DAN ADAM CHAPTER 27

DAN ADAM CHAPTER 27 

 Washegari Dada da kanta ta yafa mayafi ta shigar da Ummi makwafta suka yita ganinta tana nunamusu jikarta diyar Hasiya. Ummi har ta rasa inda za ta saka kanta don murna, fararen hakorannan nata sun kasa rufuwa, a karshe suka dawo gida. Batun Mariya kuwa, Dada har mancewa ta ke yi da ita don dagaske jininta yafi haduwa da diyar Hasiyarta. Koda suka dawo anan waje suka tarar da Malam Balarabe da mahaifinsa suna hira. Ta daure fuska tamau kamar bata ta6a dariya ba, ko sannu da zuwan Malam Balarabe bata amsa ba. Ta gaida mijinta ta yi gaba. Haka ya sauke ajiyar zuciya ransa duk ba dadi. Malam ya girgiza kai. “Kar ka gajiya, ka cigaba da rok’onta gafara, Fatima mace ce mai hakuri saidai tana da zafi idan an ta6ota, ni nasan tana kaunarka matuka, na sha kamata tana kuka duk akanka, yanzun kuma da ka zo sai ta yi fushi? Karka damu zata sauko.” Wannan magana ta karfafawa Malam Balarabe gwuiwa, ya saki fuskarsa sosai. “Ai ni na yi mata laifi, dole na bita a sannu.” Murmushi kawai Malam ya yi. “Ina matarka ne?” Gaban Malam Balarabe saida ya fadi, cike da damuwa ya labartamishi dukkan abinda ya faru tun bayan mutuwar Hasiya kawowa yanzu da Saude ta haukace da irin tone-tonen da ta yiwa kanta. Malam banda ambaton Innalillahi babu abinda ya ke yi, tausayi matuka na Ummi da dannasa ya mamayeshi. “Yanzu Hasiya saida ta yi aikatau? Allah Mai Yanda Ya so da bayinSa.” Shima Malam Balarabe da jikinsa ya yi sanyi ya amsa da eh. Kafin ya sanyomishi batun maneman auren Ummin. Da kuma irin taimako da suka yiwa Ummin a rayuwa. Malam ya danyi jim sannan ya numfasa. “To, shi lamari na aure ai na Allah ne, kwarai sunyi mana halaccin da suka cancanci mu dauki diyarmu mu basu. Allah Ya za6amata abinda ya fi alheri.” Malam Balarabe ya amsa da amin. Haka sukayita hirarsu abin sha’awa. Bayan Magriba suna zaune suna hira a tsakar gida har Dada, Ummi na kwance ta yi matashi da cinyarta ita kuwa tana aikin tsefemata kai tana fadan tabar kai kitso ya tsufa. Ita dai banda murmushi babu abinda ta ke yi, ta lumshe idanunta, gatan kawai ta ke gani tamkar a mafarki. Wayarta ta dauki k’ara, ta bude idanunta da sauri, tun dazu ya ke kiranta a hanya saidai ganin tana cikin mutane ne yasa ta jin kunyar dagawa, ta janyo wayar a sanyaye ta ce. “Dada tsaya na amsa waya.” Dada ta saki kannata, ta dan dubi Dada, ita din kuwa ta zubawa ido, kawai sai ta mike a guje ta fada daki tana murmushi daidai lokacin da ta ke amsawa da sallama. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta ji ya saki wanda ta ji shi har cikin ranta. A sanyaye ya amsa sallamar gami da fad’in. “Ki yi hakuri kin ji don Allah.” Ta kasa gane inda maganarsa ta dosa, ta yi hakuri fa? Yaya Faruk ke bata hakuri? “Hakuri kuma? Akan me?” “Ba ki ji yanda hankalina ya tashi jin shiru ba ki amsa wayata ba Ummi, har ina niyyar biyo bayanki Gombe.” Ta numfasa sannan ta murmusa, duk a zatonta wani abin ne daban ko kuma cewa zai yi ya fasa aurenta. “Kai zan bawa hakuri Yaya Faruk, wallahi muna tare da su Dada ne ni kuma kunyar daukar wayar na ke yi.” Ya yi murmushi mai sauti. “Karki damu, ya wuce, saidai dagaske ina jin zan shigo Gombe karshen satinnan, nisan ya na takurani, na soma gajiya da rashin ganinki.” Ta kasa cewa komai sai murmushi, a haka Dada ta shigo daukar damammiyar furarta a kwanon sha ta ganta, duk sai ta diririce, Dada murmushi kawai ta yi ta fice. “Kin yi shiru, dagaske za ki iya ganina.” “Ba ka kunyar su Daddy?” Ta fada cikin sanyin muryarta. Ya dan yi dariya. “Haba Ummi, Daddy fa ki ka ce? Kar ki damu, sunsan irin kaunar da nake miki wacce sai na daure matuka na ke iya 6oyonsa, bansan wace irin addua ki ke min na har kullum kaunarki ke k’aruwa cikin raina.” Ta girgiza kai tana dan dariya kawai. Sun dan jima suna hira sannan suka yi sallama. Koda suka kammala sai ta kasa fita ta yi zamanta a dakin ta kwanta saman gadon karfen Dada tana game. Can jimawa kadan Dada ta shigo tana fadin. “Wai ‘yarnan ba ki gama wa…” Ganin da ta yi mata kwance tana wasa da waya yasa ta rike ha6a. “Au, tsifar kenan? Shi ne ki ka yi kwanciyarki anan? To kin kyauta ai daman dare ya yi nima hannuna ya gaji, taso ki sha fura ga farfesu can Abida ta aikomiki.” Ta mike tana mai kokarin rufe kanta da dankwali don sam bata mance tsifar ake mata ba, kawai nauyinsu ne ya hanata fita. “Allah Yasa ba sukari sosai a ciki irin na dazu.” Dada ta murmusa. “Kema bakya son sukari sosai? Allah Ya jik’an Boddo, itama haka ta ke ko kadan bata son sukari. Komai naku dai daya.” Jin haka yasa Ummi zamowa daga gadon bayan ta amsa da amin. “Ni kuwa Dada wai da wa Ummana ta yi kama tsakanin kakana da kakata.” Jin haka yasa Dada zama gefenta gami da dubanta fuska a sake. “Mahaifiyarki ta dauko kamannin Kakanki Usmanu Lamido, wanda suke kama sosai shi da yan uwansa, musamman babbar yayarsu Bintu dake aure garin Adamawa da yaranta uku, danta namiji guda ne Allah Ya azurta mata shi, a hannunta Karamar uwarki (Zahra) wacce suke kira da Inno ta girma, ana shirin aurenta ta rasu. Idan da zaki ganta itama marigayiya Zahra, sai ki rantse mahaifiyarki ce don kamannin da kuma jini. Ta jinjina kai kafin ta k’ara da fadin. “Wai akwai yan uwanmu ne a Adamawan nan sosai? Naga har kanwar Baba itama can aka ce ta yi aure har ta rasu.” “Dangantaka mai karfi kuwa da Adamawa, duk kuwa da asalinmu Kwami da Jar Kwami, saidai mazajenmu da iyayenmu sun yi tafiye-tafiye, wasu suka yada zango Adamawa har suka tara iyali. Ba acan ne shi Lamido Shuaibun ya auro mahaifiyar Yakubu mijin marigayiya Aishatu kafin kuma su rabu ta koma can, a hannunta Yakubun ya girma ai wani zuwansa nan ya ga Inna Boddo a Jar Kwami ya nuna yana so, sai mutuwa ta rabasu.” Ummi zata k’ara magana saidai bata samu dama ba, don Dada mikewa ta yi. “Kinga, tashi mu je ki sha fura sai mu zo ki ban mijinnawa a waya mu gaisa don na lura sai kumbiya-kumbiya ki ke kada ya ji muryata ya fasa da ke.” Jin haka Ummi ta yi dariya tana rufe fuskarta, Dada ta fice itama tana yar dariyar. Washegari…. Washegari misalin