Cikakken tarihin Abdul d one
SUNA: Abdulkadir Muhammed
INKIYA: Abdul D One
AIKI: Mawaki
AURE: A Shekarar 2022
MATAKIN KARATU: secondary
GARI: Katsina
KASA: Nigeria
WANENE ABDUL D ONE
Abdulkadir Muhammed Wanda akafi Sani da Abdul D One ya kasance shahararren matashin mawakin hausa mai cike da dumbin basira.
Sanna yakasance babban yaron umar m shareef a harkar waka
HAIHUWARSA
Anhaifi mawakin ne Abdul d one a garin funtuwa dake jahar katsina a Nigeria
KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN ADAM A ZANGO
KARATUN SA
Kana matashin mawakin abdulkadir Muhammed ko kuma Abdul D One yayi karatunsa na matakin primary da secondary ne a mahaifarsa cikin garin funtuwa dake jihar katsina
FARA WAKA
Mawakin Abdul d one ya fara waka tun da jimawa a
mahaifarsa funtuwa sannan ya farane da wata waka da yayiwa wani gidan Saida ruwa (fiyo wata) domin tallata hajarsu.
Sannan bayan wani lokaci Abdul d one ya koma jihar Kaduna wadda hakanne yayi sandiyar haduwarsu da Jarumi Umar M Shareef
DAUKAKARSA
Daukakarsa ta farane tun bayan fitowar wata wakarsa me taken Abin da yake raina wadda aka saka a fimdin mansoor kuma jarumi sannan mawakin Umar m shareef ya hau wakar hakan yasa wakar ya samu daukaka wadda a iya cewa wakar itace itace bakan da miyarsa.
KUNDIN WAKOKI (AlBUMS)
Mawakin abdulkadir Muhammed (Abdul D One) yayi Albums da dama a tsawon rayuwarsa na mawaki
kamarsu
-Sako dagazuciya
-Narike so
-Kece tawa
-Tushen alkawari
Dadai sauransu
Aure
Mawakin yabada mata Daya wacce ya aureta a farkon Shekarar 2022.
KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN HAFSAT IDRISS
JERIN WAKOKI
sannan yayi wakoki da dama da suka hada da
_Wakar fimdin Mansoor
_Abinda yake raina
_Wakar fimdin Jaruma
_Mahaifiyata
_Maryama
_Zainabu
_Ina sonki
_Matata
_Akwai bayani
_Shalelena
_Kasata
_Sako daga zuciya
_kece tawa
_Nana Aisha
_Hafsat
Dadai sauransu
Sannan jarumai da dama sunsha hawa wakokinsa
Cikin harda
*Jarumi Adam A zango
*Jarumi KB international
*Jarumi Umar m shareef
*Jaruma Maryam yahaya
*Jaruma zee pretty
*Jaruma maryam ab yola
Dadi sauransu
HADAKa
Sannan ya samu damar yin waka tareda mawaka da dama daga cikin mawakan hausa kamarsu
*Umar m shareef
*Hamisu breaker
Dadai sauransu
KARIN BAYANI
sannan kamar yadda mawakin ya zayyana
Tun yana karami yake da ra,ayin waka hakan yasa bayan yagama makaranta ya sunduma izuwa harkar waka
Kana wakar da tafi burgeshi daga cikin wakokin nasa itace waka me taken “abin da yake” raina wadda aka saka a cikin fimdin mansoor
Duk dacewa bai San adadin wakokin nasa ba amma dai itace bakanda miyarsa daga ita kuma sai waka me taken
Mahaifiya
Sannan kamar yadda yacigaba da fadi mawaki kafin haduwarsa da umar m shareef hassan crown ne megidansa a harkar waka amma a yanzu bashi da wani megida bayan Umar m shareef
Saidai duk da mawakin bai sanar da tarin kyautar girmamawar da yasamuba amma yace yasha karban kyautuka da dama daga wajaje da yawa
Zaku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube mesuna NW HAUSA TV domin samun Karin bayani dangane da cikakken tarihin abdul d one