DA MA NI CE CHAPTER 11 BY JAMILA UMAR TANKO

Da sauri Malaika ta cire wayar daga kunnenta

  • ta duba sunan mai. kira.
    “Nastin Abdul Nasir’
    Wai Rigijigafji!! Zo ku ga murna da
  •   ladabi gaba daya ta sauko daga kan gado ta durkusaa kasa.

Malaika ta gaishe da Nasrin. Ta yi mata kirari

gami -da addu’oin samun nasara a rayuwarta. Sai Nasrin ta fara mamakin yadda

*. Malaika, ta iya kalamai haka amma bata yiwa mai gidanta. Ta gasgata Malaika tana da cikekken hankali babu tabin hankali haka tana da ilimi da dubara ba gabuwa bace. Ta kudiri niyyar sai ta nemo daga ina matsalar ta ke. Yar jarida me neman labarai.

“Nasrin tana gyara zama tana juyi a kujerar ofis dinta ita kadai ce, dan yau gaba daya abokan aikinta sun fita aiki. Nasrin ta yi murmushi ta ce, “kawata, na kira in gaishe ki ne kuma in ji lafiyar yaranki ..da mai gidanki. Yaya kuma yaro mai sikila?

” Ina fatan ya ji sauli.”• Malaika ta washe baki ta ce, “lafiya alau kawata, Allah Ya bar mu tare.”

Nasrin ta ce Ameen Yau fa kira na yi

muyi hira sosai dan ba ni da aikin yi

Sai Malaika ta dafe kirji, aka tayi murmushi ta tashi bazar-bazar ta dawo falo ta zauna akan kujera aka yi bake-bake, jinta take tamkar da shugaban kasa take magana, ita kuma ta zama minista.

“lah dan Allah da gaske kike Nasrin?

Amman na ji dadi, ashe kina sane da kiran da nake yi miki kullum? Wato aiki ne yake hana ki amsawa. Na zaci wulakanci ne ma dan kin ganni talaka.”

Nasrin ta ce, “haba dai ai ke ma ba talaka bace kyakykyawa dake gashi sunanki mai dadi  kuma naga alamar ke jinin sarauta ce ma

‘Shamaki’. Ba ni tarihin rayuwarki Malaika.

Dadi ya rufe Malaika, ta yi dariya ta ce,

“Kwarai nice kuwa jinin sarauta. 

LABARIN MALAIKA

Sunana”,Malaika, sunan mijina shamaki  garinmu karamar hukumar Bichi. Mahaifina attajiri ne, mai kudin gaske ga sarauta amma ya rasu, ni kadai ya haifa

‘yan uwansa suka cinye min gado. Na zo na auri talaka yana ta gana min wahala ni da yarana.

Shine nake so ki kawo min agaji nima in fita daga wahalar nan.”

****

Malaika ta fashe da Luka. Sai Nasrin ta yi shiru hankalinta ya tashi ta kasa tantance mai gaskiya a tsakanin mijin da matar. Nasrin ta Ce,

“Malaika daina kuka ki fada min abubuwan da mijinki baya yi miki na hakkin aure.”

Malaika ta goge hawayen da daman bai zubo ba ta ce, “gidan haya nake dan Karami mai kunci, daki biyu kanana, idan zafi ya zo ba iska numfashinmu na cikewa, sai ayi wata ba’a Kawo wutar lantarki ba, muna cikin duhu ba mu da jannareto, babu ci, babu sha, dari daya yake ba ni ko naira hamsin kudin cefane kuma a ciki zan sayi ruwa. Ga yara uku daya ba lafiya.Kayan jikina a yayyage, kamar almajira, makawabtana ma basa kawance da ni saboda duk sun fini.”Nasrin ta girgiza kai cikin damuwa ta ce

“bashi da shine ko yana da shi ya boye?”

Malaika ta cije baki ta ce, “yana da shi ya boye baya bani sai dai ya kashewa yan matan waje da danginsa.”

Nasrin ta dafe kai dan tausayi, ta fada a bayyane

“me yasa mazan Hausawa suke mugunta ne? Allah sarki Malaika, ki ci gaba da hakuri. Kin ji? Ita rayuwar aure lada ne kuma wannan jarabawar itace zata kai ki ga shiga aljanna, idan kika yi hakuri za ki haye.

Malaika ta fashe da kuka ta ce, “shiyasa kika ga ina ta binki rannan da muka hadu, ko Allah Zai sanima ki samar min aiki a Abuja in samu in rike ‘ya’yana. Auren nan ya ishe ni daman kullum cewa yake zai sake ni ya auro wata.”Nasrin ta girgiza kai ta ce, “kada ki sake ki kashe aurenki, aure daraja ne da shi ki zauna kirike ‘ya’ yanki. Za ki iya sana’ a a gida ba sai kin fito ba, Abuja kuma ta yi nisa, ke da kike Kano. Aiki a Abuja kuwa sai ka yi karatu mai zurfi kin ga ke ba kiyi ba.”

Malaika ta zabura ta ce, “ai na yi karatu da yawa dan nagama sakandire na yi diploma.”

Nasrin ta zare ido ta ce, “da gaske, ashe kawar tawaba sauki? To gaskiya ko koyarwa ce ya kamata a samo miki anan unguwarku bai kamata ya tauye ki ba.”

Malaika ta ce, “ni dai gara in zo Abujar nan in same ki in ma ba aikin ba in kwana biyu nima in ga gari an ce kamar a turai garin yake, ban taba zuwa ba. Sai dai makwabciyata ce suke hutu acan idan ta je ta dawo sai ta dinga yi mana yanga, da jiji da kai. Ina so nima in je Abujar nan, Nasrin ki taimaka min.

Nasrin ta girgiza kai ta ce, “kullum ina fama da aiki amma Karshen wani watan za mu shigo Kano aiki zan neme ki sai mu ga yadda

Hmmm