Cikakken Tarihin Rabi’u Rikadawa (Baba Dan Audu)

Cikakken Tarihin Rabi’u rikadawa

SUNA: Muhammed rabiu rikadawa

Inkiya: rabiu rikadawa

AIKI: jarumin fim, producer, darakta, comedian

SHEKARU: 5 Feb 1972

MATA: Daya 1

YARA: Shida 6

GARI: kaduna

KASA: Nigeria

Cikakken Tarihin Rabi'u rikadawa
Baba Dan Audu

WANENE RABIU RIKADAWA

Rabiu rikadawa na Daya daga cikin shahararrun jarumiai a masana,antar shirya fina-finan Hausa na kannywood.

Cikakken sunansa Muhammad rabiu rikadawa amma anfi Saninsa da rabiu rikadawa yakasance jarumi, darakta kuma producer amasana,antar ta kannywood.

HAIHUWA

Anhaifi rabiu rikadawa ne a garin Kaduna a shekarar alib dubu daya da dari tara da Saba’in da biyu 1972 kafin daga baya ya chanja sheka izuwa jihar kano shida iyalansa gaba daya wadda tin asalima iyayensa Yan Kano ne.

Rikadawa dai sunan unguwa ne a karamar hukumar modobi a jihar kano Wadda Ana Kiran jaruminne saboda nanne mahaifar iyayensa kuma yayi hakane saboda mutane sugane asalin tushensa.

IYALI

Kana Jarumin rabiu rikadawa yana da Mata daya da yara shida 6 daga ciki maza hudu 4 mata 2 yana kuma zaune tare dasu duka a cikin jahar kano.

FARA FIM

Yafara fitowa a fina-finan hausa ne tunda jimawa amma daukakarsa tafarane tun bayan fitowarsa a manyan fina-finai kamarsu Afra, baya da kura, Matar mutum, mati da lado da dai sauransu.

KARANTA:  CIKAKKEN TARIHIN DADDY HIKIMA

JERIN FINA-FINAI

Jarumin yafito a fina-finai da dama kamarsu
-baya da kura
-mati da lado 2014
-jamila da jamilu
-alkalin kauye 2015
-Adam, jinin jikina
-ga fili ga me doki
-lamiraj
-afra 2015, Dare 2015
-badi ba rai 2012
-dare daya 2012
-there’s away 2016
-hauwa, murahdi 2011
-cikin waye, farar saka, wata Riga, fulani
-takaddama 2018
Da dai sauransu
Sannan yana daga
cikin jaruman cikin shirin labarina na aminu saira wadda ake haskawa a tashar arewa 24.
Dagawa Shirin mazajene Wadda ake sakewa a manhajar YouTube 2022

 

Cikakken Tarihin Rabi'u rikadawa
Rabiu rikadawa

HADAKA

Yasha fitowa tare da jarumai da dama na masana’antar shirya fina-finan Hausa Wanda sun hada da:

*Adam A zango
*Ali nuhu
*Rahama sadau
*Jamila nagudu
*fati Shu,uma
*daddy hikima
*nafisa abdullahi
*maryam booth
Da sauransu

KARIN BAYANI

Kamar yadda jarumin ya zayyana yana da Mata daya yanada kuma burin karawa a duk lokacin da ya samu dama.

Sannan babban abinda yafi tada masa hankali shine lokacin da yaji ana yada cewa ya mutu yayin da shikuma yana nan a raye.

Domin samun Karin bayani dangane da cikakken tarihin rabi’u rikadawa daku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube NW HAUSA TV

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *