DAN ADAM CHAPTER 8
Ahmad Bashir Danzaki, haifaffen garin Kano. Ya kwashi tsawon shekaru sittin a rundunar sojoji yana aiki kafin ya yi ritaya. Matarsa d’aya tun lalle, Hajiya Fatima wacce suke kira da Hajiya Babba. Yaransu shida cif, Usman shine wanda ya yi karatunsa kacokam akan kasuwanci. Ridwan ke bi mishi, shi din ya kasance kwararren likita a fannin mata, sai Haidar wanda ya ke lauya, sannan Faruk wanda yake ma’aikacin banki. Baraka wacce suke sa’anni da Adnan da Iklima, tana aji na karshe a sakandare wanda tare suke tafiya. Sai auta Ikram, wacce sa’ar Ihsan ce, itama tare suke tafiya da ihsan, suna aji na biyu a babbar sakandire. Umarul Faruk ya kasance ma’abocin son zane, daidai da dakinsa idan ka shiga haka zakayita cin karo da takardu masu dauke da zane kala-kala. Sau da yawa haka mai gyara sashensa, Bala, zaiyita kwasarsu yana zubarwa. Son zanensa bai ragu ba saida ya soma aiki ka’in da na’in, alokacin ya zamana babu kwakkwarar lokacin zane, wani sa’in kuwa sai ranar da babu aiki yakan ta6a. Idan kuwa ka ganshi a falo, to fa hira ce ta motsa. Kokuma yan uwansa sunzo nan zasu had’u suyita kwasar hira suna dariya har mahaifinsu. Rayuwarsu tana tafiya cike da sha’awa, ga ilimin addinin da na boko. Babu mai takurawa wani, hakan bai hanasu kiyaye dokokin Ubangiji ba.+ WANNAN KENAN.. *** *** *** Alhaji Atiku Modibbo zaune a k’ayataccen falonsa bayan ya kammala cin abinci. Ya kai duba ga sanyin idaniyarsa da ta fito daga d’akinnasa bayan kammala feshe d’akin da maganin sauro, murmushi suka sakarwa juna, ya rik’o hannunta ya zaunar da ita a gefensa. “Bakya tsufa Madina, menene sirrin?” Mami tayi dariya gami da yin farr da ido. “Oh Abban Ihsan, kai dai kullu yaumin baka rabo da zolaya.” Ya yi dariya. “Ina zolaya anan? Babu sai tsagwaron gaskiya.” Sukayi dariya. Ya rik’o yatsunta yana murzawa. “Kiramin d’ana.” Ta cire yatsunta, zata mik’e ya dakatar da ita. “Ina wayarki? Kiyi amfani da ita mana.” Ta sa hannu ta dauki wayar a saman tebur kafin ta hau laluben lambar Adnan. Lokacin yana zaune a falo suna kallon Dadin Kowa suna kyakyata dariya har Ummi dake gefe zaune. Bayan ya d’aga ta sanarmishi kiran Abba, a take ya mik’e ya fita. Da sallama ya shiga falon bayan sun amsa. Ya k’arasa ga Abbansa ya zauna agefen kafafunsa. “Abba gani.” Da murmushi saman fuskarsa ya dubi d’annasa. “D’an Abba, ya makaranta? Naji kun soma jarabawar karshe ko?” Adnan ya sosa kai yana murmushi. “Eh Abba, komai yazo karshe in sha Allah.” Abba ya jinjina kai. “To haka akeso, Allah Ya taimaka.” Mami da Adnan suka amsa. Ya cigaba da magana. “Kaje kayi nazari dakyau, saika zo ka sanarmin makarantar da kakeson zuwa k’aro karatu a k’asar waje. Kada kayi gaggawa ka bi sannu, idan ka sanarmin sai mu bincika mu ga yanayin ingancinsa. Allah Ya yi maka za6i na alheri.” Wani dad’i ya daki zuciyar Adnan, ya yita nanata ambaton Allah a zuci, a k’arshe cikin tsananin murna da d’oki ya hau yin godiya ga mahaifinsa. Haka ya tashi ya koma falon Mami cikin tsananin murna. Yana shiga ya saki k’ara don tsabar farinciki har yana doka tsalle. Tunda suke basu ta6a tsallaka Nijeriya ba, sai a wannan karon da yake fatan burinsa ya cika. Gaba daya suka zubamishi ido. Ihsan a guje ta taso. “Yadai broda?” Nan ya sanarmata, ai don dadi itama ihun ta sanya gami da rungumeshi, shima Fahad agefe yana tsalle. Ummi kanta itama saita tsinci kanta cikin farinciki matuk’a, domin burinta ta ga duk wani masoyinta cikin farinciki. Ya yi dakinsa a guje, Ihsan ta mara mishi baya tana mai cewa. “Yi browsing mu dudduba makarantun.” Bayan shigewarsu ta numfasa, babu jimawa da shigarsu wayar Adnan ta dauki k’ara. Da sauri Ummi ta mik’e ta dauka da zummar kai mishi. Hoton Faruk ta ci karo da shi 6aro-6aro akan screen din wanda Haidar ke rik’e da hannunsa shi kuma yana dubansa da murmushi mai bayyana hak’ora. Gaba d’aya sai ta tsinci kirjinta na bugu. “BRO FARUK.” Sunan dake saman screen din kenan, ta ajiye wayar da sauri, ta kama hanyar d’aki har lokacin wayar na k’ara, haka ta juya ta koma ta dauka. Haka kawai ta tsinci kanta da d’agawa batare da tasan dalili ba. Ta gwada (sliding) wajen koren kamar yanda ta sha ganin Adnan ya yi idan zai d’aga waya. Cikin sa’a kuwa ta soma jin maganarsa yana sallama. Ta kasa magana don gaba daya ta tsorata, jin maganar Adnan kawai ta yi a kanta. “An kirani ko?” A razane ta juyo ta mik’amai. Kasa magana tayi sai kai data gyad’a. Allah Ya taimaketa batare da Ihsan suka fito ba. Ta juya da sauri ta nufi dakinta. Tana ji sadda yake fad’in. “Afuwan dan uwa wallahi Ummi ta d’aga, fitowata kenan daga d’aki.” Daga haka ta shige ciki da sauri. Shigarta d’akin ba wuya ta ji an kwankwasa k’ofar, a gigice ta dubi bakin k’ofar. Adnan ne tsaye yana murmushi. Ya mik’omata waya. “Kar6i, za ku gaisa da Yayana. He’s my best.” Ya k’arashe cikin muryar rad’a yana mai kanne mata ido d’aya, ta yi mamakin rashin ganin kowace alama a fuskarsa kamar yanda nata fuskar ya nuna tashin hankali tsantsa. Ta kasa kar6ar wayar har saida ya yi mata magana karo na biyu, alokacin tasa hannu ta kar6a, kasancewar har lokacin cikin zumudin daddadan albishir na mahaifinsa yake, yasa yana mik’amata ya juya zuwa dakinsa on don ganin abinda Ihsan ta binciko da (Laptop) dinsa. Ta tsaya cak tana duban wayar har lokacin a matukar tsoro take. Kawai sai ta ji idanunta sun cika da kwalla, to wai me zata ce? Inama tun farko bata d’aga wayar ba? Batasan cewa ya katse ba saida ta ji sabon ringing wanda ya kad’a har cikin ranta. Hotonsa ne dai 6aro 6aro wanda idan kiran ya katse bata gani, hakan ya tabbatarmata cewa a sunansa kawai ya sanya. Tana hawaye ta danna ta kara a kunnenta, ji takeyi inama kada ta d’aga, ita kam ta shiga tara…! Assalamu alaikum.” Ta fad’a cikin rarrauniyar muryarta wanda sautin kuka ya ta6a. Faruk dake tsaye a barandar dake a sama wajen dakinsa yana duban farfajiyar gidannasu, ya numfasa jin muryarta. “Waalaikumussalam, Ummi kina lafiya?” “Umm, ina wuni Yaya Faruk.” Ta fad’a gami da kai gwuiwoyinta k’asa kamar yana ganinta. Murmushi ya yi lura da ya yi na cewar ta tsorata da shi. “Lafiya lau.”+ “Wai Ummi dodo na zame miki? Gaisuwa kad’ai na buk’ata fa…” Sai kuma ya yi shiru kafin ya d’ora maganarsa. “Ok, daman naji ance ke kika d ‘aga waya ne, shiyasa na buk’aci k’anina da ya ba ki mu gaisa. Fatan komai lafiya?” Ta ja ajiyar zuciya wanda ya jishi har cikin ransa, ya tsinci kansa da lumshe idanu. “Lafiya lau, ya su Hajiya? Agaishesu don Allah.” Ta burgeshi, hakan da ta yi ya nuna tana da hankali. Murmushi ya yi mai ban mamaki wanda da wani cikin yan uwansa zai ganshi da ya zargi koda wata budurwarsa ya ke wayar. “Zasu ji, thank you.” “Um.” Shiru ya biyo baya ta cire wayar a kunnenta ta ajiye gefe gami da zuba tagumi. “Na shiga uku, meya kaini d’aga wayar Yaya Adnan tun farko? Yanzu wace masifar zan jawowa kaina?” Tayi maganar a fili wanda tsaf ya shiga kunnen Faruk kasancewar bai riga ya katse kiran ba, sai lokacin ya kashe ya sake kira. Har razana ta yi gami da ja baya. Ido waje ta duba ta ga shine har lokacin, ta d’aga ta kara a kunnenta. “Ba..bari na mik’aaa mishi, ya fita.” Ya girgiza kai tamkar tana ganinsa alokacin da ya koma d’aki ya zauna saman kujera. “No, ke nake nema ai. So nake nasan masifar da na jawo miki?” Muryarta na rawa yayinda hawayenta suka zubo ta girgiza kai. “Wal..walla…” “Ki zama jaruma a komai na rayuwa Ummi, matsoraci bai zama gwani. Duk abinda zakiyi a rayuwa kiyishi da zuciya d’aya, ki zauna da kowa zaman gaskiya. Komai da zakiyi kiyi don Allah ba don wani halitta ba ok?” Ta gyada kai gami da numfasawa, sosai nasihar ya shigeta, haka kawai ta tsinci kanta da jin wani sanyi a zuciyarta. “Nagode Yaya Faruk.” Ya yi murmushi mai sauti kafin ya amsa. “Mu’assalam.” Daga haka ya katse wayar, batayi gangancin k’ara wani tad’in a fili ba sai a ranta. Gaba daya batasan cewar kiran bai katse ba. Lamarin ganinsa takeyi tamkar a mafarki, wai itace ke waya da Yaya Faruk? Ikon Allah! Yau kuma meke a kansa? Haka tayi lamo a saman katifa cike da fargaba, sallamar Adnan ta sanya ta mikewa zaune tana mishi murmushi na yak’e. Fuska a sake ya kar6i wayarsa da take mik’o mishi gami da fadin. “Har an gaisa? Wai daman kun ta6a gaisawa da shi?” Ta gyada kai. “Eh, shi ya taimaka ya kawoni gida ran fatin Yaya Haidar ai.” Ya dan daga kai alamar tunani kafin kuma ya dan daga gira. “Oh, na tuna anyi haka fa. Kinsan Yayannawa ba dai kirki ba.” Murmushin dai ta k’ara yi sannan ya juya ya fice. Ta zauna ta yi tsuru cike da tunanin wannan lamari. A karshe dai da ta ga babu wani abu da ta tsinkayo ta share batun. *** *** *** ‘Me nayi?’ Ya jefawa zuciyarsa tambayar da baisan amsarta ba. Ya jingina kansa jikin kujera gami da k’urawa talabijin ido. Babu abinda ya yi banda sada zumunci. ‘Kar ka d’arsawa zuciyarka wani abin daban, kana tausayinta ne kawai.’ Cewar wani sashe na zuciyarsa. Ya kauda maganar gaba d’aya ta hanyar kunna talabijin.3 *** *** *** Sallamar da aka doka ne ya katse hirar da Habiba ke kwasa da mijinta. Ganin mai sallamar yasa duk suka washe baki, mijinta Yahuza ya mik’e. “Kai lale da mutan Kaduna.” Fad’in Habiba kenan tana kokarin gyara tabarma. Bayan sun zauna aka shiga gaisawa, Habiba ta zari gyale ta fita siyo ruwa. Hajiya Munira kenan, ‘yar kanwar Yahuza mijin Habiba, wacce ke auran babban ma’aikacin gwamnati a Kaduna. Ta zauna suka soma gaisawa da kawunta yana tambayar sadda ta iso. “Kwanana biyu kenan ai Kawu.” Ya jinjina kai kafin su cigaba da hira a haka har Habiba ta dawo dauke da leda mai ruwan sanyi da lemu tana fad’in. “Um, kaga fa tsabar zumud’i ko kudi ban dauka ba, bari yarinyarnan su zo su mik’a mishi.” Suka dara sannan aka hau hira. A haka Dija ta dawo ta samesu. Ta ji dadin ganin Munira, suka shiga hira harma a karshe Munira ta nuna tana gayyatarta Kaduna koda na sati ne. Babu musu Dija ta nuna zata. Kawu Yahuza da Habiba sunyi murna kwarai, ko ba komai sa dan huta da surutun mutane na cewar anbar yarinya ba aure sai gantali. Man aka tsaida idan Munira zata wuce, tare zasu tafi. Koda ta gama kwanakinta a kauyen, suka shirya tare da Dija da yaranta biyu, direbanta ya kwashesu zuwa Kaduna. *** *** *** ABUJA Ranar juma’a da misalin karfe bakwai, gaba daya yaran Hajiya Babba sun had’u suna hira kamar dai yanda suka saba, duk juma’a anan suke wuni matuk’ar ba wani aikin ne ya tasowa dayansu ba ko duka. Wannan lokacin ma Faruk baya tare da su, a haka ya dawo daga aiki ya samesu suna ta zuba hira suna dariya ga kayan marmari agabansu a babban faranti an yayyanka suna sha. Yana sanye cikin riga kalar sararin samaniya, ya d’ora kwat dinsa bak’i akan hannunsa na dama, d’ayan hannun kuwa (briefcase) ne, gaba d’aya fuskarsa ta tona gajiyarsa. Suka amsa sallamar da ya yi ciki-ciki. Cikin dariya Ridwan ya dubeshi. “Kaga manyan ma’aikatan banki.” Gaba daya suka dara, shi kuwa gogan sai ya k’ara marairaice fuska ya karaso ciki ya zube a saman kujera gami da fad’in. “Wash!” Haidar ya birkita sumarsa. “Sannu lil, haka muke fama.” Faruk ya murmusa. “Kai, anya kana aikin da mukeyi?” Cewar Likita (Ridwan) kenan. Usman ya cafe. “Mu da ke wuni a shago sai mu ce me?” Nan da nan kuma sai hira ta koma musu tamkar wasu abokai kowanne yana k’ok’arin nunawa sauran zafin aikinsa musamman Babban Yaya da Likita wanda idan da sabo sun saba. Ikram na goyon bayan likita ayayinda Baraka ke bayan Barista Haidar kasancewar itama fannin da ta ke son karanta kenan. Faruk dai sulalewa ya yi zuwa dakinsa don watsa ruwa. Bai fito ba saida ya yi wankansa tsaf ya sanya riga t-shirt bak’a da farin wando wanda da kadan ya wuce gwuiwa, kasancewarsa farin mutum, ba karamin kyau da haske ya yi ba, ya jona wayoyinsa a chaji ya fito. Alokacin sun nufi masallaci, shima ya bi bayansu. Tare suka shigo gaba daya har Daddy dinsu. Bayan an kammala cin abinci ne, kowanne Daddy ya tambaya ko da wani matsalar. Duk suka tabbatar mishi babu, Babban Yaya ke sanarmishi zai je Kano ganin wani babban dan kasuwa da ya buk’aci ya shigo mishi da kaya suyi lissafi. Daddy ya gyada kai. “Allah Ya bada sa’a.” Suka amsa da amin. Faruk wani abu ya tuno hakan yasa ya dubeshi. “Ko nayi maka rakiya?” Babban Yaya ya washe baki. “Wallahi da ka kyauta, daman banson bin hanya ni d’aya babu abokin hira.” “Toh kai baka da wani uzurin ne goben?” Cewar Daddy yana duban Faruk. Faruk ya daga kafada kadan yana girgiza kai. “Babu.” “Ai kuwa da kun biyamin gidan Alhaji Labaran, akwai saurin auren ‘dansa ran lahadi, bazan samu zuwa ba. Kuje a madadina.” Sukayi na’am har Haidar na fadin ba don yana da abin sabgogi ba a goben da ya bisu. Faruk ba murmushi ya karkata wuya zuwa saitin kunnen Haidar. “Kaidai fad’i gaskiya, Intee ce zata hanaka zuwa.” Haidar ya dubeshi ya harara da wasa, hakan ya bawa Faruk dariya, ya saki murmushi mai bayyana hak’ora.+ Basu jima ba anan, duk matasan suka mik’e. Haidar saida ya tsaya a falon Faruk sukayi kallon ball kafin ya wuce gidansa bayan waya da Intisar ta dameshi da shi. Faruk haka kawai yakejin nishad’i game da zuwansu Kano. Yana matukar kaunar k’ara sanyata a idanu. *** *** *** Washegari kuwa misalin tara suka bar Abuja da Babban Yaya, koda suka isa saida sukayi La’asar a gidan kakansu Modibbo suka ci abinci sannan Babban Yaya ya k’arasa ga abinda ya kawoshi, shi kuwa Faruk waya ya yiwa Adnan ya sanarmasa yana Kano, ba jimawa kuwa sai ga Adnan suka fice yawo. Idan ka gansu kamar abokai don babu laifi shima Adnan ba dai tsawon k’afa ba. Saida suka gama zagayansu sannan suka nufi gidansu Adnan domin ya gaisa da Mami. Ummi na zaune a inda ta saba, wato can hanyar kicin tana kallon tashar cartoon wanda Fahad ya sanya, ko kadan kallon ba dadi ya ke mata ba, asalima ba ba fahimtar komai take ba, wannan dalilin ne yasa ta mik’e gami da nufar hanyar d’akinta. Ya yi daidai da sallamarsu. Adnan na gaba, yana biye da shi. Ta amsa tana dubansu. Yana sanye da riga T-shirt ja da dogon wando bak’i. Shima idanunsa cikin nata, ta tsinci kirjinta da bugawa da sauri-sauri. Da sauri ta zube tana gaisheshi cikin rawar murya. Ya sauke ajiyar zuciya kafin kuma ya amsa. Daga haka ya bi bayan Adnan, ta mik’e jiki a sanyaye ta karasa dakinta da sauri. Juyowa ta yi a sadda ta kai kofar shiga, suka had’a ido sa’ilin da yake cire takalmi shima din ita ya waigo. Alokaci guda suka janye idanunsu bayan da suka ji wani sauyin yanayi na daban a jinin jikinsu. Ta yi wuf ta fad’a d’aki, tana jin ihun Fahad yana ambaton sunansa. Ihun ne ya janyo hankalin Ihsan da Mami wadanda suke dakin daga cikin falon Mami suna magana akan dinkin da za’a yiwa Mamin na ankon bikin Baraka. Da sauri Ihsan ta fito, ganin Faruk ta hau dariya, cikin daga murya tace. “Mami dagaske ya ke, Yaya Faruk ne.” Jin haka yasa Faruk suka k’arasa ciki, daga lokacin kunnuwanta suka daina jiyo sautikansu. Ta zauna a kasan kafet tana mai jingina kanta jikin bango. Haka kawai ta tsinci kanta da murmusawa. Wani sanyi ya doki zuciyarta. Ta tabbatarwa kanta akwai wani abu a ranta game da Faruk, tafi danganta abin da kauna ta don Allah irin wacce ta ke yiwa Antinta Amina, haka kawai Faruk ke burgeta. ‘Kodai kina sonshi?’ Gabanta ya fadi jin tambayar da ya darsu a zuciyarta. Ta zaro ido kamar wani na ganinta. ‘Ina ni ina Yaya Faruk? Ai ko zan so wani na gwammace ya kasance cikib samari masu takuramin a hanyar makaranta da dai son abinda bazan ta6a samu ba.’ Ta ayyana a ranta, tunaninta ya katse sa’ilin da ta ji Fahad ya kwalamata kira. A kofar dakin sukayi kici6us, ya sanarmata wai ta zo ta k’aro faranti su Yaya Faruk zasu ci abinci. Ta amsa da to, a sanyaye ta gyara daurin dankwalin atamfarta sannan ta bi bayansa. A zaune ta gansu a saman tebur gaba daya, ta dauke kanta ganin shi dinma gogan idanunsa akanta suke, kicin din ta fad’a ta bi umarnin Mami. Ta dauraye ta goge sannan ta karasa garesu cikin sassanyar tafiyarta, sam bata da kwaramniya…