DAN ADAM CHAPTER 33

DAN ADAM CHAPTER 33

 Ranar ko waya bai samu damar yi da amaryartasa ba. Dukkan wani masoyi ga Ummi zai so ganinta a wannan rana don kuwa ta yi kyau ainun, har wani kumatu ta ajiye, kasancewarta fara k’al, sai kunshinta ya yi kyau ainun, hakanan siraran kitson da akayi mata shima ya taimaka kwarai wajen fiddo da zahirin Hasiya Abdullahi. Karfe hudu aka sanya na yin Budar Kai saidai ba’a soma ba sai karfe biyar harda mintuna, anan kofar gidan zaayi. Ummi ta hade cikin wata hadaddiyar shadda kalar sararin samaniya wacce ta sha aiki, suka sanyamata Alkyabba, duk a cewarsu itama jinin sarauta ce don kuwa jika ce gidan Lamidon Jar Kwami. Shima angonnata ya sanya riga da wando sai kuwa babban riga ta shadda kalar na Amaryartasa. Hular nan ta zauna d’abas a kansa, shi kansa Angon wani kamshi da annuri kawai ka ke gani saman fuskarsa. Fuskar Amarya a rufe ruf, haka aka riketa har mazaunin da aka tanada mata, Ango na zaune tare da su Haidar sai kuwa abokan karatu da na aikinsu, sannan danginsa mata a baya suna fuskantar Amarya Ummi da nata dangin itama daga bayanta. Algaita kawai ka ke ji ana busawa awajen, nan aka soma inda Ango Faruk ya mike, Haidar da Jafar wano abokin aikinsa sune a gefensa, haka ya nufi wajen Amaryarsa mata na faman gud’a da hanci ya bud’e fuskar Amaryarsa kuma matarsa, idanunta a k’asa tana faman doka murmushi yayinda ta ke kokarin danne kukan da ke son kwace mata. Nan ya soma zuba ruwan kudi waje ya cika da sowa da gud’ar mata, bayan ya gama nasa suma abokansa suka soma kafin daga bisani bayan komawarsu danginsa su tashi suma su yiwa Amarya nasu lik’in. Bayan sun kammala ne, itama Amarya ta mike da Amina da Abu kanwar gidado suka isa ga Angon wanda ya kasa dauke idanu daga kan Amaryarsa yana ji kamar ya dauke abarsa su gudu. Durkusawa ta yi suka mik’a mata turare na maza mai tsada da dadin kamshi ta hau fesa mishi, ya lumshe idanu ya bude yana dubanta, hawayen da ta ke kokarin dannewa saida suka zubo, ta daure ta daukesu da sauri, sannan ta amshi hankicif a kunyace ta hau goge mishi gumi kamar yanda aka koyamata, habawa zo kaga sowa da gud’a, su kuwa su Mami, al’adar Gombe ta tafi da su matuka don abin ya burgesu musamman ganin ba kure kamar yanda Abubakar ya koyawa Faruk haka din ya yi shima. Daga haka Amina ta mik’amata bandir na dari-dari, nan ta shiga lik’amishi itama, abin ya burge matuk’a, bayan ta kammala suma danginta suka dan yi nasu lik’in sannan aka dau hotuna wannan karon Ango Faruk babu wani batun iyayi na rashin son hoto har yayyunsa na zolayarsa yana dariya, daga nan kuma aka tashi taro….!Ikram zaune ta yi shiru yayinda yan uwanta ke faman danne-dannensu a waya, babu kunya Jidda da Fadila harma Baraka na aikin sanya hoton Amarya da Ango a dp, harma da aikawa group na zuri’a Baraka ta yi. Intisar na kwance saman katifa tana shan iskar fanka ga tulelan cikinta wata shida tana kallonsu da sauraron hirarsu tana dariya jin Aisha na fadin. “Um su Yaya Faruk ashe shi yasan me ya hango da ya mak’alewa ‘yar aikin Mami.” Suka kara darawa. Hankalin Intisar ya kai ga Ikram, ta zunguri bayanta da kafarta. Ikram ta dubeta, da hannu ta yi mata alamar tambaya na meke faruwa? Ta yi murmushin yak’e sannan ta girgiza kai a nufinta babu komai. Intisar itama murmushin kawai ta yi duk da ta fahimci lallai akwai abinda ke damun Ikram din, tun zuwansu ta yi sanyi kamar wata miskila yanzun. Ita kuwa Ikram ganin haka yasa ta wayancewa ta hanyar mikewa ta dubesu. “Bari naga Hajiya Mama.” Daga haka ta mike ta fito tsakar gidan, saidai kai tsaye waje ta fito inda matasa da wasu cikin matan gidan ke tsaitsaye, wata hira ta ke yi wasu kuwa kawai gaisawa da yan uwa. Ta yi ta faman wulk’a idanu tana mai fatan ganin Gidado, cikin sa’a ta hangoshi saidai hangen nasa baiyi mata dadi ba don kuwa tsaye ya ke da Hafsa sai wata mace wacce ta kasance Yaya awajen Gidadon suna hira da dariya, ta kasa dauke idanu daga kan Gidado wanda ayau shigar fararen kaya ya yi ya dora bak’ar hula akansa. Babu zato ya kallo gefenta, murmushi ne saman fuskarsa, murmushi ta sakarmishi ba tare da ta san lokacin da ya su6uto mata ba sannan ta yi saurin kauda kai ta juya ta koma ciki. Ya soma fahimto wani abun a irin kallon da Ikram ke yi mishi, ya sha kamata tana satar kallonsa daga sun hada ido sai ta kauda kanta, a farko ya dauka kuskuren fahimta ne saidai zuwa yanzun ya soma saka alamar tambaya ga hakan. Ya basar da tarin tambayoyin da ke yawo a kwanyarsa ya cigaba da maganar da sukeyi akan zuwan Hafsa Abuja inda ya ce babu inda zata je ita kuwa ta kawomishi abokiyar shawararsa kuma yayarsa Sumayya akan ta lalla6ashi saidai firr ya k’i aminta acewarsa ta ji da karamin cikinta tunda tana fama da laulayi, dole ta hakura don daman karambani ya kaita matsawa kanta akan zuwan saninta da Gidado, shi din kaifi daya ne. Misalin takwas da rabi na dare Ummi ta samu waya daga Mijinta akan ta fito yana kofar gida. Ta nunamishi akan ya yi hakuri akwai mutane ya nuna baisan zance ba. “Na baki mintuna biyar karki wuce Malama, gani kofar gida. Mutanen ai sun san mijinki ne.” Ta ajiye wayar a sanyaye ganin ya katse ba tare da ya ko saurareta ba. Dada ta dubeta, don ta shigo wajen Dada daukar chajar wayarta. “Idan kiranki ya ke karki k’i zuwa Boddo, mijinki ne.” Daga haka Dada ta fice, a kunyace ta mike rike da chajar ta fito, saida ta wuce wajen Amina ta bata har wayar sannan ta yafa mayafi akan doguwar rigar jallabiya da ta sanya don bacci daga haka ta fita tana ra6e-ra6e. Ta ci sa’a mutanen kofar gidan sun ragu sosai, ta hau lek’e-lek’e saidai ko mai kama da shi bata gani ba, sai hon da ta ji wanda ya sanyata duban motar, jeep bak’a wuluk sai shek’i ta ke, ba ka ganin na cikinta. “Bismillah Amarya, angon na ciki.” Cewar Jafar kenan abokin aikin Faruk wanda bata sanshi ba sai a yau ta soma ganinsa. Ta gaisheshi tana sunkwui da kai, ya amsa, kafin ta isa ya budemata kofar baya, ba musu ta shiga ta zauna sannan ta rufe kofar. Sanyin Ac da na tsadadden turaren Faruk Danzaki shi ya soma bugar gangar jiki da kofofin hancinta. Ta dan d’ago ta dubeshi, wannan katon sanye ya ke da riga fara k’al da dogon wando bak’i, ganin sun hada idanu yasa ta saurin sauke kanta. “Ina wuni.” “Bazan amsa ba, keda ki ka so ki k’i fitowa wani wai mutane.” Ta yi shiru tana wasa da zoben hannunta. Ganin shima bai ce uffan ba yasa ta fadin. “Ka yi hakuri don Allah.” Ya lumshe ido yana murmushi alokaci guda kuma ya tura yatsunsa na dama cikin sumar kansa. Ba zato kuma ta ji kansa saman kafafunta yana duban fuskarta, yanayin jikinta ya sauya, ta na mai jin wani iri tun daga tsakiyar kanta har kafafunta. Bata kuma ankara ba, ya kunna wayarsa hakan ya taimaka wajen ganin fuskarta sosai, ta runtse idanu zata kauda kai saidai bata samu damar hakan ba don tuni ya ajiye wayar ya janyo fuskarta zuwa tasa. Nan kuma lamura suka chanja daga gareshi zuwa gareta. Don kansa ya saketa ya na dubanta, ita kuwa mayafinta ta sha zata rufe fuskarta yayinda ta ke faman sauke ajiyar zuciya. “Kimin alfarma daya, kinji?” Ya yi maganar cikin rad’a, a hankali ta daga kwayar idanunta ta dubeshi, idanunsa a rufe sai ta ganshi kamar mai shafa mai na k’ara hasken fata sakamakon hasken da ta ga ya yi mata. Bai saurari amsarta ba ya bude idanu cikin nata ta yi saurin wayancewa da kallon kasa. Murmushi ya yi. “Abinda ki kemin a waya shi na ke fatan samu yanzu.” Gabanta ya buga, ta dubeshi kadan ya shagwa6e fuska. “Please.” “Ka yi..” “Ba za ki bar motarnan ba sai kinyi ko kuma na wuce dake Otal.” Ya fada babu alamun wasa, tasan sarai zai iya aikatawa. Ta runtse ido tana ji kamar ta yi me, ta daure ta kai hannu ta ja wayarsa ta danne hasken da hannunta, da sauri ta aikata abinda ya umarceta, dariya ya yi gami da mikewa zaune. “Matsoraciyata.” Ta hau murza idanu da hannu tana murmushi. “Na yi masifar kewarki Ummina, ina kara sonki a kowane rana.” Shiru ta yi tana mai jin wani dadi a kasan ranta. “Inama zan iya bayyanamaka irin son da nake maka Yaya Faruk?” Ji ta yi ya dora kansa a kafadarta ya sanyata jikinsa da hannu daya. “Mezai hana Ummina, please sanarmin, na jima ina son jin kin furta kina sona da bakinki ba don bansani ba, saidai ina son ji.” Ta hau rarraba idanu, ya akayi maganar zuci ya fito fili har ya shiga kunnensa? Ta hadiyi miyau, anya zata iya? ‘Ki ka yi wancan ma bare wannan?’ Cewar wani 6angare na zuciyarta. Ta ji ya kara matsar hannunta. “Please Ummi, taimaki Faruk dinki kinji? Ji yanda kirjina ke bugu don kaunarki.” Ya kai hannunta saitin kirjinsa, aikuwa bugun ya ke da sauri-sauri. Ya kai bakinsa saitin kunnenta. “Zuciyata zata fashe da sonki.” Ta lumshe ido tana jinta kamar a Aljannah, murmushi saman fuskarta ta yi kasa da kanta. Dakyar ta bude baki ta yi magana. “Ina…ina…” Sai kuma ta yi shiru. “Say it please.” Ya yi maganar da siririyar murya, ta kasa jure sakonnin da ya ke aikamata, ta kara runtse idanunta. “Ina sonka.” “Irin wanda na ke miki?” Ya yi tambayar ba cikin nutsuwa ba, ta rasa bakin amsawa, shi dinma bai saurari amsar ba ya cigaba da jero tambayoyin kamar a dakin jarabawa. Ita dai Um kawai ta ke binshi da shi, yanda ya ke mata yasa har hawaye ta ji sun zubomata na tausayi da kuma tsananin kaunar Faruk, ta ji ko k’uda bata kaunar ya shiga tsakaninsu, ta ji ta kara sallama mishi zuciya da gangar jikinta, ta ji nan duniya babu abin so da kauna gareta sai Faruk. Shi kadai tallin tal ta ke so ta ke kauna koda kuwa za’a kawomata wanda yafi Faruk komai da komai, ita sai Umar-Faruk Danzaki, babu gudu babu ja baya….! So kenan…!!! K’arar wayar ce ta firgitasu, ya ja tsaki gami da dauka. Jafar ne, ya soma mishi magana akan dare ya yi haka kuma ga hadari a garin. Dole ya amsa da toh sannan ya ajiye wayar ya kwantar da kai saman kujera yana duban Ummi da murmushi saman fuskarsa. Ta kauda kai tana gyara zaman mayafinta. “Saida safe.” Cewarsa, ta amsa, “Allah Ya tashemu lafiya.” Daga haka ta soma kokarin bude kofar. “Ummina.” Ta juyo tana dubansa. “Ina sonki dagaske fa.” Murmushi ta yi wanda yasa ta k’ara burgeshi. “Nima haka.” Daga haka ta yi saurin bude kofar ta fice. Jafar ya shiga shi kuwa ya tsallako gaba suka bar unguwar. Ta yi mamakin ganin har wasu sunyi bacci, saida Amina ke sanarmata cewa goma ta wuce sannan ta yi guum kawai da bakinta duk kunya ta isheta sai kuma ta hau fadin. “Lokaci yanzu ba dai gudu ba, Allah Yasa mu cika da imani.” “Amin dai.” Cewar Amina da sauran wadanda basu kai ga bacci ba suna masu danne dariyar da ta tahomusu. Washegari aka rankaya Jar Kwami inda aka ga tsoffi aka gaggaisa shima Ango ya je suka ganshi sannan ya wuce da tawagarsa a ranar, su kuwa su Ummi ba su suka baro Gombe ba sai washegari bayan ta sha nasihu daga iyayenta da kakanninta, Malam Balarabe har kuka ya yi na ganin zai kara nesa da diyartasa saidai wannan karon hankalinsa kwance tunda yasan gidan aure ta nufa. Mutan Jar Kwami kowa aka nuna mishi Mami da su Hajiya Mama matsayin surukan matar da Abubakar zai aura wato Ihsan sai su hau cigiyarta saidai ace musu bata zo ba, koda Ihsan ta ji baki kawai ta ta6e don har kuka ta yi sakamakon ganin hoton Ummi da Faruk saidai ko zata mutu ta barshi kenan, amma har lokacin akwai ragowar tabon sonsa cikin zuciyarta. *** *** *** ABUJA Amarya da danginta har ma da dangin miji suka iso gaba daya, Hajiya Babba da su Hajja wacce ta sauko ta dangana, suka tarbesu hannu bibbiyu. Har da kishiyoyin Mami, wato Hajiya Binya da Lubna da yaransu, su Iklima yanzu gaba daya ta chanja kamar ba ita ba don har rungume Ummi ta yi. Ummi a dakinta ta sauka da kawayenta wannan karon ko Amina ba’a ware ba. Saida sukayi sallah sannan aka ci abinci, a ranar ne zaayi Dinner, ango ya wuce da amaryarsa. Gidan a cike suka iskeshi sakamakon ranar ne Hajiya Babba ke yininta. Wanka suka sanya Ummi ta yi ta hade cikin wani tsadadden leshi ja mai adon duwatsu, dinkin ya zauna d’abas a jikinta, haka aka rufemata kai aka kaita wajen su Hajja, nan suka rufarmata da nasihu, bayan kammalawa aka wuce da ita wajen Hajiya Babba da kawayenta har su Hajiya Mama gaba daya, suma suka tofa nasu albarkacin bakin har Hajiya Babba na fadin. “Ummi diyata ce daman.” Wannan furucin ya yiwa Ummi dadi matuka, abin mamaki wajen la’asar sai ga Husna da abokan karatunsu na Islamiyya, ashe Faruk din da kansa ya kaiwa Husna kati na dinner party ta bawa abokan karatunsu harma da na yinin Hajiya Babba inda duk suka sanya ankon da suka yi, har kunya ta ji don tasan ta fadawa Husna bikin kuma suna waya saidai bata samu damar bata kati ba. Su Fati burinsu bai wuce na son sanin waye mijin ba don har lokacin Husna bata sanarmusu komai ba hakanan ko hotonsa basu gani ba. “Ni dai Anti Ummi sai rarraba idanu nake naga ta inda zan ga Yayanmu.” Ummi murmushi ta yi kawai. “Za ki ganshi.” Husna ta dara. Nan kuwa Ummi ta shiga nunamata yan uwanta suna gaisawa. Ihsan kwance saman gadon Ikram tana waya da Abubakar, Ikram na gefe tana duba mahadin kayan da zasu sanya na dinner party wani leshi ne ruwan hoda saik uwa sauran yan mata sa’anninsu, Intisar ta shigo, ta dubesu kaf sannan ta tsaida idanunta kan Ikram. “Kanwata zo.” Ta dubeta kafin ta mike ta maida kayanta sif ta bi bayanta. Kai tsaye yar barandar Hajiya Babba suka isa wacce kana iya hangen harabar gidan ta nan. Ta dubeta da kulawa. “Ki fadamin damuwarki don Allah Ikram, ke ba ki lura da sauyin da ki ka yi ba tun kafin soma bikin Yaya Faruk? Menene ya ke damunki haka da har ki ke ramewa? Kin koma wata shiru-shiru kamar ba Ikram din da na sani ba mai yawan hira da dariya.” Ikram ta ji gabanta ya fad’i, wato har an fahimci damuwarta? Ta k’ak’alo murmushi. “Kai in-law, nifa babu abinda ke damuna…” “Karya ki ke wallahi, ko yanzu kin fuskarki ta kara tona miki asiri, lallai kina cikin damuwa saidai kuma idan ba ki yarda da ni ba ne shiyasa bakyason sanarmin. Barin kashi a ciki fa ba ya maganin yunwa. Yanzu gayamin, me ya hadaki da hoton wannan Gidadon a jakarki, dan uwan Ummi?” Idanuwa a waje ta ke duban Intisar, ga wasu ruwan hawaye da suka ciko mata. Daidai lokacin Gidado da Abubakar da kuma Haidar suka shigo harabar gidan suna hira da dariya kamar dama can sun saba, daman suna kofar gidan, hankalinsu ya kai garesu, suka dubesu, Gidado ya saje da yan birni, sanye ya ke cikin farar shadda marar nauyi mai tsada cikin wanda Abubakar ya dinka mishi don Abubakar mutum ne mai yiwa yan uwa sosai, sam abin hannunsa bai rufemishi idanu ba, barshi dai da son ta6a mace idan yana sonta wanda ya ke fatan ya daina. Su kuwa basu ko lura da su ba har suka wuce, Ikram hawayenta ya zubo wani irin wutar so tana kara ruruwa cikin zuciyarta har batasan lokacin da ta dubi Intisar ba ta soma magana bayan ta rike hannunta. “Ina sonshi tun sadda na soma ganinsa a hoto.” Ta kwashe labarin komai ta sanarmata har zuwa sadda ta fahimci yana da mata. Ta karashe tana kuka, kasancewar wajen gilas ne yasa na falo ma yana kallonsu, Hajiya Mama ta kwala kiran sunan Intisar. Ikram ta juya baya da sauri tana share fuska, Hajiya Mama ta karaso. “Ku kuma lafiya? Me ya sami Ikram din?” Ta fada tana duban Ikram mai share fuska, Intisar ta wayance. “Um wai kanta ke ciwo shine abu bai kai ya kawo ba ya bata haushi wai ana damunta da hayaninya a daki.” Hajiya Mama ta hau ta da fada. “To shine za ki zauna kina faman kuka, jimin aikin banza, ke kuma ki ka biyemata? Zo ki je ki bata magani mana, kuma ku soma shiri ga Magriba ta yi yanzu za’a wuce.” Suka amsa da toh. Intisar ta dubi Ikram cike da tausayi. “Shakka babu wannan lamari ya bani mamaki matuka wallahi, amman ki bari za mu yi maganar daga baya, mubar nan kafin Hajiya Mama ta dawo.” Suka fice. Wajen biyar da rabi Ummi ta amsa kiran Daddy don yi mata nashi nasihar. Kanta a rufe da mayafi, ga mamaki nan ta tarar da Faruk, ta zauna ta gaisheshi ya amsa fuska a sake. Nan ya shiga yi musu nasiha mai ratsa jiki da jini har ta kai Ummi ita mace mai rauni soma hawaye, shi kuwa gogan gaba daya jikinsa ya yi sanyi matuk’a, can kuma ya sallami Ummi, ta yi mishi godiya bisa karamcin da ya yi mata, ta nuna ta daukeshi matsayin uba gareta, ya ji dadin kalamanta da addu’o’inta gareshi. Ya yi mata fatan alheri gami da sanyamata albarka. Haka ta koma dakinta jiki babu kwari, yan uwanta yan Gombe da yawansu sun wuce ganin gidanta da kuma kai ragowar kayan da suka zo da shi da na gudunmuwa da ta samu. Karfe bakwai na dare aka soma shirin tafiya Party, alokacin sun dawo gida kowannensu na yaba tsarin gidan Faruk da Ummi. Har hotunan suka nunamata banda murmushi ba abinda ta yi, kwarai ya tsaru duk da cewa flathouse ne. Ana wannan shirye-shiryen ne wata arniyar mota jeep ta shigo harabar gidan, inda wasu mata su bakwai suka sauko. Da gudu Husna ta isa garesu ta rungume, Fati ta nemi sanin ko su waye musamman ganinsu da anko wanda yafi na mutan gidan kyau da tsada, kafin ta amsa mata wata motar bus ta k’ara shigowa, nan kuwa ta ga matan rututu duk cikin ankon suma, wani arnen leshi suka sanya saidai suma kalar ruwan hodar ne, sun yi kyau har sun gaji da haduwa. Dariya Jidda ta yi tana duban Fadila. “Wannan (ta nuna wata ‘yar fara-fara doguwa cikinsu) Farha sunanta, schoolmate dita ce, ina yawan basu labarin kawata Ummi shine fa suka ce sai sun zo bikinta, kinga ango saida ya bani katin kowaccensu ya ce na bawa duk wasu masoyansu, nan da ki ke gani har da yan groups dinmu na whatsapp. Su Sally, Bingel, sophie, Fatima Aminiya, Ummu abdool, shamsiyar katsina, Ab kura, shukra, Dg da sauransu wallahi suna da yawa ne.” Fati ta dubesu, tabbas kuwa harda wadanda suka girmewa Ummi. Suka shiga ciki don gaisawa da mutanen gidan kafin su wuce wajen fatin. Husna zata bisu Fati ta janyota ta dawo baya. “Wai wane group da wanne ki ke fad’a?” Dariya Husna ta yi, akwai yar Taskira, su Neena su sholingaye su Aisha da Sadiya, akwai yan Rof gaba dayansu wasu ta gidajensu zasu je, da yan Classic Ladies ga Matan Aljanna da Matan Aure Only, da Matan Aure na antinmu Amina Mamser, ban rageki ba, kaf yan Dm masoya labarun soyayya mazansu da matansu kalilan ne bazasu ba wato tsoffin haka ma yan group din khalisat da…” “Ke ya isa, wallahi kinsa na kara jin son halartar fatin nan, Angon ma nafi dokin gani, kai Ummi ta godewa Allah wallahi, mutane ai rahma ne.” Dariya Husna ta yi. “Muje mu karasa shirinmu Madam.” Suka rankaya ciki. Wajen takwas aka soma tafiya, saida aka ragu sosai Ango ya iso daukar Amaryarsa….!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *