Cikakken Tarihin maryam waziri
SUNA: Maryam Musa waziri
INKIYA: Maryam waziri
SHEKARU: 9 November 1992
AIKI: Jarumar kannywood
MATAKIN KARATU: Degree
AURE: 2022
GARI: Gombe
KASA: Nigeria
WACECE MARYAM WAZIRI
Jaruma maryam Musa waziri wacce akafi sanida maryam waziri, takasance daya daga cikin matasa kuma fitattun jarumai a masana’anatar shirya fina finan hausa na kannywood.
HAIHUWARTA
Maryam waziri takasance haifaffiyar Jihar gombe karamar hukumar kaltingo sannan jarumar ta kasance batangaliya (yaren tangale).
Kana ta girmane a jihar takumayi karatunta na primary da secondary cikin jihar Sannan Anhaifeta a 9 ga watan Nuwamba 1992.
Izuwa yanzu jarumar tanada shekaru ashirin da takwas 29 a shekarar (2022).
KARANTA: CIKAKKEN TARIHIN ALI NUHU
KARATU
Maryam tayi karatunta na matakin Primary a makarantar waltagona memorial nursary and primary school sannan tayi karatunta na matakin gaba da primary wato secondary a makarantar federal government girls college bajoga.
Bayan kammala karatunta na secondary ta koma jihar borno domin cigaba da karatunta inda ta karanci Harkar ilimin kasuwanci ko cinikayya ( wato business education) a jami’ar Maiduguri UNIMAID.
FARA FIM
Shigowarta Masana’antar fim
Jarumar tafara ra’ayin fim tun a makarantar secondary saboda tana daga cikin masu shirye shirye da kuma raye raye idan antashiyi a makarantar.
Amma tashigo masana’antar ne bayan kammala karatunta na jami’a a lokacinda take bautar kasa.
Karanta: CIKAKKEN TARIHIN YUSUF SASEEN
Acewarta tashigo masana’antar shirya fina finan hausa ne da taimakon abokinta kuma Dan’uwanta mai shirya fina finai Khalifa CBC Wadda shine ya fara mata fim data fara fitowa kuma taja ragamarsa maisuna muguwar mace, Mai bada umarni Ali gumzak ko shine wanda yabada umarnin shirin.
Bayan fitowarta a muguwar mace tafito cikin shiri masu dogon zango kamarsu yanzamani , dakuma labarina sannan tafito a shirin fim da aka shirya a gombe mai suna aminan juna da ya ko kishiya daga bisani a kannywood tafito a shirin yakin mata dasauransu
Tambayar da akaimata na wasu jarumai ne sukafi burgeta Tace fati Mohammed da kuma marigayi Ahmad S Nuhu
IYALI
Kawo yanzu maryam waziri batada Aure (2021).
Sannan Su ukune wajen haihaifansu maza biyu da ita ta uku wacce itace karama.
Mahaifinsu mallam Musa ya rasu a shekarar 2011, Mahaifiyarsu daga bisani itama ta rasu a shekarar 2014
JERIN FINA FINAI
-Aminan juna
-Dan halak
– Labarina shiri mai dogon zango
-Muguwar mace
-yakin mata
-yan zamani
– dasauransu
Kana daku iya ziyartarmu a shafinmu Na YouTube mesuna NW HAUSA TV Domin samun Karin bayani dangane da cikakken tarihin maryam waziri