DAN ADAM CHAPTER 31

DAN ADAM
CHAPTER 31

Zirga-zirga ta ke yi a dakinta ko kayan makarantar ta kasa fiddawa, can dai ta k’arasa fisge dankwalinta ta ajiye gefe, har da ribbon din da ta ke tufke yalwataccen gashinta na fulanin usul, ta zaune gefen gado.
‘Kai anya kina da hankali Ikram? Me za ki yi da DAN KAUYE?’
Shine tambayar da wani sashe na zuciyarta ta jefomata.
Ta runtse ido sannan ta ja tsaki gami da mikewa tsaye.
“Craziness!” Ta fada a fili sannan ta rage kayan jikinta ta fada wanka.
Bayan fitowarta ne daga ita sai tawul ta tarar da kira har sau uku a wayarta, ta yi saurin dubawa, biyu daga wani saurayinta ne Khalid wanda kawai ta ji ba ta yi murna da kirannasa ba, ba kamar a baya da ya ke dan burgeta ba, ta shareshi ta bi bayan kiran ‘yar uwarta Ihsan wacce itace ta kira sau daya.
“Ke ina ki ka shige ne ina nemanki?”
Cewar Ihsan. Ta dan dara,
“Yi hakuri baiwar Allah, wanka na shiga fa. Ya akayi, ya su Mami?”
“Mami ta fita siyayyar tsaraba na mutan Adamawa, ke ni bugowa na yi na ji ko da waccan munafukar za’a je?”
Murmushi Ikram ta yi.
“Babu inda za ta je, gobe ma zata koma kauyensu. Ina Man dinki?”
Ta ja guntun tsaki.
“Yana can inda ya ke, na ji yana batun shima ba za’a soma bikin Yayannaki yana nan ba don zasu je dangin Abbansa.”
Dariya Ikram ta yi karo na biyu.
“Me ye na tsakin wai? Kefa ki ka cemin kin soma sonshi.”
“Bazaki gane ba, ya iya tsara kalamai wallahi, matsalar daya yana son sanyomin batun zai min kaza da kaza bayan aure. Haka fa zuwan da ya yi satin da ya wuce, wallahi har rungumeni yaso yi na kauce. Amma hakan bai hana ni sonsa ba, saidai banason hakan ne kawai.”
Baki Ikram ta ta6e,
“Sai hakuri da neman tsari daga sharrin shaidan, mai yiwuwa saboda shi kadai ya tashi gaban iyayensa shiyasa, kinga kuma yanda suke ji da shi.”
Tsakin dai Ihsan ta k’ara yi.
“Kawai kuma don shi daya gaban iyayensa sai ya zama haka?”
“Au ai shikenan toh, naga wai ko sangartashin da akayi ne ya janyo hakan. Kodayake bar batun wannan, za ki yi ankon Yaya Faruk? An fiddo.” Cewar Ikram.
“Allah Ya sauwake!” Cewar Ihsan cikin daga murya. 
Ikram ta ja tsaki sadda ta isa ga sif din kayanta da zummar fiddo na sanyawa. 
“Kefa wani zubin banza ce, rashin yinki bakisan kamar kin nunawa mutane har yanzu kina sonshi ne ba, ai wallahi gwara ki yi ki cekare abinki, ga Abubakar dinki a gefenki. Ke kanki kinsan hakan ma abin alfaharinki ne tunda gayen karshe ne shima a haduwa.”
  Ihsan ta yi shiru sai kuma ta amsa.
“Barni tukun, sai na yi tunani. Bari na barki kada na cinye miki dan katin.”
Daga haka suka ajiye wayar.2
  Ummi kuwa tun a daren ta karasa shirin kayanta, sun yi waya da mutan Gombe ya fi sau uku a ranar duk su dinma d’okin zuwanta suke yi. Yau ko ta kan abincin dare bata bi ba don ta dage wajen shirye-shiryenta, daga ta rufa akwati sai ta tuna da wani abin ta bude ta sanya, kamar yanzu da ta ke kokarin sanya wasu kayanta da zata bayar, tana cikin jerasu ciki ne, Faruk ya yi sallama ya shigo.  Ta amsa tana mai duban kofar, fuskarsa cike da damuwa, kananun kayan da suka zame mishi jiki yau dinma su ya sanya. Cikin dauriya ta sakar mishi murmushi don kuwa ta fahimci sam tafiyar ce baya so saidai don babu yanda ya iya ne. Kafin ta yi wani yunkuri ya karaso ya kwantar da kai a kafadarta gami da rikota jikinsa ta gefe, ta lumshe ido batare da ta yi yunkurin hanashi ba don tuni ta daina wannan sai idan ta ga abin zai fi karfinta tukunna. 
   “Tafiya za ki yi ki bari mijinki?”
Ta sunkuyar da kanta tana duban hannuwansa dake cike da gargasa. Har lokacin murmushi ta ke.
  “Kaima ai tafiyar za ka yi.”
Ya dago gami da sanya bakinsa saitin kunnenta. 
  “Ba zan samu rakiyarki ba kuma ko?”
  Ya fada a shagwa6ance, numfashinta sai safa da marwa ya ke yi, ta kasa cewa uffan kasancewar ya cigaba da sarrafata son ransa, haka har tsayuwa ta nemi gagararsu. 
    Can kuma ya dago kai yana dubanta da idanunsa da suka yi k’ank’an. 
  “Na yi? Kin amince?”
Ta zaro ido tana dubansa. Abin ya ba shi dariya, ya ja kumatunta.
   “Matsoraciya, kodayake na ga kin rage tsoron, oya tell me, ya akayi ya ragu?”
  Ya karashe yana mai zama gefen gado ita kuwa na saman kafafunsa. Shiru ta yi kawai tana murmushi, ya ja karan hancinta har saida ta yi ‘yar k’ara. 
   “Wani 6angaren kunyarki na burgeni, yana k’aramin sonki sosai, ina son mace mai kunya, shine babban ado ga diya mace, yanmatan yanzu basusan wannan ba, za ki yi mamaki idan ki ka ga yanda mata ke tallata kansu ga maza, za ki yi mamaki idan ki ka hau yanar gizo yanda mata ke aika hotunansu babu ko rufin kallabi da sunan neman mijin aure alhalin basusan cewar sam mazan da suka san abinda sukeyi bazasu kallesu da daraja ba, ke har fa wajen biki kawo tallar kawunansu suke yi ga maza har kuwa inda suke, za kuma ki yi mamakin ganin mahaukatan da ke tallatawa mijinki surarsu.”
Ta hade fuska kadan. Ya kara matsarta a jikinsa yana dan murmushi.
“Saidai sun yi kadan, tsarin Allah muke nema koyaushe daga sharrinsu, in sha Allah zai karemu. Kinsan a inda na tsani kunyarki?”
  Shiru ta yi ganin ya maimaita yasa ta girgiza kai. Saitin kunnenta ya yi mata rad’a. 
  Ai batasan sadda ta runtse ido gami da kokarin zamewa ba, saidai ba rikom ragon namiji ta samu ba. Dariya kawai ya yi mata. 
  Ya fi awa daya a dakin, daga an soma hirar arziki zai hau lalubenta, sannan a cigaba har dai a karshe ya fita sakamakon Daddy da ya yi kiransa ta waya yana nemansa, wannan ya sanyashi tafiyar dole.
   Kwance ta ke tana faman juyi, can kuma idan ta gaji ta ja tsaki, wai meyasa haka ne? Ina ita kamarta ina kuma wani dan kauye? Meyasa ta kasa daina ganin hotonsa a kwayar idanunta, ta mike zaune gami da jingina da katakon gadon, batasan sadda hawaye ya zubomata ba, ba  don komai ba sai don takaicin wannan lamari, abin kunya ne babba agareta, ta ja wawan tsaki cike da jin haushin kanta, wannan kuwa abu ne da bazata ta6a bari ya yiwu ba, wai ta ce KO A MAFARKI….! Ta yi adduoi ta shafa sannan ta kwanta, har dai bacci ya yi awon gaba da ita.
   Washegari tun Asuba da Ummi ta farka bata koma ba, karfe bakwai zasu wuce, kai tsaye wanka ta fad’a ta sanya leshinta ruwan hoda marar nauyi.
  Karfe bakwai kuwa aka fidda akwatinta, bayan sun kammala karyawa, Faruk har dakinta ya zo kafin ya wuce ofis suka yi sallama, haka ta wuce cikin kewarsu da kuma d’okin zuwa ga mahaifinta da kakanninta…!!!
   Sai wuraren karfe daya suka isa Gombe, kai tsaye Tudun Wada suka nufa, da yaran gidan ta soma tozali a kofar gidan, da gudu suka shiga ciki domin sanarwa jama’ar gidan, dariya kawai ta yi sannan ta ja jakarta ta hannu ta yi ciki, a zaure suka yi kici6us da Anti Halima wacce ta taho ganin ko dagaske suke, ai kuwa ta rungumeta suna murna gami da lale marhabin da Amarya. Suka karasa ciki, ganin Dada tsaye tana rarraba idanu na son ganin ta inda zata 6ullo yasa ta k’arasawa a guje gami da rungumeta, Dada ta dan tureta cike da farinciki. Kafadarta ta dafa.
“Use Hasiya, kun sha hanya.”
Dariya ta yi. Haka suka yi ta nan da nan da ita kamar wannan ne ganinsu na farko da ita. 
   Saida ta gabatar da sallah sannan ta isa dakin Malam, yana kishingide yana gyangyadi saman darduma, sallamarta ce ta sanyashi wartsakewa yana mai amsawa fuska a sake. Bayan sun gaisa ne ya ke tambayar mutan Abuja. Bata jima sosai ba ta koma ciki. Sai yamma iyayensu maza suka dawo daga kasuwa, alokacin har direban da ya kawo Ummi ya juya bayan ya gabatar da sallah ya ci abinci. Malam Balarabe ya yi farinciki da ganin diyartasa. 
Sai bayan Magriba suka samu ke6ewa da Malam Balarabe, anan ta ke jin labarin zuwansa Ringim bayan tafiyarta, inda ya sanya gidansa a kasuwa, ya hada kan kudadensa ya sallami Haruna yaronsa mai tayashi aikin balangu a kasuwa sannan ya taho da zummar idan an siyar Malam Yahuza zai aikomishi da kudaden. Hakan ya yi mata dadi, shikenan sun rabu da Ringim kenan. Ya shiga bata labarin kiran da ya samu ta waya daga Daddy cewar kada ya yi komai na kayan daki shi zai yi don shima diyarsa ce, ya sanarmata koda ya ji hakan, ya ji abin banbarakwai, ya so tambayarta ta waya saidai yasan ba lallai ta samu labarin, koda ya sanarwa yan uwansa, su kansu sunyi mamaki, Malam da kansa ya sanya suka kira Daddy. Bayan an gaisa ya ce. 
   “To kai Alhaji ayi haka? Kwa daukarwa kanku nauyi har haka?”
Dariya Daddy ya yi ya nuna zai iya yiwa Ummin haka koda ace ba dansa za ta aura ba, acewarsa itama diyarsa ce.” Jin haka har Malam saida ya yi kukan farinciki, ya yi mishi godiya da binsa da kyawawan addu’o’i, Daddy ya nuna bakomai, tunda har suka bawa dansa aurenta sun mishi komai a rayuwa. 
  Ummi jin dukkan lamarin ta ke yi wani iri, jikinta ya yi sanyi, ko kusa bata da masaniya kan abinda ake ciki a Abuja. 
  “Kada ki bani kunya Hasiya, ki yi kokarin bin mijinki tsakani da Allah, tabbas Umar yaro ne nutsastse, ki godewa Allah don kuwa kin yi babban sa’a, yana sonki kuma iyayensa suma suna sonki, ki zauna da su da zuciya daya, wanda zai yi maka haka a rayuwa lallai bai kamata ka yar da shi ba.”
Har da hawayensa alokacin da ya ke fadin haka gareta, ita kanta saida ta share ruwan hawayen, acan kasan ranta kuwa, adduo’i ta ke ta jerowa ga Daddy da iyalinsa. 
    Kwanan Ummi biyu a Gombe, su Hajiya sun wuce Adamawa gaba dayansu har Modibbo. Saidai banda su Ihsan da sauran yaran masu zuwa makaranta da kuma surukansu. 
   Ita kuwa sosai su Abida suka shiga gyarata, duka-duka bikin a wannan lokacin bai fi saura kwanaki goma sha biyar ba, a bakin Dada ta ke jin cewa har mutanen Adamawa suma zasu zo. Dattijuwa Binta, tsohuwa mai ran karfe kenan Yaya ga Dattijo Manu(kakan Ummi) da zuri’arta wadanda rabonsu da Gomben tun rasuwar Inno.
    Gaba daya sai ta k’ara ji ta d’okantu da son ganinsu. 
    Duka-duka su Hajiya kwanansu biyar a Adamawa suka dawo har da wasu cikin yan uwansu wadanda sai bayan biki zasu koma, wasu kuwa sai dab da biki sannan zasu iso. 
  Shirye-shirye sosai akeyi, ba ga nan Abuja da mutan Kano ba, ba kuma ga can Gomben ba. 
    Amarya Ummi ta murzu iya murzuwa, idan ka ganta sai kace bata ta6a shiga rana ba tunda ta zo duniua tsabar kyau da murjewa da fatarta ta yi, ga shi kuma daman lokaci ne na damuna ba ranar ake yi sosai ba. Kayan gyara mace kuwa, har gajiya ta ke yi da sha, don Dada bata barta ba, haka suma surukan Dadan, (Anti Halima da Abida), daga sun ke6e da ita suke duramata. Kusan kullum sai sun kai ukun dare suna waya da ango wanda ya nuna gaba daya kewarta ya isheshi, har rantsuwa ya yi mata akan wani lokacin ji ya ke kamar ya yi tsuntsuwa ya biyota Gombe. Dariya kawai ta ke yi wani lokacin, wani lokacin kuwa tausayi ya ke bata. 
  Amina kuwa, tun kafin tafiyarsu Hajiya Adamawa ta kirata akan ta dawo.  Ana sauran kwana biyar biki da yamma tana zaune ta gama yin sirace na gyaran fata, hannunta rike da kofi wanda aka kad’a madara da wani gumba, su Abida sun sanyata gaba har da wasu yayyunta daga Jar Kwami akan sai ta shanye, kiran Amina ya shigo wayarta, dakyar suka bata wayar don da fari sun k’i wai sai ta shanye, wayar duk ta koma yaluwa, aun gaisa ta ke sanarmata cewar ta iso Gombe tana tasha wai ta yi mata kwatancen unguwarsu, ai Ummi daskarewa ta yi a zaune don mamaki, gani ta ke wasa kawai ta ke yi, saida ta rantse sannan ta saki dariyar murna.
  “Bari na bada a yi miki kwatance.”
Ta mikawa Abida wayar, nan ta kwatantawa direban Adaidaitan. 
  Ummi kasa zama ta yi, zata mike suka dakatar da ita, batasan sadda ta kwankwade maganin ba don hankalinta ya tafi ga Antinta. Dariya suke mata saidai bata ko sauraresu ba ta sanya dogon hijabi ta yi sashen Dada cike da mamakin yanda akayi Hajiya Mama ta barta ta zo.
  “Dada! Dada!!”
Suka yi kici6us a kofa.
“Lafiya Boddo?”
  Ta rungumeta.
“Ga Anti Amina nan zuwa, ta Kano wacce na baki labarinta.”
Itama Dadan ta hau farinciki.
“Kai Alhamdulillah, shiga ki yi wanka kafin ta karaso, bari na hadamiki ruwan dumin.”
Ai da gudu ta shige ciki ta dauki roban sabulunta, sosanta shanye a saman igiya ta ja, Dada da kanta ta hadamata ruwan wanka ta fad’a. 
Tana daga bandaki ta ji muryar Amina na gaggaisawa da mutanen gidan dake mata lale. Ai sauri-sauri ta shiga yi, tana fitowa ta ajiye bokitin sabulun anan kofar dakin Dada, hannunta rike da soson ta fada ciki sai jikin Amina, suka hau dariya. Dada ta kai mata dundu a baya.
“Ke kam Allah Ya sauwaka miki, kai Boddo, a jik’e fa ki ke.”
Ummi na dariya ta mike zaune,
“Wallahi murnar ganinta ne, ta yimin bazata.” Dada ta kar6i sosannata ta fita tana dariya. 
   Amina wacce ke dubanta fuska a washe ta kamo hannunta ta zauna gefenta.
“Wai kece kodai mafarki nake yi?” Cewar Amina.
“Ai Anti ni zan ce ina mafarki ma wallahi, ban ta6a zaton za ki zo Gombe ba, ya akayi ki ka zo?”Kedai kya yi mamaki, wallahi kamar wasa daman ina tunanin zuwan, kawai sai shekaranjiya Hajiya Mama ana zaune ta ke cemin ke kuwa bazaki Gomben ba wajen kawartaki? Ai bansan sadda na hau washe baki ba, daman naso zuwa Inna ta hana na tambaya don itama gani ta yi ba mu jima da dawowa daga Nijar ba kuma ace na k’ara tambaya zuwa Gombe. Ashe Allah Ya yi zan zo din.”
Suka yi dariya suka cafke, Dada ce ta kara shigowa dakin dauke da kwanon ruwa, ganinta yasa Ummi saurin mikewa don sanya sutura, kama baki Dada ta yi.
“Oh ni Fatima, yanzu ke fisabilillahi ba za ki sanya kayanki ba, ke kuma Aminatu kina ganinta ba za ki yi mata magana ba?”
Amina cike da jin dadin yanda Dada ke mata kallon ‘yar gida ta amsa.
“Ki yi hakuri Dadarmu, hirar yaushe gamo mu ke yi, rabonmu da juna tun kafin ta zo wajenku.”
  Kya6e baki kawai Dada ta yi tana murmushi.
“Ai shikenan, ga ruwa ki sha.”
Ummi na sanya kaya suna hira.
“Anti ina Bello?”
“Bello yana nan, ai na fadamiki biki kuma sai bayan azumi ko? Nan da wata biyu ya yi saura in sha Allah.”
  Murmushi Ummi ta yi.
“Allah Ya nunamana, ai kamar yau ne.”
  Ranar yini sukayi hira da Amina. Shi kansa Malam Balarabe da a ranar ya soma ganin Amina ya yaba kwarai da hankalinta, ta sha addua ba kadan ba wajensa da Malam akan irin kyautatawar da ta yi ga jininsu. 
  Da daddare bayan sun gama cin tuwo suna kwance saman gadon Dada suna hira har suka gangaro kan gidan Mami bisa tambayar da Ummi ta jefamata na ko sun shirya da yan uwanta. Baki Amina ta ta6e.
  “Kema kinsan fad’ansu fa babu inda zai je, sun shak’u da juna tun suna yara. Duk da na ji Mamin bata shiga shiryen-shiryen aurenku amman ta ce Hajiya Mama ta kai musu dinkin anko wuri daya, yanzu fa jikinta ya yi san…ke ga labari.”
Ta fada har tana kaiwa Ummin bugu a baya ta mike zaune, Ummi ta karkato tana mai zaro idanu da bude kunnuwa.
   “Asiri ya tonu, bayan dawowar su Mami daga Adamawa da kwana biyu Abban Adnan cikin dare idanunsa ya gane mishi Hajiya Binta na tone-tone bayan windon dakinsa, bai ma gane kowacece ba, Mami ce a dakinnasa ita dinma idanunta biyu, ganin ya fita da sauri ta mara mishi baya, saida suka zagaya suka isketa tana kokarin binne wasu layu, ke wallahi idan karshen mugunta ya zo babu mai iya tserar da mutum idan ba Allah ba, kuma daman shi Allah ba Ya zalunci, mata ta rude, har kusan sakinta ya yi, itace har da durkusawa neman alfarma wajen Mami akan ta taimaka ta tayata rokar gafararsa. A daren bai sauraresu ba, kiris ya rage a saketa saidai ta ci darajar ‘ya’yanta, dakyar da sudin goshi ta samu ya yafemata, saida Mami ta sanya baki sosai. Amma fa nima ina daga kicin ina aiki na ji Mamin suna hira da Hajiya Mama don gida ta zo ta sameta. Tun daga lokacin kuwa jikin Hajiya Bintar ya yi sanyi, har sashen Mami ta je ta fayyacemata mugun kullin da ta yi mata Abba ya juyamata baya da kuma yanda ta so had’e baki da ke amma ba ki bata goyon baya ba, tana kuka ta nemi gafarar Mamin, yanzu ba ki ga idan kin je gidan ki ka shiga sashenta yanda zata kar6eki ba, wallahi sai kinyi mamaki, duk ta yi sanyi har sashen Mami ta biyo Hajiya Mama suka gaisa, Iklima itama yanzu duk ta chanja kodayake ance ita wani saurayi ne ya yaudareta ya kaita gidan masu zaman kansu zai yi mata fyade, kinsan Iklima yar son zuwa party, dakyar Allah Ya kwaceta a hannunsa sakamakon zuwan yan sanda kame, aka hada har ita, saida ta kwana biyu a kaso Abba ya ce babu inda zai taka ya je belinta, sai fa can cikin yan uwan Ummanta ne suka je suka yo, ranar kuwa ta ci duka wajensa don har  makaranta ya hanata zuwa yanzu ya ce aure zaiyi mata.”
  “Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun! Duniya kenan, Allah na godemaka da bani na furtawa Mami komai game da abinda ya faru ba, nasan ba lallai lokacin ta yarda da ni ba.”
Amina ta yi murmushi.
“Bari kawai, saidai gaskiya bansan ya ta daukeki ba yanzun, na ji dai Hajiya Mama na yi mata nuni da cewar ke yarinya ce ta gari da wata ce tuni za’a hada baki a cutar da ita. Saidai tsakani da Allah ban ji amsar da ta bata ba. Amma in sha Allahu fatanmu bai wuce Allah Ya ganar da ita ba, itama ta amsheki hannu bibbiyu.”
  Ummi tan numfasa cike da jin dadi, itama nan ta hau bawa Aminan labarin dukkan abinda ya faru a zuwanta Abuja bayan ta 6oye sirrinsu da mijinta. 
   Amina ta janyo wayarta.
“Ai kuwa nima ki yi magana a sakani a group din ina so wallahi, Husna ta yi miki dabara wallahi har na ji ta burgeni.”
“Daman ai kina son mai sona.” Cewar Ummi tana murmushi. Suka yi dariya. 
   Gidan ya k’ara dinkewa da yan uwa daga Jar Kwami da Kwami harma da wasu yan uwan na can kauyuka wadanda Ummi batasan alak’arsu ba,  Inna Boddo bata samu zuwa ba adalilin ciwon k’afa, mutanen Adamawa basu suka iso ba sai ana sauran kwana biyu a soma biki a Gombe, yanda aka tsara kuwa, zaayi saka lalle da kamu rana daya sai kuwa yini na rana daya sannan washegari litinin a wuce Jar Kwami ta yi sallama da yan uwa ran talata kuwa a tafi kai Amarya Abuja inda anan kuma zasuyi nasu yinin da party kala daya.  
   Ango Faruk koyaushe korafinsa baya wuce na rashin sahibartasa a kusa da shi, ita kuwa bata gajiyawa da rarrashi da ban hakuri, kamar yau ma ta samu ta shige d’aka bayan fitar mutane tarar mutanen Adamawa da aka ce sun iso tana amsa wayarsa inda ya ke sanarmata zai biyo jirgi ya zo sannan ya koma washegari da wuri yanda iyayensa ba zasu ankara ba. Ta hau ba shi hakuri.
  “Wai ke bakya jin yanda nake ji ma ko? Allah kuwa Ummina har ‘yar rama na yi na riga na saba da jin duminki.”
Ta zaro ido sannan ta toshe baki da hannu sakamakon dariyar da ya so sanyata, to duka-duka ma yaushe aka yi daren da har gari zai waye? Wannan kam tasan ya so fad’ar ne kawai. 
  “Don Allah Yaya Faruk ka yi hakuri,  kwana nawa ya rage a…”
Fahimtar da ya yi ta ji kunya yasa shima ya basar.
  “To idan kina so na hakura sai kinyimin abu daya, kin yi alk’awarin za ki yi?”
  Ta dan yi shiru kafin ta gyada kai, daga can waje tana ji ana cigiyarta cikin wadanda suka zo daga Adamawa don har da muryoyin maza. Ta kara shigewa lungu.
“Eh.”
“Kiss me.”
Ta zaro ido, to ta ya ya? Kamar yasan bata sani ba ya gwada ta hanyar yi mata. Ta lumshe ido tana murmushi, a kunyace ta mannawa wayar sumba ganin an doso dakin sannan bata jira komai ba ta kashe, ya yi daidai da shigowar Amina a guje. Ta dubeta.
“Ke fito ki tayani ganin ikon Allah, kodai idanuna ne sukemin gizo.” Fadin haka yasa Ummi mikewa a rude, Amina ta ja hannunta jikin windon dakin suna lek’awa, itama daskarewa ta yi ta kasa kwakkwarar motsi ganin wanda bata ta6a zato ba…!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *