DAN ADAM CHAPTER 19

DAN ADAM CHAPTER 19

  Ya bud’e dakinta, saidai Binta ya gani wacce ke yawo a tsakar dakin tana jiran dawowarta, ganin Yalla6ai da kansa yasa ta russunawa ta gaisheshi, batare da ya amsa ba ya jefomata tambaya. “Ina Ummi?”+ Ta girgiza kai. “Bata shigo ba tun bayan fitarta.” Ya juya kai tsaye wajen garden ya nufa, acan kuwa ya ganota durkushe k’asan bishiyar mangwaro tana faman kuka sosai. A gigice ya isa gareta ya durkusa kusa da ita. Jin motsi ne yasa ta dago kanta da sauri, ganin shine yasa ta numfasawa. “Kaga abinda muka janyo ko? Ni nasan wannan lamari ba mai yiwuwa bane.” Baisan sadda ya rik’o hannunta ba. “Wa ya gayamaki bazai yiwu ba? Kada ki damu da abinda ya faru domin na zo miki da kyakkyawan albishir, iyayena sun amince da aurenmu.” Ta yi sakato tana kallonsa, babu alamun wasa ya ke yi, ganin ta yi shiru ya girgiza hannunta. “Ba mafarki ki ke ba fa Ummi, dagaske sun amince da zancen aurenmu. Godiya ya kamata muyi ga Ubangiji.” Ta lumshe ido, ta rasa irin yanayin da ta ke ji a jikinta, ji ta yi yana kokarin mik’ar da ita, a kunyace ta zare hannunta daga nasa ta mik’e, jerawa sukayi suka soma tafiya tamkar basu so, kallo daya idan kayi musu, zaka so kayita kallonsu tsabar dacewa da sukayi da juna. Ya dubeta. “Ummina shiru fa, kiyi magana please.” Ta share ruwan hawayen da suka k’i tsayuwa. “Yaya Faruk.” Ya tsaya a gefen kujera mai lilo ya zauna, sannan ya yi mata nuni da gefensa. “Zauna nan.” Ba musu ta zauna jikinta a sanyaye. Ya juyo yana fuskantarta yana ji tamkar ya had’iyeta don so da tsantsar kauna. “Ina sauraronki.” Ya fada cikin kankan da murya tamkar wanda baya son magana. “Kamar fa ‘yan uwanka ba…” “Shiii..” Yasa yatsa a saman le66anta, ta kauda kai tana mai takaicin yanda bayason ta kawomishi zancen abinda ya kasance gaskiya kuma shima ya sani. “Ya dace ka bani dama ka ji abinda zan fada Yaya Faruk, akwai babbar matsala da kai ka ke mata kallon sassauk’a. Yaya Faruk kana da labarin Ihsan na sonka?” Ta karashe tana kallonsa, shima ita ya ke kallo, kenan dai shi 6oyon ma da ya ke mata ta sani? Abu daya ne bazai iya sanarmata ba, batun auren da Hajiya ta ce zaiyi da Ihsan don bai dauki hakan mai yiwuwa ba, kuma ba wai don Hajiyartasa bata isa ba, aa, sai don kokusa ba shi da tsarin had’a mata biyu a gidansa. Saidai abinda ya ba shi mamaki, bai wuce ta yacce akayi tasan da cewa Ihsan na kaunarsa ba. Ya kauda fuskarsa yana mai dan hade gira. “Ya akayi kika sani?” Ta yi murmushi mai ciwo itama ta maida dubanta ga wata shuka a wajen. “Shi so ba’a 6oyonsa, itama nata ya fito fili, k’alilan ne basu san tana sonka ba a gidan…” “Kinga ya isa haka please, ya isa. Ke bakya kishina ne? Bakya jin wani abu a ranki idan kina had’ani da wata bayan ke? Bazan iya rayuwa da kowace mace ba bayan ke. Ummi wai kinsan waye Umar Faruk kuwa?” Ya k’arashe yana mai tsuramata ido da wani murmushi. Daman ba kallonshi ta ke yi ba, wasa kawai ta ke yi da yatsunta. Ya girgiza kai. “Shikenan dai. Ban labari game da farin cikin da zaki yi ranar da aka shafa fatiha?” Maganar ma sai ta bata dariya, ta rufe fuskarta tana murmusawa. Karaf akan idanun Ihsan wacce ta fito don bawa wani mai wankin gidan ya siyo mata kati don kiran Maminta, ta jima tsaye tana kallonsu basu sani ba, hawaye kawai ke zuba daga idanunta. Ta k’arewa Ummi kallo, ta yi wani kyau a suturar dake jikinta, sannan ta dubi Faruk wanda ya bawa inda ta ke baya, ya wani duk’ar da kai a gaban Ummi yana lek’en fuskarta kamar mai shirin kai mata sumba. Nan duniya ta ji ta k’ara tsanar Ummi, ta k’ara tsanar Faruk da wai suke takara a sonsa da ita. Ina ita ina had’a masoyi da wacce tasan ta fi? Faruk ya cuceta, inama bai soma son Ummi ba ita ya so? Katin da bata bada an siyomata kenan ba, da gudu ta koam ciki tana rusa kuka, a kicin ta yada zango ta yi mai isarta sannan ta fito ta fada bandakin dake falon ta wanke fuskarta ta koma sama zuciyarta na wani irin zafi. Daddy ya cigaba da yiwa Hajiya nasiha mai ratsa jiki gami da nunamata shi fa lamari na aure ba’a dole, ya amince da bukatarta na aurawa Faruk duk su biyun saidai su dage da mik’a lamarin ga Allah kafin komai, a karshe ya ce su bar maganar nan zuwa kwanaki uku. Hajiya ta aminta da hakan, ta kuma sanarmishi cewar a gobe Ummi zata koma Kano. “Badai don maganarnan ba?” Ta girgiza kai tana dan murmushi duk don ta kwantarwa da mijinya hankali. “Ko kusa, saidai Madina ta buk’aci hakan tun ba yau ba, daman ina shirin sanarmaka sai wannan al’amari ya 6ullo.” Ya jinjina kai alamun gamsuwa. “Shikenan ai, Allah Ya nunamana. Shima Ridwan zan ganshi gobe, banason abinda zai kawo rikici tsakaninsu.” “Hakane.” Hajiya ta amsa kafin ta mike don kawomishi ruwan lipton wanda ya saba sha duk dare. *** *** *** RINGIM Abu kamar wasa, k’aramar magana ta zama babba, don kuwa tuni Deen ya damk’awa Dija mak’udan kudi ta had’o lefenta. Tare da Saude da Baba Habiba suka shigo kasuwar Kano, nan suka shek’o kayayyaki masu dan karen kyau da tsada don har saida Deen ya k’aramusu kud’i. Yan uwa daidaiku ne kawai suka halarci ganin lefen don kuwa acewarsu abin kunya ne da abin tirr irin wannan cin amana da suka yi ga Munira. Kuma tabbas Allah bazai barsu ba, to ance wanda ya yi nisa ba ya jin kira, ko a jikinsu wai an tsikari kakkausa, Malam Yahuza abin na damunsa a kasan zuciya saidai babu abinda zai iya cewa, haka zai zauna tare da Balarabe mahaifi ga Ummi ya yi ta gayamishi bayason auren, shima kasancewar ba wani kata6us ne da shi a gidansa ba, saidai ya ce “To ya zaayi banda hakuri da addua? Matar mutum babu makawa sai ya aureta indai Allah Ya kaddaro tasa din ce.” Haka suna gani matansu suka shiga shirye-shirye, an kai Dija wajen bokanya yafi sau biyar ana mata tsafe-tsafe don ta mallaki zuciyar Deen. Aikam sai haukacewa ya ke k’ara yi akanta, Munira dai yanzu abin ma ya ca6emata don hatta Yaransu ba shiga harkarsu ya ke ba, idan ka gansu kasan suna cikin tashin hankali marar misaltuwa. Har ana washegari Asabar daurin aure, Deen bai samu wata fuska daga yan uwansa ba, Munira kuwa a ranar ta juma’a ta iso Ringim din suna k’ara jajanta lamarin da yan uwanta, iyayenta kuwa nasiha kawai sukai ta binta da shi akan ta yi hakuri ta rungumi kaddara. *** *** *** ABUJA Misalin takwas na safe, Ummi ta kammala gyara sashen Hajiya duk jikinta a dar-dar, burinta ta yi ta kammala ta bar wajen kafin wani ya risk’eta, saidai cikin rashin sa’a tana murnar har ta kammala za ta tafi ba wanda ya fito, Ihsan ta fito falon tare da Ikram. Daman tun jiya suke dakonta. Tsayawa ta yi kyam tana kallonsu, fuskarta alamu na rashin gaskiya ya bayyana, ta numfasa dakyar tana mai hadiyar yawu, suka k’araso har inda ta ke, idanunsu k’arara ya nuna alamun 6acin rai, babu ma kamar Ihsan wacce bacci 6arawo ne kadai ya saceta shima cike da mafarke-mafarke. “Ina kwana…” Bata kai ga k’arasawa ba ta ji an dauketa da wani zazzafan mari, ta rik’e kuncinta lokaci guda kuma ta saki bokitin hannunta tana duban Ikram fuskarta cike da tsananin damuwa, tuni hawaye sun soma sauka a fuskarta. “Kinyi kad’an a mareni saboda ke ba kasa tararki na rama wallahi! Ke din banza! Sa’arki daya ma jiya a gaban wadanda suke da daraja aka mareni, da tun jiya na huce. To saidai mu din an koyamana tsayawa iyakar matsayinmu bamu saba ketarewa ba, ke kuwa da alama ba ki samu wannan tarbiyyar ba tunda har ya kasance kinyi tsaurin idon kai kanki inda aka fi karfinki. Banza mai kwadayi.” Ikram ce ke wadannan kalaman tana mai jifanta da wani banzan kallo, ba ta ce uffan ba, ta sa hannu zata dauki bokitin Ihsan ta buge hannun da k’afarta. “Aiki kuma a gidannan ya k’are miki, sannan ki sa a ranki muddin yau muka isa Kano zamanki a gidanmu ya k’are, sai naga ta inda zaki auri Yaya Faruk din. Banza kawai!” Ummi da ta kasa dagowa daga durkushen da ta yi, ta runtse idonta cikin jin zafin wannan abu. “Meke faruwa ne?” Suka tsinci muryar Hajiya, da sauri suka nutsu kamar ba su ba. “Bakomai Hajiya, k’arewa Matar Yaya kallo mukeyi.” Cewar Ikram tana dariya ta raini. Hajiya ta daure fuska. “Ku bar wajen nan tun ban sa6amuku ba.” Suka juya suna gunguni suka koma daki. Hajiya ta zauna saman kujera ta yi shiru tana kallon Ummi dake faman goge ruwan da suka zubar suka 6ata mata guganta, tana yi tana hawaye. Murya na rawa ta gaida Hajiya, Hajiya ta amsa mata. Saida ta kammala sannan ta mik’e da zummar barin wajen, ta dakatar da ita ta hanyar kiranta, jin yanda Hajiya ta kira sunanta da sanyin murya, yasa ta dan ji sauki na rad’ad’i da kuma fargabar da ta cikata. Ta amsa a ladabce tana mai zama a gefe kanta a k’asa. “Kiyi hakuri Ummi, nasan daman tunda Sadauki ya 6ullo da maganar aurenki, dole irin haka ta faru koma fiye da hakan kafin a samu fahimtar juna. Ni ban ta6a k’in ki a zuciyata ba, haka kuma ina miki kallon mutum kamar kowa mai nata darajar ta daban. Ko yanzu hakurinki yasa kin k’ara samun wani gurbi a zuciyata. Ki sani, ni mai son abinda Sadaukina ke so ne matukar ba abin assha bane don haka kema na yarda da lamarinki da shi. Kar kice kuma zakiyi amfani da wannan damar ki cutar da d’ana, bazan ta6a lamunta ba. Idan kin d’ore a yanda kike yanzun to fa zamu shirya da ke. Sannan Ihsan…” Sallamar Gogan ya katse Hajiya daga maganarta, suka amsa suna dubansa. Idanunsa shima a kansu da mamaki, musamman ma na ganin yanda abar kaunarsa ke fidda ruwan hawaye saidai bayason cewa wani abu don gaban Hajiya ne, fatansa dai kada Hajiya ce ta sanyata kuka. Ya karaso cikin shigar kananun kaya wanda ya nuna shaidar ya yi wanka, ya zauna gefen Hajiya yana mai gaisheta, ta amsa fuskarta a dan sake ba kamar jiya ba da ta daure mishi, hakan ya dan sanyamishi nutsuwa. Ummi ta gaisheshi batare da ta dubeshi ba, ya amsa yana bin fuskarta da kallo, yana son ya tambayi dalilin kukanta saidai babu dama. “Je ki sai na nemeki, kin shirya kayanki?” Ta gyada kai, Faruk ya yamutsa fuska yana duban Hajiyarsa cikin rashin fahimta, bayan fitar Ummi dauke da bokiti da tsummokarai, ya dubi Hajiya. “Ina zata?” “Kano zata koma mana, ko ka manta daga can ta fito?” Ya daure fuska yana mai kauda kai. “Idan har a matsayin yar aiki zata je don Allah ayi hakuri Hajiya.” Ya karashe fuskarsa cike da damuwa kwarai. Ta yi shiru tana dubansa, ta gama karantar ba karamin so ya ke yiwa Ummi ba, tasan halin d’anta, wannan magana har cikin zuciyarsa ya ke yinta. “To yanzu Sadauki za’ayita rike musu ita ne? Karka manta fa kawota akayi Kano aikatau asalinta ba ma’yar garin bace.” Ya lumshe ido kafin ya bude. “‘Yar Ringim ce. Kuyi hakuri har ta cika watanta, idan wacce ta kawota ta zo Kanon, sai aje har Ummin ayiwa mahaifinta bayani don Allah Hajiya. Amma yanzu ba girma kuma ta cigaba da aikatau, a duba wannan lamarin Hajiyata.” Hajiya ta gyada kai cike da gamsuwa. “Shikenan, na ji zanyi tunani.” Bayan fitarsa daga falon ta rasa ma abin yi, mikewa ta yi ta nufi dakinta. Karshe dai ta yanke hukuncin kiran kanwarta Hajiya Mama, don ita har nauyin Hajiya Madina ta ke d’an ji a yanzu. Hajiya Mama ta dauka, bayan sun gaisa ta ce. “Sadiya kina jina?” “Ina jinki Hajiya.” Ta koramata dukkan yanda ake ciki tun daga jiya da Faruk ya zo musu da maganar Ummi har zuwa yanzun da ya ce shi bayason komawarta aikatau Kano. Ta k’ara da fad’in. “Ki ban shawara Sadiya, kwakwalwata ta cushe, na rasa abinda zanyi, ina kuma jin tsoron Madina ta ji maganarnan daga bakin ‘yarta.” Hajiya Mama da ta sandare don mamakin wannan al’mari ta numfasa. “Allah Mai Iko, wannan shine ana zaton wuta a makera. Karki damu Hajiya, ni banga aibu a aurensa da Ummi ba matukar zai had’a har ita Ihsan din kamar yanda ku ka ce, don bazamu so wannan abu ya kawo matsala a zuri’armu ba. Amma don Allah kamar yanda Genaral ya ce, ku daure kuyi bincike sosai akan Asalin yarinyar nan, Ummi dai a halayya bata da aibu daidai gwargwado yarinyar akwai hakuri da sanin yakamata sannan har gwaje-gwaje ayi ko don gujewa wani abu da zai je ya dawo. Ki kwantar da hankalinki, daman yau zanje saloon, zan fasa idan yaso na sanarwa Alhaji na je gidan Madinan. Allah Ya za6a abinda yafi alheri.” Cike da jin dadin kalamanta Hajiya Babba ta ce. “Kai da kuwa kinyimin babban taimako wallahi, nagode sosai.” “Haba Hajiya, kina gaba da ni ai kin wuce haka, na tabbatar Madina ba zata kawo matsala ba in sha Allah.” Ta jinjina kai. “Ina fatan hakan.” A karshe sukayi sallama da zummar duk yanda akayi zata sanarmata. Ummi ” Ya kira sunanta wanda ya yi sanadin katsewar aikinta da baya sauri don kusan rabinsa tunani ne ja gaba da zubda hawaye. Ta d’ago a sanyaye ta dubeshi, ya zauna gefenta duk jikinsa a sanyaye, ganin haka yasa ta yi kokarin maida kanta ga aikinta, saidai bai bata dama ba don kuwa da sauri yasa hannu ya taro ha6anta. Gefen fuskarta na hagu ya zubawa ido ganin yanda shatin yatsu ya fito 6aro-6aro, hakazalika wajen ya yi jawur, ya dubi tsakar idaninta da nasa idanun wadanda har sun soma kad’awa don 6acin rai. “Wa ya mareki?” Shi ne tambayar da ya jefamata cikin kakkausar murya. Ta girgiza kai tana sheshshek’a. “I’m asking you, who slap you?!!” Ya yi maganar cikin tsawa batare da ya ko tuna cewar wacce ya ke yiwa bata jin yaren ba. Ta runtse ido don a zatonta ma duka zai kawomata. “Ka yi hakuri don Allah.” Ta yi maganar cikin muryar kuka, ya sauke hannunsa gami da yamutsa sumar kansa idanunsa a runtse, baya son jin kukanta ko kadan. A tausashe ya kara fadin. “Naji, gayamin wa ya mareki?” Ina, ba fa zata fad’a ba, batason tashin hankali ya k’aru a gidan sanadiyyarta. “Idan kana kaunar Allah da Manzonsa (S.a.w) abar maganar, ni ba wanda ya mareni ma.” Yanda ta ke maganar gwanin ban tausayi yasa shi saukowa. “Shikenan tunda kin 6oyemin, share hawayen fuskarki.” Ba musu ta sa hannu ta sharesu. “Meyasa ba ki sanardani yau ake shirin tura ki Kano ba?” Ta sunkuyar da kanta, dagaske ba kaunar Kanon nan take ba don ta tsorata da kalaman Ihsan. “Kin dauka bazan sani ba? To babu inda za ki k’ara takawa da sunan aikatau in sha Allah, idan kinga kin bar nan to fa sai da niyyar tafiya gidanku.” Jin haka yasa ta dubansa, ya gyada mata kai. “Dagaske.” Kawai sai ta tsinci kanta da murmusawa, ta tuna Ihsan da alwashin da ta ci akanta, kenan dai Allah Ya yi nufin ku6utar da ita? “Tunanin me kike? Kin ma karya kuwa?” Kai ta gyada. “To yanzu wannan ruwan da ki ke faman tsoma yatsunki ciki, zai iya sanyaki mura, kinga tashi mu shiga ciki. Bala!” Ya juya ya soma kwalawa mai kula da shukoki kira, mintuna k’alilan sai ga Bala ya iso, ya russina a ladabce. “Ranka ya dad’e.” “Matse ka shanya wadannan.” “To.” Ya dubi Ummi da wani kallo wanda ta kasa jurewa. “Muje ko?” Ta kauda kanta ta soma tafiya. Bala ya soma wanki yana binsu da kallo cike da tunane-tunane a ransa da kuma mamaki, to me ya had’a kashi da fura? “Ikon Allah.” Ya fad’a a fili sannan ya cigaba da abinda ke gabansa. *** *** *** KANO Ta kama baki cike da mamaki sadda ta ke fitowa daga d’aki sai kuma ta saki fuska tana ‘yar dariya-dariya. “Ikon Allah, ashe dai yaronnan da gaske ya ke, to, halan dai yau 6atan kai kikayi?” Hajiya Mama ta ja guntun tsaki tana dariya alokacin da ta cire takalmanta ta k’arasa har falon Mami na biyu tana fadin. “Jimin ke da wata magana? Sai kace wacce ta kwashi shekaru bata lek’o ba.” “Aa, ba zancen shekaru, saidai idan ban manta ba rabon da ki zo gidannan tun kafin bikin Baraka, saidai fa a waya ko kuma idan na je.” Ta dan dara. “To naji marar mantuwa, ai gani yau na lek’o.” Mami ta zauna tana dariya. “Na ganki kam.” Hajiya Mama ta bi Mami da kallo cikin shak’iyanci ta ce. “To wannan k’ibar kuma fa? Anya Fahad bai kusa samun k’anwa ko k’ani ba?” “Um, haka fa shima Abbannasu ke fad’i, wai duk na chanja kodai juna biyu gareni.” Hajiya Mama ta gyada kai. “Da alamu dai wallahi, amman ki je asibiti ki ji tunda ba kiyi girman da za ki tantance ko kina da ciki ko babu ba.” Ta k’arashe tana ‘yar harararta, sai ma ta bawa Mamin dariya, suka dara. Sun dan ta6a hira sai kuma Mamin ke sanarmata cewar yau Ihsan zata dawo tare da Ummi. Alokacin ne Hajiya Mama ta taso da maganar da ya kawota. “Ke, ni wata magana ma na zo miki da shi, aikoni Hajiya Babba ta yi wajenki.” Cikin rashin fahimta Mami ta ce. “Toooh, meyafaru? Ba dai wani abun na rashin d’a’a Ihsan ta yi musu acan ba.” Hajiya Mama ta ja tsaki tana mai kokarin cire mayafi. “Kinji wata maganar kuma, to idan hakanne ai bata wuce Hajiyar da kanta ta lallasata ba, wa zai tsaya wani kawo miki k’ara?” Murmushi Mamin ta yi, tasan hakanne don ko kusa Hajiya Babba bata fiye daukar raini ba ba dai kamar Hajiya Mamar, wacce ita sha yanzu magani yanzu ce duk kuwa da cewar tana da mutunci kwarai. “Abinda ya ke faruwa shine…” Ta kwashe bayanin cikin hikima ta gayamata. Mami tunda aka ambaci Ummi aka jogana da Faruk ta daure fuskarta tamau, duk da Hajiya Mama ta lura da hakan, bata fasa cigaba da bayaninta ba saima kauda fuska da ta yi daga dubanta har ta kawo karshe da fadin. “Kinsan dai Yaya Fatima awajenmu da kuma yanda muka dauketa, ba zata so abinda zai ta6amu ba, nikam ban ga wani aibu a yin haka ba, duk da kema nasan babu wani abu da…” “A ina? Bazai yiwu ba wallahi. Haba Hajiya Mama, ban ta6a zaton zakuyimin haka ba, da ace ba ciki daya muka fito ba zan iya kiran haka da ‘YAN UBANCI! Abin kunya abin turr ace keda Hajiya Babba jinina, ku ne kuka amincewa Faruk had’a Ihsan kishi da ‘YAR AIKI? Ko don Ihsan ba ku ku ka haifeta ba? Wannan wane irin magana ce haka kika zo da ita?” Maganar ta ke yi a matukar fusata, idanunta ya rufe akan makahon son da ta ke yiwa d’iyartata wacce ita ta kasance mace d’aya da ta rage agabanta, wacce ta ci burika akanta da kuma ranar aurenta, ta ya ya tashi guda zaayi tunanin had’ata kishi da wacce bata isa ba? Lallai acewarta wannan tsagwaron cin amana ne da yan uwanta sukayi gareta. “Kina da hankali kuwa Madina? Yau ni Sadiya ki ke yiwa haka? Anya kina cikin hankalinki?” Ta dubi Hajiya Mama da idanunta wadanda suka cika da 6acin rai. “Ina cikin hayyacina wallahi, amman tabbas idan magana ce ta gaskiya wannan rashin kyautawa ne, Hajiya Babba ta nuna kaunar nata a fili.” “Wallahi Madina kin ban mamaki, ashe haka kike?!! Ashe son diyarki zai iya chanjaki bansani ba? Aure ba kaddara bace? To wallahi bar ganin ana lalla6aki, ba fa tsoronki mukeji ba don ba kece sama da mu ba, aurene kuma yanda Hajiya ta fada hakan zaayi idan Allah Yaso, idan kin isa saiki hana!” “Ayi, amman ba dai da diyata ba, har abada ba zata yi zaman kishi da Ummi ba, abu ne da Ihsan ba zata ta6a aminta ba, ni na haifeta kuma nasan halinta, bazata ta6a son haka ba. Idan dagaske kaddarar ne, meyasa bai fad’o kan diyarki ba…” Bata kai ga karasawa ba adalilin marin da ta dauketa da shi. “Bansan ba ki da kunya ba sai yau, kuma wallahil azim muddin ina raye idan Allah Ya kaddaro babu mahalukin da zai hana auran Ummi da Faruk. Kina nan kuma itama ‘yar taki tana nan tana gani za’ayi, ta je kada ki barta ta yi kishi da ‘yar aikin da kike ikrari, akwai mazajen ‘ya’yan masu kudi da mulki, kina iya had’ata kishi da su. Sannan ina mai tabbatar miki Madina, akwai ranar k’in dillanci, sai kinyi dana sanin wannan abu da kikayi, sai kinji kunyar kanki Madina.” Daga haka Hajiya Mama ta dauki jakarta da mayafi ta kama hanya tana zubda hawaye, a haka ta shuri takalmanta har tana had’a hanya. A farfajiyar gidan suka hadu da Anti Amarya wacce ta dawo daga gidan wata kawarta, ta lura da yanayinta saidai baki kawai ta saki tana kallonta, Hajiya Mama itama ganinta ne yasa ta dan saita kanta duk da kuwa bai hana komai 6oyuwa ba. Anan kofar gidan ma Adnan ya dawo daga yiwa wasu abokansa sallama sakamakon tafiyarsa da ta k’arato nan zuwa kwana biyu ya ci karo da ita, daga yanda ta amsa sallamarsa ma yasan ba lafiya ba, ta shiga mota direba ya ja suka bar wajen. Hawayenta ya kasa tsayuwa, wannan wane irin rana ce ta zo musu? Kamar yanzu ne suke wasa da dariya da kanwartasu, ace har lamari na aure ya had’asu rikici na ban mamaki. Wai yau Madina ce ke kiran sun ci amanarta, ta nuna suna mata son kai, wannan abu da me ya yi kama? Har take nuna basu suka haifi Ihsan ba ga da ga. Ran Hajiya Mama ya k’ara jagulewa, ta kasa hadiye kukanta, haka hawayenta ya yi ta zubowa tana daukesu da mayafinta. Babu abinda ta fi tunowa sai yanayin shakuwarsu tun suna k’anana har zuwa girmansu, yau sa6ani ya shiga tsakaninsu akan auren Ummi da Faruk. Ta runtse ido. ‘Madina ina kika mance tarbiyyar da iyayenmu suka bamu? Yaushe kika chanja daga kyawawan d’abi’unki? Ya akayi kika bari son ‘yarki ya rufemiki ido har haka? Wannan abu abin kunya ne ya shiga kunnen iyayenmu. Abin kunya ne gareki idan Hajiya Babba ta ji wannan lamari.’ Tana dukkan wadannan maganganun ne cikin zuciyarta. Akan hanya wayarta ta yi k’ara fiye da sau biyu amman ta kasa d’auka, tsoron dagawar ma takeyi, me zata iya cewa Hajiya Babba? Sam bazata iya da wannan abin kunyar ba wanda ta ke ganinsa tamkar a mafarki. Adnan cikin sauri ya shiga wajen Maminsa, saidai bata falo hakan yasa ya nufi dayan falonnata, nan ma batanan, a karshe ya yanke hukunci shiga dakinta. Gefen gado ya sameta zaune tana kuka. Hankalinsa idan ya yi dubu to yau ya tashi, ya isa gabanta ya durkusa. “Mami meke faruwa ne? Ga Hajiya Mama ta fita hankalinta a tashe tana hawaye, kema ga ki na tarar dake kina kuka, rasuwa akayi ne?” Ta share hawayenta. “Da rasuwa ce to da sauki don ansan tana kan kowa, wannan yafi mutuwa k’ona zuciya Adnan. Yau akan Ummi har Hajiya Mama ta mareni, sai nace tun tasowarmu da ita sa6ani irin haka bai ta6a shiga tsakaninmu ba.” Kansa ya danyi dum, ya kasa tantance tak’amaiman yanayin da ya shiga. “Ummi kuma?” Ya furta yana dubanta. “Kwarai kuwa.” Ta kwashe maganat ta gayamishi, ya dan ji hankalinsa ya kwanta, daman ba yau ya fahimci akwai wani abu a zuciyar Faruk game da Ummi ba, shi yasan daman irin haka zata faru wataran, Faruk ya ce zai auri Ummi. Saidai Ihsan fa? Bai ta6a kawowa tana son Faruk ba. Tabbas shi bai ga aibu a had’asu ya auresu ba. “Kayi shiru?” Ya dago ya dubi mahaifiyarsa. “Mami shi fa lamari na aure Allah ne Ya tsara abinsa, babu wanda zai chanja kaddararsa. Kuma…” “Tashi ka ficemin! Shashasha kawai da baisan kishin nasa ba.” Sum-sum ya fice don ya lura ta shiga cikin zafi, da alama babu abinda zai iya fadamata a yanzun ta fahimta. Har ace ta manta irin gwagwarmayar da ta sha a baya wajen Abbansu, har ace zata mance komai na duniya rubutaccen al’amari ne, idan Allah Ya yi za’ayi, za’ayin? Ya waigo yana mai dubanta, waya ya ga ta dauka ta na kokarin kira. Gabansa ya fad’i kada fa ta ce zata kira Hajiya Babba. Da sauri ya isa gareta ya rike hannunta. “Don Allah Mami karkiyi haka, ki duba zumuncinku, kada a sanadin abinda bai kai ya kawo ba ki 6ata kyakkyawar alak’arku da yan uwanki wadanda kowa ya gani sai ya yi sha’awarta.” Sai kuma jikinta ya danyi sanyi, ta dubeshi fuskarta har lokacin a daure. “Tashi ka ficemin Adnan tun ban kai ga ta6a lafiyarka ba.” Ya tashi jiki a sanyaye ya fice, bata fasa kiran ba saidai jin da ya yi Ihsan ta kira ta ke tambayar ko ta taho, hankalinsa ya dan kwanta. STORY CONTINUES BELOW *** *** *** ABUJA Hajiya Babba duk ta bi ta damu akan rashin amsa kiranta da Kanwarta Sadiya bata yi ba, batason kiran Mami tukunna. Ihsan ta shigo da sallamarta ta yi shirin tafiya don tuni an fita da kayanta, sam lokacin ma batasan anfasa tafiyar da Ummi ba. Ganinta yasa Hajiya sakin fuska tana dubanta. “A’a, d’iyata har an fito?” Fuskar Ihsan ba walwala sosai ta amsa. “Eh Hajiya, an fita da kaya ma.” Hajiya ta gyada kai. “Zo ki zauna mu danyi wata magana.” Ta zauna a gefen Hajiyar kamar yanda ta umarceta. “Ihsan inaso kiyimin kyakkyawar fahimta akan maganar da nakeson yi dake. Zamanki anan tare da mu yasa na fahimci kamar kina son Sadauki, ban tabbatar da hakan bane saida naji daga bakin Ikram. To sai kuma Sadauki ya zo mana da zancen Ummi tashi guda da sunan ita ya ke so da aure. Saidai ya amince zai hadaku tare ya aura. Ina fatan baki da matsala akan hakan?” Takaici ya hana Ihsan magana, lallai ma ta yaya ake zaton za ta yi zaman kishi da ‘yar aikin gidansu? Wannan ma jawowa kai raini ne wallahi. Haushin Hajiya ma ya hanata cewa uffan har lokacin kanta yana k’asa. Hajiya ta yi shiru tana karantarta, sai kuma ta numfasa. “Ki je Ihsan ki yi tunani, bazan matsamaki ba. Ke tawa ce, bazan k’i farincikinki ba kema, bazan kuma so k’untata miki akan wata ba. Dake da Sadauki abu daya na daukeku, babu wanda zanso shiga hakkinsa.” Ihsan ta sauke ajiyar zuciya. ‘Kedai kome za ki ce daga baya ne kin riga kin nuna son danki fiye da kowa.” Cewar Ihsan a zuciya. Shigowar Binta ce ya katse maganar. Suka amsa sallamarta. “Ya ce ta fito.” Ta mike Hajiya na mata adduar komawa lafiya itama tana godiyar abubuwan alherin da suka bata. Saida zata shiga motar ne ta dubi Ikram. “Wai bada Ummi za mu tafi ba?” Kafin Ikram ta amsa Hajiya ta amsa. “Ki je zata zo.” Ran Ihsan ya k’ara yin bak’i, kenan plan dinsu da Ikram ya tashi a banza? Niyyarsu da zarar ta koma Kano a koreta sai aga ta aurenta da Faruk, ranta ya yi wani irin daci, a fusace ta shiga motar ta banko murfin. Mamaki ya kama Hajiya, anya babu wata a k’asa? Daman ta lura kamar bata yi na’am da maganganunta ba. Haka ta bi bayan motar da kallo, tuni haushi da 6acin rai yasa Ikram juyawa ciki. Watakil nan gaba ma Ummi ta zama mai mulkar kowa a gidan, don taga alama ta samun kar6uwarta wajen Hajiya da Daddy. Acewarta DAN ADAM tara ya ke bai cika goma ba, zasu ga hali na butulci da Ummi za ta yi musu nan gaba indai akayi auren. Don ta sha jin labaru na irin hakan. Ummi duk tana kallon abinda ke faruwa, daman tun jiya da dare Hajiya ta sanarmata an fasa tafiyar da ita, sannan Faruk ya kira ya bata tabbacin kada ta sake ta shirya da zummar komawa Kano, ta daina aikatau daga ranar. Ta saki labulen kicin din gami da sauke ajiyar zuciya ranta ya danyi haske, ko babu komai alwashin da Ihsan ta ci akanta bazai tabbatu ba. Yanzu ita ina tasan zata ta samu motar garinsu idan suka korata? Saidai da tambaya kam. Ita har fargabar komawarta Ringim take, ko wane k’alubalen zata fuskanta a wajen Saude da Babanta? “Ke!” Ta firgita matuk’a ta juyo idanunta a zare kirjinta a sama don ji tayi har numfashinta ma kamar yana barazanar daukewa. Ganin Binta yasa ta dafe kirjinta gami da rufe ido tana sauke ajiyar zuciya. Dariya sosai Binta ta sanya, Ummi ta girgiza kai. “Wallahi ba ki ji yanda na tsorata ba, kai Binta saiki kashe mutum.” Binta cikin dariya ta daga mata hannu. “Yi hakuri, daman cewa nayi bari nagani ko za ki tsoratan, na manta yanzu ke fa a tsorace kike da kowa ma.” Ta yi murmushi tana tattare tafarnuwar da ta zubar a k’asa don kid’ima. “Na yi zaton Ikram ce ko Ihsan din ce ta dawo.” Sukayi dariya. Kafin kuma Ummi ta cigaba da 6arar tafarnuwa. Binta ta dubeta sa’ilin da ta janyo robar kifin da ta saka a ruwa don ya yi kankara ta soma kokarin gyarawa. “Wai ni don Allah meyasa ban ta6a jin kin fad’i wani daddad’an kalami na soyayya ba game da Yalla6ai? Sai nake ganin kamar ya fi sonki fiye da yanda ke kika daukeshi.” Wannan tambaya ta Binta, yasa Faruk cin burki daga kofar kicin don ya zo ne daman da niyyar tuhumar Ummi dalilinta na barin waya a daki ga shi yana ta kira. Ko wanka baiyi ba, hankalinsa na ga abar kaunartasa. Zai so jin amsar da zata bawa Binta. Hakan yasa shi yin cak yana mai zubamata ido don sun ba shi baya. Ummi ta yi murmushi wanda har gefen kumatunta ya lotsa. Batasan sadda ta soma magana ba. “Ni nasan yanda nake jin Yaya Faruk a raina Binta, akwai da yawa daga abubuwa wanda ba sai ka 6ata lokaci wajen bayyanashi ba, watakil ya nuna kansa wataran. Ina son Yaya Faruk fiye da kaina, zan iya sadaukar da nawa farincikin don kawai ya samu nasa. Binta me zance ga mutumin da ya daraja ni ya nunawa duniya ni din mutum ce mai daraja? Ke kuwa idan ban kaunaceshi ba me zan mishi?” Binta ta yi dariya. “Tabbas kinyi gaskiya, kin kuma burgeni matuk’a. Allah Yasa wannan kauna taku ta d’ore har ku haayyafa ku tara zuri’a guda taku.” Kunya ta hanata amsawa face murmushi da tayi. “Ameen.” Jin muryarsa yasa duk suka juyo a razane, ta zaro ido duk ta bi ta diririce, shikenan ya ji abinda ta ce kenan? Ji ta yi kamar ta nutse a k’asa don kunya. Ita kuwa Binta tana yar dariya ta russuna ta gaisheshi, ya amsa fuska a sake yana duban Ummi. Ita dinma gaisheshi ta yi dakyar sakamakon harshenta da ta ji ya yi nauyi duk don tsabar kunya. Ya amsa yana ji kamar ya nufeta ya rukunkume don dadin da kalamanta sukayi masa. “Zo nan Ummi.” Ya fad’a gami da juyawa ya fita. Ta bi bayanshi da kallo, daga shi sai dogon wando da singilet bak’a. Ta dubi Binta wacce ke zungurar kafadarta tana mata nuni da ta je. Ta yi murmushi mai bayyana hak’ora cikin muryar rad’a ta ce. “Anya bai ji maganarmu ba?” “Lallai ke dinnan, to meye idan ya ji? Daman kinason fadamishi kin kasa kinga ya hutar da ke.” Ta girgiza kai gami da wanke hannunta da handwash sannan ta mara mishi baya. A tsaye ta tarar da shi wajen hanyar da zata sada ka da sashensa. Ya kura mata ido kamar ya hadiyeta. Ta kauda fuskarta ta karasa gareshi. “Meyasa kike barin wayarki a daki sai nayita kira bakya d’agawa?’ Yana maganar cikin muryar shagwa6a kamar wani k’aramin yaro, abin ma sai ya bata dariya, idan yana wannan shagwa6ar wani kyau ya ke yi mata, ita dake mace ma bazata iya yinta ba. “Ka yi hakuri, aiki ne mukeyi.” “Naji, maimaita abinda kika fad’awa Binta yanzu a kicin.” Ta zaro ido tana kallonsa fuskarta dauke da murmushi, shima murmushin ya yi ya daga mata gira. “Kinyi zaton ban ji ba ko? Na ji dukkab tattaunawarku, oya idan dagaske ki ke maganarki ki cemin ‘Ina sonka Faruk’ na ji.” ‘Innalillahi…’ Ta karantota har karshe a ranta, gaba daya ta diririce. Shi kuwa dagaske ya ke, don tsayuwarsa ya gyara yana jiranta. “Kinyi shiru.” Ta hau wasa da yatsunta, murya a raunane ta ce. “Ni..ni ban ta6a fad’a ba fa.” “Shiyasa nakeso ki fad’amin, ya zama ni ne farko nine kuma karshen wanda za ki fad’awa hakan ok?” Ta runtse ido, yau ta shiga uku, ji ta ke yi kalaman sun yi mata nauyi da tsauri, bazata iya fad’a ba. Ya dan saka saman yatsansa manuniya ya zunguri hannunta. “Kin yi shiru Ummina.” Ta ja baya kadan ta hadiyi miyau. “Ka yi hakuri don Allah.” Ya lura a tsorace ta ke ma, sai kawai ya yi murmushi. “Ki ka ce ba ki da abinda za ki biyani? Ke kuwa ki ke da shi, kawo kunnenki ki ji.” Bata motsa ba, tuni shi kuwa ya matso da bakinsa dab da kunnenta. Maganar da ya fad’i ce ta rud’ar da ita, da gudu ta juya ta koma kicin. Ya bita da kallo yana dariya kafin ya juya ya soma tafiya. Wayarsa ta dauki k’ara, ganin Haidar ne yasa shi dauka da sallama. Bayan sun gaisa Haidar ya ce. “Ya Man, na ji ka shiru, ka kuwa fad’awa su Daddy?” Faruk yana taka matattakala yana murmushi ya shafi sumar kansa. Kafin ya soma kora mishi duk yanda akayi harma da rikicinsu da Dakta Ridwan da kuma cewar Hajiya na sai ya auri Ihsan ma. “I just don’t know what to do brother, ban ta6a son Ihsan ba, ban kuma ta6a yi mata kallon budurwa ba, ina mata kallon kanwata wacce ban bambanta ta da Baraka da Ikram ba.” Haidar wanda ya yi shiru ya soma magana. “Duk wannan bai dameni ba, kamar yanda ku ka samu sa6ani da dan uwanka ba Faruk, zan so ka je ka sameshi har gida ku fahimci juna. Banason akan lamarin aurenka a samu rarrabuwar kai a family, it’s something that never happen, so please don’t let it now.” Ya gamsu matuka da zancen yayannasa. Daman shima ya sauko daga fushin da ya yi da Dakta saidai kunya ce ta hanashi zuwa gidansa ya ba shi hakuri, wai shine ya nemi yi mishi rashin kunya akan ya ta6a matar da ya ke ji cikin zuciya da gangar jikinsa. Maganar Haidar ta katseshi. “Batu kuma na Ihsan, wannan ba yanda ka iya, ka zamo mai biyayya ga umarnin iyaye ko don ka cika d’a nagari. Ka yawaita addua akan neman za6in Allah ka ji?” Ya zauna a karshen matattakala batare da ya bude kofa ya shiga ba falonnasa ba, murmushi dauke saman fuskarsa na jin dadin maganganun dan uwansa ya ce. “Na ji Brother, zan yi yanda ka ce, bari na yi wanka nayi breakfast, zan je gidan Dakta idan ma ban sameshi ba zan shiga asibitin.” Ya ji dadin maganarsa. “Yauwa that’s my lovely brother, haka nake son ji. Nasan anjima zai shigo, gwara ka je kafin shigowarsa, nima ina nan tafe bayan Magriba idan Allah Ya yarda, don na k’ara ganin surukartamu da akai mana 6oyon fuskarta.” Dariya Faruk ya yi kafin suyi sallama ya mik’e ya fad’a d’akinsa. STORY CONTINUES BELOW *** *** *** RINGIM Bud’a ne ya cika gidan Baba Habiba sakamakon auren da aka daura na Zahraddeen da Khadija. Yawanci gaba daya danginta ne suak halarci bikin, daidaiku ne cikin dangin Malam Yahuza suka zo, wadanda zuwansu ma ba amfani awajen Baba Habiba don acewarta sun zo kwasar rahoto da gulma. Ita da aminiyarta Saude sun yi shiga ta sutura har kala uku ana yi ana chanjawa, Amarya kuwa kusan kala biyar ta yi domin wannan ranar. Da yamma Amarya na cikin taron jama’a suna gaisawa, wata yar uwarsu ta zo kiranta. “Kizo kinyi bak’i fa daga Kano.” Ta bi bayanta da mamaki don iyakar saninta bata da kowa a Kano. Gabanta ya bada wani bugu mai karfi ganin Raihana cikin shiga ta wata shegiyar shadda mai tsadar gaske, daidai da sark’ar da dan kunnenta abin kallo ne, ballantana kuma idan ka dubi agogo da awarwaronta kasan na gwal ne. Tana da ‘yar k’iba hakanan doguwa ce, ba laifi tana da kyau daidai gwargwado, wacce suke taren itama ta ci nata adon har ta gaji da haduwa. Murmushi Raihana ke jifanta da shi da wani dan iskan kallo wanda bai kyautu a matsayinta na yar uwarta mace ta yi mata ba. Ta daure ta k’ak’alo murmushin yak’e ganin cewa cikin mutane ne. “A’a, Raihana kece a garinnamu? Sannunki da zuwa.” Raihana da har lokacin bata bar murmushi ba ta amsa. “Yauwa Dijat , ke kuma haka akeyi?” Dija ta rude gudun kada ta ce wani abu da mutane zasu dagosu, tana shirin kwa6arta Baba Habiba ta karaso wajen duk ta had’a zufa saboda shiga da fita. Ganinsu yasa ta washe baki kamar gonar auduga, ta bisu da kallo daga sama zuwa k’asa sannan ta dubi Dija. “Wadannan fa?” ‘K’awayena ne na yanar gizo, sun zo tayani murna ne.” “A’a sannunku kun ji ko? Ina wuninki?” Ba kunya ta gaishesu, kasancewar suma yan duniya ne sai suka amsa. “A’a baza’a barsu anan ba kinga nan a cike yake, kaisu gidan Saude su zauna. Bari na kar6o muku muk’ulli.” Daga haka ta karasa ga Saude ta Kar6o ta damk’awa Dija. “Jeki can na kawomiki kazar ma ki ci acan kinga asiri a rufe.” Ta fada cikin k’ank’an da murya. Dija ta murtuke fuska. “Aa, ki barshi sai dare.”. “To shikenan.” Ta ja su Raihana zuwa gidan Saude. Bayan sun zauna Raihana ta rik’o hannunta idanunta sun kada tsabar kishi. “Ba ki kyautamin ba Dijat, yanzu wannan kwalliyar duk don Deen kikayi ba don ni na ganki na ji dadi ba? Haba Dijat, ba ki ta6a yimin kwalliya irin haka kin aikomin na gani ba.” (Wa’iyazubillah) Dija ta daure fuska gami da zame hannunta. “Ki bar wannan magana mana Raihana, ke meyasa kike da sa6a alk’awari? Ban gargadeki kada ki zo gidanmu bane?” Raihana ta yi raurau da fuska. “To ya na iya tunda dai kin kashe wayarki kwana biyu bana samunki, ni kuma hankalina duk ya tashi na ji tsoron kada ki juyamin baya shine na zo.” Dija ta ja tsaki sannan ta mik’e. “Ina zuwa.” Daga haka ta fice, Raihana da abokiyar tafiyarta, Saima, suka bita da kallo cike da shaawa. Saima ta maido dubanta ga Raihana. “Ashe dai a kauye ana samun mata har haka? Ke kam kinyi dace.” Ta daure fuska. “To meye naki ciki?” “Aa, bakomai ranki ya dade, ni mamakin ma da nakeyi ya zaayi kamarki ki zauna wai wannan ta gagareki juyawa? Haba Hanah, dubun da suka fi ta ma kin shawo kansu ta hanyar malamai balle kuma ita?” Raihana ta numfasa. “Ni wannan so nakeyi mata na gaske, ba don ta kafe akan wannan shegen Deen din ba da har aurenta zan so yi. (Waiyazubillah) saidai ya zo yana son yimin shigar sauri.” Saima ta jinjina kai, lallai ba karamin so take yiwa Dija ba, banda haka, manyan mata nawa ne suka so samun wannan damar amman ta k’i basu sai ita? Duk yanda taso ta shawo kan Dija abu ya ci tura don kwata-kwata bata bada fuska ba, ta ce ko menene sai ta je Kaduna, haka gwuiwa a sake Raihana ta juya bayan ta bata makudan kudade da suka girgizata. Washegari aka tattarata aka mik’a Kaduna gidan Deen, har lokacin Munira bata dawo ba tana Ringim don ta ce bazata iya ganin rawar kan da mijinta zaiyi akan yar uwarta ba da ta ci amanar yan uwantaka. Gudu ta ke yi itama tana binta a guje suna k’ara runtumawa cikin dajin da babu gida gaba babu a baya, har ya kai ta taka k’aya, ta zube a wajen tana numfarfashi, takobi ne shar6e6iya sai kyalli ta ke, doguwar mace kyakkyawa ce rik’e da wuk’ar kafin akan idanunta ta fuskarta ta rikid’e zuwa kalar kore. “Saina kasheki! Saina kasheki ke Makira!!” Tana ihun kuka tana fadin kiyi hakuri na tuba Hasiya karkimin haka don Allah. Amma ina bata ko saurareta ba ta daga takobin nan, ai kuwa ta fasa k’ara. Yi ta ke babu kakkautawa duk ta hargitsa mutanen dakin, suka rirrik’eta, fadi take. “Zata kasheni! Wayyo zata kasheni wallahi! Ku taimakeni!” Cikin gigita Saude ta kai hannu ta toshemata baki. “Ke Habiba shiga taitayinki, mafarki kikayi?” Sai lokacin Habiba ta gane ta farka, ta dubi jama’ar dakin ‘yan rakiyar amarya Kaduna ta sauke ajiyar zuciya gumi yana ta tsastsafowa daga goshinta, ita kuwa Habiba idanunta a zazzare, rashin gaskiya ya bayyana k’arara akan fuskarta. Tana jin matan na fadin addua ya dace ta dungayi idan ta yi mafarki. Har dai kowa ya koma makwancinsa. Dabara ta fadowa Saude. “Tashi muje ki sha ruwa.” Suka mike suka fita zuwa kicin, ta dakata gami da rike kafadar Habiba. “Gayamin wane irin mafarki kika yi?” Habiba wacce har lokacin jiki ke rawa ta zayyanemata komai, hankalin Habiba ya tashi, ji ta yi hanjin cikinta sun kad’a. “To, meke shirin faruwa haka? Mun shiga uku.” “Ba ke kika shiga uku ba Saude, ni da na ganta ganin idona ai ni ce da shiga uku.” Saude ta dubeta da idanunta da sukayi kwalkwal. “Kada fa allura ta tono garma?” “Kar ki damu, da zarar mun koma zanje wajen bokanya, ko menene zata sanarmana sai a dauki mataki.” Saude ta jinjina kai cike da gamsuwa. A karshe suka koma makwancinsu batare da ko ruwan Habiba ta iya sha ba. *** *** *** KANO

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *