Cikakken tarihin shu’aibu Lawan kumurci
SUNA: Shu,aibu Lawan
INKIYA: kumurci
AIKI: Jarumi, producer,darakta
GARI: Kano
KASA: Nigeria
WANENE KUMURCI
Shahararre kuma fitaccen jarumi a masana,antar shirya fina-finan hausa na kannywood Shu,aibu lawan wadda kukafi sani da kumurci
Yakasance jarumi ne da yayi suna sosai musamman a bangaren dabanci
KARANTA: Cikakken tarihin saratu gidado
HAIHUWA
Kana Anhaifi jarumin ne shuaibu lawan ko kuma kumurci a jihar kano cikin garin kano a unguwar gedi-gedi
Ya kuma girma anan kuma yayi karatunsa duk a mahaifarsa jihar kano.
KARATUNSA
Sannan yayi karatunsa na matakin primary a gedi-gedi primary school kuma yayi karatunsa na gaba da primary wato secondary a sabuwar kofa junior secondary school sannan yayi senior secondary school a KTC kano sannan bayan wasu shekaru yaci gaba da karatunsa na gaba da secondary a college of technology inda ya karanci (art and design)
FARA FIM
Kana jarumin Shu,aibu lawan wanda akafi sani da kumurci ya fara harkar fim ne
ata dalilin abokin kuma dan unguwarsu (Hafizu bello) wadda yakasance daraktane amasana,antar ta kannywood
Sannan hafizu bello shine yasa masa ra,ayin fim saboda a duk lokacin da yagansa yakance masa daka dace da harkar fim har,izuwa lokacin da shima yaji cewa yakamata yakwada kodai iya
Hakan kuma yasa ya kwada kuma ya iya
Sannan fim nashi na farko da ya fara fitowa amasayin jarumi shine dijangala wadda wasu suke yiwa fimdin lakabi da dijangala ta mai gari
Bayanshi kuma yafito a fina-finai fiye da dubu biyu (2000)
Sannan ya samu sunan kumurci a wani shirin fim mesuna ukuba wadda jarumi aminu shareef momo ya shirya
JERIN FINA-FINAI
Kana amasayinsa na jarumi a masana,antar ta kannywood ya samu damar fitowa a fina finai na soyayya da na dabanci da dama kamarsu
_Dijangala
_Daba
_Ukuba
_Zanen hali
_Ruwan idona
_gwamnati
_Galaba
_Gadan ga
_Dare daya
_Ba,asi
_Farida
_Shu,uma
_munayat
_Turare mai kamshi
_sa,ar mata
_Hadarin gabar
_Inda rai
_Mazan fama
_Albashi
_Almustapha
_Goma ta wuya
_Harira
_Fansa
_Zaman idda
_Daukaka da sira
Dadai sauransu
Karanta : Cikakken Tarihin Nazifi Asnanic
HADAKA
Sannan yafito tare da jarumai da dama a fina finai da dama amasana,antar ta kannywood kamarsu
*Jarumi Alinuhu
*Jarumi Adam a zango
*Jaruma Fati shu,uma
*Jarumi daddy hikima
*Jarumi Mai shunku
*Jaruma Jamila nagudu
*Jarumi Aminu shareef momo
*Marigayiya balaraba
*Jarumi tanimu hassan kano
*Jarumi al,amin buhari
*Jaruma nafisat abdullahi
Dadai sauransu
KARIN BAYANI
Kana kamar yadda ya zayyana jarumin ya fito a fina-finai na soyayya da na dabanci fiye da dubu biyu 2000 a masana,antar ta kannywood
Sannan shima da kansa ya shirya fina-finai da suka Kai takwas wadda suka hada da
_harira
_Goma ta wuya
Dadai sauransu
Sannan fim da yafi samun alheri aciki shine Goma ta wuya
Kana fim da yafi birgeshi daga cikin fina finansa shine
-Fansa
Kuma jarumin da yafi burgeshi a masana,antar shine marigayi rabilu musa ibro
Sannan kuma aminu shareef momo ne babban abokinsa amasana,antar ta kannywood
Zaku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube mesuna NW HAUSA TV Dangane da Cikakken tarihin shu’aibu Lawan kumurci