takwas bayan sun gama karyawa suka yi shirin tafiya, kamar kullum, yau ma Malam Balarabe ya shigo har dakin Dada don gaisheta, saidai ko kallo bai isheta ba, Ummi tana duban mahaifinta cike da tausayi har ya gaji ya kara da fadin. “Za mu wuce.” Uffan ba ta ce ba sai ma mikewa da ta yi ta fita, ya dan bita da kallo jiki a sanyaye kafin ya dubi Ummi. “Idan kun gama sai ku fito, bari na je nan makwafta wata gaisuwa na dawo.” Ta amsa da to, bayan fitarsa ta ja bakin mayafinta mai adon jajayen fulawa ta rufa akan riga da siket din dake jikinta na wani fari da jan yadi, ta ci kwalliya don ta fi so suna ganinta cikin lumana koda suna fushi da mahaifinta su huce. Idan ka ga Ummi ba zaka ce itace ba, ta yi kyau kwarai hakanan ta ciko a kwana ukun da sukayi kacal, babu damuwa babu mai tsangwamarta ko kuma jifanta da kallon banza balle uwa uba gorin gida. Shigowar Dada ne ya katse tunaninta, ta rataye bakar jakarta. “Kaga ‘yata ta fito.” Ta dan tamke fuska don har zuciyarta bata jin dadin abinda Dada ke yiwa mahaifinta. Ganin haka yasa Dada ta rude. “Ke meyafaru? Ko wani abin ya ce miki?” Ummi ta dan karyar da wuya sa’ilin da ta ke zura takalmi kamar bata so ta ce. “Don Allah Dada ki daina yiwa Babana haka ba dadi, don girman Allah ki yafemishi. Ya yi muku laifi saidai shima ba laifinsa ba ne, da kanta Saude ta tona dukkan mugun ayyukan da ta yi ciki har da..” Zata fadi na kashe Ummanta da ta yi sai kuma ta yi shiru don batasan zafin da zata kara dauka ba. “Bari ki ji kadan daga abinda ya faru.” Ta soma koro mata bayani a gajarce, da kadan cikin zaman da suka yi da Saude bayan mutuwar Hasiya da aikatau da ta yi da irin karamcin mutanen da suka dauketa aikin har zuwa komawarta Ringim da yanda abubuwa suka kasance har da haukacewar Saude da kai Habiba gidan yari. Ta dubeta. “Naso 6oyemiki cewa kashe Ummana sukayi saidai naga kamar ba amfani. Komai da ya faru babu laifin Baba, idan hakane nima zan iya yin fushi ai tunda babu wani cikin yan uwan Ummana da ya nemeni, amma na yi hakuri da na fahimci ba ku da laifi kusan laifin na Saude ne tunda Baba ba cikin hayyacinsa ya ke ba. Ko don wannan don Allah ki yafemasa.” Dada ta dan daure fuska. “Jeki suna jiranki, Allah Ya saukeku lafiya, ki gaidamin Inna Boddo.” Ummi ta dan yi murmushi a sanyaye kafin ta amsa da toh sannan ta juya ta fita. Dada ta bita da kallo, kafin bayan fitarta ta zauna da6as a saman gado. Kawai sai ta soma shar6ar kuka tana ambaton Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun! Ashe haka lamuran suka afku? Ko jiya Malam ya yi niyyar fadamata saidai bata ba shi dama ba asalima tashi ta yi ta bar wajen. Ta tausayawa dannata ainun amman daman wanda bai ji bari ba zai ji hoho, illar rashin jin maganar iyaye kenan, sai gashinan ya janyowa kansa bala’i. “Allah Ya jikanki Boddona, Allah Ya yi miki rahma.” Ta fada a hankali. Acan kuwa su Ummi suka gama sallama da kowa suka kama hanyar Jar Kwami har Haruna wanda shi ya yi musu rakiya. Bayan sun isa kai tsaye gidan Lamido Shu’aibu yaya awajen Manu kakan Ummi. Ummi ta dubi gidan, gidan gargajiya, saidai babba ne, suka shiga ciki. Anan kofar gidan k’asan ‘yar rumfa, Lamido Shu’aibu ne kishingide saman wata darduma akan tabarma, ga wasu dattijai su biyar zaune gefensa ana hira, saidai ganinsu ne yasa su maida hankali garesu. Ummi ta lura da mutum uku masu kamanni farare ne saidai tsufa ya dakusar da haskensu. Malam Balarabe da Haruna ne suka karasa suka durkusa wajensu, yayinda Ummi da Mariya suka durkusawa a gefe suma. Bayan an gaisa, Lamido Shuaibu cikin harshen fulatanci ya ke tambayar ko su waye. Shima ya ba shi amsa da fillancin ai tuni waje ya karade da murna, Malam Balarabe ya karasa suna dafashi baki a washe, wani har da goge kwallar farin ciki. Tsoho Mai ran karfe Usmanu Lamido ya dubi Malam Balarabe da harshen fulatanci ya ce. “Ashe da rabon na kara sanyaka a ido kafin na mutu Abdullahi?” Kunya ta bi ta cika Malam Balarabe ya hau bada hakuri yana nuna ba laifinsa bane. Ya waiwaya ga su Ummi. “Ku karaso nan.” Suka taho, Ummi ta durkusa ta gaishesu, suka zubamata idanu. “Wannan itace diyar wajen Hasiya, itama Hasiyar sunanta, Ummi.” Suka yi kabbara. “Ai ko baka fada ba na ga kamanni, matso gareni Boddo.” Cewar Dattijo Usmanu. Ummi ta matsa gareshi tana jin hawayen farin ciki na kokarin zubomata. Ya rungumeta ya fashe da kuka, itama kasa jurewa ta yi ta sanya kukan, bawan Allah jikinsa har rawa ya ke yi. Saida aka basu baki sannan ya yi shiru. Ya dagota yana shafa fuskarta kamar Boddonsa. Ta karasa ga Lamido Shuaibu shima ya dafa kanta yana murmushi mai bayyana hakora, duk girma ya kamashi dakyar ya ke gane mutane. “Allah Ya yi miki albarka. Ya ji kan Mammarki.” Ta amsa da amin. Bayan duk an gama gaisawa sukayi cikin gidan inda tuni labari ya je musu ga diyar Hasina ta zo daga burrni. (Lol). Nan aka zubawa Ummi ido ana kallonta baki sake, wasu dakyar suke samun karfin gwuiwar gaishe da su sakamakon ganin tsantsar kamanninta da mutan gidan. Kai tsaye Haruna ya nufi da su 6angaren Inna Boddo wacce tuni labari ya iso gareta saidai babu mai kaita ta ganota. Inna Boddo wacce ko tashi bata iya yi saida wanda sakamakon ciwon kafa da ta ke fama da shi, tana zaune a tsakar gida cikin rumfa saman gadonta na karfe don koyaushe nan ne wajen zamanta saidai yaran gidan su zo nan tayata hira. Shigowarsu ce ta katse tunaninta, ta zubamusu ido, tana hada ido da Ummi ta zaro ido. “Boddona!” Sai kuma ta soma kuka tana mikamata hannu, a guje Ummi ta karasa ga kakarta don ta gane wacece daga sunan da ta ambata, suka rungume juna. Fuskar kowannensu cike da farinciki. Bayan an gaggaisa, ta ke tambayar Malam Balarabe sadda ya dawo, a kunyace ya bata amsa ya kara da neman gafara. Ta yi kamar bata ji ba don kuwa kokusa bata da rikeshi ba. Mariya dai an zama yan kallo sai rarraba idanu kamar shege a rabon gado. Ranar Ummi dai ra rasa inda zata sanya kanta don dadi, haka ta wuni cikin yan uwa, dangi sai zuwa akeyi rututu ganinta. Wasu sunfi danganta kamanni da yanayinta da Inno Zahra data rasu saidai