CIKAKKEN TARIHIN ABUBAKAR BASHIR MAISHADDA

Cikakken tarihin abubakar Bashir maishadda

SUNA: Abubakar Bashir abdulkarim

INKIYA: Abubakar Bashir maishadda

SHEKARU: 1991 (shekaru 30)

AIKI: producer

MATA: Hassana Muhammad

GARI: Kano

KASA: Nigeria

 

Cikakken tarihin abubakar Bashir maishadda
Maishadda tareda amaryarsa Hassana Mohammad

WANENE BASHIR MAISHADDA

Cikakken sunansa Abubakar Bashir Abdulkarim wadda akafi sani da abubakar bashir maishadda ko kuma maishadda yakasance shahararren furodusa a masana,antar shirya fina-finan hausa na kannywood wadda za’a iya cewa babu kamarsa a wannan zamanin duba da yanayin gwazonsa abangaren aikinsa na producer da yadda ya dauki Sana,arsa da muhimmanci yake kuma mutuntata.

Maishadda yakasance na hannun daman jarumi ali Nuhu hakanyasa a duk lokacin da ya shirya fim Ali Nuhu yake bada Umarni kokuma yafito matsayin Jarumi.

HAIHUWA

An haifeshi ne a Shekarar alib 1991 a watan December a jihar kano karamar hukumar Dala a unguwar dan dishe.

Sannan Yakasance dane gaAlhaji bashir abdulkarim dakuma Hajiya safiya Sani na’ibi.

Shine mamallakin kamfanin maishadda global resources ltd Kamfaninda a yanxu za’a iya jerata a matsayin kamfani na Daya zuwa Uku na masana’antar.

KARATUNSA

kana yayi karatunsa na primary school da secondary school hadi da makarantar gaba da secondary duk a jihar kano.

AURE

AB Maishadda yayi aure a ranar 13/03/2022 Wanda amaryarsa takasance daya daga cikin jaruman kannywood wacce tauraronta ke kan haskawa wato Jaruma hassana Muhammad yusha’u wadda akafi sani da hassana Muhammad.

Cikakken tarihin abubakar Bashir maishadda
Maishadda

FARA FIM

Abubakar bashir maishadda ya fara harkar fim ne a shekara ta dubu biyu da sha biyu (2012) amma ya fara shirya fina-finai nasa na kansane a shekarar alib dubu biyu da sha hudu (2014).

Acewarsa izuwa yanzu yashirya fina-finai wadda baisan adadinsuba a masana’antar ta kannywood.

Sannan yace mahaifinsane wadda yasa masa ra’ayin harkar fim saboda tin yana karami duk wani sabon fim na Hausa da ya fito a bakinsa ake fara samun labarin fimdin a unguwarsu  yana fitowa mahaifinsa zai sayo musu su kalla.

Karanta CIKAKKEN TARIHIN DADDY HIKIMA

JERIN FINA FINAI

sannan ya shirya fina-finai da dama a masana’antar ta kanywood a masayinsa na furodusa da suka hada da.
_Hauwa kulu
_Mariya
_Hafeez
_Sareena
_Jaruma
_Ciwon idanu
_Gidan abinci
_Biki budiri
_Burin Fatima
_Mujadala
_Dijen rama
_Bintu
_Fati
Dadai sauransu.

Kuma fim da yafi birgeshi daga cikin fina finan nasa shine (Hauwa kulu) duba da darasin da fimdin ya isarwa al,umma

An shirya fim din ne saboda yadda matsalar fade ya addabi jama’a kuma fimdin ya fadakar sosai game da hakan.

Wakar da tafi birgeshi itace wakar fimdin mariya wadda mawaki umar m shareef ya rera.

KYAUTAR GIRMAMAWA

Kana yasha karban kyautukan girmamawa da dama kamarsu.

• Africa magic viewers choice award 2015 Matsayin best producer

• Africa magic viewers choice award 2016

Matsayin best film producer
• City people entertainment award 2017
Matsayin best producer

• Zuma festival award 2019 best producer da fimdin mariya

• City people entertainment award 2020 best film da shiri mesuna Hauwa kulu

KARIN BAYANI

Kana kamar yadda ya zayyana abubakar bashir maishadda babban burinsa a rayuwa shine yaga cewa ya shirya fim a duk wata masana,antar shirya fina-fiani na duniya kamarsu:

Hollywood
Bollywood
Dollywood
Tollywood
Dadai sauransu

amma ba a iya masana’ntar kanywood ba ko kuma nollywood.

Daku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube mesuna NW HAUSA TV domin samun Karin bayani dangane da cikakken tarihin abubakar Bashir maishadda.

https://youtu.be/REqnK7cpi1U

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *