gadon yakwanta ta daya gefen gadon tareda jan bargo ya lulluba musu duk tanajin shi hakanan kuma tana mamakin badai yana nufin zasu kwana gado daya bane ba dukda batason yaji muryarta amma seta ce”Yaya Imam kasauka don Allah”….
Kawai jitayi yajanyota zuwa jikinshi tareda dorata saman cikin shi wanda lokaci guda kamshin turarenshi yagama mamaye mata hancinta sa hannu yayi ah waist dinta yayinda ta cusa kanta cikin wuyanshi cikin muryar dabaisan yanada itaba yace”meyesa?”……..
kaman zatayi kuka tace…
“ammadai kasan baikamata bako?”….
Murmushi yayi sannan yashiga shafa bayanta yana”the kiss or the way you’re on my body right now?”,yayi mata tambayar cikin rada wanda hakan yasa tsikar jikinta yin wani irin yaar…..
Dakyar ta’iya cewa”komai ma”, hakanan muryarta na cracking…
Yanda tayi maganar ah tsorace seda tasashi sakin dariya batareda yashiiryaba sannan yace”waye yaja?”…..
STORY CONTINUES BELOW
Dagowa tayi tana kallonshi cikida mamaki daga mata girarshi yayi tareda dora fuskarshi kan nata yana..
“uhmmm fadamin,waye yaja?”…….
Wannan karan harnumfashin su haduwa yakeyi ga kamshin bakinshi dake kara rikita ta batasan sanda hawaye sukafara mata welcome daga idanunta ba itakam takasa gane kan mutumin nan shida yace zasu rabu then why is he behaving this way now?….
Dayake bedside lamp din akunne wannan dalilin yasashi ganin hawayenta cikeda damuwa yace…
“kuka zakiyimin Asma’u,sabida nayi kissing dinki amatsayina na mijinki?..
Tana hawayen hakanan fuskokinsu na hade tashiga girgiza masa kai ahankali alaman aa,dan furzar da iska yayi daga bakinsa kafin yace..
“besides wayaja,you wanted to shout shiyasa narufe bakin ki banason kitada mutanen gida shiyasa”………..
Cikin Yar siririyar muryarta tace…
“nifa bahaka bane ba?”…..
Cikin rada yace…
“to miye ne,tell me Asma’u?”….
Daga kanta tayi daga nashi sabida uncomfortability datakeji hakanan tanashirin sauka ah jikinsa yasake matse hannunshi ah waist dinta in a very command tune yace”you’re not going anywhere”…..
Sake sakin kuka tayi sannan tafara magana”to kabarni mana inyi magana”…
Dariya yayi yana kwaikwayon muryarta ta shagwaba”waya hanaki magana to daman?”……
Turo baki tayi sannan tace….
“aidai kasan rabuwa zamuyi ko then why are you behaving this way with me”…….
Yafi minti uku beyi magana ba sema kallon kyakyawar fuskarta dayakeyi don ah tunanin bazata sake mai magana ta rabuwa ba,ah tunaninshi they’ll catch things up and move on with their lives,in a very calm voice yace….
“are still thinking about that?”……
Cikeda takaicin banzan tambayar da yayi mata bayan yariga dayasan komai tace”you said you’ll free me from this relationship after everything is normal and alhamdulillah komai is normal now Yaya Imam I need my freedom too,inason insan inda dare yayimin”……..
Lumshe idanunshi yayi ahankali kafin yabude su kan nata,in a very cool voice yace….
“after all that happened out there the other day,do you still think I’ll free you from this relationship?”, yakarashe maganar yana kallon farararen idanunta dahar yanzu suke cikeda ruwan hawaye dakyar ta’iya girgiza masa kai tareda cewa”Kai kafada ai da bakinka bawani ba”……..
Shima girgiza matakan yashigayi alamar aa kafin cikin murya mekama da rada yace”you’re wrong Asma’u,I don’t want to free you from this relationship anymore infact i want to cage you in this relationship”,yayi maganar tareda sake dora kanshi kan nata itakam wannan karan kukanta harda shesheka hakanan itakanta tarasa shin farin ciki zatayi komi,kode Almustapha yafara sonta ne kaman yanda tajima tana fama da soyayyarshi ah zuciyarta cikin yar siririyar muryarta tace”why do you want to do that Yaya?”…….
Murmushi yayi sannan yabata amsa ah takaice”you’ve done so much for me and most importantly you’re my Wife”…….
Wani irin kututun bakin ciki ne ya tsaya mata arai watoma bawai don yana sonta baneba,kawai don yanason yayi returning favours din da tamishi,lallai Itama tayaudari kanta datayi tsanmanin someone like Almustapha will love her in return,lallai ta yaudari kanta datayi expecting so much from him lumshe idanunta tayi yayinda hawaye ke running ah cheeks dinta hakanan wasu ke zuba ah fuskarshi shima lumshe idanun nashi yayi hakanan yakejin hawayen nata kaman wanda akezuba mishi ruwan dalma ah kokon zuciyar shi,why does she like wasting her precious tears,shi kam ita komaima abun kuka ne agurinta kokuma miye laifinshi don yanuna yanason zama da’ita,atunaninshi she’ll be happy with the decision bawai tafarayimai kukan dabaisan dalilinsa ba tunda yajima dasanin tana tsananin sonshi, jiyayi tace”don Allah kada kayimin haka,ka sake”,bebari takarashe fadin “ni” dinba yakuma hade bakinsu guri daya,by Allah bayason jin wayannan kalaman daga bakinta hakanan bayaso tadauki zunubi bayan shiyafara cewa he’ll let her go bawani ba”,haka yacigaba da kissing dinta very passionately sede wannan karan batayi reciprocating ba she’s just busy crying and trying to go away from him shikuma hakan bakaramin konamai zuciya yakeyiba, jin kukan nata nakokarin yimashi illa yasashi sakin bakinta kafin yasa both hands dinshi yariko fuskarta yana”basai kin roki saki agurinaba banason insake jin wannan kalmar daga bakin ki kokin manta cewa addinin mu yahana mace tanemi saki gurin mijinta batareda yamata wani kwakkwaran laifi ba?”…….
Cikin kuka tace”to ya zanyi kai kayi min alkawari”……..
Cikeda damuwa yamayar dakanta cikin jikinshi tareda rungumeta yana”shhhhh,stop crying I’ll let you go if that’s what you want”……….
Shiru tayi acikin physique chest dinshi hakanan takasa koda cigaba da kukan ne se sauraran heartbeat dinshi da takeyi ahankali……..
Can taji yace”but not now kibari se after nadin sarautana please,i need you by my side”,yayi maganar murya ah raunane ……….
Girgiza mishi kai tayi alamar to dukdama batasan yaushene nadin ba amma abu daya tasani she can never reject his offer,Jin kamar bata
ansa shiba yace….
“kinji Asma’u?”……
“To kawai tace mishi,ita so far as he’ll let her go aishikenan don Allah yagani bazata iya zamadashiba batareda yanasonta ba,koba komai wataran zai iya goranta mata”……
Acikin kunnenta yayi mata rada…
“go to sleep now, it’s so late in the night”…….
Kokarin tashi take takoma kan sofa amma seyayi saurin miskuto da’ita yamaidata kasanshi kaman zatayi kuka tace”kamin nauyi Yaya Imam”…….
Murmushi yasaki tareda janyewa daga jikinta yakoma gefenta tareda dora kanshi kan pillown da kanta yake suna facing juna in a very calm voice yace “go to sleep now”,gyada mishi kai tayi tareda dan jan baya sannan tasaka kanta cikin kirjinshi don batason yanda numfashinsu ke gaurayuwa yanasata jin wani iri shima baidamu ba sema dago fuskarta dayayi yacire mata hijab dinta sannan yamaida ta cikin jikinshi kan kacemai bacci me dadi yayi awun gaba dasu………..
Ranar Almustapha da Asma’u kusan makara ma sukayi sallar asuba donma shine yafara tashi hakanan yaji anashirin tada sallah ah masallaci gashi dole seyayi wanka cikin sauri yajanyeta daga jikinshi yashige bayi wanka yayi sannan yadauro alwala yafito yashirya cikin ash jallabiyanshi kafin yawuce masallaci Allah yataimakeshi limamin najan manyan surori wannan dalilin yasa yasamu raka’a daya koda yadawo dakinshi yawuce don tadata tayi sallah gabadaya yamanta tana fashin sallah ma………….
Koda yashiga dakin still tana kwance abunta se sharara bacci takeyi in a very calm voice yashiga kiran sunanta”Asma’u, Asma’u?”……
Mika tayi ahankali tareda sakin hamma duk yana kallonta dakyar ta’iya bude idanunta tana turo baki cewa yayi”kitashi kiyi sallah har an idar ah masallaci”……
Tsabar takaicin tashin ta dayayi daga daddadan baccinta batasan sanda tasake jan bargo ta lullube kanta ba,wara idanu yayi cikeda mamaki yana”au komawa ma kikayi?”…….
Cikin shagwaba tace”Ina banayi”……
“Medin?”…
Wannan karan kamar zatayi kuka jin yadameta tace”sallan mana”…..
Dariyane takusan kubcemai don seyanzu abun yafado masa ma dakyar ya’iya cewa”to sorry ai mantawa nayi”….
Itadai bata kulashi bama bare yayi tunanin taji ahankali yatashi yafice don zuwa suyi karatu dasu Amira itakuma tacigaba da baccinta hankali kwance………….
*****
Kusan baccin datayi rabi da rabi ne sabida tsoron kada ayi mata sata cikin dare hakanan tana tsoron yanda take mace someone might take advantage of her dukdama securities na zagaye da gurin tako’ina sedeme aisudinma mazan ne ahaka har gari yafara wayewa dakyar tasamu tayi alwala tayi sallah kafin tafita ah airport din taxxi ta tara wanda dakyar tasamu kasancewar safiya ne sosai mutane basu fara fitowa yin ayyukansu ba me taxxi dinne yace…
“Ina zamuje Hajiya?”……..
Ahankali tace mishi park zaka kaini…..
Cemata yayi to don daman shima he’s educated rashin samun aiki dawurine yasashi fara neman nakansa sabida yanzu inka ce seka jira gwamnati subaka aiki to gaskiya kana tareda wahala agabanka……
STORY CONTINUES BELOW
Sanda suka Isa park din Allah yataimaketa tanada kudin Nigeria ah jakanta tunwanda tatafi dashi bata canzaba,dari biyar taciro tabashi godiya yayi mata sannan yaciro mata kayanta ah boot yana tambayarta wani gari zata”Zaria”,tacemishi kafin yadauki kayan yayi cikin tashan dashi harwurin da akesamun motar Zaria yakaeta sannan yabama mutanen kayan sukasaka ah boot godiya tayi mashi kafin yatafi hakanan tana karema akwalan motocin gurin kallo batasan sanda wasu hawayen suka zubo mataba for the first time zata shiga commercial car ah rayuwarta baki daya hakanan ita bashiga commercial car dinbane damuwarta aa wanda takeyi donshi din bemasan tanayi ba ganin tana kukan ne yasa me karban kudin yace “kiyi hakuri Hajiya ke bakuwa ce ko?”……
Gyada mishi kai tayi ahankali aranshi yace “darabon zansamu wani abu”,kamar mutumin kirki yace kawo kudin motan to,cikin raunanniyar muryarta tace”nawane kudin motar?”…..
Ahankali yace dubu uku yanda ma yan uwan aikinshi bazasujiba babu musu Sumayya taciro kudi ah jakarta tabashi,yar murmushi yayi yana”Hajiya komai na duniyarnan hakuri akeyi,kije kishiga motan kizabi seat,gyada mishi kai kawai tayi sannan tawuce gun motar Sharon ce daman sekawai tashiga gaba duk ah tunaninta driver ze shigo sutafi amma har takwas shiru sema gani tayi wani passenger yazo yashiga baya da mamaki tacema mai karban kudin”Daman ba tafiya zamuyi ba?”……..
Aikuwa gabadaya Yan gurin sesuka kece da dariya hakan bakaramin kona mata rai yayiba amma setayi shiru because she’s not in the mood to deal with them mutumin ne yayi kokarin rike dariyarsa sannan yace”se motar tacika tukun”……
Gyada mishi kai kawae tayi (I want to use this opportunity wurin janyo hankalin masu cutar wasu sabida rashin sani,kusan inbaku biya anan ba zaku biya acan dayawan mutane yan kasuwa sundauki abun nan amatsayin normal thing ne,agurinsu ba komai bane don kunga mutum besan kan guri ba ko besan kan abuba sekuyi taking advantage of their innocence ku cuceshi,it isn’t fair wallahi, what’s there Inka fadi gaskiya, what’s there Inka karbi halal dinka batareda kaci haram ba wallahi tamafi albarka donka cuci mutum kudin bewuce kakashe shi ah ranar ba koma ka kashe shi tahanyar banza gakuma zunubi daka deboma kanka,Allah yasa mudace yakumasa mufi karfin zukatanmu,Amin ya rabbi)….
Motarsu bata tashiba se wuraren karfe goman safe don seda passengers suka gama zuwa haka suka kama hanyar Zaria gabadaya Sumayya ah takuretake sabida seda aka karamata wani namiji ah gaba wai bibbiyu ake zama haka takyalesu batace komai ba don gani take batada lokacinsu ma ita ah yanzu fatanta daya Allah yasaukesu lafiya kawai………..
****
Sulaiman tunda yatashi yayi wanka yafita masallaci besake komowa bangarensa ba don hakanan kawai yakejin takaicin Zaliha din aransa sannan shima yanajin haushin kanshi daya bata hadin kai tunda tun da itake gudunshi,sau nawa yake nemanta but she always shun him down batama la’akari da situation dinsa seyanzu da taga Itama tana takure shine zatazo tayi taking advantage of his innocense,se karfe goma yabar masallaci sannan yakoma bangarenshi don shiryawa yaje yaduba jikin Mai Martaba,samu yayi ko Ina fes fes dashi babu datti hakanan wani sanyayyar kamshin turaren Maiduguri ke tashi ga bayin dakeyima Zaliha aiki sekai kawo sukeyi ah parlourn hakanan suka dinga zubewa suna gaidashi cikeda ladabi dakai kawai yadinga ansa musu kafin yawuce dakinshi nan ma agyare don an tsaftace koina bakamar yanda yafita ya bari dasafe ba kyabe baki yayi kawai sannan yashige wanka abunshi cikin mintuna arba’in yagama shirin shi cikin kayan sarauta sannan yafito daniyar wucewa bangaren Mai Martaba cikin sauri tatareshi da runguma tana”good morning sweetheart”kafin tadago tayi mashi light kiss cikin sigar shagwaba tace”mekatsaya yi waje,I missed you”………….
Tureta yayi sannan yace”Zaliha banason irin haka”…….
Cikin sigar lallashi tariko hannunsa tana”nasan nayi maka laifi but believe me I want to reform now,inason inmanta baya kaima kamanta mu fuskanci future, seyanzu nagane bankyauta maka ba hakanan niba matar kwarai bace daban bi abunda kakeso ba,nayarda kayi hakuri nayi kuskure”,wani harara ya watsa mata sannan yafizge hannunta cikin nashi tareda nuna mata dan yatsa….
“your fake repentance bazai taba shigana ba Zaliha and mind you I’m not that stupid that I’ll believe you so easily,inkinason tuba miyasa bakiyaba tunda seyanzu dakike ganin takusa kwabe maki sannan zaki wani zo ki dameni?”…..
STORY CONTINUES BELOW
“kuma inbaki fita harkataba I’ll deal with you sequarely”yakarashe maganar ranshi ah matukar bace sannan yafice dukda haka binshi tayi tana kadawo kaci breakfast to ko haka zaka fita?..
Kojuyowa baiyi ba bare ya kalleta seda taga ya kule matada gani sannan tajuyo tadawo parlourn tana ajiyar zuciya she’s just trying so hard wurin ganin ya yarda da ita amma shi kwata kwata yaki bata hadin kai ma sede komai zaiyi bazata hakuraba harsaita cinma burinta don haka kawai bata tunanin zatabar Asma’u tayi succeeding,ta zubar mata da mutunci agaban Bayi hakanan kuma itace dalilin dayasa asirin Magajiya ya tonu so,she’ll not let her go like that kamar yanda tacema Magajiya zata cigaba da aikinta,yes zatacigaba sede ba akan kowa se Asma’u, because batada wani goal daya wuce taga Asma’u tana bakin ciki ahyanzu hakanan batada burin daya wuce tarabata da Almustapha wanda ai aganinta daman sabida shi ne take komai inta rabata da gidanma baki daya taga nayi ai, murmushin keta tayi sannan tashiga kiran Lantana …….
Jiki na bari Lantana takaraso gaban Zaliha tareda zubewa kasa tana”Gani Gimbiya” ………
Ah dakile Zaliha tace”nikam bance kinemo min Salma ba tundazu?”….
Kan Lantana na kasa tace”tazo dazu kina wanka shine tace zata koma kada abokanan aikinta sufada ma uwardakinsu tatafi yawo don sunsamata Ido daman inyaso dayanma zata sake dawowa”…….
Gyada kai kawai Zalihan tayi don batason azo abi diddigi ma agano cewa gurinta take zuwa wannan dalilin yasa bataji haushin rashin jiranta da Salman batayiba,”jeki”,shine abunda tacema Lantana din……
****
Seda tagama shirinta cikin supern da yasha design mekyau yayinda flowers najikin atamfan anyi using mint green,white dakuma black bakaramin wanda amsar jikinta kayan yayi ba ahankali tajuyo tadubi Hajja dake breakfast haikan mani’an tace”Hajja nayi kyau?”………
Murmushi Hajja tayi sannan tace…..
“bakadan ba jikalle na”,takarashe maganar tareda ajiye last kashin naman Kazan dake hannunta don tas tayi dasauran, ahankali tawanke hannunta cikin ruwan da aka kawo aroba sannan tace “yanzu kidauki mayafinki kije kima mijin naki magana mu gaisa ko babu dadi tun jiya inanan bamugaisa ba”…
Asma’u seda taji zuciyarta ta buga don dasafe ma yakoma bacci tasilalo tagudu batareda yasani ba itafa shirin zuwa duba jikin Mai Martaba tayi yanzu ba wani abu ba sannan bamatason haduwa da Almustapha din ah yanzu jintayi shiru ne yasa Hajja cewa”yakikayi shiru?”…….
Cikin in Ina tace”yi hakuri Hajja yanzu zantafi”,takarashe maganar tareda bude wordrobe dinta tadauko wani hadadden mint green gyale tayafa sannan tadauki wayarta tafice tana to ki kintsa kafin muzo ko Hajja……..
Gyada matakai kawai Hajjan tayi yayinda Asma’u tawuce dakin Almustapha badan ranta yaso ba samu tayi yagama shirin shi kenan yana sanye da farar shadda abunshi kannan se sheki yakeyi ga wani fresh dayayi kana ganinshi zaka gane kwanciyar hankali yafara zama mai sosai,da kamshin turaren ta yagane isowanta donda tsayuwa tayi daga bakin kofa bayan ta tura kofar……
Yaganta amma seya kyaleta shima don yau jiyake da sarauta zallah bakin gado yakoma yadauki wristwatch dinshi yasaka sannan yadauki hularsa yakoma gaban madubi yasaka hular wanda hakan yakarama fuskarsa wani irin haiba dakyau kafin daga karshe yadauki wayar sa yazo zaifice duk tana tsaye agurin…
Ganin yana niyan fita batareda yakulataba yasata saurin kamo hannunshi kaman zatayi kuka tace…
“fita zakayi bakamin magana ba?”…..
Murmushi yasakar mata kafin yace…
“to mezan cemiki Asma’u,bayan keda kika shigo dakina ko kallon inda nake bakiyiba”,yakarashe maganar tareda janyota zuwa jikinshi yana karema dan simple makeup din fuskarta kallo ga pink lips dinta yasha wet lips daya kara haskaka shi ahankali yace”kwalliyan na menene?”…..
Turo mai baki tayi tana…
“zanje duba jikin Abba nefa,shine nace ba’in fada maka Hajja nanan fa kuma baku gaisa ba tunjiya tare sukazo dasu Asiya”……..
Murmushi yasaki dukdama bason matar yakeyi ba hakanan bayajin zaiji dadin zamanta ah gidannan don tana iya muzgunama Asma’u itakuma bazata taba nuna makowa ba after all she’s her grandmother,sede yazaiyi?…
Ya’isa yace ma Hajja ta tattara inata inata tatafi ne?…….
Sake turo baki tayi ganin yana karema pink lips dinta kallo kafin tace….
“kabari mana Yaya imam,magana nikefa”……..
Batareda yabata ansaba yadaura kanshi kan nata yanashirin hade bakinshi da nata daba karamin burgeshi yayiba ayanzun itakuwa cikin sauri takawar dakanta gefe, murmushi yayi tareda sakinta kafin yafice ah dakin binshi tayi abaya ganin yayi hanyar dakinta da sallama yashiga dakin yayinda ya tsuguna kasa ganin Hajja nazaune bakin gado”Ina kwana Hajja”…………
Cikeda kunya Hajja tace”lafiya Lau Yarima,yakake,yafama da jama’a?”
Munsameku kalau dai?…
Murmushi kawai yasakarmata batareda ya’iya cewa komai ba kafin daga karshe yatashi yana nizan fita Hajja……..
Tashi Hajja tayi tana”adawo lafiya, Allah yabada saa’…..
Aranshi ya ansa da amin kafin yajuya don ficewa Asma’u ma sallama tayima Hajja kancewa zataje duba mai Martaba,adawo lafiya Hajja tayi mata kafin tafice taja kofan dakin sannan tabi bayanshi cikin sauri tana”Fada zaka?”…….
Tsayawa yayi harta iso inda yake kafin suka cigaba da tafiya atare hakanan babu wanda yace uffan cikinsu harsuka isa bangaren Mai Martaba sede yalura tunda suka taho aketa kallonsu hakanan bayin kezubewa suna gaidasu……….
Adakin Mai Martaba suka samu Sulaiman da Dad yayinda Dad din kebama Mai Martaba abinci ah baki da ladabi suka tsuguna suka gaida shi da jiki…………
Gyada musu kai kawai yakeyi don baida karfin yin magana ma da alama begama warwarewa sosai ba gashi dukya rame cikin kwana biyunnan din duban Sulaiman Almustapha yayi”yaushe ya farka Sulaiman?”……
Ahankali Dad yace cikin dare yafarka amma bema jimaba yakomai bacci and likitan ma yazo yadubashi da safe yace Bpn yasauka alhamdulillah amma kada abarshi yafara fita tukunnan don jikinshi begama warewa ba…….
STORY CONTINUES BELOW
Cikeda gamsuwa Almustapha yace”Allah yabashi lafiya”…
Amin cewar Dad da Sulaiman din kafin Dad yakarada “kozaka kirawo Khairiya ne tunda yafarka yake kiran sunanta yana akaishi yaganta dakyar muka bashi hakuri yake breakfast ma yanzu babu yanda zamuyi mubarshi yafita batareda jikinshi yayi kwariba”
Gyadakai kawai Almustaphan yayi dukda kuwa bawai maganar takai har ranshi baneba, because to be sincere bayason yayi dragging Ummi into this, it’ll only hurt her feelings shikuma bayason hakan Allah yagani sede on the other hand kuma bazai iya budan baki yacema Abban bazaiyi abunda yace dinba shiyasa ma kawai yagyada masa kansa sede da mamakinsu sukaji Abban nace wa….
“you don’t to, I’ll go see her myself bata cancanci tazo gurina dakanta ba”……….
Cikeda damuwa Dad yace”To Abdul haryanzu jikinka baigama warwarewa ba haryaushe zaka iya fita fisabilillahi?”…..
Dan murmushin dayafi kuka ciwo yayi sannan yace”you don’t have to worry I’ll wait harsanda naji karfin jikina,hope she’s fine too?”, Mai Martaba yayi maganar yana kallon Almustapha….
Gyada masa kai Almustapha din yayi,sunjima agurin Mai Martaba din kafin suka fice su ukun inda sukabarshi da Dad don baki sunfara yawa masu zuwa duba jikinshi………
“Tunda suka fito daga bangaren Sulaiman yace nikam kwana biyu bamu gaisada Mom ba inaganin xanyi bangarenta tukunnan”,yakarashe maganar tareda canza direction din da sukabi cikin sauri Asma’u tace”zanje nima Yaya Sulaiman”, dariya yayi sannan yace “to Yaya Asma’u”,haka tayi saurin iso Sulaiman din suka fara tafiya tare sakan baki Almustapha yayi tareda binsu da kallo cikeda mamaki wato ma shi ko oho zasuwani tafi subarshi ganin basumasan yanayiba yasashi tabe baki tareda yin hanyar bangarensu don sauya kaya yafice zuwa gun Mallam Hudu gama yakwana biyu bai lekasu ba………
Tundaga nesa Sulaiman yahango wata akwati ahannun dogari kaman na Sumayya amma sebaice komai ba harsuka karasa kofar bangaren sede da mamakinshi Dogarin ma nan yashiga cikin sauri yakirashi da ladabi ya juyo yana mika gaisuwa batareda ya amsa ba yace”kayan wayene wannan”….
Da ladabi Dogarin kecemishi na Sumayya ne bakaramin mamaki yayiba don haka seyace kana nufin itace tadawo?…..
Gyada mishi kai Dogarin yayi sannan yace…..
“Bejimaba taxxi yasauketa akofar masarautar nan tun dazuma tashige gida shine natahomata dakayanta”……
Cikin sauri Sulaiman yakarasa cikin parlourn sede babu kowa batareda yayi wani tunani ba yayi hanyar dakinta sede arufe gam cikin raunanniyar murya yashiga Kiran sunanta”Sumayya,kibude kofar please”……
Haka yadinga kiran sunan ta amma shiru kakeji itakuwa tanazaune bakin gadonta hawaye nata ambaliya hakanan tanajinshi amma taki tashi tabudemai,tomema zaice mata yanzu bayan ko kira yabata hakuri ma baiyi attempting yiba jin kukanta na neman tona mata asiri yasata saurin tashi tashige bandaki wanda rufo kofar bandakin da tayi ne yasashi gane tana cikin daki……..
Cikeda damuwa yace”menayi mata,why is she not opening the door?”, yakarashe maganar yana kallon Asma’u da damuwa……
Itama cikeda damuwan tace”kunyi fadane,ko wani abun yahadaku?”…
Haram Asma’u babu abunda yahadamu wlhy I know I’ve been refusing to answer her calls due to the situation I was in but I never expect her to react this way,bantaba tunanin zatayi tunanin biyowa motar haya tazo gidaba and that’s the most annoying part,she must have suffered alot on her way home,I know Sumayya she’s very fragile”yayi maganar ah rikide hakanan baidaina buga kofar dakin ba daga karshe ciro wayanshi yayi yashiga kiran layinta babu kakkautawa hakanan daga shi har Asma’un suna jin wayar na ringing ah dakin ammataki dauka……..
Dafe kanshi yayi tareda cewa”ya ilahi,jinake kamar in balla kofarnan”,wai what’s wrong with you Sumayya,talk to me,kizo kisauke haushin ki akaina if you’re that angry,come and hit me may be you’ll be at ease after doing that”, yakarashe maganar cikin tsawa tareda buga kafarshi dakarfi ajikin kofar, he’s just so tired of banging the door so yake yaganta ido da Ido ya lallasheta,so yake yaji miye damuwarta why is she so angry with him don yasan wannan fushin dashi ake dondaba dashi take fushin ba yanada tabbacin she’ll look for him first,yana cikin wannan tunanin sukaji tana kokarin bude kofar gabadaya suka maida hankalinsu kan kofar tunkan ta wangaleta yayi saurin bude kofar,kallonta yatsaya yi gabaki daya idanunta sun canza launi hakanan idanunta sun kumbura tsabar kuka cike da takaici takaraso gabanshi tashiga dukan kirjinshi tana”you want me to hit you right?”…
Then I’m hitting you,you want me to beat the hell out of you right?….
“Then I’ll do that”, takarashe maganar tareda fara bugun duk inda tasamu ajikinshi hakanan tana kuka maitsuma zuciya Asmau dake shirin hanata Sulaiman yayi saurin daga mata hannu alamar ta bari seda Sumayya tayi mai isanta kafin tasake kai mai wawan bugu ah kirji tana…
“why am I not feeling at ease,miyasa zuciyata takasa daina kuna haryanzu?”….
Sulaiman baisan sanda yajata zuwa jikinshi ba tareda rungume ta so very tightly,like his life depends on her hakanan idanunshi suka canza launi lokaci guda”I’m sorry Baby, I’m so very sorry Summyna”, yakarashe maganar yana kara sakata cikin jikinshi itakuwa kukan tacigaba dayi babu kakkautawa gashidai shidin ne yabata mata rai and she ended up crying on his body hakanan kuma shine me rarrashin…….
“Asma’u saurin juya kanta tayi ganin yanayin da suke ciki tareda yin gyaran murya amma basumasan tanayiba and she trust them completely wannan dalilin yasata shigewa dakin Mom sede da mamakinta batanan,itamadai tayi mamakin ace Mom nanan anata wannan babatun bata fitoba ai abun da kamar wuya”………
STORY CONTINUES BELOW
Dakyar yasamu ta tsagaita kukan nata kafin yakama hannunta ahankali suka shige dakin nata zaunar da ita yayi bakin gado kafin yatsuguna gabanta tareda hade hannunsu guri guda cikin sigar lallashi yace…..
“kiyi hakuri Sumayya nasan na bata miki rai but believe me that was never my intention,I thought recieving your calls ze iya tada miki hankali inkika jini cikin damuwa shiyasa naki daga calls dinki infact daga karshema kashe wayar nayi sejiya da Yaya Almustapha yakunnata da dare sabida yasha nemana baya samuna, I’m extremely sorry,had it been nasan hakan zaisa hankalinki yatashi dabanyiba yakarashe maganar muryarshi ah raunane”……….
Sumayya daharyanzu hawaye na zuba ah idanunta tace”I think this day will be the end of our relationship Yaya Sulaiman,kadaina ganina amatsayin wanda kakeso please just consider me as your sister,kafara ganina amatsayin su Amira kamar yanda kakeyi ada I think this will be the best for both of us”,takarashe maganar tana goge kwallarta bakaramin jijjigashi maganar Sumayya tayima Sulaiman ba hakanan lokaci guda idanunshi suka kada sukayi jazir,he really can’t believe it,badai Sumayya is trying to leave him because of his Mother ba,badai laifin mahaifiyar sa nason shafan relationship dinsu da Sumayya bane ba tokodai intayi mashi haka batayimashi adalciba hakanan intayi mashi haka tacuce takuma cuci zuciyarshi donkuwa bayatunanin zai iyayima wata irin soyayyar dayakeyimata muryarshi na cracking hakanan idanunshi sunyi jazir yace”are you by any chance leaving me because of my Mother’s deeds?”,wannan karan he couldn’t hold back his tears don zuba sukafarayi ahankali Sumayya da is very shock jin abundama yake tunani tace”haka nace maka?”….
“Why are you trying to blame me,why are you making it as it’s my fault,miyasa kake zargina”,tayi maganar cikin tsawa akan abunda bashike raina ba?”…..
Shima cikin tsawan yace”yakikeso inyi to Sumayya,why will you change all of a sudden hakanan nasan sabida naki daga wayarki be isheki hujjan dazaki furta irin wayannan kalaman ba,if you’re not leaving me because of my mother then kifada min,akan me zakice muyi ending up this relationship!?”….
“Why don’t you go and ask your wife”………
Cikida mamaki yace”kina nufin Zaliha?”…
Wannan karan wani irin harara ta watsa mishi kafin tace”kanada wata matar bayan itane”,in a very confused look yace”me Zaliha tayi maki Sumayya?”,yayi tambayar cikeda damuwa,sakin wani kukan tayi sannan tace”kaje katambayeta mana zata fadama,har ita takeda bakin fadamin magana donna kira cikin dare da ace tasan the situation I was in she wouldn’t have done that besides tama fini gaskiya miyasa zankira married Man so late in the night bayan yana iya kasancewa tareda iyalinshi,miyasa zan takura muku tayi maganar tana kallonshi da idanunta dake cike da tsantsar kishinsa kafin tace”you love your wife don’t you?”………
Damamaki yake kallonta, he’s just speechless and out of words yama rasa maizai cemata hakanan zuciyar shi nayi mashi wani irin kuna da ace Zaliha na gabanshi yanzu da babu abunda zai hanashi kai mata duka Sumayya Jin yayi shiru yasata cewa”she can have you all I’ve no problem with that takarashe maganar tareda juyamai baya”……..
Cikin sauri yatashi yadawo setin inda fuskarta yake kafin yace”kina kokwanton irin sonda nike miki ne Sumayya?”………
Cikin kuka tace”to yazanyi Yaya Sulaiman?”…..
Jinjina kai yayimata ahankali sannan yatashi tsaye yana”I’ll prove you wrong Sumayya”,yayi maganar tareda fita yabar dakin hakanan belurama da Asma’u dake tsaye bakin kofar dakin ba tsabar ranshi na matukar bace barinma masarautar yayi baki daya don yasan muddin yanufi Zaliha yanzu bakaramin maka zatasha agurinshi ba shikuma bayason yazamo daya daga cikin mazajen dasuke dukan matayensu,he don’t want to be a coword like them….
Asma’u karasawa tayi cikin dakin sannan tadafa kafatun Sumayya ahankali tana”Sis kidaina kuka?”……..
Dago kumburarrun idanunta Sumayya tayi sannan tace”inbanyi kuka ba maizanyi Sis Asma’u,i love him so much and I can’t live without him sede it seems like shi son da yakeyimin din bana kwarai bane tunda har ya cuceni”……
Cikeda mamakin kalaman Sumayya Asma’u tace”yacuce ki kuma Sumayya,meye yayi maki?”……
Cikin kuka tace”bakiji conversation dinmu bane nayi tunanin kina bakin kofa ai tunda har kikashigo yanzudin”…….
Sa hannu Asma’u tayi tana goge ma Sumayya hawayenta kafin tace”as far as i know Sulaiman ba cutan ki yayi ba indai har akan abunda naji kuna magana ne”,cikeda Jin haushin Asmau ganin tana kokarin goya ma Sulaiman baya tace”isowar dare nayi fa and it’s all because baya daukan calls dina,I thought something bad yafaru dashi ne shiyasa hankalina yatashi but all I could get was her harsh words after calling his number don ya turomin number Yaya Idriss, haka nakwana ah airport jiya and on top of that nabiyo motar kasuwan daban taba hawaba”,cikeda tausayinta Asma’u tace”sorry on his behalf dukdama aganina aishi babu laifinshi Sumayya”….
Yasan kintaho ne?….
Girgiza mata kai tayi alamar aa,kafin Asma’u takarada”shiyadaga wayar dakika Kira?”….
Nanma aa Sumayya tace kafin Asma’u tace”fine,he didn’t know Zaliha picked your call Sumayya kuma indai kikace zaki biyema wannan matar you’ll end up regretting batada wani buri daya wuce ta batawa mutane rayuwarsu, Yaya Sulaiman abun tausayine hakanan shi mutum ne dayakamata kiyi mishi uziri ah irin abubuwan dayake going through,atunanina babu wanda yakamata yayi understanding pain dinshi kaman ke inkuma kina fushi don ya kwana da matarshi ne gwandama kidaina,kima gode Allah dashiba me neman mata awaje bane Sumayya sannan atunaninki kinyi mishi adalci inkikace bazai kasance da Matarsa ba bayan yanada bukatarta,I really think this’s absolutely not fair Sumayya inanan agabana kwanaki kafin kikoma yayi miki maganar zeyima su Abba maganar kunason juna ayi maku aure amma kika ki,ke kinason ki karasa karatun ki kuma hakan dakikayi baisa yadaina miki sonda yake miki ba,he fully support you and he’s willing to wait despite all the wahala dayakesha gurin matarsa dukda baifadaba but one mere look zakayi masu kagane hakan”, Asma’u takarashe maganar tareda tashi sannan tace”I trust Yaya Sulaiman, he’ll surely prove you wrong, he’ll prove to you that he’s best husband that you could ever ask for kede kicigaba da addu’a kawai”,hakanan Asma’u tafice tabar Sumayyan nata tunane tunane itakadai…..
******
Dayanma Salma taje bangaren Zaliha tareda gaidata batareda Zalihan ta amsaba tace…
“nikam kwanaki danabaki abu kisa ah dakin Yarima kinsaka ne?”…….
Cikeda ladabi Salma tace”nasaka Gimbiya”…..
“To ita Asma’un bata gani bane?”,Zaliha tayi maganar ranta ah bace cikin in ina Salma tace….
“inaganin bata ganiba don inasaka musu ido sosai”……….
Zungurinta Zaliha tayi kafin tace badai kinsa ah inda shizai gani harya daukeba batareda tasaniba,cikin sauri Salma tace”…aa Gimbiya acikin drawer din da yakesa takardunsa nasaka kuma yakan rufe gurin ne sannan su Hindatu bayan wata dai dai akace suna shiga suna kadewa to jibi zasu yi inada tabbacin zasu gani suna kuma iya nunama Gimbiya din tunda ba lallai susan kwalban giya bane”
Jinjina kai Zaliha tayi kafin tace”tashi kije bari mujira zuwa jibin muga inma akwai abunda zakiyimin zan aika ah kiraki”……..To Salma tacema Zaliha kafin tatashi tafita don komawa bakin aikinta………
Dab da sallar maghrib su Hamida suka iso masarautar itada driver din da Sulaiman yatura yadaukota direct bangarenta tawuce directly hakanan ko’ina agyare yake fes fes kaman wanda ba barin gidan tayi na tsawon watanni ba gakuma bayinta dasuka saba mata aiki duk sunanan wanda tana da tabbacin aikin Sulaiman ne wannan din bana kowa ba,dakyar ta’iya zama bakin gado tareda dan dafe kanta hakanan takejin haushin kanta dakuma mijinta na miyasa zaiyi mata har saki uku lokaci guda bayan yasan she’s carrying his Baby and on top of that she love him unconditionally ah dan zaman dasukayi,hakanan tana tunanin halin da uwarsu take ciki ayanzu,bata dawani buri daya wuce taje taganta amma koma miyene she’ll wait for her Brother first dawannan tunanin tatashi tadauro alwala ah bandaki sannan tazo tatada sallah……
Sulaiman baishigo gidaba sai wuraren tara da rabi na dare hakanan bangaren Hamida yawuce direct don tun bayan datayi sallah takira tafada mishi isowarsu……….
Samunta yayi kwance ah dakinta yayinda Laure data kasance Baiwarta tun ada kezaune kasa tana mata massaging kafarta cikeda kulawa don daman asalin ita baiwar Hamida ne inbaku mantaba ko ada haduwarsu da Hajiya Muniba aboye ne sukeyinta don taimaka mata…………
Zama yayi bakin gadon yayinda Lauren tagaida shi cikeda ladabi ansawa yayi kafin yace”bayanzu kinayima Hajiya Muniba aikiba?”……
Gyadamai kai Laure tayi kafin tace”Daman tuncan ah Gimbiya Hamida nikewa aiki kuma sabida tatafine shiyasa nakoma gun Hajiya Muniba amma tunda yanzu tananan shine Hajiya Muniban tace indawo inayimata kaman yanda nikeyi ada tunda nafada mata tafi sabo dani”…….
Sulaiman yaji dadin zancen don yariga yajima dasanin yanda Hamida takeda Laure,tafi yarda da’ita hakanan dukwani aiki dayashafi harkarta tafison saka Lauren sede kuma wani bangaren na zuciyarshi na raya mishi ai Hamidan tadawo dun dun ne bawai kwanaki kadan zatayi takoma ba itakuma Hajiya Muniba tayi tunanin hutu tazota may be shiyasa tace Lauren tazo”,dan kyabe baki yayi sannan yadubi yayar tasa”ya hanya?”……..
Murmushin dayafi kuka ciwo tayi sannan tace alhamdulillah Bro,yakake?……
Dan shafa kanshi yayi yana murmushin yaken shima”not that bad”, Laure dake zaune ganin kaman suna bukatar sirri seta tashi tafice abunta Allah yagani har ranta takeson Gimbiya Hamida amatsayin uwar dakinta hakanan tana fatan Allah yasa kada Itama tacigaba da bin halin uwarta dukda ma ita babu abunda tayi ko ah da din,she was just rude to her blood sisters and tadaura rayuwarta kan yin waya da tsohon saurayinta dakuma social media baki daya wanda hakan yasa batadamu da alamuran mutane baki daya bama…………..
Tashi Hamida tayi tazauna yayinda Sulaiman yadaura idanu kan dan karamin cikin Hamida cikeda takaicin abunda mijin nata yayimata, ahankali yace “Dagaske sakin ki yayi Sis?”…
Gyadamishi kai tayi ahankali yayinda idanunta suka ciko da kwallar da take boyewa tundazu ahankali yajanyota jikinshi tareda rungumeta yana fadin”sorry,you don’t have to worry Allah yasa hakan shiyafi alkhairi”……
Amin Hamida tace tareda karawa da”Amma aikoba komai seyayi tunanin unborn child dinmu ko?”…….
Gyada mata kai Sulaiman yayi sannan yace….
“kinyi mishi wani abunne?”…..
Jijjiga kai tayi alamun a’a kafin tace”from the beginning kaman auren bazai yi kyau ba amma zamana dashi I came to know he’s a very simple and honest person Sulaiman,baida hayaniya and despite him being from a royal family becika girman kaiba wannan kyawawan halayen nasa sukasa nafara sonsa though I never express my feelings but I’ve changed my attitude from being cold to being nice to him dukdama in inason abu nadinga mishi naci kenan harsai yayimin shiyasama danaji labarin abunda yafaru da Mama nadinga mishi maganar zanzo ni gida amma yaki nikuma raina yabaci don aganina ai baikamata yayimin haka ba shiyasa mukayi kaca kaca haryakaishi gayimin saki with which i was very shocked, he’s never like this hakanan baya daukan mataki batareda yayi tunani ba it’s unlike him to divorce me akan silly abu haka”………..
STORY CONTINUES BELOW
Sulaiman dake shafa gadon bayanta yace…
“do you have any enemy over there?”…..
“His Aunt,she never like me sabida taso ‘yarta ya aura and the Daughter too she hates me way too much”,tayi maganar ahankali and kasan GIDAN SARAUTA wani makiyin nakama backstabbing naka zainayi without you knowing,some will pretend to love you while baswa sonka harcikin zuciyar ka”……
Gyada mata kai yayi sannan yace”bazamuyi zargin kowaba ayanzu sabida zato zunubi ne koda yakasance gaskiya,koma miyene we should keep praying and shida yamiki haka he’ll surely come back looking for you yanzu kikwantar da hankalinki,take very good care of my unborn niece Allah natareda mu and please don’t think of doing anything stupid akan Mama komai yafaru da’ita ita taja kuma inafatan yazame maki ishara and believe me harda alhakin mutane data dauka shiyake bin mu ayanzu”…….
Goge kwalla Hamida tayi tareda gyadamashi kai kawai don ita daman babu abunda tayi niyan yi damuwarta ma ayanzu sun isheta dukdama tanason kallon Magajiya din taga wani hali take ciki,dagowa tayi daga jikin Sulaiman din sannan tace bazai yuyu Inga Maman ba?….
“You can’t,babu maiganinta and wannan order ne da Dad yabayar we can’t change it just keep praying for her Allah yasa tagane gaskiya”, Sulaiman yayi maganar murya ah raunane kafin yakuma tambayarta da”kinci abinci ne?”…..
Eh kawai tace mishi kafin yatashi tsaye yana”go to sleep now and if you need anything just let me know,maganan fadama Abba batun divorce dinki kibari seyasamu sauki sosai ganinki ah gida na’iya sake tayar maida hankali kinji”…….
To tace mishi kafin yayi mata saida safe sannan yafice zuwa bangarenshi yauma samun koina agyare hakanan yawuce dakinshi yayi wanka yasauya kaya zuwa na bacci kafin ya kwanta yanason jin muryan Sumayyan amma yasani komi zaiyi bazata taba picking calls dinsa ba don haka kawai seya lumshe idanunshi tareda jan bargo yarufe kanshi,yafi mintuna talatin bacci baidaukeshi ba hakanan yanaji aka bude kofar aka shigo amma baidamu da duba wayebane don yanada tabbacin Zaliha dince…..
Zuwa tayi tashige jikinshi baice mata komaiba dukda kuwa irin kunan da zuciyarshi keyi mishi,itane tafara cewa”Sweetheart inakaje tunsafe daka fita bansake ganin ka ba and na ajiye maka lunch dinka haka dinner ma sede babu wanda kataba cikin biyun”…..
In a very calm voice yace…
“miyasa kika daga min waya jiya?”……
Seda kirjinta yabuga tsabar yanda yayi maganar don dukda ahankali yayi maganar jidaya zakagane akwai bitterness cikin ta……..
Kame kame tafarayi….
“tana ta kiranka ne cikin dare and banason katashi shiyasa nadaga”……….
Sulaiman daya kasa daure zuciyarshi daga zugin da takeyimashi ya yakiceta daga jikinshi tareda yin wulli da’ita gefe wanda harta kusan faduwa daga gadon kafin yatashi yazauna yana nunata da yatsa sannan yace…
“kinsan halin da ta shiga bayan abunda kikayi kuwa”……
Zaliha ma da ranta ke mata kuna tace….
“ita batasan miye darajar me aure bane dazata kiraka da daddare?”…….
Wani harara ya wurga mata sannan yace”dukdai rashin saninta na darajar aure batakai kiba hakanan inada yakinin tafiki sanin darajar aure because ke bakida bakin daza kiyima wani ma irin wannan maganar,I love Sumayya and I want to marry her so,you can’t change that fact gwanda kidauri damara shirya zamada da’ita indai dagaske kikeyi kinyi nadaman abubuwan dakikayi sannan kije kisameta kibata hakuri don ba dagangan takirani ba a irin wannan lokacin,nan yayima Zaliha bayanin abunda yafaru kafin yakara da,inkinje kinbata hakuri only then zaki samu fuska daga gareni sabida nida kika gannin nan banason damuwa I want a peaceful and happy family inkuma ke baki shirya yin hakan ba kina iyamin magana babu takura ni me iya sallamarki ne”,yakarashe maganar tareda komawa yakwanta sannan yace “kifita min ah daki I want sleep now”….
Zaliha jitake kaman ta kwallah ihu haka tatashi tafice zuwa dakinta zuciyarta nayimata wani irin kuna,wai har Sulaiman ne zaice mata zaiyi mata kishiya don ubanshi kishiyarma kuma Sumayya lallai akwai aiki agabanta haka takasa bacci ranar itakadai tana sakawa tana warwarewa hakanan zuciyarta nabata harsaitayi abunda yacedin sannan Itama zatasamu hanyar cika burinta…….
****
Around 10:30pm Asma’u se zubama Hajja hira takeyi dukdai dan karta korata dakin Almustapha hakanan aranta tanata addu’ar Allah yasa bacci yakwashi Hajjan don itama tasamu takwanta ah dakin sede da mamakinta har shadaya da rabi Hajja ko gyangyadawa bata farayiba sema cemata datayi “waike baki tafiya dakin mijinki ne?”…….
Turo baki tayi kaman zatayi kuka kafin tace”Hajja hirafa mukeyi kuma ba bacci nikejiba”…….
STORY CONTINUES BELOW
Rike baki Hajja tayi cikeda mamaki tana”ammana lallai yarinyar nan,harsai kinajin bacci tukunnan zakije dakin mijin naki wallahi Asma’u kiyima kanki fada don inkikayi wasa kinaji kina gani wata zata zo ta kwace miki miji dan ras ras dashi”,Hajja takarashe maganar tareda tashi tsaye tana “baridae kigani”Asma’un kam kasa cewa komai tayi sewani kumbura bakida take tayi itakadai aranta tana itakam datasan haka Hajja take dabazata taba maraba da zuwanta ba wallahi sede kan ta ankara har Hajja tajanyo igiyar charger tana”jirana kikeyi ko,to ganinan nazo”, takarashe maganar tareda yin kan Asma’un tana”yarinyar da kyaunki da komai zaki jamana kishiya don rashin hankali na damunki,to miyema auren don gidan ku?”………
Asma’u tunda taga Hajja tabiyota tafice aguje batareda tadauki wayarta bama bare hijabi tana Hajja kibarni indauki hijabi na da wayana please,wani harara Hajja ta daka mata tareda tura kofar tarufeshi gam tana”inbaki zuwa dakin nashi seki kwana anan tsaye”………….
Babu yanda Asma’u ta’iya haka tawuce dakin Almustapha don yaukam ko tsayuwa ah parlourn ma batayiba,yanajinta tatura kofar dakin amma yayi kamar bejiba sema sake jan blanket dayayi yarufe kanshi dashi donshikam harya kwanta tundazu dukdama yakasa bacci,he was just feeling as if something is missing hakanan minti minti yakeji tana fado mishi arai dukda yakasa yarda cewa itace dalilin hanashi baccin yau,koda tashigo wutan dakin ah kashe yake se bedside lamp dake kunne ganin hakan ne yasa tayi tunanin yayi bacci…
Karema gadon nashi kallo tayi tareda maida kanta ga sofa din dake gabanta dan gajeren tsaki tayi tareda komawa ta kunna wutan dakin sannan tawuce gurin wardrobe dinshi bude wanda take tsanmanin samun bargo aciki tayi sannan tadauka takoma takashe wutan sannan tadawo takwanta kan sofa din tareda lullube jikinta bakidaya sede har wajen mintuna talatin bacci yakasa daukanta bata ankara ba kawai taji an yaye bargon wani irin bude idanunta tayi cikin sauri amma kanma tace wani abu harya kwanto jikinta tareda maida musu bargon ya lullube su kaman zatayi kuka tace”Yaya Imam!”………….
Batareda ya kulata ba yasa hannunshi ah waist dinta ya rungume yana sake gyara kwanciyar shi,shikanshi yarasa dalilin dayasa yakasa bacci yaudin shikadai hakanan zuciyarshi tabashi dayaje gareta may be he’ll be able to sleep peacefully,jin yayi shiru ne yasata kara cewa”Yaya imam dai?”……
In a very cool voice yace”Uhmmm”……
Turo baki tayi ah wuyanshi wanda kesashi jin wani yaaar kafin tace”ammadai kasan gurin nan bazai ishemu bako?”………
Yar murmushi yayi yana”dakin wayene?”……
Kaman wata karamar yarinya tace”naka”….
Dago da fuskarta yayi yana kallo kafin yace”Better,so kinga I’ve the right to sleep wherever I want to ko?”…
Kaman zata fashe da kuka tace”gori zakayimin to?”…….
Dan zare hulan dake kanta yayi still yana kallon kyakyawar fuskarta tareda shafa gashin kanta kafin yace”nidai bance ba”…..
To ka barni inkoma gadon ni don nan yayi mana kadan, kawai jitayi yamaida kanta kirjinshi tareda kai bakinshi kunnenta yana”shhhhhhh,and I’ve the right to decide on where my visitor will sleep tunda dakina ne remember!,so, go to sleep now”………
Batasan sanda tayi shiruba jin yanda yayi maganar yayinda ahankali yakuma dago da fuskarta tareda kissing forehead dinta calmly sannan yace”Good night Wife”……..
Itadai batace mishi komai ba harta fara jin saukar numfashin shi ajikinta da alama bacci yadauke shi dagowa tayi tana kallon fuskar shi so cute,gashi yana baccinshi peacefully cikeda rashin damuwa batasan sanda murmushi ya subuce mataba hakanan ta tsinci kanta da pecking forehead dinshi Itama sannan tamaida kanta jikinshi tana mamakin shi din wani irin mutum ne,ba ajimaba Itama baccin yayi awun gaba da’ita……….
*****
Washegari jikin Mai Martaba yayi sauki sosai don yaukam har parlour yafito yayi breakfast dinshi tareda Dad seda suka gama sannan yadubi tilon Dan uwan nashi yana”I’m feeling okay now”…..
Murmushin Dad yayi sannan yace” And I should take you to your Darling Khairiya”…….
Dariya Mai Martaba yayi kawai sannan yagyada mishi kai tareda cewa”Ya akayi kasan abunda yake raina”……
“Lol, I’m your One and only Brother remember?”,cewar Dad din murmushi Abba yayi dukdama shikam bawai yatuna komai bane na rayuwar soyayyar dasukayi ammadai he’s quite sure komai da akafada din gaskiyane tunda gashi harda shaidu and she has suffered alot because of him sabida haka yakeson yadawo mata da happiness dinta by asking for her forgiveness itada Ya’yanshi and yanason ya roketa kan ta aureshi so that they can start afresh sumanta baya su fuskanci future hakanan sucigaba da addu’ar Allah yabashi ikon tuno memories din baya don he really want to remember each and everything that happened back then atleast it’ll help him to build a better future dukdama yana ganin shikam yanda suka tsufan nan wani rayuwa ne zasuyi na jimawa?…
Sede koma miye ne hakanan koma shekaru nawane suka ragemai he want to spend his remaining time with his loved one’s ba,ba masu yaudararsa ba dason ganin downfall dinsa………..
STORY CONTINUES BELOW
Dad dakanshi yataimaka mishi yatashi kafin suka fita daga bangaren nashi hakanan dogaraye nabinsu ah baya har suka isa bangaren su Almustapha inda dogarayen suka tsaye daga waje yayinda su Dad din suka karasa ciki da sallama………
Parlourn babu kowa hakanan ko’ina agyare yake fes fes yayinda babu abunda ke tashi agurin se kamshin turaren wuta medan karen dadi wanda ke tafiya da zuciyar me shaka wanda wannan din duk aikin Asma’u ne sabida shirin tarban abokin mijinta Dr Na’im da Almustapha yafada mata yauda safe kan cewa yace zaizo lunch gurin amarya ayanzu hakama tana kitchen tana karema kayan abincin kallo, gabadaya tarasa mezata dafa masa wannan dalilin yasa tashiga kiran Almustapha din,aikuwa seda wayar takusa tsinkewa sannan yadaga sallama tayimai kafin ya ansa….
Ashagwabe tace”Yaya Imam narasa mai zan dafama abokin ka”…….
Dan sosa kanshi yayi tareda kallon Na’im dake gefenshi sannan yace”komiye ma kiyi, it’ll be okay…..
Sake turo baki tayi kaman tana gabanshi”ayya am to katambayeshi mana miye favourite dinshi”,cikeda takaici yace “I can’t”,sabida shi haushima tabashi bata taba tambayarshi mezaici ba komai taga dama girkamai takeyi amma dayake abokinshi zaizo harwani special abu takeson dafamai,lallai ma yarinyar nan”……..
Itama rai bace ta katse wayar tana mita”ba laifinkabane ba laifina ne dana kira miskili irinka”……
Hindatu dake gefe dariya tayi sede kafinma tayi wani magana sukaji Rukayya tashigo aguje tana haki kallonta sukayi dukansu biyu yayinda tace”Mai Martaba yazo,cikeda kidima Hindatu tace kina nufin bangaren nan?”……..
Gyada mata kai tayi, Hindatu da damuwa tace shine ba afadama bare agyara guri sabida tarbansa fisabilillahi itadai Asma’u dariya ma suka bata yanda duk sukabi sukawani rude kafin taraba tagefensu tafice tana ku kawo musu kayan motsa baki………
To kawai sukace yayinda takarasa parlourn fuskarta daukeda murmushi ta tsuguna tareda gaidasu Abba din…..
Shine yafara cewa”Daughter yakike?”…..
Lafiya Lau Abba ya karfin jiki?…
“Alhamdulillah” yabata amsa yayinda Dad yace Almustapha yafita ko?….
Kanta nakasa tace eh Dad anma Ummi naciki, murmushi Dad yayi sannan yace kicemata tanada baki cikeda jin dadi Asma’u tatashi tawuce dakin Ummi inda tabar Abba kirjinshi nata dukan uku uku haka su Hindatu suka kawo kayan motsa baki suka koma kitchen………..
Asma’u kuwa koda tashiga dakin Ummin samu tayi tana shafa mai da alama ma daga wanka tafito,harta juya don fita tabata guri taji Ummin nacewa”yazaki koma kuma?”….
Cikeda kunya tace”Ummi inkingama shiri zandawo”…..
Dariya Ummi tayi sannan tace zo zauna abunki nagama ai kaya kawai znsaka,hakanan babu yanda Asma’u ta’iya dole takoma tazauna sede wasa tashigayi da hannunta har Ummin tagama sa kayanta kafin tace”I’m done,hope I’m safe Habibty?”…..
Dariya Asma’u tayi sannan tace”laa Ummi bakine fa kikayi ah parlour”,”Baki kuma,daga Ina”, Ummi tayi tambayar cikeda curiosity…..
Ahankali Asma’u tace…
“Su Abba ne da Dad”………..
Take Ummi taji gabanta yashiga bugawa dakyar ta’iya cewa”kice musu bananan don Allah Habibty”,jiki asanyaye Asma’u takarasa ga Ummin tareda riko hannunta sannan tace”Ummin mu”…….
Dagowa Ummin tayi tana kallon surukartata nervously,kallo daya zakayimata kagane cewa bakaramin tashi hankalinta yayiba lokaci guda in a very calm voice Asma’u tace…
“what will you gain by running away from him Ummi?”……..
Shiru Ummi tayi yayinda idanunta suka ciko da kwallah lokaci guda,magana Asma’u tacigaba dayi”it’ll only bring you pain Ummi,you need to be happy as well,it’s high time you forget about your past and move on besides miye laifin Abba,shima cutanshi akayi he was never at fault”……
Ummi batasan sandama tafara kukaba secewa datake”I know Habibty,he was never at fault I’m just too nervous it’s been long bamu haduba banshirya ganinshi yanzuba kigane Dear,banshiryaba”Ummi tayi maganar tana kuka murmushi Asma’u tayi tareda kwantar da Ummin ajikinta tana”to Ummi tunda baki shiryaba no one will force you kikwantar da hankalinki I’ll go tell them that you’re sleeping”……..
Gyadakai kawai Ummin tayi dakyar Asma’u ta lallashi Ummin hartayi shiru kafin tatashi tafita jiki ah sanyaye Allah yagani batason yimasu Mai Martaba karya sede yazatayi?……
Karasawa tayi garesu kafin tace”tana bacci”….
STORY CONTINUES BELOW
Dad ne yayi murmushi irin nasu na manya kafin yace”tadai ki fitowa ko Daughter ?”…….
Asma’u dai kunya kamar zatayi yaya yayinda Dad yadubi kanin nashi sannan yace”let’s go we’ll come back later semuji shidinma wani excuse za ayimana,mudai munsan bazamu gajiba”……….
Abba dake gefe yace”I’m not going anywhere zanjira harta tashi”……
Dad baiyi mamakiba hakanan yasan Mai Martaba da kafiya don haka seya sallami Asma’u sannan yashiga kiran layin Almustapha yace masa yazo gida yanzunnan haka yafadama Mom, Hajiya Muniba,Sumayya Sulaiman da Hamida da tuni Sulaiman yafada masa tazo gida and he told him everything about her,yafison ayita takare yau din tunda Mai Martaba dinma is being stubborn………
Wuraren karfe daya kowa yagama hallaruwa except Afiya da Amira dake school wanda suma anje daukosu yanzu don haka Dad yace su mazan suje suyi sallah kafin isowan su Afiyan aikuwa hakan akayi zuwa karfe biyu kowa is ready hakanan Almustapha dakanshi yashiga ya yi convincing Ummi tafito dukda shima he’s against it sede yazaiyi………
Yana rike da hannunta suka shigo parlourn hakanan tunda suka fito daga dakinta Mai Martaba yazuba mata narkakkun idanunshi yayinda zuciyarshi ke raya mishi anya wannan mahaifiyar Almustapha ce?…..
She still looks very young da in ancemaka ita tahaifeshi zaka iyacewa bahaka baneba sede irin masifar kaman dasukeyi ne kadai zai iyasawa kayarda don wanda yacika musuma cewa zaiyi yayarsa ce,yasan Khairiya dajimawa he knows her face sede rayuwar dasukayi na dadi ne yakasa tunawa baki daya,karasowa sukayi cikin parlourn tareda zama yayinda Dad yayi gyaran murya tareda bude taron da addu’a kafin yace ma Mai Martaba yayi magana………
Mai Martaba dake feeling nervous yadubi side din da Ummi take yace”Khairiya!”……
Yanda yakira sunanta batasan sanda hawaye suka fara zuba ba she’s been waiting for this very day,ranar da Abdulrahman dinta zai budi baki yakira sunanta dawannan kakkausar muryar tashi medan karen amo da dadi,tsabar yanda takeji kasa amsa kiranma tayi sema dago idanunta datayi tasaka cikin nashi”……..
Ahankali yacigaba da magana shima yana kallonnata”I don’t know what you and my children went through hakanan I wasn’t there with you to support you but believe me after knowing all that happens I can feel the pain Khairiya dukda nasan bazaikai nakuba hakanan nasan no matter how I try bazan taba iya gushe abubuwan daya faru daku ah baya ba but I’m still asking for your forgiveness, I’m sorry for not being a trustworthy husband and I’m sorry for leaving yourside during those harsh moments”, Mai Martaba yayi maganar tareda folding hannunshi hakanan idanunshi sun canza launi lokaci guda Ummi dake gefe cikeda tausayinshi tace”it was never your fault Abdulrahman tunda jimawa nasan da haka and believe me right from that day nariga na yafemaka, Allah yayafe mana baki daya”, besan sanda hawaye yayi slipping ah idanunshi ba hakanan yana mamakin”how can someone be as kind as she’s,after all that happened tayafe mishi so easily,adaidai wannan lokacin yagane cewa yayi loosing mace abaya hakanan yayi loosing uwar Ya’ya tagari”,dakyar ya’iya cewa thank you kafin yadubi su Almustapha din tareda sake folding hannunshi yana shirin neman yafiyansu akaro nabiyu amma dasauri Afiya da Amira suka karaso gareshi tareda shigewa jikinshi suna kukan farin ciki, Amira ne ta’iya cewa”Don Allah Abba karkace komai, we’ve forgiven you for a long time now and munsan ba laifin ka bane ba”……
Yayinda Afiya tace”let bygones be bygone Abba”…….
Lumshe idanunshi yayi tareda shafa kansu hakanan yanajin kaunar yaran nasake ratsa cikin jikinshi babu abunda yake furtawa se alhamdulillah because he never thought it’ll be this easy barinma ta bangaren Ummi……
Hamida dake gefe tana ganinsu idanunta Itama suka ciko da kwallah kafin tayi breaking silence din dake parlourn tahanyar tashi takarasa kusa da Abban sannan takira sunayen Afiya da Amira ahankali….
Dagowa sukayi suna kallonta atare yayinda tayi fuskar tausayi in a very calm voice tace”I’m a very horrible Sister,i cheated you girls,nayi making life dinku miserable back then but believe me I regret all that I’ve done, I’m really sorry”, takarashe maganar tana kuka mai tsuma zuciya Afiya ne tashiga goge mata kwalla tareda sakin murmushi…
“what’s the need to say all this Sis?”……
Yayinda Amira taje saitin kunnenta tana”kinbude little secret dinmu yanzu seda kikasa Abba yaji”………..
Hamida batasan sanda ta rungumi yan kannen nata ba tsabar kauna da nadaman abubuwan da tayi masu abaya, Abba dake gefene yace kuskus din me kukeyi?…..
Dad ne yace”kyalesu sunfi kusa inkace zaka shiga kuma kaine dajin kunya gwandama mukoma inda mukafi kauri”,Dad yakarashe maganar tareda tashi tsaye dasauri Mai Martaba yace”To angama maganarne tukun?”…….
Wara idanu Dad yayi tareda sake komawa yazauna yana”to ai bansaniba nadauka iyakacin maganar daza ayi kenan ah taron”……..
Dariya su Sulaiman sukayi yayinda su Hamida ma duk sun juyo yanzu suna kallon Abba da Dad din………
Wannan karan Hajiya Muniba ne tace”ah to nimadai inabayan Mai Martaba nasan dai maganar nan dasaura”…….
“Lol,to ai shikenan anbarmuku kukarasa”,cewar Dad din murmushi Hajiya Muniba tayi sannan tadubi bangaren da Almustapha da Ummi kezaune ahankali tatashi sabida dizziness datake yawan ji kwanan nan kafin takarasa inda suke tareda zama gaban Ummin itadai Ummi kanta nakasa takasa cewa komai tundazu ahankali Hajiya Muniba takamo hannunta wanda hakan yasa Ummin dagowa tana kallonta itama murmushi Hajiya Muniba tayi kafin tace”zan ari bakin Mai Martaba inci mishi albasa dukda baifadaba nasan abunda yake ranshi kenan,don Allah Aunty Khairiya kiyi hakuri kikoma dakin ki,kiyi hakuri kimanta baya kucigaba da rayuwarku da Mai Martaba kaman da it might sound weird to hear this from me but believe me I’m saying it from the bottom of my heart,inasonki amatsayin abokiyar zama sannan Mai Martaba was a friend and a Brother kafin yazama mijina and from all labarin danaji nasan farin cikinshi lies in you Aunty.so,I want you to bring back that happiness please”………..
Dad dake gefe yayi murmushin jin dadin abunda Hajiya Muniba din tayi kafin yakarada….
“indai anyafe mana ayi hakuri akarbi kokon bararmu to”……..
Ummi kam kasacewa komai tayi se hawayen farin ciki wai itane yau akecemata takoma dakin mijinta,mijintan ma Mai Martaba…….
Mai Martaba daya gaji dajiran jin ansa daga gareta yace”Khairiya kindaina so na ne?”,yanda yayi maganar seya baka tausayi wani irin harara ta wurga mishi tana murmushi”ni haka nace maka”….
Dariya yan parlourn suka kece da yayinda Sulaiman yayi dungure yana”Ya Allah wanga soyayyar tsofi ta burgeni, Allah kasa Sumyna tasoni irin haka koda furfurata”………
Aikuwa gabadaya suka maida kallonsu kanshi suna dariya seda yagama dawowa daidai sannan yagane baran baramar dayayi cikeda jin kunya yashiga sosa kai Sumayya kuwa jitake kaman ta nutse kasa tsabar kunya……
Dad ne yadubi Sulaiman din cikeda tsokana donshi tuni yariga daya ganosu tunba yau ba sannan yace”naji kaman kace wani abu Son?”……
Kame kame yafarayi”uhm Abba, Dad daman wai,daman”…..
Dariya sukayi duka Dad din na “oh kanason ‘Yartawa bazaka iya fitowa kafada ba da nayi niyan baka amma tunda you’re not sure of your feelings se inbama wani kawai”……
Ai Sulaiman baisan sanda ya’isa gaban Dad dinba yana”Wallahi Dad inasonta,I love her so much kawai banason fadane batareda nanemi izinintaba”……
Murmushin jin dadi Dad yayi sannan yace”to alhamdulillahi batunyauba nikeson hada irin wannan zumuncin sede nibamaison in takurama yara baneba shiyasa nazuba muku idanu, Allah yasanya alkhairi indai tani ne nabaka Sumayya halak malak Sulaiman because I know you’ll be the best husband ever”…….
Murmushi Sulaiman yayi yana”nagode Dad”…..
Abba dake gefene yace”kujimin danyen hukunci ita tace tana sone?”……
Lallai Abdulrahman bakasan yaran nanba,tunyaushe suke kus kus batareda munsaniba I’m very sure sun fahimci juna besides koba ta so zamatafara so”,cewar Dad din….
Aa bazaayi haka ba inji Abba kafin yajuya ga Sumayyan yana”Zonan Daughter”…..
Sunne kanta tayi cikin cinyarta don hakanan setaji yau tanajin kunyar Abban sosai,dariya Dad yayi mashi sannan yace”kagani ko”….
Still Abban bai daddaraba yace….
“kinason Sulaiman Sumayya,fadamin inkinason shi inko bakyaso babu maiyi maki dole kinji Daughter na”,yayi maganar cikeda rarrashi,Sumayya tashi tayi tashige dakin su Afiya datake ganin yafi mata kusa dasauri hartana neman yin tuntube tsabar kunya…..
Alhamdulillah shine abunda Abban yace kan kacemi Sulaiman yatashi zaibita Dad ne yace”kaji marar kunya”,dariya Abba yayi sannan yace”kyaleshi gado yayi wallahi don nidai yau nikeso amaida min Matata”, Sulaiman dabaikai ga karasawa dakin da Sumayyan take ba yayi saurin juyowa yana”Abba nima wallahi inda hali ahada adaura bayan sallan la’asar ga sadakina ma ahannu, Sulaiman yashiga lalumen kudi cikin aljihunshi”………..
Murmushin Dad yayi sannan yace Allah yashiryi Father and Son kumadai baza abi maganarkuba sabida suma matan sunada right hakanan suna bukatan lokaci su shirya so do not rush muyita addu’a Allah yazabi abunda yafi alkhairi kawai……
Amin suka amsada yayinda Mai Martaba yace”gobe zamuyi magana da yan fada semuyi finallizing date din nadin sarautan Almustapha inyaso se ahada da bikin baki daya don inban mantaba suma ba ayi bikin aurensu ba ance zaabari se lokacin nadin sarautarsa…. 2
Gyada kai Dad yayi yayinda Almustapha yadago yana kallon Asma’u wanda Itama daidai lokacin tadago da kanta……
Murmushi yasakar mata wanda batasan dalilinsa ba kawae se Itama tamayar mishi aranta tana”kode dadin ze rabu dani yake ji?”…..
Haka aka rufe taron da addu’a yayinda mazan suka fice don wucewa masallaci already har ana kiran sallar la’asar……..
Asma’u dayau tayi wankan tsarki tayi sallar laasar Itama sannan tadawo kitchen tana ta mitan itafa tarasa mezata girkama Dr Na’im gashimadai da alama yafasa zuwa lunch din sede dinner may be tunda bataga Almustaphan yazo tareda shi ba kuma shima urgent call akayi mashi kan yadawo gida, Hamida ne takaraso kitchen din fuskarta daukeda murmushi tana”Sister Inlaw surutun me kikeyi ke kadai?”……..
Juyowa Asma’u tayi cikeda damuwa tana”laa shine kikazo harnan dakin fadi me kikeso za akawo miki har daki”…….
Yanda Asma’un tayi seda tasa Hamida dariya,dakyar ta tsagaita sannan tace”bafa wani abu nazo nemaba gurin ki nazo muyi hira”….
Cikeda jin dadi Asma’u tace…
“muje dakina mana to”…..
Girgiza matakai Hamida tayi tana”ba aiki zakiyi bane?”….
“I can do it later ai”,aa muyidai tare ko sokike kibarmin Dan uwa da yunwa?….
Dan shafa kai Asma’u tayi kafintace”ama abokin shi zanyima girkifa I’ve been thinking of what to cook for him because this’s the first time dazaizo gidannan cin abinci”……..
Dariya Hamida tayi”Is he also a Doctor?”….
Gyada kai Asma’u tayi yayinda Hamida tace”just cook something not that heavy kinsan Doctors da iyayi basu cika son cin abinci menauyiba da dare”…..
Something not heavy like?….
Murmushi Hamida takumayi ganin yanda Asma’u tadamu unnecessarily kafin tace”like jollof din dankali kina iya yinshi ruwa ruwa and zaki iya saka vegetables like ganyen albasa or alayyahu aciki yanda zaisashi yin kamshi da kyau”…..
Seki mishi black tea me hadeda kayan kamshi if you’ve,godiya Asma’u tayi mata tana”Zaki tayani ko?”…..
Wara idanu Hamida tayi tareda cewa”I don’t know how to cook fa”…..
Cikeda mamaki Asma’u tace”really?”…..
Gyada matakai Hamida tayi sannan tace”nadaisan haka Doctors suke shiyasa nafadamiki hakan but inzaki koyamin inaso,I really want to learn how to cook”…….
To kina gani,cewar Asma’u din yayinda suka shiga aikin girkin tare tana nuna ma Hamidan yanda zatayi harsuka gama suka zuzzuba ah kwanukan dasuka dace sannan suka wuce dakin Asma’un tana “Aunty Hamida nagaji wallahi”…….
Zama Hamida tayi tana”aidole kin aikatu ba kadan ba ai”…..
Murmushi tayi tareda dago wayarta tana dubawa nan taga massage din Almustapha nakan cewa Na’im din yace sai dare zaizo wurgi tayi da wayar tana mamakin yanda akayi Hajja tasaba da Ummi sosai yanzu haka tasan tanacan gurinta tanata yimata zuba……
Harsu Afiya suka dawo daga islamiya Hamida nanan bangaren nasu hakanan takejin batason barinsu sabida kota koma can bangarenma she’ll just be lonely……..