ita tana da yawan barkwanci da dariya, wasu kuwa sun fi karkata ga Hasiya. Ranar fura da nono har saida ta ture, ga cima kala-kala da aka kawo musu. Mariya tana samun yaran abokan wasa shikenan kuma ta saki jiki har ta fice tare da su. Ranar Ummi ta mance dukkan wasu bakkan cikinta. Kwanan Malam Balarabe biyu suka juya tare da Dan uwansa da kuma Mariya wacce itama ya ke son kaita ganin dangin mahaifinta wadanda bata sani ba, ba kuma yaso nan gaba azo baya raye ta tambaya ba wanda ya sani. Ummi ta zama ‘yar lele, kullum cikin hira, idan ta jima wajen Inna Boddo, nan kakanta zai nemeta, nan ma ba jimawa sauran matan musamman uwa ga Inno da Binta, Danejo itama zata shiga nemanta, don tunda ta ga Ummi ta ji kamar Innonta ce ta dawo. Rayuwa kenan, bayan wuya sai dadi idan har mutum zai jure ya yi hakuri da dukkan lamura, Allahu Ya bamu ikon juriya da hakuri ba don isarmu ba, Amin. Ranar talata da misalin biyar na yamma, Ummi da wata yar uwarta Abu wacce itama jika ce a gidan suna tafe a hanyarsu ta zuwa gona kaiwa baban Abun abinci. Ummi na sanye da doguwar riga bulu mai adon fulawoyi bakake, ta tufke gashinta wanda tun tsifar da Dada ta yi mata bata yi kitso ba, fuskarta fayau, ta yafa mayafi akanta bata ko daura dankwali aciki ba, sai gashin ya yi tudu a tsakiya kadan, tana wasa da karar dake a hannunta. Suka tsinci muryar yayan Abu, Gidado yana kwalamusu kira ta bayansu. Tsayawa sukayi gami da juyawa, gaban Ummi ya yi wani mugun faduwa ganin wanda ke tare da Gidado. Murmushi tattausa ya ke jifanta da shi da kallon dama na fadamiki… Kasa kwakkwarar motsi Ummi ta yi, ya hade cikin farin yadi wanda ake ganin farar singiletinsa ya dora bak’ar hula hakanan takalminsa bak’i ne. Ya yi kyau kwarai duk ya chanjamata. Abu ke tambayar Gidado abinda ya faru. Daidai lokacin da suka karaso wajensu ya kasa dauke idanunsa daga Ummi. “Bak’o ki ka yi, tare da Mai sunan Baffa(Usman kanin Malam Balarabe) ya zo, bayan an gaisa kuma ya ce bazai jira ku dawo ba na yi mishi rakiya.” Duk wannan dogon bayanin da Gidado ke yi gareta ita gaba daya jikinta ya yi sanyi, Yaya Faruk? Ina ya baro aikinnasa? Yanzu babu kunya ya cewa su Daddy zai zo wajenta? Wayyo, wannan abu akwai kunya. Saida ta ji Abu ta gaisheshi da hausa ne ya amsamata da fulatanci har Abu na dariyar mamaki, itama ta dawo hankalinta, ta tuna ashe fa shima bafulatanin ne. Ta durkusa ta gaisheshi da girmamawa kamar yanda ta saba. Ya amsa, Gidado ya dubesu. “To, za ku juya ne ko mu wuce tare?” Faruk ya dubeshi har lokacin fuskarsa da walwala. “No ku karasa, ta nan za ku biyo ko?” “Eh.” Abu ta amsa. “Idan kun zo nan sai mu koma tare.” Suka amsa da to kafin su soma tafiya, shi kuwa baice uffan ba ya soma tafiya ya nufi wajen wani dutse ya sanya hankicif gami da zama. Garin babu rana sai ma hadari da ke haduwa. Ya dubeta, ta sunkuyar da kanta ta soma takowa don ta fahimci manufar kallon, gefe ta dan zauna. “Sai ki ka ga Faruk ko?” Ta murmusa. “Ai na yi mamaki, naga kuma yau ranar aiki.” Yana binta da kallo ya amsa. “Kar ki yi mamaki, kina da daraja da matsayi babba awajena wannan yasa ni daukar hutun sati kawai don na zo na ganki. Na horu da yawa fa Ummina, ji yanda na ajiye k’ashin wuya sadda ke ki ke mulmula k’iba har wani tumbi ki ka ajiye.” Ya karashe a shagwa6ance kamar yana gaban Hajiyarsa. Kunya da dariya ta kamata lokaci guda. Ta dan ja mayafinta da ya zamo har ana ganin kwantaccen gashin goshinta wanda ya kusan haduwa da gira. Tabbas tasan ta yi k’iba saidai bata hango tumbin da ya hanga ba. Ya dan daga gira. “Dagaske nake.” “Um, ya akayi ka zo nan?” “Garin masoyi yana nisa ne?” Bai saurari amsarta ba ya cigaba. “Zuciyata ce ta kasa samun nutsuwa, rashin ganin mahadinta kwana biyunnan ya jefata cikin tarin damuwar da ba za ki gane ba. Da naga ina neman mutuwa kawai na yanke shawarar biyo jirgi na taho Gombe. Ina isa kai tsaye na kira Babana, shi kansa ya yi mamakin jin wai ina Gombe, ya fadamin sunan unguwar ya ce idan na shiga tasi na hadashi da direban. Ya mishi kwatance, Alhamdulillah, don kuwa Ummina yan uwanmu sun min kyakkyawan tarba sannan sun ji daga bakin Baba cewa ni ke son aurenki. Jiya na iso Gombe, sai yau na taho nan. Kin gane dagaske Faruk bai iyawa babu Hasiya?” Ta rufe idanunta tana murmushi, har cikin ranta wani wutar kaunarsa ke kara ruruwa. Bata ji tashinsa ba sai bude ido da ta yi ta ganshi durkushe gabanta ya kuramata idanu yana murmushi, yayinda ya tokare hannun damansa saman dutsen. Sunkuyar da kanta ta yi. “Mu godewa Allah da Ya amsa mana addu’armu ya sadaki da farincikinki, na tayaki murna ainun Ummina. Abu daya ya rage mana.” Ta ji sarai abinda ya ce sai ta basar. “Nagode Yaya Faruk.” “Dayan fa? Ba za ki yi tambaya akansa ba?” Ta dan saci kallonsa yanda ya ke maganar cikin rad’a-rad’a. Ya kashemata ido daya, ta yi kasa da kanta da sauri. “Ko bakyaso ki ganki a gidana matsayin matata?” Da sauri ta karkata ta kauce daga saitinsa tana mai ambaton Innalillahi a fili don ji ta ke kamar ta dora hannu a kanta don kunya. Dariya sosai Faruk ya shiga yi adaidai lokacin da iska ta yi awon gaba da mayafinta, ta rike kannata tana mai da na sanin fitowa ba dankwali, tunda suke da Faruk bai ta6a ganin gashinta tsirara har haka ba, ya yi mata kallo daya yana mai kauda kansa da sauri alokaci guda ya na mai tsintar yanayinsa da chanjawa, ita kuwa da sauri ta janyo mayafin ta rufe gashinta sannan ta mike tsaye, muryarta ba rawa ta ce. “Yaya Faruk mu tafi kada ruwa ya riskemu anan kaga har yanzu ba su tahowa.” Ya sanya hannuwansa cikin aljihun wando, yana mai shakar daddad’ar iskar da ke kadawa, kafin ya juyo ya dubeta sannan ya yi kasa da kansa. “Muje.” Ya fada cikin yanayi na mutuwar jiki. Ta fahimci kamar yana niyyar barin hankicif dinnasa anan, shi kuwa yana sane ya yi hakan, ta dan saci kallonsa, ganin ba ya kallonta yasa ta dauka da sauri ta cusa a riga, ya yi kamar bai gani ba sai ma juyar da kan da ya yi yana murmushi ya soma tafiya. Suna cikin tafiya suka ji yo muryar su Abu da Gidado, hakan yasa suka tsaya suka jera tare suna tafiya da dan sauri-sauri ganin yanda ake iskar sosai, don ma a dazun ba wani nisa Ummi da Abu su ka yi ba ya taddosu. Suna dab da karasawa aka soma yayyafi, cikin taimakon Ubangiji ruwa bai tsuge ba sai bayan isarsu gidan. Suka yita godiya ga Allah. Faruk bisa jagorancin Gidado ya koma dakin Dattijo Manu, wanda a yan kwana biyunnan ne ya dan ji saukin jikinsa don yana fama da hawan jini. Bayan sunyi sallar Magriba, Faruk ya sanya (jacket) sakamakon sanyin da garin ya yi, sannan suka shiga hira da harshen fulatanci, Faruk ya daukeshi tamkar Modibbo, Dattijo Manu na watso mishi tambaya game da ko su fulanin ina ne yana amsawa dalla-dalla. Kafin shima ya labartamishi nasu, ya ji dadin hira sosai da Faruk din, shima Faruk din ya sake da shi ainun don bai ji nauyin sanarmishi yanda ya ke kaunar Ummi ba wanda hakan ba karamin dadi ya yi masa ba. Cikin tsokana ya ce. “Saidai fa banason kara yin nisa da amaryata.” Dariya Faruk ya yi. “Karka damu, akai-akai za ka dunga ganinta, idan ta kama ma ai sai mu daukeka mu maidaka Abuja.” “Kayya, barni inda nafi wayo, nan Buba ma ya yi da ni akan na koma can birni Gombe wajensa na k’i.” Duk suna maganar da fulatanci suna dariya. “Nima inaga mun kusa zuwa Adamawa, amma fa da Amaryata.” Cewar Faruk cikin wasa da dariya har ya bawa Dattijon dariya. Saida ruwa ya tsagaita sannan Inna Boddo ta umarci Ummi da kai musu abinci, ta yi tsuru da ido saidai ganin ba yanda ta iya ta ja Abu suka wuce tarr kowanne dauke da kwano bibbiyu don har kaza aka soyawa Faruk, gaba daya dattijan ke haduwa su ci abinci tare saidai ruwa yanzu ya hana hakan ita kuwa tunani ta ke yi Faruk dan gayu dan hutu da shi anya zai iya cin cimarsu? Haka dai suka karasa da sallama, bata kallesu ba, kai a kasa ta gaida Dattijo Manu, ya amsa yana fadin. “Amaryata ki yi zamanki anan kinji? Sai kin iya fillanci.” Murmushi kawai ta yi, duk yanda Faruk ya so su hada ido ta k’i, saida suka kawo musu komai har ruwan wanke hannu da na sha na randa mai sanyi sannan suka fita. Ummi kuwa kowa a gidan cewa ya ke ta yi sa’a ga shi mutumin kirki ga shi kuma bafulatani shima, murmushi kawai ta ke yi ba ta cewa komai. Tana kwance a dakin Inna Boddo, Innar na cikin sange(mosquito net) an lullu6eta da bargo mai kauri sosai saboda sanyi. Bayan ta tabbatar Innar ta yi nisa a bacci ta fiddo hankicif din ta rufa a fuskarta tana mai shak’ar kamshin idanunta a lumshe, murmushi saman fuskarta. Wayarta ta soma k’ara da sauri ta zarota daga k’asan filo ta danna kada Inna ta farka, Faruk dinne kuwa. Ta dafe kirji kadan, a hankali ta sauka daga gadon ta fito waje ta zauna. “Ummina.” “Um.” “Na yi mantuwa fa a wajen dazu.” Ta zaro ido gami da hadiye miyau na fargaba. “Mantuwar me?” Ya danne dariyarsa yana duban Dattijo wanda munsharinsa ya hanashi runtsawa kwata-kwata. “Hankicif dina, ko kin ganshi?” Idanunta ya yi kwal-kwal, to ta ce me? Ta ganshi yana wurinta? Me zata yi da shi da bata mayarmishi ba? “Kinyi shiru.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *