DAN ADAM CHAPTER 29

DAN ADAM CHAPTER 29

 Koda ta koma daki, kwance ta iske Abida saidai bata kai ga baccin ba. A kunyace da alamun rashin gaskiya. Abida bata ce mata uffan ba, itama ta cire mayafin jikinta sannan ta hau ta kwanta bayan ta yi alwala ta kashe musu fitila. Ta lullu6e jikinta da bargo tana tunano abinda ya faru yanzun. Runtse ido ta yi ta bude, ganin abin tamkar mafarki ta ke, ta dan saka hannu ta mintsili kugunta, nan take ta yamutse fuska irin na jin zafi. Sai kuma ta rufe kanta da bargo tana murmushi, shakka babu dagaske ne, amma kuma abin ya bata tsoro. Har Baffa da Abida suka yi kwana biyu bisa umarnin Gen. Ahmad don su niyyarsu washegari su juya. Ummi wasan 6oyo ta ke yi da Faruk, don daga ta ji Magriba ta yi zata shige daki suyita hira da Abida. Hakanan idan ya bugo waya bata dagawa. Washegari kuwa yana tafiya ofis, suma su Abida suka tattara suka wuce, har hawaye ta yi haka suka rabu zukatansu cike da kewa. Tare sukayi komai da Binta na abincin rana, har lokacin Ikram bata dawo ba. Acewar Binta, ba zata dauwama acan ba, koda ta yi an dai riga da anyi abinda bata so, Ummin ta zama matar yayanta. Hajiya Babba zaune a falonta tare da Ummi da har lokacin bata saki jikinta ba, waya Hajiyar ke yi da Hajiya Mama. A karshe ta dubi Ummi dake zaune a kasa tana mai mik’amata wayar. “Amsa ku gaisa da Sadiya.” Kunya ta cikata sanin kowacece Sadiyar, Hajiya Mama. Ta kar6a a kunya ta yi sallama. Daga can Hajiya Mama ta amsa mata murya a sake. Ummi ta gaisheta, ta amsa. “Sannu surukarmu, kinga yanda Allah ke ikonSa ko?” Kanta kawai ta dukar tana murmushi. “Um.” Ta fad’a a kunyace. “Allah Yasa alheri, Ya baku zaman lafiya, sai a dage a nemi ilimi banda wasa kinji ko?” Ta gyada kai.” “To Hajiya.” Daga haka ta mik’awa Hajiya Babba wayar, itama sallamar suka yi. Bayan sallar isha’i tana kwance saman gadonta, ta juyawa kofa baya, ba bacci ta ke yi ba saidai ta yi shiru tana tunane-tunane, ga ruwan sama da ake kwarawa kamar da bakin kwarya, sam ba ta ji sadda ya murda kofar ba sai jin mutum ta yi a bayanta ya rungumota. A firgice ta mike zaune za ta yi ihu ya yi saurin rufe mata bakin. “Shii…” Ta tsaya tana mai dubansa daga shi sai riga marar hannu sai dogon wando na Adidas, ta sauke ajiyar zuciya, ta ja baya, ya saketa, ta sauke kafafunta daga saman gadon shima ya yi yanda ta yi yana mai dubanta fuskarsa a daure. Sai wani jan riga ta ke yi don sanye ta ke da t-shirt mai karamin hannu sai zani da dankwali, gaba daya t-shirt din ta matseta don kuwa ba Ummin da ya sani a baya bace, wannan ta yi k’iba ta k’ara haske. Ya kauda kansa yana ta6e baki kadan, tana gaisheshi saidai bai amsa ba. Ya zarce da maganarsa. “Laifin me na yi ki ka k’i amsa wayata sannan bakya tunanin zuwa gaisheni kafin na fita ko kuma idan na dawo, kin manta yanzu duk wadannan hakkine a wuyanki?” Ganin ba alamar wasa a fuskarsa ta kara sunne kanta. “Ka yi hakuri don Allah.” Shikenan ta gama da shi, wuyarta ka ba shi hakuri, yana iya yafemaka. Ya dubeta yana murmushi. “Ya wuce.” Da dabara ta janyo hijabinta zata sanya caraf ya rike hannun. Ta dubeshi kamar za ta yi kuka shima ya narkar da nashi idanun cikin nata. “Wai Ummina yaushe ne za ki bar wannan halin? Har yanzu kunyar…” Sai kuma ya yi murmushi sadda ya je janye hijabin. “Kodayake, laifina ne.” Ta ja baya a tsorace tana mai turo baki kadan don ita gani ta ke yi ya takura rayuwarta. “Nidai don Allah ka fita kada Hajiya ta leko ta ganka.” Ya dan daga gira yana gyada kai. “Oh, gani na nawa kuma? Da nasan ita ki ke tsoro ai da ban shigo ba, yanzu tashi ina bukatar shan ruwan lipton, saidai nafison ki cire wannan ledar ta jikinsa ki zazzage garin ki zuba sugar idan ya dahu ki tacemin, ok? Idan kin kammala ki kawomin.” Ya mike ya yi gaba batare da jiran amsarta ba. Ranta a dan 6ace ba ta bishi da kallo ba don komai ba tasan wayo zaiyi mata dole ta shiga sashensa. Yanzu idan ya ce zaiyi mata abinda aka ce kada ta yarda sai an kaita gidansa fa? Ta kauda wannan tunanin ta mike ta chanja kaya zuwa doguwar rigar jallabiya ta sanya hijabi sannan ta fito. A falon ta tarar da Hajiya na shirin ratsawa sashen mijinta, ta dubeta. “Ya akayi Ummi?” A kunyace Ummi ta bata amsa. “Shayi ya ce na hadamishi.” Hajiya ta gyada kai ta yi shiru, kamar ta ce wani abu sai kuma ta chanja tunani da fadin. “To idan kinje ki dawo.” Daga haka ta shige abinta, Ummi ta gane hausar. Ta mike ta sauka. Kicin din har an kashe fitilu, sai walkiya da ke haskoshi ga kuma karar ruwan sama wanda ake makashi sosai. Ta kunna fitila a ranta tana mai godiya ga Allah da wannan yanayin na damuna mai dadi. Saida ta kammala kamar yanda ya ce sannan ta juye a flask ta sanya karamin kofin tangaran a filet dinsa sannan ta nufi saman. A bude ta tarar da shi don haka ta shiga da sallama, fitilun a kashe suke sai ko hasken talabijin da ke aiki, yana zaune a falon da laptop saman cinyarsa yana dannawa. Shigowarta ne yasa shi maida dubansa gareta. Ya sauke kafafunsa saman tebur ta ajiye kafin ta zubamishi. “Gashinan.” “Thank you.” Ya fada cikin kankan da murya, ta juya ga kallon barandarsa wacce ke a bud’e ga kuma labulen dakin dake kadawa har ruwa na fallatsowa, ta ga alamun baya jin sanyin. “Saida safe.” Zata mike ya fisgota. Cikin kankan da murya ya ce. “Na sallameki ne?” Ummi wacce yanayinta ya sauya ta kasa magana sai girgiza kai. Ya gyara mata zama sannan ya sa hannu ya soma kokarin ciremata hijabin. “Ke bakya jin zafin gari ko? Cire ki shak’i iska mai rahma.” Bata da kata6us har ya cire ya yi saura daga ita sai hular kanta da doguwar rigar. Ta hade hannuwanta wuri guda gami da dan muskutawa ta ja baya da shi. Idanunsa akan laptop saida ya murmusa, wai shi yarinyarnan ke kakkaucewa? Ya share batunta ya soma shan ruwan shayinsa yana danne-dannensa cikin email account dinsa. Ita kam Hajiya kawai ta ke tsoro, yanzu don Allah idan ta ji ta shiru me za ta ce? Faruk bai k’ara duban inda ta ke ba sai bayan ya kammala sannan ya kashe laptop dinsa ya dubeta. Duk ta 6ata fuska kiris ya rage ta soma kuka. Yasa hannu ya janyota jikinsa. “Zo ki fadamin me ya 6ata ranki?” Babu amsa, ya shafi gefen fuskarta har zuwa wuyanta nan ma ba ta ce komai ba, ganin yana kokarin yin son ransa ne yasa ta saurin rike hannunsa gami da ja baya. “Don Allah zan tafi kada Hajiya…” “Tell me, Hajiya ki ke aure ko Faruk wai? Tsoron me ki ke yi mata haka alhalin tasan kina wajen mijinki? A baya ina miki haka ne?” Ya na magana a hankali saidai muryar na nuni da 6acin rai. Ta girgiza kai sai kuma ga hawaye, runtse ido ya yi gami da kwantar da kansa jikin kujera, ba kuma yaso ta zargi ko abinda ya ke so daga gareta kenan, baya son 6acin ran Ummi. Saidai shi kunyar ce baya so, yanzun kuma ya lura harda tsoro ma. Tunda ya ke a rayuwarsa bai ta6a ko rungume wata diya mace ba balle ya aikata wani abin. Ya ja guntun tsaki. “Tashi ki tafi. Saida safe.” Ya yi maganar a sanyaye. Ta dubeshi sai ta ji soyayyarsa na karuwa ga kuma tausayi, tasan bata kyauta ba. Murya na rawa ta ce. “Don Allah ka yi hakuri Yaya Faruk.” Ya dubeta yana murmushin karfin hali da kokarin hadiye abinda ke taso mishi. “Karki damu ba fushi na yi ba, muje na raka ki.” Suka mike yana rike da hannunta, ya janyo hijabinta ya sanya mata, ta zura takalminta, suna isa kofa baisan sadda ya fisgota ba har ta firgita, ya hada bakunansu wuri guda, saida ya gaji don kansa ya saketa ya ja baya kadan yana dubanta. “Goodnight.” Itama da sauri ta fita, ya rufe kofar. Ta juya ta dubi kofar sannan da sauri-sauri ta fice tana numfarfashi. Wannan daren daga ita har shi sun jima kafin bacci ya kwashesu… *** *** *** Abu kamar wasa, Ummi ta shiga yi mishi 6oyo, duk wata hanya da zasu ke6ance ta tosheta, shi kuma idan ya ganta tare da Hajiya ba ya iya cewa uffan don mikewa ta ke yi ta bar falon. Zuwa yanzu ta dan soma sabo da Hajiya don Hajiya Babba ta sakarmata sosai ta yi ta janta da hirar Gombe, itama har ta sake ta yi ta bata labari. Bai kara sanyata a ido sosai ba sai ranar Asabar, shima ta fito cikin shirin Islamiyya ne. Gabanta ya fadi, ta durkusa ta gaida Hajiya sannan ta gaisheshi. Ya tamke fuska kwarai har Hajiya saida ta yi mamaki. “Ba kai ake gaisarwa ba?” Cewar Hajiya. Ya yamutse fuska kadan. “Lafiya.” Ya mike. “Hajiya bari na je na dawo.” “Aa, to ka tafi da ita mana kawai. Tunda duk hanya ne.” Ya runtse ido kadan sannan ya yi gaba, Hajiya ta dubeta. “Tashi ku je.” Ummi wacce duk jikinta ya yi sanyi, ina laifin mai sonka? Ta ji haushin kanta na 6atawa Faruk rai, mutumin da ya so ta tun kafin ta zama ‘yar gayu haka, tun tana matsayin ‘yar aiki. Sam bata kyauta ba, Faruk bai cancanta ta dunga 6atamishi rai haka ba. Ta iske tuni ya fiddo motar yana jiranta, ta karasa kanta a k’asa, ta bude gaban mota ta shiga, sanyi da kamshi ya doketa, garin ya yi sanyi hakanan babu rana kamar zaayi wani ruwan. Ta rufe kofar gami da satar kallonsa saidai ko inda take ba ya kallo, fuskarsa babu digon walwala, gaba daya haushin kanta ya kamata, suka soma tafiya nan ma babu alamun zai shiga harkarta, wannan ne dalilin da yasa ta daure ta soma magana dakyar. “Yaya Faruk.” Bai amsa ba hakanan bai kalleta ba. Ta sunkuyar da kanta idanunta suka ciko da ruwan hawaye, ta dubeshi cikin rawar murya. “Yaya Faruk don Allah ka yafemin.” Ya lumshe ido ya budesu yana mai duban gefen da zai yanka kwana, can cikin zuciyarsa babu dadi, ji ya ke tamkar ya janyota ya rarrasheta, ko kusa ya tsani kukanta. Ita kuwa ganin ya yi shiru yasa ta kauda kanta ta maida dubanta ga gefenta tana sharar hawaye. Shiru ya biyo baya har dai suka isa. Daidai Islamiyyar ya tsaya, dalibai har sun shiga wasu kusa na tsaitsaye a k’ofa, gaba daya suka zubawa motar ido don ganin wanda zai fito. Ya cire (Lock), bata dubeshi ba ta bude kofar ta fita bayan ta share fuskarta. Haka ta shiga ciki, mintuna uku da shigarta suna tsaye wata Malama na tambayarta ko ita sabuwar daliba ce, ya shigo. Gaisawa ya yi da wani Malami sannan ya yi ciki zuwa ofishin headmaster bayan ya yi mata umarnin ta biyoshi. Nan ya bada hakurin rashin zuwanta na tsawon lokaci, ya nuna babu komai. Aka sallameta ta fito, da isarta kofar ajinsu suka hadu da Husna da wasu. “Lah, ashe dagaske ki ke Fati, Hasiya ce.” Cewar Husna kenan, Ummi cikin rashin fahimta ta dubesu, saidai kafin ta ce wani abu, ta ji suna duban bayanta wata na fadin. “Gashinan wallahi, wayyo Allah, very handsome, please Hasiya ki hadani da shi, wallahi yayanki ya min, kalar mijin da nake fata kenan.” Cewar wata Shukra Aminu. Wani mugun kishi ya turnuk’e Ummi, ta juya ta dubi Faruk sa’ilin da ya ke kokarin sanya kansa a waje ya fice. Sanye ya ke da bak’ar t-shirt bodyhug wanda ya taimaka wajen fiddo da kyakkawar halittar da Allah Ya yiwa jikinsa na kirar karfi, sai farin wandon jeans da ya sanya, sumarsa kwance luf, bak’ak’irin kamar mai sanya (hair dye). Ta juyo ba ta ce uffan ba ta nufi ciki, tana jinsu suna kod’a mijinta saidai bata da bakin magana. Gaba daya suka biyota ajin. Husna ke tambayarta game da Gombe, su kuwa tambaya suke akan Faruk, duk sun isheta, Allah Ya taimaketa Malam ya shigo ajin, wannan yasa duk aka nutsu. Ranta a matukar 6ace ya ke, har aka fito sallah basu bar bibiyatar da son jin ko wanene ba, tana tsaye bakin famfo tana daure dankwalinta, jiran Husna ta ke yi ta idar su bar wajen, idanunta ya kai ga Ikram suna nufo famfon ita da tawagarta. Ba shiri ta ja hijabinta ta rufe fuskar gami da basu baya, saidai duk da hakan bata tsira ba Ikram ta ganta, saidai bata ko nuna tasan da itan ba bisa gargadin Haidar wanda ya gargadeta sosai akanta. Dogon tsaki ta ja kawai wanda Ummin ta ji, daidai lokacin ne kuma Husna ta kammala ta dubeta. “Mu tafi.” Suka bar wajen zuwa masallaci. Zuciyar Ummi ko kadan babu dadi har aka tashesu, direba ya dauketa. A farfajiyar gidan suan fakawa ta fito, idanunta ya kai ga baranda Gogannata. Yana makale da earpiece a kunne, hannunsa na hagu lemun gwangwani ne da ya ke kur6a, sai sketct-board a gabansa yana zane. Ta dubeshi sosai, ganin zai kallota ne yasa ta saurin k’asa da kanta gami da soma tafiya zuwa ciki, ta goge kwallar da ta tahomata. Wannan cutarwa ne, ba zata jure wannan fad’an nasu ba. Ba haka ya sabarmata ba a mu’amalarsu. Bayan sun gaisa da Hajiya, ta shiga ciki ta watsa ruwa ta sauya kaya zuwa riga da siket na Atamfa mai fari da (orange), bata daure dankwalin ba saidai kawai rufashi da ta yi. Fita ta yi zuwa kicin wajen Binta. Anan ta zauna, Binta ta yi akan ta ci abinci saidai ta ce ita sam bata jin yunwa duk kuwa da irin yanda ta ke jin yunwa na addabarta saidai damuwarta na rashin ganin fuskar Faruk yafi komai damunta. Tana daga kujera yar tsugunno suna hira da Binta. Anan ta ke bata labarin yanda suka yi da Ikram. Dariya sosai Binta ta yi. “Duk yanda akayi ba banza ta kyaleki bata tofa ba.” Murmushi kawai Ummi ta yi wanda bai kai zuci ba, da ta ji hirar babu abinda ta ragemata sai ma k’ara hargitsata da ta yi don kuwa Binta ta sanarmata da zuwan matasan gidan da iyalinsu gobe, anan zasu wuni, duk sai ta ji hankalinta ya k’ara tashi, hakan yasa ta mikewa. “Bari dai na dan zagaya.” Kai tsaye (Garden) ta nufa, zama ta yi saman lilo ta kwantar da kanta jikin igiyar, a sannu ta ke lulata tana tunani, rayuwarta na tafiya daki-daki, daga matsayin yar aiki zuwa ta surukar gida, har ta gangaro ga irin kyautatawar da Faruk ya yi mata zuwa ga yanzu da ta 6ata mishi rai. Bata ji motsin zuwansa ba, saidai ji ta yi yana share mata hawaye. “Yaya Faruk!” Ta fada da sauri tana dubansa, sai kuma kunya ta kamata ganin dagaske ba mafarki ta ke ba shi dinne zaune durkushe gabanta yana dubanta. “I’m sorry. Ki yi hakuri kinji?” Ya fada cike da damuwa a fuskarsa, ta girgiza kai. “Ni zan baka hakuri, don Allah ka gafartamin kada Allah Ya yi fushi da ni.” Ta burgeshi har baisan sadda ya dora gwuiwoyin hannunsa ba akan kafafunta yana mai dubanta. “Sai kin chanjamin suna.” Ta rufe fuska tana dariya. Ya riko hannunta gami da mik’ar da ita. “Oya, muje mu ci abinci.” Ta mike ba musu suka shiga ciki yana rike da hannunta. Kusan tare suka ci abincin a falon Hajiya, Hajiyar na sama ta yi bak’uwa mai zuwa sarar kaya. Suna ci daga zai bata a baki sai ta yi saurin kaucewa, har ya gaji ya bari, abin kan ta6a zuciyarsa, shi sam ba ya kaunar rayuwa haka, Yana yawan hangowa kansa rayuwa ta wayewa, baya kaunar kunyar Ummi ta cucesu a zamantakewa, idan har hakane, zata tauye musu jin dadi….Ya ji abincin ya fita ransa dole ya ja baya gami da zuba ruwa ya sha. Ta dubeshi, tana son tambaya ko ya k’oshi saidai ta kasa, ita batasan meyasa duk kunyarsa yanzu ta ke ji ba, ta fahimci kuma ba haka ya ke so ba. Yana kallonta tana faman juya cokali, kawai ta mike ta dauke zuwa kicin. Koda ta fito bata ganshi a falon ba, itama sama ta nufa don jin an soma kiraye-kirayen sallah. Saida ta idar sannan ta ciro Al-kur’ani ta dan karanta inda aka biyamusu sannan ta rufe. Wayarta ta dauko, tana son kiran Antinta Amina don neman shawara saidai babu kudi cikinsa, tunawa ta yi da kudin da babanta ya bata cikin wanda ta ba shi da ta taho da shi, ya ragomata koda za ta siya wani abun, hamdala ta yi kafin ta mike ta nufi jakarta ta rataye, dubu daya ta ciro sannan ta fita, daman da hijab a jikinta. Allah Ya taimaketa Hajiya bata falon hakan yasa ta zarcewa kasa. Kai tsaye farfajiyar gidan ta nufa, saida gabanta ya fadi ganin Faruk ya shigo, da alamu dai daga masallaci ya ke, shi dinma ita ya zubawa ido da mamaki, ta ja ta tsaya har ya karaso. “Ina za ki?” Ta nunamishi kudin hannunta. “Kati nake so shine zan bayar a siyomin.” Jin haka ya tamke fuska. “Meyasa ba ki sanarmin ba? Hakkina ne fa nasan dukkam abinda ki ke so, ya kamata ki chanja Ummina, banason wannan kunyar taki a yanzu, bani da bukatarta, please ki saki jikinki da ni. I’m now your husband.” Ya karashe da murya mai kamar rada sannan ya gifta ta ya yi gaba, gaba daya jikinta ya yi sanyi dole ta bi bayanshi. Sashensa ya nufa, itama ta yi nata dakin. Kwanciya ta yi saman gado ta yi shiru kawai, haka har aka soma kiraye-kirayen sallar Isha’i, ta gabatar, jimawa kadan ta fito falon bayan ta cire hijabin ta linke. Hajiya ta tarar zaune tana waya da Hajiya Mama inda suke tattaunawa akan bikin dangatan nata har ta ke sanarmata da batun zuwan su Babban Yaya gobe don tattaunawa. Ummi daman bata zauna falon ba, kai tsaye k’asa ta sauka don kuwa saida ta yi da na sanin fitowa don tuni ta fahimci maganar me sukeyi. A kasa ta samu su Binta sina kallon wani series da akeyi da harshen larabci, zama ta yi saman kujera kafin ta dubesu sannan ta maida dubanta ga talabijin din kawai kuma sai ta kwashe da dariya sosai, dariya wacce rabonta da irinta tun dawowarta daga Gombe da suna hira da Binta a kicin. Suka dubeta. “Lafiya Ranki ya dade?” Ta dan harareta da wasa don ita ta nuna sam batason sunan saidai kamar da gayya ma Bintar ke yi. Dariya itama Bintar ta yi. “Ku ku ka sanyani dariya, kun nutsu kun zubawa talabijin idanu kai kace kunsan abinda su ke cewa.” Suka dara, Samira wacce ta zo bayan tafiyar Ummi Gombe ta dubeta. “Ai soyayyar kadai idan ki ka kalla wallahi ranki fari zaiyi, kinga nan.” Duk suka maida hankalinsu kan talabijin, abinci zata ba shi da cokali yayinda ya ke jingine da filo a gadon asibiti, ya tarr ya hanata ba shi da cokalin, dole tasa hannu har wani take aka sakomusu, har idan ya 6ata bakin ta gogeshi mishi, karshe ma ya hada da yatsunta ya tsotsa. Ummi ta saci kallon su Binta suka kwashe da dariya, sai kuma suka nutsu. Shiru ta yi har da taguminta tana kallo da murmushi. Basu ji zuwansa ba, hakanan bata ko lura da sadda ya yiwa su Binta alama da su bar wajen ba, balle kuma zamansa gefenta. Hankalinta ya lula wata duniya, tunaninta bai wuce inama itama za ta iya hakan gareshi ba, sumbatar da ta ji a wuyanta ne yasa ta juyawa a firgice tana salati a fili, murmushi ya ke jifanta da shi, idanunsa sun kankance yana dubanta. Gabanta ya hau bugu, ta waiga babu su Binta ko dalilinsu, ta dubi talabijin, tuni ashe an wuce wajen sai ma likita da ta ga ya shigo dakinnasu(a film din), ta dan ja baya gami da shafa goshinta. Duk ta rasa me zata yi don kunya ta hau wasa da zoben gwal din dake hannunta wanda ya bata. Ya matso daf da ita. “Kina so kina kaiwa kasuwa kenan?” Ya watsamata tambayar cikin narkakkiyar muryarsa wacce soyayya ta cika. Ta hau girgiza kai batare da ta ce komai ba. Bai saurareta ba ya ja hannunta sadda ya mike tsaye. “Oya, taso ki ga wani abu.” Ta mike ta zare hannunta da dabara kafin ta bi bayanshi a sanyaye. Ganin hanyar da ya nufa na samansa yasa ta tsaya cak duk a firgice. Ya juyo ya dubeta idanunta ya yi rau-rau, tsoronta lokacin cin abinci ne kada Hajiya ta nemesu, kada ma Hajiyar ta dauka ita ke zuwa wajensa tunda ta ga sadda ta sauko. Hannunta ya kama ya soma taka matattakalar, tana zamewa kadan-kadan saidai bai saketa ba har suka isa. Tsoro ta ji ganin sun wuce falo har ya sada ta da k’uryarsa. Dakin yana nan yanda ta sanshi, bai jira cewarta ba ya sanyata jikinsa. Tun tana a’a, da kuma rokonsa akan ya kyaleta, kamar baisan ta na yi ba. Ganin yana kokarin zuge mata zif yasa ta yin baya da sauri ta fito falo, tsaki ya ja, abin kuma ya soma ba shi haushi, wannan sam ba zai lamunta ba, tana abu kamar wacce batasan menene aure ba, ya dauki dankwalinta ya biyota da shi, tana tsaye hanyar matattakala, mik’amata ya yi fuskarsa a murtuke. Yana dubanta da jajayen idanunsa wanda har da 6acin rai cikinsu ga kuma fitina. Wannan abun ya zama sakarci kuma, ina laifin ma da ya iya jurewa har aka daura auren? Da ace tasan yanda ya ke mutuwar so da sha’awarta da bata soma tunanin yi mishi gardama a dan abinda zai yi na rage zafi ba, sam ba shi da nufin wani abu bayan kalilan din da ya ke kwadayi a yanzun. Anan zasu samu matsala. “Kina iya tafiya.” Ta yi narai-narai da fuska. “Ki tafi nace!” Ya fada da dan daga murya, ta soma hawaye sai kuma ta juya da sauri-sauri ta bar wajen. Ta ci saa Hajiya ta yi sashen Daddy, ta wuce dakinta ta kwanta ta soma kuka. Saida ta yi mai isarta sannan ta share fuskarta, wayarta ta ji ta yi karar shigowar text, ta janyota, shi dinne ya turomata kudi daga acc na banki. Ya saba yi mata hakan shiyasa tun bata gane ba ta fahimta, bata yi wata-wata ba ta dannawa Amina kira, saidai bata sameta ba, shaf ta mance cewar sun je Nijar. Ta ciji le66anta, shigowar Hajiya Babba ne ya sa ta gyara fuskarta da sauri, ta amsa sallamarta. Hajiya ta lura akwai wani abun, ta karasa rike da wata roba a hannunta ta zauna gefen gadon. “Lafiyarki kuwa?” Ummi ta yi murmushin yak’e. “Bakomai Hajiya.” “Ya za ki cemin bakomai alhalin ga idanunki a kode?” “Kaina ke ciwo.” Ta samu bakinta da shararo karya. Hajiya ta numfasa. “Allah Ya sauwake.” “Amin.” “Rike wannan.” Ta mikamata robar, ta dubeta. “Da safe da dare ki dinga sha da madara kinji? Akwai wasu ma da na sanya akawomin, Ummi ina miki kallon diyata, abinda zan yiwa Ikram zan miki shi, wannan kunyar tawa nakeso ki daina jinta kinji ko? Ki daukeni kamar uwa agareki.” Kanta a kasa ta gyada kai. “In sha Allahu Hajiya.” Murmushi Hajiya ta yi sannan ta dafe kanta. “Allah Ya yi miki albarka, ki tashi ki je ki ci abinci.” Da murmushin itama ta amsa da toh. Ta bi bayan Hajiya da kallo, ji dai yanda mutanen nan suka dauketa da girma, ta tuna yanda ta ke 6atawa dansu a rai akan hakkinsa, dagaske batasan rayuwar aure sosai ba, duk wani kissa ko kisisina bata ta6a hirarsa da wani ko wata ba, to waye mai koyamata ma? Duka-duka idan a makaranta ake koya, yaushe ta soma zuwa makarantar? Ko wata biyar cikakkiya bata yi ba a makarantar Kano, sannan ita din ba karatun litattafai ba, hakan kuma bai hadasu da Amina, ta dai soma jin kadan daga bakin su Abida, kamar biyayya da bin umarni da sauransu. Dole ta zage damtse ta koya, kamar dai yanzu da ta ga kulawar matar nan ga mijinta duk da cewar a fim ne, amma kwarai sun burgeta. ‘Mijinki dan boko ne wayayye, sai kin zage damtse kin kula da shi.’ Cewar wani sashe na zuciyarta. A ranar basu kara haduwa ba, ta kira wayarsa yafi sau biyu bai daga ba, hakanan ta hakura, ranar bata iya baccin kirki ba. Washegari….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *