Cikakken tarihin jamila umar nagudu

Cikakken tarihin jamila umar nagudu

SUNA: Jamila Umar turaki

INKIYA: Jamila Umar nagudu

SHEKARA: 10/ August/1985

AIKI : Jaruma, ambassador na ajino moto, da globacom

MATAKIN KARATU: Secondary

AURE: Babu

YARA: Daya

ADDINI: Musulma

GARI: Bauchi

KASA: Nigeria

 

Cikakken tarihin jamila umar nagudu
Jamila Umar nagudu

WACECE JAMILA UMAR NAGUDU

Jamila Umar turaki Wanda akafi sani da Jamila Umar nagudu ta kasance shahararriyar jaruma a Masana’antar shirya fina finan hausa na kannywood dake arewacin nigeria. Sannan ta kasance ambassador a kamfanin ajino Moto da kuma ambassador a kamfanin globacom.

HAIHUWARTA

An haifi jaruma Jamila Umar turaki ne a ranar goma ga watan Augusta shekara ta dubu daya da dari Tara da tamanin da biyar 10/8/1985 a unguwar magana gumau a karamar hukumar toro a jihar bauchi a nigeria.
Inda ana ne tayi kuruciyarta Kuma tayi karatunta na arabi da Boko.

KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN RAHAMA SADAU

KARATUNTA

Jamina Umar turaki tayi karatunta na primary da Kuma secondary a karamar hukumar toro a jahar bauchi a Nigeria.

Bayan ta gama secondary ne ta yanke shawarar fara film a masana’antar shirya fina finan hausa na kannywood.

FARA FIM

Jamila Umar turaki wadda akafi sani da Jamila Umar nagudu ta fara film ne a Masana’antar kannywood a shekarar dubu biyu da biyu (2002). Tun bayan da ta yanke shawarar fara film tabar garin bauchi ta dawo Kano domin ganin cewa ta cimma burinta na zama jarumar fim a Masana’antar kannywood.

Kana Ta shiga Masana’antar fim ne a matsayin Yar rawa a shekara ta (2002).
Sannan daga baya ta samu cigaba a harkan harma tafarayin wasan barkonci da Kuma drama kadan kadan.

Ganin kokarinta a wasan barkonci da harkan drama hakan yajawo hankalin daraktoti da jaruman kannywood kanta suka fara Sata a fim nasu.

Ta fara fitowa a masayin jaruma ne a wani shiri mesuna jamila da jamilu Wanda yana daga cikin fina finan dasuka zama sanadiyar daukakarta daga bisani kuma “kauyawa” ko subulli da subulluwa wadda tayi a shekarar 2011. Tare da Abubakar sulaiman Dan auta.

Jarumar taka rawar gani a Shirin fimdin sosai. Wadda har hakan yasa tayi suna ba iya Nigeria ba harma da wasu kasashen afrika.

DAUKAKAR TA

Kana Jamila Umar tasamu daukaka a harkan fim sosai dama sauran harkokin rayuwarta domin takasance ambassador ce na ajino moto, da globacom

Nagudu har takai matsayin da ake kiranta da sarauniya a Masana’antar kannywood ganin kwarewarta a harkan fim na hausa a masana’antar kannywood.

Sannan daya daga cikin directan fim na hausa a kannywood Wanda akafi sani da Aminu saira Mai kamfanin saira movies. Yana daga cikin wadanda suga bada gudummawa wajen samun daukakarta kasancewar shine wanda ya fara sakata a fim amasayin jaruma wadda hakan yayi tashiri sosai a rayuwarta.

WASU DAGA CIKIN FINA FINANTA

Sannan jarumar ta fito a fina finai da dama kamarsu
_Hindu
_Subulli da subulliya
_Jani Jani
_Aska tara
_Wani gari
_Halisa
_Haske
_Farin dare
_Mai dalilin aure
_Jarumta
_Ali yaga Ali
_Karshen tika tiki
_Jamila da jamilu
_Maula
_Buka Africa
_Kauyawa
_Dan almajiri
_Buka Africana Shiri Mai dogon zango
Dadai sauransu.

Cikakken tarihin jamila umar nagudu
Jamila Umar

HADAKA

Takuma samu damar fitowa a fina finai tare da jarumai da yawa daga cikin masana,antar
Kamar su
*Jarumi Adam a zango
*Jarumi Ali nuhu
*Jarumi Mai shenku
*Jaruma halima atete
*Jaruma Fati Sasha
*Jarumi Nuhu abdullahi
*Jarumi Al,amin buhari
*Jarumi Sadiq Sani Sadiq
*Jaruma Maryam booth
*Jarumi Garzali miko
*Jaruma Aisha Aliyu tsamiya
Dadai sauransu

karanta: CIKAKKEN TARIHIN AUTA MG BOY

KYAUTAR GIRMAMAWA

Jaruma Jamila Umar nagudu ta karba kyautar girmamawa da dama a tarihin rayuwarta. Ganin kokarinta da hazakarta da Kuma jajircewar ta a cikin masana’antar ta kannywood

JERIN KYAUTAR GIRMAMAWAN TA

•City people movie award (Best kannywood actress of 2015)

•City people movie award (Best kannywood actress of 2016)

•City people movie award (Best kannywood actress of 2017)

•City people movie award (Face of kannywood 2016)

•City people movie award (Face of kannywood 2017)

Dadai sauransu.

Sannan daku iya ziyartarmu a shafinmu Na YouTube mesuna NW HAUSA TV dangane da cikakken tarihin jamila umar nagudu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *