DAN ADAM CHAPTER 2
Karki damu Ummi, ki cigaba da hakuri sa mik’awa Allah lamuranki. Komai kika gani, daga gareshi ne. Watarana zaki ga komai kamar ba’ayi ba, nan gaba zakiji dadi a rayuwa in sha Allah. Kada kiyi bakinciki da zuwanki gidan Hajiya, na tabbatar ko a kwana d’ayan nan da kikayi, kinga chanjin rayuwa ballantana kuma idan ya zamana kin shure satittika anan. Nasan dai duk wani wuya da zaki ci anan bazai kai rabin wanda kika labartamin ba. Hajiya bata duka, bata zagi haka kawai, saidai idan ka ta6a jininta, zata budemiki wuta tayi fada sosai harma idan baki taki sa’a ba ta goranta miki. Duk kuma wani abu na rayuwa ki daukeshi mukaddari ne daga Allah, ba wanda zai tsallakewa kaddararsa kinji ko?” Cikin jin wani sanyi ta gyad’a kanta. “Toh Anti nagode.” Amina tayi murmushi. Baccin safen da basu samu komawa kenan ba, sukayi ta hira a karshe Amina ta mike ta shiga wanka. Bayan ta fito Ummi itama ta fad’a. Ta kammala ta fito, Amina tuni ta shirya cikin doguwar riga ta yadi, daga gaban rigar, anyi adon duwatsu, ire-iren dai wanda take samu daga Hajiya Mama ko yaranta. Ummi ta dubeta, tayi mata kyau, zata soma duba jakar kayanta ta ji muryar Amina. “A’a Ummi, ga kaya ki saka.” Ta juyo don ganin ko ta ciro mata ne, saidai ta ga wasu da ba nata na asali ba, riga doguwa ce ta abaya. Ta dubi Amina ido a waje. “Lah, anya kayanki zasu yimin Anti?” Amina ta murmusa. “Wannan na jima bana sakashi, na kuma tabbatar ba zai k’i yi miki ba. Kedai gwada mugani. Idan kin kammala ki fito ki gaida Hajiya, nasan yanzu ta farka.” Ummi ta amsa da toh, Amina ta fice. Rigar ta kar6eta kwarai tayi mata kyau kasancewarta farar yarinya. Ta dauki dankwalin ta d’aure gashinta wanda idan mutum yaga yanda yayi mata, zai iya cewa tayi d’aurin acuci. Saida ta dauke shimfid’a ta d’an gyara d’akinnasu duk da ba daud’ar azo a gani don Amina akwai tsafta, sannan ta bi bayanta. A falon ta tarar da Hajiya Madina zaune cikin kwalliya tana karyawa, Amina bata nan, ta karasa ta durkusa ta gaisheta a ladabce. Hajiya Madina ta amsa fuskarta a sake, bai wuce ganin yanda Ummin tayi fes ba don ita ba mace ce mai son zama cikin k’azanta ba. Ummi ta zauna, idanunta akan talabijin, saida Hajiya ta kammala sannan ta umarceta da d’auke kayan, ta d’aukesu ta kai kicin. Acan ta had’u da Ramma tana faman gyare-gyare. Ta gaisheta a mutunce, Ramma ta amsa har tana zolayarta wai har ruwan birni ya soma kar6arta ta chanja saidai k’ashin wuya. Ita dai murmushi tayi kawai. Tana shirin fitowa sukayi kici6us da Amina, hannunta rik’e da tsintsiya da kwandon shara. “Kinga yayi miki kyau ko? Nima na gyaro d’akin Hajiya ne, kije tana kiranki ma.” Ai da sauri Ummi ta fita don amsa kiran. Wannan karon a kan kujera ta sameta tana amsa waya. Zama tayi har ta kammala sannan tayi magana. “Gani Hajiya.” Ta dubeta a nutse sannan ta soma magana. “Yauwa Ummi, dafatan dai Amina ta nunamaki dukkan ayyukan da takeyi? Toh inaso ki zamo mai rike amana, muddin kika ci amanata, bazan kyaleki ba. Yanda zan rik’i amanarki da gaskiya a matsayinki na Amanar a hannuna, haka kema nakeso ki rike, ki kula da dukkan ayyukan da zaki dunga yi.” Ta k’ara karanto mata ayyukan harma da na gyaran sashenta ciki da falonta na biyu, banda wannan da suke ciki don duk cikin aikin Ramma ne. Ta k’ara jaddamata cewar batason k’azanta, hakanan ta kiyaye tsaftar suturunta, duk sadda zatayi wanki, ta tambayi omo zata samu. A dai maganganun Hajiya, Ummi ta fahimci cewa dagaske batason k’azanta kuma tana da kyankyami. Ta rausaya kai. “In sha Allahu Hajiya zan zama mai kula da dukkan abinda kukace, nagode Allah Ya k’ara girma da arziki.” Har a ranta ta ji dad’in maganganun Ummi. “Shikenan kina iya tafiya.” ☆☆☆ Tun daga wannan ranar, Ummi ta kama aikinta sosai, Amina na taimakonta. Har ya kasance wani sa’in kafin Amina ta tashi, ta rigata tashi. Tana jin dad’in zama da Amina saboda shawarwarin da take bata, har karatu tana koyamata. Duk da cewar Amina na cin wuya don Ummi ko bak’i bata iya ba. Duk sai ta bata tausayi, haka take lalla6awa ta biyamata, amma ta tabbatar muddin tana wajen Hajiya Madina, bazata ta6a bari ta zauna mata da jahilci ba, duk wadanda suka ta6a zama sukayi aiki awajenta, ba wacce bata sanya a islamiyya ba, boko ne dai ba lallai ka samu ba. Saida Ummi tayi sati da zuwa, sannan Amina ta soma shirin tafiya don Hajiya Mama sun dawo. Gaba daya ta ji babu dadi, tana zaune gefe tana duban yanda take ninke kayanta tana sanyawa ciki jaka. Amina ta ankara da duban da takeyi mata, itama sai taji batason rabuwa da ita. “Haba Ummi, menene abin damuwa har haka alhalin muna gari d’aya? Karki damu, na tabbata zamu dunga ganin juna. Kedai ki cigaba da hakuri da zama da su tsakaninki da Allah.” Ummi ta gyad’a kai. “Toh Anti.” Sai yamma suka tafi har Hajiya da su Adnan, gidan ya rage Ummi kad’ai da Ramma. Bayan ta kammala ayyukanta ta fito farfajiyar gidan tayi zamanta. Bata kai mintuna biyar a zaune, budurwar da bazata ta6a mance fuskarta ba wacce suka samu sa6ani da Adnan a farkon ganinta da su, ta fito daga sashensu tare da k’awayenta har su biyu suna dariya. Hararar da ta sakarmata ne yasa ta dauke kanta babu shiri ta saddar a k’asa, ta gabanta sukazo wucewa, ai kuwa ta sanya takalminta mai tsini ta take yatsun k’afarta har saida tayi k’ara. Ta juyo ta rankwasheta. “Munafuka, sharri zakiyimin kina gidan ubana kina cin arziki? Shegiya kawai.” K’awayen dariya kawai sukayi, d’aya tana fad’in “Kai Iklima baki da kirki.” Iklima ta ta6e baki. “Na kaiku?” Suka fice Ummi ta mike da sauri tabar wajen, saida ta tsaya a lungun ta share kwallah sannan ta k’arasa ciki. Ta zauna a kicin tana kallon yanda Ramma ke faman had’a miya, tana dan jan Ummin da hira har ta share batun Iklima ta saki jikinta. ☆☆☆ Kamar yanda Antinta ta sanarmata, haka din kuwa akayi. Gaba daya d’akin Hajiya Madina suka tattara suka fita, duk a nata zaton, a gida za’a barta kamar yanda Amina ta shaidamata. Saidai ga mamaki, Hajiya Madina tace ta shirya su tafi. Ihsan ta dubi Mamin fuska a yamutse. “Kai Mami, don Allah ina kuma zami je da ita? Abu namu na zuri’a?” Mami ta daure fuska. “Toh gwana, saiki gayamin yanda zanyi.” Daga haka Ihsan ta ha bakinta ta tsuke. Ummi ta shirya cikin doguwar riga ‘yar kanti bak’a mai adon fari da ruwan toka a gaba da kuma hannuwa. Ta yane kanta da mayafin rigar batare da ta shafa komai a fuskarta ba ta fito. Suka dunguma bayan Hajiya Madina ta kammala shirinta zuwa wajen mota. Sunyi tafiya mai dan nisa kafin su iso wata unguwa wacce ko za’a matse Ummi batasan sunanta ba. Ta ga sun shiga wani layi, anan ma sun danyi tafiya kafin suka ga tsayawa daidai wani katafaren gida ginin bene. A zatonta anan zasu tsaya, sai gani tayi danliti ya danna ham, wani dan saurayi ya mike ya budemusu yana mai d’ago musu hannu. Wani ajiyar zuciya Ummi ta saki ganin yanda aka k’awata farfajiyar gidan da shukoki, wurin motocin da ta hango acan wata ‘yar rumfa ta ga sun nufa suma, saidai bai karasa ba ya faka. Duk suka fito, sannan ya karasa ciki. Suna gaba tana binsu a baya hannunta rike da Fahad wanda zuwa yanzu ta saba da shi ba kad’an ba kasancewarshi yaro mai son mutane. Banda kalle-kalle babu abinda takeyi har suka iso wata kofa da kai tsaye ta sadasu da wani dan karamin tsakar gida wanda aka dan yi gewaye a tsakiyarsa aka dasa shukoki. Ihun da ta ji ne ya katseta, wasu yan mata ta gani sun rungume Ihsan yayinda shima Adnan ya hau cafkewa da wasu maza a karshe suka hau rungumar juna ana dariya. ‘Wadannan kuma su wanene?’ Ta wurgawa zuciyarta tambayar, bata kai ga gama tantancewa ba ta k’ara ganin wasu yanmata biyar suma sun fito suna fadin oyoyo Anti Mami. Ukun dai ta sansu, da Intisar ne da Rukayya da kuma Maryam yaran Hajiya Mama, biyun ne dai bata sansu ba duk kuwa da cewar sun had’u a sunan Aisha. Bayan sun kammala rungume-rungumensu ne suka dunguma zuwa ciki gaba daya. Ihsan ta juyo da sauri ta matso daidai gefen Ummi. Tana dubanta duba na raini tace. “Saura kiyi karambanin biyomu, ki nemi wuri ki zauna anan.” Ta amsa da toh sannan ta ja baya ta fasa niyyarta na binsu. Bayan shigewarsu ta koma can gefe ta ja kujerar roba daya cikin hudun da ke zagaye da tebur ta zauna ta zabga uban tagumi. Ko kusa bata ganin laifin Ihsan, daman ai ita ba wata bace a wajensu face yar aiki, dole ne kuma ta cigaba da amfani da nasihun Antinta gudun abinda zai jawo a dizgata gaban mutane. ‘Dizgi?’ Ta tambayi zuciyarta, toh kuma dizgi ya wuce wanda ta gama sha awajen shakikanta wadanda su kadai ne zata iya bugun kirji ta kira a matsayin nata? Sun gujeta sun manta da ita, tunda suka kawota har gashinan ta kusa yin wata a garin da babu iya babu baba, a wajen mutanen da bata da had’i da su sai na Allah. Bata kara sanin tayi rashin uwa ba sai bayan ta soma zuwa makarantar islamiyya, yanda ake kara koyar dasu gami da nuna musu muhimmancin biyayya ga iyaye. Ita kam bata da wannan gatan, har fargabar ranar da Hajiya zata gaji da ita ta koreta daga gidanta takeyi, tana rantsuwa da Allah batasan hanyar da zata bi ta koma garinsu ba a karan kanta matukar ba Yaha ce zata zo ta maidata ba. Daddad’an kamshi da kuma zazzakar muryar da ta tsinta awajen ne ya katse mata tunani, ta d’ago kanta tana duban mai ita. Tsaye yake ya zura hannunsa na hagu acikin aljihun wandonsa, hannun damansa kuwa, waya ce wacce ya kafa a kunne. Farin bafulatani ne, kansa cike da suma, saje a kwance saman fuskarsa yayi luf-luf. Yana da matsakaicin tsawo,hakanan yana da fadin fuska kadan, idanuwansa daidai misali hakanan siririn karan hancinsa da tsukakken le66ansa ruwan hoda, ya kara taimakawa wajen fiddo da tsantsar kyawun halittar da Allah Ubangiji Ya mishi. Sanye yake cikin shadda ruwan k’asa, kansa babu hula, agogon daya d’ora a hannun hagunsa ya kara fiddo da kyawun hannunnsa wanda ke cike da gargasa. A tsanake yake fidda kalmomi, hausa da turanci kawai yake gwamutsawa, idan yayi hausa, can gaba kuma ya jefa turanci, abin sai ya burge Ummi. Tayi shiru ta zubamasa ido tana sauraron yanda yake hada yare biyu lokaci guda duk da cewa ta sha jin hakan daga Ihsan, saidai ko rabin kwarewarsa Ihsan batayi ba. Daidai lokacin da yayi sallama da wanda suke wayar da shi, suka had’a ido, babu shiri tayi gaggawar janye nata idanun daga gareshi. Koda ta k’ara d’agowa, bata ganshi a wajen ba don tuni ya koma ciki. Ta sauke ajiyar zuciya, ta tuno da ‘yar ajinsu wata Khadija, wacce bata da aiki sai hirar samari a aji, burinta bai wuce ta samu namiji kyakkyawa kuma mai kudi ta aura ba. Har mamaki suke bata, duka-duka tasan da wuya idan suma zasu fi shekara goma sha biyar kamar ita(GYARA) amma har ace sun waye da batun samari har haka, sai kuma ta tuna da cewar da ace a kauyensu ne da tuni watakila itama an aurar da ita. Abin kuma sai ya sanyata I murmushi, wa zai aurar da ita? Ai kenan ma Saude ta nunamata gata, akan kunnenta ta sha jin tana fadin saidai ta karar da rayuwarta a bauta mata, aure ne saida ta ga ana yi ba dai ita tayi ba. Hawaye ta ji suna kokarin taho mata da takaici, gaskiyar Saude tunda yanzun ma gatanan acikin hali na aikatau wanda duk a sanadinta ne, kudin da ta riga tasan na amfaninsu ne banda ita. An barta dai da wahalar. “Kamota nan!” Firgigit ta dubi wanda ya tsoratatan don gaba daya ta zurfafa cikin tunani. Ganin Amina yasa ta mikewa tsaye da mamaki, sai kuma suka hau dariya. “Kai Ummi, tunanin me kikeyi haka wai?” Ummi wacce ta kasa rufe bakinta don tsabar murnar ganin Amina ta amsa da fad’in. “Bakomai, kikacemin ba zaki zo ba?” Amina dauke da murmushinta na sabo tace. “Wallahi ban saka ran zanzo ba, Hajiya Mama ta matsamin akan na biyosu kawai.” Abin ya bawa Ummi mamaki, ta kara gaskata cewa Hajiya Mama ba ruwanta. Amina ta dubi ledar hannunta. “Ina zuwa bari na mikawa Anti Rahila famfas nazo.” Daga haka ta shiga ciki da sauri ta nufi ciki. Ummi ta koma ta zauna ranta yayi fes cike da murnar sake haduwa da Amina wacce ta dauki matsayin Anti kacokam ta bata ba don komai ba sai don yanda ta nuna kauna gareta a farkon haduwarsu da kuma yanda take da kokarin yi mata gyara aduk lamuranta na rayuwa. Bata jima da shiga ba sai gata kuma ta fito, tana kokarin jan kujera ta zauna ne ta dubeta. “Meyasa baki shiga ciki ba?” Ummi ta zaro ido kadan. “Ciki kuma? Um um, Ihsan tace kada na sake na shigo.” Amina ta ja guntun tsaki. “Bansan sadda yarinyar nan zata dawo saiti ta gane cewa shima dan aiki mutum ne ba. Ki dai kara hakuri.” Murmushi kawai Ummi tayi. “Anti ‘yan Abuja ma sunzo ne?” “Su ai tun jiya suna garinnan, basu je gidan Mami ba kenan? ” Ta girgiza kai. “A’a.” “Sunzo, Ikram, Baraka, Yaya Usman, Yaya Ridwan, Yaya Haidar da kuma Yaya Faruk.” Jinjina kai kawai Ummi tayi batare da tace uffan ba. Sai kuma suka fad’a hirar da ta shafesu, sun jima sosai anan kafin kuma wata dattijuwar mace ta leko. “Ke Amina, kuzo ku taimaka mu kaiwa bak’i abinci.” “Toh Larai.” Ta dubi Ummi. “Muje.” O Ummi ta mike gaba daya sai ta ji wani nauyi, kamar kada ta je haka take ji, fatanta kada Ihsan ta ci zarafinta a bainar jama’a. Takalma baja-baja a dan koridon shiga falon, suka shiga da sallama. Saidai abin mamaki bata ga kowa anan ba sai ta dunga jiyo muryoyi da dariyarsu daga can sama, hakan ya tabbatar mata suna can. Zugui-zugui tayita bin Amina har zuwa wani kicin mai girma. Nan taga kuloli manya guda hudu sai tarkacen filettoci da cokula da kofina a saman teburin dake tsakiyar kicin din. “Yauwa ku soma kaiwa, Amina ga ledar nan ki soma da shinfid’ata.” “Toh” kawai Amina tace sannan ta ja linkakkiyar ledar ta hada da filas guda d’aya, itama Ummi ta dauki filas d’aya don girma ne da su, ta bi bayanta suka soma taka bene. S